Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 10

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 10

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 10: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 10. Har suka wuce ciki yana shessheƙa. Ko gaishemu ma baiyi ba. Adama ce ma taje…

4,037 words

Har suka wuce ciki yana shessheƙa. Ko gaishemu ma baiyi ba. Adama ce ma taje tambayar ba'asi bayan mun shiga ɗakin. "Ummi sata yayi a makaranta a jakar wani yaron ajinsu. Yau ba ƙaramin duka akai mishi ba. Malamarmu ma tace tana son ganinki zuwa gobe ummi" Ras gabana ya yanke ya faɗi. Shikenan abinda nake gudu yanata faruwa ta tabbata Aɗɗa'u ya ɗakko dabi'un Sama da Ma'aru sak. Dan a halin yanzu shi kanshi Ma'aru mijin Layuza yayi mishi korar kare a shago. Waje na samu na zauna nabar su adama suna ɓaɓatun rashin gaskiya cewar shine dan yayi sata za'ai mishi Irin wannan dukan. Shi kuwa sai wawwara idanu yake yi. Satansu nayi na damƙeshi na riɗashi da ƙasa na samu guiwata na dira mishi ita a ƙirjinshi na kama wuyanshi kamar zan kasheshi dan baƙin ciki. Ga hawaye ya gama wanke mun fuskata. Ina gani idanuwanshi na firfitowa kamar zasu faɗo da ƙyar Adama da Uzairu zuchiyata su ka yi gefe dani na jingina a jikin kujera ina maida numfashi, Adama ta miƙar da Aɗɗa'u tsaye. "Ku shiga kuyi alwala maza su tafi masallaci maza" Sai da muka shiga ɗaki Adama tace. "Lallai Lolo baki da hankali wannan yaro daya mutu me zaki ce da ubanshi? Kamata yayi ki gode Allah wallahi. Mu yaranmu mazan shaye_shaye suke yi, matan sun ɗakko sahun abinda muka yi a baya. Babu arabi babu boko sai yawon bin bola da rafi. Adda'a zaki dage kiyi tayi mishi sai kiga Allah ya shirya miki. Lolo da ace yaranmu zasu yi rabin abinda muka yi ke kam na fahimci haɗiye zuchiyarki zaki yi ki mutu. Ki jawo ɗanki a jiki ni dai na faɗa miki. Dan Allah kada ki sake dukanshi in an kawo miki karar yayi sata, duka baya gyara sai dai ya sake kangarar da yaro" Uzairu zuchiyata yace. "Ato ta kama yaro zata kashe wallahi Lolo ki dena irin wannan dukan. Ni bamma san gidan uwar data iya duka ba. Maigogul dai da Rakiya basa duka. " Adama yanzu ace a irin shekarun Aɗɗa'u har yasan ya dinga manyan sata ina yake son in sa raina. In na fita na barsu a hannun matan uba yaya zai zama kenan?" Labbai tace. "Suna daga cikin abubuwan da ake jiye miki Lolo. Kayi da kanka ma yaya ka cika balle kuma wani ne zai yi maka" Kallonta nayi nace. Amman kinsan zaman Ƴaƴa da mafi yawan akasarin mata suke yi shike kashe musu rayuwarsu kuma hakan kesa mazan in an haihu dasu suke yima macce duk abinda yayi musu gani suke yi ko dan ƴaƴanta dole ta zauna kinsan da haka ko? Ai duk masoyina wallahi zai so rabuwata da Babangida " Ficewa nayi ina nunfarfashi na ɗauro alwala na fito. Na daɗe sosai akan sallaya inata rokon Allah akan ya shirya mun Aɗɗa'u ya dena wannan sata. Sannan Allah ya ɗorani akan Babangida inyi nasara akan wannan shari'ar. "Kizo muci abinci Lolo ke muke jira gashi har anyi kiran isha kina ta zaune a dadduma." Kuci abinci Adama bakina babu daɗi kunu kawai in Mardiyya taci abinci zata damamun." Basu ce mun komai ba suka zuba abinci suka ci. Ni kuma na tashi na gabatar da isha. Ina idarwa na hau gado dan wani irin ciwo kaina yake yi mun. Sai wajajen tara su Adama sukai mana sallama suka tafi sunƙi yadda su kwana suna son suje suyi gyare gyare a ɗakin da suka kama. Tun da yamma dama na ɗiban musu kayan abinci a cikin ragowar nawa komai da komai wanda su biyu dai in sun jalauta zai iya musu wata guda ma. Idanuna na lumshe ina tunanin taya zan ɓulloma Aɗɗa'u ne. Sallamar Babangida muka jiyo daga bakin ƙofa. Da sauri Mardiyya dake rubutu ta miƙe ta fice, Malama kuwa ta daɗe da yin bacci. Ina jin takunshi har gaban gadon da nake kwance. Ruf naima idanuna kamar mai bacci. "Sabuwa nasan idanunki biyu ki tashi dan Allah muyi magana. Ya kamata mu fahimci junanmu." Buɗe idanuna nayi yana tsaye a kaina. Kaga dan Allah ka dena shigo mun ɗaki kai tsaye haka. Sannan babu wata magana a tsakaninmu kaje kawai wajen matanka. Duk abinda zaka faɗamun ɓatabakine kawai." Ya jima yana kallona kafin ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Shikenan zan bari ranar girkinki ya zagayo sai muyi magana. Kuma kafin ranar ki shirya tarbar mijinki dan ina cikin matsananciyar buƙatarki. Ke kanki kinsan nafi samun nutsuwa dake" Dariya kawai nayi mishi a raina na aiyana. Ashe zan fame maka ciwon da kake tattalawa ka ɗauka Sabuwa daka saba turmushewa dan dole ne a baya. Zan kuwa gwada maka" Juyawa yayi ya fita na mayar da idanuna na rufe ina haɗiɗiyar zuchiyata. Mardiyya ce ta dawo ciki. "Ummi Aɗɗa'u fa yana falo yanata kuka yaƙi yayi shiru ko abinci ma baici ba. Baba ma ya tambayeshi menene yaƙi yin magana" Kiramun shi Mardiyya. Ki kuma zubo abinci ki kawo mun" Da "To " ta amsa ta fita. Bata jima da fita ba Aɗɗa'u ya shigo yanata rakuɓewa a bango. Tawo ka zauna Aɗɗa'u kaji" Jin sanyi da salama a muryata yasa ya tawo ya zauna. Sai naji tausayin yaron ya tsarga mun. Gashi a kaf yarana Aɗɗa'u yafi nuna mun kulawa in yaga banda lafiya yafi kowa shiga damuwa, hakama in ya ɓata mun rai yake shiga damuwa. Zo inga jikinka naga shatin duka" A hankali ya matso na kwaɓe rigarshi. Duk uwar da taga abinda akaima Aɗɗa'u wallahi saita zubar mishi da hawaye ko da kuwa kisa ya aikata. Bayanshi duk a faffashe ya ɗaɗɗaye. Da sauri na juyo dashi nace. Wanne malaminne yaima irin wannan dukan?" Mardiyya ce ta shigo da abinci a roba. "Malam Musa ne wanda yake musu lissafi. Haka ya dinga dukanshi ummi baki gani ba" Wani yawu na haɗiye na kalleshi yanata matsar hawaye. Nawa ya ɗauka a jakar abokin nashi?" "Dubu ɗaya ce ya ɗauka kuma bama wanda ya ganshi. Shi dai yace bashi ya ɗauka ba. Amman yaran ajinsu sunce shi ne yake ɗauke musu kuɗi a jakarsu, ko biskit." Shiru nayi kawai ina nazari. Bashi abincin yaci. Sai in kaishi kemis a bamu magani" Abincin ta ajjiye mishi amman ya kasa ci jikinshi yanata rawa, ga kuka yaƙi ya dena. Aɗɗa'u ka faɗa mun gaskiya kai ka ɗauki kuɗin abokinka, in kai ka ɗauka me ka siya?" Wani sabon kukan ya fashe mun dashi. Take jikina ya bani bashi ya ɗauki kuɗin ba. Dan ba yau aka saba kamashi da laifin sata ba. Sai dai ban taɓa ganinshi cikin Irin wannan yanayin ba. Miƙewa nayi na ɗakko mayafina na yafa. Daure kaci abincin muje kemis ɗin bakin titi a baka magani maza. Ka daure" Yana cusa abincin yana kuka. Niko ina jin raɗaɗin dukan dake jikinshi a jikina. Yaci abincin aka bashi ruwa yasha. Muka tafi zuwa kemis ɗin bakin titin shigowa unguwar kemis ɗin babbane harda gadon kwantar da marasa lafiya guda biyu take dashi. Ta duba shi ta bashi magunguna muka dawo yasha nace yaje shi ya kwanta.

Babangida:.

Yana fita daga ɗakin Sabuwa ɗakin Hamida ya nufa. Tana zaune tayi bake_bake a ƙasa ta tusa tuwo a gaba amman bata ci ko loma ba. Usama yana kan kujera yayi baccinshi. Mufida kuma tana zaune tana wasanta kusa da uwarta. "Sannu da dawowa." Bai amsata ba ta miƙe ta ɗakko abincinshi ta dire mishi a gabanshi da ruwan sha dana wanke hannu dukka. "Me ya hanaki cin abincin to kika tusashi a gaba?" Kafin tayi magana maƙociyarta ta ɗaga labule tana faɗin "Maman Usama ga shinkafa da miyar da kika ce ta baki sha'awa na zubo miki" Ganin Babangida baisa ta saki labulen ba. Da dariya ta gaisheshi tare da sake yi mishi ya jiki. A daƙile ya amsa. Hamida ta miƙe ta karɓo robar da aka shaƙeta da shinkafa da miya da nama ga latas da tumaturi da albasa a wadace, ta wuce Babangida tazo ta zauna a ƙasa. Mamakinta yasa ko kular abincinshi ya kasa buɗewa. Ita kuma tana dariya tazo ta wuceshi ta zauna ta tusa robar abincinta a gaba tana ƙoƙarin soma ci Babangida yayi gyaran murya, da sauri ta ɗago ta kalleshi. "Akwai abinda kake buƙatane, naga har ruwan wanke hannu na ajjiye maka?" "Wato har lalacewata ta kai lalacewar da zaki ji gwaɗayin shinkafa da miya da latas Hamida, har baki ji kunya ba kika faɗa mata ya baki sha'awa baki ji kunya ba dan Allah? Daga faɗawa jarabawa tun kafin ace an soma fuskantar wani irin yanayi har kin soma nuna maitarki a fili, nafi ƙarfin ki zubar mun da daraja wallahi" Ranshi yayi mummunan ɓaci, itama ta gane hakan sarai amman har cikin ranta daɗi taji sosai ko dan ƙuntata mata da yayi ranar daya ɗauki kwana ya kaima sabuwa. Hausawa suka ce tsautsayi baya wuce ranarshi. A wulaƙance Hamida tace. "Laifine dan kawai naji sha'awar shinkafa da miya da nama? Yau ɗaya dana siyo soyayyen kifi na watsa a taliyar da naci da rana kar kaso kaga da yadda naci abincin, ragowarma sai almajirai na baiwa" Cikin nuna zafi da baƙar zuchiya irin na mai naiman dalili ƙarfi da yaji Babangida ya dubi Hamida yace. "Kuma ni ko a gidanku banga kuna cin nama sau uku a abinci ba. Sau ɗayane a miyar dare ina ubanki yaga kuɗin da zai girke muku nama kamar yadda ni nake girke muku.?" Yana faɗar haka ta miƙe tsaye cike da tsiwa da rashin daraja tace. "A_a kada ka kuma dan wallahi ka zagi ubana saina zagi naka uban. Ka ganni na sam darajar iyayena ni ba lusarar matarka mazanaciyarnan bace da take zaune kake zagin iyayenta ba" Murmushi mai ciwo da ɗaci yayi, yana jin wani abu na soya mishi a zuchiyarshi wanda shi kanshi baisan menene ba. Muryarshi a dashe cike da sanyi yace. "Na sake ki saki ɗaya. Sai kije gidanku a dinga yanka miki saniya kina karya kumallo da'ita ƴar ƙaruna" Ƙirji Hamida ta dafe tare da zaro idanunta waje. Kunsan mata nada wata ta'ada ko yaya miji yake duk lalacewarshi da zaran ya furta kalmar saki sai jikin mace yayi sanyi tarara ko da kuwa ita da bakinta ta nemi sakin kuwa. Wannan yanayin Hamida ta shiga babu shiri ta zube a gaban Babangida ta soma yi mishi magiyar yai mata rai. "Dan Allah kada kasa aimun dariya. Wallahi kasan ina sonka wanne irin saki ana zaune ƙalau kuma? Ɓacin raine da sharrin shaiɗan. Wallahi zafin kwanana daga ɗauka ka kaima matarka ne yasa nima na ɓata maka ranka, amman na tuba ka maidani ɗakina dan ALLAH." Miƙewa yayi yana jin kanshi na sara mishi ya ƙule ɗakin Hamida harda saka sakata. Ba yau bane ranar farko daya taɓa sakin mace ba, kuma bawai Hamida na daga cikin matan da yake jin sonta bane. Asalima Farida daya saka tafi ko wacce macce soyuwa a ranshi daga cikin matan daya saka hakan bai hana ya saketa ba data kama. Amman abun mamaki a karon farko sai yaji sakin yayi mishi wani bawai. Yana kuma tunanin halin da iyayenshi zasu sake shiga matsawar suka ji labarin sakin da yayi musamman Baba Malam. Takadda ya yaga ya rubuta sakin a matsayin shaida kana ya ciro wayarshi ya ɗauki hoton sakin ya turama Sumy ta manhajar WhatsApp. "Gashi na saki wacce tsautsayin sakin ya faɗo a kanta. Gobe sai ki tattara ki kama hanya kamar yadda muka yi dake" Mayar da wayar yayi gaban ajjihun rigarshi ya buɗe ƙofar ya fito. Hamida na zaune zaman durshan a ƙodar ɗakin tana sharce hawaye taji fitowarshi babu shiri ta miƙe tare da fuskantarshi tana jaddada bashi haƙuri. "Ga takaddarki kiyi haƙuri aikin gama ya gama" Hannunta na rawa tasa hannu ta karɓa ta zauna daɓas a saman kujera tayi ƙuri har ya fice ya barta a ɗakin kukanma ƙafewa yayi tas. Da sallama ya shiga ɗakin Ƴar Shuwa duk da baiji an amsa mishi sallamar ba, sai yayi tunanin ko tana can ciki ne. Falon babu kowa ga tv a kunne fanka ma a kunne sunata aiki. Kai kawai ya gyaɗa ya kutsa kai cikin uwarɗakin. Turus ya tsaya ganin mata riɗa riɗa har su uku a kan gadonshi suna cin abinci duk sun yi watsi da ɗankwalayensu. Da sauri ya koma, su kansu duk sai suka rikice da ganinshi tunda Ƴar Shuwa ta tabbatar musu ba kwananta bane ranar. Cike da mamaki yayi komawarshi falo ya zauna a kujera ya ɗaga kanshi sama tare da rufe idanunshi, shi kaɗai yasan abinda yake ji a zuchiyarshi. Sum_sum_sum matannan suka fito suka wuce shi. Uwar gayyar ce ta zauna a kusa dashi cikin muryar rashin gaskiya tace. "Sannu da shigowa ashe zaka shigo?" Ta faɗa a ɗarare. Mugun kallo ya watso mata yana daga shingiɗe a kujera. "Waɗannan marasa albarkar su kuma daga ina da har kike ganin matsayinsu ya kai ba falo ba har uwarɗakina, akan gadona ake cin abinci. Sannan a ina kika samo su nasan dai ba ƙawayenku bane tunda daga cikin ƙawayenku ke da Sabuwa babu wacce ban sani ba?" "Matan maƙotane suka shigo, to lokacin da suka shigo ina ciki ne ina gyara kaya a wadrop shine nace su shiga" Zama yayi ya fuskanceta da kyau kana yace. "Har kinyi sabo da maƙota irin haka? Ko da yake na fahimci matan layinnan kamar basu da kamun kai ba kuma su san darajar aure ba. Ki kawo mun abinci in akwai" Ya ƙarashe maganar cike da bambami. Ita dai bata ce uffan ba ta fita ta kawo mishi abincin kamar yadda ya umarta. Bai ci yafi loma biyar ba ya sha ruwa ya miƙe ya shige ciki har uzuwa lokacin mita yake yi kamar tsohon kuturu. Da uwar harara ta bishi harda gajeren tsakinta marar sauti. "Mutum sai shegen faɗin rai da mitar tsiya. Nifa wallahi bazai yiwu ba ehe" Ta miƙe tare sa tattare kayan da yaci abinci ta fita dashi, tana shiga cikin coridor ta ji halamun wanka yake yi. Cike da mamaki ta shige ciki a gurguje ta gyara inda duk aka ɓata. "To wannan ciwonne yasa ya mance ba kwanana bane, ko ko tsabar jarfar da Sabuwa ta ɗebo mishi ne ya rikirkitashi? Ni dai nasan Hamida ke da kwana, tun yamma taci kwalliya take ta falli a tsakar gida, sai miji kuma ace ɗakina zai shigo yaci abinci harda wanka? Tabb gobe akwai rikici kenan" Dariyar mugunta ta saki, a haka Babangida ya shigo ya taddata, bai ko kalleta ba daga shi sai gajeren wando yayi kwanciyarshi. Amman me? Shine har biyun dare idanunshi a soye, idanu ya ƙurama Ƴar Shuwa wacce take ta sharar bacci abubuwa da yawa yake tunanowa a kanshi game da farkon soyayyarshi da'ita da irin yadda yake jin in ba samunta yayi ba zaima iya mutuwa." "Aisha! Aisha" Babangida ya shiga kiranta a hankali" Cikin bacci ta buɗe idanunta ta kalleshi. "Jannaty bakai bacci ba na ganka a zaune Aisha ka dawo kirana kuma hmm?" Idanunshi ya lumshe yana jin motsin san kasancewa da mace a jikinshi. Dan in ɓacin rai ya shiga kasancewa da mace ke saukar mishi da fishin nashi. Kallon da yayi mata tuni ta bugo jirginshi take ta ba da kai bori ya hau. Cikin dabara komai ya gudana duk da a hakanma saida ya ɗan fama ciwonshi. Bayan komai ya lafa ne bacci ya sureshi. Yayinda ita kuma Ƴar Shuwa ta zauna zaman dirshan zuchiyarta cike tab da tunanin yadda zata kawo ƙarshen sabon asirin jawo hankalin da Sabuwa taima Babangida da har ya iya zuwa ɗakinta yayi kwana biyu. Kuma Sabuwa ta ji mata ciwo Babangida ya kasa ɗaukar matakin komai akai. Gashi yau da Aisha gatsau ya kirata kafasiti nata zubewa. 🤣 "To ko dai yana son matarshi ne daman? Duk da dai yace sabida bakin da Baba Malam yayi mishine ne yasa yake zaune da'ita. To amman a wannan karon me yasa har Malama Babba bata son a saki Sabuwa? Ya zame mun dole gobe in ziyarci gidan Yaya Sa'a a canne zan iya dukan cikinta in ji komai tunda ita na fahimci lusara ce.

Washegari da safe SABUWA:. Bayan mun kammala karyawa yara sun yi wanka kowa yasa kayan makaranta, saina ɗauki jakata da mayafina nima na fito. A lokacin harsu Mardiyya sun fice. Ina kulle ƙofa Malama tace. "Ummi gidan Baba Maigogul zaki je? Nima zan biki ummi dan ALLAH" Murmushi nayi nace. To yanzu kuje makaranta nima makarantar taku zanje, in kuka taso kuma kinga kuna da islamiyya. Ranar juma'a nayi muku alƙawari zamu je mu kwana ma a gida asabar ma dawo" Nan suka shiga murna abunka da yaro Maman Sa'idu dake haɗa kayan karyawa tayi dariya itama. Gaisawa muka yi a gurguje nayi mata sallama muka fita. Kafin in fice a gidan na hango fitowar Babangida daga Ɗakin Ƴar Shuwa tana biye dashi da halama unguwa suma zasu je. Da sauri Babangida ya sha gabanmu. Yaran suka gaisheshi ya amsa yana fara'a harda ɗauko ɗari biyar yana ba Mardiyya. "A_a Baba ka barshi Ummi ta bamu kuɗin mota" Kallon yaran yayi sai yaji kunya. "To ku dai ƙara kunji" Hannu tasa da ladabi ta amsa suka wuce. Babangida ya dubeni, ni ko kaina gefe yake kallo, mutuniyarku tana tsallake ta cika ta batse. "Ina zaki je da sassafe haka ke da bakya kaunar zaman gidanki kisan bana son fita ko?" Idan kaga mace na ƙaunar zaman gidanta, kaje ka bincika haƙiƙa wannan gidan a ciki take samun nutsuwa. Ire_irenmu kuma sai mun fito daga gidan namu muke samun nutsuwa". Ina gama faɗin haka nabi gefenshi zan raɓa, yayi maza ya kuma shan gabana. "Amman kinsan mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba mala'ikun Allah ba zasui ta tsine mata har sai taje ta dawo ko? Ko da yake nasan ba lallai kisan wannan ba tunda... Sai yaja bakinshi ya rufe. Ƙuri nayi ina kallonshi har yayi shiru. Ba'a bani tarbiyyar sanin hakan ba a gidanmu. Mahaifina Kawaline ba Malami ba. Amman dai nasan zina masifa da bala'ice kuma mai yinta baya taɓa kasancewa cikin arziki, dama lafiya, kuma bashi ce kayi da matar wani ayi da taka matar shi wannan na sansu" Wucewa nayi da ƙarfina dan nayi niyyar da ya sha gabana to haƙiƙa saina tunkuɗeshi ya faɗi. Inaji yana kiran sunana yana bina a baya, nayi fumfurunfus. Ina zuwa titi na faɗa cikin Bus ɗin da yara suka tara muka wuce abinmu.

BABANGIDA:. Shiru yayi a gaban titi zuchiyarshi na suya mishi. Tare da tunanin to ina Sabuwa zata je da safe haka? Wata zuchiyar ta ayyana mishi. "Ko wajen Khalid zata ne kasan sun daɗe basu haɗu ba"" Take ya runtse idanunshi. "Ai sai ka tare mana abun hawa mu wuce ko tunda ita matar taka tayi tafiyarta muma ai sai mu tafi ko?" Idanunshi ya buɗe take taga sun sake nauni dole ta haɗiye masifa da bala"in da take son sauke mishi. Mashin ya tare ya ɗane. "Bus dincan da tai kwana zaka bi mun. Ke kuma ki kama hanya ki tafi wajen yaya Sa'a ni sai na dawo" Fuu mai Acabanshi ya ja suka wuce. Wasu hawayen baƙin cikine suka sulalo a kumatun Ƴar Shuwa tayi kasaƙe a titi tana mamaki har saida ta dena hango Babangida kafin ta tari abun hawa ta wuce gidan Sa'a Babangida yana biye da Bus ɗin su Sabuwa har sanda ta diresu a ƙofar makarantar yara. Nannauyan ajjiyar zuchiya ya sauke tare da lumshe idanunshi yaji wani irin sanyi da baisan na menene ba a zuchiyarshi. Wayarshi ce take ta ruri lauyanshi ke kiranshi babu shiri ya ɗauka. "Babangida ya kamata ace uwarhaka muna kotu tare da kai domin mu sake samun damar tattaunawa kafin a shiga Chamber. Sannan da fatan baka mance da takaddun lissafin kuɗaɗen ba ko?' Kai Babangida ya dafe dan ya mance da takaddar. "Barister wallahi na mance da takaddar kaina ya ɗau zafi da yawa. Amman yanzu zan juya in ɗakko bazan jima ba zaka ganni." Kashe wayar yayi, kana yaima Ɗan Acaɓa kwatancen inda zai kaishi zai kuma jirashi ya shiga ya ɗakko takadda ya fito. Basu juma ba suka iso, ɗakin Ramatu ya soma shiga tana zaune tana karyawa da doya da ƙwai ya shiga a ƙagauce. "Ramatu kayayyakina suna ɗakinnanne dan ALLAH?" "A_a kamar suna ɗakin Maman Usama ko ɗakin Maman Fati ban dai sani ba ka tambaye su" Bai bata amsa ba ya fice zuwa ɗakin Ƴar Shuwa neman duniya baiga takaddun ba, akwai kayayyakinshi a ɗakin takaddunne babu. Dakin Hamida ya shiga ya sameta a ciki tana kan haɗa kayanta ya shiga birkita kayayyakinshi na ɗakin nanma babu waɗannan takaddun sam. Yana shirin fita ne Hamida tace. "Ni inna gama zan wuce garinmu. Zan tafi da diyata, Usama kuma a wajen wa zan barshi?" Tsaiwa yayi ya dubeta ita da yarinyar dake bacci a bayanta kana yace. "Ki ba Ramatu shi kice in jini. Zan tura miki kuɗin mota Allah ya tsare" Yana gama faɗan haka ya fice zuwa lungunsu Sabuwa estira key ɗin kwaɗon ɗakin ya saka ya buɗe ɗakin ya shiga zuwa uwarɗakinta ya hau dube_duben takaddu, ya birkita kaya sosai kafin ya gansu a killace a cikin wani fail fari mai ɗauke da sunanshi. Ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin mayar da kayan Sabuwa daya wargaza mata. Ananne wata ƙatuwar leda fara mai ɗauke da hatimin shagon siyayya ya faɗo. Haka kurum yaji ya kasance cikin son ganin menene wannan abun dake cikin ledar. Hannunshi na rawa ya zazzage ledar kayan dake ciki suka zubo. Idanunshi suka sauka akan kwalin sigari ɗan ƙasar waje. Wani yawu ya haɗiye muƙut a hankali ya tsugunna ya ɗauki kwalin sigarin yana kallo Ko daya buɗa saura guda huɗu kacal a ciki duk sauran an shanye. Yarwa yayi ya kuma ɗaga wani net sai yaga rigar bacci mai raga_raga da wandonta ƙarami shima mai raga, harda rigar Mama masu tsadar gaske dan Designer ne take jijiyoyin kanshi suka shiga shocking suna kumbura suna sakewa da kansu. Yana riƙe da ɗan kamfai numfashinshi na yin sama_sama. Wannan tsarabace khalid yayo ma sabuwa shiru kawai yayi baisan a wanne yanayi shi kanshi yake ciki ba, baya iya fahimtar komai face raɗaɗin da zuchiyarshi take yi mishi, da irin luguden da zuchiyar tashi take dokawa. Sake lumshe idanun nashi yayi tare da tariyo adadin matan da yayi tarayyar banza dasu. Sai dai kash sabida tsabar yawansu tuni wasu ya mance ma dasu. Wani irin wutar kishine take ci a zuchiyar Babangida wanda hakan ya haifar mishi da jikewa sharkab da ruwan gumi. Har sau biyu lauyanshi na kiranshi amman baima sani ba, sai a kira na uku ne Allah ya bashi ikon ji. Nannauyan ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya ɗauki wayar sai dai harshanshi sai yaji sun sarƙe ya kasa magana. Zare wayar yayi a kunnenshi kawai ya tattare wannan kayan ya mayar ledarsu, ya haɗa d takaddunshi jikinshi a mugun mace ya fita Mrs Bukhari Sai mun tara gobe

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA SHA ƊAYA BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

(BANA JIN DAƊIN YADDA MUTANE DA YAWA SUKE MUN DM SUNA TAMBAYATA SHIN DA GASKE NAKE YI LABARIN SABUWA YA FARU A GASKE. ALAL HAKIƘA DUK SANDA NACI KARO DA WANNAN TAMBAYAR INA MATUƘAR JIN BABU DAƊI DOMIN HAKAN YANA NUFIN MAI TAMBAYAR YANA TANTAMAR ƘARYACE KAWAI NAKE YI. KO KUMA INA CEWA LABARIN GASKIYA NE DA WATA MANUFA. KU SANI BABU RIBAR DA ZANCI DAN NAYI MUKU ƘARYA. SHIN BAKU TAƁA JIN UBANDA YAYI ƊIYARSHI CIKI TA HAIHU BANE? AI LABARIN YAFI NA SU SABUWA MUNI TUNDA MAIGOGUL BAI TAƁA JIN SHA'AWAR YARANSHI BA. WALLAHI BILLAHI NASAN GIDAJE DA YAWA DA SUKA FI GIDANSU SABUWA KAZANTA. SANNAN KU SANI DUK LITTATTAFAINA LABARAINE DA SUKA FARU A ZAHIRI KI AMINCE KO KADA KI AMINCE WANNAN YA DANGANTA DA YANAYIN YADDA KIKE ƊAUKAN ABU. AMMAN TABBAS LABARIN SABUWA LABARINE NA GASKE. NAGODE SOSAI DA SOYAYYA ALLAH YA BAR ƘAUNA)

SABUWA TACE IN MIƘA MATA SAƘONTA GA DUK ƊAUKACIN MASOYANTA.

IYABO MA TACE TANA BIBIYAR WANNAN LABARIN KUMA TANA TAUSAYIN SABUWA SOSAI. ( IYABO MAI RAYA SUNNAH A GARKEN SHANU TSUNTSUN SOYAYYA BA. TA HAMMA BADA KANKI A SARE, AMINIYA A WAJEN UWANI TA BALBALIN, CINYAR SA MAGANIN MAI HAƊAMA BA🤣🤣)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull