Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 17
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 17: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 17. Gaga_gaga_gaga_gaga Haka abubbuwa sukaita faruwa sannu a hankali rayuwar take ta…
3,548 words
Gaga_gaga_gaga_gaga Haka abubbuwa sukaita faruwa sannu a hankali rayuwar take ta murɗawa. Yau ace Gaza yayi sara an kama shi, gobe ace sun yi faɗan daba tsakanin ƴan wannan unguwa da ƴan wannan unguwa. Haka Sama shima shine wannan sitetion gobe shine ya saci akuya gata rago zai sato. Ga ƴan matan gidanmu yau ciki, gobe zubarwa ko wanne cikinmu da irin jawo maganarshi. Ni kuwa tun bayan dana warke daga ciwon rashin Khalid na sake zamewa boƙararriya, samari masu kuɗi na yisu basu da iyaka, kuma dukkansu babu laifi suna kulawa dani a lokacin da muke tare, Allah ya saka mun wani irin farin jinin da duk inda muka shiga sai an tayani wannan dalilin yasa na zama ta gaban goshin Maigogul yana matuƙar ji dani sosai . Duk wannan farin jinin Sai dai su babu alƙawarin aure a tsakaninmu kamar yadda mukayi da Khalid, a lokacin ni kaina babu wani aure a gabana ina ganin yanda su Aliya, su Rahama, da Layuza sukai aure aka sakosu duk suna gida a matsayin zaurawa a wannan ƙadamin. Kana ina ganin masu auren gidan namu irin ƙorafe_ƙorafen da suke kawowa da irin yadda suke yau yaji gobe kome dai, jibi anyi doki in doka ko da miji ko da ƙanin miji. Wannan rashin mutuncin ba ya Aliya da Labiba a kaf gidanmu. Su baku ji labarinsu ba, da sauran ragowar ƴan uwan namu ko? Uhm kunsan ba komai bane zai zanu a rubutashi ba shi yasa. Haka nake yin samarin a rabu wasu da dalili wasu babu wani dalilin kirki. Maigogul kuma tukuru ya dawo harkar tsubbu a lokacin anyi wani irin rikicine na kawalai kunsan suma harda asirce_asirce suke jifan junansu. Maigogul da wata azal ta kamashi saida yayi wata shida a gidan yari abar kaza cikin gashinta. To da fitowarshi sai ya tsiri harkar kuma abun mamaki yana samun kudi sosai, sai ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ga bokanci, ga kawalci yana tallatama matan aure da zawarawa ha dama ƴan matan. Ni Maigogul ya ja a jiki nake ƙulla mishi magunguna sabida a cikin ƴan gidanmu na fisu sauƙin kai. Kuma a lokacin ina tare da Tijjani yana mun ɓarna da ƙudi, hannuna a sake yake ko nawa Maigogul ya tambaya in ina dashi ina bashi haka ma Rakiya, kuma ko fita nayi ina siyo kayan abinci in ajjiye musu sai suji dana cefane. Wannan dalilin yasa Maigogul ya jani a jika sosai, da sannu har nasan yadda ake dukan ƙasa, a duba taurari, da ma karanta bayanin ƙasa. Abinda ya shigemun duhu ina tambayarshi yana faɗa mun. Yace mun gada yayi a wajen mahaifinshi shi kuma ni ya zaɓa da ya gadarma. Bari kuji wani sirri. Harkar bokanci duk fa yaudarace, mafi yawanci ƙaryane da hasashe wallahi, sai wasu ƴan siddabaru da basu da wahala da ake yi( Mata muji tsoron Allah bokaye su dena yaudararmu suna rabamu da Ubangijin mu. Duk abun bugace kawai ga tarin zunubi da mutum ya ɗaukarma kanshi, uwa uba ga rashin biyan buƙata. In Allah yaso ya kamaka kuma sai kije wajen bikan ƙarya ya daka kuka ya baki, kisha kuma ki samu biyan buƙata. Amman fa ku sani Ubangijin da yayi bokan, ya yiki yana madakata yana jiranku acan zaki yi mishi bayani a inda ba'a ƙarya) Wani sa'in in naga mata sun dawo suna ma Maigogul godiya harda tukuici sai inta mamaki, domin nasan bayan tukunya da ruwan tawada nake jiƙa mishi a bokitin fenti in ban fita ba in tayashi da daddare mu ɗaura a matsayin rubutu. Mafi yawan magungunan da yake basu na sha ararraɓine, na hayaƙin kuma itacen dorot ne yake bulbula turaren binta Sudan a ciki. A hakan har sai da takai ta kawo sai Maigogul ya faɗi mata nawa zai iya gani sabida layin da ake yi mishi. Kaji kuwa lokacin su Rakiya a gaskiya sun goge wuyansu dan har wani ƙiba sukayi sunci uban talauci Rakiya ta sake haske, Maigogul ya sake wani irin kyau. A harkar bokanci aka biya ma maigogul kujerar makka na biyu, na farkon muna yara yaje wannan a harkar kawalcinshine ya samo. Gidanmu ya sake yin ƙaurin suna, da an tashi faɗa sai kaji ana kiranmu yaran ƙananan mutane gidan mutanen banza, marasa tarbiyyar islama. Gaga_gaga dai nayi saurayi riƙaƙƙen ɗan daba, ko da yaushe ina cikinsu duk wani lungu da saƙo tare muke shiga kullum cikin shigar maza nake, wuƙa kuwa a lokacin har dauri nake sha maganin wuƙa. Tare da Madubala ake farararmu mu gudu, ni dai sau biyu kwalawa na kamasu tare dani sai daga baya Rakiya, ko Maigogul su zo suyi belina, a haka ina ɗan fita club ko zuwa Hotel haka a ɓoye ba tare da sanin Madubala ba, sabida son kuɗi da kuma sabo da yawon kawai, ko kuma a buɗe kada in rufeku ince muku sabida sabon da nayi da maza namiji ɗaya harga Allah bai isata gundurata ma yake yi. Yana daga cikin illa mafi girma ga mace da tasan maza da yawa. Wallahi Allah ko ta tuba mijin aurenta sai dai kawai ta zauna dashi domin Allah, amman ba wai dan shi kaɗai zai iya gamsar da'itaba. Wasu bisa wannan dalilin suke komawa ruwa ko da auren nasu sai su kasa katange kansu ga mazajen waje, wata kuma da hannu take ƙara biya ma kanta buƙata, ko kuga sun ɓige da yin maɗigo. Iyaye muji tsoron Allah, Ƴaƴa muji tsoron Allah domin wani sa'in daga yaranne ba daga iyayen ba, wani sa'in daga iyayenne. Kamar gidanmu daga iyayenmu ne. Kunji wata sabuwar ƙaddara mai rikitarwa? Dani Sabuwa ake fita faɗan daba ina gaba_gaba in sari namiji, namiji ya sareni na mayar da kaina samodara ( samodara itace macce mai shigar kayan maza) kullum ina soke da wuƙa a ƙuguna, a rigar Mamana kuma ina saƙe da askata. Ina zaune na gasa tagumi a tsakar gida da rana fetal gidan babu kowa sai ni ni kaɗai. Maigogul yau harkar kawalci ya tafi, ina zaune mata sunfi goma da suka shigo nemanshi ina cewa dasu bayanan. Nima Ƴar Shuwa nake jira tace zamu je gidan wata ƙawaemu da tayi aure tun ɗazu nake jiranta. Da tunani da kaɗaici yayi mun yawa sai nake tunanin bari inje in sameta a gidansu ma wuce daga can. Madubala ne ya kira wayata wai yana kofar gidanmu." Ina zuwa" Na faɗa a cige irinna asalin ƴan dabannan. Ficewa nayi daga gidan ina fito Madubala yana zaune a dakali hannunshi da leda bibbiyu ya ƙurama ƙofar gidanmu idanu. Yana ganin fitowata yayi murmushi. In muna tare a keɓe ba tare da yaranshi bane kaɗai yake iyayimun murmushi. Amman in muna kangon da anan suke rayuwarsu cikin ƙazanta da guje_guje rayuwa mara ƴanci rayuwar wahala baya mun dariya sam. Zama nayi ina kare mishi kallo. Ƙatone sosai a ƙirji dan ba ƙaramin cin ƙarfe yake yi ba. Madubala hatsabibine kuma yana da haɗari sosai. Duk iskancin Gaza a ƙasan ƙafar Madubala yake dan a dabanci siniyanshi ne sarki Gaza ke kiranshi fadarshi cike take da matasa ire_irenmu da suka rasa kafaɗar da zasu jingina. "Yaya akayi Sabuwa? Naga kinyi wani kwalliya kamar fita kike son yi. Nifa kwana biyu bana gane miki kin ɗauke ƙafarki a wajena ni sai dai inzo inda kike?" Yana magana yana wani ciccijewa. Kallonshi nayi da kyau na daɗe sosai ina kallonshi amman bance mishi komai ba. Sai can nace. Madubala gajiya nayi a gidanka kullum kwalawa basu da aiki sai kawo sumame, yau a kamamu gobe mu gudu" Dariya yayi kawai ya daki dakalin da muke zaune yace. "Wallahi ba sabida haka bane ke da nasan jarumace, kina da jarumin maza kamar madubala har kina shayi? Sabuwa in kullum mutum sukum da guda zaki kashe wallahi ko an ɗaureki zansa a sakoki, mu da muke da manya a hannunmu, yarinyar Goga da kika burma ma wuƙa a ciki kinji labarinma ya tashi eh in ba yanzu ba. Ke dai faɗamun meye matsalar?" Ajjiyar zuchiya kawai na sauke. Madubala cikine dani ni kuma tsoron zubarwa nake yi" Ƙur ya zuba mun idanu. "To Sabuwa ba sai abar cikin ki haife ba tunda kina tsoron cirewa? Ni wallahi bani da wata matsala da kika ganni. Bayan kin haihu sai muyi aurenmu, ki ba masu ganin yaudarata kike kunya eh wallahi madubala zai zama Abba" Harararshi nayi. Wanne irin in bar ciki kuma? Kawai dai tsoron nake ji, naji ka bani to kuɗi in zubar dashi, da kuɗaɗen da zanyi jinyar kaina. Kana ganin irin wahalar dai da nasha a baya da ka kaini aka burge mun cikina kana jin sharaɗi da gargaɗin da Drn ya bayar akan yawan shan magungunan zubar da ciki. Girgiza kai yayi. "A_a Sabuwa ƙafata ƙafarki ina da likitan da zai zubar miki da cikin. In kin shirya muje in kaiki kawai faka_faka yanzu zai zube tuƙeshi za'ayi." Idanuna na lumshe nace. Fita zamu yi da Ƴar Shuwa ka ganta ma sai yanzu taga damar fitowa ita nake ta jira" Na nuna mishi Ƴar Shuwa da take zuwa. Ko kusa madubala baya son Ƴar Shuwa bai taɓa faɗan alkhairi a kanta ba. Yace akwai wani baƙin cikin da take ɓoyewa a zuchiyarta game dani. Ranar daya faɗa mun hakan saida tayi kwana bakwai bai ganni ba, ana takwas ne muna tsakar gida muna jimamiin mutuwar auren Labbai sai ga Madubala ya shigo jaye da ƙaton karenshi. Haka yaita bani haƙuri da ƙyar su Rakiya suka saka baki na yafe mishi. Tun daga ranar bai sake maganar banza akan Ƴar Shuwa ba, amman baya mata fara'a itama ba ƙaunarshi take yi ba ko kaɗan. "Madubala" Ƴar Shuwa ta ambaci sunanshi bayan ta iso" "Shuwa yane?" " "Lafiya lau. Ƙawata muje ko? Ina jiranki a titi" Ta faɗa tana wani keɓe bakinta tare da gangarawa. "Kinsan Allah in yarinyarnan bata bini a hankali ba saina sa an mata abinda abadan ba zata mance dani ba? Sabuwa yarinyarnan baƙin ciki take dake ko ki yarda koma kada ki yarda watarana saita saki kuka eh wallahi munafukace. Ga wannan kajine yara suka fita farauta suka samo, eh ki mana dabgensu sauran su Rakiya sa ci." Yana ajjiyewa ya haura da gudu. Madubala" Na miƙe tsaye tare da ambaton sunanshi, da gudu ya dawo gabana yana murmushi. "Wallahi ina sonki da yawa ƴar farata yaya akayi yau kinyi laushi duk maganar cikinne?" Hannu yasa ya shafo cikina ta cikin riga. Yaushe zamu je a zubar da cikin to?" "Duk lokacin da kika dawo kinsan inda zaki sameni ai sai mu tafi aje a cire. Ki kwantar da hankalinki kece kinƙi yadda muyi aure sai jana kike yi" Ya jima yana rarrashina, ni kuma duk fargaba ta rufeni. Gida na shiga na juye kajinnan a tukunya na rufe sauran kayan alatun shopping ɗin kuma na buɗe bokitin fenti na zura ledojin a ciki na fito. Sai a gidan Ƙawarmu ne Yar Shuwa ta samu zarafin tsigaleni akan na barta ita atsaye sabida wani Madubala Dariya nayi. Oh Ƴar Shuwa ke da Madubala dai kamar mage da bera bakwa jituwa" Hararata tayi tace. "Ai har adda,a nake yi Allah ya kawo wanda zai ture gwammatin Madubala a zuchiyarki wallahi" Dukan kafafarta nayi nace. Ke hattara Ƴar Shuwa na faffardeki ƴar abu ta kazan... Inason abuna fa kada kiga madubala a haka wallahi yasan abinda yake yi mutumne shi mai son ibada asalima a sanadiyyarshi sallata ta gyaru, duk irin harƙallar da ake ƙullawa da lokacin Sallah yayi yake dakatar da komai har sai yayi Sallah. Bugu da ƙari Madubala mutumne mai kirki yanayi ne fa kawai yasa ya zama haka kamar yadda muma yanayi da ƙaddara ta maishemu haka" Amarya ce ta iso inda muke da ture shaƙe da kayan ciye_ciye na amare da abubuwan sha. "To Ƴan mata asha lemu kafin abincin ya sauka. Saida na cika bakina da dambun nama kana nace. Me kika ɗaura mana Amarya?" Zama ta gyata tace. "Nasan kina mugun son jallof din manja mai bushasshen kifi to ita na ɗaura mana ina fatan wuni zaku yi dai ko? Oga bayanan yayi tafiya, koma ince ya koma bakin aikinshi saini kaɗai kaɗaici kamar ya halakani kai zaman takura babu daɗi, ku kam kunji daɗinku ina mugun kewar club sosai" Ƴar Shuwa tace. "Mu da muke fatan mu shige daga ciki ya kike sage mana guiwa kuma" Ki shige daga ciki dai. Wa yadda nake zamaninnan bafa zan zauna a ƙarƙashin mutum ɗaya ba wallahi. Ya gama sukurkutani ya sakoni, ko kuma ya sake auro wata" Hararata Ƴar Shuwa tayi tace. "Sai a ƙarƙashin madubala riƙaƙƙen ɗan iskan da bai isa yayi yawo a fili ba?" Yafa isheki haka wallahi Ƴar Shuwa. In fa nabar madubala dake ba daɗi zaki ji ba. Dan kina aminiyatane yake ɗaga miki ƙafa fa. Ya zaki dinga aibatamun masoyina dan wulaƙanci ina fa sonshi Amarya tace. "Uhm kan ku ake ji. Ni in kuna da sigari bani in zuƙa ko zan samu sukuni yaushe da rabon a hadu" Sigari na ciro dukkanmu muka kunna ko wacce tana zuƙa cikin ƙwarewa muna hirarmu. Yanzu ke mijinki yana tunanin wata ta kirki ya auro haka ma surukanki basu san kurace da fatar akuya ba" Ina gama maganar na zuba ƙwayoyi a bakina na bisu da lemo" "Uhm haka fa kafin ya tafi muka je gaishe da uwarshi. Harda niƙab na saka yanata masha Allah. Ni kuma na sane sabida tsaro wallahi. Amman fa auren ya isheni gashi ba wani jarumi bane, babu armashi abun sam. Yadda samarin waje suke suna da bambanci da mazajen aure fa. Shi wannan baifa iya wata soyayya ba ko sumba kala ɗaya rak ya iya. Baya ɓata lokaci wajen yimun wasa burinshi biyan buƙatarshi gasu da san kai in tasu buƙatar ta biya ke ko oho in faɗa miki." A nan gidan muka wuni muna hirarmu da shaye_shayenmu sai bayan la'asar mukai mata sallama. Ni bamma koma gida ba wajen madubala na wuce ita kuma Ƴar Shuwa gari ta shiga abunta. Ina dira cikin tabkeken kangon yaranshi dake murza tabar wiwi na siyarwa suka hau jinjina mun cikin girmamawa a matsayina na yarinyar ogansu. Kunji nace na dura ko? Kangon bashi da ƙofa, an fitar da ƙofar amman sai aka shafeta kuma. Wannan kangon a hannun wani bawan Allah wani mai kuɗi ya siya, bai siya domin ya gina ba, ya siyane domin su madubala su zauna a ciki suna sana'arsu ana biyanshi kamisho. Da yawa yawan kangwayen da suka kasance matattarar ƴan shaye shaye in kun lura ba'a fiye ginewa ba, zaku iya sanin kangon da yafi shekara goma a matsayin kanko ko? Yawancinsu a kangon akeson a barsu. Shi yasa wannan aikin masu unguwannine daya kamata su dena barin kangwaye cikin unguwanninsu suna daɗewa. Da zaran sunga kango ya daɗe kamata yayi a tuntuɓi mamallakin kangon domin aji daga gareshi. wallahi babu irin baɗalar da ba'ayi babu irin ɓarnar da ba'ayi, idan nace komai ina nufin komai. Kafin a lalata na waje ƴan cikin layi suke soma lalacewa. "Matar OGA ki shiga yana ciki sai dai suna ganawa ne da baƙi" Cewar Laka wanda ya kasance na amanar madubala. To Laka bari in shiga ba wani abu godiya nake yi " Inayi ina cicciza tare da gyara zaman wuƙar dake ƙuguna ina tafe irin ta ƴan daba mata. Babban falon dake cikin kangon a ciki madubala yake duk wani ganawa da baƙinshi. Manyan mutane masu faɗe aji, da wanda baki bazai ma iya faɗinsu ba sabida muƙamin su. Ina zaman zamana ni Badiat azo a tattareni babu ruwana ehe😃 Babu sallama babu komai na shiga ina haɗe hanya a mugun cake nake sosai. Kujerar da Madubala yake kai na faɗa idanuna a rufe nayi_nayi in buɗesu na kasa maganganunsu daga saman kaina nake jinsu. "Wai yane Alhaji ya da mugun kallone haka. Kayanane wannan ka kuma zuba mata na jiyamu eh" Figo yayi maganar yana ɗaga murya tare da daka tsawa. "Ayi mun afuwa ai bansan Madam dinka bace na zaci irin ƴan balaja'un da suke zuwa siyan kayan ƙari ne." Ni daga haka ban sake jin muryoyinsu ba, na dai ji sanda Madubala ya gyara mun kwanciyata, ya ɗakko jaket dinshi ya lulluɓemun ƙafata dashi. Bani na samu kaina ba sai bayan isha na farka babu kowa a kangon, ga dai fitilar aci balbal nan a ajjiye a ƙasa. Miƙewa nayi na shige inda suka mayar banɗaki fitsari nayi na zari ruwan leda ina yin alwala na jiyo motsin durowar su Madubala cikin kangon. Magariba da isha duka na haɗa ina sallamewa muka haɗa idanu da Madubala yayi shiru yanata kallona amman sai naga jikinshi duk a mace a karon farko da naga karaya cikin idanunshi kenan. Matsowa nayi kusa dashi ina shirin zama saiya ɗaurani a cinyarshi. ( kui haƙuri dan Allah yanayin labarinne yazo da hakan) "Damuwata guda ɗaya kar muje zubar da cikinnan a samu matsalar da zata iya cutar mun da lafiyarki. Kinji sharaɗin da Dr Hashim ya bayar. Ɗazu bayan mun rabu can asibitin naje na sameshi nayi mishi dukkan bayani.yaita wani mun faɗa uwa ya samu ɗanshi saida na taka mishi birki. Sabuwa anya ba zaki bar cikinnan ba? Ni dai ina sonki yaro kuma ina da tabbacin nawa ne, inma ba nawa bane dani a cikin ubanshi. Muyi aurenmu kawai"" Lamo nayi a ƙaton ƙirjinshi inajin gabana na dokawa. A_a a gaskiya bazan haihu a gaban iyayena ba. Sannan inma ina son in haihu Maigogul bazai yarda ba. Ko ka mance yadda kuka kwashe watannin baya ne? Yanzunma dafa ya sani da wani zancan akeyi. Kaini kawai a zubar in huta" Rungumeni yayi tsam a faffaɗan ƙirjinshi harda wani bubbuga mun bayana. Banci abinci ba madubala ina jin yinwa" Ɗago fuskata yayi muka kurama juna idanu baƙin bakinshi ya zura a nawa. (Afwan dan Allah) Mun jima a wani yanayi shigowar Laka ne ya katse ma madubala hanzarin shi. ", Kai Laka zo kaje ka karbo ma Sabuwa abinci maza. Sabuwa to me zaki ci?" Saida na jujjuya idanuna na sake rikirkita madubala kafin nace. Soyayyar taliya mai hanta, sai dafaffen ƙwai da Fanta Ɗaɗɗara" "Kaza fa bakya so?" Uhm bana so waɗanda ka kawo mun ma suna gida bansan ko Rakiya ta dafesu ba. Amman nasan tana gani tasan aikinka ne" Nan da nan Laka ya siyo mun abinci, fargabar abinda kaje kazo sai muntsinar raina yake yi bai bani damar dai cin abincin yadda ya kamata ba. Madubala ya kama hannuna muka nufi katanga. A wuyanshi ya saɓani na ɗale katangar na zauna. Ina kallo yayi tsalle ya kama bulo ya hauro ya same ni. Saida yayi dube dube na marasa gaskiya kafin ya dira ni kuma ya taimaka mun na kuma hawa wuyanshi. Tara a asibiti tayi mana a gaban Dr. "To tunda ka biya sai ta biyoni mu je ciki ko"? Madubala yayi mishi wani irin kallo. "Ahhh ban gane ta bika ku shiga ba. Ban gane ba anyi yamma da kare?" Dr cikin Laluma yake magana tare da cewa. "Dr Tabawa tana cikin ɗakin ita zata yi mata kamar dai wancan. Abinda yasa nace da'ita tazo muje akwai matane a ciki guda biyu suma cikin ake cire musu ɗaya matar aurece kaga bazai yiwu ka shiga ba" "Sabida me shine kai zaka shiga? Kaga bari in faɗa maka gaskiya sai dai mu shiga tare ko kuma mu jira a gama musu su matan cikin" Yana ciccijewa ni dai nayi zugum. "Baka fahimta ba" Miƙewa madubala yayi ya zaro wuƙa daga ƙugunshi ganin wuƙarnan Dr yayi saurin miƙewa yace. "Muje ayi mata mu sallameki" Ƙwafa madubala yayi yace. "Da dai yafi. Sabuwa wuce muje" Haka madubala yasa Drn nan a gaba muka wuce ɗakin wankin ciki inda a ciki likitocin da basa tsoron Allah suke zubarma da ire irenmu ciki da matan auren da bansan dalilinsu na zubar da cikin sunna ba. Dokace a ko wanne asibiti ba'a cire ciki sai da babban dalili wanda za'a iya rasa rai. Amman a ko wanne asibiti kuma duk tsaronshi akwai ire_iren Dr da Dr Tabawa marasa tsoron Allah masu cin amanar aikinsu Haka na kwanta ina damƙe da hannun Madubala har aka gama duk abinda za'ayi. Jinine ya soma ɗibata nadai ji Madubala na ambaton sunana da ihu daga haka ban sake sanin a ina nake ba dama ga Allura anyi mini."
MRS Buhari Tsokana anan shine Wannan littafin wallahi babban darasine a garemu Ƴar uwa ki nutsu da yawa ki dinga bin komai daki daki zaki fi fahimta sabida kiyi alƙalancin gaskiya da gaskiya. A iya wannan page ɗin akwai darrusa da yawa. Wanne darasi kika ƙaru dashi a cikin wannan page ɗin dan Allah? Faɗi ra'ayinki a ɗakin sharhi. Ƴan uwa ku fito mu tattauna Ni ina da abun faɗa da yawa amman na zaɓi magana akan yawan ibadar Madubala da duk iskancinshi Sabuwa tace shi ya sata take sallah akan lokacinta.
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA SHA TARA BADIAT IBRAHIM MRS BUHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t . 18066696785. Hussaina Bello
HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAUƘI DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI? H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE MAZA TUNTUƁE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA. KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ƘWARƘWATAR IDANU