Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 14
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 14: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 14. SABUWA:. Da nauyin jiki sosai na tashi a madadin in ji dama_dama. Gabana sai naji…
4,489 words
SABUWA:. Da nauyin jiki sosai na tashi a madadin in ji dama_dama. Gabana sai naji yanata tsananta bugawa ko ina na jikina a mace sai nake ji a jikina wani babban al'amari zai faru, amman a raina sai nake aiyana ƙila sakina Babangida zaiyi shine al'amarin da nake jin faruwarshi a jikina. Da wannan hasashen na ƙwarara jikina na tashi nayo alwala na gabatar da sallar asuba, nayi zaune akan sallaya inata roƙon Allah ya bani nasara a kotu. A wajen na karya, ina wajen har yara sukai mun sallama zasu tafi makaranta. Sai wajajen sha ɗayan rana na rarrafa na shiga wanka, doguwar rigar yadi na zura a jikina, babu batun mai, bare turare, ko kwalli ko dankwali na kasa ɗaurawa sai dai hula na saka da na gaji da ɗaurawa yana kuncewa, rigar jikina ada caras take zama a jikina a yanzu kuwa sai yawo nake yi a cikinta damma wuyanta tsukakkene saɓanin sauran da wuyansu yake a buɗe dole sai haƙura nayi na ajjiyesu wasu da yawa a ciki kuma na yima su Labbai kwalimarsu. Muje Adama zuwa sha biyu zamu shiga kotu." Adama tace. "Kafinnan Lolo bari muyi magana ta gasken gaske lallai kina son ki kashe aurenki ki dawo gida kici gaba da zawarci? Bana so daga baya kizo kina ɗan daka ce baki yi bane. Gashi a halin yanzu naga sauyi tattare da Babangida sosai" Murmushi nayi saida muka fita falo kana na dubeta nace. "Nadamar Babangida ai ta dole ce Adams ko kin manta a yanzu bashi da gida, bashi da motar da mata zasu bishi? Duk da nasan a baya da yayo aure aure bashi da gida babu motar, amman ai dole yanzu yayi nadama ko dan igiyar auren uwarshi da aka haɗe tare da nawa. Adama ko zaki iya faɗa mun menene ribar aurena da Babangida in kika cire Ƴaƴa da muka samu. Shikenan dan gidanmu na da baƙin fenti sai in zauna da wanda bama ƙaunar juna ni dashi? Ko kuwa shi Aure dole ne? Naji a wani kaset inda malam Aminu Daurawa yake faɗan jerin sunayen sababban da suka mutu basu da aure ciki harda mace, gami da bayin Allah waɗanda sukai ma addini hidima har suka bar duniya babu aure. Adama nifa ba wai zan rabu da Babangida in auri kowa bane, a_a inaso in mayar da hankalina waje gudane in san inda rayuwar kanta ta dosa. Kinsan Allah da dai inci gaba da amsa sunan matar Babangida gara in dauwama babu Aure " Adama zata sake wata maganar na haneta, itama kanta tasan waye Babangida da irin wulaƙanci da tozarcin da yayi mun da dangina harma da Ƴaƴana. Har muka ƙarasa kotu babu wanda yace da wani uffan, ni da ƙyar ma nake jan numfashina. Kotu tayi cikan ban mamaki. Acan na tadda Ƴan gidanmu. Ga dangin Babangida suma kusan duk ƴan gidansu sun hallara mazansu da matansu. Jikina a saɓule na ƙarasa wajen Baba Malam da Wawo, daga nesa Baba Malam ya yafitini na isa inda suke. "Sabuwa wannan irin rama haka subhanallah kiyi haƙuri ki rage ma kanki damuwa yanzu shari'ar zata soma tafiya in sha Allah da sannu zaki cimma burinki kinji ko?" Kai kawai na gyaɗa haka suddan naji jikina yanata rawa. Ina wajensu Baba Malam lauyana ya ƙaraso a gaggauce isowarshi ke da wuya lokaci ya cika duk muka rankaya zuwa cikin kotun. Waje kowa ya samu ya zauns sai ɗan tashin hayaniya kasancewar alƙalin bai shigo ba tukunnah. Sha biyu da mintu biyar alƙali ya shigo duk muka tashi cike da girmamawa har saida alƙali ya zauna kana muka zauna bisa dokar kotu. "Ayau ɗaya ga wata wannan kotu zata sake sauraran shari'ar Sabuwa wacce ta kawo mijinta ƙara tana neman ya saketa" Numfashi na ja a hankali tare da ɗan dafe gefen zuchiyata dake wani irin dokawa ga zazzaɓi kau a jikina. "Ko lauyoyin dukka ɓangaren biyun suna cikin wannan kotu su tashi su gabatar da kansu?" "My Lord sunana Barrister Ahmad Ahmad nine lauyan wanda ta shigar da ƙara nagode my Lord " Ya zauna cike da girmamawa lauyar Babangida ta miƙe itama naga kamar yau ita kaɗai tazo. "Sunana Asabe madaki nice lauya mai kare wanda ake ƙara" Bayan alƙali yayi rubutu tare da dogon nazari can yace. "Ko lauyan wacce tayi ƙara yana da wata hujja mai ƙarfi da zai iya gabatarma da kotu?" Zumbur ya miƙe tamkar wanda akaima allurar zabura. "Akwai my Lord. Inason in gaiyato surukin SABUWA Malam Baba domin ya zame mana shaida ta farko " Ajjiyar zuchiya na sauke tare da lumshe idanuna da suke mun wani irin yaji. Ɓangaren Babangida na kalla, haƙiƙa naga damuwa sosai shimfiɗe a fuskarshi, haka ma Malama Babba nata baya musaltuwa. Murmushi ne ya suɓucemun. Muryar alƙali ce tasa na nutsu. "Kotu na neman Malam Baba ya fito gabanta" A tsanake Dattijon ya fito tare da tsaiwa a cikin ɗan akwakun tsaiwa. Barrister Ahmad Ahmad ya ƙaraso gabanshi. "Malam ko zaka faɗama kotu sunanka da halaƙarka da Sabuwa dama Babangida?" "Sunana Malam Baba kamar yadda ake ce mun. Ni mahaifin Babangida ne, Sabuwa surukatace" "Kaji abinda Sabuwa tace game da ɗanka Babangida sannan tace kai kake ciyar da'ita kake shayar da'ita ya abun yake?" "Ina da ja ya mai Shari'a. Barrister Ahmad Ahmad yana amfanine da salo na ɗaurama shaida magana a baki, koko ince ɗaurashi akan abinda yake son ya faɗa wanda hakan ya kauce ƙa'idar aiki." Alƙali ya jinjina kai. "Barrister Ahmad Ahmad a kiyaye" "In sha ALLAH my Lord" "Haƙiƙa duk abinda Sabuwa ta faɗa hakane. Na ɗauki tsawon lokaci ina biya ma yaranta kuɗin makaranta, kuɗin motar zuwa makarantar dama kuɗin tara duk ni nake biya.Batun ciyarwa ya ɗakko asaline a lokacin da shi Babangida ya auro wata mata daga lokacin ne ya dena ba Sabuwa da yaranta abinci. Ko da ta kawo mun ƙarar saina bata haƙuri ni na ɗauki nauyin ciyar dasu har kawo yanzu da nake magana anan ni nake basu abinci. Haka ma sutura kamar da Sallah, ko wani ankon biki duk ni nake yi mata" Kai barrister Ahmad Ahmad ya gyaɗa yace. "Am Malam shin Babangida bashi da halin ɗaukar nauyin iyalinshi ne, ko kuwa Sabuwa da yaranta yake yi ma haka?" "Sabuwa kaɗai da yaranta yake yima haka. Mutumin da a lokacin yake da gidan kanshi, kamfanin kanshi, ga motar hawa, yana iya ɗebe matanshi su tafi umara ai kaga yafi ƙarfin ciyarwa" Numfashi na kuma ja tare da saukewa da ƙyar dan ji nayi numfashina yayi mun wani irin tauri na ban mamaki. "My Lord iyakar tambayar da zan yi mishi kenan" Cewar Barister Ahmad Ahmad. Alƙali yace. "Ko lauyar wanda ake ƙara yana da tambaya?" "Akwai My Lord" Tattakowa tayi har zuwa bakin ɗan akwakun. "Malam Baba ko zaka iya faɗama kotu yadda akayi Babangida ya auri Sabuwa?" "Zan iya faɗa miki yarinya. Su suka ga juna suka amince da junansu mu kuma iyaye mukai musu ido" Gabanane ya faɗi ras. Sai naga Barrister Asabe madaki tayi dariya tace. "Amman a yadda labari yazo mana Babangida baya son Sabuwa kaine ka tursasa mishi harma ka kafa mishi sharaɗin muddin ya saketa saika tsine mishi" Shiru ne ya biyo baya na wani lokaci. Malam Baba ya dubi Malama Babba tayi saurin sauke kanta ƙasa, kai ya girgiza dan yayi imani wannan aikinta ne. "Hakane kenan Malam Baba?" "Ina da ja ya mai Shari'a" Barister Ahmad Ahmad yayi saurin ƙwatan malam Baba sai dai kash ƙorafi bai karɓu ba. "Barrister Ahmad Ahmad dole malam Baba zai amsa tambayarnan" Asabe madaki ta dubi Malam Baba tace. "Kotu kai take saurare" "Hakane yarinya abinda kika faɗa. Amman wani babban daliline wanda sirrine na cikin gida yasa na faɗi hakan" "My Lord a wannan gaɓar nake so wannan kotu ta duba wannan shari'ar da kyau Shari'a ce mai sauƙi. Babangida iyayenshi yayi ma biyayya yake tare da Sabuwa tsawon shekaru fun goma sha. Malam Baba yaso ya ciyar da Sabuwa da yaranta ne sabida shi ya haɗa auren bawai dan Babangida ya gaza ba. A binciken da nayi a kab layin da gidan Babangida yake babu gidan da ya kai nashi abinci kuma iyayen ita kanta Sabuwan shaida ne. Sabuwa sharri kawai take ma Babangida domin ta haɗa shi faɗa da mahaifinshi amman bai rageta da komai ba. Inaso wannan kotu ta bani dama in kira Rakiya mahaifiyar Sabuwa tazo ta bayar da shaidar abinda ta sani" Hawayene suka gangaro a guraben idanuna masu zafi. Alƙali yace "Zamu tafi Sallah mu je mu dawo kafin Rakiya ta fito ta ba da nata shaidar." Yana gama faɗin haka ya miƙe yabi ƙaramar ƙofa. Duk kowa saiya soma fita ni kam saida Adama ta tallafeni kana na iya miƙewa tsaye a hankali muka fita. Kasancewar anata kiraye_kirayen sallah a masallacin kotun hakan bai bamu damar cewa komai ba, alwala kawai aka shiga kiciniyar yi. A zaune na gabatar da Sallah na daɗe a raka'ar ƙarshe goshina a ƙasa sai kuka kawai nake yi, kaina da idanuna kuwa kamar zasu zazzago. Ina idarwa Rakiya tace. "Kuka yanzu ne dai zaki yi mai hujja ba dai ke taurin kai gareki ba? Ko ɗigon tausayinki bana ji kin haɗa kai da uban miji sabida son zuchiyarku" Miƙewa nayi na barsu a wajen na koma barandar bakin kotun nayi zamana ina mayar da numfashi. Nasan Rakiya zata jagula komai amman dukkan abinda Allah yayi mai kyaune a raina na gama yanke hukuncin matakin daya fi dacewa dani tuni. Abinci Babangida ya turo Ramadan dashi takeaway biyu nawa ɗaya na Adama ɗaya. Lafiyayyar party jallof rice ce wacce taji hanta ga kaza ƙatuwa akai sai fanta ɗaɗɗara. "Lolo ki daure kici, sai ki watsa magungunanki ɗaya har ta wuce kusan da minti ashirin" Cewar Adama wacce take ma wannan abinci cin yinwa." Bana jin ko ruwa zan iya kurɓa Adama ke dai kici maganinma ki barshi zan sha in muka koma gida" "Amman Lolo wanne irin in muka koma gida ke da kike cikin ciwo" Dan Allah Adama ki barni. Ciwon dake zuchiyata yafi wannan ciwon da kuke kallo, asalima ciwon zuchiyarne ya haifi waɗannan ciwukan. Madamar ina amsa sunan matar Babangida ku cire rai da rayuwata dan wallahi yadda nake ji mutuwa zanyi. A haka muka sake shiga kotu ko gani da kyau bana yi. Sama sama na dinga jiyo Rakiya. "Wallahi ƙarya take yi. So take ya saketa ta auri tsohon saurayinta wanda shi Babangida ya kamasu tare kawai. Amman ita da take cewa babu abinci a gidanta itace fa take taimakonmu da abinci da kuɗi. Iyakar abinda muka sani Babangida na ƙoƙarinshi...." Bansan da waɗanne kalmomi Rakiya ta ƙarashe jawabinta ba, dan kunnuwana doɗewa suka yi. Sai ji nayi alƙali yace. "Bayan sauraren wannan ƙara, da yin nazarin hujjojin da suka gabata wannan kotu ta kori wannan ƙara" Shima a iyakar haka kunnuwana suka dena jiyo komai bafa suma nayi ba, ina kallon mutane suna ta fita a kotu Adama da Labbai suna riƙe dani har muka fita. Ku kaini gida Labbai kada ku kaini in mutu a ɗakin Babangida" "Kiyi haƙuri Lolo kada ki kashe kanki, yanzu in muka kaiki gida wani ƙarin baƙin cikinne gara muna tare dake acan gidan kafin mu san abunda zai biyo baya. Amman Rakiya sun bani mamaki bana wasa ba." "Niko basu wani bani mamaki ba. Kuɗi masu yawa Malama Babba ta aiko Wawo jiya da daddare ya kawo musu, Rakiya da Maigogul akan kuɗi babu abinda ba zasu iyayi ba wallahi." Sama_sama nake jinsu gani ido a buɗe ina tafiya da ƙafafuna amman babu hankali a tattare dani. A falo muka ya da zango tunda na rufe idanuna hawaye sukaita sakkowa a idanuna naƙi buɗewa. Babu irin bam baki da magiyar da su Labbai basui mun ba, amman naƙi magana. Har su Sadiya da Uzairu zuchiyata, da Sama sun zo naki magana fur, na ƙi buɗe idanuna. Sun kai kusan magriba sunata mayar da zance tare da tattauna abunda su Rakiya suka yi a katu sabida kuɗi. Dana gaji da ji da bin bango na rarrafa na ƙule ɗaki na saka sakata. Babu wanda yayi yinƙurin biyoni suma sun lura kaɗaici nake buƙata. Ƙaramin akwatina na jawo na buɗe durowa na zuba kaya wallahi bansan wanne irin kaya na zuba ba, sai tarkacenmu na mata, na kulle akwatinnan, na jingineshi tare da ƴan uwanshi, ƙaramar jaka na ɗakko baƙa na mayar da ƴan kuɗaɗena ciki, da su katin ɗan ƙasa da Atm card ɗina guda biyu sai ɗan kunnen goid ɗina dana yaran. Itama jakar na adanata kafin na buɗe sakatar da bin bango na shiga banɗaki, ina jiyo yara suna mun sannu naƙi magana bana tunanin ma harshena zai iya sarrafuwa harya bada harafin da za'a fahimta. Alwala na ɗauro na koma ciki a ɗakin na tadda Adama suna waya da Gaza tana labarta mishi abinda su Rakiya suka aikata. Ni dai daga zaune na yi sallah. "Lolo ga abinci ki daure kici ko dan ki samu lafiya kinga ya kamata ace kin sha magani. Da ido kawai nake binsu naƙi yin magana. Sai abun ya shiga basu tsoro kuma duk sukai cirko_cirko a kaina. Ana cikin haka muka jiyo sallamar Babangida. "Shigo Babangida gara da Allah ya kawo ka. Shigowa yayi muka haɗa idanu nayi mishi wani irin kallon da saida ya tsorata. "Kaga Lolo babu ci, babu sha, babu uhm babu uhm_uhm tunda muka baro kotu." Take ya firgita yace. "Adama kamar yaya ban gane me kuke son kuce mun ba." A mugun tsorace yayi maganar Labbai ce tayi mishi bayanin yadda zai fahimta. A hankali ya tsugunno a gabana ya zuba mun ido kawai yana kallona. "Sabuwa kina jin abinda nake faɗa? In kina ji amsa kika kasa mayarwa bakin ki yaƙi buɗewa ki ɗaga mun kai" Ban ko nuna da wasa naji abinda yace ba. Hannunshi ya ɗaura a kaina a tsanake ya soma karanto Qur'ani cikin kira'a mai daɗin saurare. Ni dai ko tari yafi awa ɗaya yana mun karatu banko yi tari ba, sai hawaye dake ta zuba a idanuna" "Babangida anya Lolo ba gamo da aljanu tayi ba kuwa, ko ko dai baƙin cikin abinda ya faru a kotunne duk yasa ta koma haka. Kaima dai hanyar daka biyo gaskiya yau dai ɗaya in ɗana baka kyauta ba. Taya zaka haɗa kai dasu Rakiya sabida Allah, sabida kasan babu abunda ba zasu iyayi akan kuɗi ba ko? To yanzu ga abinda hakan ya haifar" Ni dai idanuna a lumshe suke. Adama da Labbai suka kinkikeni zuwa kan gado suka shimfiɗeni. Ina jin sanda Babangida ya zauna akan gadon ya riƙo hannuna. "Adama wallahi duk abinda kika ga ya faru a kotu bani da masaniya a kanshi. Yadda kuka ji nima haka naji. Ni bama wannan ba lafiyar Lolo yanzu itace a gabana, in har batai magana ba zuwa gobe da safe sai mu wuce da'ita asibiti. Kuyi haƙuri dan ALLAH ni dai naja komai ni na lalata komai lokaci bai kure ba zan gyara abinda na ɓata da hannuna. Wallahi ina son lolo inason zama da'ita" Wayarshi ce ta shiga ruri Da sauri ya zaro a ajjihu tare da karawa a kunnenshi. "Assalamu alaikum Kawu Manga. Barka da dare" Daga wayar Kawu Manga yace. "Abin duk da ake gudu ya faru. Kazo gida ka samemu yanzu. Malam yana cikin mawuyacin halin da babu Lallai ka iso ka taddashi da ranshi. Ina jiye maka tsoron Yaya ya rasu da baƙin cikin ka Babangida kazo maza" A mugun gigice ya miƙe baice komai ba ya fita har yana tuntuɓe tsabar firgici. Adama tace. "Malam ne naji ta wayar ance baida lafiya. Ni Labbai wallahi tausayi Babangida yake bani. A wannan karon nadamarshi ta gaske ce ga mahaifinshi yana fishi dashi oh ni Adama wannan Aure" Haka dai sukaita tattaunawa a tunaninsu bacci na samu, ni kuwa nasu baccin nake jiran samuwarshi in kama gabana in tafi inda yafi dacewa dani tunda dai ƙarfi da yaji bariki suke son in shiga ai sai in koma ruwa." Na daɗe idanuna suna rufe ina sauraren muryoyi da motsi, har yara duk sun shigo sun dubani ina jinsu. Daga inda nake kwance ji nake tsabar jiri tamkar gadon sama yake tashi dani. Ina dai jirace har na soma jin saukar munshari halamar bacci yayi nisa. A hankali na buɗe idanuna, amman me sai naga bana ma gani sosai duhu_duhu nake gani. Cikin dakiya da dauriya na miƙe zaune, nafi tsawon minti biyar kaina na hajijiya. A hakan na yinƙura dafe da gadona. Jakar hannu kaɗai na ɗauka ko mayafi babu na fice a ɗakin da bin bango. Cikin nasara har na fice a gidan ban haɗu da kowa ba. Ina isa titi na tari mota. Hotel mafi kusa zaka kaini ni baƙuwace" Nayi mishi maganar a hankali tamkar wacce take a bige. "Shata ne Hajiya?" Murfin gaban motar na ɓalle na faɗa da ƙarfi na zauna ina dafe da kaina. Tsabar ciwon kai ko haske bana son bude idona in gani. E shata ne kai dai muje" Figar motarnan yayi muka bar bakin unguwarnan. Na barta kenan har gaba da Abada ba zasu sake sakani a idanunsu ba. MRS Buhari
Sai monday in Allah ya nuna mana Son so.
Ku faɗi ra'ayoyinku Shin Sabuwa abunda tayi shine daidai. Ko kuna ganin da bata shiga duniya ta dage akan neman saki. Wasu ma suna ganin gara Sabuwa taci gaba da zama da Babangida ko????
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA SHA BIYAR BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
INA MIƘA SAƘON GAISUWA A GAREKU MASOYA WANNAN LITTAFIN HAƘIƘA INA GANIN RUWAN COMMENTS ƳAN BATI. COM MA BA'A BARKU A BAYA BA SAƘONKU YANA ZUWA GARENI SON SO💪🏼🤺
Mai mota a ina kasan zan samu kayan caja kai da daddarennan?" Nayi maganar a hankali dan ji nake tamkar kaina zai rabe gida biyu. "Duk wannan cakewar batai miki ba har sai kin sake hawa gajimare? Amman Hajiya daga gani ke babban kaine. Bari muje bakin kusfa akwai masu saida kaya a titi" Kai tsaye kusfa ya kaini, wajen a baya muke zuwa sayen kayan harka. Motarmu na tsaiwa matasa biyu suka ƙaraso suna rige_rige. Jakata na buɗe na ciro dubu ashirin na miƙa ma saurayin da shine yai nasarar kunno kanshi cikin motar. Haɗin makara kusa zakaimun kar ka cire komai" Da mamaki ya kalleni. "Ke wallahi zaki iya haukacewa in nai miki hadin makara kusa. A mazan ma sai manyan kai kina mace ina ke ina haɗin makara kusa. Ai naga mata sunfi yin haɗin sha ka lula shine daidai abinda kanku yake ɗauka. Jibeki a ƙwale kin kasa mallakar kanki amman kike neman makara kusa" Dariya suka saka shi da mai motar. Samari kai dai bani, ka haɗamun da sigari kwali biyu" Jim yayi yana juya kuɗaɗen daga baya dai ya dubeni da kyau yace. "Wannan ba Lolo bace ƙanwar Gaza ba, ko ba ita bace?" Ni dai kaina kawai na dafe da nake ji tamkar zai tarwatse dan tsananin ciwo. Ganin ban saurareshi ba yasa ya kirgo kayan kuɗina ya miƙo mun muka wuce, mai mota ya saukeni a Hotel na biyashi kudinshi na shiga a hankali. Motoci sai shiga cikin hotel ɗin suke yi kasancewar ƙasa ƙaton club ne ( gidan rawa da lalatartun mata da maza ke zuwa domin alkata biɗala) ga mata matasa da waɗanda suka mallaki hankalin kansu, ko wacce cikin shigar banza take. Wajen sai hada_ hada akeyi tamkar rana Allah kaɗai yasan ƙarfe nawan dare ne a lokacin. Dogon falon zangon baƙin. Wani dattijo a baya suka shiga da wata yarinya da bata wuce Mardiyya ba tana biye dashi. Da ganinta sabuwar shiga ce dan sai kame jikinta take yi, kuma tana ta dan kalle kallenta. Mu kula da yaranmu wallahi. "Daki kike so Hajiya, ko tare kuke da Alhaji ne?" A_a ɗaki nake so a bani" "Muna da ɗaki ɗaya, muna da mai ciki da falo wanne kike so?" A bani mai ciki da falon" Na yi maganar a hankali. Takadda ta bani na cike da sunan Mardiyya na ɗakko lambar da ban santa ba na saka tare da adireshin bogi. Wannan dattijo sai kallona yake yi yana murmushi irinna cikakkun mazan bariki Hmm. Sabida rakiyar asara shi ya biya mun kuɗin ɗakin gashi kwana biyu na rubuta. Godiya kawai nayi mishi. Ɗakinmu a jere yake, tare dasu ma muka hau ƙafar benen da zata sadamu zuwa ɗakunan kwanan da suke a jere cikin tsari. "Hajiya sannu ko?" Yace dani yana satan kallon berar da bansan me zai kwasa a jikinta ba. Ɗakina na buɗe na shiga na tura ƙofa kana na jingina a jikin ƙofar. Ɗakin nake ƙarema kallo, tsari da haɗuwar ɗakin, gami da ƙamshi, da ruwan wajen kaɗai ya isa ya sakkoma da mutum nutsuwa. Duhune ba sosaiba mamaye a ɗakin, akwai hasken jar wuta a kan durowar dake manne da gado daga cikin ɗakin ya bada ɗan gasken da mutum zai iya ganin tafin hannunshi. Idanuna na mumshe wasu hawayen baƙin ciki suka shiga zubo mun. Shaidar da Rakiya ta bayar a kaina a kotu da yanda suka nuna sunfi son kuɗi sama da rayuwata yafi komai damuna. Shikenan gaku ga kuɗin da aka baku kuita ci har duniya ta naɗe Sabuwa kuma kun rasata har duniya ta naɗe dama ba damuwa damu kukai ba, asalima duk matsaltsalun rayuwarmu kune. Tur_tur da iyaye ire_iren su Maigogul da Rakiya. Wallahil azeem irinsu sunanan a cikin gidaje masu yawa waɗanda suke cikin abunne zasu gane zafi sa raɗaɗin da zuchiya take ciki. Ji nake kamar in bulbulama kaina fetur in ƙyasta ashana. Jakata na buɗe na zaro sigari a kwali inason in kunna bani da ashana. Jefa jakar kan kujera nayi. Na shiga ciki kai tsaye banɗaki na shiga na saki ruwan sanyi a kaina ya dinga zuba. Dana runtse idanuna mutane uku nake gani a idanuna Babangida Rakiya, Maigogul waɗannan mutane ukun sune matsalar rayuwata. Ƙwaƙwalwatace ta shiga tariyo tarin tulin rashin tarbiyyar da muka taso a cikinta. Taya ma zamu yi tarbiyya alhalin masu bada tarbiyyar ma tarbiyya suke buƙata?" Kuka mai ciwo na fashe dashi. Na jima ina tsaye ina kukan baƙin ciki kafin daga bisani da naji kaina na neman tarwatsewa na ɗauro tawul na fito daidai buga ƙofar ɗakina da ke jiyowa. Jikina kuwa zazzaɓi ba'ama wannan maganar. Dan ruwan sanyin da nayi wanka dashi wallahi daya sauka a jikina yake komawa na zafi tsabar yadda jikina yayi kau. Daga ni sai tawul ɗinnan ruwa na ɗiga a kaina na buɗe ƙofar mu kai ido huɗu da wannan dattijon. Sai karema zatina kallo yake yi. Lafiya kake bugamun ƙofa?" Firgigit ya dawo hayyacinshi. "Am dama inaso in ɗan tambayeki ne tare kike da wani ne, ko dai kema bakuwace a garin kamar ni?" Baƙuwa ce bansan kowa ba" Na bashi amsar a taƙaice. "To masha Allah. Abinci zansa a kawo mana ke me kike da buƙata in sa a kawo miki? Sunana Alhaji Hazallaha kefa?" Ya ƙarashe yana dariya har saida haƙoranshi na makka sama da ƙasa suka bayyana. Mardiyya sunana. Farfesu ma ya wadatar, in zasu kawo dan ALLAH su haɗo mun da laita inaso zan sha sigari" Har zan mayar da ƙofata in rufe ya miƙo mun laita daga ajjihunshi. "Gashi, ai ni bana rabo da'ita a duk inda nake. Zan neme ki ko da zuwa anjima ne" Hannu nasa na karɓa na rufe ƙofata. Saida nasha sigari kara biyar a take kafin na soma jin ɗan dama_dama daga cikin azabar da zuchiyata take ciki. Amman me ina tuno Ƴaƴana sai zuchiyata take ta sake yin baƙi Oh ko wacce iriyar rayuwa su Mardiyya zasu shiga bayan jin labarin guduwana oho. A duk inda na tsinci kaina zan kasance mai yi muku adda'a." Sigari na sake kunnawa na ci gaba da zuƙa ina fesar da hayaƙin idanuna ina jinsu a bushe kamar babu digon ruwa a cikinsu. Ƙwanƙwasa ƙofa naji anayi a hankali. Tashi nayi na zura rigata na fito na buɗe ƙofar. Ma'aikaciyar hotel ɗince riƙe da turen silver ɗauke da kwanon farfesun kaza, sai tea da ruwa mai sanyi. Hanya na bata ta wuce ciki, ɗakin cike yake da hayaƙi har tari saida ya turniƙeta da sauri ta fice, na mayar da ƙofata na rufe. Da ƙyar na iya cin cinyar kaza ɗaya, dan jinta nake a bakina tamkar maɗaci, kayan ƙari dai na watsa a bakina na biyeshi da ruwan tea mai zafi. Na jingina a gado ina murmushin da yafi kuka ciwo Idanuna na lumshe sai nake hasko rayuwata ta baya nake ganinta tamkar yanzu abun yake faruwa a gabana.
WAIWAYE:.
Kamar yadda kukaji a baya Rakiya Ƴar kano ce iyayenta sunyi rayuwa a ƙaramar hukumar Bebeji dake jihar kano kafin daga baya kuma Allah ya amshi abinshi. Har gobe family house ɗin su Rakiya yana nan a Bebeji, kuma muna zuwa biki, mutuwa sunane kaɗai bama zuwa kundai san ƴan ƙauye da sha'anin haihuwa. Itama ƙannenta, da yaransu suna kwaso jiki su tawo duk wani sha'ani namu, haka suddan ma suna zuwa mana ziyara. Zumuncinne yasa ma Tsahare ta dawo hannun Rakiya da zama bayan mutuwar Aurenta.
Maigogul kuma asalin mahaifinshi Malam Buba Ɗan wanka irin bararo ɗinnanne mazauna ƙasar nijar cikin garin damagaram nanne asalin tushensu. Malam Buba Ɗan wanka ya kasance bafatake ne suna fitar da kayan fataucinsu zuwa ƙasar Ghana. A wannan zuwa fataucinne Allah ya haɗashi da matarshi Fatima ita kuma asalinta basudaniyace haifaffun Ghana mazauna Ghana cikin garin kumasi. Sukai aurensu suka haifi Maigogul da ƙaninshi Isuhu suke nan yaran da Allah ya basu. To sun zauna a ƙasashen afrika da dama irinsu, Angola, kamfala, Kongo, da dai sauransu daga ƙarshe suka yada zangonsu na ƙarshe a jihar jigawa. To a wannan tafiye_tafiyen da akaita yi Maigogul da Isuhu annan idanunsu ya buɗe sosai. Iyayen Maigogul Allah yayi musu rasuwa tun su Maigogul suna ƴan Samari dai haka. Sun mutu sun bar musu tarin dukiya da zanarai amman dangin Malam Buba Ɗan wanka suka yi rub da ciki kan dukiyar, sukai watsi da zumunci, suka kasa ɗaukar nauyin ci gaba da karatun su Maigogul, izaya babu iriyar wacce ba'a ganama su Maigogul ba. Kuma mahaifinsu yana da tarin raƙumai daya barsu a hannun ƴan uwanshi. duk suka haɗa suka cinye suka bar su Maigogul a wulakance Wannan shine tsanin daya zame ma Maigogul silar faɗawa bariki. Babu iriyar halastacciyar sana'ar da bai jarababa amman babu riba, duk abinda ya taɓa sai ya lalace mishi. Sai daga baya Maigogul ya faɗa harkar kawalci ta dalilin Amininshi cicib da suke kwana a ɗaki ɗaya. kamar wasa sai harkar ta soma kai mishi har ma ya auri Rakiya kayi nayi suka soma tara iyali. Wannan shine asalin salsalan tushenmu. Shi yasa Allah ya yimu kyawawa farare sol duk da a cikinmu babu wanda ya kama ƙafar Maigogul a kyau sai Uzairu zuchiyata dan kamar kumbo ne kamar gatanta shi da Maigogul. (Na yanke muku tarihin Rakiya da Maigogul sabida labarin asali na Lolo ne ba iyayenta ba) Wannan kenan.