Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 7

Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 7

Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 7: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 7. Babangida yana zaune a kujera mazaunin mutum uku ya miƙe kafarshi a kujerar ga filo…

3,970 words

Babangida yana zaune a kujera mazaunin mutum uku ya miƙe kafarshi a kujerar ga filo an jingina mishi a wajen hannun kujerar. Matanshi duk suna ɗakin ko wacce tana harɗe a kujera rannan nasu kicin _ kicin. 1 sitter na samu na zauna bance da kowa komai ba, babu wanda yace dani ƙala. Yara suka wuce suka duba Babangida sai wani fara'a yake yi musu ta gaibu, su kuma dake ma basu sababa Sam sun kasa sakewa dashi. Mardiyya kuje ku kwanta nima ina zuwa" Tashi suka yi suka fice, na dawo da dubana wajen Babangida nace. Kasa anyi kirana, gani to" Murmusawa yayi tare da cewa. "Lolo kenan. Hakane nasa an kiraki domin ina da magana uku da nake son mu tattauna muhimmai, kuma ya shafi iyalin gidan baki ɗaya" Murmushin na mayar mishi ina ƙare mishi kallo. Wai yau ni Babangida yake ma magana da taushi? In baka mutu ba zaka sha kallo shegiya duniya. Katseni yayi ta hanyar cewa. "Ga Ramatu nan matatace da Ɗanmu ɗaya, sai abinda yake cikinta. A ƙa'ida ba dole bane in zan yi aure saina sanar daku ba. Sabida manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ma yayi aure ba tare daya sanar ma iyalanshi ba, sabida ba laifi bane. Ganin damane, amman ku mata kun ɗauka ma cin amanane yin hakan. Wannan laa ba huruminku bane. Wannan kenan, gata nan yanzu kun santa. Ramatu a iyakar zaman satikan da kika yi damu na san kin riga kin gane lissafin abokan zamanki. Ma'ana wacece babba wacece mabi da'ita ko?" Ya kalli Ramatu. A gatsine tace. "Zan dai gane in ka ganar dani. Taya ma zan gane da kaina alhalin matan naka girman kai garesu, tunda nazo suke kishi dani mun kasa samun daidaito. " Ƴar Shuwa ce ta ɗan ja tsaki, hakan sai ya bani murmushin da sautinshi yasa muka haɗa idanu da Ƴar Shuwa harma dan tsokana nayi na ɗaga mata kira. Ita tasan me nake nufi sarai, a cikin shika_shikan rashin arzikin Babangida bata ga komai ba. "To kinga wannan itace Sabuwa matata ta fari kenan uwar manyan yarana da suka fita yanzu itace mukai auren lalle. Sai Hamida gata kin ganta ita ke bi mata, sai maman Fati wacce ta kasance Amarya kafin zuwanki. Da fatan kin fahimta ko?" "Na fahimta." To sai batu na biyu shine yafi mahimmanci. Kunga wannan gidan da muka dawo akace muku za'ayi gyara a wancan namun? To zance na gaskiya ba hakan bane. Anan zamu ci gaba da zama wannan rayuwar da muka yi ta a baya ta wuce sai dai mu shiga sabon nema in da rabo sai a samu arzikin da yafi na da" Da mamaki duk muke kallonshi, duk da ni mamakina ƙalilinne domin bai shafeni ba. Ta wani ɓangaren naji daɗin jin wannan labari gaya. "Ban gane me kake nufi ba Jannaty. Kana nufin karayar arziki ka samu ko kuma me kake nufi da a wannan tsukukun gidan da layin zamu ci gaba da zama. Aikin ka fa, kamfaninka fa motata kuma da aka karɓa?" Tunda kuka ji Jannaty ai kunsan wake magana. Duk tabi ta ruɗe dake dama ba zaman auren bane ya kawota ba, gashi na santa da idon cin nera. Ai wallahi bata ga komai ba tukunna. Hamida tace. "Baban Usama dan Allah kai mana bayani meke faruwa mu iyalanka ne yana da kyau musan halin da kake ciki, sannan mu san ya akayi dukiyar taka ta salwanta dare ɗaya?" Idanunshi suka kaɗa sukai jawur dasu. "A halin yanzu iyakar abinda zaku iya samu kenan. Abubuwa da yawa sun cunkushemun tunanina. Amman ku daure kayan abincin da kuke dasu ku jalauta tunda kunga ba lafiya bace dani balle in fita ko aikin ƙarfine in samu inyi ba. Kowacce ta tattala na hannunta." Amarya Hala tace. "Allah ya rufa asiri ya mayar da arziki. Zamu yi haƙuri da sauyin rayuwar in sha Allah " Ƴar Shuwa ta wani harareta. Ni dai narasa dalilin da yasa Babangida ya zaunar dani, duk abinda yake faɗe banji ta yadda suka shafeni ba. A tunanina ma takaddata zai bani wallahi. Magana ta uku ta ƙarshe shine yau na dawo zan soma rabon kwana daga ɗakin Sabuwa tunda itace babba" Dukkansu su ukun suka ce . "Me?" Hamida nan ta shiga sababin itace da kwana wallahi ba za'ai mata jure ba. "Sannan da kake cewa a ɗakinta zaka soma rabon kwana da can ba da bakinta tace ta sallamar ba. Matar da ta makaka a kotu, ka kamata da wani namijin daban har" "Ke Hamida dakata da kalamanki haka. Ba nazo dan muita tattauna magana bane. Na sanar muku ne dan ku sani. Da kike cewa ta sarayar da kwanan nata, to ai ba ita take aurena ba, a bayan ma ganin damanane ba juyani akeyi ba. Mata baku san da usulubin da zaku yi magana da miji ba. Haba dan Allah dame zanji ne" Da faɗa yake maganar. Ƴar Shuwa kuwa ƙuri tayi kawai tana jijjiga kanta da halama ta shiga ruɗanine shi yasa tayi shiru. Miƙewa nayi na dubeshi sai huci yake yi kamar kumurci nace. Allah ya mayar da sabon arziki na halal. Batun rabon kwana ma karma ka ɗaura ma kanka jarfa. Ai yanzu bana cikin jerin matanka ma dan haka kayi zamanka a tsakanin matan so. Ni zaman Baba Malam nake yi ai ka sani" Hanyar waje na nufa sai ji nayi yace. "Kina nufin shi kike aure kenan ko yaya?" Juyowa nayi na ƙare mishi kallo tsab nace. Babangida kacigari kenan in shi nake aure ai kafi kowa sani. Na yi ficewata.

Babangida:.

Uwarɗakin Hamida ya shige fuu ya shiga neman wayarshi data Sabuwa. Ƴar Shuwa tayi tsaki tace. "Aikin banza aikin hofi" Tayi ficewarta falo ya rage babu kowa ko wacce tayi ɗakinta tana ta kaikawo tare da jujjuya al'amura. Hamida tabi Babangida ciki, a lokacin yaga wayoyin harya saka a aljihu zai fito Hamida ta shigo. "Nifa babu inda zaka je. Damme zaka raba mana kwana da matar da take bin maza kalan kaje ka ɗakko cuta ka saka mana" Kallonta yayi yana nazari har zaiyi magana wata zuchiyar ta kwaɓeshi. Sai kawai yasa kai ya fice yana tafe a hankali yana sake karema gidan da tsarin ɗakunan kallo har ya iso ƙofar ɗakin Sabuwa. Daya tura sai yaci sa'a a buɗe ƙofar take. Saida ya shiga yana ƙoƙarin saka sakata saiya fahimci wajen saka sakatar ne baya riƙe sakatar ya lalace. Sai kitchen ya fito ya ɗakko kujerar tsugunno ta mata ya shiga ya tokare ƙofar da'ita. Wuta yasa hannu ya kunna haske ya gauraye falon ya shiga ƙarema falon kallo, me yake kallo tunanin me yake yi oho shima bazai iya cewa gashi ba. Yadai san tunda zaman kotunnan ya matso yake jin faɗuwar gaba duk da yana da riƙaƙƙun makiran lauyoyin da ya tabbatar sai Sabuwa ta raina kanta. Amma dukka haka bai samu nutsuwa ba. Gashi hankalinshi na kan ya duba wayar Sabuwa yaga da maza nawa take mu'amala sannan shi wancan Khalid ɗin sau nawa ya kwanta mishi da mata. Idanunshi ya rufe yana huci wani irin baƙin kishi na turniƙeshi. A tsanake ya leƙa ɗakin yara ya ga su Aminu ne kaɗai a ciki. "Wato su Mardiyya suna ciki tare da Sabuwa kenan?' Sai ya nufi koridon da zai sadashi da ɗakin Sabuwa. Tun daga ƙofar koridon yake jiyo shewar Sabuwa da yaran. Dab da ƙofar ya tsaya a lokacin Mardiyya tana faɗama Sabuwa sunan saurayinta. "Sunanshi Haladu yace mun. Amman babbane, kuma yace mini yana da mata yaranyarshi ɗaya." Idanu Babangida ya zare tare da jijjiga kai. "To amman ke kina sonshi ne?" Ya jiyo muryar Sabuwa tana tambayarta. Ƙuri yayi ya sake baza kunnuwa dan son jin me zata ce. "Ina son shi ni tsoron auren me mata nake yi, dan gudun kada watarana abinda Baba yayi miki a rama a kaina. Ummi ance duk irin zaluntar mata da miji zaiyi akan ƴaƴanshi ake ramawa. Kuma shima Baba yasan da hakan. Ƙirji Babangida ya dafe tare da runtse idanunshi yana jin tamkar ya faɗi ya zube tsabar tashin hankali. "Mardiyya wannan gaskiya ne. Amman in sha Allah abinda Babanku yayi mun bazai sauka a kanku ba. Ina binku da adda,a babu dare babu rana. Sannan ki sani ko wanne bawa da ƙaddararshi shima mahaifinku ki dinga yi mishi adda'a sai kiga komai ya zama labari. In dai yayi miki ki bashi izinin yazo yaga Babanki ayi magana a san da zamanshi. Da kike cewa bakya son kishiya ai zaki iya auren saurayi yayo miki kishiyoyi ma daga baya. Ni ɗin ai ni Babanki ya soma aure daga baya ne ya auro ragowar matan daya aura. Bakya ganin har Aminiyata ya aura, ba gashi tana zaune harda rabon haihuwa a tsakaninsu ba?" Cikin dauriya da rashin guiwa Babangida ya tura ƙofar ya shiga da sallama. Tsorata dukkansu suka yi"

SABUWA:.

Mamakine ya kamani to ta ina Babangida ya shigo, a iyakar sanina ni na saka sakata da hannuna. A sanyaye kome ya sanyayashi yace. "Mardiyya ke da Malama ku ɗauki katifarku kuje falo ku kwanta" "A_a Babangida ka koma ɗakin matanka ni wallahi ba zaka kwana mun a ɗaki ba.' Ya wani kalleni yana mun nuni da yara. Yaran da a gabansu babu samfurin zagi da cin zarafin da ba yayi mun a gabansu ba "To naji su jirani a falo inaso muyi magana ne dake dan Allah ina neman wannan " Ni dai bance uffan ba, Mardiyya ta kama Malama suka fice. A durowar gefen gado ya zauna, yayi shiru, ni kuma ina ƙarshen gado na jingina kaina da fuskar gadon babu ɗan kwali a kaina sai doguwar rigar bacci ba mai sharara ba, kuma ba mai santsi ba cotton. "Sabuwa dan Allah ina roƙon ki arziki ki janye wannan ƙarar da kika shigar ki dubeni ki ceceni. Ni da kike ganina ina buƙatarki Sabuwa hannuna bazai iya sakin ki ba. So kike tsinuwar mahaifina ta hau kainane Sabuwa. Kinfa san da ydda mukai Aure sanadiyyarki har gobe Baba Malam baya shiri dani, watso mun kayana yayi kinsan komai. Bayan anyi aurenmu yace muddin na sakeki bai yafe mun ba, kuma zai saki malama Babba. To Sabuwa ko dan yaranmu ashe ba zaki ji mun tsoron tsinuwar mahaifina ba?" Iko sai Allah wai kunji yadda Babangida yake yi da muryarshi kuwa? Hmmm ni kuwa tunda ya soma maganarnan ko gezau banyi ba. Ai babu soyayya a tsakaninmu, yana riƙe da igiyar aurenne domin gudun bakin Baba Malam, ba dan yana son yaci gaba da riƙeni a matsayin matarshi bane. Sannan bazai so yayi silar mutuwar auren Malama ba. Wannan dalilin yasa Malama Babba take tunanin zata siyi su Maigogul da kuɗi. Ni kuma a wannan karon ko bola Babangida zai hau ƙarewar tsinuwa wallahi saiya sakeni. Harya huta yaci gaba da maganarshi, banko kalli banzan ba. "Nayi miki alƙawarin zaki same ni a yadda kike so. Zan gyara abinda na ɓata. Sabuwa nasan na kai ki bango ne. Ki daure ki karɓi tubana dan Allah Sabuwa kiyi hakuri" Ji nake dan baƙin ciki kamar in dira a wuyan Babangida wallahi. wai me maza suka ɗauki mace ne, tambayarku nake yi maza me kuka ɗauke mu? Ƴan iska marasa tunani ko? Yanzu shi Babangida a nashi tunanin da hankalin maganganunshi sune zasui tasiri inci gaba da rayuwa dashi? Ai wallahi na gama har abada. Miƙewa nayi na lalubi hulata na saka na nufi hanyar fita in bar mishi ɗakin ma gudun kar inyi kuka yaga wallena. "Sabuwa dan Allah ki tsaya karki fita ki dawo. Ni zan fita ku yi kwanciyarku, ni falo ma ya isheni sabuwa" Tsaye nayi cak dan ko motsi naki yi. Da yayi magana sai inji wani ƙududu yaimun tsaye a maƙoshina. Sum_sum ya fita, harya tafi ya dawo. "Batun saurayin da yake neman Mardiyya kuma Tun wuri ta faɗa mishi tana da wanda zata aura. Ai kema kinsan waye mijinta tun tana ƙasan mararki. Amman a hakan kike son ki bata ƙofar gabatar mun da wani sabida son rikici." Dariya nayi ƴar guntuwa. Shewar dila kake yi. Bama ɗan Sa'a ba kab zuriyarku babu wanda zan amince in bashi auren Mardiyya balle kuma Ɗan wajen Sa'a matar da tafi ƙaunar mutuwata. Bafa mardiyya kaɗai ba yarana ba zasu taɓa aure a cikin haularku ba" Ƙur yayi yana wani bina da kallon maita irinna mayun harijan maza. "Sabida ke kaɗai kika haifeta, ko kuma ba ni bane ubanta Khalid ne ko? " Duk yadda kace, in ka bar mishi ai zai" "Sabuwa!!!" Ya faɗa da ƙarfi saida na razana nayi baya. Ga hannunshi ya ɗaga kamar zai dokeni. Take idanunshi suka tara ruwan ƙwalla na zallan kishi jikinshi yana rawa a hankali ko me ya tuno oho sai naga ya sauke hannun ya juya ya nufi falo, da ƙyar yake jan ƙafarshi dan kishi ya kassara mishi ɓargo bashi da laka. Kan gado na koma na juya ma ƙofa baya. Su Mardiyya na shigowa nace su saka mun sakata. Ta kulle ɗakin suma suka kwanta. Raba dare nayi cur ina kuka, da dai naga kuka da tunani na shirin birkitamun ƙwaƙwalwata bisa ga birkicewar da take ciki dama. Saina miƙe na fito na ɗaura alwala na durfafi Sallah inayi ina tsiyayar hawayena.

Babangida:.

A sanyaye ya fito falon, har su Mardiyya sun soma bacci a ƙasan kafet ya tasheta suka wuce ciki. Ya yada fulon kujera a ƙasan kafet ya kwanta da dabara sabida karaya da ciwon hannunshi, damma hannun a sagale yake da wani abu kamar jaka data biyo ta wuyanshi ta riƙe hannun a ƙirji. Wayar Sabuwa daya cika dam da chaji ya kunna ya jira ta gama daidaituwa ƙirjinshi na dokawa ya shiga manhajar wahatapp kasancewar Data a buɗe take sai saƙwanni suka haukata wayar sukaita shigowa musamman na groups ɗin da take, na gyaran aure dana littattafai. Yakai a ƙalla minty goma yana kallon saƙwannin har suka gama shigowa. Cikin charting ɗinta da khalid ya shiga. Ya turo mata saƙwanni sunfi ashirin. Na ƙarshen ƙarfe takwas na daren ranar ya turo, kuma yana online. Yawu Babangida ya haɗiye muƙut hawaye suka zubo mishi na kishi, baiga komai ba fa tukunna.

_Baby Suger ina fatan wawan mijinki bai sake dukanki ba dai ko?_

Shine saƙon farko bayan anyi wannan rikici.

_Baby Suger wayarki bata tafiya sam. Ina cikin damuwa domin bansan a wanne halin kike ciki ba, ga hawan jini da kike fama dashi, nine kaɗai maganinki mai rarrashin zuchiyarki_

Idanunshi ya runtse wani abu nayi mishi ɗillin ɗil a zuchiyarshi da tsaƙiyar maɗigar kanshi. "Hawan jini. Sabuwa hawan jinine da'ita? Ni kake kira wawa? Zaka ga wawanci wallahi." Duk maganganunnan nashi da yake yi idanunshi a rufe ruf suke. Wani hoto ya buɗe yaga khalid a kwance tsirara. Da sauri ya miƙe zaune babu shiri dan har fama hannunshi yayi, ina ciwon zuchiya yafi ciwon da takobi yake iya jima gangar jiki. Da sauri Babangida ya dinga haurawa sama har yazo farkon chart ɗinsu ya dinga bi daki_daki yana haki. Wajen da yaji Sabuwa na ragargazo mishi kalaman ƙauna sai ya ja dogon numfashi yake iya wucewa, ya dinga tafiya yana ganin yadda suke haɗuwa da yadda ta kwakkwana ba tare da shi ya sani ba. Da yadda take tura mishi hotunan tsataicinta A taƙaice saida Babangida yaga komai har ƙarshe. A wannan daren haukacewa ne kawai baiyi ba, ya daki kujera harya gaji, yayi kuka irin kukan da a rayuwarshi bai taɓa yi ba, zuchiyarshi tana mishi wani irin ciwon da alƙalami da tawada ba zasu iya rubutawaba, harshe bazai iya furtawa ba. Miƙewa yayi ya shiga zagaye zuchiyarshi na faɗa mishi gaskiya. "Laifinka ne kaine ka nisanta kanka da ita. A lokacin da take fita ta kwana a waje. Kaima a lokacin kana club, ko wajen Sumy kana yin irin abinda wani yake yi da taka matar." Saitin zuchiyarshi da yake ji tamkar zuchiyar zata faso ƙirjin ta fito ta zagwanye ya damƙe yana rufe idanunshi. Wasu siraran hawayene suka gangaro mishi masu zafin gaske. Burinshi ya mance da abubbuwan daya gani. Sai dai ina yasan har abada bazai goguba. Zama yayi a kujera zazzaɓi yana sakko mishi, zuchiyarshi na faman bugawa, wani abu na sakko mishi wanda shi kanshi baisan menene ba. A ranshi ya ƙudure har gaba da abada ya dena mu'amula da matan banza. Kuma da kanshi zaije ya sallami Sumy. To ɗanshi dake wajenta yayi Yaya dashi, wa zaiba riƙon yaron, me zaice in aka tambayeshi daga ina ya samo ɗa? Wannan yana daga cikin illolin bariki. Idanunshi ya lumshe yana jin tsanar Sabuwa da tsanar kanshi na sakko mishi. Ba sallah, babu salati, babu istigifari yana zaune akayi kiran sallar farko. Idanunshi da fuskarshi baki ɗaya sun yi jawur sun kuma kumbura. Da ƙyar ya shiga banɗaki ya shasshafa alwala ya fito, raka'atanil fajir ya gabatar yana mai jin kunyar mahaliccinshi a bisa kauce dokikinshi da yayi. Allah ya bashi sani, yasan illolin zina, yasan irin lalacewar da mazinaci yake tsintar kanshi a ciki, shike ma wasu wa'azi amman shi yaƙi hankalta. Kai ya girgiza "Kaicona" Ya fice zuwa Masallaci jiki babu laka. Yana ta juyayin hawan jinin da Sabuwa ke ɗauke dashi.

SABUWA:. Jin fitar Babangida yasa na tashi Mardiyya. Mardiyya kije kiyi wanka ke da malama. Kafinnan ki soma tashin yaran can su yi alwala su tafi masallaci" Ina gama faɗa mata na ta da kabbara. Bayan na idar da Sallah, nayi addu'o'ina saina haye gado dan kaina kamar zai fashe haka nake jinshi, numfashina ma naji yayi nauyi. Bani na farka ba sai goman safe idanuna sunyi nauyi sosai. Nasan bani da damuwa Mardiyya tayi ma ƙannenta duk abinda ya dace sun kama hanyar makatanta, kafin in kwanta dama na ajjiye musu kuɗin mota a saman durowar gado. A hankali na sakko da naji cikina na wani irin murɗamun. A falo nake jiyo muryoyin su Babangida, ko da su waye oho. Wanka na wuce nayi na dawo na zura riga mai sauƙi na kuma fita. Ƙofar shiga falon na tura na shiga ban kalli kowa ba nayi ficewata, na dai ji wani ɗan kanzagi daga cikin abokan Babangida yana cewa. "Sannu Madam" Watsin ruwan tsarki nayi dashi nayi fitata. Ɗumamen tuwon jiya su Mardiyya suka ci, ga kari biyu ta ragemun ta barmun a cikin tukunyar miyar. "Maman Mardiyya yau sai yanzu kika fito dake kece da Oga? Ahh Lallai zamu zo ɗiban hadda a wajenki" Cewar Maman Sa'idu kenan. Duk matan lungun suna zaune ko wacce a kujera tare da wasu gungun mata da banyi tunanin a gidan suke ba. Ga wani kwangirin kwano a gabansu. Ɗan murmushi nayi muka gaisa da matan wajen. Wallahi bana jin daɗine ma shi yasa. Dan ko su Mardiyya bansan sanda suka tafi makaranta ba" Maman Sa'idu tace. "Na tambayesu ma ina kike suka ce kina bacci. Sai kika bar Babansu da kiciniyar yi musu kayan kari shi da baida lafiya. Sai daga baya Mardiyya ta karɓa ta ƙarashe musu." Sai naji kaina ya ɗaure a raina na shiga jujjuya maganar amman dai na kasa fahimta. Wata zabiya ce ta katsemun tunanina da muryarta mai zaƙi da karaɗi kamar ta Ɗaye manna ( Habibty) dan da waƙa baiwar Allah'nnan zata yi da zata samu a jikin waƙa. "Toh ni dai Mamam Mardiyya zo ga haja kema ki zama memba kafin Maman muklisiyya tazo ta kwace mun ke. Duk matan lungunnan da matan maƙotanku gasu a wajena suke siyayya kuma wallahi nake faɗa miki kuɗaɗe suke tatsa a wajen mazajen nasu shi yasa zaki gansu kullum fes dasu ga cin abinci me kyau. Kiga mace da yamma fes da'ita ta ɗau seti network ciki da waje." Shewa suka saka harda tafawa. Nima saida na dara. Ina dai daga kitchen ɗina nace. Hmm ni da megida babu lafiya ina ni ina shan kayan harka. A dai bari in ya samu lafiya" Carab wata matar tace. "To ga ƙananan kaya na gwanjo amman giredi ne sosai zo ki zazzaɓa. Gudun kada su rainani dai yasa na ƙarasa wajen inda ta buɗe buhun kayan na shiga ɗagawa. Gaskiya suna da kyau babu laifi sai dai in ba siye zaka yi ba. Wata riga mai ruwan hoda na ɗauka me hannu ɗaya da baƙin wandon da suke tare. Sai wata riga mai ruwan makuba ita kuma da dogon siket yadin yayi kyau sosai. To na ɗauki wannan nawa ne kuɗinsu?" Cikin washe baki tace. "Tunda ke sabuwar kostoma ce ba da ɗaya da ɗari biyar na miki ragin ɗari biyar." To nagode bari in kawo miki kuɗin." Na wuce na koma kitchen ɗina na daura ɗumamen tuwona a gas, ina ƙoƙarin shiga ciki su Mustapha suka fito na basu waje suka fice. "Sabuwa zamu je asibiti su Mustapha zasu kaini ni saina dawo" Ganin yadda matan lungun suka kureni da idanu yasa nace. Sai ka dawo" Murmushi yayi mun, ni sabida baƙin ciki ma sai naga kamar kuka yake yi. Shigewata ciki nayi na ɗakkoma mai gwanjo kuɗinta. Na gama dumamen tuwona na dafa ruwan bunu nayi shigewata ciki. Ina karyawa sai ga Ƴar Shuwa tayo sallama ta kunno kai tana ƙarema ɗakin kallo. Sau ɗaya bisa kuskure dana ɗaga kai naga itace ban sake ɗagowa ba. "Sabuwa ina Babangida yake? Kin hanashi ya leƙo ya duba mu sabida mugun hali. Ai ni daman nasan ba zaki iya barin gidan Babangida ba. Kinbi kin asirce kab danginshi sai roƙonshi suke yi akan kada ya sake ki. Nace ko kin dawo da bokancinki ne Sabuwa?" Da ƙarfi take maganarta indai maƙotana suna zaune a inda na barsu to tabbas suna jinta. Dan na lura a shirye tazo tsab danta sanarma Babangida cewar ni boka ce, ta fasa wani ƙwai, shima babban saita fallasashi. Ba tasan a yanzu in ƙwayayen sun Kai dubu so nake ta fasa uban kowa ya huta warin ya turniƙemu duk mu mutu ma." "Dake nake yi bokanya Sabuwa mai bama mata asirin mallakar kishiya, ko mallakar miji, ko kassara kishiya. Ki sani asirinki bazai taɓa tasiri a kaina ba nafi ƙarfinki tun da bare yanzu" Sama da ƙasa Allah bai bani ikon tankawa ba. Har na soma jin matan lungun suna magana. Kafin in aune sai naga daga waje an hankaɗo Ƴar Shuwa ta shigo, tana shigowa sai ga Aisha mutan zango da Sadiya sun shigo harda sa sakata." Ina ganin haka nayi kukan kura na dira a wuyan ƴar shuwa nan dambe ya turniƙe a tsakankaninmu, na hana su Aisha saka mun hannu. Ai ita tasan baki ta fini ba dai ƙarfi ba. Nayi mata dukan Allah ya tsine uwar mai ƙarya. Matan gidanne suka bankaɗo ƙofa suka ƙwaceta. Da mugun gudu na shiga ciki. Nayi kata_kata na dawo baya wuƙa ko wani makamin nake nema da zan illata ƴar Shuwa tura ta kaini bango, daidai nake da ko wacce ƴar abu ta kazan... Frime ɗina me glass na ciro a bango na fito da gudu . Da Allah ya bani nasara a tsakiyan kan Ƴar Shuwa na fasa frime ɗinnan. MRS BUKHARI

HAYYA HAYYA ƳAR SHUWA YA JIKIN KUMA. WUYA A HANNUN SABUWA AN FASA FRIME A KAN ƳAR SHUWA

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA TAKWAS BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

SADAUKAR.

NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFI ZUWA GAREKI MRS JAY NAGODE SOSAI UBANGIJI ALLAH YA BAR ZUMUNCI SON SO💪🏼

Assalamualaikum brkanku d warhaka hmmmm Wani kaya sai amale tohhh mata masu capacity matan kwarai 🥰🥰🥰ga ramlex Mai kayan daa kayan buje 😀😀😀😀akwae Package na uwargida Package na amarya Package na mejego Tsimi baure Tsimi magarya Hadin tattabara Hadin kaxa Hadin ciccibi Gumban Madara Gumban ridi Gumban waken soya Karin dandano Xuman matsi Manta uwa Hadin mallaka Hadin bita xaixai Hadin tsuguno hmmmmm gareku mata akwae adashen gata duk sati 2k hadi Mai kyau xaayi muku duk Mai bukata ga no 07069722234 ko 07044503983 snnn dn Neman Karin bayani ku tuntubi wnnn layukan 🥰🥰🥰🥰🥰

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull