Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 11: Idan kaya ya gaji gammo ma ya gaji 5 Chapter 11. Mrs BUKHARI

3,521 words

Mrs BUKHARI

Aimun haƙuri kwana biyunnan ina da uzirine shi yasa kuke ganinshi babu yawa. Afwan masoya. [10/31, 11:22 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI 13

Kunyi ready ku koyi skill ɗin da ke kawo kuɗi! Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace, ko ku iya video editing kamar professionals - to wannan class ɗin naku ne! 💪🏽

📚 Za ku koyi: 🎧 Voice Over (recording, editing, delivery) 🎬 Video Editing (cuts, transitions, subtitles & more!) 💻 Practical + Real Project Training

📍 Location: [TELEGRAM ]

Payment: 9163354359 Sa'adatu Adamu Opay

Send receipt via 📞 Contact: [07044292865] 🗓️ Registration ongoing - Limited space available!

💥 Kada ka tsaya jiran lokaci - ka shiga yanzu

TASKAR BADI'T

WANNAN SHINE JADAWALIN SHIRYE SHIRYENMU DA WANNAN TASKAR TAKE GABATARWA YAYIN DA BA'A LITTAFI DOMIN ƘARUWARMU BAKI ƊAYA MU GUDU TARE MU TSIRA TARE.

MASU SON KASANCEWA TARE DA MRS BUKHARI GAREKU GA LINK NAN DUK MAISON KASANCEWA MEMBER SAI YA SHIGA A DAMA DASHI IN SHA ALLAH. ANA ƘARUWA MUNA FAƊAKARWA DOMIN AN HAƊA MALAMAI DATTIJAI WAƊANDA SUKA SAN DARAJAR MUTANE SUKA SAN ME SUKE YI. DUK DA ZAMU SABUNTA SHIRYE_SHIRYEN NAMU IN SHA ALLAH KU KASANCE TARE DANI A KULLUM

RANAR MONDAY 8:00 PM A GAMA 9:30PM

Shirin """"TARBIYYAR YARANMU"""

MASU GABATARWA ( MAMAN KHAIRY) (ANTY BADI'AT) (KHADIJA MAI DOKI) (ANTY ZEE) RANAR TALATA 8:00AP A GAMA 9:30PM

shirin """"AMFANIN TSABTA GA MACE"""

MASU GABATARWA (MRS BASH) (MRS BUKHARI) (MAMAN KHAIRY)

RANAR LARABA 4:00PM A GAMA 6:00PM

Shirin """TAURARUWAR MAKO"""" SHIRIN DA ZAI DINGA ZAƘULO MANA MATA DOMIN SU BAMU TARIHIN GWAGWARMAYARSU A GIDAN AURE.

MASU GABATARWA (HAJARA ALIYU) (OUM INTEESAR) (MAMAN SAFWAN)

RANAR ALHAMIS 8:00PM A GAMA 9:300

Shirin """MATSALOLIN MATA DA WARAKA"""" SHIRIN DA ZAI DINGA ƊAUKO MAUDU'I YANA TATTAUNAWA AKAI. MUSAMMAN MATSALOLIN DA SUKA ADDABI MATA. SANNAN ZA A DINGA KARANTA TAKADDUN MASU TURO MATSALA, DA BASU SHAWARI ME KYAU""""

MASU GABATARWA (Ummu Inteesar) (Mum khairy) (MRS BUKHARI)

RANAR JUMA'A 12: 00PM A GAMA 2:00PM

Shirin """"ADO DA KWALLIYA""" MASU GABATARWA (KKhadija maidoki) (Mrs BUKHARI)

RANAKUN ASABAR DA LAHADI KUMA RANAKUN HUTU IN SHA ALLAH. DOMIN KULAWA DA ME GUDA DA YARAN GIDA BAKI ƊAYA.

SABUWA:

Murmushi nayi lafiyayye. Saina tsaya kawai ina kallonsu suna sauke kayansu daga mota sai dariya suke ci ko me suke tattaunawa oho. A fili nace. Ohh ni Sabuwa Ƴar daba, mai biye_biyen club, da biye_biyen maza yau ni Allah ya azurta da waɗannan yara na albarka harda jika? " Daga daf dani naji Omri yace. "Inason ganinki a cikin yanayin daba kina ciccije baki, kuma wai kin iya sara? " Illahirin kunya saita lulluɓeni na juyo na ƙanƙameshi bana so mu haɗa idanu. "Zaki sani inna kama bakinnan naki mai daɗi da yake kiramun mata ƴar daba. Kuma in haƙuri kike so nayi tabbas yau sai kin mun rawar culub na gani in ba haka ba himmm." Dariya nayi ina ƙoƙarin zamewa yana ƙara haɗani da jikinshi. "Ina sonki sosai Wazirat ina son komai tattare dake. Kuma wallahi inason Baba Alhaji burgeni yake yi ɗan wanka ba. Shiga raine dashi sosai shi yasa fa Mama take kishin shi da yawa ni bana ganin baikenta" Dariya muka saka nace. Kayi nayi jarabar duniya" Kafin in rufe bakina ya buge mun tare da tureni a jikinshi da gaske ranshi ya ɓaci. "Na lura bakya ji wazirat akan cewa Maigogul da kayi nayi wallahi zamu samu mugun matsala dake meye haka? " Fuu ya fita ni banma taɓa ganin ɓacin ranshi haka ba sai duk na damu sukuku na fito falo na tadda mai aiki na shigar musu da jakunkunansu ciki. Duk sai suka nufoni suna kiran sunana. Dukkansu na haɗa na rungume sai ga hawaye sharshar sai muka fashe da kuka. Sauban na gefe. Omri ne yazo ya ɓanɓaresu amman Aɗɗa'una yana riƙe da wuyana. "To ayi haƙuri kukan murnane haka Aɗɗa'un Ummi ayi haƙuri kaga ƙannenka Malama da Hajara zasu yi maka dariya." Murmushi yayi tare da sakina. Har ƙasa suka tsugunna suka gaisheshi ya amsa cike da kulawa. "Ya kuka baro Baban naku da matan Baban naku?" Aminu ne yace. "Duk suna lafiya Dady sunce a gaisheku" "Sauban illo ya ka baro iyayenka?" "Duk suna lafiya sunce a gaidaku" "Muna ansawa da kyau" Mardiyya ta sakko sabon goyonta ta miƙa ma Alhaji Zaidu ya amsa yana murmushi mai sunan Babangida kenan. Ɗayar sunan Sabuwa aka saka mata a gidan kakarta Sa'a aka barota dama kusan tun daga yaye ma tafi son gidan Sa'a sabida yadda take ji da'ita. kunji ƙudurar Allah Kitchen na shiga ni da mai aiki muka soma fito da abinci. Tare da Alhaji Zaidu aka baje akaita liyafar ciye_ciye anayi ana hirar yaushe gamo. "Ni wajen Maigogul zani ummi" Cewar Malama. Omri yace. "Ai Hajara dai ta ture gwammatinki kai Alhaji Baba fa akwai farin jini. Sai dai yayi ƙwarƙwara da malama to" Dariya muka saka dukkanmu ni kam harda ƙwarewa. Tare da yara mazan suka tafi masallaci ni kuma na ja matan zuwa ɗakina muka yi sallah. "Ya kika baro takwarata babu matsala ne a wajen wa kika barta? Ai irin wannan tafiyar da ba zaki barta ba kowa ai yana son ganinta. Ni nama fi son ganinta fiye daku, da Babangida kika bari a gida ni yafi mun" Dariya suka saka na hararesu. "Ummi bakya son ganin Baban nawa? " Ko kaɗan kuwa" Sai tayi murmushi kaɗan naga fuskarta ta sauya. "Allah sarki Baba ni tausayi yake bani sosai daya rasaki" Kinci gidanku Mardiyya kul na kuma ji" Sai malama tace. "Ummi mun dawo gidan Baba da zama Kawu Wawo ya koromu har yana cewa Babanmu wai kangararre. Ummi dan Allah ni zan dawo nan" Shiru nayi ina tunani nasan in sama da ƙasa zata haɗe Babangida bazai taɓa yadda Malama dai ta dawo wajena ba. Malama kiyi haƙuri ki zauna a gidan Babanku. Ni kinga a baya duk yadda gidanmu yake haka nake son abuna. Duk abinda kike so zan dinga miki kinji ko? " Sai ta ɗaga kanta. Mardiyya ki dinga leƙasu akai akai kece uwarsu kin sani ko Addana? " "To Ummi zan dinga leƙawa" Dawowarsu daga masallacine yasa muka rankayo muka dawo falon nan akaita hira. Omri ya tashi ya shiga ciki nasan dama da yamma yace mun akwai inda zashi, saina bishi. Ina shiga ya haɗe rai kicin_kicin. A hankali na isa gabanshi ya ƙuramun idanunshi sai naji gabana ya faɗi ras. Omri menene dan Allah? Sai yayi ajjiyar zuchiya. "Kukan me kike yi da kika ga yara uhm. Kina kewar rashin kasancewarki dasu a gidan Babansu ne, koko Baban nasu sukutum kika tuno" Da sauri na haɗe bakinmu waje guda mun jima sosai kafin ya matsa. Kada kayi tunanin komai. Wallahi kukan na farin cikin ganinsu da girmansu ne kacal. Me akayi akayi Babangida? In duk duniya ni dashi muka rage wallahi bazan iya komawa hannunshi ba haba omrina" Sai kuka sabida anzo gaɓar na riga na tsokalo zuchiyar tashi. Wallahi duk sai ya ruɗe ya shiga aikin rarrashi harda ban haƙuri. Mata a kula in baki san logon mijinki ba kina ruwa. Kunga dai ya ɓige da bani haƙuri a madadin nice zanta haƙilo. "Ya'isa kishine ya hautsina mun ruwan kaina. Nama fasa fita kwanciyata kawai zanyi. Kije ki samu yara ki nuna musu ɗakinsu su huta sai kizo ki mun tausa uhm" An gama ranka shi daɗe. Sauka nayi na kaisu ɗakunansu dake jere dana juna. Na Sauban da Matarshi daban nasu Aminu daban, sai Malama a ɗakin Hajara. Ku yi wanka ku kwanta ku huta sai zuwa magriba sai mu fita ko? " Aminu yace. "Hmm Umminmu gaskiya kina jin daɗi wai muyi bacci fa? Da'a Dutse ne da yanzu ina can ina gararanba har dako yi nake yi wallahi" Murmushi nayi nace. To ai ya ƙare yanzu kaine kayi ƙumun baki da yanzu da aikin ka a hannunka ai. Amman kace dako koyarwarfa kai da kake riƙe da Babban ofishi" "Hmmm ummi ai Kawu wawo ya sallameni a ofishinnan ya ɗaura ɗanshi shike kula da littattafai" Shiru nayi. Can nace. Shi Baban naku kuma yana gani? " "Bashi da tacewa ne Ummi" Aminu kuna cikin wani hali kenan? " "Baki koya mana ƙaryaba zamu faɗa miki halin da muke ciki in muka nutsa" To shikenan ku watsa ruwa hu huce gajiyar Dutse. Nan na barsu na dawo na soma yima omri tausa daga tausa kuma dai kun gane... Tare muka yi baccin mune har magriba kafin muka tashi a gurguje yayo wanka ya fito. "Ku shirya inna dawo sai mu fita muci abinci a waje uhm" Bai jira amsata ba ya fita. Saida nayi wanka nayi sallah kafin na fito. Yara suna falo duk sun sake kaya. Kuzo mu fita Samari" Dariya suka yi, suka bini a baya. Omri yana mota yana jiranmu. Sauban nace ya shiga gaba ni na zauna a baya tare dasu. Muka je gidan cin abinci kowanne ya zaɓi abinci yaci ya more abunshi da zamu dawo aka siyo tsire da yogot nanma da akayi isha muka baje muka sha sulalewa Omri yayi ya barni, dama Sauban ya daɗe da guduwa. Zama na gyara na fuskancesu nace. Aminu ina jinka menene damuwar da kuke ciki? " Kai ya sauke yayi jim. Ka faɗa mun akwai abinda zaku ɓoye munne? " "A_a Ummi wallahi Babane yana cikin wani hali kasuwarshi tayi ƙasa sosai, bashi ma da kuɗin siyan kayan Baban bola a wajen yara masu kawowa. Gashi Kawu Wawo baya yin biya akan kari. Babu abinci a gidan wallahi, shekaranjiya da jiya Adda ce ta kawo dafaffen abinci akaci a gidan" Mamakine ya kamani nasan Babangida ba malalaci bane wajen ciyar da iyali tabbas. Jarabawace ta sameshi a sakamakon jinyar Ƴar Shuwa arzikin nashi ya ƙare. Murmushi nayi ai a tunanina in an kawo mishi abinci dafaffe bazai ci ba. Ashe in kaga ƙi gudu sa gudu ne baizo ba. A gaskiya na tausaya ace mutum magidanci mai kuɗi da ace abinci a gidanshi babu ga tarin iyali. To Aminu Allah ya kyauta zamu tallafa da abinda muke dashi in zaku tafi sai ku kai mishi. Ku shirya gobe zamu je gida, sannan jibi kuma zamu je Malam madori kuje kuga su Rahama" Daga haka nayi musu sallama na koma wajen mijina. Washegari sassafe yayi tafiya zuwa Abuja bayan ya karɓi takaddar Aminu yace. "Ka samu aiki Aminu a kamfanin Abokina aiki mai kyau da tsoka. Wata na gaba zaka soma zuwa tunda kaga wata saura sati guda ya ƙare. Zaka dawo nan Kano da zama ka sanarma Babanka kaji? Ni zanyi tafiya sati ɗaya zanyi" "To Dady nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi" Sallama yayi musu ya fita. Har cikin mota na rakashi na labarta mishi halin da gidansu Aminun yake ciki. "Ashsha Wazirat. To ki basu kayan abinci duk abinda kike ganin ya dace a basu su kai mishi a haɗa da dubu ɗari da hamsin, matan kuma ko dubu hamsin_hamsin ki basu su kama sana'a zama hakan babu daɗi sam. Ni zan wuce Allah yayi ba dake za'ayi tafiyar ba" Mun jima a mota muna soyayyarmu kafin da ƙyar mukai sallama ya tafi. Yana fita muka shirya muka nufi gida nan muka wuni Maigogul da Uzairu zuchiyata basanan wai sun tafi China saro yaduka Allah mai iko. Sai naji gidan Babu daɗi daga Rakiya sai Hauwa sai su Madamcy Sama shi yana shagonshi dake ƙofar gida. A daddafe mukai wunin dai. Ko ince rabin wuni dan munje gidan Aisha da Sadiya. Washegari na ɗebi kayan abinci da kuɗi da turamen zani, turare, mayafai, takalma. Kwalima sosai nayi musu muka nufi Dutse anan Layuza da Raliya da Qamriyya da Labbai suke Aure duk saida muka zaga na basu kayan hatsi da kwancen sutura, mun daɗe a gidan Labbai tare muka wuce malam madori da'ita. Gidan Rahama muka dira tunda itace Babba ita kuma bata da kishiyoyi sai yaran miji. Taji daɗi sosai Adama ce ta zagayo ko mayafi babu. "Lolo irin wannan kaya rigi rigi kai gaskiya mun gode dama muna da biki kice zamu fito fes damu a cikin kayan manyan mata." Rahama tace. "Ni girman su Aminu ke bani mamaki to ai ya zama saurayi sosai Aminu sai Aure, ji Malama yadda itama ta zama? Iko sai Allah rayuwa" Dariya muka yi. Mun kusan biyun dare muna ta hirarmu ta zumunci a gidan Rahama duk muka kwana mijinta baya nan yayi tafiya, ita kuma Adama ba ita ke da girki ba" "Adama kin saki jiki sai haɓaka ƙiba kike yi wuyanki na neman shigewa" Cewar Labbai dake ba ɗiyarta nono. "Ke dai bari ai wannan ƙiba ta tsone ma kishiyoyina idanu sosai. Sabida ko tafiya Alhaji zaiyi ni yake sawa a gaban mota kinsan farar mace, ga mace mai ƙiba da cika idanu. Amman yanzu kam cikine dani wallahi" Ciki? " Duk muka haɗa baki, sai muka kwashe da dariya. Mu da muka zo da zummar kwana ɗaya saida mukai biyu, daga nan muka nufi gidan Salaha kun mance da'ita ko? Ita tana gaba can da malam madori a ƙauye take sosai dan motarmu ta sha wuya sosai. Nanma muka kwana ɗaya na sauke mata abinda zan sauke mata na ƙara mata jari mukai sallama sai kano bayan mun sauke Labbai. Kwananmu biyu da dawowa suka shirya tafiya. Buhun shinkafa biyu, katan na taliya biyu, kus_kus katan ɗaya, shinkafar tuwo rabin buhu, buhun semobita uku, sai mangyada babbar jarka yalo ɗaya na basu nace su kaima Baban. Su kuma matan uban atampace naba ko wacce ɗaya da dubu hamsin ɗinta. Su kuma nayi musu sha tara ta arziki Sauban na bashi kuɗin mai suka tafi Hajara sai kuka take yi ita zata bisu.

Dutse:. Kasancewar ba da wuri suka fita ba sai magriba suka isa ƙofar gida. Babangida na tsaye a ƙofar gida yaga suna ta fito da kayan abinci niƙi_niƙi. Saubanne ya ƙaraso ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Babangida. "Lafiya lau Sauban lallai kun sha Kano ai na zaci kwana biyu zaku yi kacal ashe ba haka bane abun. Waɗannan kayan fa? " Aminu yace. "Baba zamu yi maka bayani." Kayan duk suka shigar kana suka fito zuwa masallaci. "To Mardiyya ga abincin Babanku ko shi zaki ci? Kinga bamu san kuna hanya ba abincin kai da kai dama aka dafa" Cewar Hameeda data miƙa ma Mardiyya kular Babanta" "A_a Mama inna je gida ko taliyar ƴan yara na dafa mana muci. Ummi tace a gaisheku duk ta bada saƙo ma a babbaku" Duk sai suka washe baki Ƴar shuwa kuwa kasaƙe tayi daga zaune tana kallon kayan abincin da aka dire a tsakar gidan. Sallamar su Babangida ce tasa ta ɗago. "Wutarmu gocewa tayi ne, naga ko ina da wuta mu bamu dashi? " Hameeda tace. "Yaya Wawo ne ya cire dama gidansu shi ke bamu wuta, yace kaja mana a falwaya kai tsaye" "Ikon Allah wai Wawo me yake nema dani ne, malama Babba kuma duk tasan abinda yake yi kuwa? " Ajjiyar zuchiya ya sauke duk suka zauna Sauban dai yana waje yana jiran matarshi. "Wai daga ina wannan abincin haka masu yawa? " "Ummi ce tace mu kawo maka harda kuɗi? " "Sabuwan tace a kawo mun, kunje kun tona mun asirin gidana kenan Aminu, Mardiyya har dake? " Mardiyya tace. "Kayi haƙuri ta tambayemu babu matsala ko shine muka faɗa mata akwai sabida Ummi bata son ƙarya bamu taɓa mata ƙaryaba bata koya mana ba. Baba kayi haƙuri ai kana buƙatar kayan abincin. Ga wannan kuɗinma Dady yace a kawo maka. Waɗannan ledojin nasu Mamane da jari dubu hamsin hamsin a ciki. Aminu mimmiƙa musu ni zan tafi" Hannu Babangida yasa ya karɓi damin kuɗin jikinshi yayi sanyi sosai tsoron Allah ya sake kamashi. "Mun gode Allah ya saka da alkhairi zan kirashi ma in sha Allah" "Baba nima ya samamun aiki sati me zuwa zan soma zuwa can Kanon zan koma da zama" Murmushi yayi yace. "Sabuwa tayi mun wayo ta dai ɗaukemun kai ko Aminuna? " Sai suka yi dariya. Su Hameeda sukaita godiyar kuɗi da atampa Mardiyya dai tayi musu sallama tabi mijinta suka tafi. Babangida na gama cin abinci ya nufi gidan Malama Babba acan ya tadda wawo ma. Bayan sun gaisa Babangida yayi ƙorafinshi akan Wawo. "To Baba kayi haƙuri kaja wutar taka daban zaifi. Batun yara kuma gaskiya bai kyauta ba ta wani ɓangaren ta wani ɓangaren zamansu a gidan bashi da amfani gara ka kula dasu yafi. Batun kuma Aminu daya cire a Matsayi tun farko ni wannan matsayin na faɗa bana Aminu bane Malam yayi ne dan ya cusa mun baƙin ciki kawai" Murmushi Babangida yayi yana mai nadamar kawo ƙaran ma da yayi. Kiƙewa yayi jiki ba ƙwari yace. "Saida safenku" "To baka ce komai ba ka kawo ƙorafi anyi maka bayani ka kuma miƙe? " Cewar Wawo sai zazzare idanu yake yi. Babangida yace. "Wawo kenan Khairan in sha Allah. Ai duk wanda yayi guga yace zai ɗebi duniya ƙarshe inya jawo bazai ga komai ba." Ya saka kai ya fice. A wannan dare Babangida da ƴar Shuwa sun kasa runtsawa shi damuwar yadda ƴan uwa suka juya mishi baya yake ciki, da kuma mamakin yadda Allah yake jujjuya lamura wai yau shine mijin Sabuwa da Sabuwa suka rufama gidanshi asiri? Ita kuma ƴar Shuwa nata na hassadane da ciwon wai yau Sabuwa ke cikin irin wannan daular da har dubu hamsin bata ɗauketa a bakin komai ba har zata iya raba musu su huɗu. Ga atamfa mai tsada ga hilimin kayan Abinci? Allah al hakim. Gaga_gaga _gaga _gaga Rayuwa taci gaba da garawa. Aminu ya koma Kano yana aikinshi duk wata yana zuwa ganin gida, kuma kusan shi ya ɗauke nauyin abincin gidan Babangida har saida Aɗɗa'u ya kawo ƙarfi shima ya samu aiki anan Dutse shine suka raba a tsakaninsu. Babangida dai tunda wannan dubu ɗari da Hamsin ta shigo hannunshi saita hayayyafa itace ta haihu ta dawo miliyoyi abubuwa suka warware da taimakon Allah ya sake buɗe kamfanin niƙa kayan Baban bola da motarsu ta sufurin kaya zuwa Lagos. Yayi gida ya tashi a kusa da su Wawo nan ɗin tunda nashi ne ya riga da ya biya Baba malam kuɗin gidan kafin ya rasu sai ya zuba haya. Yana da ƴar motarshi ta hawa, ya wadata iyalinshi da abinci dama haka yake tun farko Rayuwa ta daidaita tayi kyau kamar ba'ayi komai ba. Cikar kamala da Dattijantaka irin na Baba malam ya fito sak a aiyukan Babangida da mu'amalarshi. Amman me harfa zuwa wannan lokacin zuwa yau da littafinnan yazo ƙarshe ba'ayi wannan rabon gado ba. Da an yinƙuro Wawo zai yinƙura sai salwantar da hakkin marayu yake yi. Kawu Manga yayi iyakar yinshi Babangida ya roƙeshi ya zuba idanu. Harma ake raɗe_raɗin Wawo asiri yayi musu shi yasa suka kasa yi mishi bore, suna ji suna gani yanata ɓalɓanta dukiyarsu. Wannan kenan"

Sabuwa:. Rayuwa ta sake miƙawa Hajara har ta shiga sakandare ajin farko. Su Gaza sun hayayyafa girma yazo musu sosai. Uzairu zuchiyata shima yaranshi uku dukka Maza. Masa'u kuwa yana rihab mun kaishi hauka yake yi tuburan wallahi. Maigogul yayi tsufa mai kyau ga shekarun amman ba wani ciwo, da ƙafafunshi yake zuwa ko'ina gaye baifa daina ba. Hauwa da Rakiya duk sanda rikicin Rakiya ya tashi dole sai sunyi wannan faɗa musamman in Hajiya Balaraba ta kawo musu ziyara. Nasan kunata son jin ƙarshen Hajiya munubiya sai kuka ji shiru ko? Wannan labarin ba ƙirƙirarre bane har yanzu Hajiya munubiya tana raye Allah ya ara mata lokaci, kuma tana yawan turoma da Omri saƙo ta waya akan ya maidata ɗakinta. A wata majiyar ma mai ƙarfi naji ance bata dena bin bokaye ba. Ƙarshen zaizo ne, in Allah yaso kuma ya barta har sai ta mutu ta koma gareshi saita girbe abinda ta shuka. A iya haka inaga labarin yazo ƙarshe Mungode da soyayya wallahi nima zanyi kewa masu son ganin hotona kona Dad ayi haƙuri dan Allah. Amman fa bazan mance da waɗanda sukaita aibatamu ba. Kuma abadan bazan mance da waɗanda sukaita mana uziri ba. Na mance, a yanzu ina da izifi talatin a kaina, kuma na haddace wasu hadisai da dama ina iyakacin daidai ƙoƙarina waj kiyaye dokokin Ubangiji. Ilimin boko dai ban koma ba, sai dai Allah yayi mun arzikin samun mijin daya ɗaurani kan komai na nemanshi duk wata ƙasa da zaije dani muke zuwa, kuma duk wani meeting ina gefenshi. Na waye na goge irin gogewar da ko ƴan bokon babu abinda zasu nuna mun sai turanci ko? Shima Uzairu zuchiyata yana zuwa muna yi inata kan koyo wallahi. Yarana dukka ni dasu munje mun yi umara na biya musu da kuɗina.

ALHAMDULILLAHI LITTAFI YAZO ƘARSHE ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA DARASHIN DA MUKA KOYA. KUSAKURAN DAKE CIKI KUMA ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA. WANNE BABBAN DARASI KE KIKA KOYA TUNDA DARUSSAN SUNA DA YAWA? IN MAKI AKACE KI BA WANNAN LITTAFIN DAGA ƊAYA ZUWA ƊARI MAKI NAWA KIKE GANIN ZAI SAMU? WACCE KALMA CE TAFI BURGEKI CIKIN RUBUTUN?

SON SO SAI UBANGIJI YA SAKE SADAMU A SABON LITTAFI SABUWAR TAFIYA. CAU CAU CAU, EH WALLAHI WUYA A TYPING WUYA A KWAMENT, WUYA A EHH TO SAI EH ANJIMANKU INJI GAZA. ⚔️⚔️⚔️⚔️🗡️🗡️⛏️🔪⚔️🤺🤺🤺🤺🪚🛠️🛠️🛠️🛠️🤺⚔️🔪

Mrs BUKHARI

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull