Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 10

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 10

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 10: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 10. Yau dai tun safe nake shiri gida nake son zuwa naje na…

4,893 words

Yau dai tun safe nake shiri gida nake son zuwa naje na wuni. Jiya da yamma su Rahama dasu Labbai suke faɗa mun sun zo gida shine nima nake son ayi hirar dani. Fitowa nayi na tadda Omri a zaune yana lallatsa na'ura Hajara na gefenshi tana aikin da aka bata a makaranta. "Ranki shi daɗe irin wannan kwalliya duk tasu Yaya Rahaman ce? " Zama nayi ina murmushi nace. Goggona je ki ɗakko mayafinki zamu je gida" Dariya tayi ta tafi a guje ta je ta ɗakko mayafi da takalmi. "Kin ganta sai zumuɗi take yi zata je gidansu Mamanta" Ai kasan zumuɗinnan duk na Maigogul ne. Sabida tana cin daɗi a wajenshi ai shiyasa" Wata hararar soyayya yayi mun nayi saurin kama bakina nace. Aimun Afuwa Alhaji Baba Dad" Dariya muka yi dukkanmu. Ya miƙe ya sako malum_malum ɗinshi ya kara hula muka fito harabar gidan tare. "Mamana inna taso office zan biyo ta gidan sai mu dawo tare ko? Ki gaishe da su Mama da Alhaji Baba" "To Abba sai ka dawo Allah ya tsare" Bayan motata ta shige mu kuma muna tsaye. "Akwai abinda kike buƙatane kuma Wazirat? " A_a kayan abincin tun ɗazu nasa Amina ta saka a bayan mota, kuma akwai kuɗi a hannuna Omri" "To shikenan sai nazo Ƴar budurwata. Ni naga kin sake kyau da haske anya kuwa ba ajjiyata bace a jikinki ba ki gayan gaskiya" Dariya nayi mishi kawai na shige mota maigadi ya buɗe mana get muka fice a jere har muka zo iyakar inda zamu rabu, yayi mun hon ya wuce mu kuma muka miƙe. Ina riƙe da sitiyarin mota ina wasa dashi a titi ina nishaɗi tare da tuno Sabuwar da data yanzu. Ni kaina wasu abubuwan inna tuno wallahi illahirin kunya ce ke kamani. Aminu ne yayo kirana. Aminu ya dai sarkin kiran waya kenan? " Daga cikin wayar yace. "Ummi yaushe zaki sake zuwa jikin Baba malam ya sake tsananta yanzu haka ma an fito dashi za'a mayar dashi asibiti ne? " Subhanallahi jikin sake tashi yayi Aminu? Dama jibi Abban Hajara yace zamu sake zuwa mu duba jikin. In kaje asibitin ka samu ka haɗani da Malama Ƙarama a waya. Kuyi ta yi mishi adda'a jibi sassafe zamu kamo hanya kaji Aminuna? " "To shikenan ummin mu Allah ya kawo ku lafiya a gaishe mun da Goggo" Goggo zata ji zan turo maka da ɗan na kashewa inna tsaya zanje gidansu Rakiya ne" Da haka mukai sallama ina hango fuskar wannan Dattijon arzki mai abun mamaki. Ina roƙon Allah yayi yaye mishi. A haka muka isa gida muka taddasu sai lokacin suke karyawa anata dariya ana musu. Maigogul ke soya musu doya anata juyewa a ƙaton tire ana ci ga miyar ƙwai ga shayi ya sha madara. "Ga Goggo ga Goggo. Zo taho ƴar nema" Cewar Maigogul Hajara taje ta ruƙunƙume Maigogul suna dariya. Rakiya taja tsaki tace. "Aikin banza kai Allah ya shirya Maigogul zanga sanda in yananan zai bari inyi daraja" Taɓata nayi nace. Haba Rakiya dan Allah ki dena kallon wannan abun a rashin daraja. Mufa muna sonku dukkanku a yadda kuke" Tace. "Amman da zaɓe za'ace za'ayi ai da gudu ko wacce zata sunkuceshi ko? Allah dai ya bamu lafiya. Ya shi Alhajin yake? " Lafiya lau yace a gaisheku kayan abinci yana bayan mota ma" Saita washare bakinta. Nan muka hau gaggaisawa Maigogul har Kitchen na bishi muka gaisa yau shi yayi musu karin kumallo a gidan ma Allah sarki ya sake tsufa furfura ta sake rufe mishi ragowar baƙin gashin nashi. Dawowa nayi cikin su Adama muka buɗe hira sabuwa. Adama tayi kyau ta sake haɓaka ƙiba. Rahama goyo ne ma a bayanta na ɗa namiji wata takwas. Su Aisha Sadiya duk suna gidajen Aurensu zuwa dai ko wacce tayi daga gidan nata mijin. Su kuma su Adama sai suka biya ma Labbai suka tawo. Gaza ya zama mutum sai dai muryarshi da zubinshi bazai taɓa eh canjawa ba yananan a yadda kuka sanshi, sigarinma yana ɗan sha gaskiya har yanzu. Sama ma babu laifi ƙazanta ta ragu sosai yaranshi biyu, Gaza ma yaranshi biyu Anyi ma Maigogul takwara ba don son ranshi ba sai dan son ran Madamcy dan shi yana takaicin irin kamannin ma da Rakiya ƙarama tayi da Maigogul. Bayan da aka gama karyawa sai muka shiga gyaran gidan masu wanke_wanke nayi masu shara nayi nan da nan muka kammala komai. Lokacin sha biyu tayi Maigogul ya fito tare da Hajara zasu tafi shago. Ya ci malum malum na wani yadin maza mai mugun kyau kayan gasu da ɗaukar guga gaskiya yayi kyau. Miƙewa nayi nakai mishi kuɗinshi na duk wata da nake basu. Bakinshi a washe ya amsa shima fa a ƙadamin da ake Maigogul da kuɗinshi amman baya raina wanda zai kuma samu. Rakiya tace. "Ai sai ka bada na cefane tunda dai ka samu kuɗi" Maigogul yace. "Rakiya ho kullum na cefanannan ina fa bayarwa yanzu ai ba da bane" Kuɗi ya ƙirga ya bata abun mamaki ohh rayuwa kenan. Maigogul yayi mana sallama shi ya tafi kasuwa tare da Hajara dan fafau taƙi zama dama ita da Maigogul babu dama ne. Muna Kitchen muna girki nake tambayar Labbai ya man ƙuli. "Ai wallahi man ƙuli sai dai ace masha Allah jari ya haɓaka ya zama babba. Cicib ma a wajena yake siyan tunkuza da ita yake gashin tsiren dare da yake yi. Kinsan sana'ar daya koma kenan. Da rana zuwa yamma yana toya doya da kwai da kaza a wajen da daddare sai ya gasa tsire da masa ana ciniki wallahi babu laifi." Adama tace. Ni da nake da shagon kayan kwalliya da su turare ba'a cewa komai ina ciniki sosai. Babu ruwana da tenshon da sassafe nake ficewata a shago nake karyawa naci daɗi ranar girkina kuma akwai wata ƴar budurwa da take zama mun a shagon. Ga Rahama itama sana'ar turaren wuta ya karɓeta sosai wallahi ai babu abinda zamu ce dake wallahi. Su Sadiya ma anata kitso da ƙunshi da kwalliya, babu laifi gidanta baya rabo da mata. Aisha ma tana taɓa ɗinkin kowa dai na kan sana'arshi." Sallama muka jiyo kamar muryar Uzairu zuchiyata a falo. Ai kuwa sai muka ji Rakiya tace. "Uzairu zuchiyata kaine haka bagatatan? " Duk sai muka fito Uzairu zuchiyata na tsaye da gajeren wando da riga amles ga akwatuna manya shaƙe da kaya. Suna haɗa idanu da Labbai ai sai suka soma dariya Uzairu zuchiyata harda birgima a ƙasa. Wallahi sabida mugunta har hawaye suke yi. Muma duk dariyar muke ta faman yi a haka Hauwa ta shigo da jakarta taci riga da wando da hijabi na makaranta abinta Rakiya ma shine a jikinta. "A_a dan jakar uba daga zuwa sai dariya" Cewar Hauwa itama dariyar take yi. Rakiya da abin ya isheta tace. "Aikin banza Rahama mu zamu fita zamu je gidan suna daga can zamu wuce islamiyya mu sai mun dawo. Muje Hauwa ko gulma zaki tsaya ji" Suka fice Rakiya na zage_zage. "Ni naga bariki Labbai Auren turawa ko bala'i da masifa. Tsiya tsiya muka rabu ta sake ni dai kuma na saku na rabu da ƙaƙai. Ƙyal ƙyal ƙyal" Muka sake ɗaura dariya kamar cikina zai ƙulle. Labbai na hawaye tace. "Garin yaya aka sakoka Uzairu zuchiyata. Ni na ɗauka iya wuya zaka yi biyayya ai? " "Me inji akuya? Na sha gashi fa Labbai ai ni da auren dattijai inaga har abada wata ƴar budurwa zan samu in Aura kawai tunda na fita da fitata nayi gini na tawo da kuɗaɗe ai shikenan. Yarinyar da muka haifa ta mutu. Cikin dake jikinta ne fa ya ɓare mitsiyaciyar sai ga lauyanta wai bani da ƙashin arziki kawai ita mu rabu. Wallahi daga haka shikenan ta saka hannu nima na saka. Na kuma rubutama mitsiyaciya saki uku na islama. Ta dinga fashe fashen kaya tana shan giya tana amai. Ba shiri na bar gidan kada taje ta rataye kanta" Habawa me zamu yi ba dariya ba. Kiran wayar Aminu ne ya katsemun dariyar na shiga Kitchen na amsa wayar. "Ummi Allah yayi ma Baba malam rasuwa yanzunnan" Innalilliahi, wa'inna'ilaihil'raji'un" Kalmar da naita nanatawa kenan na fashe da kuka ina salati. Da sauri su Adama suka baibayeni nace. Baba malam ne Allah yayi mishi rasuwa. Ku shirya bari in kira Alhaji Zaidu yanzu zamu wuce Dutse" Ai kuwa kiranshi nayi yace to gashinan zuwa dashi shima za'aje. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso shi da Maigogul. Motarshi Ni da Adama da Rahama, muka shiga. Motata kuma Maigogul ne zai tuƙa Labbai da Uzairu zuchiyata ne suka shiga su Sadiya da Aisha a gida muka barsu. Ni dai muna tafe ina kuka Omri na rarrashina. Ga wayata sai kira akeyi na kasa ɗagawa sai Adama Omri ya miƙa ma wayar take amsawa su Mardiyya ne suke ta kira. Mutuwar wannan bawan Allah ta dokeni fiye da tunanin mai karatu wallahi. Da muka iso cikin unguwar, wallahi jama'a sun cika kafatanin unguwar ga motoci ma damƙam babu ma wajen ajjiye mota sai daga titi muka ajjiye motocinmu muka ratso mutane. Ƙofar gidan kuwa ba'a magana wallahi gidan ma ya gagara a shiga sai Aɗɗa'u ne ya jamu zuwa gidan Kawu Manga dan a lokacin ne ake ƙoƙarin fito da gawar a sallaceta. Allahu Akbar wannan bawan Allah yayi mutane sai yabon alkhairanshi da halayenshi nagari akeyi. Su Maigogul kuwa dasu aka sallaci gawar aka wuce maƙabarta duk dasu, sai da aka tafi maƙabarta ne muka samu damar shiga cikin gidan. Cike damƙam da mata anata koke_koken al'ada. Zubewa nayi a gaban su Malama sai kuka. Malama babba ce ta dafa ni tace. "Sai haƙuri Sabuwa ayi haƙuri. Sa'a kaita ɗakin su Aminu ita da ƴan uwanta su karɓi gaisuwar acan Mardiyya ma da ɗiyarta tana ciki" Sa'a ce ta ɗagani nabi bayanta, su Adama suka mara mun banya. Ina ji wata tana cewar. Uwargidan Babangida ce ta da uwar manyan yaranshi. A ɗakinsu Aminu na tadda su Hameeda da su Hala da Sumayya. Ƴar shuwa ma tana ciki idanun kowa jawur anci kuka an ƙoshi Mardiyya na zaune ɗiyarta na cinyarta a zaune. Da sallama muka shiga Sa'a tace Ƴar Shuwa ta sauka a bakin gado ta bani waje. Ɗingisa ƙafarta tayi ta sauka na zauna. Nan muka shiga jajantama juna mutuwar Ƴar Shuwa wallahi ta ɗago ta kalleni takasa sabida kwarjinina da haibata ta cika ɗakin wallahi, dolen doliya ta fice a ɗakin ta koma dokin ƙofa duk ta lalace ta jeme. Sai da maza suka dawo nan gida ya sake kacamewa da gaishe_gaishen mutuwa, su Wawo duk sun leƙo nayi musu ta'aziyya haka ma Babangida ya leƙo. "Mun gode sosai Sabuwa. Naga su Maigogul da maigidanki ma duk dasu muka je maƙabarta Allah ya bar zumunci Adama mun fa gode" Allah sarki ai babu komai" Na faɗa a taƙaice. Ana haka Uzairu zuchiyata ya kutso cewar in leƙo ga Alhaji yana so yayi magana dani. Fitowa nayi na sameshi tsaye shi da Babangida a kusa da turakar Baba malam. Dana iso sai Babangida yace. "Bari in koma waje Alhaji sai ka fito" Saida ya kalleni kana ya fita. Ni kuma hankalina na kan mijina. "Wazirat kiyi haƙuri kukan ya'isa haka ki yi haƙuri dan Allah. Dama cewa nayi ko za'a siyo kayan abinci ne a kawo ko kuma kuɗin zan baki kya ba iyaye? " A_a a siyo kayan abincin. Kuɗinma sai a basu babu komai zasu riƙe a hannunsu, nima ina buƙatar kuɗi" "To shikenan Yaya Uzairu zuchiyata zai kawo miki kuɗi zamu je dashi mu siyo kayan abincin in damƙa a hannun Baba Mardiyya" Yana saka kai zai fita. Ni kuma na ɗaga ƙafata kenan zan juya sai naji marata ta murɗe sai ga jini na bin tsintsiyar ƙafata. A guje Adama tayo kaina.

Ayi haƙuri yau ba yawa ina da uzirine da babu gara babu daɗi Mrs BUKHARI [10/30, 7:20 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 12

"Lolo lafiya jini ke zuba a jikin ki fa? " Adama ta tambaya a kiɗime dam na riƙeta dam wani irin mugun ciwo nake ji mai tsanani. "Mardiyya maza daure kirawo Uzairu zuchiyata mu fita da'ita maza aje asibiti" Cewar Rahama da suka firfito kafin Uzairu zuchiyata yazo har Labbai ta riƙeni ida da Adama mun soma tafiya sabida Rahama ruɗewace yasa tace a kira Uzairu zuchiyata ba wani abun ba. Ai kuwa hankalin kowa ya dawo kanmu anata tambayar meke faruwa. Muna fitowa wani guda ya faɗo a ƙasa kwaɓal shikenan cikin nasan ya ɓare. A kiɗime Alhaji Zaidu da Babangida suka ƙaraso. "Meke damunta take zubar da jini? Alhaji mota zaka ɗakko maza mu kaita asibiti Sabuwa sannu" Babangida ke magana a kiɗime shima Alhajin a kiɗime ya ɗakko mota Maigogul dai duk yadda akayi bayanan ya shiga gari. Tuni aka kaini asibiti inah ciki kam ya zube mahaifata tayi dameji sosai harma likitocin sunyi mamakin yadda mahaifar ta iya ɗaukar ciki ma. Kano muka dawo asibitin malam Aminu Kano wallahi mummunan labari ina kwance babu yadda nake ashe mahaifar tawa aka cire sukutum ta lalace ikon Allah ne yasa Hajara ma tazo duniya a yadda likitocin suka ce kenan. Nayi kuka nayi kuka sosai. Amman me? shi bawa baya wuce ƙaddararshi kuma sai dai ince Alhamdulillahi tawa ma tayi kyau tunda ina da yara biyar to me kuma nake nema. Cire mun mahaifa shine tambari mafi muni da bazan mance dashi ba a sakamakon yawon banza da zubar da ciki, da shan ƙwayoyi. Ƙalubale a gareku yaran mata masu bin maza da yawan shan ƙwayoyin zubar da ciki ku kalli Ayar da aka saukar a kaina ta zame muku abun tsoro. Ina kwancannan a asibiti aka mayar dani asibitin kuɗi mai kyau sosai. Haka dangi sukaita sintirin zuwa dubiya abun mamaki harda su Sa'a da Kudidi a zuwa dubiya a bisa jagorancin su Aminu da Babangida. Amman in banda dangina babu fa wanda yasan da batun cire mahaifa, ba abu bane da za'aita yayatawa ba. Alhaji Zaidu kuma kullum a cikin rarrashina yake tare da yi mun wa'azi. Ba tani nake ba taka nake ji. Dole akwai buƙatar ka sake aure ko dan ka hayayyafa kaga haularka" Na faɗa ina hawaye. Shafa kaina yake yi yace. "A baya tsawon shekaru nawa nayi a rayuwa ba haihuwar harma an cire rai da haihuwar ma sai Allah ya bani mamana. Shin nasan zan sameta ne ma, ko kuwa nasan ma ina haihuwar bare ince ga ranar da zanga jinina? Ke kaɗai zaki rayu dani har abada. In har zaki iya aurena a matsayin juyi, to tabbas zan rayu dake a matsayin mara mahaifa Allah ya raya mana Hajara kwana nawa ma ya ragemun nafa tsufa kece bakya gani" Murmushi nayi nace. A fuska ba. Amman zuchiyarka da ƙarfinta haka ma a.... " Sai nayi shiru muka yi dariya yace. "Ai sai kin faɗa wazirat bazan barki ba Allah" A kunne na raɗa mishi abinda nake son raɗa mishi. Yayi dariya sosai, sai naji sanyi a zuchiyata. Ko wanne bawa fa yana da tashi kalar ƙaddarar ta wani tafi ta wani ne. Kuma kowa aka ba dama yana da abun faɗe a bakinshi tabba, ko ba haka bane makaranta? Watana ɗaya da kwana biyu a asibiti aka sallamomu muka dawo kuma gida. A lokacin ana shirye_ shiryen Auren yaran Rahama biyu da ƴar Adama tsiran na sati biyu ne, anko ma haɗewa akayi. Ga Gaza ma wai Aure zai ƙara yaga farar bakanuwa ta sace zuchiyarshi abinka da jinin Maigogul. Uzairu zuchiyata kuma yana ta soyayya da ɗiyar ƙanwar Hajiya Balaraba wata ƴar boko wayayya, ta ganshi suka yadda da junansu lokaci shima kawai muke jira. Bayan an sallamoni da wata biyu muka yi bikin Ƴar Adama sati na sama mukai na yaran Rahama. Kishiyoyin Rahama sun sha ruwan mamakin ganin yadda ta koma da irin bajintar da mukaima yaran na kayan ɗaki dan uban na kwance ma jinya yake yi. Mu mukai komai hatta abincin da za'aci na taron biki mu muka yi. Bayan na dawo Kano da wata guda kuma muka shiga Auren Gaza da Uzairu zuchiyata anan Kano Gidan Hajiya Balaraba akayi Auren Uzairu zuchiyata shi dai ɗan ɗakinta ne kuma ita ta haɗa mishi ma akwati Gaza kuma a gida akayi bikinshi. Amare duk suka tare a gidansu Kayi nayi rayuwa dai taci gaba da yin kyau tana shurawa a hankali a hankali. Uzairu zuchiyata yana shagon Dad tare suke gudanar da kasuwanci. Ya zuba kuɗi da agoguna suka ƙare sai ya saro da ƙudinshi aka ci gaba da harka daman shagon na ƴan gayune irinsu. Su kaɗai sun isa su baka sha'awa in siyayya kaje yi shagon irin kece wankan da suke yi ba abu bane na wasa wallahi.

Babangida:. Yana zaune a tsakar gida yayi tagumi shiru gidan babu wuta sai fitila a tsakar gidan. Ƴar Shuwa ta kawo mishi abinci ta dure mishi ta kawo ruwa. Abincin ya buɗe ya saka cokali ya soma ci babu ƙorafin ba'a kawo mishi a ɗebi da kanka ba. Dake rayuwar ta mugun juya mishi baya. Kamfanin da yake aiki dasu an rufe kamfanin ƴan chinan sun sallami kowa, ɗan wajen Baban bolanshi da yake ɗan siyan kaya shi kaɗai ne dashi a hakan ake jalautawa kasuwar tayi baya sosai. Sai koyarwa da yake yi dai a haka ake ƙuƙutawa. "Dama nace Babansu Fatima abincinmu wallahi ya ƙare iyakar ragowar kenan yau na girke mana ko ɗumame ba za'a samu ba shine nace bari in sanar maka" Kafin yace wani abun Hala ta fito ta zauna a dokin ƙofarta zafi ya isheta a cikin. "Baban Mardiyya yarannan fa dukka an korosu a school ba'a biya musu ba. " Tun yaushe aka korosu amman? " "Wallahi ai tun ranar Litinin fa aka korosu." Rai ya ɓata yace. "To amman mai yasa ba'a sanar mun bane? " Ƴar Shuwa tace. "To ana ta batun tuwo yaushe zamu sanar maka wani batun makaranta. Yanzu kana gani yau kuɗin cefane ma bamu samu a wajenka ba. Aminu ne daya shigo fa ya bada kuɗin cefanen shi yasa ma akayi girkin" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Babu komai gobe za'ayi biyan makaranta sai inga abinda za'ayi akan abinci da makarantar yaran. Allah ya ƙara rufa asiri" "Ameen amman nace ya batun rabon gadon naku ne. Yau kusan shekarun Baba malam biyu da rasuwa ace har yanzu anƙi tayar da rabon gadonnan naku wawo sai wadaƙarshi kawai yake yi, harfa mota ya sake matanshi ya sake musu kujeru fa? " Idanu ya lumshe tare da yin murmushi yace. "Gado ba abun dogaro bane, abinda ka tara dashi zaka dogara ai. Wawo da Bashiru sune manya idanu mu dole zamu saka musu. Amman faful basason ayi batun rabon gadonma. Gidajen haya da shagunan haya dai su dama suke karɓan komai. Makaranta ta dawo hannun Wawo sai wata yayi goma ma bai biya malamai ba to muna kai kuka wajen Allah babu komai wata rana sai labari." Shigowar Aɗɗa'u da kayansu kici_kici ne yasa Babangida yayi shiru ya zuba ma Aɗɗa'u da malama idanu. "Lafiya Aɗɗa'u daga ina a darennan kuma na ganku da kaya" Babangida ya tambaya a ɗarare. "Dama Kawu Wawo ne yace mu dawo gidan Babanmu. Malama ƙarama ta gargaɗeshi amman yace sai mun dawo shine na haɗo mana kayanmu muka tawo" Mamaki ya kama Babangida amman kuma rayuwace ai. "To shikenan ku shiga ɗakina kuyi kwanciyarku, kunci abinci ai ko? " "Munci Baba" "Ina shi Aminun to ya barku kuka tawo ku kaɗai? " Cewar Sumayya Maman Amir da fitowarta kenan. "Yaya Aminu baya nan baisan ma mun tawo ba" Tace. "To Allah ya rufa asiri" Yaran suka shiga ciki Babangida kuma ya rufe abincin da loma huɗu kawai yayi ya fita sai gidan Wawo tunda gidan dama a jere yake katangarsu ma a haɗe. Izinin shiga wawo ya mishi a tsakar gida ya sameshi a saman kafet yana cin shinkafa da miya da latas ga zoɓo mai sanyi da ruwa mai sanyi. "Yaya dama yarane suka dawo wai kace su dawo wajena shine nace bari inji shin da gaske ne? " Kai ya gyaɗa yace. "Tabbas ni nace su dawo hannunka kaci gaba da riƙesu zai fi. Kaga sauran yaranka ma naga an dawo maka da biyu mata ai gara ka haɗa da yaran Sabuwa ko? In kuma ka gaza ba sai ka turasu wajen uwarsu ba tunda attahiri take Aure" Yawu baƙin ciki ya haɗiye yace. "Babu zancan gazawa yarana ba zasu yi zaman agolanci ba zan ci gaba da kulawa dasu wanda akayi mun ma nagode" "Daga baya kenan yara kusan huɗu yanzu haka suna can suna agolanci kuma ai yaranka ne me yasa baka je du ka ɗakkosu ba? " Murmushi yayi yace. "Nayi yinƙurin haka ragowar iyayen yaran sun hanani yaranne. Biyu daga cikine suka amince shi yasa aka kawo biyun. Sannan ai su da yawansu da cikinsu aka tafi shi yasa bawai na gaza bane. Nagode mu kwana lafiya' Ya miƙe ya fita zuchiyarshi na turiri ya jima a waje yana tunanin ya zaiyi ya dinga bin ɗakuna alhalin ɗakunan cike suke da yara maza da mata. Matan suna ciki da iyayensu mazan na falo. Can yana tsaye ya tuno Kitchen ɗin gidan yana da girma sosai ma kuwa ƙaton Kitchen ne. "To sai dai ko wacce ta kwashe kayanta a Kitchen ni in koma ciki kenan. Allah ya rufa asiri." Shigewa ciki yayi yayi zamanshi a tabarma. Duk sunyi shiru saiga Aminu ya shigo da leda har biyu a hannunshi. "Aminu kadawo? " "Nadawo Baba sannu da gida. Mama ina wuninku? " Ya dubi matan uban duk suka gaisa yace. "Su Aɗɗa'u ance sun tawo ko Baba? " "Suna ciki inka shiga ita Malama ta fito taje ɗakin Maman Amir acan zata ci gaba da kwana cikin ƴan uwanta. Ku kuma yaranku mazan su biyo su Aminu suci gaba da kwana a ɗakina daga gobe, damin yau tare dasu zan kwana. Zuwa gobe da safe duk ku kwashe komatsanku na Kitchen na zubarwa a zubar na adanawa a ƙarƙashin gado a adana can ɗinne zai zama ɗakina." Ledojin da Aminu ya shigo dasu ya ajjiyema uban ya shiga ciki. Babangida ya buɗa ledar yaga biredai manya har uku sai sikari da madara da ganyen shayi harda kwai rabin kiret. Murmushi yayi tare da yin hamdala gami da shi ma Aminu albarka. Haka dai Babangida ya miƙa ma Ƴar shuwa ledarnan tunda itace da girki. Da safe aka sha shayi da biredi da ƙwai. Yara duk suna gida ba zuwa makaranta. Su kuma su Hamida da kwalimar fitar da kaya a Kitchen suka soma sassafe. Aminu ne ya leƙo ya tari Babangida da yake shirin fita. "Baba dama zuwa gobe in Allah ya kaimu muna son zamu bi Adda zuwa Kano. Sannan Ummi tace in zo da takadduna tunda anan na kasa samun aiki. Koyarwar kawai nake yi kula da littattafan da nake riƙe da ofishin Kawu Wawo ya sallameni ya saka Muntari a kujerar" Shiru Babangida yayi kamar ruwa ya cinyeshi kamar ma bazai magana ba ba dai yace. "Haka akayi? To shikenan ragowar maganar inna dawo aiki saimu tattauna" "To shikenan Allah ya tsare." Babangida ya saka kai ya tafi kasuwa yayi da Ƴar shuwa akan in sha ɗaya tayi ta turo yara su karɓa musu cefane. Haka ya tafi kasuwar tunda dai yaje har zuwa sha ɗayan yaro ɗayane ya kawo mishi wasu tukwane ya Auna amman bashi ma da kuɗin da zai karɓi kayan. Dole yaron ya tafi ya kira masu zuwa ɗiban kayan ƙarafe su biya suma suka ce sai zuwa gobe zasu biyo tanan. Dole haka da yara suka zo karɓan cefane ya ɗebi kayan ƙarafai shima ya kai aka auna aka bashi kuɗin. Da kuɗin yayi musu cefanen iyakar abinci rana yace zai taho dana daren. Yana wajen har magriba yana tubkewa da warwarewa dole dai haka ya rufe wajen ya nufi gida. A hanya suka haɗu da Mustapha ƙafarshi duk ƙura. Tafawa suka yi. "Babangida kacigari Babangida makeljacsin" Dariya suka yi Babangida yace. "Kai dai baka da girma saina jiki wallahi" "To ya za'ayi ya rayuwa Babangida? " "Mustapha yanzu haka daka ganni ban basu abinda zasu girka ba ni suke jira ni kuma ban samo ba" Mustapha ya zura hannu a ajjihu yace. "Dubu biyu ce dani da'ita nake saka ran zasu siyo gasara da sikari a dama da safe a siyo ƙosai ko bibbiyune aci a tashi. Bari mu raba sai mu ƙarasa gida akwai taliya sai in baka ko leda biyu ce" Ajjiyar zuchiya Babangida yayi, yasa hannu da godiya ya amshi kuɗin. Suka je ya bashi taliyarnan leda biyu. Saida suka yi magriba kana ya nufi gidan. Yana shiga ya tadda kowa a tsakar gidan suna ta cin shinkafa da miya harda kaza ga lemun kwalba anata tsiyayama yara wutar nefa ta haska tsakar gidan tanwar. Da sauri Maman Fati ta shinfiɗa tabarma a gefen Kitchen har an saka labule. Ledar hannunshi ta karɓa ta shiga ciki sai gata da kofi ta ɓalle shiwebs ta tsiyaya ta miƙa mishi. "Sanyaya maƙoshin bari a kawo abinci" "Baba sunnu da zuwa" Yara suka soma mishi yana amsawa. Saida ta zuba mishi abincin miyar sai ƙamshi ga kaza manyan yanka ƙirji da cinta, ga latas cakuɗe da kabeji ta zubo a kwano daban. "Daga ina wannan abincin ina aka samu kuɗi, ni dai nasan na fita ban bar komai ba? " "Tabbas baka bar komai ba dan hatta abincin ranan mun dai shasshafa da babu akace gara babu daɗi. Mardiyyace da bayan la'asar mijinta ya kawota duba su Aminu da jin ba'asin wai tafiya zuwa Kano da zasu yi. Ita ta kawo abincinnan a dafe harda lemun kwalba rabin kiret wallahi ta kuma bamu dubu bibbiyu" Shiru kamar ruwa ya cinyeshi sai hankalinshi ya tashi ya shiga wani irin yanayi da farin ciki haɗe da damuwa. Tunaninshi ya koma mishi shekarun baya sanda Sabuwa ke dafa abinci duk sanda zata je gida takai sabida tasan basu dashi. Ashe kenan haka take yaye ma Ahalinta damuwa a zauna aci ana farin ciki shi yasa duk gori bata taɓa denawa ba kenan? Gashi yau Mardiyya ta ɗanɗana mishi irin farin cikin da Maigogul da Rakiya suke shiga harma da su Uzairu zuchiyata. Ya jima yana fassara wasu yanayi na baya kana ya ja numfashi ya sauke yace. "Allah yayi mata albarka. Harta iya yo girki mai yawa ta kawo da har ya ishi gidannan? " Ƴar Shuwa tayi mishi nuni da kular data ciko ta tawo dashi a ƙalla abincin ciki zaiyi mudu biyu. Shigen kular da Sabuwa ke cikawa takai gida a duk sanda zata je. Ashe kaima iyaye dafaffen abinci yana da daɗi da sauƙaƙewa musamman in ansan basu da hali sosai. Ashe yana daga cikin tausayawa da nuna kulawa ga ahali. Ashe yana daga cikin nuna ƴan uwantaka? Ajjiyar zuchiya ya sauke yayi murmushi. Damma Allah ya so shi bai taɓa hanawa ba sai dai gorin masifa tabbas ƙila daya taɓa hanawa ta hanu kuma ba lallai Mardiyya ta iya kawowa ba. Amman dake wannan na daga cikin tarbiyyar da Sabuwa tayi musu kuma tasan basu da hali yanzu shi yasa tayo wannan abincin ta kawo. Madallah da Sabuwa mai sabon aiki. Kiran sallah aka soma dole ya dubi su Aɗɗa'u yace su taso su tafi masallaci. "Abincin ki kai mun ɗakina acan zanci. " Ya miƙe suka je sallah. A hanyar dawowarsu yake sanar musu ya amince suje Kano goben tare da Mardiyya. Suna dawowa kowanne ya shiga neman wajen kwanciya shi kuma ya shiga ɗakinshi. An share an wanke an saka labule a taga da ƙofar shigowa, ga katifar yara nan ƙarama sai tabarma babba da aka baibaye ɗakin da'ita. Abincinnan yana ci yana farin ciki har ya gama ya kora da shiwebs tare da yin hamdala. Washegari ragowar abincin aka ɗumama sai aka siyo biredi aka haɗa dashi da ruwan bunu. Duk da haka miyar tayi ragowa dayawa Ƴar shuwa ta damƙama Sumayya tunda ta fita a girki ita zata yi na rana. Sai ga Mardiyya da safe sun zo ɗaukar su Aminu sai shiri suke yi dama duk sun yi ma wanka. Da safenma bata barsu haka ba ta riƙo musu masa mai ƙuli cikin roba mai hannu babba ga ƙuli. Babangida kuma ta kawo mishi cincin mai yawa da dambun nama. Tare da Sauban suka shiga har ɗakin Babangida suka gaisheshi ta ajjiye mishi wannan kwano. "Jiya na dawo na tadda abinci akace ku kuka kawo. Sauban anfa gode Allah yayi albarka ya baku zaman lafiya." Da ameen suka amsa Ƴar shuwa ta ciko kwano da masa baɗe da ƙuli ta kawo ma Babangida tunda shi dama bai kai ga karyawan ba. Yaita ma su Sauban godiya. Da zasu tafi Sauban ya ɗakko dubu biyar ya bashi. Mardiyya ta bashi dubu biyu. Har bakin mota ya rakasu bai baro wajen ba saida motarsu ta ƙule. "Baƙar tukunya mai fidda farin tuwo. Allah mai fidda rayayye cikin matacce." Ciki ya koma ya zuba musu cincin da dambun nama yace su rarraba. Ya ɗakko dubu uku yaba Sumayya tunda iyaka abincin dare zata yi akwai miyar sutu ma tumaturi da ɗan bushasshen kifi kaɗai za'a watsa a ƙara mata afki sai ayi ko da wake da shinkafane, ko shinkafa da taliya tunda suna da'ita. Kulle ɗakinshi yayi ya musu sallama ya tafi. Su mardiyya suna tafe anata hira har suka iso Kano cikin Aminci. Sabuwa na tsaye a Kitchen taga shigowar motarsu Harabar gidan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull