Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 8
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 8: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 8. Ji kuke taratsatsa, take jini ya soma zuba kwalbar ta sameta a gefen kunnenta ta…
3,831 words
Ji kuke taratsatsa, take jini ya soma zuba kwalbar ta sameta a gefen kunnenta ta yankata sosai. "Mun shiga uku Maman Mardiyya zaki yi kisan kai" Cewar Maman Sa'idu. Ni kuwa dana ƙyalla idanu na hango kwalbar koka kola ai saina surota da sauri. Da Ƴar Shuwa tana tsaye tana cin ɗamarar faɗa, jini na zuba mata duk ya ɓata wajen. Ganina da wannan kwalba yasa ta fice a guje. "Wallahi kuyi ta kanku ƴan daba ne dukkansu" Matan maƙota suka runtuma suka bita a guje matan gidanne kaɗai suka tsaya sunata bani haƙuri. "Muna jiyota tana kiranki da boka kin asirce miji. Wannan ai ba ƙaramar magana bace. Yanzu fa da mai gidan yananan sai kiga in ba wani ikon Allahn ba sai kiga ya kama. Kishiya duk yadda kuke burinta ta ganka a ƙasa Allah dai ya kyauta" Nan suka gama surutansu suka bamu waje. Aisha ce ta gyara wajen da jini ya ɓata ina zaune ina huci. Aisha yaushe a gari zuwa ba sanarwa?" "Wallahi sabida zaman shari'arku ta gobe nazo. To naje gida naji Maigogul yana cewa shi bazai je kotun ba. Rakiya dai tace saita je yana bazata ba. Har Hauwa dasu Layuza wai zasu je." Baki kawai na taɓe ta kuntomun goyonta ta miƙo mun. Wuni guda muka yi dasu muna hirarmu duk da hankalina baya jikina ma sam wallahi. Saida suka ci abincin dare da na gama girkashi tun biyar na yamma. Suna fita sai ga su Mardiyya Ramadan ya dawo dasu gida. Ana magriba Babangida ya shigo da sallamarshi hakan yasa dole na miƙe nayi shigewata ciki. Ina jiyoshi yana cema Mardiyya ta zubo mishi abincin. Ina goge kaya ya leƙo. "Sabuwa meya haɗaki da maman Fati ta kirani tace wai kin fasa mata bayan kunne saida taje asibiti?" Kallonshi nayi bance uffan ba na maida hankalina kan gugar da nake yi. Shigowa yayi ya zauna a bakin gadona. "Sabuwa!!" Ya faɗa da wani irin taushin yaudara. Nasan yasan bazan amsaba shi yasa ma ya soma magana. "Ina dai ƙara roƙonki akan shari'arnan dai Sabuwa. Kima Allah Sabuwa ki janye wannan shari'ar Sabuwa ƴaƴanmu fa zamu jama abun faɗe, ki sani wannan abun bazai taɓa yi musu daɗi ba. Yanzu Sabuwa zaki so ace a kanki Baba Malam ya rabu da Malama Babba? To bari in ƙara faɗa miki duk da nasan kin sani. Baba Malam cewa yayi muddin alƙali yasa na rabu dake, to Malama Babba tasa a ranta tamkar shine ya rabu da'ita. Igiyar data sarƙe aurenku yace a haɗe take, ba za'a tsinka taki nata ya zauna ba. Ko yau ɗinnan naje dan in gana da Baba Malam amman yaƙi. Malama Babba tana cikin gida babu lafiya, ya hanani shiga cikin gidan ya haramtamun hakan. Yayu da ƙanne duk muna cikin damuwa, ga tsinuwa a kaina Sabuwa. Dan Allah ki zauna kiyi tunani dare ɗaya kike dashi" A sanyaye ya miƙe ya fice. Ni kuwa mamakine ya kamani. Ohh dama wannan dalilinne yasa Malama Babba take ganin zata siye mu dan ita ta cinma burinta ko, ni kuma ko oho. To ai kuwa saidai mu zama zawarawa dani da'ita shari'a babu gudu babu ja da baya wallahi. Gugar ma sai naji na kasa tsulum na haye gado nayi rigingine inata tubka da warwara.
Wayewar gari:. Yara na tafiya makaranta na shiga aikace_aikace shara wanke_wanke da wankin yara duk nayi. Na yi girki na ajjiye a kula dan bansan in mun tafi ƙarfe nawa zamu dawo ba. Tara na safe sai ga Adama da Rahama sun shigo. Babangida yana falo suka shigo. Yau dai ya amsa gaisuwarsu harma da tambayar yaransu. Dama a tsaye yake zai fita suna gama gaisawa ya fice. "Sabuwa jiya fa su Sa'a sukai ayari suka je gida wajen Rakiya da Maigogul. Bakiga kaɓakin arzkin da suka kai musu ba. Manja, maggi, shinkafa, taliya harda kuɗi. Abinda suka tattaunane bamu sani ba jiya ina gidan, amman Maigogul ya kironi waje." Jikina duk sai naji yayi tulus guiyoyina naji sun sare. Wayata ce ta shiga ƙara Barrister Ahmad Ahmad ne yake kirana. Jikina murus na ɗaga kana na saka a kunnena. "Assalamu alaikum. Sabuwa ya kamata ace nan da tara da rabi ki ƙaraso kotu kafin a shiga zama mu ɗan ƙara tattaunawa ko?" To barister yanzu ganinan fitowa" Kashe wayar nayi na dubi su Adama nace. Bari in ɗakko mayafina mu tafi lauyanane ya kirani" Mayafi da jakata na shiga na ɗakko muka haɗu muka fice kai tsaye babbar kotun cikin gari muka nufa. Mun shiga kotun tara da arba'in. Da Babangida na soma haɗa idanu suna zaune da abokanshi da wasu da ban sansu ba. Can gefe Malama Babba da Malama ƙarama ne a zaune suma harabar kotu dai ta cika har ƴan gidanmu ma naga sunzo harda Uzairu zuchiyata da Sama, Gaza dai ban ganshi ba. Keɓewa muka yi da lauyana. "Inaso ki nutsu kada ki ruɗe duk abinda alƙali ya tambayeki ki nutsu ki amsa mishi a tsanake. Kuma amsa ɗaya ake bayarwa ko sau nawa za'a tambayeki kada ki canja daidai da kalma." Kai na ɗaga mishi kawai ni magana ma na kasa. Gashi kusan duk harabar kotun ni suke kallo face ragowar mutanen da suma muka shigo muka taddasu da basu sanni ba ban sansu ba. "Akwai wani sabon labarine?' E akwai barister" Nan na zaiyana mishi yadda muka yi da Babangida jiya. Da labarin da su Adama suka kawo mun yanzu" "Da kyau waɗannan maganganun suna da matuƙar amfani zamu adanasu da akwai gaɓar da zamu sokota. Yanzu muje an soma shiga kotu" Wucewa yayi ya barni, ni kuma na koma wajensu Adama. "Mu jenku Sabuwa anata shiga mu muna tsaye" Inji Adama kenan. Sai da su Babangida suka wuce mu kafin muka bi bayansu zuwa cikin kotun. Kotu dai a mugun cike take yau maƙil cikin ƙanƙanin lokaci kotun ta cika har babu wajen zama dole wasu suka tsaya daga waje, ciki harda Hamida da Amaryar Babangida Ƴar Shuwa kam ita da uwarta summa riga mu shiga kunnenta naɗe da audiga. Da halama ba shari'armu kaɗai za'ayi ba. Dan duk inda na waiga sai inga bansan mutanen ba dan sun fimu yawa sosai. Karfe goma dot alƙali ya shigo ta wata karamar kofa. Duk muka zabura muka tashi, bamu zauna ba har saida alƙali ya zauna kana." Mai karanta ƙarane ya miƙe da takadda a hannunshi ya soma jawabi kamar haka. ", Ayau ashirin da biyu ga watan maris ne zamu saurari ƙara mai lamba ɗari da shittin. Ƙarar da Halima ta shigar tana tuhumar mijinta Baballe da handame mata kuɗaɗen gadonta tare da siyar mata da gidanta data gada." Ashe ba shari'armu za'a soma ba. Kai kawai na girgiza maza da yawa son zuchiyoyinsu kawai suka sani." Alƙali ya ɗago kai yace. "Lauyan Halima in yana kusa ya gabatar da kanshi." Wani lauyane ya miƙe tare da cewa. "Cike da girmawa ya mai Shari'a sunana Barrister Buhari Ladan nine lauyan wacce ta yi kara wato Halima. Nagode ya mai Shari'a. Yana zama wani lauya ya miƙe shima yace "Sunana barrister Ibrahim Abubakar nine lauyan wanda ake ƙara wato Baballe. Nagode mai Shari'a." Alƙali yace. "Ko lauyan wacce take ƙara yana da shimfiɗa da zai ma kotu?" A zabure da zafin nama ya tashi. "My lord Halima matar Baballe ce suna da yara huɗu tare dukka mata. Mahaifinta ya rasune shekarar biyu da suka wuce ya rasu ya barma yaranshi su Halima kadarori da ruwan dukiya. Jinƙai irin na mace akan mijinta da Halima ta nuna ma Baballe shine. Da aka raba aka bata gadonta na gida da ruwan kuɗi miliyon bakwai. Kuskuren da tayi saita damƙama Baballe miliyan biyar a hannunshi tace ya ja jari dasu. Kasancewar yana taya abokinshi saida motoci saita bashi shawarar me zai hana ya dinga bin abokin nashi zuwa kwatano suna ɗakko mota tare tuwaris. Akan wannan dalilin Halima ta ba Baballle kuɗinta kuma ba kyauta ba da sharaɗin zasu dinga raba duk wata riba da aka samu harya gama biyanta kuɗinta. My lord kuɗinta basu fito ba, a tsakaninta da Baballe babu mutuntawa daga karshe da kuɗinta yayi aurenshi ya kama ƙatotin gida ya saka amaryarshi, ya sai motar zagaya gari da'ita. Ita Halima da yaranta ya barsu a ƙunci. Hakan baiyi mishi ba kuma kwatsam Halima na zaune da yamma a gidanta ranar talata biyar ga wannan watan. Sai taga Baballe da dillalai masu duba gida. Data tambayeshi lafiya saiya kada baki yace da'ita ya saida gidan harya amshe kuɗinshi dan haka shi ya saketa ta tattare kayanta ta bar gidan. Akan wannan rashin adalcin da Baballe yayi ma Halima ta shigar dashi ƙara sabida ƙila ya amta da hukuma. Ina neman wannan kotu mai alfarma data dubi halima ta kwato mata hakkinta. Nagode mai Shari'a " Kai na girgiza ina kwatanta girman wautar da Halima tayi. Ko da yake bana kira hakan da wauta ba, ita a tunaninta shine mijinta shine makwafin ubanta a wannan lokacin, kuma dashi kaɗai ta amince shi yasa ta danƙa mishi ragamar dukiyar tata. Shi kuma ya tata mata wannan rashin mutuncin. Muryar alkaline ya katse mun tunanina. "Lauya mai kare wanda ake ƙara yana da abun cewa ne?" "Ya mai girma mai Shari'a ina da ja akan dukkan abinda lauyan wacce tayi ƙara ya faɗa a matsayin shinfiɗa. Sannan ya kamata ya iya harshenshi wajen tabbatar da laifi akan wanda ake tuhuma, domin zargine ba tabbas" Alƙali yace. "Barister Buhari Ladan a kiyaye jingina laifi kai tsaye ba tare da an tabbatar ba." Lauyan wanda ake ƙara yace. "My lord Halima matar Baballe bata ba Baballe ko sisin kwabonta ba. Asalima shi da kanshi ya roƙi ta taimaka mishi da jari taƙi. Kowa yasan Baballe mutum ne tsayayye ba mai macacciyar zuchiya ba. Babu ko sisin kwabon Halima a hannunshi. Batun gida da take ikrarin ya siyar ya saketa. Ya mai girma mai Shari'a itace ta siyar da abinta sabida kishin auren da mijinta yayi wai itama sai an kama mata hayar tabkeken gida kamar yadda ya kamama Amarya. A wannan gaɓarne ya saketa kuma Allah ya baka yawan rai yanzu haka a cikin kotunnan ya dawo da matarshi. Nagode my lord " Halima dai sai share hawayenta take a kusa da juna muke inaji tana sambatu masu zafi da raɗaɗi. "Bayan sauraren ƙara da wannan kotu tayi, da shimfiɗa da lauyoyin ɓangare biyu suka yi. Wannan kotu ta ɗage ƙararnan zuwa ashirin da biyu ga wata na gaba. Tana buƙatar lauyoyi na ɓangarorin da su kawo hujjojinsu masu ƙarfi domin kotu taci gaba da saurarensu. Sai ƙara na gaba kuma" Mai karanto ƙara da ake kiranshi da turanci ko mene nadai kasa haɗe turanci amman ai kun ganeshi ko? Saiya miƙe yace. "Sai ƙara mai lamba ɗari da sittin da ɗaya wacce Sabuwa ta maka mijinta mai suna Babangida a kotu bisa tana neman ya saketa sakamakon kasa cika hakkokinta na Aure.' Alƙali yayi rubutu yayi rubutu kana yace. "Zamu je hutu na rabin awa in mun dawo saimu saurari ƙaran." Wannan guduma ya buga, yabi ta ƙofar baya ya fice. Nan take kotu ta ɗauki hayaniya Ƴan uwan Halima suka shiga tsinema Baballe, da wannan muka runtuma zuwa wajen kotu. A wajenne muka tarar da Baba Malam, da su Rakiya da Maigogul suna zazzaune. Gefe guda na zauna nayi tagumi. Baba Malam ne shi da Barister Ahmad Ahmad suka karaso inda nake. Gaishe da Baba Malam nayi da girmamawa ya amsa kamar kullum. "Sabuwa kar ki karaya naga halamun mutuwar jiki a tattare dake. Zan baki duk gudunmawar data dace. Dangane da shirin da Babangida da gyatumarshi suke yi bazai yi tasiri ba da izinin Allah. Akan son zuchiyoyinsu da cimma manufofinsu kawai suke. Kai na gyaɗa nace. Allah ya bamu nasara Nagode sosai Baba Malam" Maigogul ya karaso wajen a hargitse. "Lolo inaso zanyi magana dake ta ƙarshe kafin ayi zaman kotunnan. Gara da Allah yasa kuka fito' Magana zanyi, muka haɗa idanu da Baba Malam ya girgiza mun kai halamar kada in musa mishi. Jiki ba laka na miƙe nabi bayanshi har zuwa wajensu Rakiya da Hauwa, dasu Adama. "Lolo ashe ba zaki ji maganarmu ba kin dage sai kin tozarta uban ƴaƴanki ke akan daidai kike ne. Wanne irin iskancine baki tata a gabanmu ba. Kin dace kin auri malami ɗan gidan malamai a kab ƴan uwanki babu wacce baki fita dace ba. Ki duba irin mazan da suke aure daga ƴan iska sai ƴan abu ta kazan uba. Adama zawarci, Labbai zawarci, ƙannenku duk zawarci Salaha, da A'isha, da Rahama ne fa kaɗai suke zaman Aure. A ɗakin Hauwa kuwa Layuza ce kaɗai sai Qamriyya da aka kawo sadakinta za'ayi bikin. Dame kike so inji Lolo. So kike ki tozarta kanki ba wani abun ba. In Dai baki janye wannan Shari'ar ba, ki sani ko Babangida ya sakeki ba zaki zauna mun a gida ba saidai ki kama haya kamar yadda su Adama akace sun kama haya suna shirin tarewa. ni dai na faɗa miki" Tunda maigogul ya soma maganarshi nayi ƙuri ina kallon waje guda. Rakiya itama ta kama taita ragargazata da yi mun tone tonen abubbuwan da bana ko ƙaunar tunosu ma. "Lolo kiyi ma kanki faɗa ato. Duk wuyar gidan Babangida kinsan yafi gidan ubanki. Ba'a rageki da ci da sha ba, suturarnan kina dasu yaranki suna karatunsu. Duk abinda kika samu mu shi muka rasa muka zauna har saida aka koremu muka haƙura. Yaranmu duk sun kama irin layinmu na bin maza baka isa ka hanasu ba sabida babu abinci, babu sutura yaya zasu yi suyi rayuwarma.' Inji Adama kenan. Ina tsaye nayi shiru har lokacin shiga kotu yayi. Bance musu kuci kanku ba har suka gama. Kai kawai nasa na wuce cikin kotu ko gani banayi sosai sabida jiri. Kotu ta cika da dangina dana Babangida, harma da ƴan kallo waɗanda ba'a fiye rasasu a kotu ba. "Lauyoyin ɓangare biyu su gabatar da kansu. Barister Ahmad Ahmad ne ya tashi ya gabatar da kanshi. Kafin lauyan Babangida ya miƙe. "Sunana barrister Abubakar Shagari nine lauyan wanda ake ƙara tare dani akwai abokiiyar aikina wanda tare zamu yi aiki. Nagode my lord." Yana zama abun mamaki sai wata lauya mace ta miƙe. "Sunana barrister Asabe madaki. Nagode my lord." Kai na gyaɗa wato su Babangida a shirye suke lauyoyi har biyu? Allah ya bamu lafiya. "Ko lauyan wacce tayi ƙara yana da shimfiɗar da zaima kotu?" Gabana ya faɗi ras. Barister Ahmad Ahmad ya miƙe yace. "My lord Sabuwa ta shigar da ƙaran mijinta Babangida ne a bisa dalilai masu yawa kamar haka. Na farko Babangida baya ciyar da Sabuwa da ƴaƴanta. Na biyu baya biya ma yaranshi kuɗin makaranta. Hatta da sutura baya musu, bai damu da lafiyarsu ba. Uwa uba ya jingine Sabuwa tsawon lokaci baya sauke hakkin daya rataya a kanshi na mu'amalar Aure. Sai dai duk ranar da yaji sha'awarta yazo ya nemeta ta hanyar ƙarfi. Babangida yasha ya doki Sabuwa ya hakke mata tamkar namijin da ke ma yarinya fyaɗe. Daga baya ma ya ajjiyeta a gefe ta fita daga jerin matanshi a zahiri saidai a baɗini matarshi ce. Cin mutunci da cin zarafin iyayenta babu wanda bayayi mata. Da wannan ne Sabuwa taga cutuwar tayi yawa take roƙon wannan kotu mai alfarma data kwato mata hakkinta. Sannan ko a musulunci Babangida bai sauke hakkin da Allah ya rataya mishi akan iyalinshi ba. Ba'a aure babu abubuwannan dana lissafo. Nagode my lord" Wasu siraran hawayene suka shiga aikin yawo a kumatukana. Barister Asabe madaki ce ta miƙe. "My lord duk abubbuwan da lauyan Sabuwa ya faɗa zamu iya kiranshi a ƙage. Sabida Babangida yana ciyar da Sabuwa yana shayar da'ita kuma yara suna zuwa makatanta. A yanzu haka ma suna makaranta. Ya mai Shari'a Babangida yana neman hakkinshi a wajen Sabuwa sakamakon bin maza da take yi da aurenshi. Malama Sabuwa har a hotel take kwana da maza da aure a kanta. Akwai sanda Babangida ya kamata ita da Khalid wanda ya kasance tsohon saurayin ita Sabuwa ne tun tana budurwa. Sabuwa a titi tayi dambe da mijinta Babangida sabida kawai ya kama Khalid da dambe. Wanta kuma ya sari Babangida a kafaɗa shi da sabuwa suka haɗu sukaita dukanshi. A ta dalilin wannan saida Babangida yayi fin sati uku a asibiti, ga rauni a kafaɗarshi ga karaya duk a hannu ɗaya. Ya mai girma mai Shari'a Babangida yana neman a fitar mishi da hakkinshi." Zama tayi. Ni kuwa sai haɗiyar zuchiya nake yi zufa na keto mun. Barister Ahmad Ahmad ne yace. "My lord ina da ja. Lauyan wanda ake ƙara kwatakwata ya sauka akan layin shari'ar da muke yi . In tuhumarta Babangida yake son yi ƙara zai shigar shima domin a kwato mishi hakkinshi. Yanzu muna magana ne akan Sabuwa da ta kawo karan Babangida da tana son ya saketa" "Ina da ja ya mai Shari'a " Cewar baristar Abubakar Ibrahim daya miƙe. Alƙali ya bashi damar yin Magana "My lord Batister Asabe madaki tana kan layin shati'a ta yiwu sabida halin rashin kamun kai da bin mazan banza ne yasa Babangida ya watsar da lamarin Sabuwa. Tunda yasan tana bin maza taya zaici gaba da ɗaukar ɗawainiyarsu. Ya mai girma mai Shari'a wannan shari'ar tana da girma muna buƙatar a bamu lokaci domin gudanar da binciken daya kamata a tsanake. Sannan a duba wanda ake tuhuma bashi da cikakkiyar lafiya kullum yana zuruftun zuwa asibiti wankin ciwone, asalima kwananshi uku da aka sallamoshi daga asibiti. Muna buƙatar lokaci mai tsawo. Nagode my lord " Bayan alƙali yayi rubutu, yayi rubutu saiya ɗago yace. "Ko lauyan wacce take ƙara yana da ƙorafi?" Miƙewa yayi yace. "E akwai ya mai girma mai Shari'a. Muna roƙon wannan kotu mai alfarma da kada taja wannan shari'ar domin Sabuwa tana cikin damuwa sosai. Sannan mara lafiya tunda yana iya zuwa asibiti zai iya halartar zaman kotu. Ƙorafina kenan nagode my lord" Tunda lauyoyin Babangida suka soma magana nake tsiyayar hawaye babu ƙaƙƙautawa. Zuchiyata har tsalle take yi mun tsabar bugawa. Dana waiga na kalli ƴan uwan Babangida matan da Malama Babba saina ga suna cike da farin ciki. Ƴan uwanshi maza kuma girgiza kai kawai mafi akasarinsu suke yi. Dubana na mayar kan Baba Malam wanda na kasa fuskantar a cikin irin yanayin da yake. Ta ɓangarensu Maigogul sai naga tamkar sunfi su Malama Babba ma farin ciki. Su Adama kuwa ko wacce ranta a ɓace yake da dukkan halama suna tayani jin zafin abinda ke faruwane. "Bayan sauraren ƙara da wannan kotu mai alfarma tayi wannan kotu ta ɗage wannan ƙara izuwa ɗaya ga watan Mayu. La'akari da shi Babangida da ake tuhuma bashi da ishasshiyar lafiya. Kotu ta bashi dama yaje yayi jinya kafin ya dawo aci gaba da sauraren wannan shari'ar. Sannan tuhumar da Babangida yake ma Sabuwa bai shafi shari'ar da muke yi ba. In hakan suke so sai ya shigar da sabon ƙorafi. A zama nabiyi lauyoyin ɓangare biyun zamu basu damar soma gabatar da hujjojinsu." Ya kwaɗa gudumar kotu duk aka miƙe. Ni kam saida Adama ta tallafamun kafin na iya tashi. Bana ko ganin gabana Adamace ta zame mun garkuwa. Da muka fito harabar kotun lauyana da Baba Malam ne suka tareni. "Sabuwa ki kwantar da hankalinki ki dena ɗaga ma kanki hankali. Ko wata nawa aka saka na sake zaman kotu zaizo ne. Kuma duk yadda azzaluman lauyoyi suka kai da iya sharri dole za'a kai ƙarshen wannan shari'ar dole. Barister Ahmad zai nemo wani lauyan suma su zama su biyu. Shari'a yanzune za'a soma. Adama ki daure tunda naji labarin mutuwar aurenki kije ki zauna da Sabuwa ko dan ɗebe mata kewa. Ramadan anjima zan aikoshi da kuɗin cefane da kayan abinci ya kawo muku." Godiya nayi mishi kawai Sama da Uzairu zuchiyata ne suka ƙaraso inda muke tsaye, su Maigogul kuwa suna keɓe da Babangida. "Lolo wannan tonon sililin har ina, kinji fa abinda lauyan mijinki yake cewa a kotu. Wai hotel_hotel kike zuwa mu'amala da mazan banza. Wai shine nace wai dama baku watsar da rayuwar da kuka gudanar a baya ba. In da anji talaucine ya sakaku kaucewa yanzu da kike gidan aure kuma me yasa kika kauce? Adama kinsan Allah nakai zuchiyata nesa ne da muna fitowa zan cukume Babangida ayi wacce za'ayi. Allah yasa Gaza bayanan yana canma a kulle me yau da anyi batacciya.' Adama tace. "Sama duk fa abinda yake faruwa Sabuwa fa akan daidai take. Abinda kaji lauya ya faɗa sharrine. Ina Khalid tsohon saurayin Lolo?" Ta tambayeshi Uzairu zuchiyata yace. "Wannan baban nacin zaki ce mun" Adama tayi dariya tace. "Shifa. To a asibitin da ita Lolo take kai yaranta yake ranar taje asibiti saiya ganta ya rago mata hanya ya kawota gida. A bakin titi a cikin mota fa ya gansu shine yayi mata wannan sharrin. Dake shima ɗan iskane shi yasa tunaninshi ya tafi can. Mu faɗama kanmu gaskiya Babangida fa taceccen ɗan duniya ne fa. Maigogul da Rakiya suma kuɗi suke yima. Mu bi bayan ƴar uwarmu kawai Sama" Kai Sama ya girgiza yace. "Wallahi hakane wai duk basu suka ɓalɓanta rayuwarmu ba, sun haifemu sun watsar damu muna gantali a titi ba. Ai shi yasa ni aure ma zanyi ciniki harya faɗa Lolo muje gidan naki sai mu tattauna acan ance kun sake gida ana muku gyara a wancan gidan naku." Duk wannan bayanin da yake yi zaku ce faɗa akeyi yanayi yana ihu da wauware hannaye. Ɗunguma muka yi dukkanmu muka nufi gidana. A bakin titi wajen samun abun hawa muka tarar da su Sa'a suna tsaye kome suke jira ohon musu, sai wani kallon ƙyama suke yi mana sabida dattin da Sama yayi. Niko a raina ina faɗin ai kallon ƙyamar auroni ya kusan zuwa ƙarshe tare da Malama zamu zama zaurawa. Muna tsaye motar da zata ɗebesu ta fito suka shige,motarsu Baba Malam na binsu, sai ta su Malama Babba, sai ta samarin gidan. Mu kuma muna dai tsaye duk abin hawan da muka tare sai suce banan zasu yi ba. Daga ƙarshe sai hawa muka yi muka rage tafiyar muka sake shiga wani abun hawan. Su Rakiya tun muna neman abun hawa suka zo suka wuce mu a mota Maigogul ke tuƙin motar wata haɗaɗɗiyar mota ko kallonmu shi kan baiyi ba ga kiɗa ya sakar musu Rakiya mandiya tana gaban mota. Da sallama muka shiga gida. MRS BUKHARI
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA TARA BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Assalamualaikum brkanku d warhaka hmmmm Wani kaya sai amale tohhh mata masu capacity matan kwarai 🥰🥰🥰ga ramlex Mai kayan daa kayan buje 😀😀😀😀akwae Package na uwargida Package na amarya Package na mejego Tsimi baure Tsimi magarya Hadin tattabara Hadin kaxa Hadin ciccibi Gumban Madara Gumban ridi Gumban waken soya Karin dandano Xuman matsi Manta uwa Hadin mallaka Hadin bita xaixai Hadin tsuguno hmmmmm gareku mata akwae adashen gata duk sati 2k hadi Mai kyau xaayi muku duk Mai bukata ga no 07069722234 ko 07044503983 snnn dn Neman Karin bayani ku tuntubi wnnn layukan 🥰🥰🥰🥰🥰
BABANGIDA:.