Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 15

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 15

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 15: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 15. A tsakar gida muke kusan dukkanmu gidan. Hauwa da nata tawagar Ƴaƴan a waje ɗaya.…

5,140 words

A tsakar gida muke kusan dukkanmu gidan. Hauwa da nata tawagar Ƴaƴan a waje ɗaya. Haka ma Rakiya da nata ƴaƴan muna zazzaune anata cin musu kamar yadda aka saba. Rakiya dai tana zaune tana cin farar ƙasa da ƙatotim cikin Autarmu marigayiya Sailuba haihuwa ko yau ko gobe. A lokacin Rahama itace babba dan Adama tayi aure. Tana zaune tana ta fesa turare a jikinta gashi dama ta ɗauki wanka iyakar ƙurewar gayu ba fariya ba Allah ya hore mana kyau gamu farare sol dukkanmu, wannan hasken shi ke sake ɗaukar hankalin maza a kanmu" "Rahama in zo ki bani na sigari ne inaso zan shiga gari kinsan fisge yafi daɗi da daddare ƴan yara da ake aikensu siyo kayan karyawa irindu biredi da sikari yanzu sunata tafiya zamu je mu datse hanya" Cewar Sama babban wanmu a maza. Gaza yace. "Kai dai kaji kunya wallahi ka nemi sana'a ya fiye maka wannan kananun sace_sacen a unguwa" Rahama ta miƙe tsaye tare da cewa. "Uhm ko ya nemi sana'a ko kada ya nema ni kam Rakiya na wuce." Maganarma irinta yara marasa kunyarnan sunayi suna keɓe baki da harara. Rakiya tace. "To kar dai ki mance in zaki tawo in ganki da leda niƙi_niƙi wannan kazar ta gidan gona mai manyan cinyoyinnan" Dariya Rahama tayi kawai ta fice. "Ikon Allah wai na kwance ya faɗi" Cewar Hauwa da bata ƙaunar taga ana zaman lafiya. Rakiya dai ikon Allah bata bi ta kanta ba sam. Da ɗaya da ɗaya manyan ƴan matan duk suka fice zuwa gari ko wacce taci kwalliya, mazan ma ko wanne ya kama gabanshi banda Uzairu zuchiyata da yafi ƙaunar ya ganshi a cikin mata ana cabcabcewa dashi. Shine a kafaɗan wannan shine a kafaɗar waccan Gidan ya rage daga su Rakiya. Sai ni sai Uzairu zuchiyata sai Halima, da Sadiya da Salaha, da mabaruka a ƴan ɗakinmu kenan. Ragowar duk sun fita, wasu daga cikin tun yamma suka fice abinsu. A ɗakin su Hauwa kuma daga ita sai Sajida sai Binta kaɗai duk sauran basa gidan. Nima a shiryena nake tsab Ƴar Shuwa nake jiran shigowarta muma mu shiga gari kamar yadda muka saba party ma na murnar zagayowar Haihuwa Anisan Ajinmu ta gayyacemu kuma club ɗin na manyan yarane duk yawonmu bamu taɓa zuwa wannan hotel ɗin ba. Ina cikin leƙen hanyar waje sai muka jiyo shigowar Ƴar Shuwa babu ko sallama sai sunana da take kira, babu wanda ya damu. Tana isowa na jata muka shige hautsinannen ɗakinmu da babu komai a ciki daga katifa sai sib ɗin da ko murfi babu kaya kuwa duk sunyi amai. "Ya akayi mu shirya mu tafi ko goman dare akace za'a soma kinga tara har ta wuce." To ai sai mu shirya nifa tun ɗazu daman ke nake ta jira. Ina zuwa bara in ma Salaha magana ta aramun kayan da taje party dasu jiya ke kinga kyansu kuwa? Saurayinta ne ya siya mata." Muna cikin maganar ta shigo ɗaukar mayafinta. Yauwa Salaha dan Allah wannan kayan da kika sa jiya kika je party su zaki aramun wani party aka gayyacemu mai zafi wajen zai tara manyan yara." Kallona tayi sama da ƙasa taja tsayi. "Bama ki da hankali Lolo" Tana faɗin haka ta nufi hanyar waje. Jawota nayi na shiga zaginta. Ni kike cema bani da hankali? Na faffarɗeki dan abu ta kazanki" Rakiya ce tabuɗe labule tace. "Zaku soma ba uhm hum ai kunma daɗe baku yi ba. Sakakkata Lolo jiranta akeyi a waje. Ki saka kayanki kuma kuyi tafiyarku tunda dai tace ba zata baki ba, ku fice ku bamu waje mu sha iska" Ai wallahi nima ta bar ganin komai a wajena in ara mata." Na ja tsaki maimakon in saketa salin alin sai na ingizata ta faɗa kan gado. Harna gama binciken kayana ina mita Ƴar Shuwa kuma sai shafa hoda da janbaki take yi tana dariyar da ke sake ƙular dani. Sai a wajen sadiya na ari wando, Halima kuma ta ara mun riga da takalmi. Agogo da ɗan kunne da sarƙa, da ɗan mayafine kaɗai nawa. Nan na zauna zaman kwalliya saida muka dai cinye lokaci goman ma a gida tayi mana. Turaren Maigogul na bincika a akwatinshi na bi jikina na dinga fewasa. "Lolo lallai zaki haɗu da Maigogul kin sanshi sarai ba'a taɓa kayanshi bai gane ba, akan wannan turaren sai kin gane kurenki jine bakya yi" Rakiya data shigo tayi tsaye a kanmu take magana faɗa_faɗa. Mayarwa nayi na ja hannun ƴar Shuwa mukai ficewarmu, a ƙofar gida muka ga Salaha a cikin wata jibgegiyar jeep tana taɗi Labbai ma mun ganta a can titi ita kuma a jingine saurayin nata yake a motar ita kuma tana kan motar a zaune jikinsu na gugar na juna. Abun hawa muka tare muka shige abinmu. Sai zumuɗin son ƙarasawa wajen party Ƴar Shuwa take yi, ni kuma maganganun da Salaha ta faɗamun nake nazari a kansu. Sai nake ganin kamar ni ce koma baya a ƴan gidanmu ko wacce nada samarinta masu kuɗi da mota, aita kashe musu kuɗi amman ni na tsaya ina biyema Junaidu da ɗan jarin tabar da yake kasuwanci gabaki ɗaya in an haɗa nawa ne? Da ƙyar fa yake iya mun anko, kaza a sati sau ɗaya yake sai mun." "Ke mun fa iso. Duba kiga manyan yara anata kawosu a mota. Ji wannan zalihan ajin namu a motar da saurayinta ya kawota kut Lolo kinga kyan wai da tayi kuwa?" Tsabaragen abubbuwan sun caɓe mun banko kula yar Shuwa ba nayi sakkowata a motar muka biyashi yayi wucewarshi. Zaliha Abdulhadi ta kallemi tana murmushi na wani banka mata uwar harara, ita kanta ta san dan wajen ya tara manyan yarane da yau saina ci abu ta kazan... Mu je Ƴar Shuwa kima dena kallonsu mu da muke taƙama da farar fata kuma har me za'a faɗa mana " Jayeta nayi muka bi ayarin mata da maza zuwa cikin inda ake partyn Sai ka nuna takaddar shaidar gayyata za'a barka ka wuce. Muma haka dai muka nuna muka shiga, kamar yadda kowa ke zama haka muka zazzauna. Teburane mai kusurwa hudu biyu maza biyu mata haka aka tsara wajen ga ruwan gora da abun sha a gaban kowa. Rabi da kwatan jama'ar wajen duk ƴan ajinmu ne sai sababbin sani da suka cikace kwatan. Makarantar fa ni da kaina na saka kaina a ciki sabida na taso da sha'awar karatu gaskiya. Tashin kiɗa ne kawai yake tashi an ƙawata wajen da balanbalo masu kaloli da yawa uwar party tayi kyau itama fara ce amman ba irin farinmu ɗaya da'ita ba. Awa biyu cir akayi ana wannan biki, rawa kuwa ni da ƴar Shuwa kusan mu muka cinye wajen dan ba ƙaramin iya rawa mukai ba. Ba'a soma bikin ba dama dai sai sha ɗayan dare karfe ɗaya aka tashi, an rarraba jakunkuna ciccike da kayan tanɗe tande. Muna tsaye a titi babu ma abun hawa sam waɗanda samarinsu suka kawosu duk sun tafi sai tsirari ire_,irenmu. Wata mota ce ta dalle mana idanu fitowarta daga cikin Hotel ɗin kenan. Idanu muka haɗa da mamallakin komar ko ince matuƙin motar a taƙaice. Kallon da yayi mun kallone da tuni na saba da ganin irinshi a wajen samari, sai dai wannan na musamman ne. "Ku tawo mu kai ku gida ƴan mata in mota kuke nema ai ba zaku samu ba" Hannun ƴar Shuwa naja muka karasa bakin motar. Gidan baya muka shige kasancewar akwai mutum a wajen mai zaman banza. "Wacce unguwar zamu kai ku ƴan mata?" Cikin yanga irin tamu ta mata Ƴar Shuwa tace. "Unguwar Zai zaku kaimu. Mun gode fa sosai" Murmushi yayi yace. "Ai babu komai kune kuka zo bikin murnar zagayowar haihuwa ko? Dan lokacin da muka shiga Hotel ɗin a lokacin mutane suke kan zuwa" Duk wannan maganar abokin matuƙin motar ne yake yi. Shi mai tuƙin hankalinshi yana kan titi rabi, rabin kuma yana wajena dan duk ɗago kan da zanyi zanga ni dai yake kallo ta cikin madubi. Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mun ba Allah ya sani a zuchiyata na dinga roƙon Allah yasa suce suna sonmu.samarine ƴan gayu da ganinsu yaran masu dashi ne, kuma ko wannne da ƴanshi daidai da misalin da hankalin masu karatu zai ɗauka, ai dai kunsan irin kyan ƴaƴanmu Hausa Fulani? To irin wannan kyan. "Tunda muka ɗakkoku Sagiru yake tazuba kamar rediyo bai baku damar gabatar da kanku ba balle muma mu gabatar muku da kanmu gashi har mun kusa unguwarku" Wannan matuƙin motarne yayi magana da murya mai daɗi. Ƴar Shuwa da Sagiru sukai dariya ni kuma ɗan murmusawa nayi kawai. "Ni Sunana Aisha laƙanin sunana Ƴar Shuwa kasancewata ƴar asalin yaren Shuwa arab tsantsa. Ƙawata kuma sunanta Sabuwa amman da Lolo ake kiranta" "Sabuwa Sabuwa. Ta kuwa dace da sunan gatanan sabuwa dar da'ita. To ni dai sunana Khalid abokina sunanshi Sagiru amman yafi amfani da Sagee." Nan dai mu kai ta ɗan hira har suka kawo mu bakin unguwarmu. "Da zai yi kyau ku saka mana lambobin wayoyinku anan muma jibi muna da party na bikin murnar zagayowar haihuwar Khalid muna gaiyatarku amman namu bikin na kwanane dan ƙarfe ɗayan dare za'a soma zuwa biyar na asuba. Da fatan babu matsala zaku iya halarta ko?" Carab nace. Babu wata matsala tunda kun gaiyacemu za mu yi iya yinmu mu halarta. Sai dai ƙarfe ɗaya ba zamu samu motar da zata kaimu ba" Na ƙarashe maganar tare da amshe wayar ina daddanna musu lambobin wayoyinmu a lokacin waya batai yawa a hannun mutane barkate ba. Sagiru yace. "Tunda kuna damu ai baku da matsala in dai kunsan ku ba irin yarannan bane da ake takura musu a gida ba gudun kada a samu matsala. Zamu zo har nan mu ɗaukeku ku dai ku shirya kawai" Khalid yace. "To in da hali Sabuwa gobe zan zo in ɗaukeki ki raka ni shopping ina fatan babu matsala ko?" Wani irin farin ciki naji tare da jin sanyi a zuchiyata dan na fahimci Khalid ni yake so tunda yace zan rakashi shopping. Idanu na kaɗa irinna yara marasa kunya nace. Baka da wata matsala ƙofa a buɗe take kana iya zuwa ka ɗaukeni duk sanda kaga dama, kuma zaka iya zuwa dani koma inane" Wayarsu na miƙa musu muka fito. Rafar kuɗi ƴan ɗari bibbiyu suka biƙo mana na dubu goma goma. Godiya mukai musu Khalid ya wani kashe mun idanu tare da mun murmushi. Nima idanun na kashe mishi muka shiga layinmu babu kowa a layin sai haushin kare kawai kake ji. "Ke Sabuwa gaskiya mun yi babban kamu yau" Hehehe Ƴar Shuwa ke dai bari dai komai ya kankama wallahi saina rama Abinda Salaha tayi mun ko zata mutu na dena bata aron koma menene. Ke dai shiga gida gobe zamu haɗe zan shigo gidanku da safe" Sallama mu kai ma juna kowacce ta shige gida. Gidanmu a buɗe yake a ko da yaushe ko da na shiga ɗakinmu mutum uku kaɗai na tarar duk sauran basu dawo ba. Waje na samu a ƙasa nayi kwanciyata tare da yin matashin filo da hannuna. Mtwss ba dole su Labbai su so kwanan waje ba ma fiye da kwanan wannan ƙaddararren gidan ba. Shikenan mu a haka zamu ƙare rayuwarmu muna kwanciya a ƙasa" A fili nake mitata bana tsoron kowa to. "Ke dai bari Lolo. Wallahi kwanan gidannan ko wahala. Tun ɗazu nake kwance bacci ya gagareni, ga sauro ga zafi ga kwanan ƙasa ƙashinka na sukan ƙasa. Amman in a waje ne kaci kaji, ka kwanta a katifa ko gado mai laushi ga ac in gari ya waye a baka kuɗi masu yawa a dawo dakai har gida" Mabaruka dama ba bacci kike yi ba?" Miƙewa muka yi zaune tace. "Idona biyu Rakiya sai tusa take yi ga gwarti duk ita kaɗai baccin duk sai ya gagaraa zuwa ga zafi. Wuta aka yanke mana ashe tun yamma ban sani ba saida aka kawo wuta sannan Rakiya take faɗa mana. Yanzu sai zuwa gobe da safe zamu harhaɗa kuɗi mu biya kuɗin wuta mu biya kuma wanda zasu mayar mana da wutar. Kai wallahi na gaji da gidannan Lolo" Baki kawai na taɓe to me zance. "Menene a ledar buɗe mana mu gani" Harararta nayi Amman kinsan dai sai da safe za'a rarraba kowa yaci ko? Cake ne da su samosa a ciki sai lemuka. Ke in faɗa miki nayi wani babban kamu zan baki labari zuwa da safe mu kwanta bacci nake so nayi." Komawa muka yi muka kwanta. A wannan daren tunanin Khalid fur ya hanani sukuni abinda nafi tunowa shine sunana daya nanata sau biyu da kashe mun idanunshi na hagu da yayi. Duk da nasan iskanci yake nufi, amman naji dadi sosai kuma a shirye nake tsab in bayar da kaina bori ya hau. Ba akan Khalid na soma samari ba, ina da samarina wanda babu inda basa taɓawa a jikina dan in samu na abinci amman dai daga iya haka ake tsayawa. Samarin yanzu basa iya kashema mace kuɗi ba tare da ana ban gishiri in baka manda ba. To a gidanmu babu tausayi, babu duban ƙanƙanta komai mu muke yima kanmu da zaran yaro ya kai shekaru bakwai to kuma shikenan magana ta ƙare nauyin kanshi ya ratayane a wuyanshi, inya fita ya nemo ruwanshi, in ma bai nemo ba cikinshi. Akan Khalid nake jin zan sallama kaina dan ya riga daya sace mun zuchiya harda kuma kwaɗayin abun duniya gaskiya sabida kana gidanmu dole ka nemi kuɗi. Washegari sai bakwai na safe ni dai na samu na tashi nayi sallar asuba. Rakiya na zaune tana kallon Rahama da take yayyaga kaji tana kasawa a tire. A guje Rahama ta fice a ɗakinmu taje bakin magudana tamkar zata amayar da hanjin cikinta tai ta sheƙa Amai. Shikenan itama dai nasan ciki ta kwaso duk da ba wannan bane karo na farko ba. "Mitsiyaciyar yarinyarnan yaushe yaushe aka zubar mata da ciki amman har ta kuma kwaso wani ciki ni Rakiya duk wuyar da tasha" Tana gama faɗin haka ta yinƙura ta miƙe tana tura cikinta gaba ta fice. Baki na taɓe batun yin ciki da zubar dashi a gidannan ba komai bane mun saba da ji tun bamu kai haka ba. Bazan iya ƙirga Adama da Layuza sau nawa suka yi ciki aka zubar ba. Uzairu zuchiyata ne yaci gaba da rarraba namannan, na miƙa mishi ledata ya kwashe da dariya. "Su Lolo kuma me aka samo mana?" Hararar wasa nayi mishi tare da cewa. Wai me ka ɗaukeni ne my Heart?" Salatin Maigogul muka jiyo a tsakar gida a guje na fice na bar su a ciki. "Me zan gani wai duwawu ya mutu ya bar zani?" Cewar Maigogul Yana tsaye ya ɗau wanka tamkar wani hamshakin mai kuɗin gaske, komai na jikinshi mai tsadar gaske ne ga gogul da kullum yake manne a idanunshi dan bama gaye hakkinshi. Bakinshi kullum yana taunar cingam tamkar tsohuwar karuwa" "Me kuwa zaka gani? Ciki tayo mu kuma a haka zamu ƙare kenan a sintirin zuwa kemis karɓo maganin zubar da ciki. Ka kasa sauke nauyin da Allah ya ɗaura maka damu da yaran duk ka barma duniya mu" Da tsawa yace "Ke Rakiya yi mun shiru jarababbiyar mata wacce ta zamemun tsiya. Ina da yara farare tsula_tsula irin wannan zan dafasu ne in sha kome kike so? Ah ni shikenan talauci da buga bugar rayuwa ya dakushemun ƙuruciyata da kyawuna sai su in dakushe musu? Da sannu haƙonmu zai cimma ruwa zasu auri hamshaƙan masu dashi na ƙasarnan. Ke waye yayi miki ciki nace dan ubanki Isuhu?" Ya dubi Rahama yana zazzare idanu" "Alhaji Audu ne yayi mun?" "Kinsan gidanshi ince dai ko, ko wajen aikinshi inda dai zamu iya zuwa mu sameshi?" Kai ta gyaɗa halamar ta sani. Tabb Rahama ta taro rikici wallahi na sani.

To mutanene mun shiga waiwayen rayuwar lolo ta baya da sannu zaku ji dukkan abinda ya shige muku duhu Son so fisabilillah.

Ina da ɗan tsokaci kaɗan akan masu zagin lolo, da masu ganin rashin kyautuwar hukuncin data ɗauka na guduwa. Shin kunsan menene cutar damuwa wanda a turance ake kiranta Deepretio? Zan faiyace muku cutar zaku jita. Allah yasa mu dace son so Mrs Bukhari ce

IDAN KAYA YA GAJI.. GAMMO MA YA GAJI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA SHA SHIDA

"wanke fuskarki maza ke da Lolo ku same ni a waje cicib yana jirana a mota dama" Yana gama faɗin haka ya fice yana saɓa malum malum ɗinshi ga ƙamshi yana zubawa. "Allah ya kyauta halin Maigogul sai shi. Duk shi yake goyon bayanku kuke duk abinda kuke so. Lolo ɗakko mata mayafi maza ku je ni wallahi sha'anin zube_zuben cikinnan ya fita a kaina" Baki na taɓe na shige ciki na ɗakko mayafina dana Rahama, sai wayata. Na cika naman kaza a bakina kafin na fito. A wata baƙar jibgegiyar mota mai numfashi muka samu su Maigogul a ciki shine a mazaunin direba sai ɗan daudun abokinshi da sana'arsu ɗaya ba'a iya rabasu ko da yaushe tare suke. Gidan baya muka shiga Maigogul ya ja motar muka bar unguwar. Wayata ce ta shiga ruri tunda naga baƙuwar lamba nasan tabbas Khalid ne,da sauri na ɗaga wayar tare da sanyaya muryata sosai. "Hello" Na faɗa muryar ƙasa_kasa. Jin muryarshi yasa na sake faɗaɗa murmushina. "Sabuwa tun jiya kika baiwa zuchiyata aiki sai ɗebewa da kashewa take yi. Ban taɓa samun macen data warce zuchiyata a kallo ɗaya ba sai ke" Idanuna na kaɗa wanda hakan dabi'atace da kuma wannan salon nake jan hankalin maza gareni. In kuwa hakanne ashe dani dakai duk kanwar ja ce. Ni ko baccin kirki banyi ba. Kuma zuchiyata cike take fal da zumunɗin sake sanyaka a idanuna ko zata rage nauyin da tayi. A takaice ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya?" Murmushi yayi tare da sake nanata sunana. "Sabuwa kenan. Zan dai kasance cikin ƙoshin lafiyane kaɗai inna ganni tare dake. Wannan fararen idanun da in kikai fari kike tafiya da zuchiyata su kaɗai idanuna suke son gani. Yaya za'ayi in ganki, zaki iya zuwa wannan hotel ɗin da muka haɗu jiya ina kwance a ɗaki mai lamba sifili tamanin da biyu" Sake far nayi da idanuna nace. Ehh tom yanzu dai bana gida mun fita da Babanmu da yayata sai dai fitar bata daɗewa bace ka bani lokaci zan zo in sameka." Ajjiyar zuchiya naji ya sauke take na lumshe idanuna a zahirin gaskiya nima a matse nake in ƙone dan dama tuni a tafashe nake, na fahimci Khalid lamarinshi ba mai sauƙi bane shima. "Zan tanadi ruwan zafi, harma da farfesu da shayi mai zafi duka. Ina jiranki zan bar miki ƙofar a buɗe da kinzo ki shigo kawai" Da wannan muka yi sallama na sauke wayata. Maigogul ne naga yana murmushi yana jijjiga kanshi. Cicib kuma sai waye wayenshi yake yi. Rahama kuma tayi lamo a kujera sai nuna ma Maigogul hanya take yi. Ji nake da ace nasan Khalid zai mun tayin zuwa inda yake da bazan taɓa biyo su Maigogul ba. "Ga gidannan Maigogul" Hannunta ya juyo ya kalla ƙaton gidan samane mai get. Dariya yayi yace. "Hmm Lolo shiga kice ana sallama da Alhaji Audu maza. Ke kuma ki fito mu jingina a jikin mota mu jirasu" Ɓalle murfin motar nayi na isa ƙofar gidan da mamaki ina tura ƙofar naga ta buɗe babu sakata. Gidan ƙatone na gasken_gaske sosai ga motoci biyu a wajen da aka tanada na musamman domin su babban falon gidan na nufa. Ƙofar a rufe take saida naita bugawa sai ga wata da gani mai aiki ce. "Lafiya wa kike nema?" Saida na harareta nace. Lafiyarce ta kawo haka. Matar gidan kuma fa tana ciki ne?" "Tana ciki wa zance mata?" Ba kowa zaki ce mata ba, kice dai tayi baƙi ne tare muke da mahaifina" Jin na ambaci haka yasa ta saki fuska tare da shigewa ciki. Ba'a jima ba Hajiyar ta iso ga kyau ga iya wanka iyakar ganin wanda ya samu rabo. "Baiwar Allah daga ina?" Daga Zai. Alhaji Audu Mahaifina yazo nema yana waje" Nan take ta haɗe girar sama data ƙasa, sai cewa tayi. "Hanne! Hanne!!" Ta kira ƴar aikin nata, da sauri ta fito. "Je ki leƙa waje ko zaki ga mahaifin wannan yarinyar kizo ki faɗa mun. Ba karen hauka bane ya cijeni ba da zukeƙiyar budurwa zata zo neman mijina in kuma haɗasu dashi ba" Hanne ta wuce aiken da uwargijiyarta tayi mata, ni da'ita muka shiga kallon juna ita nata na karantar yanayinane. Ni kuma nawa na tunanin inda maza zasu ajjiye kwaɗayi nake yi. Duk yadda muke da kyau matar Alhaji Audu ta fimu kyau haske kaɗai zamu nuna mata. Ni da na ɗauka in namiji ya auri mace kyakkyawa ire_irenmu wanke hannu ka taɓa shikenan buƙatarshi ta biya? Ashe bayan tiya akwai wata cacar fa kenan. Hmm matan gida akwai gagarumin aiki wurjanjan a gabanku. Dawowar Hanne ne yasa Hajiya ta ɗauke idanta a kaina. "Hajiya da gaske ne. Mahaifinta yana waje yana jiranta" Ajjiyar zuchiya ta sauke, kana tayi ciki da sauri. Ba'afi mintuna uku ba sai ga goga naku ya fito cike da kamala da haiba a ido ciki fal fasiƙanci. Sai kallona yake yi nasan dai bazai wuci kamannina da Rahama yake kallo ba. Saida muka fita yaga Rahama da su Maigogul sai yayi turus, tare da saurin rufo get ɗin gidanshi. "Rahama lafiya, su waɗannan ɗin waye su daa zaku zo mun har gida kusa ai kirana?" Ƙasa_ƙasa yake magana tare da waige_waige yaga ko jama'a zasu zo wucewa su gammu. "Ni ne mahaifin Rahama nazo ne muyi magana akan ɗanka dake cikin Rahama tabbataccen mara mutunci ƙaton banza harma da hofi. A haka dai kamar na Allah" Da sauri ya iso kusa da Maigogul. "Baba dan ALLAH kaimun rai inada manyan yara mutuncinane zai zube in Maganar ta fito. Wallahi bansan tana da ciki ba." Maigogul yace. "To yaya kake so ayo kenan Dattijon biri? Dan wallahi ni ba ƙaramin aikina bane yanzu in haɗo kan jama'ar layinnan kab ɗinsu in labarta musu abinda ake ciki ba. Muyi tunɓele a wajennan mu bafa komai bane. Ya zaka keɓe da yarinya kace baka san haka zata iya faruwa ba sabida iskanci. Kaji mun ɗan abu ta kazan.. "In babu damuwa mu haɗu a ges house ɗina mu tattauna a tsanake muga yadda zamu bulloma lamarin ayi haƙuri Baba a rufa asiri duka. Bani account number ɗinka in baku na mai a dai yi haƙuri a rufa mun asiri. Akan rufin asirina zan iya baku ko nawa ne. Rahama ki saka baki Baba yayi haƙuri. " Baki Maigogul ya washe ni da Rahama sai kallon kallo aka barmu dashi. Cicib yace. "To inane ges house ɗin naka yake da yamma sai mu zo ayo magana ayita ta ƙare kai waye bazawara da jaka?" Bai bashi amsaba dan yana kwashe account number Maigogul a wayarshi shi kuma yana karanto mishi sai da ya gama jerasu ya danna iyakar sifilin da yasan dole ya sanyaya ran Maigogul kana yace. "Ita Rahama zatai muku jagora" Sai da cicib ya daki tsakiyan jallabiyar jikinshi da hannunshi kana yace "Acan kuke haɗuwa kenan? To ai shikenan" Ya ƙarashe yana fari gami da gyara kallabin dake kanshi. "Alhaji kuɗi sun shigo duk yadda kace haka za'ayi da Rahama dani duk abinda kace muyi shi zamu yi." Murmushin mugunta Alhaji Yayi ya share zufar da ada ta tsattsafo mishi ya dubi Maigogul yace. "Shikenan da yamma misalin ƙarfe biyar ina jiranku" Da wannan mukayi sallama muka shiga mota, shi kuma ya koma ciki. Ni ina Allah _Allah muje gida in je wajen Ƴar Shuwa. Rahama kuma sai mita take yima Maigogul shi kuma da Cicib sai zageta ta uwa ta uba suke yi." A ƙofar gida Maigogul ya sauke mu bai ko shiga gidanba yace muje shi sai ya dawo. "Maigogul kuɗin da aka bayar baka bani ko sisiba..." Ai kafin Rahama ta ƙarashe magana ya yi mata daƙuwa. "Kinci gidanku Rahama. Ai kinsan koma yayane dole zan yafuta muku wani abun ke da Rakiya ko? To amman ki bari da yamma zan zo in ɗaukeki in muka je muka dawo sai azo ayi kasafin kuɗin baki ɗaya. Wannan karon dai kin samu mai maiƙo ba irin wancan faƙirin yaron talakan banza ba. Ni kam saina dawo" Baki na taɓe nayi wucewata gidansu Ƴar Shuwa na barsu nan. Mama tana tsakar gida tana wanke_wanke Ƴar Shuwa kuma tana zaune sai shafa hoda take yi, ƙanwarta kuma tana duba girki a murhu. Mama sannu da gida" Dariya tayi tace. "Iyayen yawo kenan. Ai tunda naga Shuwa tana shafa hoda nasan yau dai sai an ganku bakwa gajiya ku kam" Dariya kawai nayi naje kusa da Aminiya na zauna. Aminiya albishirinki Khalid fa yana Hotel yana jirana ke yau ina cikin murna" Hannu ta miƙo mun muka kashe. "Kinga kwalliyarnan da nake rangaɗawa? Fita zamu yi da Sagiru nima wai zai kaini in siya kayan da zan sa gobe na birthday. Naje gidanku sau uku baki dawo ba. Naje na tarar Amina babu lafiya" Baki na keɓe nace. Bar bani labarin ciwo. Muddin suna kwaso cikin shege ai ba zasu yi rabo da ciwo ba. Ƙawata kice kema kin gama birkita Sagir ɗin naki?" Dariya muka saka. "Ke kinga yadda yake marairaice mun a waya kuwa? Kun sanni babu dama kuma damace a garemu zagewa nayi na dinga buɗe bandir bandir na kalaman soyayya ina shiryasu a zuchiyarshi. Ke dai me kike so ni in ɗakko miki a wajen shopping ɗin"" Yauwa turare nake so mai kyau ki ɗakko mun. Bani da turare ragowar Humrar da kika bani ita zan shafe a jikina tas. Bari in tashi ke gara ke kinyi wanka ma." Saida na miƙe tsaye nace da'ita. To ni me kike so in kawo miki in mun fita?" Miƙewa tayi tsaye. "Muje gidan naku kayanki zan saka wannan lace ɗin dai" Rankayawa muka yi zamu fita. "Shuwa baki bamu kuɗin yaji da man ba" Hannu ta cusa a rigar Mama ta mika ma Mama ɗari biyar muka fice. Gaza muka tarar a tsakar gidan yana wankin kayan sawarshi ga MP a gefenshi yana jin wakar ƴan tauri. Rakiya kuma tana bakin ƙofa an kawo mata wasu labulaye tana gani. Ga Hauwa a bakin murhu ta gangama tukunyar ruwan zafi Amina kuma tana kwance magashiyan a kan tabarma kusa da ɗakinsu Babu wanda muka kula Ƴar Shuwa ta shige ɗakinmu ni kuma na kandami ruwa a bokiti na ɗauki sosona da sabuluna a kan tagar ɗakinmu nayi banɗakinmu da sauri. Ban jima ba na fito wanka Gaga gaga nayi brush shi wannan har yafi wankan nawa daɗewa. Na shiga ɗaki na tadda Ƴar Shuwa ta saka kayana tana waya. A gaggauce na shafa mai ina ƙoƙarin saka siket na atampa Yar Shuwa ta sauke wayarta a kunnenta "Ke ni kam na wuce yana bakin layinnan. Duk yadda ake ciki zamu yi waya" A guje ta fice. Rahama ta hararemu harda tsaki, ni dai ban bi ta kanta ba saida nasa kayana tsab na zauna zaman kwalliya, shima ɗauri zama na musamman nayi mishi ga kitsona na ƙari har gadon bayana nayi kyau sosai jikin atampat kalan sararin samaniyane ( sky blue) da kuma baƙin bulu ( blue Black) na samu ɗankunnena da sarƙa baƙaƙe na saka, ina dai da gyale baƙin Blue takalmine dai sai Halima ce take dashi. Gaban akwatin Maigogul naje na saci turare na feshe jikina dashi. Ina kan fesawa ne wayata tayi ruri. "Ke Lolo ana kiranki kiyi hanzari" Cewar Rahama dake kwance. Da sauri na iso inda wayar take Khalid ne yake kirana ba shiri na ɗauki wayar tare da karawa a kunnena. "Baby gani a ƙofar layinku maza ki fito ni na gaji da jiranki a ɗakin hotel ne shine na biyo ki" Kash dan ALLAH ka ɗan shigo ciki Zaka ga wani gida mai jan buhu ka tsaya daidai ƙofar gidan zan fito" Murmushi yayi wanda saida naji wani abun ya tsikaramun. "Girmanki ai ya wuce haka. Bama sai kin haɗani da Allah ba. Tuni harna shigo layinma ki tsaya a tsanake kiyi mun kwalliyar da tabbas zaki ƙarasa ruguza kuzarina. Inason kwalliya inason mace mai gashi" Farfar nayi da idanuna kawai nace. "Shikenan sai na fito" Ina faɗin haka na ajjiye wayar. Rahama dan ALLAH nayi kyau. Ko kina ganin a cikin kayana akwai wanda suka fi wannan kyau in saka? Sabon saurayi nayi mai mota yazo ya ɗaukeni zamu fita." "Kinyi kyau. Amman da zaki saka wannan doguwar rigar taki ta yadinnan cottin zaifi wannan yi miki kyau kinsan jan kala yana ɗaukar farin mutum. Shi yasa ni kaya in babu ja a jiki bana sawa. Rakiya ce ta shigo. "Ahh tabarakallah Allah nagode maka daga Bani kyautar yara tsala_tsala haka. Lolo sai ina kuma? Baki ga yadda kikai kyau ba?" Ina kan zakulo material ɗin da Rahama tace nace. Wallahi dama zanje siyayya da saurayinane Rakiya. Yauwa Rakiya wannan doguwar rigar tawa ta yadi ko kinsan ina take jannan?" "Ai kamar Ƴar Shuwa rannan ta aiko ƙanwarta na bata bata dawo dashi ba. Ai kayan jikinki ma yayi. Ba atampar ankon bikin da kukayi bane sati biyu da suka wuce ba? Kar ki canja jeki a haka farar mace ai bata bukatar wani kwalliya mai yawa. Matso in gyara miki ɗaurin" Matsowa nayi ta gyara mun tai ta yi mun adda'ar tsari. "A shigo mana da kayan daɗi. Inta kama ma sai kice bari ki ɗauki katan na taliya ko buhun shinkafa in shagon siyayya kuka je. Kinga ma daɗe muna dafawa." Tana gama faɗin haka na suri takalmin Halima uwar masifa nasa na fuce. "Ni Rahama baki faɗa mun yadda kuka yi da uban naki ba. Ina ma wai kuka je ne?" Daga haka ban kuma jinta ba. Tun daga zauren gidanmu muka haɗa idanu da Khalid yana sanye cikin yadin boyel na maza fari sol ga wata jar dara a kanshi wacce ta ƙarama kyanshi kyau. Wani irin kallo da Khalid yayi mun haƙiƙa ya ƙara ninka mun sonshi a zuchiyata sosai. Murfin motar na ɓalle na shiga. Ƙamshi da sanyi suka ratsani. Sama yayi da gilashin motar ya nutsu yanata kallona sama da ƙasa. Ƙur idanunshi suka tsaya a wushiryar dake ƙirjina. Ya ɗago ya karema tsakiyar idanuna kallo. "Sabuwa wallahi tunda nake ban taɓa haɗuwa da macen da ta warce zuchiyata lokaci guda ba sai a kanki. Ina da ƴan mata manya waɗanda suka fiki shekaru, amman ke a rana ɗaya kika sukurkutamun zuchiyata. Ke kinga yanda kika yi wani irin mugun kyau kuwa? Wato farar mace duniya ce" Murmushi nayi tare da fari da fararen idanuna masu kama da madara. Sake lumewa yayi a kujera ya sake shiga wani irin yanayi. Ina iya karantar soyayyata a idanun Khalid da ma gangar jikinshi." Ƙaran wayatace ta katse mun zaren waiwayena.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull