Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 12
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 12: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 12. Da sallama Ƴar Shuwa ta shiga gidan Sa'a ta taddata a bakin pampo kan kujerar…
3,778 words
Da sallama Ƴar Shuwa ta shiga gidan Sa'a ta taddata a bakin pampo kan kujerar tsugunno ga wanki a gabanta cikin baƙin bawo. Amman a lokacin data shiga waya take yi sai salati take rabkawa. Jarka Ƴar Shuwa ta ja kiyy ta samu waje ta zauna kusa da Sa'a. "Kai amman Babangida kwai ɗan banza. Yanzu dan ALLAH in Baba Malam yaji wannan maganar me zamu ce mishi. Ace Babangida tunda dai ya soma girma yake jaye_jayen magana? Allah ya kyauta gobe dai zan shigo yau da wanki na tashi mun tara kayan wanki da yawa" Kashe wayar tayi tana tsaki. "Lafiya Yaya Sa'a ake aibata mana miji me kuma yayi?" Baki ta taɓe tare da cewa. "Hmm ke dai ki bari kawai Abokiyar zamanki Hamida Babangida fa ya saka wai jiya da daddare. Yanzu ya dace kenan abinda yayi fisabilillahi yana ganin anata tunanin yaya za'ayi da batun kotu da Sabuwa ta dokashi, ga batun karayar arzikinshi hakan duk bai isheshi ba. Yanzu nan da wasu watannin in dai Babangida ne sai dai kuji ana shigo da kayan Amarya, koma yayi a ɓoye kamar yadda ya auro waccan marar kunyar Amaryar taku." Shiru Ƴar Shuwa tayi tana tunanin dalilin da yasa Babangida ya kwana a ɗakinta jiya kenan alhalin ba kwananta bane. Wani farin ciki taji a zuchiyarta marar misaltuwa a zahiri kuma sai ta nuna ma Yaya Sa'a abun ya taɓa ta sosai. Amman ita bama Hamida bace a gabanta ba dan ta riga da tasan tafi karfinta. "Hmm ni dama Sabuwa ya saka daya fi ai. Kinsan Yaya Sa'a kamar Sabuwa ta asirce Abban Fatima kuwa? To kinga yama dawo yana mana rabon kwana da'ita matar da take bin maza kalan yaje ya kwaso cuta ya saka mana. Yanzu ma haka tare fa muka fito dashi muka sameta a hanya zata tafi yawon barbaɗanta data saba, shine ya tareta ta faɗa mai inda zata je taƙi fur a titi ta tafi ta barmu shine ya tari Acaɓa ya bita shi, ni kuma nayo nan. Ƙaddarace dai tasa kuka haɗa iri da su Sabuwa. Mahaifinta fa kullum zaki ganshi da mata, har cikin gidansu yake kawo ajjiyar karuwai duk wani iskancin duniya ya ƙare a gidansu Sabuwa, ai gara ya saketa ya huta da wannan tozarcin" Wawuyar ajjiyar zuchiya Sa'a ta sauke a duniya babu wacce ta tsana sama da Sabuwa. Kuma tana mai baƙin cikin tseratar mata da aurenta da Baba Malam yake son yayi. Da ba dan ya riga ya haɗe igiyar auren Sabuwa data Malama Babba ba ai da tuni wani zancan akeyi ba wannan ba. "Hmm ke dai ki bari. Ai kinsan Baba malam yace in ya saketa to tsinuwace zata bishi kinji dalilin da yasa Sabuwa ta samu waje ta miƙe take tatala rashin mutuncinta. Kuma ai kema kinsan in mijinku ya saketa a bakacin auren Malama babba ne kinsan komai ai. Babangida kuwa da kike ganin yana lallaɓata so yake ta janye ƙarar data shigar gudan kada tayi nasara tsinuwar Baba Malam ta bishi. Kinsan akan wannan maganar Malam Baba ya hana ma Babangida shiga cikin gida kwata_kwata? Ai Sabuwa sai dai muce Allah ya tsine mata albarka. In sha ALLAH sai ta wulaƙanya a gidan Babangida muguwa azzaluma" Ajjiyar zuchiya Ƴar Shuwa ta sauke a ranta take furta. "Kenan babu ta yadda Babangida zai saki Sabuwa kenan, tare zasu ƙare rayuwarsu? Ina wallahi ko tsirara zanyi yawo sai na karaɗe bokayen Dutse da kewayenta na farraƙa Babangida da Sabuwa, so nake yai mata korar kare. Dan nasan babu wanda zai aureta muddin ta bar gidan Babangida. Ga ƙannenta da yayunta nanma duk an sakosu suna gaban iyayensu" "Gaskiya in yana neman albarka bazai iya sakinta ba. To amman Yaya Sa'a in alƙali yasa dole ya saketa fa?" Ƴar Shuwa ta kafe ta da idanu. "Hakanma in sha ALLAH bazai faru ba. Kinsan Allah ai in tasan wata bata san wata ba. Wannan shari'ar data jajiɓo da bakinta zata janye in sha ALLAH. Bata isa taci nasara ba, ba wai dan muna sonta ba" Haka sukaita tattaunawa Ƴar Shuwa na taya Sa'a wanki har suka gama, suka kuma runtuma zuwa kitchen itace da girki. "Ni Banga Anty Nasiba ba yau tunda nazo. Nasan kuma ba mai zaman ɗaki bace" Baki Sa'a ta taɓe. "Tana asibiti mahaifinta ne babu lafiya shine take jinyarshi" Ƴar Shuwa tace. "Ah kice ke kaɗaice da gida kiyi yadda kike so. Kishiya ko masifa" Sa'a an sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi tace. "Ai kuwa ji nayi kamar kada ta dawo gidan. Ai da ƙyar fa ta yarda ta tafi jinyar. Kinsanta da maganar son turaka. Saida yatta tazo gidannan tayi mata tatas shine ta haɗa kayanta ta tafi. Kuma fa mai gidan kullum sai ya je asibitin ya kai musu garar arziki. Ai kishiya komai zaman lafiyan da kuke yi to ta ciki kawai na ciki. Kinga matarnan ba ƙaunata take yi ba. Kishi dai_kishi dai da taga sutura a jikina ko jikin yara ta soma zafin zuchiya kenan tai ta tuhumarshi shi kuma yana mata rantse_rantse namiji_namiji sai dai a barsu da halinsu kawai." Haka har suka gama girkinnan bakinsu bai huta ba sai aibata abokan zamansu gami da yi musu ƙage suke yi.
Babangida:. Ranshi a mufun haɗe ya shiga ya gurfana a ƙasa a gaban Malama Babba. Kawu Manga ya nemi waje a saman kujera . "Yaya kuma akayi Malama irin wannan kiran gaggawa ya sake yo wata tsiyar ko?" "Ina kwana Kawu?" Cewar Hamida wacce da ganinta taci kuka ta ƙoshi. "Lafiya lau ya kwanan yaran, da abokan zaman naki?" "Duk muna lafiya" "To madallah" Babangida ne ya gaishe da Malama Babba tace. "Ni ban kiraka dan ka gaisheni ba. Ai burinka bai wuce hawan jini ya kasheni ka huta ba. Yanzu ana cikin damuwowi kala_kala me yarinyarnan tayi maka daka saketa?" Kawu Manga ya shiga salati harda cire hularshi. "Saki kuma? Yaro sai kace mai aljanu. Shin Babangida lafiyarka ƙalau kuwa nace kana da hankali da zaka saki yarinyar mutane a irin wannan lokacin duk mutunci da karamcin iyayenta. Tukunna ma mai tayi maka da har ka saketa?" Shiru babu amsa yaƙi magana fur. Kawu Manga yace. "Ke hamida faɗa mana abinda ya jawo sakin. Sannan saki nawa yayi miki?" Nan ta labarta musu iyakar abinda tasan ya haɗasu. Kawu Manga yace. "Babangida ka mayar da'ita ɗakinta yanzu kaji na faɗa maka. Mu birne maganarnan tun kafin ta tsallake gidannan." Malama Babba tace. "Zancan banza zancan wofi kenan ma. Ai ya zame mishi dole ya maidata ɗakinta. Sabida kai saki baya baka wahala akan shinkafa saika saki mace" Dundu ta sakar mishi a gadon bayanshi na baƙin ciki. "Ashsha abi komai a hankali Malama duka da ɗaga murya ba naki bane. Ke ba ishasshiyar lafiya ba. Zai mayar da'ita ma kiyi haƙuri. Kai Babangida" Ya ambaci sunanshi, sai lokacin ya ɗago kanshi ya dubi kawu Manga. Kafin Kawu Manga yace wani abu wayarshi ta shiga ruri Mustapha ke kiranshi. "Zaka iya ɗaga wayar taka in tana da mahimmanci" "A_a Kawu Manga babu damuwa Mustapha ne, inna fita zan kirashi" "To to ai shikenan. Yarinyarnan kayi haƙuri ka dawo da'ita ɗakinta. Ka kuma ba mahaifiyarka haƙuri." Shiru ya kuma yi, ga Mustapha ya dameshi da kira sai saka wayar a silet yayi. Can dai yace. "Kuyi haƙuri bazan iya ci gaba da zaman aure da'ita bane, sabida wani dalilin da fasuwarshi dani daku bazai mana dadi ba. Malama Babba kiyi haƙuri ba ƙin bin umarninki nayi ba. Dole ce tasa nayi sakin akan dalili mai ƙarfi. Kuyi haƙuri bakin alƙalami ya riga da ya bushe" Ya ja baki yayi shiru. Malama Babba ma ta rasa abinda zata ce, domin bata taɓa tunanin zata bashi umarni ya ƙetare ba. Tasan yana bakin ƙokarinshi wajen bin umarninta. Abinka da Ɗa da uwa kuma ɗan dama yafi soyuwa a zuchiya fiye da sauran. A take Malama Babba taima ɗanta uzuri da wannan kalmar ta malam bahaushe da yake cewa mai ɗaki shi yasan inda yake yi mishi yoyyo. "To shikenan Babangida dani da gyatunarka ba zamu matsa maka ba akan dole sai ka dawo sa matarka ba. Domin babu dole a cikin aure. Ke hamida sai ki daure ki koma ɗakinki ki yi idda in iddarki ta cika Allah bashi saiki tafi in rakaki har garinku" Hamida da jin haka ta miƙe rai a ɓace diyar ta miƙar tsaye ta ɗaura akan cinyar Malama Babba ta suri akwatinta. "Ga yaranku nan ni dakai har abada. Kuma ka sani zakuntata da kayi in sha ALLAH sai surukanka kaima sun ɗanɗana maka baƙin cikin da kake ɗanɗanama naka surukan. Ke kuma kici gaba da biye mishi in sha ALLAH sai yayi ajalinki" A zafafe Babangida ya miƙe zaiyi kan Hamida Malama Babba da Kawu Manga suka dakatar dashi. "Ɗan kuka mai zama uwarshi jifa. Babangida kabi duniya a sannu. Kai kaji kalaman da yarinyarnan ta faɗa ko? Kayi ƙoƙari ka gyara ɗabi'unka ina ji maka tsoron ka samu yaro irinka, wallahi duniya ba zatai ma daɗin zama ba.Jibi a sanadinka kasa na bawo gidam aurena na dawo hannun Ɗana Malam da ranshi da lafiyarshi ya koreni a gidanshi, inta kama ma rabuwa dani zaiyi kuma duk sanadin jaye_jayen maganarka. Bazan maka baki ba abun sai yayi maka yawa. Allah ya sani ina sonka Babangida shi yasa kake wahalar dani. Jibi yarinya ƙarama da matarka ta dire mun a cinyata. Ga Hauwa tsohuwar matarka yau ɗinnan ta kawo ɗanka ta danƙama Malam. Shi kuma malam ya kira kudidi ya bata, ga Mufida Hamida ta dure mun ga Usama. Kukane yaci ƙarfinta Kawu Manga yace. "A dai taru ayi haƙuri dai. Yara kuma shi Usama ya tafi dashi ya ba matanshi. Ita kuma wannan zan ba mata a cikin gida suci gaba da riƙonta, ga Mariya na da ɗiya sa'arta kinga ta samu ƙawa. Kai Babangida kama hannun yaronnan kuje, mutumin kawai." Babu shiri ya fice yana sharce zufar data tsattsafo a saman goshinshi. Sumy ta gama dashi ta dalilinta yau yana ji yana ganin Malama Babba na zubar da hawaye amman bashi da hannun share mata. Duk da wannan kukan daɗine akan fasuwar ƙwan da yake son yaga ya rayu ba tare da fashewa ba. Abinda Babangida ya mance shine shin za'a dauwama ana ɓoye ma Amir asalinshi ne, ko za'a dauwama ana tafiya a mazaunin Amir agolane da Sumy ta tawo dashi gidan aurenta? Yana fita ya zaro wayarshi Mustapha ne dai yaketa kira. Tabbas yasan da matsala banza bata kai zomo kasuwa wannan kira babu ƙaƙƙautawa. "Mustapha wannan kira haka. Allah yasa muji alkhairi?" Mustapha daga wayar yace. "Babu wani Alkhairi kai da nake ta kiranka tun abun na faruwa. Sabuwa ce wannan matsiyacin yazo ya ɗauketa a bakin makarantar yara a mota. Shine naita kiranka baka ɗaga ba." Wani irin hajijiyace ta kusan buga Babangida da ƙasa babu shiri ya jingina da bango numfashinshi yana fita da sauri_sauri. A take kamanninshi suka sauya, idanunshi da jijiyoyin kanshi duk suka fito. Runtse idanunshi yayi yana sauraren zuchiyarshi. Wani irin mugun tsananin kishin Sabuwa ke dafa zuchiyarshi da gangar jikinshi harma yake iya jin zai iya kashe Khalid ya kashe Sabuwa kowa ya huta." "Babangida kana jina kuwa. Inata magana naji shiru?". "Ina jinka. Ya kaimun ita Hotel ko, ya danne mun ita ko Mustapha?" Cikin wata iriyar muryar da baisan yana da'ita ba yayi maganar. Shi kanshi Mustapha yayi mamakin jin muryar abokin nashi da irin furucinshi. Ya dai san baya son Sabuwa a rayuwarshi, amman yasan Babangida na da wani irin kazamin kishi. "A_a basu je Hotel ba. Sun shiga store yayi mata siyayya, sai a bakin titi daya parking motar sun daɗe suna ciki bana iya ganin me suke yi. Sai ya sauketa a gida. Lokacin da nake ta kiranka sun shiga store siyayyane naso kazo ka same shi mu ƙaddamar mishi sai baka ɗaga wayar ba" Idanu Babangida ya lumshe yana ji tamkar zuchiyarshi zata jijjige ta faɗo. Yayi magana ya kasa haɗa kalmar da za'a fahimta sai in'ina kawai. Wayar ya kashe kawai ya figi hannun Usama suka bar wajen. Wani irin zafi da raɗadi yake ji. Allah Allah yake ya isa gida ya ajjiye Usama yabi Sabuwa har gidansu ayi duk wacce za'ayi in ba dukan mutuwa yayi mata ba, ƙila ajalinshi ta shirya yi da baƙin ciki." Banko ƙofar gidan yayi babu kowa a tsakar gidan, yana kallon ƙofar ɗakin Sabuwa ya ganta a buɗe. "Usama jeka ɗakinsu Khalifa ina zuwa yanzu kaji?" "To Baba" Cewar Usama. Kama hanya yayi turyan_,turyam zuwa ɗakin su Khalifa har saida yaga shigarshi kana ya nufi lungunsu Sabuwa."
Sabuwa:. Ina kwance ina karanta wasiƙar jaki na ji an banko ƙofa an shigo. Kafin in yi wani yinƙuri Babangida ya cabke wuyana gam ya shaƙeni. Idanunshi duk sun fiffito tamkar shi aka shaƙe bashi ya shaƙe ba, har wani tararren hawaye nake hangowa a guraben idanunshi. "Wato ke Sabuwa har yanzu baki haƙura da wannan la'ananne. Khalid ɗin ba ko? Sabida kinga ina raga miki ne yasa kike wasu abun. Ƴar iska wacce sukai gadon iskanci. Mace da aurenta harda budurwar Ƴa amman tana raba jikinta ga ɗan balaja'u. Yau kasheki zanyi in kashe shi dan ubanku nima a kasheni duk mu huta" Da wani irin ƙarfin murya mai salon dashewa yake magana irinta basawan india sak kun tuna maganbo na shirin ɗin kwaila? To sak muryar da yayi kenan. Idanuna sai fitowa suke yi dan Babangida ba imanine dashi ba sai sake makuremun wuyana yake yi. Ni kuma sai kiciniyar ƙwacewa nake yi amman yaƙi sake ni. Hannu nasa na biji ƙasanshi da dukkanmin ƙarfina. Ihu yayi ya sakeni tare da riƙe ƙasanshi da hannunshi mai lafiya. Miƙewa nayi na diro daga gadon da gudu ina haki. Wallahi Babangida kayi kaɗan ka rabani da Khalid ni dashi sai mun yi aure mun haifi yar.." Kafin in karashe Babangida yayi wani kukan kura ya buge bakina da iyakar ƙarfinshi. Take naji bakin kamar ba nawa ba. Rungumarshi nayi ina shirin yin faɗa dashi. Ayau dai na kasa dan ran maza ya ɓaci fyaɗani yayi a gado yana nuna ni da yatsa. "Sai dai a mafarki wallahi Sabuwa bazan taɓa rabuwa dake ba .Kuma ko dan sabida Khalid kina cikin gidannan babu inda zaki je wallahi kinji na rantse. So kike ki kasheni da baƙin ciki ne Sabuwa kome kike so. Shin Khalid ɗin fina yayi iya tarairaya, ko ƙarfin mazantaka zai nuna mun ki faɗa mun nace" Ya ƙarashe maganar da tsawa tare da runtse idanunshi har saida hawaye ya surnano a idanunshi guda ɗaya. Zama yayi jikinshi a mace a bakin gadon, nima ina zaune a gadon ina maida numfashi ga jini sai zuba yake yi a bakina, bakina ya aune yayi suntum. Ya daɗe yana kallon waje ɗaya kome yake kallo oho. Ni kuma sai lumfashi nake yi gami da haɗiye kukan dake tunkudo kanshi da kanshi dan ko kasheni Babangida zai yi na dena kuka a gabanshi kuma bazan ƙara ba. "Sabuwa daga yau sai yau in kika sake fita wallahi Allah ɗaya kenan komai zai iya faruwa. Haba sabuwa ya kamata ki kare mana mutuncin Ƴaƴanmu, ko baki kame kanki dan aurena dake kanki ba, ai kya kame kanki dan darajar Ƴaƴanmu. Idan kika sake haɗuwa da Khalid ko na kamaki kina waya dashi Sabuwa zan kasheshi Allah. Dama tunda kika shigo rayuwata nake gamuwa da bala',i." Nima shigowa rayuwata da kayi bala'i da masifa ne. Haɗuwa da Khalid kuma yanzu na soma Babangida. Kai ka kame kanka daga matan banza ne. A kunnena nake jiyo nishinka kana mu'amala da karuwarka. Kaine wannan zangon baƙin kaine wancan zangon baƙin. Suma duk matan da kake mu'amala dasu iyayen wasu ne, ƴaƴan wasu ne, ƙannen wasu ne. Narantse da Allah ko da tsiya ko da arziki sai ka sake ni. Kuma ko dan baƙin ciki ya kasheka ni sabuwa saina Auri Khalid. "SABUWAAAA" Ya faɗa a zafafe tare da ɗaga hannunshi yana so zai dokeni, jikinshi har rawa yake yi. Hannun ciwonshi na doke cike da mugunta. Dan wallahi na shirye in baiyi wasa ba saina sauke hannun duka. Ina gudun kada a ƙara mana tsayin shari'a ne kawai. Lumshe idanunshi yayi hawaye masu yawa suka zubo a guraben idanunshi. Wallahi yafi minti goma a tsaye tamkar mutum mutumi daga bisani ya buɗe idanunshi ya sauke a kaina. Idanunshi sun zama tamkar garwashin wuta. "Ki kasheni in rataya a wuyanki kinga wuta zaki shiga kai tsaye. Ni da kike kallona a matsayin Ra'asujjarima sai in shiga aljanna kina kallo" Yana kaiwa nan ya fice da wani irin mugun sauri. Sakata na saka ma ƙofata na jingina a jikin ƙofar ina sulalowa ƙasa a hankali ina kuka mai gunji. Nafi awa ɗaya ina kuka wallahi har saida na soma ganin duhu_duhu kana na yi shiru inata faman sauke ajjiyar zuchiya kuma"
Babangida:. Yana zaune a falon Sabuwa idanunshi a rufe shi ba kuka yake yi ba amman zuchiyarshi kuka take yi sosai. Zafin zuchiya, zafin maganganun Sabuwa,yasa ko zafin ciwon da Sabuwa ta jangwale mishi baya ji. "Ko da tsiya ko da arziki saika sake ni. Kuma ko dan baƙin ciki ya kasheka saina Auri Khalid. Wannan furucin na Sabuwa yafi komai dagula Babangida sosai. Maganar sai kaɗa mishi ƙararrawa take yi a zuchiyarshi. Idanunshi ya buɗe ya ƙurama hoton Sabuwa dake gefen TV a ajjiye kallo. Wani abu yake ji game da'ita wanda bai taɓa jin irinshi ba tun farkon yin tozali da'ita a bariki har kawo yanzu in banda yau da yaji abun. Murmushi yaima hoton kamar zararre ya soma magana da hoto. "A gidana zaki dauwama babu wani namijin da zai sake mallakarki indai ni Babangida ina taka doron ƙasa. Shi kuma Khalid zan nemo inda yake zanje in ja mishi kunne na ƙarshe akan ki, in bai ji ba Sabuwa komai na iya faruwa dama kece Ƙaddarata a rayuwa." Fasa kuka da Sabuwa tayi ne yasa yayi shiru yana sauraren amon kukan da take yi mai gunji. Kanshi ne yaci gaba da sarawa tsabaragen kishin dake bijiro mishi idanunshi har ƙanƙancewa suke yi suna lumshe kansu. Miƙewa yayi da sauri zai fita. Wata zuchiyar tace dashi. "In hawan jininta ya tashi kuma tana kulle wani abun ya sameta sanadinka fa?" Cak ya tsaya babu shiri ya tatttaka har ƙofar ɗakin yayi shiru yana jin yadda take shekkeƙa har yaji ta sassauta."
SABUWA:. Da rarrafe na rarrafa na haye gado na lulluɓa da bargo. Hawana gadon ke da wuya na jiyo bugun ƙofar Babangida tare da amon muryarshi. "Sabuwa ki buɗe ƙofar nan nace miki" Idanuna na lumshe ko muryar Babangida bana fatan kunnena ya saurara balle kuma in ganshi. "Sabuwa ki buɗe kiyi haƙuri da dukan da nayi miki" A karon farko dana ji kalmar haƙuri ta fito daga Babangida zuwa gareni kenan. Amman shi mayaudari yakan yi komai damin ya samu abunda yake so. Dama Babangida gwanine wajen iya tsari ai. Ya daɗe yana magiya da rarrashi, amman ko tari naƙi yi dan kada ma yaji daɗi. Asalima rarrafowa nayi na watsa magunguna a baki na kora da 5 alive ɗin dake cikin kwali a ajjiye a gefen durowar gado a ƙasa nayi kwanciyata har bacci ya soma fisgata ina jiyo bugun ƙofar Babangida har bacci yai nasarar surata na dena jin motsin duniya baki ɗaya."
Babangida. Bugun duniya Sabuwa ta buɗe ƙofa taƙi buɗewa tayi magana taƙi yi' motsinta ma baya ji shab, sai tsoro ya kamashi jikinshi dai babu laka ya fice daga ɗakin Sabuwan zuwa ɗakin Ramatu. Tana zaune a falo tana cin dafaffiyar masara. Yaran kuma sai wasan su suke Khalifs sai tsokanar Usama yake yi. Kallo ɗaya Ramatu tayi mishi taga damuwa mai tsanani akan fuskarshi. "Usama kama hannun ƙaninka ku je tsakar gida kuyi wasanku ko?" "To Mama. Khalifa kazo muje" Ya ja hannunshi suka fita suna dariya kuruci dangin hauka. Nutsuwarta ta tattara waje ɗaya ta ba Babangida. "Lafiya na ganka a cikin irin wannan yanayin da ban taɓa ganinka a ciki ba?" Idanu ya buɗe yace. "Zazzabi ke damuna. Kuma naje na samu Malama Babba can na tadda Hamida kinsan mun rabu to abun dai babu daɗi" Baki ta taɓe tace. "Ƙararka ta kai wajen Malama Babban kenan, amman meya haɗaku?" Wani kallo yayi mata tasan in bashi yaso ayi hirar abu ba ba'ayi balle abinda ya shafi saki da baya tattaunawa da ko wacce mace. "Zan shiga ciki in ɗan kwanta dan ALLAH kar ki shigo kaɗaici kawai nake buƙata. Ga Usama nan ki haɗa da Khalifa ki riƙe" "Me kace ɗan kishiya wai in riƙe kake nufi?" Ta ƙarashe Maganar tana dariyar rainin hankali. Bai kulata ba, dan a yadda yake ji in kulata zaiyi ƙila itama korata gidansu zaiyi sai dai kash ya kulle ƙofar saki ya gama saki har abada. Hakanne yasa yayi shigewarshi ciki ya haura kan gado duk ƙasa, zanin gadon kuwa duk datti. Tsaki ya sake yana tuno lokacin da take amarya irin yadda taƙe cabtace jikinta da muhallinta. Amman fa banda yanzu tundai daga cikin Khalifa ƙazantarta ta bayyana haƙuri kawai yake yi. A haka ya kwanta a gadon yana kallon sama Tunanuka da dama yake yi tun daga farkon rayuwarshi izuwa yanzu. Zuchiyarshi sai hasko mishi kusakuran daya tabka a rayuwarshi take yi. Barinma ɓangaren neman matan banza wanda sanadin abokai yayi zurfi a ciki, shine harda ajjiye mace a matsayin dadiro gashi a yau yana ji yana gani zai aureta ba dan yana jin ko ɗigon sonta ba, sai dan kawai rufin asirin kanshi, da shi Amir da aka sameshi bata hanyar data dace ba. Nadama Babangida yayi ta tafi cikin tirela. Tunano adadin littattafan addini daya haddace a wannan kan nashi ya shiga yi, da yadda ya san Qur'ani ya rubuta da hannunshi, yake iya tafisirin ayoyinshi, da irin Yadda yake koyar da magidanta, matan aure, dama ƴan matan. Akwai sanda wani matashi ya tambaye shi aibun zina da inda Allah maɗaukakin sarki yayi bayaninta a littafi mai tsarki. Amsar daya bashi ya tuna da irin yadda ya kwashe mintuna talatin cur yana lissafo musu illolin da zina ke haifarwa a hakanma bai gama ƙirga musu illolinta ba sabida ƙarancin lokaci. "Allah na tuba Allah ka yafe mun. Allah kai kace kana son bayinka masu tuba. Allah na tuba bazan sake aikata zina da dukkan wani babban laifi ba. Allah ka soni ka amshi tuba na. Allah kasa kada wani ƙato ya sake take mutuncin aurena Ya Allah ka tsaremun Sabuwa ta ya Allah. Ka shirya mun ita kamar yadda na shiryu nima Mrs Bukhari Danƙari
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA SHA UKU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
INA MIƘA SAƘON GAISUWA A GAREKU MASOYA WANNAN LABARIN.
Ramatu:.