Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 1

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 1

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 1: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 1. IDAN KAYA YA GAJI.... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU

4,333 words

IDAN KAYA YA GAJI.... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

LABARI MAI DAƊIN SAURARE

*Abinda ya faru shine* *Jiya da daddare da misalin ƙarfe bakwai na dare wata lamba ta kirani cikin ikon Allah na ɗauka sabida ban fiye ɗaga waya ba nafi gane a turo mun saƙon karta* *kwana.* *Sai tace dani* *"Ƴata dan ALLAH hutun da kika ce zaki yi na* *tsawon kwana goma yayi yawa ki daure zuwa monday in dai da hali kici gaba da rubutun dan* *ALLAH. In ina karanta littafinki ina samun nishaɗi sosai. Ƴata Ubangiji Allah ya huwace miki baiwar tsara rubutu da fikrar hausa sosai. Ni tsohuwar ma'aikaciyar jarida ce, nafi shekara talatin ina karance karancen littattafan hausa irin nasu Ado gidan dabino, Balaraba Ramat, Anty Bilki funtua* *Amman Ƴata salon rubutunki ya bambamta da na ragowar marubuta. Hausarki, sunayen jarumai, da* *yadda kike amfani da daɗaɗɗun kalaman hausa, bugu da ƙari sunayen littattafanki sunfi komai burgewa."* *Mun yi maganganu da'ita sosai na yaba na kuma yi mata godiya dattijuwace sosai.* *Na yi mata alƙawarin monday zanci gaba da posting da izinin Allah.* *Maigidana daya dawo* *masallaci na bashi labari sai ya umarceni da yau lahadi in soma posting ɗin kawai.*

*Mamana gashi na* *soma posting sabida girman soyayyar da kika nuna mun* *Masoyana a duk inda suke da bazarsu nake taka rawa. In babu ku babu BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.*

001

SABUWA:.

Hannu na saka zan amshi ledar da Khalid yake miƙo mun ina murmushin cusa haushi. Ban aune ba naji an warce ledar tare da tunkuɗeni gefe naje na faɗi na dauje hannuna. Babangida ashe ya fito a mota da gudu kamar mayunwacin zaki. "Dan ubanki waye wannan, wanne kwarto fasiƙin maƙiyin Allah da manzonsa ne wannan. Au ashe Sabuwa har yanzu baki dena bin maza ba da gasken dai duk fitar da kike yi maza kike bi?" Da sauri na miƙe ga mutane har sun soma taruwa" "Malam koma me kake tunani bai kamata ka shiga ɗaga murya a hanya haka ba. Matarka ce fa, ya zaka tunkudeta haka" Karku daɗa kar ku raga iyakar abinda Khalid ya faɗa kenan Babangida ya kucuneshi ya soma cunkusa mishi manyan ashariyar da kamar a bakin tasha aka haifeshi yana yi yana jijjiga Khalid idanunshi kamar gauta. Ka sake shi Babangida, zanma baya""" Hannu yasa ya zabga mun mari, ya sake marina bakina ya fashe. Ya sake ɗaga hannu kenan Khalid ya riƙe hannun gam jikinshi na rawa yace. "Kar ka sake dukanta in kai baka san darajarta ba ni nan nasan darajarta. Baby ashe ɗan balaja'u kike aure ban sani ba, madoki wanda baisan darajarki ba?" Habawa Khalid bai rufe baki ba Babangida ya runtumashi da ƙasa, dambe ya kaure kica_kica jama'a suka haɗu kamar yaƙi mata sai tittiɗowa suke yi sada gidajensu. Da kyar aka raba faɗannan Babangida ya shiga labartama jama'ar da suka taru. "Matatace fa kwarto ya kawota har gida, har yana mata siyayya fa, saina kasheki Sabuwa wallahi, shima sai ya mutu. Mutuwa nima zanyi uban kowa ya huta. Yana faɗan haka ya cabke wuyana ina kakari yana dukana. Da ƙyar aka ɓanɓare Babangida a jikina. Duk ya fasa mun wuyana. A guje na faɗa motar Khalid, ana in fito naki fitowa Babangida kamar zai haukace haka yake ji. A guje ya gangara. "Malam ja motarka ka bar wajennan dutse yaje ɗakkowa zai ragargaje maka mota" Da sauri Khalid ya buɗe motar ya shigo, yana ma motar key muka hango Babangida da ƙaton dutse a hannunshi, habawa a guje muka hau titi har muka kusan kaɗe wata baiwar Allah mai ciki, dutsen da Babangida ya harbo ya fashe ma Khalid gilashin bayan motarshi.taratsatsatsa Gudu muke yi Babangida na binmu a mota. Ka kaini gida Khalid, na gama auren Babangida na gama zama dashi kenan har abada." "Amman babu matsala Baby jini ne yake zuba a bakin ki da hannunki fa muje asibiti" Idanu na lumshe na waiga Babangida na biye damu a mota. A_a ka kaini gida kaga biyo mu yake yi, in kuka kuma haɗuwa zai iya maka komai" Ƙwafa yayi yace "Rabu dashi bai isa yayi miki komai ba, ni kuma daidai nake dashi. In yana jin shi tataccen ɗan iskane ni ubanshi ne a iskanci" Idanuna na runtse ina kuka mai ciwo yarana kawai nake tunowa kada wannan labarin tozarcin ya iskesu shin Yaya zasu ji musamman Mardiyya da Aminu? Ajjiyar zuchiya nayi dana tuna ƙarshen zamana da Babangida ne wa'adin ya cika, wannan abinda ya faru kaɗai na cancanci ya sakeni, dama banje inda naje domin a kwato mun hakkina ba. Ban buɗe idanuna ba sai a ƙofar gidanmu, Khalid na tsayawa Babangida ya fito a mota da kanshi ya buɗe motar ya fincikoni yana neman dukana. Jikinshi yana rawa. Dira nayi a wuyanshi na shiga dukanshi tako ta ina, haukacewa nayi duk inda na samu naushi nake yi, idona ma a rufe yake. Ashe an cika a layi anata tsogumi, Rakiya da Adama ne suka ɓanbareni a jikin Babangida. Wanda a tsaye kawai yake jikinshi na rawa, idanunshi na hawaye. "Kayi hakuri dan Allah Babangida. Rashin hankali ke damunta ne shi yasa" Murmushin takaici yayi kawai idanunshi sun riƙide yace. "Kamata nayi da wani ɗan iskanta fa ya kawota har gida. Dake baku bata tarbiyyar arziki ba shi ya kawota gida. Ni zata daka harta zubarma da jini? Kuma ku wani fito kuna bani haƙuri wallahi saina kasheta. Sabuwa amman wallahi sai kinyi ɗan da kace ba'a haifeki ba. Komai yazo ƙarshe kurunƙus shi kanshi mai ɗaure miki bayan yau dai zai sallama zamana dake yazo ƙarshe" To se me IDAN KAYA YA GAJI GAMMO MA YA GAJI. Tuni nabi hanyar nemo ma kaina mafita. Me za'ayi da aurenka auren ƙaddara wawa jahili daƙiƙi kawai" Ina faɗin haka na shige cikin gida ina kukan fitar rai. Duk wannan bidirin Hamida fa tana tsaye ake yinshi abun yafi ƙarfin tunaninta ne. Rakiya da Adama ya suka ƙare oho ga mata duk an fito kallo sai riƙe baki suke yi. "Ke Lolo wai dama dake akeyi ne, eh ya naga jini a jikinki yana gudana ne wanne ɗan abu ta kazanne?" Cewar Gaza da bansan ya fito daga firzin ba. Babangida ne ya dokeni ya tara mun mutane a unguwarmu da ƙyar na iso gida Gaza kaje ka ramamun wallahi bazan Yadda ba" Miƙewa yayi tare da neman hanyar waje tar da cewa. "Kutumar dumadu lahira ga baƙo" Maigogul ne ya taso a guje ya bishi, ni kuma na zube a tabarma ina kuka kaina kamar zai fita. Ni dai ina jiyo ihu daga waje, Hauwa ma da gudu ta fita tana salati. Wani yanayi na shiga wanda nake shiga in ƙunci yaimun yawa nafi awa uku bansan meke faruwa ba, kaina sai jujjuyawa yake yi, ga maganganu a kaina ina ji can kuma saina dawo hayyacina. "Sabuwa sannu. Rakiya kinga ta samu kanta Alhamdulillah" Cewar Maigogul dake bakin gadon da nake kwance. "Sannu Lolo, daure ki tashi ki watsa ruwa Rakiya ko Adama su kaiki gidanki. Kinga uban mijinki ma yanzu yabar gidanan" Da ƙyar na buɗe bakina nace. Narantse da Allah bazan koma gidan Babangida ba sai dai sama da ƙasa ta haɗe" "Babu inda zata je. In akayi wasa fa sai in ƙarashe Babangidan uban kowa ma ya huta. Ya sabida rashin sanin darajar kai Dattijo kana ganin yadda ya cire imani yaima yarinya duka ace kuma ta wani koma. Babu inda zata je in dai ni Gaza ina numfashi. Uban mijinta ai bashi yake aurenta ba, bafa sonta yake yi ba. Wallahi domin rufin asirinsune kawai yake lallaɓa Lolo nine ubanta daga yau" Maigogul yace. "To duka ai ka rama mata saranshi fa kayi Gaza. Kuma ai kana ji yace fa da wani namijin ya ganta. Tsinannen halinsu ashe bata dena ba. Dole ya doketa ai, kana gani uban mijin ya biyo bayanta yadda muka yi dashi data farka za'a mayar da'ita" "A_a Maigogul ni ina ganin a dakata da batun komennan har komai ya lafa tukunna. Duba da irin saran da Gaza yayi ma Babangida " Cewar Rakiya, ina dai jinsu da masu cewa in koma da masu cewa in bari ƙura ta lafa duk dai, basu san hukuncin dana ɗauka bane amman in tayi wari zasu ji a lokacin nayi musu bayani.

Babangida:. Yana tafe a mota jini na ɗibanshi Hamida tana gefe tana salati. "Abban Usama kabi komai a hankali ka gode ma Allah daya tuna asirinta. Ohh ace mace da aurenta tana bi kwararo kwararo bin maza, mu muna zaune zata kwaso mana cuta. Babu mamaki ma infection ɗin dake damun mu duka gidan ita taje ta ɗebo mana" Idanu ya lumshe ƙwaƙwalwarshi na hasko mishi hoton Khalid da Sabuwa data shige motarshi. Babu shiri ya tsaida motar a gefen titi yana haki. Malama Babba sai kiran wayarshi take yi. "Kada ki ɗauki wayar ɗauko wayarki ki kira mun Mustapha ki bani shi" Ya ƙarashe maganar tare da cije leɓenshi na ƙasa. Kafaɗarshi sai jini take yi, ga saran da Gaza yayi mishi ya shiga sosai har wajen ya soma kumbura. Hamida ta miƙo mishi wayarta Mustapha nata "Hello Hello" "Mustapha kazo ka kaini asibiti dan Allah" Nan yaima Mustapha kwatanceN inda suke ba'a jima ba sai gashi acaɓa ya saukeshi. Ganin yadda jini ya ɓata kayan Babangida da motar ma da yake ciki saiya tashi hankalinshi. Sai da Mustapha ya kira wani kofur abokinsu ne ya shige musu gaba a asibiti kafin aka karɓi Babangida, a lokacin jini ya ɗebeshi ko gani bayayi ga zuchiyarshi kamar ana soyawa dan ƙuna a sume akayi cikin ɗaki dashi. "Wai meya faru hakane, rikici ne ya haɗasu da wani kome?" Hamida ta kwashe labari tsab ta labartama Mustapha. Hankalinshi yaji ya tashi ainun yasan yadda Babangida yake da matuƙar kishi wannan dambarwa yanzu aka soma, shi kuma wannan farka ko a ina yake sai sun nemoshi. "Bani kiga wayoyin nashi in riƙe mishi. Su Baba Malam sun san me ake ciki kuwa?" Wayoyin ta miƙa mishi. "Wannan baƙar wayar Maman Mardiyya ce lokacin da abin ya faru ta faɗi shine na take ta. Banyi tunanin su Malama Babba sun san halin da ake ciki ba yana da kyau a sanar musu. Yau munga tozarci da abun kunya. Babu kunya ta kule motarshi shi kuma yaja suna shirin guduwa" Kai kawai Mustapha yake ta jinjinawa. Kiran Malama Babba ne ya sake shigowa wayar a karo na barkatai. Mustapha ya ɗauka tare da karawa a kunne kana yayi sallama. "Muryar Mustapha kamar nake ji. An kashe mun Babangidan ko? Wallahi sun jawowa kansu bala'i dan bazan yarda ba." "A_a bai mutu ba Malama ki kwantar da hankalinki muna asibiti yanzu dai aka shiga dashi, saran dai ya shiga sosai. "Shikenan gamu nan zuwa asibitin hankalin kowa a tashe yake"

GIDAN SU B HOUSE

Sauke wayar Malama Babba tayi a kunnenta. "Malam kaji wai suna asibiti da Mustapha abokinshi. Sai muje ko? Ka kira Wawo yazo ya kaimu" Jim Baba malam yayi tare da dena rubutun da yake yi a allo yace. "Ki je ki kira Ramadana yazo mu je, Wawo yana wajen aiki ai ba sai an rabo shi da wajen aikin ba. Allah dai ya kyauta tsuntsun dai da yaja ruwa shi ruwa kan doka, kuma duk wanda yasai rariya yasan zata zub da ruwa" Kuka Malama Babba ta kuma fashewa dashi tace. "Anya malam kana ƙaunar Babangida kuwa?" Girgiza kai yayi yace. "Ko kaɗan. Da ana canja ɗa da tuni na canja Babangida daga tsatsona. Kaf haulata babu mai muguwar ɗabi'ar Babangida." Shigewa ciki tayi tana kuka. Baba Malam kuma ya shiga tunano baya Sallamar wani bawan Allah mai saye da surt ce ta katse tunanin Malam Baba. "Ameen wa'alaikas Salam. Bawan Allah daga ina?" "Daga kotu alƙali Muhammad Muhammad ya rubuto sammaci yace in kawo gidannan. Surukarka Sabuwa ce ta shigar da ƙaran ɗanka Babangida kacigari. Wannan sammacinne ranar zaman kotun yana jiki Malam zaku gani. Sai a daure a halarci kotu kuma dan Allah a tabbatar takaddar taje hannunshi." Salati Malama Babba ta saki wacce fitowarta kenan Ramadan na riƙe da hannunta. "To Shikenan wannan takadda in sha Allah zata je hannunshi, kuma da zaran lokaci yayi zai zo, da kaina zan kawo shi" Hannu Baba Malam ya saka ya karɓi takaddar. Ya juyo ya zuba ma Malama Babba da Malama ƙarama idanu, can ya dubi Ramadan yace. "Kayi musu jagora kuje asibiti. Akwai inda zani yanzu daga can zan biyo" Malama ƙarama na son magana amman tana tsoro dan Malam kaifi ɗaya ne. Dole haka suka wuce asibiti shi kuma ya nufi gidansu Sabuwa a karo na biyu. Sallama yayi a bakin ƙofar gidan dan ya rasa yaro ɗan aike"

SABUWA:. Fitowata daga wanka kenan, Rahama da su layuza duk sun zo, gasu Sadiya anata mayar da zance. Na jiyo sallama tabbas Muryar Baba malan ne. Maigogul ne ya fito daga ɗakin Hauwa. "Yauwa Lolo ki daure ki shirya in mayar dake. A cikin gidannan babu uwar abinda zaki tsinta. Zawarawan gidan ma neman makafa suke yi balle ke da mijinki yake da rufin asirinshi, mu kanmu dake fa muka dogara. Ni dai na faɗa miki wallahi Allah sai kin koma" Fu ya fice, nima na shiga ɗakinmu a hankali, zancan ake dai ta tattaunawa, kowa yana da damar faɗin albarkacin bakinshi da duk abinda yake so yace. Mai Rakiya ta miƙo mun mai gurguwa babu ko murfi duk datti cikinshi. Kaya kawai na zura, goduwar rigar kanti da Sadiya ta ajjiye mun. "Rakiya ke da Lolo kuzo, ku zo da tabarma" Gabana ya yanke ya faɗi, Rakiya tayi saurin miƙewa ta fice, Adama ta bi bayanta da tabarma, ni ko sai da Maigogul ya leƙo yai mun dakuwa. "Ungo nan. Kaga ne mun ƴar nema zaki fito ne ko saina shigo nayi miki ɓarin makauniya"? Bakina a ture na suri mayafin rigar jikina na fita. Dukkansu suna kan taburma ni suke jira. A hankali na isa na nemi waje gefen Adama na zauna kaina a ƙasa. Gyaran murya Baba malam yayi yace. "A kwanakin baya Sabuwa tazo mini da batun in amince Babangida ya saketa, na rarrasheta na bata haƙuri ta koma gida. To a wannan karon nasan tabbas rigima ce ta kaure a tsakaninsu, rigimar da ta lafa shekaru fin goma. Yanzu haka ga takadda daga kotu an turo mana Sabuwa ta maka Babangida a kotu, shine nazo inji ba'asin musabbabin abinda ya haɗa rikicin, da dalilin yin ƙarar" Nan dukkansu suka shiga sallallami, Maigogul kuwa yinƙurawa yayi ya kawo mun wani wawan dukan da zafinshi ya jima yana ratsa tsokokin jikina. "Zauna Maigogul abi komai a hankali Sabuwa fa tana da gaskiyarta. "Wacce gaskiya malam bata da hankaline da zata maka mijinta a kotu dan ubanta, dame ya rageta ba dai hakuri akeyi ba. Da ba'a haƙurinnan ai da itama fa ba zata zo duniyar ba" Maiduguri ne yake magana duk a daburce da halama lamarin ya doke su sosai. Rakiya dai sai tafa hannayenta take yi kaina na ƙasa ina ɗigar hawaye. Gaza daga can gefe yana ma Rahine wanka yace. "Kaga Ƴar gari. Wallahi baki taɓa burgeni irin yau ba" "A_a ai mata uzuri shekaru goma sha ba kwana goma bane ba. Nasan abubbuwa da dama da ku baku sanshi ba dangane da tafiyar aurensu. Amman menene dalilin rikicin?" Maigogul ne ya zage ya labarta mishi yadda abun yake. Idanu ya runtse ba tare da yaso jin gaskiyane ko ba gaskiya bane. Yace "Batun shigar da ƙaran akan menene shi kuma Sabuwa?" A mugun sanyaye nace. Saki nake nema Malam Baba kayi haƙuri" Da sauri ya ɗaga mun hannunshi akan in yi shiru, muƙut na haɗiye maganata. "Sabuwa zan miki tambayoyi ki amsa mun su ki daure ki kuma dena kuka." Ina shessheƙan kukan baƙin ciki da tsagwaron tantagaryar nadama na gyaɗa mishi kaina. "Kin shirya rabuwa da Babangida kin tabbatar, sannan kin shirya zawarci da kaucema kuskure da kauce hanyar da akabi a baya, sannan Sabuwa ki sani Shari'a zata iya baki ƴaƴanki, to in bata baki su ba kin shirya haƙuri, sannan zaki karɓi duk halin tagaiyara ko tozarci da ƙasƙancin da zaki gansu a ciki? Dan daga ranar da kika rabu da Babangida daga lokacin duk tallafin da nake yi zai ƙare, hatta Islamiyya sai an biya musu zasu je balle boko da ba tawa bace. Hatta ubansu yabar sake shigo mun gidana. Sabuwa!" Ya kirani da murya ta gaske. Bakina na rawa na amsa. "Kin shirya ma duk waɗannan lissafin da nayi miki, da waɗanda tunanina bai kawo su ba?" Rakiya tace. "Babu ma Kotun da za'a shiga Malam dan Allah maganar nan a barta Sabuwa dai ba ita ta haifo kanta ba, ni da Adama da daddare zamu rakata gidanta. Sannan shima Babangida a bashi haƙuri da abinda ya shiga tsakaninsu da Gaza. Shaye_shayenshi yayi bata faɗa mishi gaskiya ba ko maigogul?" Ta tambayi Maigogul dake hararata. Da sauri yace. "Sosai ma. Kaga muma fa in yayo shaye_shayenshi ya dibga sai yazo yace uwar tashi zai zane, ko kaji ma ya kirata da matarshi. Ayi haƙuri " Malam Baba yace. "Assha Allah ya kyauta. Ai Maigogul duk wannan fa ba damuwa bace, addinin Musulunci addinine mai sauƙi, nima da kaina ina sulhunta aure, wasu ma in abun yaƙi sai in turasu kotu daga ƙarshe kaga an rabu. Sabuwa ki amsa mun tambayoyina duk kin karɓa?" E Baba malam na karɓa babu damuwa" Idanunshi ya runtse tare da riƙe kanshi yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi. Sautin ɗura ashar na Maigogul kawai kake ji a wajen sai zagina yake yi yana mangareni. Gaza kuma ya taso shima ya tsaya akan Maigogul sunata faɗi in faɗa. "Maigogul dan Allah kabi komai a hankali duk wannan bashi bane. Ke Sabuwa da daddare ki shirya Rakiya da Adama su mayar dake ɗakin ki, kije ki zauna har aga menene sakamakon ƙarshen shari'a. Ki sani da aure a kanki shi wannan bawan Allah kar ki sake haɗuwa dashi, aji tsoron Allah Sabuwa" Da sauri na ɗago jin ya ambaci in koma ɗakina, magana nake son in yi amma nauyi da kwarjininshi yasa dole na sunne kaina ƙasa ina hawaye. "Ji mana kai Dattijo bafa eh zata wani koma ba in faɗa maka gaskiya" Baba Malam ya dubi Gaza yace. "Abi komai a hankali Sabuwa ta koma ɗakinta har sai an gama Shari'a" Miƙewa yayi yai mana sallama ya fita. Dawa Allah ya haɗa su Maigogul in bada ni ba. Nan wannan yace wannan, wannan yace wancan akaita zagina tare da aibantani. Har Sadiya tana duban tsabaragen idanuna tana cewa dama in Babangida ya sake ni ita ya aureta duk bala'i zata zauna. Gaza shima ya saka tijara shi yana bayana.

ASIBITI:.

Isowar su Malama Babba ke da wuya aka fito da Babangida daga ɗakin ƙaramar tiyatar da akayi mishi a hannunshi, a gadon marasa lafiya aka wuce dashi zuwa ward ɗin maza. Malama Babba sai sharce hawaye take yi, a kaf yaranta Babangida shine mafi soyuwa a gareta, inda zaɓi za'a bata na ta zaɓa sauran yaranta duka, ko Babangida shi ɗaya tilo, to da shi zata ɗauka. Ba wai dan ya fisu biyayya ba, sai dan irin yadda yake da shiga ran duk wanda yake tare dashi. Baba Malam yana mutuwar son Babangida da yabon ƙwazonshi a baya kafin Sabuwa ta shigo rayuwarshi. "Ku daure mu jira daga waje yana buƙatar hutu, sannan kai inason ganinka a office ɗina." Cewar Dr A_A NAFAƊA kenan tana kallon Mustapha dake waya da Wawo. Da sauri ya kashe wayar . "Malama kuje ku zauna a waje Ramadan ya zauna dashi zanje ganin Dr yanzu" "A_a ni kam bazan iya fita daga ɗakinnan ba ƙarama kije ki zauna a waje Sa'a da su Kudidi suna hanyarsu suma" Da Malama ƙarama da Mustapha da Dr tare suka fita, Malama ƙarama ta nemi waje ta zauna Mustapha yabi bayan Dr A_A NAFAƊA zuwa office ɗinta, a hanya suka hadu da Wawo dasu Sa'a. Wawo yabi bayan su Mustapha, su Sa'a kuma suka wuce zuwa wajen su Malama Babba. "To Alhamdulillah mun yi mishi tiyata a hannun nashi, anci sa'a karaya ɗaya aka samu a hannun, kuma anyi gaggawar kawo shi asibiti baku ce na hausa zaku yi ba. Jininshi yayi matuƙar hawa ainun yana cikin damuwa a zahirin gaskiya. Amman dangane da tiyatar mun yita cikin nasara. Amman ya kamata aɗauki mataki akan duk wanda ke da sa hannu akan wannan saran. Gaskiya hannun yaso ya kutsure mishi tun daga tushe, kuma ƙwararrene yayi saran da ƙwarewa a kan gaɓa ya sareshi" Ajjiyar zuchiya Wawo ya jawo tare da saukewa a hankali kana yace. "Mungode sosai Dr. Wannan faɗa kuma rikicin cikin gidane, amman za'ayi ma tubkar hanci in sha Allah. Yanzu dai babu wani abu ko Dr?" Bayan ta gama rubutu akan fail ɗin Babangida tace. "Ƙwarai babu wani abu a yanzu, zamu rikeshi har zuwa hannun ya soma sauƙi gudun famawa. Kuna iya tafiya" Godiya suka yi mata suka fito. A hanya Wawo ya tsayar da Mustapha yace. "Mustapha kasan waye Alhaji Abubakar Baban Bola?" Kai Mustapha ya gyaɗa yace. "Tabbas na san shi, suna harkar kasuwanci sosai da Babangida, kusan zan iya cewa oganshi ne. A lokacin da Babangida zai siyo injinan niƙa ƙarafai ta hannunshi ya samu hanya ya haɗashi da ƴan Chinan da ya sai injin ɗin a hannunsu." Hannu Wawo ya zura a aljihu yace. "Biri yayi kama da mutum akwai danshin gaskiya a maganganun Alhaji Abubakar Baban Bola tabbas. Amman duk da dai maganganunshi akwai ɗaurewar kai a ciki, amman dai zamu bashi haƙuri ya bari har Babangida ya farfaɗo inji ta bakinshi" Mustapha yace. "Wani abunne ya faru a tsakaninsu?" "O_o o_o yafi ƙarfin a tsaya daga tsaye ana maganar amman akwai gagarumar matsala babba in dai abinda Alhaji Abubakar Baban Bola ya faɗi ya zama gaskiya. Muje maza mu same su" Da sauri_sauri suke tafiya har suka iso ward ɗin. Wayar Babangida kuwa tunda ya kwanta Ramatu ke rangaɗa mishi kira bata nan tana Sokoto, kuma wai tayi sare_saren kaya shi yasa take kiranshi ya tura mata kuɗi kimanin dubu ɗari biyu da hamsin. Da taga yaƙi daga wayar ne sai tayi mishi saƙo Mustapha ya girgiza kai kawai tare da yin ƙuri yana kallon waje guda. Shima kanshi a cikin matsalolin matan gida da tulin ƴan matan daya tara a waje yake. Yanzu haka lokacin da Babangida ya kirashi yana asibiti yakai budurwarshi anyi mata allurar zubar da ciki. Dole a asibitin ya barota ita da ƙawarta. Shigowar wayar Sumy ne ya dawo dashi daga tunanin daya shige mai zurfi. Matsawa yayi nesa dasu sa'a da tun zuwansu suke ta mayar da zance ya ɗaga wayar Sumy.

Ya kuka ji labarin? Yanzu ne muka soma shigowa asalin gundarin littafin nagode sosai da wannan soyayya da kuke nuna ma wannan labarin.

Uzairu zuchiyata yana miƙo saƙon gaisuwarshi ga duk masoyanshi.

Sabuwa ma tace tana godiya da uzirin da kuke ta yi mata. Tana bibiyar duk wani sharhi.Ina godiya sosai sai Allah ya kaimu gobe. MRS BUKHARI

IDAN KAYA YA GAJI.... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA 2

INA GODIYA A GAREKU DUKKAN ƊAUKACIN MASOYANA.

INA MIƘA SAƘON TA'AZIYYATA ZUWA GA IYALAN TSOHON SHUGABAN ƘASA BABA BUHARI. ALLAH YA BA IYALANSHI HAƘURIN RASHIN SHI. ALLAH YAYI MISHI RAHAMA.

"Honey ya inata kiranka baka ɗaukar wayata ne?" Sumy ta furta a hankali cikin salon debe hankali. Mustapha yace "Ke Ƴar balaja'u ba Honey yana kwance a asibiti babu yadda yake ƴar wahala kike wani kashe wayar" A kidime Sumy ta tambayi dalilin, Mustapha ya fyeɗe mata biri har wutsiya ya ɗaura da cewa. "Wayarshi na hannuna, kuma a ko da yaushe wayar zata iya komawa hannun mahaifiyarshi dan haka sai ki tsagaita da kirashi kar kije ki kira mishi ruwa. Kinsan gidansu malamai ne gaba da bayansu dan Allah a kiyaye Sumy na sanki baki da mutunci" Suka dan tattauna fisha haka, kafin sukai sallama daga ƙarshe Mustapha ya dawo mazauninshi. Isowar Baba Malam yasa su Sa'a yin shiru, yana isowa Ƴar Shuwa na isowa kamar tare suke, harda mahaifiyarta suka tawo. Tare da Baba Malam aka rakasu Ɗakin da Babangida yake ciki. Malama Babba da Hamida suna zaune duk sunyi tagumi, shi kuma mai jinya yana kwance yana bacci numfashinshi na fita a hankali a hankali, ga kafaɗarshi ɗaure da bandeji, ga kuma inda akai mishi gyaran karaya a tsintsiyar hannun nashi ga karaya ga ciwo. Baba Malam ya ƙurama fuskar Babangida idanu, me yake tunawa sai Allah sai shi da yake tunawa. "Yanzu Malam Sabuwa ce har zata ɗauki Babangida ta maka a kotu sabida rashin ta'ido, duk halacci da fifikon da kake bata a cikin surukanka da abinda zata saka ma da Ɗanka kenan, sannan a kamata da wani ƙato da aurenta dake ta kwashe kayanta daga gaban ma'aiki shine da abinda zata saka mana kenan? Ko da yake ita dama karuwa bata da alƙawari. Wannan ciwon da suka jima ɗana wallahi bazan yadda ba." "Ke Saratu ya isheki haka nace. Lafiyanki kuwa, ya matar ɗanki zaki dinga kiranta da karuwa a gaban abokan zamanta?" Shiru Malama Babba tayi ta sauke kanta. Fin shekaru ashirin rabon da taji Malam ya datsa sunanta, sai gashi akan Sabuwa yayi. "Allah ya bashi lafiya ni zan koma gida tunda dai ɗan gatane ga dangi da matanshi baibaye dashi" "Haba Malam ya zaka ce haka. Yaya akeso in yi da raina dan ALLAH?" Idanunshi ya kafa mata babu shiri ta yi shiru. "Ina nufin harke, su Sa'a ma kowa ta tafi gidan mijinta. Ramadan ya zauna dashi, matanshi ma zuwa dare su kama hanya su koma gida umarnine Ramadan kaɗai zai zauna" Yana dasa aya ya fice. Dole ƙanwar naƙi Malama Babba ta miƙe tabi bayan Malam tana sharce ƙwalla. Su kuma Hamida da Ƴar Shuwa aka barsu zuchiya fal tunanuka ko wacce da abinda take saƙawa. Su Sa'a dukka sai da suka shigo sukai musu sallama kana suka wuce jiki a sanyaye. Abinci dai gashinan harma yayi yawa a asibitin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull