Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 2

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 2

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 2: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 2. Baba Malam:. Yana gaban motar Wawo su Malama Babba suna baya. Sa'a da su Alawiyya…

3,970 words

Baba Malam:. Yana gaban motar Wawo su Malama Babba suna baya. Sa'a da su Alawiyya sun tafi a motar mijin Sa'a da ta tawo da'ita. Motar kowa yayi shiru sai tafiya akeyi, Baba Malam yana ta ambaton Allah a zuchiyarshi karfin hali yake yi a duk abinda akaga yana yi. " Baba Malam akwai abinda ya faru ɗazu ina wajen aiki wani Alhaji Abubakar Baban Bola yazo ya same ni akan Babangida. To maganar da yazo mun da'ita gaskiya da girma." "To ai sai ka bari muje gida tukunna ko, nan ba wajen tattauna magana muhimmiya bane" Cewar Malama Babba wacce fuskarta duk hawaye. Sarai Baba Malam yasan abinda take nufi a wannan karon ya shirya maganin kuwa. Da isarsu gida matan suka shige gida, su kuma su Wawo suka tsaya a waje. Sai da akayi isha Malam ya shiga gida kasancewar juma'a babu karatu. Wawo Malam yace ya kirawo Malama Babba da Malama ƙarama su same shi a turakarshi. Malama ƙarama itace ta soma shiga da sallama, Wawo ya amsa mata yana gefen kafar Malam yana mishi tausa. Zamanta ke da wuya Malama Babba ta shigo idanunta duk sun kumbura halamun taci kuka ta ƙoshi. Ganin Malama ƙarama ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba. Bata kaunar ayi maganar Babangida a gabanta, gashi bata san ma ko menene ba. "To kai Wawo muna saurarenka bismillah " "To shi Alhaji Abubakar Baban Bolan abinda yake cewa shine yana bin Babangida kuɗaɗe jimillar kuɗi kusan miliyan Saba'in. Sabida ni yadda yai mun bayanin komai hatta injinan da Babangida ya shigo dasu daga China da kuɗin shi Alhaji Abubakar Baban Bolan aka siya. Sannan akwai kuɗin manyan motoci na kamfani wanda da kuɗin shi aka siya. Kuma ya ari ruwan kuɗaɗe a hannunshi dai masu kauri. Yadda sukai tsari da Babangida shine zai dinga cire mishi kaso huɗu bisa ɗari na duk abinda kamfani ya samu. To an soma Allaha_Allaha sai abubbuwa suka rikirkice, sakamakon shi Alhaji Abubakar Baban Bola baya ƙasar kusan shekaru biyar. Ya ɗaura wakilai da zasu dinga karɓan wannan kaso amman Babangida ko sau ɗaya bai basu ba. Shine shi daya dawo ƙasar ya nemi yazo mu gana domin hakkinshi, kuma maganar ma ya shigar da'ita kotu. Wannan shine abinda ya faru" Salati kawai kake ji na fitowa daga bakunan su Malama Babba. Kuka ta rushe dashi tana salati. Baba Malam yace "Kuma a rubuce su kai komai ko da baki suka yi abinsu?" "Yazo mun da takaddu duk ga saka hannun Babangida, kuma yana da kwafi na takaddun yarjejeniyar shima" "Waye yayi mishi garanto shi Babangidan?" Wawo yayi jim kafin yace. "Gaskiya ba dai muyi maganar garanto ba." Baba Malam ya dubi Malama dake dafe da ƙirjinta yace. "To ke kinsan wani abu game da wannan lamarinne tunda duk abinda yake shukawa yana faɗa miki. Ko kai Wawo ka san da zaman maganar nan?" "Wallahi Allah Malam bani da masaniya akan komai. Nima yadda ka jita yanzu, nima yanzun na jita" Cewar Malama Babba kenan. Wawo yace. "Nima gaskiya bansan komai ba. Amman biri dai yayi kama da mutum irin yadda lokaci guda Babangida ya samu manyan kuɗi yanata damawa. Amman dake sana'ar Baban Bola sirrine a cikinta ni shi yasa ban zargi komai ba." Baba Malam dai sai gyaɗa kai yake yi gami da murmushin da shi kaɗai ya barma kanshi sanin dalilin yinshi. Malama Babba kuwa bata aikin komai sai kuka. Ta rasa dama me zata ji abubuwa goma da ashirin sun dameta. Ga Babangida babu lafiya, ga wannan tonon sililin daya kuma samun Babangida, ga SABUWA ta shigar da ƙara, kotu biyu a lokaci guda. Malama ƙarama kuma Allah kawai take ambato. Baba Malam yayi gyaran murya yace. "Inaga kai Wawo ka garzaya ka sanarma shi Baban nashi Manga domin yasan halin da ake ciki. Banyi tunanin yasan Ɗan nashi ma babu lafiya ba. Kuma shi yaji zai iya ɗaukar Babangida a matsayin ɗa. Wannan takaddar ta kotu itama ka tafi mishi da'ita. Ko da yake zan ajjiyeta a wajena." Wawo jiki a sanyaye yace. "Amman Malam " "A_a wallahi Wawo kar ka soma. Dan nasan inda kake nufin isa, ka adana kalamanka. Kuma na kirakune domin kuji halin da ɗanku yake ciki, da rayuwar da ƙaddara ta sake zana mishi. Tashin hankalin Babangida ba yau bane farau ba yau bane ƙarau ba. Ni wallahi ko ma a jikina. Kuna iya tafiya kowa ya kwanta" Dole suka miƙe suka fice ko wacce ta nufi ɓarayinta. Wawo ya wuce wajen kawunsu ya shaida mishi duk halin da ake ciki. Yayi mishi alƙawarin gobe sassafe zai garzaya asibitin, kuma yana son ya gana da Alhaji Abubakar Baban Bola. A cikin wannan daren Cikin Malama Babba, Malam Baba, Wawo, Malama ƙarama babu wanda ya runtsa, ko da yake ba a wannan karon ne kaɗai Babangida ya hana idanun iyayenshi bacci ba. Baba Malam kwana yayi akan sallaya, yana sallah yana istigifari domin istigifari tana warware matsaloli masu yawan gaske. A kunnuwanshi akai kiran sallar assalatu.

SABUWA:.

Muna shiga ciki Maigogul da Rakiya suka dira a kaina da zagi da cin mutunci iri daban daban. Fatansu da burinsu shine duk wuya in zauna a gidan Babangida. Ni kuma a wannan gaɓar na gwammaci in koma gidan masu zaman kansu da dai in koma gidan Babangida. Kuma nayi alƙawarin ko sama da ƙasa zata haɗe bazan yadda muci gaba da aure ba. "Ɗauki mayafinki ki wuce mu mayar dake ɗakin ki marar ɗa'a kawai. Labbai Malam Habu zai barki ki je yau ku kwana da Lolo gobe ki dawo?" Maigogul ne yake tambayarta. "Zai yarda dake ba nike da girki ba sai nanda kwana shida ma girkina zai zagayo, har kwana biyu ko uku ma ai sai inyi" Ta ƙarashe maganar tana fara'a. "Rakiya fito muje in dena ganin fuskar ƴar abu ta kazan ubannan a gabana" Ni dai na zari mayafina wayata akai mata neman duniyarnan ba'a sameta ba, sai lokacin na tuno sanda wayar ta faɗi sanda nake ƙoƙarin ceton raina a hannun Babangida. A motar da Maigogul ya aro ya kaimu, sai murza sitiyaei yake yi tamkar motarshi. Basu yi shiru ba har muka kawo gida maigogul ya matsa hon maigadi ya buɗe muka shiga. Su Mardiyya na gani a zaune a bakin part ɗina Mardiyya na tsakiyarsu Malama na cinyarta, Aɗɗa'u da Aminu ko wannensu na gefenta hannunsu dafe da cinyarta. "Dubi can Lolo. Tun ba'a kwana ɗaya ba rayuwar yaranki ta soma wulaƙanta ji besu a yashe. In baki yi wasa ba sai sun dawo yaran tsakar gida ki dai kiyaye wallahi. Kin sakko mun shiga ne koko Yaya Ƴar abu ta kazan uba?"" Ya karashe maganar da tsawa. Da sauri na fito ina kwalla, ta ganin yarana a zaune illahin jikinsu da ruhinsu cike da kewata, a guje Malama tazo ta rungumeni. Su Mardiyya kuma suka nufi wajen Maigogul. Sai da muka zauna a falo Mardiyya tace. "Ummi har bakin titi muka je muka tsaya ko zamu ga dawowarki. Anty Amarya tazo har ɗakinnan tace wai har abada ba zaki sake dawowa ba, kuma wai kinyi abin kunya" Aɗɗa'u yayi carab yace. "Da naje masallaci ma tureni abokina yayi wai an kamaki da wani a mota" Wani abune naji ya tokaremun zuchiyata da ruhina yana barazanar tarwatsa nutsuwata da lissafina. Nayi nadama nadama ta har abada, ni Sabuwa na jawoma yarana abun kunya kan abin kunya dam abun kunya mufa a cikinshi muke dumu dumu gaba da baya ma. Maigogul ne ya hau yara da faɗa yana faɗa musu sharri akaimun. "Rabu dasu sharrine yaushe lolo zata yi haka. Ƙaninane ya kawota a mota to shi Babanku bai sanshi ba shine su ka ɗanyi rikici fa " Ku tashi ku tafi kuje ku kwanta. Mardiyya in kin dafa abinci ki kawo ma su Rakiya." Bajewa Maigogul yayi tare da cewa. "Amman a hakan kike son ki dawo gabana ga ƙannenku in banda yawon tambaɗa basu saka komai a gabansu ba, kema so kike ki koma ruwa kiyi fatali da damarki. Ke da Adama kun ƙi nutsuwa son maza ya shiga jikinku ainun" Dawowar Mardiyya da abinci niƙi_niƙi ta zuzzuba a plate ta jerosu a ƙaton tire shi ya katse mishi zancan. Da kanshi ya amshe tiran. "In akwai moltina ɗakko mun Mardiyya mai sanyi" Ya karashe yana dariya. Itama dariyar tayi tace. "Bari dai a kawo muku koka kola moltina jiya ta ƙare." "Ƴar baɗo to kawo mana hahahaha 😆" Zaman cin abinci su Labbai suka zauna yi, anayi ana ƙara jaddadamum in gode Allah abinci da nama zuƙu_zuƙu ga koka kola ga A c ko ina tas. "Wallahi da nice ke ko kullum sai Babangida ya lakaɗamun duka saina zauna dashi har ƙarshen rayuwata. Ke nifa ko sakina yayi ban saku ba" Carab Maigogul daya cika nama a bakinshi yace. "Allah yayi miki albarka Adama haka akeso. To a aure irinna zamaninnan a banza talaka ma zai jibgeki ya haɗaki da tuwo miyar kuka lami, kuma kiga mace tayi zamanta. Balle ki dubi irin gida da cimar da Lolo take ci. Dake tasa muguwar nufaƙa a zuchiyarta ko ƙiba da irin murjewarnan irinna matan masu dashi ta kasa yi" Rakiya tace. "Yo ba ga Labbai ba. Jiya fa Malam Habu ya haɗasu du matan nashi yaita labtarsu har ƙofar gida. Ina ɗaya daga cikin ƴan kallo. Ina kallon mitsiyaciyar yadda take shafa kuncinta daya fasa mata. Zuwam Gaza ne fa ya lafar da rikicin." Haka dai sukaita nacin zance, ni dai har saida suka tafi na sauke ajjiyar zuchiya. A daren ko baccin kirki wallahi banyi ba, in saƙa wannan in kwance wancan haka na dinga yi. Wajajen sha biyun dare motar Ƴar Shuwa ta shigo gidan ita da Hamida ina tsaye a window ina kallonsu. Suma mamaki suke yi ganin ɓarayina da gaske har'a ɗakin baccina. Ɓarayina naga sun nufo nayi murmushi na koma kan gado. Ina jiyo sunata dukan ƙofa har Mardiyya ta taso zata bude ƙofar na leƙo nace. Maza je kiyi baccinki basai kin bude ba. Dama idanunta a rufe yake dan bacci. Sun daɗe sosai suna buga kofar da suka ga dai babu sarki sai Allah sai suka ja jikinsu ko wacce ta tafi ta kwanta. Da sassafe kuma na tashi da kaye_kayen tattare suturuna tare da fitar da kayan wanki. Ga babu waya a hannuna inaso in roƙi Khalid alfarman ya ɗaukar mun lauyan da zai tsaya mun a kotu. Babangida dai nasan yana da lauyanshi na kamfani dake kular mishi da dukiyarshi. Labbai naje na samu a kitchen tana bare dafaffen ƙwai, Mardiyya kuma na zuba indomi a plate. "Lolo kinata aiki jiki ba lafiya ba maimakon tunda kin sha tea kin hadiyi magungunanki ki kwanta ki huta ma ranki, amman sai haɗa kaya kike yi" Baki na taɓe kawai na dubi Mardiyya dana fahimci kamar taso ta gane wasu abubbuwan. Mardiyya kuyi sauri ku tafi makarantar islamiyya kada ku makara takwas fa saura kuna gida" "To ummi yanzu da munci zamu tafi. Amman ummi gidannan zaki bari kiketa haɗa kaya?" Kallonta nayi tsab na jima bance komai ba rungumar da malama taima kafafunane yasa na lumshe idanuna. Kuje ku dawo Mardiyya zan yi miki bayani in sha Allah. Sannan ku taya Babanku adda'a baida lafiya an kwantar dashi a asibiti. Mardiyya ki kula da ƙannenki ke kanki inaso ki kula da kanki sosai" Malama tace dani. "Ummi zaki bani cake naje dashi makaranta?" Dariya dukkanmu muka yi, kuruciya dadi gareshi. Zan baki uwar masu gida. Amman kuɗi zan ba Mardiyya ta sai muku." A gurguje suka gama karyawa na sallamesu. Ina shirin karɓan aron wayar Labbai sai kira ya shigo wayar tata. Ɗagawa tayi ta kara a kunnenta. Baba Malam ne yake nema na ashe. Miƙo mun tayi. "Surikinki ne Sabuwa" Da sauri na karɓa kana na kara a kunnena gami da sallama. Cikin ruwan sanyi Baba Malam ya amsa mun. Na gaisheshi ya amsa mun da fara'a. "Sabuwa inaso Labbai ta rakaki kije ki wuni da Babangida a asibiti. Ki girka abinci ki kai mishi. Sannan ni zan taimaka miki har sai kin rabu da Babangida." Naso nayi gaddama dan nasan zuwana bazai haifar da ɗa mai ido ba. Amman dattijon tausayinshi nake ji kuma nasan yayi mun ƙoƙari ni dai bai taɓa hantarata ba. To Shikenan zamu je" "Ki daure har a sallamoshi ki dinga zuwa ɗin. Har gobe mijinki ne tunda bai sake ki ba. Kin ɗauki lauya ne?" A kunyace cikin ruɗewa nace. A_a" Murmusawa yayi yace. "To in kin amince zan ɗaukar miki lauya a matsayin gudunmawata ta son rabaki da Babangida kamar yadda kike so. In kuma zaki ɗauka da kanki Shikenan. Sannan kada ki tanka abokan zamanki, ko su Sa'a in suka kawo miki fitina." Nagode Baba Malam. Kuma na amince ka ɗaukar mun lauyan nasan ba zaka cutar dani ba" Albarka ya saka mini tare da yi mun sallama." Wayar na zare a kunnena kawai. "Gaskiya Lolo ni ina baki shawara ko dan Baba Malam da Ƴaƴanki ki zauna a ɗakinki dattijonnan yana sonki" In zauna sabida su in kashe kaina ko Labbai? To ku dena ɓata bakinku kinsan Allah da girma yake ko Babangida bai sake ni ba, to na gama zaman gidanshi abadan. Kuma ni dashi daga nan har kotun ƙoli. Ke dai gama karyawa ki samu abu me sauƙi mu dafa mu tafi asibiti" Kafin tace wani abu kawai muka ga Ƴar Shuwa a kanmu a tsaye riƙe da ƙugunta. "Au ke dake marar zuchiyace an kasa zama a gidan me dattin hula shine ashe dawowa kikayi. Kuma har kin samu damar cin abinci Jannaty yana kwance a asibiti silarki har yanzu bai farfaɗo ba? Babu shakka uhm lallai" Sama da ƙasa Allah baisa dukkanmu mun kulata ba. Sai ji mu kai ta kuma cewa. "Ai dai ƙaryarki ta ƙare Sabuwa, kuma wallahi saina fasa ƙwan da kika daɗe kina tsoron warinshi. Kuma dole ki bar mun Babangida " Miƙewa tsaye nayi ina murmushi nace. Babangida na bar miki shi ke da matarshi Hamida, da sauran waɗanda zasu biyo baya, harma da tulin karuwanshi na waje. Batun fashewar ƙwai kuma da kike magana akai ya daɗe bai fashe ba dan uban ƙwan. Kuma ki sani wallahi duk yadda kike jin kina son Babangida, kuma shima yana sonki, fashewar ƙwannan zaki yi mamakin yadda zai raba aurenki da Babangida babu zato babu tsammani. Ni kuwa kinga a daidai wannan lokacin ma nafi son ƙwan ya fashe ƙila ba saimun shiga kotu ba salin alin zai bani takaddata in wuce gidanmu. Ke kuwa nayi imani kinfi son zama dashi fiye da komawa gidan ubanki. Kina nan a gidannan babu rabuwa a tsakaninku. Gaki ga Babangida wallahi kinji na rantse babu kaffara akwai wata rana da zata zo, wacce ko sunan Babangida baza ki so jin an ambata ba. Ke a tunaninki wai butulci kikai mun, ko kuma kin haɗe kai da Babangida domin ku sake cusgunamun, alhakin baki san kanki kika kashe ba. Kinga takani da cin kashin da Babangida yayi mun sai yayi miki wanda yafi nawa munanan ranar zata zo. Labbai gareki ki fitarmun da wannan shegiyar a ɗakina. Ko kuma wallahi in farke mata ciki" Na dubi Labbai tare da sake faɗaɗa murmushina. Ai kuwa dama me neman ayi ce dama Labbai tana mikewa ta daki ƙirjin Ƴar Shuwa. "Ke ƙaramar karuwa ƙaramar ƴar balaja'u zaki fita ko saina rungumeki mun kashe juna." "Bazan fita ba ni da gidan mijina. Wannan part ɗin nawa ne da zaran Sabuwa ta bar gidannan" Dariya nayi na nufi kitchen ɗina na zaro wuƙa mai kamar adda wacce ake sara kaza ko jan nama, ina huci na fito ina ciccije bakina dan tsohon tsumina na daba ne ya tashi. Ina fitowa da dai Ƴar Shuwa taga wuƙa kuma sarai tafi kowa sanin wacece Sabuwa, tasan maza da mata nawa na sassara a gabanta. Babu shiri ta fita a guje nima na take mata tana gudun ceton ranta, ina gudun cin mata. Ƙasa na sara inda ta ɗauke ƙafarta take wajen yayi wani irin tartsatsin wuta. Da mahaukacin gudu ta faɗa part dinta. Ƙaramar ƴar balaja'u kawai kika ce bakya ji. Ni daku da duk wanda zai kawo mun iskanci mu zuba na dawo asalin Sabuwa ta wacce ake tsoron nuna ma yatsa" Labbai ta jijjiga kafaɗata tace. "Baki taɓa burgeni irinna yau ba Sabuwa, naso ki sari ƙugun matsiyaciya gaba bata iya haihuwa da kanta ba." Ciki muka koma labbai ta shiga aikin girki, ni kuma ina kwance ina numfasawa sama_sama har ta gama mukai wanka kana muka kama hanyar asibiti. Dama da shirina tsab na tafi duk wacce ta nuna mun yatsa saina ɓallashi abinda ya tafasa ya daɗe bai ƙone ba. Wuƙa na soke a ƙuguna duk shegiyar data nuna mun yatsa saina sareshi. Da tambaya aka nuna mana ward ɗin maza muka shiga. Anan muka ga gungun abokan Babangida sun zo dubiya, sai Ramadan dake jinyarshi. Dukkansu babu wanda baiyi mamakin ganina a asibitin ba. Kunu nasha nayi kamar bansan Allah yayi ruwan tsaron kowa a wajen ba. Sai mamaki suke yi, da girgiza kai gayyar marasa kamun kai kawai. Ramadan ne ya miƙo mun kujera na karɓa na zauna ina ciccije bakina MRS BUKHARI

Sai Allah ya kaimu gobe kuma. #Team Uzairu zuchiyata #Team Maigogul #Team Gaza #Team Sabuwa #Team Babangida kacigari

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955 IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA UKU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955

"Sabuwa ya me jikin?" Jiki ai ku zan tambaya tunda dai zuwana kenan a gabanku ai kuna gani" Da gatsali nayi ma Mustapha maganar. Tsohon munafuki. Babu shiri suka dawo cikin nutsuwarsu. Bashiru ne yace. "Allah dai ya kyauta ya kiyaye gaba. Mujenku zuwa yamma in mun taso wajen aiki mazo" Fita suka yi Ramadan ya take musu. Mtwss ƴan iska gaiyan marasa mutunci. Kinga Waɗannan shaiɗanun abokan nashi su suke sake ingiza me kantu ruwa. Matayensu wahala kab suke sha, gasu da shegen son mata. Dubi yadda Mudassir ya ƙura miki idanu kamar tsowon maye" Baki Labbai ta sake. "Tabbb lallai da ganin idandunansu ƴan duniya ne. Ai bazan mance lokacin bikinki ba irin akuyancin da suka goga mana ba." Shigowar Ramadan yasa mukai shiru. Babangida nake ƙarema kallo a kwance samɓal hannunshi a mugun kumbure ga bandeji naɗe da kafaɗarshi, bakinshi ya bushe leɓennan baƙiƙƙirin sigari ta gama cinyeshi. Isowar Malama Babba da su Kudidi da Naja'atune ya dawo dani daga duniyar tunanin da nake ciki. Malama Babba ta wani kalleni ta girgiza kanta bata ce mun komai ba. Sai Kudidi ita uwar fitsara sai cewa tayi. "Sabuwa bakya ganin Malama Babba ne da ba zaki gaisheta ba. Sannan mema ya kawoki asibitinnan babu kunya babu tsoron Allah? Alhalin kece silar kwanciyarshi a asibiti. Sannan maganar kotu dan baki san menene shari'a ba shi yasa. Mu kanmu kotu zamu maka Gaza wallahi sai mun yi shari'a daku." Har Baba Malam ya iso kanta shi da Kawu Manga Kudidi bata sani ba sai maganganu take yi. Ni kuwa wallahi albarkacin Baba Malam taci yau da saina nuna mata gajanci. Dan harna saka hannu a ƙugu zan zaro wuƙa in tsinke mata hannu sai naga shigowarsu shi yasa na rabu da'ita" "Yayi kyau fetsararriya, ke Kudidi matar wan naki kikai ma tsaye aka kike ci mata mutunci, irin tarbiyyar da Mahaifiyarku ta baku kenan? To yayi kyau. Babba kin kyauta a gabanki ake irin wannan abun. Ko da yake ga Babangida ma ke kika lalatashi. Batun kai karar Gaza kar inji kar in gani" Haƙuri take son bashi dan jikinta har rawa yake yi. Baba Malam ya koɗa mata tafi. Malama Babba itace aka bari da runtse idanu. "Haba Yaya ayi haƙuri dan Allah " "Manga su basui haƙuri ba sai nine zanyi. Ni dasu wake da ikon zartarwa? To wallahi in na sake ganin ƙafafuwanku a asibitinnan saina sassaɓa muku. Abar Babangida matanshi suyi mishi jinya. Duk kuma wanda ya kuma tayar da wata magana zai fuskanci fishina irin wanda bai taɓa gani ba a rayuwarshi. Mata_ matan kada inji labarin wacce tazo. Ƙarama kaɗai na ba izinin zuwa ta duba shi ta tafi, mazan kuwa ko wanne zai iya zuwa" Kawu Manga yace. "Assha Yaya in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Ya kamata a tattara komai a watsar tamkar ba'ayi ba. Malama Babba dasu Kudidi yanzu dai ku zo muje in mayar daku gida." Malama Babba ta miƙe tana huci ta wuce fuu zuwa waje, yaranta suka mara mata baya. Kawu Manga ma ya bisu. Ina wuni Baba Malam?" Na faɗa a mugun sanyaye. Cikin kamalar da ta zame mishi ado yace. "Sabuwa lafiya lau. Allah yayi miki albarka da kika bi umarnina. Kiyi haƙuri da abinda su Kudidi sukai miki zan ɗauki mataki. Shi yaro Allah ya bashi lafiya" Harya juya zai fita ya dawo. "Sabuwa babu waya a hannunki ne, na kira layinki baya shiga. Gashi lauyan dana ɗaukar miki yana son ku gana domin ku tattauna." Wayar tawa faɗuwa tayi ban ganta ba" Jim yayi yana nazari can yace. "Ramadan kaje ka siyo ma Sabuwa waya da sim ka kawo mata. Ka saka mata lambata ta kirani" Cikin mutuntawa Ramadan yace. "To Baba Malam bari inje yanzu ta kula da Yayan" Godiya nayi ma Baba malam. Tare suka fita da Ramadan. Bai jima ba sai gashi da waya Asha harda sabon sim na zain wanda a yanzu ya zama Airtel da can kuma sunanshi Econet. Shi da kanshi ya saka mun sim ɗin a wayar ya kunna. "Gashi Maman Mardiyya. Nasa miki lambar malam akwai kyautar kuɗin kira nera ɗari da suke bayarwa zaki iya kiranshi dashi. Sannan dan Allah kiyi haƙuri da abubuwan dake faruwa" Amsar wayar kawai nayi. Babu komai Baban Amina." Muna cikin haka Hamida da Ƴar Shuwa suka shigo. Mu dasu babu me kula wani. Sai harare_harare nake yi. Ɗigimi har mahaifin Ƴar Shuwa saida yazo ya duba Babangida. Ƙannenta kuwa da mamanta sun jima sosai sune har azahar. A masallacin asibitin mu kai Sallah ni da Labbai. A cikin masallacin na kira Baba Malam yaga number na, ya sake jaddadamun lauyan zai kirani dai. Godiya nayi mishi na kashe wayar muka koma barandar da muke zaune dukkanmu. Muna zuwa muka ga dangin Hamida an taso har mata biyu da wani dattijon da in ba mahaifinta bane, to ƙaninshi ne ko wanshi tabbas. Ni dai cikin mutumtawa na gaishesu suma kuma sun amsa da daraja harma da tambayar me jiki. "Sabuwa ina yini ya mai jikin?" Hmm kunsan wake wannan maganar? Ƙawata Fiddausi wacce itama tare muka taso daga baya ne suka bar layinmu suka yi gini. Har sunan Malama tazo mun, duk matan da Babangida ya aura a baya duk da ita akayi mun dannar ƙirji. Daga baya ne aiki ya mayar da mijinta kaduna ya tarkatasu suka koma sai ya zamana sai dai muyi waya. To ashe itama tana tare da Ƴar Shuwa tunda gashi tazo mata" Lafiya lau Fiddausi jiki da sauƙi" Na faɗa da fara'ata ƙaƙas. "Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne" Ameen" Na faɗa a taƙaice. Ramadan ne ya fito da sauri. "Maman Usama, da Maman Fatima Babangida ya farka yana nemanku" Da sauri suka miƙe suka shiga. Har suna rige_rige Niko da idanu kawai na bisu na taɓe bakina.

Babangida:.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull