Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 11

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 11: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 11. Yana fitowa Ɗan Acaɓa ya soma bambamin faɗa akan sai an ƙara mishi kuɗi shi…

3,761 words

Yana fitowa Ɗan Acaɓa ya soma bambamin faɗa akan sai an ƙara mishi kuɗi shi wallahi shi tallahi bazai yarda ba. "Zan ƙara maka ko nawa kake so muje ka kaini kotun cikin gari" Ya faɗa cikin wata nutsuwar da shi kanshi baisan yana da'ita ba. Yana zaune a Acaɓa amman tunaninshi yana wajen Sabuwa da kayan dake ledar hannunshi. "Khalid Allah dai ya tsine maka albarka. Dake kai tantirin ɗan iskane hankalinka kwance kake mu'amala da matar wani, harda kawo mata tsarabar kayan karuwai. To mijinta ka siyo ma ta saka mishi, ko ko A_a ka siyo ne dan a saka maka ka kalla kaji daɗi?" Duk wannan maganganun a cikin zuchiyarshi yake yinshi. Kanshi ne ya sara mishi take wani jiri da zazzaɓi ya sakko mishi. Babu shiri ya soma ambaton Allah Amman zuchiyarshi sam taƙi nutsuwa, in bansa tunzurashi da zuchiyarshi take yi bata komai. Har hango sabuwa yake yi a ɗakin hotel a gaban Khalid da wannan rigar baccin a jikinta. "Malam anya kuwa kana da hankali ka duba nafi minti uku ina cewa mun iso amman babu um babu um_um." Sai lokacin Babangida ya fahimci dashi fa ake Magana, ɗago kan da yayi yaga lauyanshi da Kawu Manga a gaban Acaɓar. "Ashsha Babangida jikin naka ne ya kuma tashi ne, da ganin yanayinka kana cikin matsanancin ciwo." "Kawu mai girma ma kuwa. Ku taya ni da adda'a kawai ita nafi buƙata ba lallai bane in warke daga cutar da zuchiyata da tunanina suka kamu dashi ba" "Kuɗina dubu biyu waye wai zai bani ne?" Cewar Ɗan Acaɓa da aka ƙureshi har zuwa bango. Dubu biyu Kawu Manga ya ciro aka sallami mai acaɓa ya wuce su kuma suka rankaya izuwa Chamba. A ciki ya tadda Alhaji Abubakar Baban bola tare da lauyanshi da ɗanshi, sai alƙali dake kujerarshi a zaune. Bayan sun samu waje sun zauna alƙali yace. "Babangida inaso inji daga bakinka shin da gaske kamfanin da kake riƙe dashi babu ko sisin kwabonka a ciki, naka juya kuɗinne da yarjejeniyar raba riba?" "Hakane mai shari'a babu jayayya ga duk abinda Alhaji Abubakar Baban bola ya faɗa. Nayi mishi laifi ina neman afuwa a sassauta mun" Anan dai aka ƙarƙare magana da kissafe_lissafe a taƙaice da nera million goma kacal Babangida ya tsira shima a hakan ba ƙaramin adalci akayi mishi ba. Shari'ar dake a chamba ce kuma akwai sanayya sannan Babu jayayya ko musu a take aka gama komai Babangida ya sanya hannu shi da lauyanshi, haka ma Alhaji Abubakar Baban bola ya sanya hannunshi shi da ɗanshi da lauyanshi. Batun bama Babangida million goma kuma yace a i mishi alfarma zuwa wani lokacin zai bayar da haka aka rufe case ɗin kwata_kwata. Suna fitowa sai ga kiran malama Babba ya shigo wayar Kawu Manga. Ɗagawarshi ke da wuya Malama Babba tace in suna tare da Babangida su tawo su sameta a gidan Wawo yanzunnan. "To shikenan gamu nan. Amman lafiya naji muryarki haka a firgice?" Malama Babba tace. "Babangida hankalinshi bazai taɓa kwanciya ba har sai yaga baƙin cikinshi yayi ajalina tukunna. Wallahi da zan iya haƙura dashi kamar yadda Malam yayi dana huta" Kawu Manga ya girgiza kai. Babangida Kuma ya sauke kanshi ƙasa dan shi baisan kuma me ya kuma aikatawa ba. "To ko Sumy ta kai Amir gidane danta fallasa asirina? A_a ai duk sharaɗin data bani ban tsallake ko ɗaya ba bafa ita bace" "Babangida muje gyatumarka na son ganinka yanzu. Barrister mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi " Hannu Babangida yaba Barrister sukai musabaha kafin yabi Kawu Manga da wani irin sanyin jiki. Yana bayan bespa Kawu Manga na tukasu tunaninshi kacokan yana wajen Sabuwa da tsarabar da take hannunshi har suka iso ƙofar gidan Wawo bai daina tunani ba. "Sai ka shige mu je ai ko, sai wani sanyin jiki kake yi kamar gaske a haka kamar ba kaiba in ka kuntuka wata tsiyar sai mutum ga riƙe bakinshi mutumin banza." Har suka shiga Kawu Manga faɗa yake yi. Matan Wawo suna tsakar gida suna aikace_aikacen mata na yau da kullum su Kawu Manga suka shigo. Nan suka shiga rige_rigen gaishe da Kawu, yara da basa makaranta suka iso wajen Babansu a guje suka rirriƙe mishi kafa Murmushi Babangida ya dinga yi musu yana shafa musu kansu. Da ƙyar iyayensu suka rabasu dashi, saida ya bada ɗari biyu kuɗin biskit, ya gaishe da matan yayan nashi kana ya shiga. Da idanu yu suka bishi suna mamakin irin halayenshi a ido gashi dai mutum har mutum mai zubin kamala, hankali da tunani. Da sallama suka shiga part ɗin da Malama Babba take ciki, ga wata yarinya tana shanya a igiyar dake ɗan tsakar gidan da halama mai aiki ce Wawo ya ɗakko. Suna saka kai Babangida yayi tozali da Hamida da Ƴaƴanta suna zaune dirshan a gaban Malama Babba "

SABUWA:.

Bus ɗinmu ta sauke mu a daidai bakin makarantar, haka nabi ayarin dalibai muka shiga cikin makarantar. Mardiyya kaini ofishin shugaban makaranta" Mardiyya ta shige gaba ina biye da'ita har ofishin. Na shiga na tarar da wata uwa itama ta kawo ƙorafi akan ɗalibai sun saka yaronta gaba da duka da tsangwama suna neman su burkita mishi tunaninshi. "To Malama kiyi haƙuri sha'anin ɗalibai sai adda'a. Amman zamu sake saka idanu sosai akan shi Jamilun da mu'amalarshi da yara ƴan uwanshi. Uhm kije gida kawai" Miƙewa tayi tare da cewa. "Shikenan Malam nagode ina fatan ganin sauyi mu wuni lafiya." Ta fita a hankali. Shugaban makaranta ya kalleni yace. "Hajiya barka da zuwa menene ƙorafinki, koko kin kawo yaro zai shiga makaranta ne?" Yayi maganar da fara'a. A_a ni mahaifiyar Aɗɗa'u ce nazo ne naji ba'asin dukanshi da akayi irin wannan dukan sai kace ba uwa bace ta haifeshi ba" Take ya gintse fuska, nima na ɗaure fuskata tamau. "Uhm naga halama. Uhm Hajiya an kuwa baki labarin sata yayi aka dakeshi kuwa, sannan kuna da masaniyar sace_sacen da wannan yaron yake yi a wannan makarantar kuwa? In ba dan darajar kakansu ba ai da tuni mun koreshi dan gudun kada ya ɓata ma yaran mutane tarbiyyarsu ta hanyar koyar dasu sata" Yawu na haɗiye muryata a kausashe, a dakushe a lokaci guda. Malam dan yayi sata sai ai mishi irin dukan da akai mishi aka farfasa mishi jiki? Shin a matsayinka na uba kuma babban malami kai kana ganin irin wannan dukan hanyace ta horar da yaro ko hanyace ta sake fanɗarar dashi. Ko tunaninka satarshi mu iyayenshi mu muka koyar dashi, ko kuwa mu muka ɗaurashi bisa gwadaben satar? Ka sani babu wata uwa da zata so ɗanta ya kasance bana gari ba. A mafiya yawan lokuta duka ba mafita bane musamman ga yara ire_iren Aɗɗa'u jawosu a jiki suka fi so da kuma nuna musu hanyar gaskiya tunda har gobe Aɗɗa'u yaro ne ƙarami kuma ina fatan Allah kar yasa ya girma da wannan halin. Kuma ku sani kuma da naku Ƴaƴan suke a kimtse wallahi Allah ba dabararku bace." Ina dasa aya na miƙe tare da zuge jakata na zaro nera dubu ɗaya na ajjiye akan teburinshi. Ga kuɗin da akace ya sata a mayar ma da yaron sannan a bashi haƙuri. Kai kuma kune malamai ya dace ku taya mu tarbiyyar yarannan domin daku suka fi rayuwa a rana awa nawa mu iyayensu muke samu tare dasu, rabi da kwatan lokutansu naku ne. Ayi haƙuri kada a sake mishi duka irin wannan duk yadda zai lalace haƙiƙa inason kayana." Juyawa nayi na nufi ƙofa har na kusan ficewa naji shugaban makaranta yace. "Hajiya!" Juyiwa nayi na kalleshi. Jikinshi yayi laushi sosai, ni kuma zuchiyata tafasa kawai take yi. "Haƙiƙa na ɗauki babban darasi a maganganunki na hikima. Na yaba da salon isar da saƙonki cikin ruwan sanyi kika dafa ni da ruwan jikina. In sha ALLAH daga yau babu wani malami da zai sake dukan Aɗɗa'u kan yayi sata. Koma me ya aikata zamu kira lambarki ko ta mahaifinshi dake jikin form mu sanar muku inma na zuwa ne sai ku zo. Baya ga wannan halin na Aɗɗa'u yaron bashi da matsalar komai. Gashi da ƙwaƙwalwa, gashi da hazaƙa, kuma yarone mai tausayi, bugu da ƙari yana da son ƴan uwanshi. Hajiya ai mana afuwa wallahi mun dakeshi ne ba dan mugunta ba, sai don gyaran tarbiyyar shi. Amman zuwanku yasa na fahimci ta inda mu kanmu muke da kuskure kuma zamu gyara" Idanuna na lumshe kawai na gyaɗa kaina tare da cewa. Allah ya bamu ikon gyarawa. Nayi maganarne haɗe da sauke ajjiyar zuchiya irin na wanda ya samu sassauci a zuchiya. Ban bi takan yaran ba na fice a makaranta. Ina tsallake ina jiran abun hawa sai naga mota ta tsaya a gabana. Gilashin motar aka zuge Khalid ne a cikin motar yana saye da fararen suit yayi kyau sosai. Ƙuri yayi mun da idanuwanshi, nima shi nake kallo ina jin wani abu a raina game dashi. "Shiga mota in kai ki duk inda zaki je Sabuwa." Da ka yi tafiyarka Khalid nagode sosai." Murmushi yayi ya fito daga cikin motar ya iso gabana yana murmushi. "Ai ban isa na barki anan wajen ba. Wai kinsan irin neman dana dinga miki ban sameki ba kuwa? Wallahi da kinsan irin halin dana shiga ta dalilin son sanin halin da kike ciki tun bayan rabuwarmu da kin tausaya mun. Ki daure muje in kai kii" Jakata ya karɓa ya buɗe mun gaban mota na shiga, ya zagaya da hanzari ya shiga mazauninshi. Idanuna a lumshe sanyin Ac na ratsani naji Khalid yace. "Ga sigari ki sha ki rage nauyin zuchiya da ganin yanayinki kina cikin damuwar da tafi damuwar da kike cikinta a baya kafin in dawo cikin rayuwarki." Sigarin na karɓa na soma zuƙa cikin salon ƙwarewa shi kuma ya ja mota ya seta ta a titi. "Ina zaki je dama?" Gidanmu zanje can zaka kaini" Kai ya gyaɗa yayi mun murmushi tare da cewa. Menene abinda ya faru bayan rabuwarmu a wannan lokacin? Naso inji daga gareki nabi duk wata hanya amman ban sameki ba, wayarki bata shiga naje har layinku aka ce mun kun tashi dole haka na haƙura. Kuma inata tunanin zaki neme ni ki sanar dani azzalumin mijinki ya sake ki nanma naji shiru" Idanuna na lumshe, saida na zubar da hayaƙin dana zuƙa tas kafin na bashi labarin abinda ya faru." Labarin duk abinda ya faru na bashi tare da ɗaurawa da cewar. Yanzu jira muke yi zaman kotu na biyu ya zagayo mu sake komawa kafinnan hannun nashi ya warke kamar yadda nauyan nashi ya bukata." Murmushi Khalid yayi tare da sakin ɗan wani ihu da yasani sakin baki da mamaki ina kallonshi. Lafiya kake ihu?" "Wannan labarin naki ai dole in yi ihu burina kice ya kusan cika na mallakarki halak malak ba tare da shamakin komai ba? Lallai zan saka himma a kan ginin da nake yi da na saka wasa amman yanzu dole in saka himma dan gidana da nake ciki bazai isheku ba." Murmushi kawai nayi na girgiza kai tare da cije leɓena kawai. Akalar motar ya sauya zuwa wani titi daban. Ina kuma zamu je, nifa ban shirya aikata komai ba asalima bazan sake aikata komai ba ko dan mutuncin yarana" Kallona yayi da kyau ya nemi gefen hanya ya tsaya. "Sabuwa wallahi sosai nake sonki ina mai tabbatar miki duk duniya babu Wanda zai soki rabin son da Khalid yake yi miki. Kada kiyi tunanin ko ina mu'amala da matan banza har yanzu kiji tsoro ko shakkar aurena. Ko ɗaya a halin yanzu bana mu'amala da ko wacce mace face ke, ke kuma kinfi kowa sanin rabin rayuwata ce ke, kada kiyi tunanin sabida jikinki nake sonki. Da gasken gaske sonki nake yi sosai." Numfasawa yayi tare da riƙo hannayena biyu yana murzawa a hankali ni dai sama da kasa Allah bai bani ikon cewa dashi komai ba. "Sabuwa nayi miki alƙawarin zan baki farin ciki a aurenmu irin farin cikin da tuni kika yanke ƙauna da samun shi. KHALID ne kaɗai yasan mutuncinki." Ɗagowa nayi na dubeshi haƙiƙa ga dai soyayya ƙarara nakan iya karantata daga ƙwayar idanun Khalid a zahirin gaskiya zuchiyata ko kusa taƙi gasgata Khalid da maganganunshi. Taya zai ga darajata bayan ni dashi muke ƙetare katangar Babangida. In mu kai Aure bazai taɓa samun nutsuwa da yarda dani ba wannan kam ya shuɗe har gaba da abada in dai a wajen Khalid ne. Jibi irin zargi da ukubar da nake sha da Babangida yanzu haka akan zargi. Ina kuma ga na auri Khalid kai ina da sakel. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da cewa. Allah yasa mu dace kai dai ka taya ni da adda'a bari dai auren nawa ya ƙare tukunna. Amman inaso mu nesanta da juna sosai ni nayi maka alƙawarin da zaran aurena ya mutu Khalid zan nemoka da kaina" Na faɗa tare da sauke kaina ƙasa. Acan ƙasan zuchiyata ina son Khalid so mai tsanani fa ina dannewane domin aure da kuma darajar Ƴaƴana. "Kina nufin ba zaki sanar dani inda kike ba, kuma ba zaki bani number wayarki ba ko me kike nufi. Sabuwa anya ba yaudarata kike son yi ba kuwa?" Babu yaudara kasanni farin sani Khalid ni kaifi ɗaya ce. Da kaina zan nemo ka, ina son samun nutsuwar da zata bani damar mallakar kaina domin in samu ƙarfin kashe wutar dake gabanane, mutuwar auren yafi komai wuya ka fahimceni dan ALLAH " Hannuna ya saka tare da jingina bayanshi a kujerar da yake zaune ya lumshe idanunshi. Gilashin motar na sauke na yar da sigarin dake hannuna na rufe gilashin, kafin na ba Khalid dukkan nutsuwata Haƙuri na share fin minti biyar ina bashi kafin ya buɗe idanunshi da sukai ja ya zuba mun su. "Naji kuma na amince, ki riƙe amanar zuchiyar da ta daɗe da yin sabo da riƙonki. Ki bani account number ki lokaci zuwa lokaci zan dinga tura miki kuɗin da zaki dinga buƙatunki." Dole na bashi account number na sannan ya harba motar zuwa titi, katafaren shagon siyayya ya shiga dani ya sai mun kayan maƙulashe kafin ya sauke ni a bakin layinnu tare da sake jaddadamun girman alƙawarin dana ɗaukarma kaina, da wannan mukai sallama da Khalid. Kai tsaye gidan da su Adama suka kama na nufa, Labbai na hango a bakin ƙofar ɗakin nasu da ƙaramin risho tana shirin kunnawa, ganina yasa ta washe bakinta. "Ah Lolo kece da safe haka? Yanzu kuwa Maigogul ya fita daga gidannan baku haɗu ba?" Ina dariyar yaƙe wanda yafi kuka ciwo nace. Bamu haɗu ba kuwa" Shigewa ciki mu ka yi, Adama na kwance a tabarma sai shantaka bacci take yi. Hiye ba shakka su Adama an samu waje bacci ma take yi har yanzu bata samu damar tashi ba. Da ace a gidanta ne ai da yanzu tana bakin murhu" Dariya muka saka ni da Labbai. Dariyar ce tasa Adama ta buɗe idanunta. Yamutse fuska tayi ta miƙe tana tsaki, cikin muryar bacci tace. "Lolo yaushe kika zo?" Kallon fuskarta nayi dama dama da kwalliya nace. Naga fuskarki duk kwalliya ta dame" Dariya tayi tace. "Bari in wanko baki inzo ki sha labari ni dai nayi kamu ALLAH." Bakina a sake har Adama ta fita. Labbai kuwa tana kwance a kasa tana dariyar mugunta dama halinta ne duk yadda akayi ba kamun arziki Adama tayi ba. Sai da Labbai ta gama dariyarta harda birgima kana tace. "Kafin tazo baki labarin bari in dafo mana taliyar yara, kinga muna ci muna hirar abun zaifi daɗi." Wata ƙatuwar leda naga labbai ta buɗe ta ciro indomi manya uku, da ƙwai uku. Ni dai mamaki ne ya gama isata nama rasa tacewa. Wayar Adama ce ta shiga ruri tana gefe na ɗakko wayar nayi na duba naga an rubuta Alhaji Bilya. Kai na gyaɗa kawai na ajjiye mata wayarta na ciro ice cream a ledar siyayyana dana ɗakko babban roba dama dan mu sha dasu Labbai ne, Rakiya ma na dakko mata ƙaramar roba da meat pie babba nasan tana son meat pie aikinta kenan ba da sallahun a tawo mata dashi. Adama ce ta shigo da sallama tana ganin kayan daɗi ta shiga washe bakinta. 5 alive ta ɗauka ta ɓalle ta sha_ta sha kafin ta sauke. "Baki ji sanyin shi ba har maɗigata wallahi kai Lolo Allah yasa a wannan karon mu shiga gidan da zamu huta." Kafin in bata amsa Labbai ta shigo da faranti shaƙe da indomi da daddaffen ƙwai. Wayar Adama ce ta shiga ruri da sauri ta ɗakko, da taga sunan sai naga ta washe bakinta. Labbai kuma nan ta shiga dariyar iskanci. Nima dai a wannan karon dariyar nake yi duk da bansan meke faruwa ba, amman kamar bazawari Adama tayi. Tsahare ce ta shigo da sallamarta. Ganin kayan ciye_ciye yasa ta hau washe baki. "Na dawo a daidai ashe a daidai. Lolo ashe kinzo?" Kaga manya manyan zawarawa ban jima da zuwa ba. Fita kika yi ne?" "Wallahi a gidan ƙawata na kwana ta haihu mijinta baya nan shine ma ya nemi alfarman inje in zauna da'ita. Yanzun ma kaya nazo zan ɗiba zuwa bayan suna zan dawo" Adama fa tana gefe tana waya wallahi sabida ƙasa da tayi da muryarta mu kammu bama iya jin abinda take cewa. Tana gama wayar muka saki shewa tamkar bamu da wata matsala a rayuwa. Alhalin ko wacce cikinmu da damuwa ƙunshe a ranta. Amman da zaran an haɗu an zauna saimu wanke ma kanmu da kanmu baƙin ciki. Muna cin abinci Adama tace. "Lolo sabon bazawari nayi mai malum malum shine Labbai ta saka shi a gaba shegiya da dariya tun jiya da dadare. Ma'u ce tazo gari ta ɗaukeni muka je bikin ma'aikatan kamfaninsu. To acan muka haɗu dashi. Baƙauye ne amman wallahi akwai kuɗi, kuma kamar lusari ne kashe ma mace kuɗi bai fiye damunshi ba." Labbai tana gama haɗiye ƙwan data saka a baki tace. "Wai ke kinga malum_malum ɗinshi zata yi yadi goma, gashi ƙato sosai gashi da tsayi. Lolo ƙafarshi duk faso, amman ke da ganin motarshi wallahi kuɗin akwaisu, amman a fatarshi babu wani halamun hutu" Dariya mu ka yi dukkanmi. Ahh Adama kice koma ta kama babban kifi? Amman ai baki gama idda ba yana da kyau ki sanar mishi" Saida Adama ta tsotse romon hannunta kana tace. "Na sanar dashi tun jiya. Ya kuma ce zai jirani in gama iddata sai yazo mu sasanta kanmu." Yauwa hakan yafi. Amman gaskiya ki aureshi da zaran dai kin gama idda kar mahassada su shiga su fita. Kinsan da yazo ɗaya biyu layinnan ba lallai yazo na uku ba magulmatan layinnan zasu korar miki shi" "Ke dai bari Lolo. Duk da naji yana cewa ba'a cikin garin dutse iyalanshi suke ba, bazan ƙi aurenshi ba tunda yana da kuɗi. Dama na rantse na maya da in kuma auren wahala gara in zauna inta zawarci. Ke tunda wannan babban kifi yazo hannu Lolo ai babu sanya. Zan ɗanje ma wajen wani malami ya ɗan rubuta mun fahami, ko ke zaki rubuta mun ne Lolo?" Dariya kawai nayi dan nasan tsokanata take yi sarai. Rakiya ce ta buɗe labulen ɗakin. "Babu shakka Lolo ashe da gaske ke ɗin Uzairu Zuchiyata ya gani ɗin. Wato yanzu sai dai ki wuce gida kizo nan ki baje duk abinda kika kawo kuci anan ko? Yayi kyau" Shigowa tayi ta nemi waje ta zauna. Ba haka bane Rakiya yanzu zuwana ban jima ba. Kuma kema ga naki tsaraban da ban na ware miki. Indomi kuma nasu Labbai ne suka dafa mana" Miƙa mata ƴar ledar ice cream da meat pie ɗinta nayi ta karɓe tana washe bakinta. "Allah yayi albarka. Jibi ƙoƙarin duk da Babangida yake yi a kanki amman a haka kike son. Tozarta kanki. Yanzu jibi Adama goɗai goɗai da'ita tsofai_tsofai tana zawarci, banda sauran ƙannenki. Abidan Hauwa ma mijin ya sakota yanzunnan da ɗanyen goyo yanzu isowarta tun jiya suke cin tafiya a mota. Wannan bai isheki ba a_a sai kin kaso aurenki kema kinzo kin jeru dasu kuci gaba da ɗakko mana maganar da kuka saba. Ni dai bance komai ba, gabaki ɗaya farin cikin ma da nake ciki sai naji ya gushe mun. Babu shiri na miƙe nayi musu sallama. "Kifi ruwa gudu dan ubanki. Yara babu da wacce ka isa, babu dama ai muku magana sai ku hau dokin zuchiya. In kinso kada ki sake zuwa har mahadi ya bayyana ja'irar kawai." Harna fita Rakiya ina jiyo muryarta tana zagina. Kai tsaye na hau abun hawa ya mayar dani gida. Ina shiga uwarɗakina naga kaya a zuzzube halamun an yi mun bincike, ga takaddu baja_baja a gadone, a ƙasane. Cikin takaici da tunanin to waye ya buɗe mun ɗaki na shiga gyara kayana ina tsaki, duk da zuchiyata na zargin Babangida ne. Na fi awa biyu ina gyara wardrobe dan kusan dukka kayana gogaggu ninkakku an zubo mun dasu, haka na gyara komai na mayar da komai muhallinshi, kana na fito kitchen dan in gyara kwanuka. Yauwa Maman Sa'idu dan ALLAH waye kika ga ya buɗe mun ƙofa?" Na tambayi Maman Sa'idu dake shanyar kayan yara. "Babansu Mardiyya ne ya shiga. In banda abinki waye zai shigar miki. Ko da yake abu da me kishiyoyi" Murmushi kawai nayi mata, dan a zahiri da wasa tayi maganar, amman ni nasan har cikin ranta tayi maganar. "Ab maman Mardiyya ashe kuma Babansu Mardiyya ya saki Maman Usama? Kaik abu baiyi daɗi ba ɗazunnan ta fita daga gidannan da kaya niƙi_niƙi ita da wata ƙawarta" Wani irin mamakine ya kamani, bawai na sakin ba tunda ba abu bane sabo a wajen wanda yayi sakin ba. Mamakin da nake yi wani auren Babangida zai sake jajiɓowa a hakan a gidan haya ga kudin da yake taƙama dashi babu? Wato maza masu auri saki tamkar masu aljanu suke, da zaran aljanin saki ya hau kansu to fa sai sunyi suke jin daɗi. Haka da zaran aljanin ƙarin aure ya hau kansu to sai sun ƙaro. Hmm Allah sarki, Allah yasa hakan ya zame mata alkhairi. In kuma da sauran shan ruwan auren nasu Allah ya daidaita tsakaninsu" Ina gama faɗin haka na koma ciki nayi kwanciyata a gado ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomun haɗuwata ta farko da Babangida haɗuwar da har gaban abada bazan dena dana saninta ba. Ranar data zame mun ranar tarihin da bazai taɓa ciruwa a cikin tarihin rayuwata ba. Ajjiyar zuchiya na sauke tareda share hawayen da suka gangaro daga guraben idanuna.

Mrs Bukhari

Sai mun tara gobe IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA SHA BIYU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

GIDAN SA'A:.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull