Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 9
Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 9: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 9. Abubuwa sun yi sauƙi sosai dana baro wannan gida na dawo…
4,038 words
Abubuwa sun yi sauƙi sosai dana baro wannan gida na dawo Malam madori. Ga magungunana dasu na tawo da rubutuna da dai komai. Wallahi tunda na dawo ban sake wani ciwo ba face na laulayi. Ƴan uwana naga soyayya maɗaukakiya a wajensu ko da yaushe cikin sintirin zuwa dubani suke yi. Da lokacin aikin Hajji yayi aka maye kujerata da Hauwa suka tafi suka je suka sauke farali suka dawo. Alhaji Zaidu Maigogul yana faɗamun irin damuwar da yake ciki sosai akan rashin ganina ko rashin waya dani. Amman ko da yaushe a cikin hidima dani yake a haka a haka har cikina ya isa haihuwa ranar monday na wayi gari da naƙuda zanga_ zanga su Adama suka rufu a kaina. "Allah ya raba lafiya. Aisha kirawo wayar Maigogul yace data soma naƙuda komai dare a kirashi" Cewar Rahama dake riƙe dani, ni kuma sai zufa nake haɓakawa. Ai cikin hukuncin Ubangiji kafin awa uku na haifo yarinyata mace ƙatuwar gaske lafiyayya kuma tana faɗowa ta fashe da kuka inya_inya. A hankali wata iska ta soma kaɗamun illahirin jikina sai nake jin tamkar an saukemun dala da gwauron dutse a kaina wallahi. Nayi lamo ina kallon Rahama na yanke ma yarinya cibi Adama kuma tana saka mahaifa a leda, Aisha na ƙoƙarin tattare leda da zanin da aka shinfiɗamun. "Lolo Allah mai iko wannan yarinya zata ga gata irin wanda sai an yi mamaki. Allah sarki Alhaji Zaidu ko wanne irin farin ciki zai yi sai Allah. Murmushi nayi nace. Alhamdulillahi Rahama nagode Allah ya yasa yarinyarnan ta fito lafiya kuma da ranta gata lafiyayya. Kishiyar Adama ce ta leƙo tace. "Kaddai mai ciki ce ta haihu Adama. Muna aikace aikace sai muka ji kukan jariri? " "Eh wallahi Hafsatu itace ta haihu ta samu mace" "Ah Allah sarki Allah ya raya ya inganta lafiya" Rahama tace. "Adama dubo ruwan wankan da kuka ɗaura in yayi lolo tayi wanka taji daɗin jikinta" Ai kuwa nan da nan aka juye mun ruwa na shiga banɗaki na dinga dukan jikina da ganyen runhu ina jin wani daɗi. A bayan gidannan kafin in gama wanka naci kuka naci kuka kamar me na farin ciki da godema Allah kafin na fito. Ai kuwa takalman su Rakiya da Maigogul na gani. A hankali na shiga yarinyar tana hannun Maigogul ya rungumeta tana nannaɗe a cikin bargon farin seti na kausar. "Sabuwa ashe Allah ya nufa har kin sauka? Ga yarinya mai kama da mahaifinta masha Allah. Ko jiya sai da shi Alhajin yazo ya duba su kayi nayi ya kawo kayan abinci. Dake ma Goggonshi Amfana ta rasu da ƙanin mahaifinshi Kawu Abdullahi tsiransu kwana ɗaya rak." Zama nayi a kusa da Hauwa nace. Allah sarki tsohuwar arziki Allah ya kai haske kabarinta ya gafarta musu baki ɗaya. Lallai Alhaji yayi rashi sosai. To Maigogul wanne suna za'a saka ma yarinyar sunan mahaifiyarshi ko sunan Goggon? " Maigogul yace. "Ni ina ganin ki saka mata sunan Goggon tunda ita kika sani kuma ta soki sosai kuma tana da amana kamar ba kishiyar uwaba, ba irinsu Hauwa bane da ana binsu da Alkhairi suna bin mutum da sharri ba. Zanyi mata huɗuba da sunanta in sha Allah. Sai ki shirya kuna haɗe arba'in zaki koma ɗakin mijinki" Murmushi kawai nayi. Akaima yarinya huɗuba da sunan Goggo Amfana wato Hajara. Farfesu Adama ta kawo mun da shayi mai kauri naci na ƙoshi Maogogul ya ɗaukeni ni da Rahama ya kaimu asibiti a can Dutse aka duba lafiyata da lafiyar yarinya. Ananne likita tace ai na ƙaru sai an yi mun ɗinki. Ai kuwa haka akaimun ɗinkinnan Maigogul ya tasomu a gaba muka dawo. Ɗakin Adama cike da dangi suna ta cin jallof ɗin shinkafa da wake ta manja harda su Gaza da Sama da matansu duk sun tawo ɗaki dai shaƙe da mutane. "Lolo sannu ashe Allah yayi yarinya eh ta shaƙi iskar duniya? Shekaranjiya muka dawo daga kwatano, jiya kuma Alhaji yace in dawo Dutse in duba su Rakiya ƙarama wallahi. Baki ganshi ba duk ya fita hayyacinshi wallahi lissafinshi ya kunce. Kinsan fa yayi jinya kusan watanshi ɗaya a asibiti lokacin da asirin matarshi ya tuno ya gane duk ita take ɗaurama yaran da eh ya aura ciwo. To shine da ya kamata ya tabbatar da hakan yaita jinya a asibiti" Hawayena na share nace. Kuma yanzu ita Hajiyan tana ina? " "Tuni ya eh saketa fa. Maigogul yafa san komai bai eh faɗa muku ba ashe? " Maigogul yace. "To dama na bari ta haihu ne inta samu nutsuwa sai taji dukkan abinda ke wakana" Nayi mamaki sosai, sannan ko babu komai naji farin ciki da Hajiya munubiya ta fita a rayuwar Alhaji Zaidu. Ni dai bazan iya yafe mata akan halin da ta jefani ba abadan. Haka mukaita zaman jego ni da ƴan uwana mata ko da yaushe suna tare dani su suke mun komai. Ana gobe suna sai ga Maigogul da ƙatin ƙatin ɗin tumakai har biyu da kayan abinci him sun tawo da Hajiya Balaraba. Ranar suna matan ƙauyen malam madori ne suka zo suka taya mu suna. Ni dai sai sharar hawaye nake yi ina tuno wannan sunan da ace a gidan Alhaji Zaidu akayishi irin hidimar da za'ayi bana wasa bane irin taron da za'ayi shima bana wasa bane gaskiya. Allah sarki haka ƙaddarar tazo a rubuce abu mai mahimmanci shine Alhaji Zaidu Allah ya nufa zai ga jininshi a duniya kafin ya mutu. A haka taron suna ya watse lami lafiya. Washegari kuma suka tashi da suyan nama gida duk ya kaure da ƙamshi tako ta ina. Ni dai ina daga ɗaki an zubo mun nama mai zafi ina dankwalar namannan da yajin daddawa ina korawa da kunun kanwa lafiyayye. Jego nake yi mai daɗi inci in sha in yi wanka in yi kwanciyata ƴan uwana zasu yi mun komai. Hajara kullum tana hannunsu suna lelenta ko kuma tana bayan Rahama. A zamanmu a Malam madori ƙanin mijin Adama ya ƙyalla idanu akan Rahama ya ga farar fata sai ya turo wanshi akan shi fa yana so. A lokacin shekarar matarshi ɗaya da rasuwa ta barshi da yara tara da cikin na goma Allah ya amshi abunshi. Rahama tayi na'am dashi harma an saka ranar biki. Gidansu jere yake da gidan Adama, manomine sosai yana da arziki irin na ƙauye babu laifi sai dai fa riƙon yara masu yawa haka ba abu bane mai sauƙi. Amman kuma dake mafaka Rahama take nema tuni ta yadda zata riƙe yarannan ta kama sana'a da zata dogara da kanta kamar yadda Adama Allah ya albarkacin kasuwancinta hakama Labbai gashi Allah ya taimaki Labbai cicib ya daina daudu sai dai muryarshi bata dawo sak ta maza ba abune ma mai wuya gaskiya. Haka tafiyar tashi sai a hankali yana dai ƙoƙartawa. Ga fuskarshi tayi duhu sosai kamar mutum ya saɓule ya warke haka fuskarshi wallahi ta zama abun tausayi sai sai yana shafa man kaɗanya ance zai rage mishi wannan ƙonewar. Ana gobe zamu yi arba'in muka tarkato Maigogul ya dawo damu Dutse muka ya da zango a gida. Naga Sama sana'arshi ta shagon saida su biskit siga madara abun babu laifi wuni yake yi a shago yana ciniki babu laifi, magazin shima Allah ya kawo mishi tashi shiriyar mahauta yake bi yana sana'ar nama harma ya samu teburi a wata ƴar kasuwa anan yake saida nama. Kuma babu laifi yace a rana yana siyar da kaso ɗaya bisa takwas na naman balamar saniya. Ma'aru ma yana dako a kasuwa amman Masa'u gaskiya kamar ya haukace kawai gaskiya babu ragowar hankali a tattare dashi sam. Washegari muka yi arba'in a ranar Maigogul ya kira Alhaji Zaidu yake shaida mishi mun dawo daga gidan magani zai iya zuwa ya dubani jiki yayi sauƙi fes. Ina zaune ina ba Hajara Mama sai ga Maigogul ya leƙo ina kan gadon Rakiya su basanan sun tafi islamiyya. "Lolo yau ki shirya tarbar mijinki na sanar dashi kun dawo. Nasan nan da awa huɗu zaki ganshi baki ji yadda yake kabbaraba.. Sai ki yima Hajara kwalliya tayi kyau taita ƙamshi yau dai ubanta zai gana da'ita. Yau Alhaji Zaidu zaiji ɗumin kininshi. Nasan dai naci kujerar makka ko kyautar ƙaton gida a Kano wallahi. Ina da burin in kwashe su Kayi nayi mu koma Kano dukka da zama nagaji da sunturi kuma hakanne zai tilasta mata barin kayi nayinta tunda anyi magiyar duniya taƙi ta dena. Kano yadda take da faɗi kafin a saba da mutane ma ai kinga aikine. Maza a shirya Hajara, kiyi mai liyafar abinci ga kaji can na siyo miki" Murmushi nayi idanuna cike da hawaye wallahi ina matuƙar son Maigogul komanshi kuma burgeni yake yi sosai. Gashi da tunani da hangen nesa ba kamar Kayi nayi yadda take nuna adankiya a kanmu ba. Ai kuwa nan na bar Aisha suna zaɓama Hajara kayan sakawa ni kuma na wuce Kitchen na wanke kajinnan na ɗaura tafashensu bayan nasa ɗanɗano da kayan ƙamshi. Risho na kunna na ɗaura tuwon shinkafa. Miyar ganye nayi mishi da kaji gundun gundun ga lafiyayyen tuwona na tuƙeshi sosai. Labbai kuma na barta tana gyaran falo har an bunka mishi turaren wuta. Ina banɗaki ina wanka Alhaji Zaidu ya iso yana zaune a falo. Ina jiyoshi yana ta faman gaisawa da su Adama. A gurguje na fito ko kwalliyar hoda kawai da kwalli na shafa na zura doguwar rigar leshi banko ɗaura ɗankwaliba dama shekaranjiya Sadiya ta yanyaramun kitson yin arba'in. Maigogul ne ya leƙo yace. "Lolo ki kintsa zai shigo ciki kawai ku zanta" Kai kawai na ɗaga mishi. Ina tsaye ina murza kulaccham da Hajiya Balaraba ta kawo mun tun ranar suna na wajen mrs bukhari sai kawai naji ya shigo da sallama. Da sauri na juyo yana tsaye a tsakiyar ɗakin saye da waganbari mai ruwan ƙasa ɗinkin malum_malum kanshi saye da wata zanna bukhar ɗin da ɗaiɗaikun gidane babu irinta. Kun ganeta nai kala kala a jiki layi layi to itace a kanshi. Ya ƙuramun idanu ƙur yana mun lafiyayyen murmushinshi wanda nayi kewa sosai. Hannayenshi ya buɗemun yana kirana. A hankali a hankali na tattako har inda yake na shige jikinshi ya matseni tsam mukaita sauke ajjiyar zuchiyar haɓarshi na ajjiye a tsakiyar kaina. Mun jima a haka sosai sai nayi yinƙurin zamewa sai yayi sauri ya mayar dani jikinshi. Naga yayi rama sosai gaskiya. Da ƙyar na zame jikina na zaunar dashi a kan katifa hannunshi riƙe da nawa. "Wazirat al sa'ada barkanki da dawowa cikin rayuwata. A kan tafiyarki naje aikin Hajji, naje umara duk ina roƙon Allah ya baki lafiya ki dawo mu gudanar da sabuwar rayuwar da babu takura a cikinta. Wazirat haƙiƙa ke wani ɓarayine na jikina. Zo ki zauna in shaƙi ɗuminki mai cakuɗe da ƙamshi." Dole na dawo kusa dashi na zauna muka sakarma juna murmushi na kewa da son keɓewa. Wata kalma mai tsada ya raɗamun ƙasa_ƙasa. Idanuna na rufe tsabar yadda naji kunya ta kamani. To yanzu dai bari in kawo maka ruwa da abinci ni da kaina zan ciyar dakai" Ina yinƙurin tashi ya cabkeni carab. "Ba ƙi nayi ba tunda nayi kewar duk abinda ya fito daga gareki. Amman ki barni in zauna dake mu zanta wazirat. Yaufa sai dai Alhaji Baba yace banda kunya dan da matata zan tafi ko a bani ɗaki a gidannan." Ai kafin in yi magana sai ga Maigogul ya shigo hannunshi riƙe da jaririya tana ta kuka kamar ranta zai fita. "Lolo ga Goggo Amfana bata mamma tasha ta ishi mutane da kukan banza" Ya dire mun yarinyar ya fice. Da mamaki da tsoro duk sun bayyana a fuskar Alhaji Zaidu har ja da baya yayi. Murya na sauke Omri kada kaji tsoro kada ka tayar da hankalinka. Kaga wannan yarinyar? To jininka ce ɗiyarka ce fid duniya wal akira da cikinta muka baro gidanka watanta huɗu a marata lokacin " Wallahi sai ga babban mutum ya fashe da kuka ya durƙusa yana ambaton Allah da ƙarfi. Hajara na miƙa mishi ya ƙanƙame yana ta ambaton Allah kawai. Maigogul ne ya faɗo kunsan halinshi ai mai makon yayi kamar baiji ba. Yana shigowa Alhaji Zaidu ya miƙe ya rumgemeshi Hajara na tsakiyarsu. "Hakane wannan yarinya taka ce in baka amince ba aje ayo gwajin jini. Na raɗa mata suna Hajara marigayiya Goggo Amfana. An yanka mata manyan tumakai an ciyar da Sabuwa da kyau. Mun yi hakanne sabida gudun cutarwar makirar matarka ta da ba sabida komai ba" Yana kaiwa nan ya fita. Alhaji Zaidu ya zuba ma Hajara idanu tana ta mutsu mutsu ta dena ma kukan sai wasa take yi da ƙafarta. Dariya yake yi yace. "Wazirat nagode da wannan irin tukuicin da kika bani. Haƙiƙa yau ranace marar misaltuwa. Ranace da ba zata goge a cikin rayuwata ba abadan. Wazirat ina sonki ina mutuwar son Goggona. Ya mayar da idanunshi kan Hajara data soma kukan yinwa. Dole ya kawota ya ɗaura a cinyata. "Bata tasha in gani ji nake yi kamar mafarki wallahi" Dariya nayi mishi na zaro mama na saka a bakin Hajara ta kama ta shiga tsotso shi kuma yana share hawaye. Wallahi cikin abinda yayi ƙasa da awa guda duk wata number dake wayarshi saida ya kira ya faɗama an mishi haihuwa akwai suna a gidanshi rana ita yau. Danginshi kuwa labari ya ishe musu family ya kacame da farin ciki da ta'ajibi. Ya zauna yaci abinci wallahi ya kasa har saida na dena dariya yaga dai fishi nake yi da gasken gaske shine ya zaune a hakanma Hajara na hannunshi. Abincin na zuba mishi na karɓi yarinyar na tusa shi gaba na dinga bashi da kaina. Da ƙyar yaci tuwo rabi yace shi ya ƙoshi ya karɓe yarinyar yanata kallo. "Wazirat kuma kamarmu ɗaya da'ita da gaskene munje asibitoci da dama domin a duba lafiyarmu domin musan menene matsalarmu na dangane da rashin haihuwa. Ƙwararrun likitoci sun tabbatar mana dukkanmu lafiyarmu ƙalau kawai Allah bai yi lokacin samuwar cikin bane. Munji a wajen likitoci fin goma ba'a najeriya ba. Da wannan dalili Munubiya ta dinga cutar da yaran da basu ji ba basu gani ba. Bari in baki labarin abinda ya faru. Zuwa nayi zan duba Goggona ance mun ta samu farkawa harma tace inzo lallai tana son ganina. Bayan na shiga ne take sanar dani. "Zaidu duk wani bincike da bin diddigi da zaka yi akan matarka kayi. Ita ke ɗaurama matanka da kake Aure ciwo. Zargina ya tabbata itace. Ka nutsu kabi kuma komai a hankali ka gano da kanka. Kada kayi mata hukunci da abinda bai tabbata. Amman ni na tabbatar maka tasan abinda yake gudana. Kada ka sake a wannan karon ka rabu da matarka ko me zai faru kar ka rabu da'ita" Hankalina a tashe nace. "Goggo kika ce tana da sa fa hannu a wannan abubbuwa da suke ta faruwa? Naga Munubiya macace mai kirki gata da biyayya" "Kai namiji ne ba lalle ka gane makircin mata ba. Bare taka tana yin makircin da wata siga ta daban. Ka zauna kayi tsam kai da kanka zaka iya rabe ɗayan biyu" Shiru nayi na bita da to sabida bana jayayya da manya. Amman ba dan zuchiyata ta yarda ɗari bisa ɗari ba. Har saida na taso a tsakankanin Rano zuwa Kano na dinga tunani game da tubka da warwarar al'amura masu dama. Sai naji ƙirjina yayi mun nauyi sosai. Bayan mun rabu daku kun tafi wazirat na shiga damuwa mai yawa. Sai Alhaji Muntada ne ya tuƙani ya kaini gida. Hajiya na zaune da ƙawayenta aikinsu kenan lissafin kuɗi na haura sama Ban jima da hawa ba ta biyoni. "King lafiya wannan damuwa haka, ko wani abunne ya faru da Sabuwane? " Saina kalleta nace. Iyayenta ne suka ɗauketa suka tafi da'ita sunce ma in aiko musu da takaddarta" Nayi tsam ina kallonta. Wallahi tama kasa danne dariyarta saida ta dara kaɗan fuskarta cike da annuri can ta lulluɓe da damuwar yaudara. "To kai wanne matakin kake ganin zaka ɗauka? " Sai nayi tunani Hajiya yanzu kaɗaici nake so ki koma wajen ƙawayenki" Hmmm wallahi data sauka sai ta jasu zuwa uwarɗakinta. Ni kuma saina sakko nazo na tsaya a ƙofar ɗakin. Abubuwan da naji basa faɗuwa hatta ni ba tsira nayi ba ƙarfin adda'ane yake riƙe dani kawai. To tun daga ranar na soma bin diddiginta har wajen bokan da suke zuwa a wudil saida na bisu na tambayi mutanen da suke kusa da wajen me akeyi a gidan dana ga mata nata shiga. "Wannan gidan ai gidan wani ƙaton matsafine matan da suka kwashe kayansu ne suke zuwa wajenshi. Sai kuma masu neman duniya wato mulki." Wazirat ko dana dawo na soma bincike ɗakin Hajiya da ɗakina na fitar da layu sunfi ashirin. Harda wata ƙwarya ina buɗewa wallahi ƙwaryar ta soma hayaƙi. Mutum ne aka zanashi da tawada a jikin ƙoƙon aka bi ƙwaryar aka zaneta da sunana da aka rubuta da ajami. Sai wani kwaɗo da mabuɗi da jan zare zagaye dashi. Na tattaro komai na kaisu sama na kira Hauwa na tutsiyeta tare da mata alƙawarin kuɗi masu tsoka. Kusan Hauwa ita Hajiya take ba aikin duk matana dana Aura a baya. Ita ke shiga ta saka laya, ko ta ɗakko suturunsu da makamantan haka. Da Hauwa da mijinta na basu kuɗi masu yawa na sallamesu. Hajiya sai wajajen taran dare ta dawo tazo ta same ni a sama a gaban waɗannan kayan. Bayan na kirawo wana yazo ya gani da ƙanin mahaifinmu. Tana ganin kayan Wazirat sai Hajiya ta soma kuka ta tuba in yafe mata tasan shikenan alkadarinta ya karye ƙarshenta yazo. In yi magana na kasa sabida yadda na kaɗu takaddar saki biyu na iya miƙa mata. Kinsan Allah kamar yadda ta fita nima sai ƴan uwanane suka zo suka fitar dani zuwa asibiti? Hajiya ta cutar dani cuta mai girma. Amman mun barta da mahaliccinmu shi yasan yadda zai yi da'ita KO? ." Gaskiya ne Hajiya ai shaiɗaniyace" Nan na bashi labarin dalilin barina gidan da dalilin farkon ciwona. "Bazan yi mamaki ba a yanzu da ace a lokacin ne kika faɗamun bazanma iya saurarenki ba" Mun yi hira sosai da sosai. Ko da zasu tafi sallah Maigogul yace in haɗa kayana zamu tafi harda su Sadiya za'aje ayi bikin suna. Ai kuwa tare duk muka rankaya harda su Adama. Sabon gida ya kaini an zuba komai da komai. Acan muka tarar da kafatanin danginshi na Rano ƴan wasu garinne kaɗai babu. Sun yi abinci jiranmu kawai akeyi. Ai kuwa muna shigowa gida ya kacame da murna ranar Hajara ta sha wahala sosai dan da daddare saida Adama ta mata wanka da ruwa zazzafa ta sha ɗauka da addu'o'i. Tunfa daga ranar jama'a sukaita tururuwar zuwa dubamu. Matan abokai ma bafa a barsu a baya ba. Yadda gidan ya ɗinke da dangin Alhaji da nawa wallahi ko keɓewa mun kasa yi sai dai Alhaji ya haɗiye ƙishin ruwanshi. Anata shirye_shiryen suna fa kuɗi yake kashewa kamar baya so Abincin sunan ma wai ma'aikatan hotel ne zasu zo suyi. Maigogul shima yace zai yi dake yaga harda maza a ma'aikatan sai ya zamana shi yake gyara musu in yaga sun kuskure yaci riga da hular girki abunshi. Ranar sunannan bazai rubutu ba wani abun ma wallahi sai ace ƙaryane amman Alhaji ya nuna bajintarshi akaina da Hajara ta ɓangaren suturu da kadara. Saniya ƙatuwar gaske su Gaza suka yanka ga tumakai wallahi har guda biyar aka yanka. Banda kaji. Suturu kuwa mun sameshi ni da Hajara ta ɓangaren dangin Alhaji dama nawa dangin kowa burinshi yayi ma Alhaji abun bajintar da zaiji daɗi. Ni yama rasa kyautar da zaiyi mun. Yace dai washegarin suna zamu wuce Dubai muje mu ci Amarci. Ai kuwa washegarin suna tun asuba su Adama da Anty Tani sukaita kasafta nama da su cincin na suna aka warema kowa nashi suka gyara mun ko'ina kafin azahar duk suka watse mu kuma wajajen bayan la'asar aka kaimu Airport ƙarfe bakwai jirginmu ya ɗaga zuwa Dubai. "Sannu wazirat masu suna sun hanani more matata sai dai inta kallonki ina haɗiye yawu uhm. Da fatan kin shirya Amarci da kuma bani hakkina da kyau ko? " Idanuna a lumshe dan nayi muguwar gajiya nayi tulus nace. Raina fansa gareka Omri sai yadda kayi dani" Murmushi yayi mun ya dubi Hajara dake ta baccinta ranta ɗaya yace. "Baiwar Allah ita bata ma san wacece ita ba. Bata san irin so da gatan dake jiranta daga wajen dangi zuwa wajen iyayenta ba uhm rayuwa kenan wai yau ni Zaidu wannan ce ɗiyata? Sai dai kash ba lallai inga girmanta ba yadda ya kamata ba. Amman ina roƙon Allah yayi mun tsayin ran da zan ɗauki ɗiyar Hajara da hannuna nima inga jikina" Allah ya amsa mana Omrina bana son maganar mutuwa sabida ita kaɗaice zata iya rabamu." Murmushi kawai yayi mun nima na mayar mishi. Ƙarfe huɗun asuba gari bai waye ba muka shiga Dubai. Kafin dai Asuba har mun yada zango a ɗakin hotel da muka kama. A Dubai muka gudanar da asalin rayuwar Aure mara algus a ciki. A nanne muka fahimci junanmu sosai da sosai, nan na ga soyayya ido da ido a baya ashe ba'ayi komai ba yanzu ne dai akeyi. Satinmu uku a Dubai muka wuce Saudiyya muka yi Umara saida muka gama aiki kafin muka ziyarci su Maman Yasmin sun kuwa ji daɗi sosai muma ziyarar tayi mana daɗi sosai. Sannan kuma muka shiga Madina wajensu Mardiyya da Sauban. Nayi farin cikin ganinta cikin kwanciyar hankali. Ta sake girma kamanninta da Babanta ya sake fitowa sosai. Abubuwan Alkhairin da Alhaji yaima Ahalina ba'a magana barinma Maigogul daya yi sama da faɗi da kaso mafi tsoka. Maigogul yana da tangamemen shagonshi na saida yadukan maza da ɗinkakkun kayan maza dama Hajiya ta buɗe mishi. Alhaji Zaidu kuma ya narka kuɗinshi wajen ƙarama Maigogul da takalman maza, agoguna, gogul, da hulunan maza zanna, da irin links ɗinnan. Shagon Maigogul abun sha'awane kayane masu tsadar gaske yake saidawa hakan yasa masu kuɗi kaɗai ke iya ziyartar shagon nashi. Samfurin ɗinki kuwa sai dai a gani a wajenshi kuma kun sani. Daga Saudiya na roƙeshi inaso ya kaini wajen Uzairu zuchiyata. Ai kuwa ya amince muka wuce Canada. Hahahahhh mutuminku ya samu duniya wallahi ya sake kyau. Fatarshi ta sake wani irin laushi da kwanciya. Munje mun tadda Felisha da cikinta ƙurbibi. "Uzairu Zuchiyata an samu duniya ka manta da hanyar najeriya" Na faɗa ina tsokanarshi. "Ka ganta ko Alhaji ta rainani wannan yarinyar. To me akeyi a najeriya tunda dai ana tura kuɗi ai shikenan. Kuma na ɗaura Gaza shi ke kula mun da gini da nake yi. Ni ko Lolo ina Rahine" Dariya muka yi dukkanmu. Suma naga da ƙaton karensu suke rayuwa da magensu mai kyau. "Amman Uzairu ya yanayin zaman auren babu matsala ko? " Alhaji ya tambayeshi. "Matsaloli ai sunfi dubu hamsin wallahi, ai ni shigo_shigo ba zurfi tayi mun. Kaga ko shekaranjiya saida tace zata sakeni wai ita ta gaji sabida ina nuna duk inda zata shiga saina rakata. Ya mata da aure zata shirya tsirara ta tafi gidan rawa? Wallahi lauyanta ne yayi mun iyaka da son takura mata. Nima wallahi so nake mu rabu Auren turawa matsiyata ko wahala. Abinda nake ji abinda ke cikinta ne. In muka rabu fa ko yara nawa muka haifa dole in barsu a hannunta shikenan sai su zama arna. Duk da ko inanan ɗin bani da iko a kansu kaico. Ai wallahi Alhaji kwaɗayi da son zuchiya baiyi ba. Ana zaman haƙuri da nadama dai" Ni ko dariya kamar zan mutu wallah. Ai dama ance in da kwaɗayi da wulaƙanci. Satinmu ɗaya a Canada muka dawo gida Najeriya ƴan uwa da abokan arziki sukaita tururuwar zuwa yi mana sannu da zuwa da duba Hajara. Na zama sita a cikin familina da familin Alhaji kowa so yake ace nice ta kusa dashi. Ashe muna tafiya Dubai su Rakiya suka dawo Kano da zama gidansu na BADAWA Ko da naje gidan naga yadda suke more rayuwa na tuno rayuwarmu ta baya a ɗaki falle ɗaya duk aka haifemu kana a wannan ɗakin duk muka rayu muka girma Allah al hakim. Gaga_gaga al'amura sukaita faruwa kwanaki, watanni, shekaru sukaita shuɗewa. Bayan wasu shekaru. Mrs BUKHARI [10/29, 9:31 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 11