Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 13
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 13: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 13. Tana zaune tana jinjina kanta tana rantsuwar ko sama da ƙasa haɗewa zata yi ita…
4,262 words
Tana zaune tana jinjina kanta tana rantsuwar ko sama da ƙasa haɗewa zata yi ita ba zata riƙe ɗan kishiya ba. Ana cikin haka mahaifiyarta da Ƙanwarta Luba suka yo sallama suka shigo" "Iko sai Allah wai na kwance ya faɗi Ramatu haka rayuwa ta juya miki baya. Ji wani ɗaki kamar faɗin store ɗin gidan tsohon mijinki Karab a kunnen Babangida wanda yake kwance yana roƙon Allah gafarar kusakuranshi. Take kishi ya murɗeshi babu shiri ya miƙe ya tattaka har zuwa bakin ƙofar ɗakin dan ya gane muryar waye. "Mahaifiyarta ce da bakinta take faɗin wannan maganar?" Kai ya jinjina ya koma ɗaki amma yana ma jiyosu. "Umma kune a tafe sai yau kuka samu damar zuwa?" Cewar Ramatu data miƙe da ƙaton cikinta a gaba. "Ramatu wai nan kuka dawo? Mai yasa Babangida bai kama muku babban gida da babban falo ba, gida babu Ac babu yalwa shi baisan inda ya ɗakko ki bane? Ko da yake ai kince kafin a gama gyaran gidanshi ne ko?" Ramatu dai murmushin da yafi kuka ciwo tayi suka gaisa ta kawo musu ruwa da abinci. Kular abincin Luba ta buɗe shinkafa ce da miya sai kifi da aka murmusa a miyar da hala ma yanzu ta murmusa kifin da zata kawo musu,dan kifin na saman miyar duƙui bai shige cikin miyar ba. "Tabb ni kam na ƙoshi abinci Babu nama babu manyan soyayyun kifi wa zaici. Umma in zubo miki?" Dariya kawai Ramatu tayi ma Luba tana tuno gidan tsohon mijinta da ita ta kasheshi da baƙin cikinta. Nama, kaji, talo_talo babu irin abinda baya jibge mata na jin daɗin rayuwa, amman nan data biyo soyayya ga irin yadda rayuwarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci. "Zuba mun in ɗan taɓa" Ta jiyo muryar mahaifiyarta wanda yayi sanadiyyar katse mata zaren tunaninta. Luba ta zuba ma umma Abinci bata kai ga ci ba Khalifa ya shigo da gudu Usama ya biyoshi. "Shi kuma wannan mai shanyayyen idon da gani ɗan Babangida ne idonsu iri ɗaya me yake yi a ɗakin ki tare da Khalifa?" Ramatu tayi ƙasa da muryarta. "Umma Babangida yana ciki kiyi a hankali. Uwarshi aka saka, shine dan ya rainani yake so in riƙe yaron wai" Baki umma ta rufe bata ce uffan ba ta shiga tura abincin a loma biyar dai ta ajjiye abincin. "Ke ni na ƙoshi abinci ba fasali, wai miyar tumaturi ce wannan koko ta jajjage ce Ramatu?' Miƙewa Ramatu tayi tare da ture Tambayar umma da fadin. "Bari in sanar ma da Babangida zuwanki yazo ku gaisa" Tana faɗin haka ta wuce. Da sallama ta shiga ɗakin idanshi biyu, ido suka haɗa yana cikin yanayin dai da yake. "Ba nace bana son ki shigo ba ina neman kaɗaici ne ba. Me ya kawoki, shikenan ni da gidana bani da ikon da zan kwanta in huta akeso ace kome uhm?" Ya kakkafeta da idanunshi da suka zama jawur. "A_a dama umma ce suka zo ita da Luba shine nace kazo ku gaisa. Sannan in akwai kuɗi a jikinka ka bani ko lemo in sai musu" Murmushi kawai yayi ya kawar da kanshi can gefe. "Kije ki faɗa musu bacci nake yi. Ai na faɗa miki kaɗaici nake nema a zahirin gaskiya bazan iya fitowa ba". Mamaki da al'ajabine ya kashe Ramatu umman tata yaima irin wannan rainin da har yake jin bazai iya fitowa ma su gaisa ba duk irin halaccin da tayi mishi? Maza kenan. "Hmmm to me" "Dakata da Allah" Yayi saurin ɗaga mata hannu ranshi ya sake mugun ɓaci, take ta shiga taitayinta. "Tun kina iya gane kanki ki kama hanya ki fice na faɗa miki kenan" Cikin ɓacin rai ta fice harda tsaki, ji yayi tsakin yayi tsaye a zuchiyarshi ya caka mishi. Amman yaya zaiyi, yana tunanin soma gyara kanshi kafin ya saita gidanshi tukunna. A haka Ramatu ta koma falo cike da fara'a tamkar babu wata damuwa a ranta. Cewa tayi dasu yasha magani yayi bacci jikinne ya ɗan motsa mishi. Su umma dai basu daɗe ba suka ce zasu tafi. Maganganun data kunso sai a bakin get suka samu zarafin tattaunawa. "Ato tun wuri ki ma kanki faɗa yarinya dake karki kuskura ki kashe rayuwarki akan wani soyayya kisan inda dare yayi miki. Abokiyar zamanki da tasan me ke mata ciwo ba gashi harya sallameta ba? To kema kiyi iyakar yinki wata ɗaya tim na baki in ganki kin dawo gida da takaddarki in kuma ba haka ba tsame hannuna zanyi a cikin lamarinki"
Gaga gaga haka rayuwa taita garawa babu daɗi ta ko wanne ɓangaren. Abubbuwan mamaki sun faffaru masu yawa a ciki harda sauyawar Babangida da wata nutsuwa da kamala daya ara ya yafa ma kanshi, kullum bakinshi cikin istigifari yake in ka ganshi. Matanshi Ƴar Shuwa da Ramatu kullum basu da aiki sai korafi, shi kuma kullum a cikin basu haƙuri yake dan a yanzu yayi ma kanshi faɗa sosai baya yawan faɗa da matanshi. Ramatu data haifi ɗiyarta mace cikin yana shiga wata na takwas da kwanaki ta haihu dan dana tana yin arba'in babu daɗewa ta samu wannan cikin na biyu, babu irin wulaƙanci da habaice_habaicen da baiji daga wajen danginta ba. Amman yayi iyakar yinshi ya danne zuchiyarshi ya rabu dasu. Ranar suna kuwa da su Mustapha suka shigo da tunkiyar da aka yanka nanma kamar dai za'ayi faɗa danma su Sa'a ba kanwar lasa bane. Shi kuma Babangida a hakanma su Mustapha ne suka sai mishi tunkiyar, da dan tashi ne ma ko yankan ba za'a samu yi ba. Dan tun ranar da Wawo yace a gaban Malama Babba cewar baya son ya ɗauki Babangida aiki a kamfaninshi sabida baya son ya rabeshi. Shi kuma tun lokacin ya dena neman taimakon kowa haka ya dinga bi islamiyoyi yana neman koyarwa, har ya samu gurbin koyarwa a islamiyoyi biyu. Malama Babba ta saida ɗan kunnen gwal ɗinta ta tarkata kuɗi dubu ɗari biyu ta kira Babangida ta bashi akan ko shago ya kama ya zuba kayan kwalliya, amman Babangida yaƙi karɓa fur dole ta haƙura. Haka abokanshi suka haɗa kuɗi dan su taimaka mishi suma yaƙi karɓa. Sai dabarar siyo kayan abinci suka yi suka rarrabama matanshi. Ta ɓangaren Ƴar Shuwa kuma dan bala'i har ɗan kunnenta ta saida ita da uwarta sukaita shiga lungu da saƙo akan lallai_lallai sai sun sa Babangida ya saki Sabuwa ko ta halin Yayane. Sun karɓo magunguna iri_iri kuma duk yadda akace Ƴar Shuwa tayi amfani da magungunan tayi. Jira suke ranar zaman kotu na biyu alƙali yasa Babangida ya saki sabuwa kawai. Ta ɓangaren kuma Hamida sun turo motar kaya tare da yayyenta sun zo sun ɗebi kayanta ɗakin ya rage babu komai a ciki, Babangida yasa ɗan makulli ya kulle ɗakin. Gabaki ɗaya hankalin Babangida yana kan Sabuwa, ya hanata sukuni sam, ko gida zata je sai dai ta bari inya fita ta samu ta tafi, da zaran kuwa ya dawo ya tadda bata gidan har gidan nasu yake zuwa nemanta ya tusota gaba su dawo suna tafe suna caka ma juna magana. Ta ɓangaren Baba Malam. Babu wanda bai sa baki akan yai haƙuri Malama Babba ta dawo cikin gida ba amman a wannan karon wannan dattijo mai haƙuri da kawaici ya runtse idanunshi yaƙi amincewa fur. Anyi zama sosai akan yayi haƙuri ya dena fushi da Babangida kuma ya barshi ya dinga zuwa gaisheshi. Wannan dai ya amince da ƙyar. Babangida ya roƙa a roƙar mishi Baba Malam akan ya barshi yaci gaba da koyarwa shi baya son a biyashi ko sisi lada yake nema amman fur Baba Malam yaƙi amincewa haka dole Babangida ya haƙura. Duk sanda kuwa yaje gaishe da Baba Malam a cikin damuwa mai girma yake tafiya. Dan bayan sallamarshi da yake amsawa sai Lafiya da yake ɗaurawa dashi, in Babangida ya tambayi ƙarfin jikinshi ma sai yayi saurin ɗaga mishi hannu, ga ciwo yana gani Baba malam yana yi a tsaitsaye."
Ta ɓangaren gidansu Sabuwa kuma Anyi bikin Sama da Rita, da kuma bikin Qamriyya dukkansu suna zaune anan dutse. Gaza kuma Allah yayi fitowarshi daga furzin ya sake zama ruƙaƙƙen ɗan daba ga ƙwacen waya, da satar mashina da suke yi. Lokaci guda Gaza ya sake sauya rayuwarshi da Abokan shi ya shiga cikin tawagar marasa jin da ake jin sunatensu a Jigawan dutse, su kansu a gida ganinshi wuya yake musu, duk kuwa ranar da zai zo ganin karnukanshi da daddare yake shugowa fuska a kulle. Ta ɓangaren Rakiya da Maigogul kuma har izuwa wannan lokacin duk sanda Sabuwa tazo gida sai ta tafi da zafin zuchiya har izuwa wannan lokacin suna kan bakarsu akan sai dai ta janye wannan ƙarar, ita kuma tana kan bakarta na son rabuwa da Babangida ko ta wanne irin haline. Akace duk abinda akasaka mishi rana komai daren daɗewa zaizo. Yau saura kwana ɗaya a sake zaman kotu. Wasu zukatan cike suke da fargaba kamar zuchiyar Babangida da Malama Babba, a yayin da wasu zukatan suke cike da fatan sakin ya yiwu a ciki harda Sabuwa da tafi kowa son ganin burinta ya cika, da Ƴar Shuwa data lashi takobin ko yawo tsirara zata yi sai Sabuwa ta dena amsa sunan uwargidan Babangida.
Sabuwa:.
Zaune nake ina kwashe tuwon dare da yamma sakaliya. Kwatsam na tsinkayo muryar Maigogul da Rakiya da Uzairu zuchiyata a tsakar gida suna gaisawa da matan gidanmu. Banji daɗin zuwansu ba sam, ni da nake fama da hawan jini ko gama warkewa banyi ba, sati biyu baya babu wanda yayi tunanin zan rayu har a asibiti na kwanta. Ciwon damuwa ( Deepretion) mai tsananine ya kamani har wani zabura nake yi, bacci kuwa saida na kai kwana biyu masu kyau banko runtsa ba. Kullum ina ƙunshe a ɗaki bana ko son ganin haske. Hakanne yasa hawan jinina shima ya hau sosai. Labbai da Adama ne sukai ta jinyata. Dangin Babangida babu wanda ya leƙo ni in Banda Wawo shima Baba Malam yake kawowa domin shi ya ɗauki nauyin duk wani kuɗi da aka kashe a asibiti. A wannan kwanciya da nayi ne dangina dana Baba Malam suka san ina ɗauke da hawan jini tare da ciwon damuwa. Babangida ma kullum da safe yana zuwa duba ni, haka ma da yamma. Da naji sallamarshi nake rufe idanuna bana buɗewa har sai naji ya fita. Yana kawo lemo da kankana kullum Sannan ana kawo abinci kullum. Adama ce ta fito daga ciki jin muryar su Rakiya. Tunda aka sallamoni daga asibiti Adama tana tare dani, ita ke mun aikace_aikace yaune ma na ɗan ƙwarara jikin nawa na fito nayi tuwo da miya, ita kuma na barota tana gyara ma yara kaya da suka hautsina a durowa" "Rakiya kune daf magriba haka?" Cewar Adama kenan. Hankalinsu Rakiya duk yana kaina. Maigogul yace. "Adama wani ciwon Lolo ta kuma yi ba'a sanar mana bane. Naga ta rame sosai tayi wani irin mugun haske. Lolo kada fa ki kashe kanki a banza da wofi kima ƴaƴanki asara." Cewar Rakiya kenan. Inda Maman Sa'idu take tsaye na kalla. Duk da a yanzu sun san duk halin da muke ciki da Babangida, da kotu da muke duk Ƴar Shuwa ta zaiyana musu tas harda ma ƙarya da gaskiya. Duk da dai hakan ba zan so su Rakiya su saki layi ba. Da dabara na miƙe. Ni kaina nasan na rame kuma ina jin jiki sosai har iska ƙaramun sauri take yi ko kuma in ta kaɗa inji kamar zan faɗi. Rakiya ku shigo daga ciki. Adama Dan ALLAH ƙarashe kwashe tuwon." Adama tace. "Ai sai da nace miki ba zaki iyaba kika ce zaki ƙoƙarta ina ƙarfi a jikinki ki ma." Shigewa ciki muka yi muka bar Adama na kwashe tuwo. Ina wuninku Maigogul?" Da fara'a suka amsa dukkansu tare da tambayana ƙarfin jikin" "Ai daga gidan Sama muke matar tashi bata ji daɗi ba shine muka je dubata Uzairu zuchiyata ya kaimu yarinyar kirki baki ga tarbar da tai mana ba duk da bata da lafiya. Kinga wannan ledar du cincin da dambum nama ne a ciki bayan munci da zamu tawo ta sake ciko mana leda" Ayya Allah ya bata lafiya" Iyakar abinda nace kenan, muka jiyo sallamar yaran. To ganin su Maigogul yasa duk suka kacame da sowa. Ni dai ina ta binsu da ido. Malama ce tazo ta taɓa wuyana. "Ummi ya jikin naki?" Sauran yaran duk sukai mun yaya jiki. Da sauƙi Malama ya karatun kuma?" "Karatu yauma na amsa Tambaya a islamiyya Baba malam ya mini kyautar Qur'ani izifi sittin yana wajen Adda" Dariyar yaƙe nayi nace. Kai masha Allah. Adda kuje maza ku sauya kaya. Su Aminu kuyi alwala kuje masallaci da Maigogul da Uzairu zuchiyata maza." Da hanzari mazan suka sauya kaya duk suka ɗauro Alwala, Maigogul ma ya shiga yayo alwala sannan Uzairu zuchiyata shima yayo suka wuce masallaci. Muma muka gabatar da tamu sallar. Ina zaune akan sallaya, Mardiyya sai shigo da tuwo take. Tuwon shinkafa ne miyar taushe da kaza da man shanu. Sai kunun Aya da yara suka roƙi Adama tai musu. Da sallama su Maigogul suka shigo. Duk muka haɗu muka ci abinci, ni tare da Adama da Uzairu zuchiyata da yaran dukka a tire ɗaya muke ci. Maigogul da Rakiya kuma kowa kwanonshi da ban. Ana ci ana hira kamar yadda muka saba a gida har dai aka gama. Ni loma huɗu nayi babu wanda ya lura, dan ban cire hannuna daga tuwon ba nakan lashi miya. Mardiyya ce ta miƙo mun ledar maganina. To kuje ɗaki kowa ya soma homewok ɗinshi kafin ayi isha kuma." Saida suka wuce kana na soma ɓallan magunguna. "To Lolo gamu dai mun sake zuwa miki akan batun rikicinki da mijinki a karo na barkate. Jiya naje wajen uban mijinki akan shi yayi miki magana yaƙi amincewa yace a barki ke ba yarinya bace kinsan abinda ya dace dake. To Lolo wallahi uban mijinki mugunta yake so yayi miki tunda ki tuna irin tababar data faru a shekarun baya a tsakaninmu dashi. Tun ranar farko ya nuna ƙyamarshi a kaina dame ke kanki da aminins cicib kuma kinsan komai. Har gobe baya ƙaunarki shi yasa shi farin ciki ma yake da wannan saki da kike nema. Kuma Malama Babba ta tabbatar mana da hakan. Malam Baba ya lashi takobin sai kin bar gidan Babangida ta ko ta halin ƙaƙane. Mu dai shawara muke baki Sabuwa ki janye wannan ƙarar kiyi haƙuri ki zauna a kan yaranki. Har abada bana tunanin cikin ƴan uwanki da kuka fito ciki ɗaya, da wanda kuke ƴan uba za'a samu wandda zata yi dacen miji kamarki. Kina gani duk gasu nan a gabanmu zawarcinma na wahala suke yi bansa Adama da dai ta samu Bazawari mai ɗan hannu da shuni. Batun aure fa ai har yanzu yaƙi fitowa kullum sai dai yazo ya ɗauketa su fita. Har gobe kun ƙi ma kanku faɗa kusan cewa ya kamata ku nutsu. To mu dai shawartarki muke yi sabida muna sonki magana ta domin Allah bama so aurenki da wannan bawan Allah ya ƙare ko ba haka ba Rakiya?" Maigogul ya ƙareshe maganarshi yana mai taɓa cinyar Rakiya. Ni sabida mamaki daskarewa nayi. Ko da yake in dai Rakiya da Maigogul ne sun fi nan. "Sosai kuwa duk abinda ka faɗi hakane Maigogul. Wannan daular dai ke kike ciki, jibi tuwo da kaza ga man shanu, jibi falonki da yaranki abun sha'awa duk wannan ni'imar kike so kisa ƙafa ki shure Sabuwa. Wai to in kin fito wa zai aureki shi Khalid ɗin kike som ki aura koko ƙaƙa kike son ayi Sabuwa?" Kaina yana ƙasa sama da ƙasa Allah bai bani ikon tankawa ba sai Uzairu zuchiyata da yace. "Rakiya nifa ina ganin a cikin zaman aure babu dole. Ku duba irin ciwon da Lolo tayi har mun cire rai da'ita duk ta dalilin aurenta kuma likitoci sun tabbatar mana da cewar wannan ciwon na damuwa ta daɗe a cikinshi, kuma har haukacewa ake yi. Duk da Babangida a yanzu nutsuwa da nadamar abubuwan daya dinga aikatawa a baya ya kamashi, duk da haka tunda tace ba zata zauna ba ku barta kawai. Ita kaɗai tasaan abinda ta fuskanta" Adama tace. "To Uzairu zuchiyata nima abinda na gani kenan a barta ta kashe auren kawai ta samu nutsuwa. " "Eh haka fa tunda kin kasa zaman aure kya hure mata kunne ta kaso nata aure tazo kuci gaba da zaman kanku mana " Cewar Maigogul da yake ta faɗa. Sallamar Babangida ce tasa ya sarara. Da fara,a ya karaso. "Rakiya ashe kune kuka zo? Ina wuninku " Ya faɗa da sabon ladabinshi na munafurci har yana zama, shi da ada sai dai su Rakiya su gaisheshi" Ai kuwa cikin rashin kamun kai suka shiga gaisheshi tare da tambayarshi kufan jikinshi, da nawa jikin" "Ah nawa da sauƙi sosai. Natanne dai sai a hankali dan kullum sai kuma rama take yi, jikin dai gashi nan." "Ta ɗaura ma kanta masifa ne kawai shi yasa abinda ma ya kawo mu kenan ka daɗa haƙuri da duk abinda take yi maka. Allah ba zai bata nasara ba, zata ci gaba da zama tare dakai" Babu kunya babu tsoron Allah Babangida yace da Maigogul. "In sha Allah na kuma gode sosai. A sake haƙuri da duk abubbuwan da suka faffaru a baya a yafi juna" Rakiya tayi dariya tace. "Babangida ai mu babu abinda zamu ce dakai sai dai muce Allah ya biya ka. Ka riƙe Sabuwa da kyau babu abinda ta rasa a wajenka, ko banza ka rufa mata asirinta damu baki ɗaya" Kallona Babangida yayi ina kallonshi ta gefen ido yana wani murmushi. Miƙewa yayi ya zaro dubu biyu ya miƙo ma Maigogul carab ya cabke kuɗin tare da hannun Babangida. Yaita zunduma mishi godiya. Sallama yayi musu ya fita Adama ta kira Mardiyya. "Maza ki ɗau tiran abincin Babanku ki bishi dashi." Mardiyya ta amsa da "Toh" Ta fita. Tunda Adama tazo Babangida ya samu gata duk ran girkina yana shigowa Adama ta zuba mishi abinci ya take cikinshi, kwananne dai ya haƙura tunda Adama tana nan. Taso ma ya dinga kwana ita ta kwana a falo, shine bai amince ba jira nayi inji yace to suga tsiya daga shi gar Adaman amman sai yace mata hakan bai dace ba ita dai ta kula dani kamar gaske. "To Rakiya tashi mu wuce. Lolo kamar yadda aka saba dai" Ya ƙarashe maganar yana dariya. Kayan abinci nasa Adama ta ɗiba musu na basu dubu biyar biyar Uzairu zuchiyata na bashi dubu biyu Adama da Mardiyya suka rakasu titi. Ni kuma ina yin sallar isha na haye gado sakamakon cikin magungunana akwai na bacci ko da yaushe a cikin bacci nake tunda dai aka sallamoni, in ba baccin nake yi ba ma bana jin daɗin komai"
Babangida:. Da sallama ya shiga ɗakin Ƴar Shuwa. Tana zaune tana waya da Mamanta jin sallamarshi ne yasa ta kashe wayar. "Sannu da zuwa" Ta tarbeshi harda fara'arta shi dai yasan ya fita da safe tana fishi da ƙorafi akan kuɗin ankon bikin ƙanwarta da yace har zuwa lokacin bai samu ba. Abun mamaki kuma ya dawo ya taddata cikin fara'a harda ɗaukar kwalliyar ƙananun kaya. "Yauwa sannu ya gidan?" Waje ya samu yaima kanshi masauki a ƙasan kafet dan ba ƙaramin gajiya yayi ba aikin koyarwa akwai wahala ( ina jinjina ga duk Malaman duniya maza da mata, malaman boko dana islamiyya) Zama tayi a gefenshi. "Ina yaran sunyi bacci ne?" Sai da ta kaɗa idanu kafin tace dashi. "A_a ɗazu mama tazo shine ta tafi da'ita" Take ya gintse murmushin da yake yi mata. "Amman sau nawa na faɗa miki ki dinga sanar dani in yarinyarnan zata je gidanku, koma ina zata je yana da kyau a nemi izinina matuƙar ina da mutunci da ƙima ko?" Kafin tace wani abun Mardiyya ta shigo da sallama riƙi_riƙi da tire ta dire a gaban Babanta. "Baba ga Abincinka" "To sannu ɗiyar kirki Allah yayi albarka" Da "Ameen" Ta amsa ta fita a tsanake. Binta yayi da idanu yana jinjina irin kamanninta dashi da irin nutsuwar da take dashi. Ikon Allah wai Sabuwa ce ta haifi yarinya kamila irin Mardiyya. "Ban gane ba, naga an biyoka da abinci sabida cin fuska" Ya jiyo muryar Ƴar Shuwa ta daki kunnenshi. Juyowa yayi ya ƙura mata idanu baice da'ita komai ba amman taga ɓacin rai sosai a tattare dashi. Tiren ya jawo ya zuba lafiyayyen tuwonnan da naman kaza cinya da ƙirji aka saka mishi. Nan ya hau zuba loma ya bar yar Shuwa da haɗiye yawu dan su yanzu da kifi suke girki nama ma sai jumma'a_jumma'a suke ganinshi kaza kuwa tunda rayuwa ta juya musu baya siya sai dai su ci a tukunyar maƙota. Sai da yaci ya ƙoshi ya sha kunun Aya kafin ya nufi masallaci a lokacin anata kiraye_kirayen Sallah. Har yaje ya dawo Tiran abincin yana wajen Ƴar Shuwa bata ɗauke ba tana dai zaune a wajen tana cin jalof na taliyar manja da bushasshen kifi tana korawa da ruwan randa. Shi kam banɗaki ya faɗa yana so ya ɗan watsa ruwa ko zai ɗanji ƙarfin jikinshi. Amman me? Ko da ya shiga banɗakin yana wanka zuchiyarshi cike da fargaban abinda kaje kazo, duk da lauyoyinshi suna ta tausarshi akan ya kwantar da hankalinshi komai zai daidaita, sannan Malama Babba ta basu kuɗi masu yawa kamar yadda ta alƙauranta musu. Ruwan zafin ya ɗebo a kofi ya zurara a kanshi idanunshi a lumshe fes yake ganin hoton Sabuwa a idan zuchiyarshi. Murmushi yayi kawai tare da saurin buɗe idanunshi yana mamakin yada yake jin da gaske yake fargabar rabuwa da Sabuwa ba wai dan auren Malama Babba kaɗai ba, shi kanshi ya fahimci yana buƙatar Sabuwa a rayuwarshi ashe? Duk da har zuwa wannan lokaci ya kasa yadda da zuchiyarshi gani yake yi sabida Malama Babba ne kawai ya sassauto daga ƙiyayyar da yake yima Sabuwan domin itace hanya mafi kusa wajen cimma buri. Ta wani ɓangare na zuchiyarshi kuma yana ƙaryata hakan sosai. Da daske yana mutuwar son Sabuwa ashe? Jin ƙaran wayarshi ne yasa ya buɗe idanunshi ya ƙarashe wankan tare da ɗauro alwala ya fito ɗaure da tawul a ƙugu. Ƴar Shuwa ya tarar a tsaye a bakin gado tana kallon wayar tashi. Sumy ce yauma ta kira, ta lura a kwanakinnan duk sanda girki ya zagayo kanta inta duba wayarshi zata ga Sumy ta kira, ko shi ya kirata banda ragowar tulin sunayen mata da suke kiran wayar tashi, duk da dai su missed call take gani, bata taɓa ganin ya ɗauki wayar ba, ko kuma ya kira daga baya ba. Bata ji shigowarshi ba ta ɗauki wayar don son jin muryar ita wannan Sumy da take kiran magidanci a irin wannan lokacin " "Hello barka da dare Hero da fatan kana lafiya?" Gyaran muryar da Babangida yayi daga bayan Ƴar Shuwa bai hanata fesar da abinda take son fesarwa ba. MRS Buhari ce Mu tara gobe IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA HUƊU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
"Ke wacce iriyar daƙiƙiya dabba jahilace da zaki dinga kiran mijin wata da daddare, har kina kiranshi Hero? Ohh kune irin matannan na layi masu tumɓele da bin mazajen mutane ko?" Ƙarasowa Babangida yayi ya fisge wayar a hannunta. "Sumy bani mintuna zan kiraki" Yana gama faɗar haka ya kashe wayar. "Menene dalilinki na ɗaga mun waya har kiyi zage_zage da macen da baki san ko ita wacece ba? Oh kina son ki nuna mata cewar ni ba tsayayye bane a gidana ba ko, ko so kike ki nuna mata cewar babu mace mai tarbiyya a gidana uhm?'" A fusace ta juyo jin furucinshi na ƙarshe. "Au naka irin borin kunyar kenan? Ai nasan ɗaya daga cikin karuwanka ne da kuka saba mu'amala tunda ma naji ta kiraka da Hero in ba tambaɗa kuka saba ba ai batun Hero bai taso ba" Maganar ta daki zuchiyarshi yaji zafi sosai. Amman sai yayi dariyar cusa haushi yace. "Eh kamar yadda kike a baya ko, in kin manta a hotel ɗin da muka soma haɗuwa ai sai in tuna miki, in kin manta abinda ya gudana da maganganun da duk kikayi ai sai a tunasar dake kisan cewar matan titin suna da yawa ba Sumy bace ita kaɗai ba. Ke naki ai yafi na kowa mijin Aminiyarki wacce duk duniya bata da kamarki dashi kike kwana a Hotel sai da kika bi dare aka auroki dole" Yana gama faɗin haka ya fice ya barta a mace a wajen da mamaki. Jakwab ta zauna a gadonta tana jiyo muryarshi yana magana da Sumy a waya, sai dai bata jin abinda yake cewa kwata_,kwaya kuma wayar bata daɗe ba taji shiru. Tana zaune tana jiran ya shigo ta tayar mishi da hankali, sai taji shiru yayi kwanciyarshi a falo har falon ta bishi ta ɗaga mishi hankali sune rikici har biyun dare, ta ko ji maganganu sosai ya zazzageta son ranshi a wannan daren taci kuka har saki saida ta nema "Sa'arki ɗaya na dena saki, amman da ke kanki ma ba zaki soma ba. Haka dai zamu ci gaba da zama da juna yau fari gobe tsumma sunnar rayuwar kenan" Da baƙin ciki Ƴar Shuwa ta kwana, Babangida kuma ya kwana da fargaba a haka dai garin Allah ya waye, aka shiga aikace_aikacen yau da kullum sassafe Babangida ya saka kai ya fice ko bi ta kan Ƴar Shuwa bai yi ba, dan fishi take yi sosai shi kuma bashi da lokacin magana da'ita dan ita ta jama kanta harya farfaɗa mata maganganun da yasan in tana da hankali dole ta zauna tayi juyayi a kansu.