Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 9
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 9: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 9. Yana bayan motar Mustapha a zaune idanunshi a rufe tun daga cikin kotun har suka…
3,902 words
Yana bayan motar Mustapha a zaune idanunshi a rufe tun daga cikin kotun har suka fito motarsu ta nausa titi bai buɗe idanunshi ba. Yana jin su Bashiru suna jinjina rashin mutuncin Sabuwa. "Ai ni wallahi Mustapha mamaki Sabuwa ta bani ban taɓa tunanin da gaske take yi za'ayi zaman kotunnan ba. Bura uba ni matata ta kaini kotu akan saki wallahi ko da bakin iyaye a kaina saina saketa. Babangida matsala ɗaya ce tasa bazai taɓa iya sakin Sabuwa ba matsalar Malama Babba. Amman da dan bakin Baba Malam ne kaɗai wallahi da tuni an saki mitsiyaciya ta kama gabanta muga wanne kamilinne zai fito ya aureta. Yarinyar da aka taimakama ji iyayenta fa da ƴan uwanta, ni naga uban harda mota yazo arowa yayi amman dai ko? Kai amman Baban Sabuwa ya mugun iya wanka. " Gabaki ɗaya suka fashe da dariya Mustapha yace. "Bashiru wallahi kai ɗan iska ne. In ba arowa ba a ina zai samu Jeep ce fa ina yaga kuɗin mallakar wannan motar.? Ko da yake kawalai wallahi ƙasar a hannunsu take" Wayar Babangida sai kuka take yi yaƙi buɗe idanunshi ji yake tamkar inya buɗe idanunshi kanshi zai faɗo. Bashiru dake kusa dashi ne ya ɗauki wayar ya kara a kunnenshi ganin wacce take kiran wayar. "Wallahi da baka ɗauki wayarnan ba da kaji mummunan labari. Ina son ganinka da gaggawa wallahi awa ɗaya na baka in ba haka ba narantse da Allah ubanka zai kiraka ya sanar maka ɗanka ya koma gidan kakanninshi. Lallai Babangida kaci abinci ka kuma yi wasa da tunanina. Allah ɗaya kenan sai ka yi dana sanin sanin Sumy a rayuwarka." Wayar a hands free take duk abokan Babangida suna ji. Babu shiri Babangida ya buɗe idanunshi tare da warce wayar. "Sumy ganinan zuwa yanzu kiyi haƙuri " Ƙit ta kashe waya "Hmm bariki kenan. Ku da ba dan bariki ba Sumy ta isa ta faɗa mun magana haka? Mustapha dan Allah juya akalar motarnan zuwa gidan Sumy kasanta muguwar mahaukaciyace saita aikata abinda ta ambata." Mustapha yace. "Amman ya zaka yi da zaman meeting da za'ayi a gidanku kuma a kanka?" Yama mance shaf amman ya zaiyi dole yaje ya soma kashe wutar da Sumy take son sake kunno mishi." "Kai dai muje kawai ai ba zama zamu yi ba" Bashiru ya harareshi yace. "Kai da wa? Wallah ba zamu shiga ba sai dai kai kaɗai ka shiga. Kaima da munji shiru sai mun kawo maka ɗauki mun kira motar ƴan kwana_kwana (fire service) " Dariya suka fashe dashi, shi kuma ya koma ya jingina bayanshi a kujerar motar. Har suka isa ƙofar gidan suna surutu. Wani yaron gidanne yace. "Laa ga baban Amiru ya dawo daga tafiya" Yana faɗin haka ya ruga a guje. Babangida a karon farko daya soma nadamar ajjiye farka daya soma kenan a rayuwarshi. Mazan dake ƙofar gidan ya gaisar sunata kiranshi Baban Amiru. "Haɗari kayi ashe Baban Amiru?" Wani ya tambayeshi, kafin ya bashi amsa Amiru fito da tafiyarshi irin ta yara ya rugungune ƙafafun ubanshi. "Wallahi kuwa Malam Hamza haɗarin mota nayi" Nan suka shiga jajanta mishi dai. Hannun Amiru yaja suka shiga da sallama cikin gidan. Matan gidan duk suna tsakar gida suna aikace_aikace. Sannu kawai yayi musu ya shige ciki. Sumy tana tsaye tana jijjiga dan bala'i da masifa hancinta har hunhuna yake yi. "Kai ka ɗauka wasa nake yi Babangida, tsawon shekaru nawa ka ajjiyeni ka hana kowa ya raɓeni, ka hanani kula kowa sai yanzu inji labarin ka cikace mata huɗu? Wallahi Allah saika saki mace ɗaya dan samamun gurbi a gidanka, wallahi Allah saina rayu dakai rayuwa irinta sunnah ko kuma inje har gidanku in fallasa asirin ka in zaiyanama mahaifinka irin tsawon zamanin da muke tare da Irin duk abinda muka aikata kuma in bashi Amiru ya kiraka ya baka ɗanka tunda tonon asirin kafi so. Ƴar balaja'uce ni cikakka. Har bidiyonka saina fitar wallahi" Zama yayi babu shiri a kujera yana ta aikin kallonta tace wannan tace wancan. "Wata ɗaya tak na baka muyi aure a gama komai shine magana. Ko ayi haka ko kuma duniya ta sanka" "Amman kinsan ko zan aureki sai kin koma gaban iyayenki kinyi istibiraɗi na wata uku kafin muyi aure ko? Kuma ki sani duk matar da zan saka itama dole sai tayi wata uku na idda kafin ta fita a sahun jerin matana, ko nayi saki in dai na mutu kafin ta gama idda dole za'ace matana huɗu kuma zataci gado. To kinga batun muyi aure a wata ɗaya bai taso ba. Sannan ke me yasa bakya bin komai a hankali ne kinata ihu so kike matan gidannan su gane irin zaman da muke yi ne?" Murmusawa tayi ta ɗaura ƙafarta ɗaya a kan kujerar da yake zaune ɗayar ƙafar tana ƙasa ta matso da fuskarta ta yadda suke jin ɗumin numfashin juna" "Wallahi baka isa kaimun wayo ba. Naji zanje gida in yi istibiraɗi, sai dai ka sani a matar auren da mijinta ya saketa zanje. Iyayena bazan taɓa bari su san Amiru shege bane. Ina gama wata ukuna sai kazo a ɗaura mana aure. Amman wallahi a ranar da zan soma ƙirgen istibiraɗi a ranar ɗaya daga cikin matanka zata soma ƙirgen idda. In kuwa baka yadda ba in tona asirinka in saki videos ɗinka da su suka cika wayata in sakarma duniya a dauwama ana tsine maka" Miƙewa yayi ya ɗaga mata hannu. "Ya'isheki Sumayya nace miki naji zan aureki. A cikin matana kafin wayewar gari zan sallami ɗaya. Gobe ki shirya ki tafi garinku, ki bani adireshinki" Dariya Sumy ta saka. Kafin ma tayi magana wayar Babangida ta soma ruri Kawu Manga ke kiranshi anacan an taru za'ayi meeting uban gayyar baya nan." "Assalamu alaikum Kawu ina hanya in sha Allah bada jimawa ba zanzo". Amsa sallamar tashi yayi tare da cewa. "To Babangida ka same ni a gidana acan zamu gudanar da meeting ɗin Malam fur yaƙi mu shiga gidanshi. Kai atakaice dai ya aikata abinda baima kowa daɗi ba. Kaga su Wawo suna ciki sai koke_koke suke yi" Rararasas gaban Babangida ya tattake yayi mummunar faɗuwa. Yana son tambayar abinda ya faru yana tsoron bugun zuchiya. "Shikenan gani nan zuwa" Da mugun sanyi yayi maganar tare da sauke wayar. "Ni zan tafi gobe ki tattara ki koma garin iyayenki. Duk halin da ake ciki zamu yi waya." Har yasa kai zai fita tace. "Babangida!" Cak ya tsaya ba tare daya ƙara ko taƙi ɗaya ba. "'wallahi Allah bazan yaudaru ba. Kafin in tafi goben sai ka kirani ka tabbatar mun da sakin ɗaya daga cikin matanka, sannan ka turo mini da copy na sakin ta wayata. In kayi haka ni kuma sai in tafi" Baice mata komai ba ya fita. Da sauri ya faɗa mota ba tare daya ce uffan ba. Idanunshi ya rufe kai da zuchiyarshi suna harbawa da ƙarfi. Basu daɗe ba suka iso ƙofar gidan Kawu Manga kamar yadda yace nan zasu kawo shi. "Shikenan ni anan zan wuni da yamma zan leƙo majalisa" Mustapha yace" "Amman yaya kuka yi da Sumy Babangida. Karfa ta tona maka asirinka?" "Mustapha in nazo majalisa da yamma zaku ji yadda akayi" Shiga cikin gidan Kawu Manga yayi da sallama. Babu kowa a tsakar gidan duk suna ciki kenan. Ga takalma birjik a ƙofar falon Kawu Manga harda tashin muryoyin ƴan uwa. Da sallama Ya shiga tare da neman waje ya zauna kusa da Wawo. Jikin kowa a mugun mace. Kawu Manga yace. "To kai Wawo buɗe mana taron namu da adda'a" Da adda'a ya buɗe taron kafin Kawu Manga ya soma magana. "Abun dai babu daɗi Malam ya yanke hukunci yayi tsauri gaskiya. Yanzu idan Sabuwa tayi nasara a wannan shari'ar shikenan Malam ya rabu da Babba kenan? In kuwa da gaske yake yi haƙiƙa bai yima Babba halacci ba, Malam bai kuma duba shekaru da Ƴaƴa ba. Ya kori Babangida daga gidanshi a baya, tsakanin Babangida da gidan mahaifinshi sai dai ya shiga ya gaishe da iyayenshi mata. To yanzu yayi mai ɗungurungum yace ko mutuwa yayi bai yafe ba muddin ƙafarka ta taka zuwa cikin gidannan. Itama Babba yace kada ta koma mishi gida ta zauna a hannun yaranta har zuwa lokacin da sharia zata zo ƙarshe. Ga takaddar sallamarka da Malam yayi a makaranya yana hannun Wawo. Babangida duk da dai duk abinda Yaya yake kai gaskiya ce kuma soyayyace yake gwada maka. Kayi abubbuwa a rayuwa masu tarin yawa, har ila yau baka dena ba tunda har ka iya auren mace har kuka haihu babu wanda ya sani a cikinmu. Wa yasan inka warke irin rigimar da zaka sake jajiɓowa" Shiru yayi yayi ƙasa da kanshi yana girgizawa. "Bazaima jajiɓo komai ba tunda yanzu bashi da ko sisin kwabo, babu sana'a koyarwan ma Baba malam ya koreshi. Ai sai yaci sa'a ne in aka gama shari'arshi shi da Alhaji Abubakar Baban Bola zai iya samun ladan juya dukiya in aka cire ma mai hakki hakkinshi. Wallahi Kawu Baba Malam ya fa fimu gaskiya a cikin wannan lamarin. Laifin Malama da yake gani shine yana ganin kamar ita kullum a bayan Babangida take. Kuma fa hakanne. Kai ko dan Malama Babba ai ya kamata ka nutsu. Gashi ta dalilinka aurenta yana girgiɗi." Sa'a tace. "Gaskiya laifin Babangida ne duk komai ma. Laifin Baba Malam riƙo shi baya mantuwa, kuma in mutuncinka ya zube a idanunshi babu mai kwaso maka wannan mutuncin. Kai Babangida kana ganin za'ayi nasara akan wannan shari'ar har alƙali yasa Sabuwa tilas ta zauna dakai? Dan naga tana da hujjoji manya wanda zata iya hamɓarar damu?" Kudidi tace. "Ni bama wannan ba Baba Malam ashe shi ya ɗaukarma Sabuwa lauya ma. Ni anya Sabuwa ba lashe zuchiyarshi tayi ba? Ina tuno bayane a lokacin da ko muryar Sabuwa da ubanta baya son ji. Amman yanzu yafi son su sama damu. Mu dai mu tsaya tsaiwar daka dan mu tseratar da auren mahaifiyarmu. Malama Babba dai ruwa yana neman ƙarema ɗan kada. Ita abinda yake damunta a ranta maganar kishi ne, ko a yanzu Ƙarama taga wallenta kuma ta cire tuta ita da ƴaƴanta a idanun Malam. A gabanta Malam ya hanata shiga cikin gidanshi. Kawu Manga yace. "To Babangida gobe shine zaman kotunku kai da Alhaji Abubakar Baban Bola. Duk da ita wannan shari'ace da za'a gudanar da'ita a camba, kuma lissafin dukiya kaɗai za'ayi. Shawarar da zan baka kai namiji ne kayi bakin ƙoƙarinka dan ganin ka shawo kan matarka kasata da kanta ta janye wannan ƙarar salin alin duk yadda zaka yi aikin naka nd. In kuma hakan bai samu ba hujjojinta suna da ƙarfin da alƙali zai iya umartarka da ka saketa. Ka nutsa sosai ko dan mahaifiyarka, wannan yarinya dai ta zame mana ƙarfen ƙafa, ko ƙadangaruwar bakin tulu." An daɗe sosai anata tattaunawa tare da tsayawa akan matsaya guda ɗaya. Wawo yace zai tafi da Malama Babba zuwa gidanshi akwai ɓangare guda da zata iya zama, zai ɗaukar mata ƴar aiki da zata dinga mata aikace_aikace dan ya riga da yasan matanshi ba lallai suyi abinda ya dace ba. Basu tsaya wata wata ba, anayin sallar azahar Wawo ya ɗauki Malama Babba da su Sa'a suka wuce gidanshi, Baba malam yana kallonsu yana zaune yana karatu abinshi. Sai wajajen bayan magriba Babangida ya isa majalisarsu nanma akaita tattaunawa akan dai abu ɗaya. Ƴar Shuwa da Hamida sai rangaɗa mishi kira suke yi a waya dama ya gaji sai kashe wayarshi yayi dukka. "Yanzu wa zaka saka a cikinsu? Ni ina ganin ka saki Hamida tunda kaga itakam ai tama jima kai da baka saba ajjiye mace ta daɗe ba" Cewar Mustapha kenan. "Kaga tashi ka rage mun hanya ka kai ni gida. Wannan sakin wacce tsautsayi ya afkama ce zata sameshi ku dai ku zuba idanu. Ita kuma Sumy da ace tasan bani da komai a yanzu ba Lallai ta yadda zata aureni ba. A tunaninta zata zone ta miƙe ƙafarta taci arziki" Bashiru yace. "Wacce dai Allah ya taimaka ita zaka saka. Kai da baka da ko sisi ka koma gidan haya shine zaka ce wani menene. Itama Sumy ai gara ta shigo ta zauna taci uwar da zata ci" Dariya suka yi dukkansu. Mustapha da Babangida suka miƙe. "Sai gobe da yamma in na shigo majalisar. Ka gaida matayenka" Ya saka kai suka wuce shi da Mustapha."
SABUWA:. Da sallama muka shiga gidan matan gidan dama maƙota duk suna tsakar gida anata zuban zance can na hango Ƴar Shuwa a tsakiyarsu anata hira harda shewa. "Sannunku fa ina kwananmu?" Cewar Adama. Nan suka amsa da fara,arsu muka yi wucewarmu zuwa ciki. A falo muka ya da zango. "Wallahi Lolo waje yayi kyau sosai. Duk waɗannan da muka wuce matan gudanku ne?" A_a Sama harda matan maƙota hira suke shigowa yi na fahimta" Uzairu zuchiyata yace. "Kada ki sake ayi wannan zaman gulmar dake. Kina ganin Ƴar shuwa a cikinsu ta mimmiƙe ƙafarta itace harda shewa. Baki ga irin wani mugun kallo da take watsa miki bane, ni ko ina ankare da'ita wallahi watarana zamu yi mata babu daɗi" Adama tace. "Ai muna nan daku wata rana Babangida sai yayi mata abinda harta mutu ba zata taɓa iya mancewa ba." Dariya nayi musu nace. Ai ko yanzu kasuwar tawatse ɗan koli yaci riba. Babangida inaga fa kuɗin da yaketa juyawa yake auran mata ya saki kamar ba nashi bane. Shi da kanshi ya taramu yake yi mana bayanin cewar wannan gidan hayan anan za'aci gaba da zama sabida shi ya rasa komai nashi hatta abinci yace musu su jalauta na hannunsu dan saiya warke zai nemi sabuwar sana'a" Rahama tace. "Kuma Lolo ke kina ganin da gaske yake yi kuwa anya, har gida da motarshi kenan ya rasa, ina ita tata motar to?" A labarin daya bayar komai ya rasa hatta kamfaninshi ya rasa balle wani gida da mota. Akwai dai abinda yake ƙasa yana dabo amman ni ba sani zanyi ba gaskiya. Shi kuma dama zurfin ciki gareshi nayi imanin bazai zauna ya tattauna da ko wacce a cikinsu ba. Shi da danginshi ai sun san inda matsalar take." Aisha tace. "Da badan wani abu ba dana rangaɗa guɗa a wajennan wallahi. Duk da haka naji daɗin wannan labarin Ƴar shuwa zata gane shayi ruwane a yanzu" murmushi nayi nace. In bata sa ya saketa ba ko? Ai ba zata iya zama dashi a matsiyaci ba. Kuɗinshi ta biyo fa ai ko a haka ta tatsa da yawa. Tunda naji labarin gini ma take yi. Ƴar Shuwa fa ba zama zata yi ba. Ni kuma zanta roƙa mata Allah akan ta ƙarashe rayuwarta a gidan Babangida. Wallahi in batai wasa ba saina kafeta a gidannan" Dariya muka kwashe dashi dukkanmu tamkar babu mai matsala a cikinmu. Sama ne yace. "Ku tsaya nifa Aure zanyi na samu macen da take sona tsakaninta da Allah. Kuma da gaske aurena take son tayi. Kuma nima a guje na karɓeta. Kune ƴan uwana naga yafi dacewa in sanar daku farko tukunna tunda su Rakiya faɗace_faɗacensu suka sani. Ni na rasa dalilin da yasa suke son maigogul har suke faɗa a kanshi." Nan muka shiga murna da farin ciki marar misaltuwa a mazan gidanmu babu wanda ya taɓa aure budurwarma in banda Uzairu zuchiyata wake kula mata cikinsu. "Kai wannan abun murnane gaskiya Sama wannan yarinya da abun mamaki take. Kuma ta ganka tasan yadda kake Sama? Kai da baka da sana'a ina kai ina jijjiɓo aure kuma ga kanka suru_suru" Murmusawa yayi yace. "Adama kwantar da hankalinki zata nema mun aiki kamar yadda taimun alkawari. Inma ni ban samu aikin ba ita tana aikinta zata ci gaba da zuwa aiki zamu rufa ma juna asiri." Ni dai baki cike da fara'a nace. Menene sunanta, kuma ita wannan mata zance dan bana ce yarinya ba a ina take?" Wayarshi kawai ya zaro ya danna mata kiran waya a lambarta ya rubuta mata Love. "Hello ki kirani zaki gaisa da ƙannena muna tare dasu" Yana gama faɗan haka ya kashe wayarshi wallahi saiga kira ta biyo shi dashi. Allah mai iko Rahama ya miƙama itace suke zaune kusa sosai. Gaisawa suka yi fes kafin ta miƙama Adama, daga Adama sai Uzairu zuchiyata ya karɓa, suna gaisawa ya miƙomun. Haka dai akaita karɓa_karɓa wajen gaisawa da budurwar Sama. A ƙarshe ya amshi wayar. "Zamu yi magana zuwa anjima muna meeting ne akan aurenmu. Ki kirani zuwa anjima" Sallama suka yi ya ajjiye wayar. "To kun dai ji muryarta kuma kun amince da maganata. Rita kenan ba musulma bace kiristace gaba da baya asalima a ƙauyensu dake mangun garin Jos mahaifinta shine fasto. mun yi alƙawarin aure da'ita zata yi addininta zanyi nawa babu mai matsama juna. Kuma ta ɗauke nauyin komai na bikin" Nan muka shiga kallon kallo. Adama harda salati da tafa hannayenta. "Ohh ni Adama gidanmu gidan daɗi ƴa taso kome gidan mijinta. Yanzu Sama duk matan dake jigawa da dutse babu wacce ka gani musulma har saika auro ahalul kitabi tazo ta haifama yara kiristoci?" "Dallah dakata waya faɗa miki yarana kiristanci zasu bi? Da kike ganina ni ba mahaukaci bane kune kuke kallona a haka fa yarana ni zasu biyo. Kuma ai ba'a cikin danginta zamu zauna ba nan dutse zan kawota anan zamu yi rayuwarmu. Ke Adama a Irin rayuwar da muke gudanarwa in ba kiristaba wama zance zan aura a amince? Nine satar kaji, nine satar awaki, nike ƙwace da fisge. kuma duk wannan halin da muka tsinci kanmu Maigogul ne ya ja mana. Yanzu ba gaku ba ko wacce ta kasa zaman aure ba. Gara in auri arniyarma babu mesa mana idanu daga ɓangarenta" Shiru muka yi dan ya fimu gaskiya akan maganganunshi. "Hakane Sama. Abinda zamu ce shine Allah ya baku zaman lafiya yasa sanadinka ta musulunta. Sai dai kai kanka baka tsaida Sallah biyar..." "Ke dan abu ta kazan ki ni kike faɗa ma wannan maganar dan kin ganni a cikinku? An koya mana Sallah ne, ko tsoho ya samu a islamiyya ne?" Adama abar maganar haka azahar har tayi lokaci babu wuya fa" Uzairu zuchiyata da tunda ake magana yake ta danne dannen wayarshi, saidai in anyi abun dariya ya dara ya ɗago yace. "Lolo yinwa cikina har murɗewa yake yi rabona da abinci tun jiya da rana fa, sai dai ɗan yayime yayime." To acici mala'ikun tauna bari in kawo abinci kowa yaci. Aisha zo muje ki haɗo kwanuka" "Ki yi zamanki Lolo bari in kawo komai" Cewar Aisha data miƙe. Yauwa zaki ga abinci a kula saiki ɗakko" Ina faɗar haka na dawo da kallona kan Uzairu zuchiyata nace. To kai Uzairu zuchiyata sai yaushene batun auren naka, koko dai har yanzu baka gaji da yaudarar ba?" Dariya yayi yace. "Waɗannan matan geton da nake kulawa na data kawai nake farautowa a hannayensu. Ni kin ganni me aurena sai irin hajiyoyinnan waɗanda suka ci suka tara, ko wacce aka mutu aka bar mata dukiya. To na dai haɗu da biyu ɗaya a Abuja take, ɗayar kuma baturiyace ma ba'a najeriya take ba. Ana dai ta buga soyayya mai rabo ce zata ɗauka. Duk da hankalina yafi raja'a akan ita buturiyar dan tafi iya soyayya da kulawa da halama tafi ta Abujan kuɗi ma" Ai nan muka samu maudu'i ana cin abinci a tare anata tattaunawa shewarmu har tsakar gida sai hirarmu da nishaɗi muke yi. Wannan ya tuno mun da lokacin da duk muke gabansu Rakiya in muka zauna mazanmu da matanmu a tsakar gida akaita musu abun babu dama. Wata rana ma a dakalin ƙofar gida muke zama da daddare muita musu. Allah sarki rayuwa. Bayan mun kammala cin abinci Sama da yayi mana sallama yayi tafiyarahi. Su Aisha ma duk suka kama hanya muka rage daga Labbai, sai Adama, sai Rahama, da Uzairu zuchiyata sai kuma ni. Mu matan muna kitchen muna girkin abincin dare wajajen bayan la'asar kenan, Uzairu zuchiyata kuma sai shafa hoda yake yi yanata hotuna dan masifa. Labbai tace. "Lolo ɗazu taɗin su Sama da Uzairu zuchiyata ya ɗauke mana hankali bamu tattauna batun kama hayar da muka yi ba ni da Adama ba" Dama nayi shiru da albasa a hannuna da wuƙa ina tunanin shariarmu ta yau data gudana na jiyo muryar Labbai. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke. Duk dariya da walwalar da nake yi ƙasan ruhina ɗamfare yake da maganar shari'arnan kamar yadda bugun zuchiya yake dokawa haka shariar take zuchiyata. Ke dai bari Labbai abunne da yawa. Wai menene dalilin kama hayar amman?" Adama tace. "Ɗakin yayi mana kaɗan sosai. Kuma maigogul yazo musu da baƙi wai sati guda zasu yi a gidan fa. Ga fitintimun gidan ni wallahi bazanma iya zama ƙarƙashin iyayeba na wuce munzulin. Shine nace ma Labbai mu haɗa kuɗi kawai mu kama haya. Dama dai ko a gidan uban naka kake zaune kai zakaima kanka komai daidai da sabulun wanka kai zaka siya abunka. Kinji dalili muka kama ɗaki a gidan Hamidu" Gidan Hamidu kuma Adama? Kinsan fa ance akwai wasu mata da suke kawo maza gidan, bakwa tsoron kada a zarge ku kuma?" Labbai tace. "Hmm Lolo kenan gaskiya auren Babangida ya riga daya birkita miki ƙwaƙwalwarki a yadda na fuskanta. Dama mu kina ganin akwai ranar da zamu tsallake zagi ne? Mu gidan namu wanne irin maza ne basa kawo su Aisha gida, a wanne irin hotel da gidan rawan darene ba'a sanmu ba?" Fitowar Maman Sa'idu yasa na yafici Labbai tayi shiru. Ramadanne na hango yana tawowa kici_kici da kayan abinci ya kawo mun harda doya guda biyar a ƙulle. "Ga waɗannan kuɗin inji Baba Malam yace ki riƙe a hannunki" Hannu nasa na karɓa nayi mishi godiya ya juya abunshi. Kayan abincin na soma bubbuɗawa. Shinkafa, wake, taliya, makaroni, kuskus, garin tuwo, maggi, farin mai, manja, maggi, kifi, da kaji guda huɗu a yanke a gyare ga dubu talatin na cefane lallai Baba Malam mutumne harda ɓari. "Wallahi Lolo irin kyautatawar da wannan bawan Allah yake yi miki ko sai inga kamar baki kyauta ba da kike shari'a da ɗanshi" Adama tace da Labbai. "A_a Labbai Lolo ba zata zauna sabida uban mijinta ba. Shi kanshi ai yasan rashin mutuncin ɗanshi sarai bawai bai sani bane. Kina mancewa da abbuwan da akayi a baya ne? Me ɗaki shi yasan inda yake yi mishi yoyyo. Ke lolo juya namannan kada ya ƙone" Miƙewa nayi na duba naman ya ko soyu tumatur niƙakke da attaruhu da akbasa a cikinshi na juye a cikin naman da man na tsayar da miyar tunaturi ɗina. Daf magriba muka gama girki daidai shigowar su Mardiyya. Aɗɗa'u naga idanunshi sun yi jawur jikinshi duk shatin bulala. MRS BUKHARI Mu tara gobe in Allah ya nuna mana.
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA GOMA BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
INA MIƘA SAƘON GAISUWA A GAREKU MASOYA WANNAN LITTAFIN SAƘWANNINKU SUNA ISOMUN WALLAHI. YAWANKU YAFI ƘARFIN ACE ZANA SUNAYRNKU ZANYI A RUBUCE. INA MUKU FATAN ALKHAIRI.
WANNAN SHAFIN NAKU NE ƳAN COMMENT SECTION SAI DA KU ANA FAFATAWA MAIGOGUL YANA GAISUWA.
https://chat.whatsapp.com/Hpz6ravGdP1AxEMkXT65bt Assallamu alaikum sisters @zee Musa collection taxo muku da kayayyaki masu kyau da inganchi kamarsu shaddar lace atamfar kayan Yara Egypt abaya da kayan kitchen kuma akan farashin mai sauki💃🏽💃🏽 Kuma tanayin adashin kayayyaki domin bawa masu karamin karfin damar mallakar abubuwan cikin sauki 🤓kyeedai garzaya domin kiyi naki
Kuma tana tura Kaya KO ina cikin yarda Allah cikin aminche kyeedai garzaya domin jinkarin bayani
Location ;Kano state💃🏽💃🏽GA number wayar domin Karin bayanin 08029882667