Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 3
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 3: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 3. Yana buɗe idanunshi wani irin zafi da tsamin jiki sukai mishi sallama. Idanunshi ya…
4,508 words
Yana buɗe idanunshi wani irin zafi da tsamin jiki sukai mishi sallama. Idanunshi ya runtse kawai yana tuno dukan ƙirjinshi da Sabuwa ta haukace tayi mishi. Hoton fuskar Khalid kuwa abadan bazai gogu a ƙwaƙwalwarshi ba sam. Idanunshi ya runtse tare da furta. "Kin cutar dani Sabuwa kin ruguza mun zuchiyata. Ashe haka nake kishinki?" Furucin daya janyo hankalin Ramadan zuwa gareshi. "Babangida ka tashi, bari in kira likita dan tace daka farka a kirata." Fita yayi yaje ya kira likita, tare ma suka tawo ta shiga dubashi gami da mai tambayoyi. "Yanzu abinda za'ayi shine a nema mishi tea ya soma sha ya warware hanginshi sai yaci abinci. Zai karbi allurai da magunguna. Malam Babangida sannu ko, Ubangiji Allah ya ba da lafiya. Sannan a kula da yawan motsa hannun gudun kada a dawo mana da aiki baya' Tana kaiwa nan ta fita akan in yaci abinci za'azo a yi mishi abinda ya dace." "Ina su Malama Babba da su Kawu Manga duk basu zo bane?" Babangida ya tambaya idanunshi a lumshe, hoton yadda Sabuwa ta faɗa motar Khalid ya shiga tariyo kanshi da kanshi a ƙwaƙwalwarshi. "Sun zo Baba Malam ne yace su koma gida. Kuma yace kada su sake zuwa ma." Bai buɗe idanunshi ba. Kuma baiyi mamakin abinda Ramadan ya faɗa mishi ba. Sai cewa yayi. "Wayata tana hannun waye, sannan ina su Hamida?" "Uhm wayarka inaga tana hannun Yaya Mustapha tunda shi ya kawo ka asibity. Ko ɗazu da safe abokanka duk muna tare anan dazu. Su Maman Usama suna waje harda Maman Mardiyya ma" Runtse idanunshi kam yayi jin an ambaci sunan Sabuwa sai yaji tamkar an watsa mishi ruwan dalma a kwanyarshi. Cikin hucin kishi yace. "Ban yarda a barta ta shigo inda nake ba sam Ramadan. Ka je ka kirawo mun su Hamida su zo" Shine kiran da Ramadan ya fita yayi musu. Suna shiga suka tarar da dabara Ramadan na ƙoƙarin zaunar da Babangida dan yace duk jikinshi tsami yake yi mishi. "Maman Usama dan haɗa mishi tea mai kauri" Cewar Ramadan dake kiciniyar sama Babangida fulo a bayanshi. Tea kakkaura hamida ta haɗa mishi daidai sha inda bazai ƙona baki ba, amman zai dumama ciki. Duk da Babangida baya jn daɗi a zuchiyarshi da ruhinshi, da gangar jikinshi hakan bai hanashi shanye tean matanshi nata aukin yi mishi sannu ba. "Sannu Jannaty. Naji mummunan labarin abinda ya afku. To ni dama na ɗauka ta dena bin maza ne tunda nayi mata faɗa a baya sosai" Wani mugun kallo Babangida ya feso mata wanda saida yasa cikinta ya ɗuri ruwa. Gashi dama amfani take so tayi da wannan damar ta yima Sabuwa sharrin da dole ma ta bar gidan Babangida. "Au munafuka ashe ke daman kinsan maza take bi shine kika rufa mata asiri? Ohh wato ke kika ɗaure mata baya tabi maza da aurena ko? Wallahi harke bazan ƙyale ba ke da Sabuwa saina ɗaureku har igiya sai tayi saura. Tare zan koreku ai in dai Sabuwa ta bar gidan kema ba zama zaki yi ba maras mutunci. Shi kuwa farkan nata kasheshi zanyi da hannuna. Zan yi maganinku duka. Wallahi ba'ayi komai ba akan Sabuwa zan iya mutuwa" Babangida da ihu da faɗa yake maganarshi. Wata ma'aikaciyar jinya ce ta karaso" "Amm kuyi haƙuri kuje daga waje sabida ba'ason mara lafiya a dinga faɗa mishi maganar da zata ɓata mishi rai. Bakwa ganin halin jinyar da yake ciki ne? Da Allah kuje waje" Ta faɗa a wulaƙance. Ƴar Shuwa sai zufa take sharewa allura na neman tono garma. Jikinta a sanyaye ta fita zuchiyarta cike da tunanin mafita. Gami da mamakin kalmar da yace akan Sabuwa zai iya mutuwa. "Kenan yana sonta dama?" Wannan amsar har Hamida ita suke ta son ji. Hamida na biye da'ita har zuwa barandar da suke zaune" "Iskanci kawai. Ƴar iska ashema tasan tana bin maza bata iya faɗa mun ba. Kenan ita ta bayar da ƙofar ayi iskancin ma? To zan kuwa kaɗasu tare kenan in huta dan wallahi itama ta fita a kaina." Idanunshi ya rufe wasu hawayen mugun kishi da baƙin ciki ya biyo gefen fuskarshi ya zubo siriri dashi. Farfesun da Sabuwa ta dafo mishi na kayan ciki shi Ramadan ya zuba mishi. "Bazanci ba tunda dai ba dole bane kaji ko?" Kafin Ramadan yace wani Abu sai ga Kawu Manga tare da Wawo da Jibrilu sun shigo. Kai da ganin fuskokinsu kasan cike suke da damuwa mai tarin yawa. "Babangida ka samu ka tashi kenan? Gara da Allah yasa idanunka biyu domin kaine kaɗai zaka iya warware mana wannan ƙullin ko zamu samu nutsuwa." Cewar Kawu Manga dake dafe da kan Babangida. "Na farka Kawu. Kaga abinda wan Sabuwa yayi mun akan gaskiya ta ko? Bazan bar maganarnan ba gaskiya Kawu." Wawo yace. "Kaga duk ba wannan ba. Al'amarin fa daya tunkaroka al'amarine mai girma. Shin kasan Alhaji Abubakar Baban Bola dai ko, sannan kasan da maganar dukiyarshi dake hannunka? Muna son ƙarin bayani, dan yanzu haka maganar tana kotu" A mugun razane yake kallon Wawo zuchiyarshi da kanshi a lokaci guda ya buga. Ma'aikaciyar jinya ce ta karaso wajen tare da katse musu hanzari da cewa. "Dan Allah ku ɗan bamu waje, zanyi mishi allura kuma zai sha magani, ba'aso ya fiye yawan magana sakamakon jininshi da ya hau." Kawu Manga yaima Ramadan da Wawo nuni da su su fita. A sanyaye suka fice. Kawu Manga na tsaye ƙyam yana kallon yadda jikin Babangida yake rawa, ita kanta ma'aikaciyar jinyar abun karfinta yafi a guje taje ta kirawo likitan da yayi aikin dare suka dawo tare. Aunashi yayi jininshi ya yi mugun hawa fiye da kima. Allurar gaggawa akayi mishi bacci ya debeshi luu. "Uhm Baba akwai wani abun da aka faɗama mara lafiyanmu wanda ya ɗaga mishi hankaline?" Kawu Manga ya sharce zufar data keto mishi yace. "Akwai Dr karayar arzikice ta sameshi" Idanu Dr ya ɗan runtse yace. "Ashsha na tayashi jimami gaskiya. Amman Baba ai asibiti ba wajen tattauna ire_iren waɗannan maganganun bane. In akayi la'akari da irin halin da shi marar lafiyan yake ciki. Nan gaba a kiyaye hakan dan Allah. Yaci abinci ne daman?" Saida ya kuma ajjiyar zuchiya dan ya riga yaga amsar da suke son ji daga yanayin Babangida tabbas komai ya tabbata duk da dai ga saka hannunshi nan akai. "Sai dai a tambayi Ramadan shine ya kwana dashi" Wayarshi ya ɗaga yayo kiran Ramadan. Yana ganin kiran sai bai ɗauka ba ya garzayo da sauri. "Mara lafiyanmu yaci abinci ne?" Dr ya kara tambaya a karo na biyu. "A_a ya dai sha tea amman da kauri. Abincin na zuba nayi nayi yaƙi yarda yaci" "Ok babu damuwa tunda ya sha tea. A kiyaye domun ba'ason hayaniya. In so samu ne duk kuyi zamanku a waje dan Allah ba sai kun shigo ba, mu zamu dinga dubashi" Tare suka fito da Dr daga ɗakin. Wawo ne ya nemi a sake ma Babangida ɗaki, a saka shi a I P U nan da nan aka maidashi abinka da kuɗi harma kulawar da ake bashi aka ninka.
SABUWA:. Mu dai muna ta zaune mu na ɗan taɓa hira da Labbai. Daga shigarsu Hamida wajan Babangida har fitowarsu, kama zuwansu Kawu Manga da fitowarsu, da sake ma Babangida ɗaki duk ina zaune ina buga lissafine kawai. Bamu muka bar asabitin ba har saida muka yi isha, muka tattare kwanukan abincinmu wanda Ramadan ne kaɗai yasha farfesun mukai musu sallama muka tafi. A nan muka baro Kawu Manga da Wawo. Hamida,tun yamma ta dawo gida ita da baƙinta. Ƴar Shuwa da ƙannenta ƙila nan kwana dan naga basu ɗaura haramar tawowa ba. Ko da muka shiga gida munyi tulis da gajiya tara da kusan kwata muka shigo. Mardiyya ce ita kaɗai a zaune a falo tana ta karatun Alqur'ani. Tana ganinmu ta miƙe. "Ummi kun dawo. Ya jikin Baba" "Jikin Babanku da sauƙi. Ina su Aɗɗa'u?" Labbai ta bata amsa. "Allah ya ƙara sauƙi. Su Aminu tun ɗazu sukai bacci. Ummi ɗazu Aɗɗa'u daga zuwa masallaci yabi abokanshi rafi da daddare da ƙyar muka ganshi. Dana dakeshi shine ya zageni" Kai kawai na girgiza wannan yaro baya ji sam. Kullum ina mishi adda'ar shiriya. Hmm barni dashi gobe da safe zaki ga yadda zamu kwashe. Kije ki kwanta muma a gajiye muke." Sallama tayi mana ta wuce ɗakinsu. Ni na wuce ciki kai tsaye zuwa banɗaki dan in watsa ruwa ko zanji daɗi, Labbai kuma kitchen ta nufa dan ta sama mana abinda zamu ci. Ina zaune ina shafa mai wayar da Baba Malam ya bani ta soma ringing. Nadai san lauyan da akace zai kirani ne. Dagawa nayi da sallama a bakina. "Ameen wa alaikis salam. Sunana barrister Ahmad Ahmad. Ina magana da Sabuwa ne wacce ta shigar da ƙarar mijinta tana neman ya saketa?" Idanuna na lumshe a hankali wani irin zazzaɓine yake hudani sosai. E nice ina wuni?' Na bashi a takaice. "Lafiya lau. Gobe inaso ni dake mu haɗu dan mu tattauna dangane da Shari'ar da zamu soma. Sabida musan yadda zamu bullowa lamarin dan shari'a a tsakankanin mata da miji sharia ce mai rikitarwa. Inason jin jawabai daga gareki." To Shikenan a ina zamu haɗu, ko zanje gidan iyayena sai ka sameni acan. A unguwar Zai suke" "Yauwa hakan yayi. Kije zanzo da misalin karfe takwas na safiya sai kiyi iya ƙokarinki kafin lokacin ki rigani isowa." A haka muka daddale na sauke wayata. "Kixo muci abinci. Indommie da dafaffen ƙwai na dafa mana sai tea" Bakinta cike da ƙwai take maganar. Ni tean kaɗai na sha na watsa magungunana. "Lolo na fahimci kamar bayan ciwon Babangida kamar akwai wata matsalar kuma. Amman ke me kika fahimta?" Ta kafeni da idanunta tana son taji ta bakina. Toh ni nafi tunanin ciwon nashi ne, ko dalilin ciwon nashi. Amman banyi tunanin wata matsala ba" "Amman da gaske ne Lolo da wano Babangida ya kamaki, ko dai baƙin zargine da jan kishi dake damunshi?" Numfashi naja tare da cewa. Da gaske ne Labbai. A mota yaga an saukeni da ledar shopping. Iyakar abinda kaɗai ya gani kenan" Tambaya take son sake jefo mun na katseta. Dan Allah ki barni inji da abinda yake damuna. Koma menene aurenmu yazo ƙarshe ko ya ganni ko bai ganni ba ba shikenan ba?" Gado na haye na rufe idanuna zuchiyata da jikina nata muƙurƙusata. Bansan sanda nayi bacci ba. Zage_zagen da Labbai naji tana ta yi a wayane yasa na farka naga gari har yayi shaa. Da sauri na shiga banɗaki na ɗauro alwala sabida tsabaragen jarabar da take ta faman yi a waya ni dai sai a ɗakin yara nayi Sallah. Su kuma sunata wanka da shirin makaranta. Sai kallonsu nake yi ina tausaya musu. Bansan yaya zasu fuskanci rayuwa ba, ban kuma san wacce iriyar rayuwa zasu yi bayan bani a tare dasu ba. Ban kuma isa cewar a bani yarana ba, domin nasan Babangida na da hujjojin da zai gabatar a kotu yasa a hanani riƙon ƴaƴan. Nima ina cikin damuwa da tsoron kada in riƙesu tarbiyyarsu ta lalace duk da bazan iya rayuwar gidanmu ba nafi son in kama haya in zauna ko zan nutsa. Aɗɗa'u zo nan" Na faɗa da murya mai kauri. Da sauri yazo wajena dukanshi nayi niyyar yi, hannuna daya kama yasa zuchiyata tayi sanyi abinka da uwa. Wato jiya dan bana nan shine Aɗɗa'u kayi tafiyarka yawo har saida aka nemoka ko? Sannan ka zagi Adda Aɗɗa'u na roƙeka da girman Allah kabi Allah kabi duk abinda Adda zata ce maka ka ɗauketa tamkar uwa. Har da kai Aminu, dake ma Malama da kike muttsuka idanu." Duk sai akai dariya baki ɗaya na dinga yi musu nasiha. Kafin na miƙe na fita zuwa kitchen dan anan na jiyo ɓuruntun Labbai. Doya da ƙwai take ta soyawa. Tana yi tana ɗure_ɗuren ashar harda sharar hawaye. "Se me dan kace in yi zamana a gidanmu. Ni da sakina kayi da yafi mun ɗan gidan taƙi zama ta zauna kawai. Ke kiji mun wannan maras mutuncin Habu, daga na ɗan tambayeshi kuɗi nera ɗari biyar fa. Shine ya zage ya shiga yi mun ɗiban albarka, har yana cewa in zauna a gidanmu in ubana ya koya mun tarbiyya na koma. In kaya ya gaji gammo ma ya gaji. Babu inda zan koma sai dai ya aiko mun da takaddata dukan ya isheni. Nifa yanzu in ba mai kuɗi ba bazan kuma aure ba. Jibeki ko dukanki akeyi zaki ci kuka ki toya ƙwai ki kunna ac ga tv ga suturu. Mufa a dakemu mu fito mu tuƙa tuwo miya lami, da safe kokkone ko sigari babu wacce take da kuɗine zata sai masa, kosai, ko ƴar tsala fa" Dariya na kwashe dashi, itama dariyar ta saka. Ke dai yi maza ki sallamesu, mu ki juye mana namu a kula maci a gida sauri nake yi kinga har bakwai tayi. A gurguje muka gama komai muka fito tare da yaran Karfe takwas saura minti goma muka isa gida. Nanma muka tarar maigogul yana yima su Rakiya tujarar daya saba. Duk suna tsaye ya faɗa su da faɗa, Rakiya ta zageshi tas. Wani abune ya tokareni a wuyana banko kallesu ba nayi shigewata ciki. Su Sadiya duk suna ciki sunata karyawa harda Uzairu zuchiyata. Da magazin. Ko wanne cikinsu da abinda yake ci, dan kowa da kudinshi ya siya. "Labbai kafin ki zauna zo ki karɓo mun waina" Cewar Rakiya data leƙo. "Ga ƙwai da biredi da doya Rakiya zai ishemu ki shigo" Ƙwafa tayi ta shigo ta baro Maigogul da Hauwa suna ci gaba dayi. Mu kuma muna karyawa su Sadiya sunata hirarsu. Uzairu zuchiyata yace. "Ashe dambarwar tsiyar da akayi kenan ke Lolo? Uhm ai wallahi Gaza yayi mun daidai. Allah ne ma ya so shi bama gidan wallahi da raunin yafi haka." Magazin yace. "Wanne rauni? Ai kasan Allah da ace inanan to sai dai gawarshi. Nifa da har ubanshi daya tako gidannan saina tsinke mishi agara Allah" Danna ƙwai yayi a bakinshi wanda ya gutsura a cikin kular gaban Labbai. "Ai ƙarshenta Rakiya a gidan gyaran hali zata ƙarke rayuwarta in dai bata dena wannan shegiyar sana'ar kayi nayin ba. Mata sai sayen kayan sata" Tana jin Maigogul ya faɗi haka zuruf ta fita dawa Allah ya haɗata in ba dashi ba. Uzairu zuchiyata a guje ya bita yana aikin dariya. Nidai lauyana daya kirani na rakici Labbai nace tazo muje. A lokacin da muka fito har gidan ya soma ɗinkewa da maza da mata ƴan ban hakuri maigogul ya tuɓe rigarshi ya doka da ƙasa zai doki Rakiya, ita kuma anata riƙeta akan yana dukanta zata rama. Ficewa muka yi a wajema matan unguwa duk an firfito anata gulma harda mahaifiyar Ƴar Shuwa. "Mutanen banza gida sai kace karnuka. Ni na taɓa ganin jahilai irin wannan gidan kuwa? Kamata yayi wallahi a koresu a wannan unguwar domin zasu lalata mana tarbiyyar yara" Allah sarki inji mahaifiyar Ƴar shuwa kenan fa. Wai me bunu a ƙunƙuru ke kai gudunmawar gobara. Wacce kalar karuwace bata da'ita a gidan nata. Su kansu masu gulmar ko wanne nada guntun kashinshi, sai dai dake ance lefe tudu ne, kahau naka domin kayi leƙen na wani. Allah dai ya basu sa'a dan Magazin zai iya fitowa nasan ya watsasu. Wani mutum ne naga ya fito daga farar motarshi, yana saye da surt baƙaƙe da baƙin gilashi, ya nufomu. Nanfa kallo ya koma kanmu gulma a kyauta. "Kece Sabuwa ko?" Ya tambaya yana nuna ni da manuniya" E nice sannu da zuwa. Ga dakali mu ɗan gangara mu zauna" Na nuna mishi dakalin ƙofar gidansu Babayo muka ƙarasa muka zauna, muka sake gaisawa. MRS BUKHARI
Sanya
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA HUƊU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾 Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽 08093932955
"Zanso insan menene dalilinki na shigar da ƙarar mijinki ya sake ki, shin wanne hujja kika riƙa a matsayin babban dalili, sannan in ba'a kotu ba bazai iya sakin ki bane?" Kaga lauyoyi duka wannan tambayoyin lokaci guda aka watso mun. Kuma ya kafe ni da baƙaƙen idanunshi yana jiran amsa. Dalilin da yasa na shigar da ƙaran shine bana sonshi, duk kwanan duniya ƙara tsanarshi nake yi. Hujjata shine. Ya dena ciyar damu, baya shayar damu, baya mana sutura, baya biyan kuɗin makarantar yara, baya mu'amalar aure dani. Sannan tambayarka ta uku tsawon shekaru sama da goma ina faɗin ya sake ni yana cewa ni dashi mutuwace zata raba, kuma badan yana sona ba sai don mugunta kawai" Kanshi ya jinjina yace. "Yana cin zarafinki ne, ko zarafin iyayenki, sannan yana dukanki ne?" Babu wanda bayayi daga cikin abinda ka lissafo. Babangida ya wuce tunaninka, wata iriyar baƙar zuchiya gareshi." Shiru yayi yana nazari can ya jefo mun wata tambayar. "Auren dole kuka yi ko Auren soyayya kuka yi?" Bazan ce auren dole ba, ba kuma zance auren soyayya ba. Babangida yayi mun irin soyayyar da babu mahalukin da zai iya yi mun ita a duniya. Daga baya ne komai ya lalace. Amman karka tambayeni dalilin lalacewar domin bata shafi shari'ar ba" Murmusawa yayi kawai kafin yace. "Iyayenki suna bayanki ne akan shari'ar kamar yadda Baba Malam yake bayanki?" Kai na girgiza nace. A_a basa bayana kona misƙala zarratin." Mijin Labbai ne yazo ya wuce mu, Labbai tayi tsaki ta bishi da harara. Barrister Ahmad Ahmad yace. "Baba Malam menene halaƙarshi dake?" Shine mahaifin mijin nawa" Har a jikinshi saida mamaki ya bayyana ba'a iya fuskarshi ba. "Ban gane ba. Kina nufin ɗanshi kika maka a kotu kuma ya ɗaukar miki lauya, yake ta jaddadamun inji tsoron Allah in yi iyakar yina a ƙwato miki hakkinki Babangida ya sake ki?" Tabbas mahaifinshi ne" "Toh Malama Sabuwa ni zan wuce in ma akwai wata tambayar zan bugo miki waya saimu tattauna. Ki kuma zauna da shirin fuskantar Shari'a ki sani kuma saɓanin hankalice, tamkar macece da ciki, kinga sanin abinda zata haifa sai Allah. Na barku Lafiya" Ya miƙe da sauri ya tafi. Nayi shiru a zaune a dakalin Labbai tace. "Wai kinsan tunda kuka fara magana da lauyannan ƙannen Ƴar Shuwa da mahaifiyarsu suke ta faman sunturi kuwa?" Baki na taɓe nace. Ina ganinsu sunata wucewa kamar ƙawayen Amarya. Naga Malam Habu ya wuce" "Malam ko buzuzu? Dallah tashi mu tafi ni. Aurene ni dashi ya ƙare" Ashe yana tawowa duk abinda Labbai tace a kunnenshi. Yana ƙarasowa buɗar bakinshi sai cewa yayi. "Aure kam ya ƙare, domin ni ba lusari bane da zan zuba idanu ina kallonki da aurena kina bin maza kamar yadda aka kama Sabuwa ba, yanzu ma ba gashi na kama ku ba. Na sake ki saki guda, dama dai kwaɗayine irin namu na maza shi yasa na auro karuwa" Naji zafin maganganun Malam Habu sosai. Musamman karuwa daya cema Labbai. Kafin in ankara Labbai ta cukumeshi tana ihu tana kwaroroto. Wallahi kafin ƙiftawa da bismillah sai ga jama'a sun taru. Malam Habu ya dinga cauɗama Labbai carbi yana jefo manya manyan maganganu marasa daɗin saurare a kanmu. Sama da ƙasa Allah baisa na iya cewa komai ba. Cikin munafukan da suka taru na kutsa na fincike Labbai a wuyan Malam Habu na jata kiyyy har cikin gida. A lokacin ƙurar cikin gidan ta lafa, Rakiya ma wanki take yi, Hauwa na kwalima. "Wai menene dama daku ake hayaniya ne Labbai. Ni naji matan Malam Habu sunata ɗuma zagi ta katanga. Kafinma mu bada amsa muka jiyo zagin. Turmi Labbai ta hau sukaita zagi in zaga da iyalan gidan Malam Habu ta karanga Da ƙyar na fige Labbai muka shige ɗaki. Yaran gidan sukaita jifa daga gidansu zuwa namu. Dawowar Gaza yasa komai ya lalace. Yana shigowa aka jefo ƙaton dutse ya sauka a ƙafar Rakiya. A guje ya shiga gidan Malam Habu, Labbai ta bishi da gudu da wuƙa a ƙugunta. Hmmm abu dai babu arziki duk matan gidan shigewa ɗaki sukai suka kulle. Gaza ya saka ragunan Malam Habu gabas ya dinga yankasu. "Ƴan abu ta kazan uba. Ku shiga ku ɗebo kayanku mu tafi. Yasin duk matar da muka haɗu a hanya sai dai ta canja hanya in ba haka ba saina farɗeta." Haka mukaita jide kayan Labbai muna ficewa dashi. A guje Rakiya ta shigo. "Gaza matsa dale katanga ka wuce ga Malam Habu da kwalawa. Take katanga maza" Ragunannan daya yanka ya suri biyu ya yaɓa a kafaɗa suna yararin jini ya haye turmi ya dire bayan lungu. Yana direwa kwalawan na shigowa a guje. Jin muryoyin ƴan sanda yasa iyalan Malam Habu fitowa. "Kaga ta'asar da yayi mun ko? Yallaɓai ku wuce da waɗannan matan dukkansu, kuma wallahi sai an biyani ragunana raguna kusan takwas a yanka mun su sabida rashin tarbiyya Gude a mayar mun da kayan Labbai ciki" "A_a Malam ka rabu dasu kawai tunda dai mai rabawa ta raba. Wallahi ina jiye mana bala'in da zai biyo baya. Ni dai Malam ka dangana kawai. Tunda kai ka yayiɓo mana dama yaran gidan farare. Meye bamu faɗa maka ba? Kar ka bari a tafi dasu, muna da yara mata kada Gaza ya turo yaranshi sui ma yaranmu fyaɗe a banza da wofi" Tana faɗan haka sai jikin Malam Habu yayi sanyi. Take yaja ƴan sandannan waje, ya suka ƙare sai Allah. "Labbai maza kwashe kayanku ku tafi" Cewar Gude da ciki ya ɗuri ruwa. Rakiya tace. "Ai ba sai kince ba. Wallahi kinyi ma kanki Alamnashara Gude da zaman unguwarnan ya gagareku.Yanzunma sai fa mun so rigimarnan zata lafa. Labbai ku kwashe kayan mu wuce miji goma ba uba goma bane. Ku ɗakko mana ƙatuwar tinkiya in dai da Bismillah ya yanka" Dukkanmu muka haɗu muka kwashe kayannan Labbai kuwa saida ta kinkimi ƙatuwar tinkiya ta fice tana ta zage zage unguwa ashe ta cika ta batse sosai da sosai. Ohhh Allah rayuwarmu tana cikin garari. Shin haka rayuwarmu zatai ta tafiya babu sauyi ne?" Muna shiga gidan muka tarar Adama tazo tana zaune da takadda akan kujerar tsugunno tana gani munata shigo da kaya babu wanda ta kula. "Adama ke kuma fa wai?" Cewar Uzairu zuchiyata daya jingine katifa. "Hmmm kai dai muje daga ciki tukunna" Ta bashi amsa tana shigewa. Tare muka ɗunguma muka shiga ɗakin duk ƴan matan basa gidan dakin kaca_kaca babu shara, kwanukan da suka ci abincinma duk yana baje a tsakar ɗakin. Ga uban suturu a a ƙasa. "Adama wannan wai takaddar asibiti ce, ko kema dai sakin naki akayine duk kika wani yi laushi? Allah na tuba da irin wannan aure ba gara zawarci sau dubu ba? Jebakki fa fara sol wanke hannu ka taɓa" Rakiya ki dena ɗaga murya na jiyo muryar Layuza a tsakar gida " Ƙasa Rakiya tayi da muryar. "Ai Qamriyya ce yau za'a kawo sadakinta da kayan Aure, wani baƙauyen zai kwasa." Baki duk muka taɓe. "Ni ba wannan ba Rakiya sakina Baban yara yayi fa in faɗa miki har saki biyu. To kinsan a baya saki ɗaya ya taɓa yi mun. Yau kwana goma cib da sakin da na saka rigimar sai dai in zauna inyi zaman Ƴaƴana wallahi yau dai a guje da bulala ya rakoni, kun ganni sai makwabta ne suka bani takalmi da mayafi. Nazo na tarar anata rikici da mijin Labbai " Ni dai take kaina ya hautsine hawan jinina ya tashi sabida damuwa. "Hmmm ai Shikenan ke da Labbai duk auren naku dai ya tsinke. Ga dai filin tsakar ɗakinnan du ya ishemu, ga wannan mitsiyaciyar itama Auren nata take so ta kaso. Duk ku dawo kuzo mu zauna ciwon zuchiya yai ajalina ga baƙin cikin Maigogul ga naku." Tana faɗan haka ta sau kukan da nayi imani sabida aurenane da zan kashe ba dan mutuwar auren Labbai da Adama ba. "Rakiya ki dena kuka kada su Hauwa su jiyoki burinsu a kullum bai wuce su gammu a ƙasa ba" "Ke dallah su gammu a ƙasan mana ai babu da abinda Hauwa ta isa goranta mun babu iriyar ƴar iskar da bata dashi a ɗakinta. Sama ne ya leƙo ɗakin Rakiya kina ciki, Adama Sabuwa kune a gidan?" "Ahh Sama ai kai zamu tambaya kaine a gidan, wai Sama ina ka shige ne?" Cewar Adama kenan. Shigowa yayi da ƴar ledar kayanshi ya nemi waje ya zauna. Duk yabi ya lalace "Ina can kasashen inyamurai neman kuɗi Adama. In ka biye ta gidannan da rikicin gidan ina mai tabbatar miki likkafanin da inka mutu da tabarmar da za'a saka daga ƙarshe nema za'ayi a rasa in dai gidannan ne. Ya kuke ya yaran naku?" Duk muka amsa mishi da lafiya, Rakiya kuwa tagumi tayi. "Wai lafiya kuwa?" Kafin a bashi amsa saiga Hauwa ta buɗe labule. "Wai yau muryar wa nake ji kamar Sama'ila dama kana duniyarnan. Yaushe da rabon mu saka a idanunmu?" Kai ya ɗan sosa. "Wallahi Hauwa balaguro kawai nayi. Na shiga duniya neman kuɗi" Haɓa ta riƙe tace. "Kuma wacce sana'ar ka kama Sama?" Harara Rakiya ta zabga mata harda jan tsaki. "Bige_bige ne duk abinda na kama yi nake yi. Amman kamar dai lokacin kirsimeti ina zaga garuruwan inyamurai ina tallen balambalo" Sai da Hauwa tayi dariya kafin tace. "Ai yafi maka zaman banzan. Kaga ƙaninka ma mijin Layuza ya kaishi shagonshi dake kasuwa yana taya shi aiki." Sama yace" "Wai ma'aru kike nufi shine aka saka a kasuwa. Yaron da ko ɓera bai kaishi sata ba? Kai Hauwa nifa ina tsoron kada yaje ya kuntaka mishi sata azo ana raba hali" Ai nan Hauwa ta shiga zage_zage haka ta saki labule. Sama kuma ya suri ledar kayanshi yakai ɗakinsu na langa_langa yayi ficewarshi. Yana waƙe_waƙe. Shi sabida tsabar shaye_shaye bama saka shi a lissafi dan ba kullum yake da hankali ba. Wataran ma sai a wayi gari dashi yaita danna ihu shi kaɗai ƙwaƙwalwar ta riga da ta taɓu. Ga ƙazanta a cikinshi kamar me. Wayata ce tayi ruri Baba Malam ke kirana. Da sallama na ɗaga muka gaisa. Sai yake tambayata lauya yazo kuwa? Nace mishi yazo yanzu ma gida nake son in koma bana jin daɗi sai zuwa yamma ko gobe zani asibiti. Da haka mu kai sallama na ajjiye wayar. Labbai taso mu tafi ni zazzaɓi nake ji gashi ban tawo da magungunana ba." "Bari in biyo ku nima Rakiya sai mun dawo kawai" Cewar Adama data miƙe. Rakiya ma miƙewa tayi. "Nima zan fita nema banci ta zama ba hantsi yayi. Kayi nayi yanzu aka soma" Tare muka fice mu makai titi, Rakiya tayi saman layinmu sana'ar kayi nayinta. Muna isa gida na kwanta a kujera sai Labbai ce ta bani magungunana na haɗiya naji dama dama. "Yanxu bari in ɗaura abinci ki daure zuwa yamma sai mu tafi asibitin ko minti goma ne muyi sai mu dawo" Kai kawai na ɗaga ma Adama, dan idanuna a rufe suke suna fitar da hawayen ciwo ga magungunan sun soma ɗibana."