Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 16

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 16

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 16: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 16. Sabuwa:.

4,112 words

Sabuwa:.

Idanuna na lumshe da suke mun wani irin yaji da raɗaɗi. Wayar ma ni bansan inda take ba, kaina wani irin mugun saramun yake yi. Miƙewa nayi na mayar da rigata mayafina a hannu, na suri jakata. Narantse da Allah a wannan lokacin bansan a wanne hali nake ba. Abun mamaki kayan mayen da nasha sunƙi su rage mun damuwa yadda ya kamata. Harna sauka na wuce dogon falo bansan ina zani ba. Sabida bana cikin hayyacina. Jina nake bani da maraba da matacciya wallahi. Ko maƙiyina bazan mishi fatan ya shiga irin halin dana shiga ba. Kuma bana mishi fatan ya kamu da ciwon damuwa. Duk masu ganin rashin kyautawata baron gidan Babangida ni nayi musu Uziri tunda sun kasa gane ba'a cikin hayyacina nake ba. Harma wasu suka kirani da jaka akan Babangida. Sai tsintsar kaina nayi a ckin club ɗin dake ƙasan hotel ɗin. Jirine ya ɗebeni na zauna a wata doguwar kujera daɓas. Dariya kaɗai naji inayi irinta zararru sai kawai na jingina bayana a jikin wannan kujerar, bana iya ganin mutane sosai, har saida na kwashe tsawon lokacin da bazan iya tantancewa ba. Nan na soma ganin ƴan mata rabi tsirara_tsirara sunata rawar gwatsile maza nata shasshafasu, aiyuka dai marasa daɗin gani da faɗe a wajen duk mai tsoron Allah. Wallahi a ƙasar Hausa a wannan zamanin ana sake sosai akan tarbiyya iyaye sun saka ƙafa sun shure amanar da Allah ya basu kan kula da ababen kiwonsu. Ranar lahira za'aji ɗumi gaskiya. Wannan rawa da akeyi a cakuɗe tsakanin maza da mata shine dalilin da yasa na sake nutsawa cikin labarina mai ɗauke da warwarar dukkan wani ƙulli da masu karatu suke ta canci kanka akai.

KOMAWA KAN WAIWAYE:.

Son so masoyana Ina godiya da irin soyayyar da kuke nuna ma wannan labarin sosai Babu abinda zance daku sai adda'ar khairori.

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

WAIWAYE:.

A hankali Khalid ya tayar da motarshi muka fice a layinmu. Hankalinshi a lokacin yana kan titi, har saida muka hau babbar hanya kana ya dawo da hankalinshi gareni. "Baby kina jin yinwa ne mu zarce gidan cin abinci, ko Hotel kawai kike so mu wuce?" A tausashe nace. To wannene ra'ayinka, kai kana jin yinwar ne, ko kuwa domin ni za'aje?" Idanunshi ya ɗan jujjiya halamar tunani kafin yace. "Inajin yinwa ni ko kumallo banyi ba, kuma kinga yanzu ƙarfe ɗayan rana tayi" Gyara zamana nayi da kyau na dawo shi nake fuskanta saɓanin ɗazu da titi kai tsaye nake kallo. Zaifi kyau ace kaci abinci ka ƙoshi. Nima dai gaskiya ko karyawa banyi ba. Mun fita da yata da Maogogul, to muna dawowa bamu daɗeba kazo" Kai ya gyaɗa motar ta ɗan shiru na wasu lokuta kafin yace. "To shikenan bari muje muci abincin. Yauwa Baby nace wannan gida mai buhun shine gidan naku?" E gudanmu kenan" Cike da ƙarfin guiwa na faɗa dan ban taɓa jin kunyar nuna makwancina ba. Kuma Maigogul yace in muka nuna gidanmu musamman ga samarinmu da suke da hali zasu fi tausaya mana tare da yi mana hidima. Wallahi kunji na rantse kamar yadda a gidan tarbiyya ake koya ma yara tarbiyya, haka a gidanmu Maigogul ke taramu yana koyar damu salon wayo, da sace zuchiyar samari, har tafiya shi da Cicib su suka koyar damu yadda ake karkaɗa jiki kunji na rantse kada kuyi zaton labarin ƙazon kuregene wannan labarin ya faru da gaske a kan karan kankin kaina. Sai dai kash Adama da Layuza duk matsiyata ƙauyawa suke aure lamarin da yake dukan zuchiyar Maigogul kenan dan shi kam ba haka yaso ba. Adama dai ita ta nace saita aure mijinta bayan sun gama yawon shagunan abokai dan wannan baida kuɗin kama Hotel riƙaƙƙen ɗan dabane sosai wanda kowa ke shakkarshi. An zuga rikici wanda bana ko fatan tunowa, dan irin gorin da akaita zuba mana a dangin mijin Adama duk bakinmu saida muka kasa magana, unguwa kanta ɗauka tayi akan wannan biki domin itace mace ta farko da aka soma Aurarwa a gidanmu, kuma Adama tayi zamani sosai, an yi wasan wuƙaƙe a ƙofar gidanmu bazan taɓa mancewa ba.Ita kuma Layuza Maigogul ne ya rantse saita auri mijinta sabida sau uku shi kaɗai yana mata ciki, lamarin da har gobe yake dukan Hauwa kenan. Kuma ya kafa dokar duk yarinyar da sau uku saurayi ɗaya yayi mata ciki, wannan saurayin ko a bola yake kwana saita aureshi. Ko da yaushe cikin nanata mana wannan dokar tashi yake. Haɗaɗɗen gidan cin abinci KHALID ya kaini, wajene na manyan mutane haƙiƙa tsarin wajen kaɗai ya isa ya burge mai cin abinci. Kuma na lura kamar gidan abincin gargajiya ne. "Barka da zuwa Alhaji me kuke da buƙatar a kawo muku, ko kuna buƙatar a kawo muku jadawalin dake ɗauke da jerin gwanon abincikan da muke dashi ne?" Cewar wata ma'aikaciyar da naga sai wani kallon Khalid take yi tana wani mishi dariya. "A_a masar gero zaki kawo mana da farfesun daɓaron saniya ( khadija maidoki) , sai kunun zaƙi da lamurje" Ya faɗa mata hankalinshi gabaki ɗaya yana kaina. Da sauri taa juya dan kawo mana abinda mukai oda. "Baby da fatan wajen yayi miki dai ko, kuma kina cin abind nasa a kawo mana? Kinsan na fison abincin gargajiya fiye da abincin turawa da zamani" Gyaɗa mishi kai nayi halamar yayi mun Saida muka take cikinmu mukai ƙat kafin muka nufi hotel. Hmmm a wannan ranar Khalid yayi duk yadda yake so yayi dani kuma tare da haɗin kaina ɗari bisa ɗari, ko matar daya cire kuɗi ya biya sadakinta iyakar moreta da zaiyi kenan. Yayi mamakin jina a yanayin daya jini. A wannan ranar mukaima juna alƙawarurruka masu tarin yawa, daga wannan ranar soyayyata da Khalid ta samu ginuwa, wannan ranar tana daga cikin ranakun da suka zamemun wata matattakala na sake fetsarewa. Daganan asalin rashin kunyata ya samo asali Khalid yace in taka uban kowa shine jigona bango majinginata sabida gidansu akwai kuɗi. Kamar yadda yaimun alƙawarin Aure tare da ɗauke mun dukkan buƙatuna. Nima haka nayi mishi alƙawarin ni tashi ce shi shi kaɗai abadan, ina ƙanƙame a jikinshi mukai bacci bamu yi sallar azaharba la'asar ma a lokacin ta riga data wuce. Sai daf magriba na tashi a nannauyan baccin da muka yi. Jikina kota ina ciwo yake yi. Ƙirjin Khalid na kurama idanu tare da fuskarshi bai ɗaya. Murmushi nayi na sakko a hankali zuwa toilet dan yin wanka. Na daɗe ina kalle_kalle. Uhm dole mana su Labbai suke ƙin kwana a gida. Nima dai da zaran mun gama sabo da Khalid wallahi barin gidannan zanyi ni dasu sai ziyara. Ruwan zafi madaidaici na saka a kaina ina wani murmushi wanda ni kaɗai nasan fassararshi. Wankan tsarki na soma yi na dan ƙara ruwan zafin na gargasa jikina da kyau. Maigogul ne ya koya mana yadda ake wanka in jini ya tsaya ya kuma faɗa mana wankan duk iri ɗayane, hatta Rakiya daya aurota shi ya koya mata. Ina kan yin wankan soso na ɗago muka haɗa idanu da Khalid wanda yayi tsaye a dokin ƙofa hannunshi harɗe a kirjinshi da dukkan halamu yama jima yana ƙaremun kallo. "Baby wanka babu gayyata, ni da ya dace ace ni zanyi miki wannan wankan Amaryata? Ni ji nake yi kamar kada ma ki tafi ki barni wallahi. Ko kuma in ɗaukeki muje gidana kawai" Dariya nayi mishi kawai. Tare muka ƙarashe wankan muka fito ɗaure da tawul. Ina tsaye babu komai a jikina ina goge kaina. Shi kuma yana zaune yanata waye_waye da abokanshi kan yadda birthday ɗin gobe zai kasance. Rigata na zura na tada sallar azahar a lokacin shida da rabi harda minti takwas. Kunji wasa da Sallah ko? Wata rana ma bana yin sallah biyar cikakku Shima ina gani daya gama wayar ya tada iƙama. Muna idarwa yace "Akwai masallaci ƙasa da Hotel ɗinnan. Bari naje na dawo. Zansa a kawo miki abinda zaki ɗumama cikinku. Baby nifa bazan iya barinki ki koma gida ba yau. Da fatan babu matsala a gida ba za'ayi miki faɗa ba? Nasan ke babbar yarinya ce. Dariya kawai nayi. Shi kuma yayi murmushi tare da lakace mun hancina kana ya fice. Saida na yi sallar magriba, na lalubi jakata na zaro wayata na daddanna lambar ƴar Shuwa Ringing biyu sai ta ɗauka. "Ƙawata yaya akayi menene labari? Kin ganni tare da Sagir ɗina" Dariya nayi. Shegiya Ƴar Shuwa nasan ta ankarar da nine dan kada in faɗo wata maganar. Har yanzu kuma tare kenan, aina ɗauka kina gida?" "A_a muna tare. Ai Yanzu ma wajenku zamu tawo tare zamu je siyayyar birthday ɗin Khalid ɗin naki" Ƙwanƙwasa ƙofar da naji anayine yasa nace. To shikenan sai kun karaso" Miƙewa nayi na buɗe ƙofar. Nayi tunanin Khalid ne ashe ma'aikatan abinci ne. Hannunta ɗauke da tire mai shaƙe da kayan abinci harda wata butar shayi. Matsawa nayi ta shigo ta ajjiye tiren sai wani gaisheni take yi. Har takwas Khalid bai dawo ba, kuma su Ƴar Shuwa basu ƙaraso ba. Tashi nayi na gabatar da sallar isha, ban idarba Khalid ya turo ƙofar ya shigo. Ko zama baiyi ba su Sagir suka ƙaraso suma. Idanu muka haɗa da Yar Shuwa wacce take maƙale da Sagir a kujera ɗaya. Kun iso kenan. Sagir ashe har yanzu dai kuna tare?" Nayi maganar fara'a cike da fuskata. Shima da fara'ar yace. "Muna tare inata shaƙar turare ɗan Maiduguri" Shi dai Khalid idanshi a kaina. Cikin muryar soyayya yace. "Baby rabu da Sagir kizo in baki abinci kici. Ƙawarmu Bismillah ga abinci nasa an kawo daku" Tashi nayi na nufi Khalid dake zaune a kafet. Cinyarshi ya nuna mun na kuwa ɗane. A tsanake ya dinga ciyar dani farfesun kaza har saida nakai geji. Sannan ya soma cin nashi, anayi anata hira. Bayan mun gama wajajen tara da rabi muka fice. Hmm kuɗi na inda suke siyayyar da Khalid yaima kanshi ba wata siyayya bace mai yawa sai kudi Takalmi, wandon riga, sai turare shine kaɗai abinda ya siya. Nima ya sai mun takalmi, wata doguwar riga tsantsararriya, sai ɗankunne da sarƙa, da turaruka manya, sai kayan kwalliya dana tsinta dama nawa suna dab da ƙarewa. "Baby ga sabulun makari, da manshi ki ɗauka ki dinga amfani dashi zai ƙara miki kyau" A hankali yake maganar a kunnena bayan ya zuba mun man da sabulun a basket ɗin hannuna. Mun kwashi kayan ciye_ciye babu laifi ni harda wani biredi mai kwakwa na siya, da kayan tea ƙananun gongoni. Sai da muka zo wajen biyan kuɗi muka san lallai kayan kuɗi aka sai mana. Haka muka fito da kaya kici_kici a hannunmu. "Sagir ku daga nan sai ina?" Cewar Khalid dake loda ledojin siyayyarmu a bayan bot ɗin mota. "Ah ban gane ba, na zaci zamu mayar dasu gidane ai daga nan. Ko akwai inda zamu je?" KHALID ya ƙuramun idanu tamkar mai karantar wani abu a fuskata. Can ya dubi Sagir yace. "Kaje ka sauke Ƙawarmu a gida. Baby kam tare zamu je gida da'ita. Na gaji sosai da mun kaisu club" Idanu Yar Shuwa ta kashe mun. Nima har ga Allah bana son ko kaɗan Khalid ya matsa a kusa dani balle har ace mun rabu. "Baby shiga mota kinji mu tafi bacci nake ji sosai" Baby inaso zan yi magana da Ƴar Shuwa" Mota ya shige da yaji nace haka. Sagir ya bishi suna magana, nima naja Ƴar Shuwa gefe. "Tabb Ƴar Shuwa haƙiƙa watan sa'armu ne ya tsaya. Kin ganni wallahi bazan yi wasa da damar dana samu ba. Nifa ko gobe yace in kuma binshi mu kwana zuwa zanyi. Kefa gida zai kaiki?" Dariya tayi mun "Sabuwa kenan. Kada ki mance na fiki buɗewar idanu, tunda ke yau aka buɗe miki wani shafi, ni kuwa tuni na daɗe da biya wannan shafin wani sabo Sagir ya buɗe mun. Ina zuwa bari kiga" Jakarta ta buɗe ta ciro wata leda ɗauke da wani abu curi biyu. Yagar ledar tayi ta sanya mun curi ɗaya a ledar ta miƙo mun. "Kinga wannan ki tabbatar kuna shiga ki saci jiki ki cusa Hmm wallahi sai kin kusan haukata Khalid dan na fahimci son da yake miki yana da ƙarfi." Ƙarɓewa nayi maza na cusa a tawa jakar. Shikenan sai munyi waya. Yau dai muma zamu kwana da ac." Tafawa muka yi, da wannan mukai sallama kowa ya kama gabanshi." Muna tafe a mota hannunshi daya akan sitiyari ɗayan hannun yana sarƙe da nawa hannun, muna hirarmu har muka gida gidansu Ashe a cikin gidan iyayenshi suke ɗakinshi dai ta wajen gidan yake tsakar gida kenan. Ta ƙofar baya ya ja hannuna muka shiga. Kada in jaku da tsayi saida na kwana biyu cir a cikin gidansu Khalid, dan ko washegari da muka je birthday muka dawo gidansu yasa aka zarto damu, ya duramun kayan maye sosai dani dashi duk a buge muka kwana. Khalid shi ya koyar dani shan kayan maye. Washegarin ranar birthday ɗin ma sai wajajen azahar na watstsake sabida a lokacin sigari kaɗai nake sha itama Akara ke bani in ɗan ja in yazo ban taɓa shan guda ba, sai dai ya kunna mu dinga sha tare. A gaggauce nayi wanka hankalina ya koma gida kuma, a wannan kwana biyun da nayi babu wanda da wasa ya kirani yaji ko lafiya. Sai Halima data kira tana mun masifa akan takalminta zata fira tanaso tasa ance mata na saka. Saida Khalid ya kuma yi mun shopping mai yawan gaske har kayan abinci nasa ya sai mana, ya siya mun waya Soni ta wannan zamanin, ya bani dubu ashirin kash a hannuna. "Baby gobe zamu yi tafiya da Abbanmu zan rakashi umara. Me kike son zan sai miki?" Kafin in bashi amsa naga su Adama sun fito daga makotanmu ita da Labbai da tukunya ƴar babba a hannunsu saida suka shiga hankalina ya dawo gareshi nan na narke mishi akan nifa bazan yarda ba. Saida yaita lallabani kana na amince mukai sallama, da kanshi ya fito ya sauke mun kayayyakina yaja motarshi ya tafi. Ina waigen yaron da zan gani ya shigarmun da kayan. Sai na jiyo ihu da faɗan Maigogul da Rakiya ya fito ta biyoshi har zaure tana yaɓa mishi magana. "Sai kuma kiyi amman kinsan Allah Rahama nanda wata uku bata gidannan dole ta auri yaronnan bazan yi rantsuwa a banza ba. Yanzu da wancan Alhajinne yayi mata cikin da gasken da sai mu shiga mu fita ai ya aureta ko dan dole. Amman tunda kunnena yaji cewar wannan mitsiyacin yaron da yake jele a ƙofar gidannan shi yayi mata aure dole. Ku ɗaura abinci anjima masu kawo kaya akace zasu kawo" "Ai kuwa baka isa ba a wannan karon. Kana ganin rayuwar wahalan da Layuza take ciki, ita kanta Adama jibi duk yadda ta lalace haka zakai ma yaran naka?" Kuguna duka biyun suna riƙe bakina a taɓe nake kallonsu. Maigogul ne ya hangoni da kayan alatun dake gabana. Da mugun sauri ya baro Rakiya. "Lolo wannan kayan abincin da ledojin kuma fa? Badai Akara bane yayi miki wannan hidimar ba. Dan ko jiya yazo nemanki gida" Ina dariya nace. Wane Akara Hmm Maigogul sabon saurayi nayi ɗan masu kuɗi kuma da Aure yake sona" Da dariya ya tuntsure dashi shi da Rakiya har suna haɗa baki da fadin. "Alhamdulillah " Tare da Maigogul muka dauki kayan muka soma shigarwa. "Gaza ga cicciɓeɓen buhun shinkafa fita ka shigo dashi" Cewar Maigogul daya saki katon din taliya a ƙofar Rakiya. "Kai Sabuwa farawa da iyawa, a lafiya dai kanwata ta kaina sai dake wallahi" Ya irin hade hannayensa irinna ƙauraye yace. "Cau_cau Lolo " Dariya kawai nayi na shige ɗaki inda anan na tarar da Rahama zaune tanata kuka, Adama da Labbai sun rufu a kanta" Rahama meke faruwa naji ana cewa zaki Auri iliya. Shi Alhajin ƙaryatawa yayi yace ba cikin nashi bane?" "Ke dai Lolo bari kinsan Maigogul dai in yaso kafiya. Munje ges house wajen Alhaji kamar yadda yace mana. Allah kaɗai yasan irin kudin da aka ba Maigogul dan ko Rakiya dubu ɗari ya bata, ni kuma ya bani dubu hamsin. Daga ges house muka wuce aka bani maganin zubar da ciki a wajen Abacha. Ina kwance cikina na murɗawa Iliya yake faɗamun yana ƙofar gida na faɗa mishi cikin nashine sabida dama nashi ne. Muna tsaye muna mayar da zance Ashe Maigogul yana jinmu shine yace nan da sati ɗaya ya turo kayan Aure da akwati da sadaki nan da kwana goma a ɗaura mana aure. Shine ya roƙi a barshi wata uku. Shine tun shekaranjiya Rakiya dashi suke rigima, Hauwa na kuma zugashi" Rahama ta karashe tana jan tsaki. Adama tace. "Ni da wannan yawon gara ki auri iliyan ai kin huta. Jibi fa Lolo da kamar ba zata yi yawo ba. Amman kunce kwananta uku ko biyu ne bata gida." Labbai tace. "Adama kenan. In bata fita ba so kike ta zauna baƙin cikinsu Rakiya ya kasheta, sannan sutura, abinci, magani in baka da lafiya, audigar yin jinin al'ada, sabulu turare, kayan kwalliya a matsayinta na mace waye zaiyi mata. Ni burgeni tayi fa. Ke meye baki shuka ba, ke da kika kwashe kayanki kika koma shagon saurayi. Ina Aliya take bata gida sai jifa jifa take zuwa. Waccan ƴar iskar ta ɗakin Hauwa itama zuwanma ta dena" Su Gaza ne suka shisshigo da kayayyakin dana shigo dashi. Kayan daɗin aka rarraba kowa ya ɗauki kasonshi, kayan abinci Rakiya ta adanasu a gefe Maigogul sai koɗani yake ta faman yi, daga ranar Maigogul ya soma ji dani dan na fita zakka cikin ƴan uwana. Ni sabida ma kaina da nauyi baccina nayi na barsu suna girkin masu kawo akwati ance yau zasu kawo. Sai bayan magriba suka iso Hmm kayansu a jakar buhu ta bacco atampa kala biyu lesiri kala ɗaya, shadda ɗaya, sai takalmi da jaka, da turare shikenan suka bayar da haƙuri haka dole aka karɓa. Hauwa kuwa saita samu abun faɗe taita yamaɗiɗi da wannan kaya a maƙota. Rahama dai duk da ɓari tayi hakan baisa ta zauna ba, kullum bata gida Kwana uku da yin wannan ranar asabar da rana Rakiya ta haifo ɗiyarta itama fara sol da'ita. Abun tausayi yarinyar wallahi. Ashe ma ba mai tsayin rayuwa bace. A lokacin ina da kuɗi kace_kace dan ko tafiyar Khalid ya aiko Abokinshi Sagir ya kawo mun kuɗi. Ga waya munayi akai akai, dubu ashirin na ƙirga ranar suna na danƙama Maigogul ya sawo rago aka yanka ga kayan abinci dama muna dashi. Ni ranar a gadon Mamansu Ƴar Shuwa muka wuni munata hirarmu ta ƴan mata muna dariya. Bayan suna Allah yayi ma yarinyar rasuwa. Mu dai mun taya ta murna. Gaza ya saka tijara akan su Rakiya suyi haƙuri da haihuwa haka. Maigogul yaita kutuntuma mishi ashariya shi kuma yanata karta wuƙa a ƙasa. Sagir wajen taran dare yazo ya fita da Ƴar shuwa kafin na nufi gida. "Ke Sabuwa" Cewar Akara da yazo ƙofar gidanmu harda yaranshi biyu sun wani tattare hanya dole naja na tsaya tare da harɗe hannayena a ƙirjina. Lafiya kake mun kiran karnuka Akara?" Hannu yasa a baki. Ya lailayo wani ashar ya ɗuma. Kar ka sake irin wannan zagin a ƙofar gidannan" Daga faɗan haka ya ƙaraso gabana kamar zai dageni. "Dan uwarki in aka kuma me zaki yi?" Kafin ya rufe baki nasa hannu na hankadeshi yaje cikin yaranshi sai su suka rikeshi. Wuƙa na zara a ƙugunshi na saka mishi a wuya. Take yaranshi suka zazzaro wuƙa. Da hannu yayi musu nuni da su mayar, ni kuma ya dubeni yayi dariya. "Dama ance mun akwai wani ɗan balaja'u da yake sunturi a ƙofar gidannan a mota. An tseguntamun wajenki yake zuwa. Kina so ki jama ɗan mutane wahala ko? Kar kiga ina sonki kiga kamar bazan iya hukuntaki ba" Hannuna ya damƙe ya murɗe hannuna zuwa bayana ya zare wuƙar. "Kuntun uba me nake gani a ƙofar gidannan Akara?" Muka jiyo muryar Gaza da fitowarshi kenan. Babu shiri suka shiga taitayinsu. Cukumeshi Gaza yayi ya makureshi a bango. Bawai ƙarfi Gaza ya fishi ba, a lokacin baifi Gaza iya iskanci ba. Amman kunsan irin Wannan mutanen suna girmama na gaba dasu, a harkar dabanci Gaza na gaba dashi. "Sai mai gida tuba muke yi adaiyi haƙuri. Sabon ɗan balaja'u ta samu shine wai yarinyarnan harni take zaranma wuƙa ta dauramun a wuya" Tsaki nayi na dubeshi nace. Daga yau sai yau kada ka sake zuwa inda nake soyayya ce na dena bana sonka" Ya suka ƙare sai Allah ni dai nayi shigewata ciki Gaga gaga lokaci yaita tafiya har KHALID suka dawo umara ya kawo mun tulin tsaraba, kuma a ko da yaushe muna yawan haɗuwa dan sai in kwana uku hudu tare dashi ko a gidansu ko a Hotel club kuwa kullum sai munjeshi Khalid dai ya bude mun idanu ya koya mun shaye_,shaye gashi da shegen san sigari duk ya ɗaurani akan layi. Da bikin Rahama Khalid ya bani kuɗaɗen anko da duk wani gyaran jiki. Akai biki lami lafiya aka kai Amarya ɗakinta. Bayan wata uku da bikin Rahama Adama ta haifo ɗanta namiji na biyu kenan kunsan ai ta farkon macece. Gaga_gaga abubbuwa sukaita faruwa daga ɓangaren gidanmu. Wannan tayi ciki a zubar, wannan tayo nata a haka har Labbai tayi aurenta ita dai babu laifi a lokacin mijinta yana da ɗan na rufin asirinshi. Kab cikin gidanmu kowa sha'awata yake yi yadda nake dama kuɗi. Sai dai ko da yaushe ni da Khalid a cikin faɗa muke, yadda samari suke kulani in mun fita. Da mun koma Hotel zai lulluɓeni da faɗa yai ta tayi, inna bashi haƙuri yaƙi hakura sai in watsar dashi dan kanshi yake haƙura yazo har gida ya sameni. Muna dai tare anata murzawa har Khalid ya gama jami'arshi. A lokacin ne ya tunkaro iyayenshi da batun aurena mahaifinshi yayi fur yace shi atafau ba lokacin Khalid zaiyi aure ba. Kuma sun riga da sun zaɓa mishi diyar ƙanwar mahaifiyarshi Zaliha. Ranar da Khalid yazo yake faɗa mun wannan maganar naci kuka tun yana iya rarrashina har ya kasa sai Ƴar Shuwa ya kira tazo ta fito dani daga motarshi. Gashi a daren da yazo mun da wannan Maganar washegari zai bar ƙasar zuwa yin digirinshi na biyu ya kasa faɗa mun. Yana jan motarshi jini ya ballemun babu shiri na durƙushe a ƙasa. Ƴar Shuwa zan mutu ki kaini cikin gida " Na faɗa da muryar kuka, sabida tsabar ruɗewar da tayi a wajen ta barni taje ta kirawo Hauwa a guje suka dawo. Rakiya bata gidan, ƴan matan gidan babu kowa. Da dai ina kwance a tsakar ɗakin Hauwa da jinin yaƙi ya tsayane dole Hauwa ta ɗaukeni zuwa ɗan ƙaramin asibitin kuɗi dake kusa damu. Sannan ta kira wayar Rakiya ta sanar mata bata jima ba sai gata. "Ɓari tayi cikine a jikinta da bai wuce wata biyu ba. zamu bata gado sakamakon ta jima tana zubar da jini. Sannan akwai wani tashin hankali da taji wanda shine yayi mata silar zubewan cikin dake jikinta." Kamar a mafarki naji Dr ta yima su Maigogul bayani. Babu shiri na buɗe idanuna na kalli Maigogul shima ni ɗin yake kallo. Idanuna na lumshe wasu hawaye suka gangaromun. Nasan da Khalid yananan yaji labarin halin da nake ciki da yanxu yananan cikin matsananciyar damuwa. Yanzu wai da gaske Khalid ya rabu dani kenan?" "Ai baki yi kuka ba tukunna. Dan nayi baƙin ciki da cikinnan ya zube ba tare da nasan ubanshi ba. To kukan na uban me kike yi haka nace?" Na tsinkayo muryar Rakiya a kaina. Maigogul ne ya hanata magana. A gurguje nayi jinya kusan na sati guda, sabida rashin gata ban warke ba aka sallameni. Ina kwance babu lafiya, ga damuwar rashin Khalid, ga takaicin ni nake saima kaina komai na ci ko sha hatta kuɗin asibiti ni na biya da kuɗina, face ɗan abinda ba za'a rasaba da Rakiya ta biya. Amman Maigogul ko ficika. Wannan shine rabuwata da Khalid zance a taƙaice. Amman mun buga soyayya sosai da sosai Mahaifanshi sun gama bincike a kan gidanmu ne suka ci karo da mummunan labari a kanmu. Banga laifinsu ba gaskiya.

MRS Buhari https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t . 18066696785. Hussaina Bello

HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAUƘI DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI? H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE MAZA TUNTUƁE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA. KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ƘWARƘWATAR IDANU

IDAN KAYA YA GAJI.. GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA SHA TAKWAS

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull