Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 19
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 19: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 19. Baba Malam:. Da duk irin halin da yake ciki jin an ambaci Babangida yazo yasa ya…
2,427 words
Baba Malam:. Da duk irin halin da yake ciki jin an ambaci Babangida yazo yasa ya shiga ɗaga hannu yana girgizawa. Yana nuna halamar baya son zuwan Babangida.Wawo ne ya matsar da kunnenshi saitin bakin Baba Malam. A hankali ya ɗago. "Malama Babba inaga ki koma gidan Kawu Manga ki kwana kawai. Zan sa Aliyu yaje ƙofar gida ya tari Babangida kada ya shigo. Da dukkan halamu baya son ganinku ne" Malama Babba ta fashe da kukan da yaci ma ace hawayenta ya ƙare izuwa yanzu. Yau a gaban kishiyarta da take ganinta ba a bakin komai ba Malam yake nuna baya son ganinta da Babangida yaron da yafi soyuwa a zuchiyarta? Ko da yake babu mamaki tunda har Malam ya iya korarsu, babu abinda bazai iyayi bama. Malama Babba sabida ƙin gaskiya da soyayyar uwa da Ɗa data rufe mata idanu. Da gaske tana kallon Sabuwa a sababin faruwar dukkan kunci, da tarwatsewar ahalinsu. Ada gidansu gidane da suke gudanar da rayuwarsu gwanin kyau gami da sha'awa. Shigowar Sabuwa shine silar rushe farin cikin wannan ahali, shine sababin haifar ma da zukata ciwon da abadan babu mai warkewa haka zalika tarihi zai ci gaba da maimaituwa a tsakankanin Ƴaƴa da jikokin wannan ahali. "Wallahi babu inda zani. Ni yafi cancanta in zauna in kula da Malam tunda nice Babba a cikin gidannan" Ta faɗa da rushin kuka. "A_a Babba" Cewar Malama Karama. A tsawace Malama Babba ta dakatar da'ita ta hanyar ɗaga mata hannu ba tare da tace komsi ba. Likit ne ya shigo tare sa Ilyasu. "To inaga ku mazan manya zaku iya tsaiwa. Ragowar dan ALLAH muna son su bamu waje. Hatta waɗanda suke dokin ƙofa in da hali su tafi dan ALLAH " Faɗin Dr kenan dake zaro kayayyakin gwaje_gwajenshi a akwatinshi na likitoci. Ficewa su Malama Babba suka yi dukkansu. Kawu Manga da Wawo ne kaɗai a ɗakin sai Malam dake cikin wani yanayi. "Wawo bari kaga inje in kaɗa Babba ta koma can gidana, kuma shi kanshi Babangida a tare shi. Ni dama nasan Yaya zai hana da ban kirashi ba wallahi " "Ai gara daya sani wala Allah yayi haƙuri da jajiɓo mana ababen kunya" Kawu Manga yayi murmushi akwai a zuchiyarshi yana girmama girman taurin kai da rashin shayi irinna Babangida. Ta ɓangare guda kuma yana tuno irin titsiye Malam da akayi ɗazu a kotu da girmanshi da komai wanda wannan titsiye shi ya ja mishi wannan ciwon. "Babba muje in rakaki gidana, kada kice komai a yanzu samun lafiyar Yaya itace a gaban kowa ke dai tawo" Bata da zaɓi dole tabi bayanshi. Ai ko suna fita acaɓar su Babangida na isowa. Malama Babba ta ƙurama Babangida idanu ba tace ga tunanin da take yi ba. Jiki a saɓule ya ƙaraso inda suke. "Yauwa Babangida riƙeta kuje can gida ku jiramu acan inaso in koma wajen Yaya" Babangida bai tambayi daliliba ya riƙe hannun Malama Babba suna tafe tana kuka mai gunji. Wannan kukan ba ƙaramin ƙone zuchiyar Babangida take yi ba. Yasan san dai silarshi duk wani abu yake fitowa daga haularsu a dalilin son kai da son zuchiya irin nashi kaico. A babban falon Kawu Manga akaima su Malama Babba masauki. "Kira mun sa'a tazo Babangida ku kaini asibiti" Da mugun sauri ya miƙe. "Bari in kira Ramadan ko Wawo ya bani keyn motarshi in kai ki" Bai jira abinda zata ce ba yayi yinƙurin fita. "A_a Babangida kada ka shiga cikin gidannan. Ka kira Sa'a kurum ni dai umarnin dana baka kenan." A sanyaye ya dawo ya zauna yana jin mashasshara. Sai da ya kira Sa'a sau huɗu ana biyar ne ta ɗaga. "Babangida lafiya a darennan. Ko dai wata rigimar ka sake rikitowa? kasan kai kam akuyarka tayi kuka" Sai da ya haɗiye wani irin yawu mai ɗaci da ƙyar ya iya sarrafa harshenshi yace. "Malama Babba ce tace kizo. Muna gidan Kawu Manga " Jin abinda ya faɗi ai tuni ta wattsake tasan ba lafiya ba. "Ganinan ina zuwa, bari in taso Baban yara ya kawo ni" Tana faɗin haka ta datse wayar. Malama Babba sai nishi take yi Babangida na riƙe da'ita matan Kawu Manga na yi mata fifita har Sa'a ta iso. Gashi taƙi fur a sanar ma su Kawu Manga halin da ake ciki. Da motar mijin Sa'a suka wuce asibiti cikin gaggawa aka amsheta. "Babangida sai dai ka kashe mana iyaye ƙarfi da yaji sannan zaka dawo kanmu. Shikenan mu tun sanda ka kai munzili abinda zai faru ya faru baka sake barin zukatanmu sun yi daɗi ba. Ko bamu ga Sabuwa ba ai muna ganin ƴaƴan da suka fito daga tsatsonta. Ƴar kawali dangin marasa mutunci. Sabida son zuchiyarka kaje ka kwaso mana masifa. Wallahi Ɗana bazai taɓa auren Mardiyya ba sai dai akan haka zumuncinmu ya yanke ni da kai Har gaba da abada ma. Sabuwa kuma Allah ya tsine mata albarka tsinanniya maha'inciya" Idanunshi kawai ya rintse haɗe da dafe kanshi da yake ji tamkar zai tarwatse. Maganganun Sa'a jinsu yake yi tamkar saukar aradu a kanshi. Sa'a ta dinga zazzaga masifa da bala'i a zaune a benci. Kiran wayar Babangida ne ya katseta. Kawu Manga ke kiranshi. Saida gabanshi yayi mummunan faɗuwa a yanzu tsoronshi ace mishi Baba Malam ya rasu, ko Malama ta rasu, ko wani abun ya faru da Sabuwa. Waɗannan mutane ukun suna da mahimmanci da wani irin matsayi da samun gurbi a dukkan zuchiya da rayuwar Babangida. "Assalamu alaikum kawu Manga" Ya faɗa cikin rarrabe kalmar. "Na'am Babangida wai kuna asibiti da Malama Babba ko?" Sai da Babangida da Sa'a suka sauke ajjiyar zuchiya kana Babangida yace. "E Kawu Manga hawan jinin nata ne itama nasan ya kuma motsawa. Muna tare da Yaya Sa'a mijinta ne ya kawo mu. Yaya jikin kuma na Malam" "Jiki da sauƙi za'ace amman Yaya da wuya ya tashi, to likita yayi mishi allurar bacci yana bacci yanzu haka. Mu kuma kowa ya watse Wawo dai a gidan zai kwana tare da shi Malam ɗin a ɗaki. Gobe da safe zan zo asibitin yanzu magani zan watsa in ɗan runtsa ni kaina bani da lafiya" "To shikenan Kawu Manga sai zuwa safen. Allah ya baku lafiya duka" Da haka sukai sallama. Itama Malama Babba allurar baccin dai akai mata dan tana buƙatar hutu sakamakon jininta daya kuma haurawa dama ba ƙarasa warkewa tayi ba. Fuu Sa'a ta shige ɗakin da Malama Babba take kwance. Shi kuma Babangida wayarshi ya zaro ya lalubo lambar Sabuwa ya danna kira. Yasan dai ba zata ɗauka ba amman Adama ko Labbai zasu ɗauka so yake yaji tayi magana ko har yanzu shiru. In ance har zuwa lokacin shiru yaje ya ɗakkota zuwa asibiti. Amman ya kira wayar ma baisan sau nawa ba ba'a ɗauka gabaki ɗaya sai hankalinshi yayi mummunan tashi. Gashi shi bashi da lambar Adama, lambar Maigogul kaɗai gareshi yanzu kuma yayi dare ace ya kirashi yana tambayar lambar Adama. Sai kawai ya kira Ramatu. Itama sai da ya kirata sau biyu ana ukun ta ɗauka da muryar bacci. "Ramatu muna asibiti ne Malama Babba bata da lafiya. So nake kije lungun Sabuwa ki dubo mun yaya jikinta. Ko ki haɗani da Adama yarta a waya inji yanayin jikin nata" Ramatu taji wani kishi ya tokareta. Dan ta lura da takun Babangida a kwanakinnan irin yadda ya mayar da hankalinshi kacokan akan Sabuwa da yaranta. "Hmm a darennan wallahi bazan ita fita waje ba tsoro bazai barni ba kayi haƙuri kuma ka fahimceni." Idanunshi ya lumshe, cikin dakewar murya marar halamun wasa ko karɓan wargi yace. "Nace kije ki kaima Yar Sabuwa waya inason inji yaya jikin nata" Kai tsaye cike da rashin tsoro da halin komai ta famjama famjam tace. "Wallahi bazan ita fita tsakar gida da daddarennan inje inci karo da aljanu ba. Sannan ai ba ni kaɗai bace matarka ba. Baga Aminiyarta ba ka ce taje ta gano maka mana dole sai ni." Tana ƙarashe maganar ta ta kashe wayar Da mamaki Babangida ya bi wayar da kallo yana ta'ajibin abinda ta aikata. Lallai zata gane kuskurenta amman yanzu damuwarshi yadda zaiji jikin Sabuwa ne. Ƴar Shuwa ya soma kira ita kam kiran duniya ma bata ɗaukaba balle ya sanar da'ita saƙon a haka Babangida yaita tunanin hanyar jin jikin Sabuwa, gashi shi ba abun hawa ba balle yaje ya dubota ya dawo. "Lallai abun hawa akwai daɗi. Inaga dole zan karɓi lifan ɗin da Mustapha da yaita nacin in karɓa ya rage mun matsala naƙi karɓa. Miƙewa yayi ya shiga ɗakin da Malama Babba take. Sa'a na zaune a kujera kamar da Kudidi take waya. Malama Babba tana kwance tana bacci a tsanake. Sai kallonta Babangida yake yi yadda take ta ƙarewa tun dai lokacin da Sabuwa ta shigar da ƙara kotu dakuma korarta da Baba Malam yayi daga ɗakinta. Kusan rabin ƙibarta ne ya zuge sai tayi haske hancinta na usil ya sake wani tsayi. "Kaga halin da take ciki ko? Ni nama ɗauka ka tafi ne naga mintu goma da shigowata" "Ban tafi ba ina waje a zaune" Bata kulashi ba, shima bai damu da hakan ba. "Zanje daga waje duk abinda ake buƙata ina waje sai ki kirani" Yana gama faɗin haka ya saka kai ya fita a ɗakin a hankali."
Adama:..... Fitsari da mumnunan mafarki shi ya farkar da Adama ba shiri ta zabura. Zaman dirshan tayi tana tunanin wannan mafarki da muni yake. Juyawa tayi taga Labbai sai baccinta take yi amman bata ga Lolo ba, saita ƙaddara tana banɗaki. Shiru yanzu Lolo zata fito a_a anjima ne ga fitsari sai sake matsar Adama yake yi. "Bari dai in ma Lolo magana fitsarinnan ya matseni yanzu haka tana ciki tana sharɓar kukan data saba." Harta fita zuwa dogon falon tana magana. Ganin ƙofar banɗakin a hangane ba ƙaramin mugun faɗarma da Adama gaba yayi ba. Da sauri ta shiga banɗakin taga babu kowa. Ba shiri ta rufe ƙofar tayi fitsari danji tayi yana shirin zubo mata. Da sauri ta fito ta shiga falo nanma wayam. Ganin ƙofar falon itama a buɗe ba ƙaramin sake tsurar da Adama yayi ba. Duk da haka saida ta leƙa lungu da saƙon falon, zuwa ɗakin yara shiru kake ji. Da gudu Adama ta koma ɗaki. "Labbai Labbai tashi Lolo bata gidannan " A zabure Labbai ta miƙe tana faɗin. "Mekika ce Adama Lolo bata nanfa kika ce to ina zata je a darennan?" Adama ta fashe da kuka tace. "Allah dai yasa ba baƙin cikin dasu Rakiya suka kuntuka mata bane yasa ta gudu ta barmu baki ɗaya ba." Labbai ma hawayen take yi tace. "Kira Tsahare ko Lolo taje ɗakinmu danta samu nutsuwa" Nan Adama ta shiga kiran Tsahare sai data kira sau shidda kafin Tsarahe ta ɗaga. "Tsahare Lolo tazo ne dan ALLAH?" Cikin muryar bacci tace. "A_a gaskiya. Ni da Sadiya da Salaha ne kaɗai a ɗakin. Lafiya amman?" "A_a babu lafiya. Yanzu kuje guda ku duba ko taje can duk da nasan zaiyi wuya taje. Amman ku duba dan ALLAH ko filashin kimun in kunje gidan" Ita kanta Tsaharen ta kiɗime. Cak ta tashi ita da Sadiya suka nufi gida sun daɗe suna buga ƙofar Rakiya kafin tazo ta buɗe. "Wannan wanne sabin salon kuma iskanci kenan. Darenma mahutar bawa ba'a barka ka huta ba. Me yasa baka kwana a inda kaje ɗinba zaka zo duk ka fitineni" A tunaninta Maigogul ne. Tana zare sakata taga su Salaha cirki_cirko" "Lafiya cikin talatainin dare haka?" Salaha tace. "Rakiya Lolo tazo nan gidan?" Ta jefo mata tambayar. "O_o rabonmu da ita tun a kotu wani abunne, ko dai Babangidan sakinta yayi? "Dama sakinne ai da sauƙi tunda ba kanta farau ba mu mai ya kashe mu da bamu da auren. Murna kuke yi in aurenmu ya mutu sabida burinku ko zamu samu mai hannu da shuni. Duk gashi sakamakon kwaɗayinku yasa Lolo ta gudu tunda dai bata nan duk yadda akayi guduwa tayi." Rakiya ta yo kan Salaha ta rufe ta da duka. Fincikewa tayi tamkar zata rama dukan tace. "Ai gaskiya ne abinda na faɗa duk kunbi kun lalata mana rayuwarmu tun kafin ma musan meke mana ciwo. Jibi ace duk kyau da farin da Allah ya huwace mana amman dai mun kasa zaman aure sakaamakon baku bamu tarbiyya data dace ba" "Anƙi a bayar mitsiyaciya sabida aurenki ya mutu shine zaki sauke mun atlarar rashin arziki ƴar iska. To daidai nake dake har ki mutu baki isa kin kaini ko ubanku buɗewar idanu ba. Lolo kuma ta daɗe bata shiga duniya ba. Tunda abinda ta zaɓa kenan tabar ƴaƴanta hannun kishiyoyi ita kuma ta bi saurayi da aurenta" Tana faɗin haka ta banko ƙofarta. Hauwa dake tsaye dokin ƙofarta tace. "Rakiya halinta sai ita. Lolon wai ba'a ganta bane?" Kafin su bata amsa kiran Adama ya shigo. "Tsahare an ganta kuwa?" Tsahare tace. "Kin ganmu a cikin gidan babu Lolo babu dalilinta gaskiya. To ku garin yaya ta fita baku sani ba?" Adama dai tana nishin kuka ta kashe wayarta. "Labbai ta tabbata Lolo guduwa tayi Kuma kinga wayarta ma a kashe take ɗib bare muji inda take. Bari in kira Babangida dai in sanar mishi a tari abun da wuri. Kai amman Lolo in guduwa tayi bata kyautama yarannan ba. Kina da budurwar yarinya mahaddaciyar Qur'ani amman ki tsallake ki barta. Duk fa yadda take ganin lalacewar aurenta da Babangida a hakan ta fimu dacen miji, ta fimu dacen ƴaƴan ma. A gidanmu kab in banda yaranta su waye ma suke karatun in banda gantali kwararo kwararo." Labbai tace. "Adama a gaskiya Lolo tayi haƙuri maƙura da Babangida. Wai shin mancewa kuke yi ne da masomin komai. Har yaushe Babangida ya soma amsa maganar Maigogul ma balle mu. Wai zagi ido da ido wannene bai mana ba? Cin kashi akwai irin samfurin da bai ma Lolo ba? Banƙi ba in ance ya shiryu. Haƙiƙa naga salama da mutuwar jiki tattare dashi sosai. Amman ki sani wanda baya sonka to baya sonka. Nifa tayi mun daidai amman dai kirashi a wayar muji. Kinga yanzu ƙila in an ganta ya sauwaƙe mata ta huta muma mu huta." Adama dai bata samu zarafin magana ba ta riga ta danna kiran Babangida:.
ASIBITIN DA SABUWA TAKE KWANCE:. Anan na kawo ƙarshen littafi na biyu. Zan tafi hutu kafin mu ɗaura littafi na uku. Ku daɗa gyara zama akwai sauran tafiya gagaruma a gabanmu. Domin jin yadda zata kaya sai kuci gaba da bibiya wasa farin girki. Dan yanzu ne muka kai rabi a labarin. Labarai suna gaba sai mun haɗu nagode sosai da soyayya son so 🤺🤺🤺
Courtesy :::Mrs jay ce 👍