Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 18

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 18

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 18: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 18. Farkawa nayi naga ledar ƙarin jini a hannuna ɗaure. Madubala na zaune a farar…

3,890 words

Farkawa nayi naga ledar ƙarin jini a hannuna ɗaure. Madubala na zaune a farar kujera fuskarshi saye da takunkumin hanci (facemask) da suwaita mai hula ya sauke hularnan ko ƙwayar idanun nashi ba'a gani. Ɗakin nabi da ido ga marasa lafiya ratata a cikin ɗakin. Madubala" A mugun razane ya ɗago muka haɗa idanu hawaye na bin gefen idanuna. "Sabuwa kar ki kuma kiran sunana nemana akeyi ruwa a jallo sabida ke nake garinnan su Laka duk yarana suna Lagos. Nima ke nake jira Sabuwa ki farka inga yanayin jikinki bazan iya tafiya in barki ba, tare zan tafi dake" Fuskata ya shafa ya zame hular tashi baya kaɗan ta yadda zan iya ganin idanshi. Me ka aikata kuma kisa?" Duk cikin raɗa muke wannan Maganar. Kai ya girgiza yace. "Ɓarnar da akasa muka aikata tafi kisa Sabuwa. To amman yaya zamu yi da rayuwarmu kullum ana farautarmu. Iyayen da sukai silar zuwanmu duniya tun muna yara suka watsar damu a titi muna gararamba babu arabi babu boko, babu tarbiyya. Kullum a cikin zaginmu da aibatamu suke. Nifa mahaifiyata tun ina yaro take yawan tsine mun. Kinsan wacce kalmar tafi amfani dashi a kaina?" Kai na girgiza mishi dan bakina yaƙi ko motsawa. "Kullum in nayi mata ba dai_dai ba sai tace mun matsiyaci, marar albarka, ɗan iska shege. Duk waɗannan kalaman ga tasirin su a tattare dani shi yasa har gobe nake ɗaura alhalin lalacewana a kanta. Duk ɗan da yake son yayi albarka ai zai kula da mahaifiyarshi ko? To ni har ta mutu ban kula da'ita ba tunda na bar mata gidan ban koma ba har sai lokacin da Ƙanwarta ta kirani tana faɗa mun jikin Mama yayi tsamari kuma sai sambatun kiran sunana take yi. Shine naje tsakanin uwa da ɗanta sai Allah take naji tausayinta muka ɗauketa muka Kaita asibiti a hannuna ta cika tana saka mun albarka tare da cewa in yafe mata tasan bakinta ke yawo a rayuwata. Sai dai kash a lokacin daya fi dacewa ta kula da rayuwata a lokacin ta barma duniya taimun tarbiyya. Sabuwa ina tuno lokacin da mahaifina yake riƙe hannuna muje masallaci sallah. Ina tuno lokacin da yake sani a gaba ya bani hadda. Shafi biyu nake haddacewa kullum fa. Tun daga mutuwar Mama na sake fanɗarewa na boƙare rayuwar matasa masu shaye_shaye rayuwace abar tausayi, rayuwar guje_guje rayuwar shan muyagun ƙwayoyi, rayuwar da duk kuɗinka ba zaka iya morarsu yadda ya dace ba. Rayuwar da al'umma kullun cikin tsine maka suke. Yanzu jibi inda nake kwana fa" Idanuna na runtse ganin shigowar jami'an tsaro cikin ɗakin da nake bisa jagorancin Dr. Madubala ga yan sanda ka gudu ka gudu. Bai juyo ba yayi tsalle ya taka cikin wata marar lafiya ya haye taga ya fice. "Tunda kika sa ya gudu to ke zamu kama ƴar iska marar mutunci" Cewar wani ɗan doka mai ƙaton ciki. Ko ɗigon hawaye babu a idanuna a wannan lokaci idanuna a runtse kawai suke na jiyo muryar madubala kamar almara yana cewa. "Gani ku kamani kada ku cutar da'ita bata san komai ba, ni kuke nema haƙiƙa na kamu" Da sauri na buɗe idanuna ina yinƙurin tashi amman wani irin azabar daya ratsa ƙasana yasa dole na koma. "Sabuwa sha kuruminki madubala naki ne har gaba da abada. Zanfa dawo ke dai ki kula da kanki kema kinsan zan fito. " Ina gani aka sama madubala anƙwa a hannu. "Sabuwa zan fito karma ki damu kan ki. Ki riƙe mun alƙawarina da na fito zamu yi aure Sabuwa. Duk wanda kika kula kin ja masa. Kai kuma Dr ka rubuta ka aje nine ajalinka" "My friend wuce mu tafi dalla kana ɓata ma mutane lokaci." Wani ɗan sanda ya daka mashi tsawa. Ina gani aka fita dashi daga cikin ɗakin da nake kukan da nake yi sabida ciwo ko fitowa bayayi, ni dai tunda wata nurse tayi mun allura ban kuma farkawa ba sai zuwa washegari na farka naga Labbai da Uzairu zuchiyata a gefen gadona suna ɗan hirarsu. "Uzairu zuchiyata maza kira Dr Lolo ta farka" Da sauri Uzairu zuchiyata ya fita. Labbai kuma hankalinta ya dawo gareni. "Sannu Lolo ashe dai abubbuwan da suka faru kenan? Shine kika kasa faɗama Rakiya ko ni halin da kike ciki. Shi yasa kwana biyunnan nake ganinki sukuku" Yinwa nake ji Labbai ku bani abinci" Na faɗa cikin muryar ciwo. "To wallahi kinga ruwan zafine kaɗai muka tawo dashi in akwai kuɗi a jikinki bayar a sawo kayan tea sai in siyo miki abinci a cikin asibitin." Shigowar wata Nurse da Uzairu zuchiyata yasa bance komai ba. Tazo ta gama gwaje_gwajenta da tambayoyinta ina bata amsa a hankali. "Kin samu kinci abinci ne? "A_a yanzu ta farka fa. Amman itama yanzunnan take batun yinwar za'a nemo mata abinci" "To shikenan ta soma sa ruwan tea a cikinta tukunna. Zuwa yamma in sha ALLAH zamu sallameta ma. Taci abincin zan kawo magani da zata haɗiya." Ficewa tayi, ni kuma na dubi Uzairu zuchiyata da Labbai inason in tambayesu da gaske an kama madubala? Amman yinwa ta hanani magana. Da hannu na nuna ma Labbai jakata ta ɗakko ta zuge ta ciro kuɗin dake ciki. "Uzairu zuchiyata ka fita ka siyo ma Sabuwa kayan tea da abinci a waje. Muma ka siyi abincin damu. Dubu uku ta ƙirga ta bashi ya fita. Yana fita Ƴar Shuwa ta ƙaraso ita da ummansu. "Labbai yaya kuma jikin na Sabuwa, naga tayi muguwar rama tayi fiyau" Cewar Mama kenan. "Wallahi kuwa Mama kin ganta. Mu bamu san bata da lafiya ba Gaza ne yazo yana faɗa mana wai yaji a bakin wasu ƴan shaye_shaye abokan faɗansu Madubala suna faɗin wai a wannan asibitin aka kama Madubala yana jinyar budurwarshi daya kawo aka zubarma da ciki. Shine muka garzayo muka tawo ashe kuwa da gaske suke. Allah sarki Madubala ance duk ragowar yaranshi suna hannu firzin za'a kaisu" Ƴar Shuwa tace. "Ance sauran suna Lagos sun riga da sun gudu. Shima Madubala ya tsayane sabida Sabuwa shi yasa har suka iya kamashi" Haka Uzairu zuchiyata ya dawo ya samesu sunata mayar da ba'asi. Da yamma Rakiya da Hauwa, da Maigogul suka zo suka duba ni. Da rana su Adama da ragowar ƴan ɗakinmu suma duk sunzo dubiya harma Aisha ta kawo lemo da Ayaba. Da yamma lis aka sallameni muka koma gida naci gaba da jinya dan da ƙyar nake zama da ƙyar nake tashi, da kudina na dinga kulawa da kaina nice shiga ruwan zafi, nice shan farfesu, har yajin daddawa nasa Rakiya tayi mun. Ƴar Shuwa kuwa kusan dawowa tayi baki ɗayanta gidanmu da zama sabida yadda ta damu da ciwona. Ni a jikina a lokacin inajin tamkar rayuwata ba zata kai ba. Harna soma warkewa ciwo ya dawo sabo jini ya sake ɓallemun ranga_ranga aka sake mayar dani wani asibitin da ban ba asibitin da Madubala ya kaini ba, su da muka je ƙin karɓata suka yi. Likitoci suka sake jaddadama su Maigogul matsawar na sake yinƙurin zubar da ciki zan iya rasa rayuwata ma baki ɗaya. "A yanzu haka mahaifata bata da wani ƙwari tana dab da lalacewa. A bincikenmu da muka gudanar bama lallai bane Sabuwa ta sake samun ciki ba. In kuwa ta samu zai kasance tasha wuya ainun ba lallai ta iya haihuwa da kanta ba. Sabida haka yana da kyan gaske a kiyaye sosai in dai kuna son rayuwarta kenan." Dr ne ya sanar da su Maigogul wannan jawabin. Kwanana shida cib a asibiti aka sallamoni muka dawo gida. Duk wata hidimar kuɗi ni nayi ma kaina saida duk ɗan abinda na tara ya ƙare a neman lafiya ta. Maigogul yana da kuɗin amman yaƙi yi mun sam. Dan a lokacin ya zama shahararren boka lamba ɗaya. Kullum mata sunturi suke yi a gidanmu. Ganin irin jinya da ramar da nayi yasa ƴan unguwa suke ta raɗe_raɗin cutar ƙanjamau na ciyo. Ni ba jinyar tafi damuna ba rashin Madubala yafi damuna. Nayi suntirin gidan yari yafi sau goma, daga baya ne aka sanar mun ba a firzin ɗin jigawa aka kullesu ba. Garin aka bari dasu. Gaga_gaga abubbuwa sukaita tafiya da daɗi babu ɗaɗi, jikina ya warware sai dai rashin ƙarfin jiki wanda shi kuma wannan sai a hankali. Yau da gagarumin tashin hankali muka tashi a cikin gidan namu har guda biyu a jejjere manya, banda ƙananu wanda dama duk wayewar gari sai mun tashi da shi. Duk da ma dai ai mu gidanmu ba'a rabo da fitintinu iri daban _daban. Ina zaune a tsakar ɗakinmu ina cin abinci a cikin robar ci ka yar wanda Ƴar Shuwa ta kawo mun. Dan a halin yanzu bani ko kuɗin saka kati abincin da zanci in ba dai su Sadiya bane suka fita suka kawo ɗan ƙwalam da maƙulashe da aka raba dani ba, sai dai in jira ƴar Shuwa ta fita in ta dawo ta tawo mun da abinda zanci, ai na faɗa muku ta dawo gidanmu da zama duka. Ƴar Shuwa tana gaban jakar kayana tana zaɓen kayan da zata saka ta fice. Labbai tana zaune tana ninkema Rakiya kayan data kwaso a wanki. Uzairu zuchiyata kuma sai waya yake yi yana kashe muryarshi. Kamar daga sama muka soma jiyo hayaniya da muryoyin maza a tsakar gida. A guje dukkansu suka fito. Ashe wai wata matace babbar mata Maigogul yaita damfararta kuɗaɗe maƙudai da sunan yana mata aiki. Tun dai yana yaudararta harta soma ganeshi. Har wankan magani yaje gidanta yayi mata. Itace ta ɗakko mishi ƴan sanda aka shigo har gida za'a kamashi. Ga mijinta sanannene sosai. Shima yace sai inda ƙarfinshi ya ƙare akan Maigogul. Anguwarmu, da gidanmu suka cika da al'umma masu gulma tabbas su suka fi yawa dan kab unguwarmu babu wanda yake ƙaunar ƴan gidanmu. Muna gani, muna ji aka wuce da Maigogul Uzairu zuchiyata da Hauwa ne suka bi bayansu dan ganin ina za'a kaishi. Rakiya jin yaje gidan matar yayi mata wankan magani ta dinga zage_zage shine dalilin rashin binsu da bata yi ba. Tace a kashe shi uban kowa ya huta. Mama ce taita bata haƙuri har tai shiru. "Rakiya ki dena wannan maganganun kina ƙara ba magauta damar suyi muku dariya ne. Tunda dai Maigogul ba kisan kai yayi ba ai da sauƙi damfara ce kawai. Ai ni na ɗauka da gaske maganin yake bayarwa" "Ina fa wani magani, muma da munyi tunanin hakan ashe kinga damfarace. Duk yadda suke son yi dashi sai suyi ni bazan kashe kaina ba. Na gaji da baƙin ciki na gaji wallahi." Sai kawai ta rushe da kuka tayi shigewarts ɗaki, hakan ya tilastama ƴan tsurku suka soma watsewa suma. Mun shiga ɗaki duk munyi duru_duru ba'afi awa ɗaya ba wani yaron maƙotanmu ya shigo da mugun gudu yake shaida mana anyi kame a kangon Gaza an kamasu duka ana tuhumarsu da manyan laifuka harma an harbi Gaza a ƙafarshi da ƙafaɗarshi da yayi yinƙurin gudu. Nan tashin hankali ya dawo sabo. Mu dai ranar duk muka shiga damuwa muka cure a ɗaki da ƴan ɗakinmu kab ɗinsu. Hauwa ma da basu daɗe da dawowa ba itama tana ɗaki da nata tawagar. "Ohh ni Rakiya miji a kulle Ɗa a kulle. Waini yaushe zan huta ne ni Rakiya?" Adama ce tace. "Ki dena wannan kukan Rakiya bashi da wani amfani mu dai yanzu menene mafita. Wacce hanyar zamu bi Maigogul ya fito, shi kuma ya shiga ya fita Gaza ya fito?" Labbai tace. "Ga Uzairu zuchiyata dashi muka je shifa Maigogul cewa yayi muyi dawowarmu gida yana da manyan mutane da zasu zo su yi belinshi. Yace dai in muka ga bai dawo ba akai mishi abinci. Gaza shi kanshi jama'ar da yake ma aiki zasu je su san yadda zaiyi ya fito." Haka dai akaita jimantawa. Munafukan unguwa sukaita shigowa jaje, da Rakiya ta gaji duk wanda ya shigo jaje da zagi take rakashi kuma dai suma gulma ce kawai ke kawosu. Har ruwa da toka take watsowa. Gaga_gaga yamma nayi irin dab magriba Rakiya ta zuba mana abincin da aka haɗa kuɗi aka dafa a ɗakinmu. "Lolo, da Uzairu zuchiyata da Adama ku kukai mishi abincin. Amman Adama yawan yajinnan da kike yi yana yawa, anan ɗin ba daɗi ba. In aurennan bazai yiwu ba ai gara a kaso shi musan kina gida kamar dai sauran ƙannenki." Adama ta karɓi kwanon abincin. "Uhm Rakiya ni da auren mutuwa yayi da saina zuba ruwa a ƙasa ai nasha. Kina jin baƙin mugu fa cewa yayi bazai taɓa iya sakina ba. Yanzun wai aure zaiyi mu biyu daya ajjiyemu bai iya ciyar damu ba. Yara wallahi wani sa'in sai dai su fita su yo bara su nemo abincin da zamu ci. Kab unguwarmu bashi ake bina ɗakin nawa ya dawo babu komai a ciki ƴan bashi duk sun sabauta ni." Baki Rakiya ta taɓe kawai, muka dunguma muka kaima Maigogul abinci. Da magiya da fari da idanu suka yadda muka ga Maigogul ma. "Yauwa sannunku. Kar ku damu zan fito. Sai dai Alhajin da nake tunanin shi zai taimaka mun baya ƙasar. Sai zuwa jibi zai turo wakilinshi da lauyanshi ayi duk wacce za'ayi. Su su Rakiya shine basu biyoku ba dake ba matan rufin asiri bane?" Adama tace. "A_a Maigogul kar ka wani ga lefinsu gaskiya" Daƙuwa yayi mata, ni dai ina jjingine a kanta ina kallo da jinsu. "Ku tafi ni zankoma ciki. Gaza ma muna nan tare dashi, amman ba sell dinmu ɗaya ba. Sai ku faɗa ma ita Rakiya. In kama uban bai kawo taba kama Ɗan ai ya kawota ko?" Ɗan sandane ya katseshi da cewa. "Lokacin ka ya cika" A faɗace Maigogul yace. "Da ya cika, da kar ya cika kana ji na sallamesu ai ko? Tunda na shigo gidannan na lura ka tsaneni." Mu dai da wannan muka dawo gida muka zuba idanu muga yadda abun zai kasance. Wasa gaske Maigogul har kwana na huɗu bai dawo gida ba. Sau biyu rak aka kai mishi abinci. Sauran kwana biyu duk cikinmu babu wacce ta bayar da kuɗin da za'ayi girki balle a zuba mishi. Mu bai renemu da tausayi ba balle mu ji ƙanshi. Dama munfi gane ko wacce ta zari kwano ta siyo abinda ranta yake so. Wacce bata da kuɗi kuwa sai dai ta sha ruwa ta kwanta, ko kuma ta fita tasan yaya zata samu abinci. Dama da ina dashine ni dole zan siya in kai mishi, to ban fara fita ba, babu samarin ko ɗaya nima a jikin Ƴar Shuwa na jingina. A kwana na huɗunne Rakiya ta rarrafa da magriba taje ta ganosu shi da Gaza duka. Itace ta dawo mana da labarin kotu za'a tura Maigogul harma an turasu jibi za'a soma zaman kotu. Su Gaza kuma ashe har an yi zaman kotu na farko suna ma gidan yari a tsare har zuwa yadda Shari'a zata kaya. Ranar shiga kotun su Maigogul mu dai dukka babu wacce taje sabgogi duk yayi ma kowa yawa. Ni dai ban soma fita ba amman dai na warware sosai sai rama. Da wanki muka tashi ni da Yar Shuwa duk kayan namu babu wanki ta gama sakesu ta jibgesu da datti. Ina kewar sigari sosai. Bari kiga in leƙa in aiki yaro ya siyo mun na ɗan zuƙa ko zan ji sanyi" Dariya Ƴar Shuwa ta saka tana ɗauraya tace. "Ƙawata lallai fa kin warke ya kamata partyn jibi mu je tare tunda har kina son komawa kan sigari" Dariyar nima nayi mata kana nace. Inaso nima inje partyn ai an daɗe ba'a haɗu ba. Talaucinnan ya gama isata na gaji. Ni sababbin kaya nake son in sai mana. Ke in kika samu kuɗi bakya ƙara mana suturu, sai dai aci banza aci hofi. Jibi kayan namu duk sun soma shan ruwa" Matsowa tayi tace. "Kin dai haƙura da Madubala kenan tunda kinga babu sarki sai Allah? Shi dai an yanke mishi hukuncin kisa" Dole in haƙura tunda na haƙura da KHALID babu ɗa namijin da bazan iya haƙura dashi ba. Akan Madubala ai bazan tsayar da rayuwata ba. Yanzu kina ganin da kuɗaɗena duk na ɗauki nauyin lalurata. Abinci ba dan kina bani ba da tuni na koma ruwa da ciwon nawa" Muna cikin wannan hirar su Rakiya suka shigo ita da Hauwa sunata jimami. Rakiya meya faru wai a kotunne?" Saida ta ja turmi ta zauna, tare da cire mayafinta ta yaɓa a igiya kana tace. "Sai nan da sati biyu za'a zauna zaman ƙarshe. Maigogul dai yana firzin an ajjiyeshi kafin wannan lokacin. Lauyoyin da aka ɗaukar mai sun so a bada belinshi abun yaci tura. Ke bari kiga in shiga daga ciki in huta. Yaran duk sun fice a gidan kenan?" E sun firfita" Na bata amsa jikina a sanyaye. Anyi haka washegari da yamma sai ga Maigogul ya shigo cikin gida babu ko sallama. Kusan dukkanmu muna gida a tsakar gida anata musu da ihu duk mun cika gidan. "Aikin kenan. Gayyar tsintsuya babu shara. Gaku dai rigis Amman yawanku bai amfaneni da komai ba. A rasa wacce take da saurayi mai wani babban muƙamin da zai iya tsamoni. Kuke nan kula talakawa kaiconku" "Kaiconka dai dan wallahi kaji kunya kuma ka faɗi babu nauyi " Cewar Rakiya kenan. Ganin yadda take huci yasa ya wuce ɗakin Hauwa. "Sannu da fitowa kai Alhamdulillah " Cewar Hauwa ta tarbeshi harda zuba mushi jallof. "Tsohuwar munakufa ai ke dai har abada ba zaki rabu da munafurci ba. Kishiya dai koma wacce irice in ba ta Aljannah bace to munafuka ce. Oh ni Rakiya wannan mata kwai sheɗaniya" Nan cacar baki da kokawa ya ɓarke a tsakaninsu. Sukaita zagi in zagan da har saida muka shiga tsakaninsu. Maigogul kuwa sunata wannan rikicin ya fito yaje yayo wanka ya zuba ado yayi ficewarshi ma "Mahaukatan banza da wofi. Ayi mata marasa kan gado har yaransu sun fisu hankali" Gaga_gaga haka wunin yau ya kasance. Washegari itama tazo da nata hautsinin Sama ya saci akuyoyi har takwas a gidan raguna dake bayan layinmu an tawo da ƴan sanda dan nemanshi. "Oh ni Rakiya naga ta kaina kishiya tara rana ɗaya ta goma na ƙofar gida. To bayin Allah ni kaina rabon da in saka Sama a idanuna zaiyi mako biyu. Bansan inda yake ba. In kun ganshi ku kamashi ai mishi hukunci daidai da Abinda ya aikata." Tana faɗan haka taci gaba da cin abincinta mu dama muna kwance ne muna ɗan hurarmu ta ƴan mata muna shewa. Da daddare muka shirya tsab ni da Ƴar Shuwa muka nufi zangon baƙi. A cikin club ɗinsu dake ta baya wanda in ba harkar ka bane bama zaka san dashi ba. Anan wannan partyn zai gudana. Abokin saurayin Ƴar Shuwa ne suka gayyaceta. Muna shiga muka ga taron na manyan yarane. Zamana ke da wuya muka haɗa idanu da wani gaye a tsaye yana rawa da wata mace, yana yamutsata son ranshi. Kallonshi nake yi babu gaira babu dalili. Shima kuma kallona yake yi. Babu shiri ya saki yarinyar, ya kutso tare da tutture mutane har ya iso garemu. "Ya akayi ƴan mata tare da wani kike ne?" Sai da nayi fari da idanuna na tabbatar na birkitashi kafin nace. Ba da namiji nake ba, tare dai da ƙawata nake" Ajjiyar zuchiya ya sauke tare da tashi tsaye ya riƙo hannayena dukka biyu muka sauya kujera inda duhu yafi yawa. Bakinshi na kan wuyana yanayi kamar mage na jin ƙamshin ɓera yace "Sunana Babangida. Laƙanina kuma kacigari"

Sabuwa:. Dawowa labari: Ji nake yi tamkar kaina zai tarwatse kiɗan dake tashi a club gabaki ɗaya ya addabi kaina. Nafi minti goma inason in miƙe amman na kasa sai da taimakon wani namiji daya fahimci tashi tsaye nake son nayi shi ya taimakeni harna ganni a tsaye Da ikon Allah sai na ganni a waje ina tafe ina gauraye hanyata hawaye na zuba a idanuna, kana a lokaci guda ina dariya na zama tamkar mahaukaciya. Ji nayi nayi karo da wani abu jiri ya ɗebeni luu na faɗi, amman sai naji ba'a ƙasa na faɗi ba na dai jingina da wani lallausan abu ne. Kamar jikin mutum

MRS BUKHARI.

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA ASHIRIN CIB😃

https://chat.whatsapp.com/IT8sWgHNT8yJcZx3E6V1yB?mode=ac_t 🛍️ Muna gayyatar ku zuwa Queens Collections - inda zaku samu kayan kitchen da kayan amfanin gida masu inganci sosai, crayfish, bedsheets, duk a farashi mai sauƙi!

🧺 Kayan more rayuwa 👛 Farashi mai rahusa 🚚 Saukin samu + Sauri a isarwa 🎁 Siyayya mai sauƙi kuma daɗi

🟢 Duniya ta siyayya mai sauƙi tana jiran ku a Queens Collections! 💃

"Subhanallah wacece wannan Kamalu?" Cewar Tijjani abokin Kamalu wanda Sabuwa ta faɗa jikinshi yana tsaye riƙe da'ita. "To wa zai sani da halama ma fa a bige take, duk da ba iyakar buguwar ba bata da lafiya zafin dake jikinta ai ya wuce misali gaskiya." "To yanzu ka jingineta gefe mu kama hanyarmu. Irin ƴan iskan matannanne wanda basa iya kama girma da mutuncin kansu. Jibi yadda take warin sigari. Ace mace kyakkyawa kamar wannan a madadin a sameta a gidan aure sai ace a club za'a sameta kaico" Kamalu yace. "Baka da tausayine wanne irin in jingineta a gefe kake cewa? . Bata da lafiya nake faɗa maka ni likitane kasan nasan aikina. Dallah buɗe bayan mota in sakata mu kaita asibiti. Ga jakarta a ƙasa ka ɗakko" Baki a wangale Tijjani yace. "Wai da gaske karuwar zaka taimaka har wani kaita asibiti zaka yi" Kamalu baice komai ba. Yasa hannu ɗaya ya buɗe motar dama a jikin motar suke. Shi kaɗai yasa Sabuwa a cikin mota, kana ya ɗauki jakarta a ƙasa ya cilla a bayan motar. "Muje Tj mu kaita asibiti kafin mu wuce. Koma karuwace ai zamu samu ladan taimaka mata. Ta yiwu taimakon da zamu yi mata yasa inta warke ta tuba." A haka dai su Kamalu suka kai Sabuwa asibitin da anan suke aiki dukkansu, kasancewarsu matasan likitoci wanda sukai karatunsu a ƙasar waje suka dawo gida Najeriya suna bama kasarsu gudunmawa. ma'aikatan jinya suka karɓeta. Zuwa ɗakin kwanciya. Kasancewar asibitin na kudi ne ko wanne ɗakin gadaje huɗu ne a ciki babu cinkoso "To Tj zamu je mu dubata tare ko kuwa shima ba zaka yi ba?. "Allah suturu buƙwui ni bazan yi mata komai ba. Sannan ai baka buƙatar taimakona. Dr Mu'awuya kuma shine a darennan shi ya kamata kaima Magana mu wuce mu gabatar da abinda yake gabanmu" Kamilu a wannan karon baiyi musu ba ya damƙama Dr Mu'awuya ragamar kulawa da Sabuwa akan duk wani bil shi zai biya ayi mata duk abinda ya dace, zuwa gobe da yamma shi zai amshi aikin dare.

Babangida kacigari:.

Da ƙyar ya isa titi sabida irin ciwon kai da zazzaɓin dake jikinshi. Gabaki ɗaya ya kiɗine ga ciwon Sabuwa, ga na Baba Malam kuma duk a kanshi. "Allah na tuba ka yafe mini. Son zuchiyata da sanin gaskiya in take shi ya jefa waɗannan bayin naka a mawuyacin hali. Ni da zina, ko hangen mata da auri saki har abadan abidina. Allah na tuba ya Allah " Babangida ya jima kafin ya samu abun hawa duk wanda ya tare sai yace ba hanyar zai koma ba kasancewar dare yayi yawancin ababen hawan masu komawa gidane akan hanya. Da ƙyar dai ya samu wani ɗan acaba ɗan layinsu dan Babangida ma ya sanshi. Shine ya ɗaukeshi suka wuce gidan kai tsaye.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull