Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 6
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 6: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 6. Haka dai lamura suka ci gaba da tafiya suna jiyawa. Matan Babangida suka ci gaba da…
3,909 words
Haka dai lamura suka ci gaba da tafiya suna jiyawa. Matan Babangida suka ci gaba da jinyarshi yau wannan ta kwana gobe waccan. Amarya dai tana turakar mijinta. Yadda na fuskanceta bata da haƙuri kamar zawayi haka take, shi yasa kusan kullum ita da Ƴar shuwa sai sun hau sama sun duro, gata da gadara da girman kai. Ni dai tun daga wannan ranar kafata bata sake taka asibiti ba. Malama Babba ma har aka sallamota banje ba. Baba Malam kam naje har sau biyu gida na duba shi. Shine ma ya sanar dani a tsanake in tattare kayayyakina waje guda, in ɓaɓɓalle gado da komai nawa dai. Bai mun bayanin komai ba, nima ban tambaya ba na dai bi umarninshi nida su Labbai mukai ta kaye_kaye. Sai da su Sa'a suka zo gidanne Ƴar Shuwa ta rakouu barayina ko zama sun kasa yi. "Ku haɗa kayayyakinku waje guda zaku tashi a gidan. Za'ayi ma gidan gyara sosai ne" Bata bari na amsa ba suka fice. Amman jikina yana bani matsala ba tun yau ba, dan na fahimci su Kawu Manga sai kai kawo suke yi hatta motar Ƴar shuwa babu. A zuwa na duba Baba malam na ukunne ma na tarar an sallamo Malama Babba sai na shiga na dubata da jiki. Ta rame ta komaɗe sosai. "Sa'a ku bamu waje inaso zanyi magana da Sabuwa" Bani kaɗai ba harsu Kudidi suma sun yi mamaki. Ni ko kaina cike da tambayar da babu wanda zai iya amsa mun. Nan duk suka zame suka fita. Cikin gadara Malama Babba tace. "So nake ki janye wannan shar'ar da kika shigar da ƙara kotu. Na yi miki alƙawarin ko nawa kike buƙata zan baki" Da mamaki na kalleta sai kawai nayi murmushi nace. Bazan iya janye wannan ƙaran ba, ko da duniya da abinda ke cikinta zaki bani. Takaddar sakina yafi mun komai" A_a dai kije kiyi tunani nan da kwana biyu kinga lokacin shiga kotu ya kusa. In kika janye zan baki kuɗi masu kauri " Daga sama muka jiyo muryar Baba Malam "Babu mahalukin daya isa yasa ta janye. Da kike maganar kuɗi kuma a ina kika samesu ni bani da masaniya a kansu? Ai dani kika bama kya samu lada. Ke Sabuwa taso ki kama hanya ki tafi gidanki" Sum_sum na ficewata ya suka ƙare sai Allah. Ina isa gida a ƙofar gidanmu naga wata ƙatuwar mota tana ta loda kayayyakin ɗaki harda gadona na hango a cikin motar. Ban gama mamaki ba Labbai ta fito da ƙatuwar randa ta cike da kwanuka da su cokula. Ga Hamida itama a gefe tanata zuba kayayyaki a buhu. Gidan duk ya hautsine Hannuna Labbai taja muka shiga cikin gidan" "Kinga muna zaune Wawo ya leƙo yace mu fito da kayanmu. Lallai Sabuwa zaku sha gyara. Amman naga gidannan babu abinda ya sameshi sai samannan da ake tadawa" Jikina a sanyaye nace. Sunce gyara za'ayi sosai a gabanki fa Sa'a ta faɗa mana. Ina Adama fa?" "Tana ciki tana fito da kaya muje daga ciki" Ciki muka shiga muka ci gaba da harhaɗe kaya. Motar ma ta cika har sun tafi kai kayan. Ni ko har mun gama fitar da kab kayanmu waje, har Adama ta share ɗakunan, ni da Labbai mun goge komai da komai. Har wajajen bayan la'asar yara suka shigo suka samemu muna jira, Adama dai tabi motar kaya da suka dawo. Maƙota duk an shisshigo dan jin ba'asi. Da an faɗa musu gyara za'ayi mana sai su shiga taya mu murna. Maman Safara,u ta daɗe sosai tare damu taso binmu ma taga waje amman ganin har an kira magriba ba'a zo ba yasa tace. "Maman Mardiyya ni kam zan tafi gida yau nice da oga, gashi dare yayi inaga sai zuwa gobe zan kiraki a wayar Labbai sai in zo in sha Allah. Allah ya sanya alkhairi ya ƙara arziki" To Ameen Maman Safara,u nagode sosai Allah ya bar zumunci. Sai zuwa goben. Ta fita bata jima ba Wawo ya shigo yai kiranmu duk aka duramu a siyana muka ɗau hanya. Motar tayi tsit kowacce da abinda take saƙawa. Bamu tabbatar da akwai matsala ba sai da muka ga motarmu tasha kwanar wata unguwar da kaɗan tafi unguwar da muka taso na da kyau. Ga hanyar shiga unguwar bata da kyau ga ba wuta sai faɗawa ramuka muke yi. A bakin get ɗin wani gida motar ta tsaya, get ɗin irin get ɗinnanne da baikai har ƙasa ba, kai me wucewa kana iya hango har guiwar na tsaye gashi duk tsatsa. "To masha Allah ga gidan da zaku zauna nan. Muje in nuna muku ɗakunanku dan ba jere suke ba." Wawo yayi gaba muka bishi a baya da yaranmu. Gidan shiru babu hayaniya, babu ko macce ɗaya a tsakar gidan. Gidane dogo ga ɗaƙuna a jere suna kallon juna. Hagu ɗakuna huɗu dama ma haka, daga bakin get akwai wani lungu dana hango ɗakuna kamar huɗu suma a jere . Wannan lungun shima lungu yake kallo da ɗakuna huɗu a jere suma kunji wata ƙudurar Allah. "Ga ɗakinki Maman Fatima can na ƙarshen hagun dama. Maman usama ga naki ɗakin na farkon hanun hagu, Amarya naki shine na tsakiyancan na hannun dama. Maman Mardiyya naki na baya ta can kwanar muje in nuna miki sauri nake yi muna da meeting a gida. Gashi muna sa ran gobe za'a sallamo Babangida daga asibiti ma. Muna biye dashi har zuwa lungun ɗakina shine na ƙarshe a lungun. Harma na hango Adama tana ta faman moping ɗin wata ƴar baranda dake ƙofar ɗakin, ko wanne ɗaki naga da baranda, kuma kamar babu kitchen a ciki dan naga duk a barandar naga iyakar ɗakunan dana hanga kitchen ɗinsu yake. Saida na shiga barandar naga harda kwanon wanke_wanke na turawa. Adama sun jera mun durowowin kitchen ɗina a wajen sun ciccikasu da kwanuka da tukwane da dai tsarkacen kayan kitchen namu na mata. "Sai yanzu kuka shigo irin wannan jimawa me ya tsayar daku haka?" Labbai ce taba Adama amsa. Su Sadiya suna ciki sunata shewa. "Wallahi Wawo ne baizo da wuri ya ɗebo mu ba. Yinwa kamar zata kashe ni." "Yinwa? Hmm muma ita muke ji. Baku haɗu dasu Gaza ba?" Sun zo ne? Gaskiya bamu haɗu ba dake muna cikin mota" Ciki muka shige yara dama tuni sun shige sai Aɗɗa'u da Malama sai murnar sabon gida suke yi. Falon ƙaramine sosai gashi kujeruna suna da girma gabaki ɗaya sai suka takure falon, banga 1 sitter ba ma. Ƙofar da nake tunanin uwar ɗakine na shiga sai naga dogon falo ( Coridor) ne ga ƙofofi guda biyu a jere, amman suna da taraza ƙofofin. Ɗaya ashe banɗakine ɗayan ɗakin kuma ɗakin baccine. Sai a falo kuma akwai wani ƙaramin ɗaki sosai yafi kama da store. "Kinga wajen Lolo amman babu ɗakin yara. Maƙociyarki tace duk wannan ɗakin suke mayarwa na yaransu. Amman asalinshi kitchen ne. Sai mai gidan ya dawo da Kitchen ƴar barandar waje. Wasu ma da kansu suka yi aiki. To kinga gadone kaɗai ya shiga, dorowarsu taƙi shiga, amman ta shiga ɗakinki. Sai kayayyakin Babangida na turakarshi duk su Wawo basu sauke ba dashi suka juya ƙila sabida babu wuri ne. Amman dai tulin kayanshi mun jera a durowarki, ɗankunnayen su Mardiyya da naki duka kuma suna ƙaramar jakarki." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da neman waje na zauna ina sake ƙarema falon kallo. Sannunku Adama, Sadiya sannunku fa. Ashe har kun garzayo. Kinga ɗakinnan sai dai su Aminu su dinga kwana a ciki, ni da matan sai mu kwana a ɗakina" Carab Aisha dake waya tace. "Babansu in a ɗakinki yake kuma fa?" Adama tace. "Ato kema kya tambayeta." Dana waiga naga yaran basa wajan sai nace. Ai kunsan rabuwa zamu yi tunda saura kwana uku ma zaman kotu. Kuma ai dama baya raba mana kwana da matanshi balle kuma yanzu kuma duk kun sani. Yanzu dai su Aisha su siyo mana ko da biredi ne sai mu sha tea tunda akwai wuta. Labbai muje ciki muyi Sallah " Ciki muka shiga bayan na sallami su Aisha da kuɗin biredi kayan tea ina dashi dama. Ina rama sallolina maimakon in huta saina shiga tattare kab suturun Babangida da Adama suka jera mun. Ko da suka shigo suka samu inata tarkace komatsenshi babu wacce ta tanka mun, kuma nasan dan sunga na mugun haɗe rainane. Akwati uku na cika, banda manyan jakunkuna huɗu dana ciki, ga takalma cikin ƙaramin buhu. Labbai taya ni muje mu kaima matan Babangida wannan kayan nashi, ni bana son Magana. Ke Mardiyya Aisha ku taso" Haka muka kinkimi kaya na ƙwanƙwasa ƙofar Hamida duk muka jibge mata kayan a ƙofa. Da waya a kunnenta ta fito. Ganin kaya yasa tace. "Zan kiraka Baban Usama ina zuwa'" Ta sauke wayar tana kallon kayan. "Wannan kayan daga ina kuma?" Kayan mijinku ne, ku ke da hakkin adana mishi" Da harara da taɓe baki tace. "Ni ina naga wajen da zan ajjiye wannan tulin kayan. Ɗakuna tsukuku kamar kabari. Sannan ai bani kaɗai bace matarshi ba. Ga Ramatu me yasa ba'a raba an kai mata ba tunda Maman Fatima tana asibiti?" Kallonta kawai nayi nace da su Labbai su tawo mu tafi dan bani da lokacinta "Maman Mardiyya kizo ki debe mun wannan kayan daga nan duk bala'in da kike nema na dashi kin tara kin samu." Babu wanda ya juyo balle ya tanka mata. Tea da biredi harda tsire su Sadiya suka siyo mana. Muka ci muka baje, su Aminu suka tafi ɗakinsu, Mardiyya da Malama suka sauke katifarsu sukai kwanciyarsu. A wannan daren nayi bacci sosai da sosai. Washegari sassafe muka tashi da aiki, yara suka ci gaba da kacaniyar shirin makaranta. Na ɗakko kuɗin mota da abun break na basu jarabawa ma suke yi Mardiyya za'a shiga ss 3 karatu ya zo ƙarshe za'ace. Aminu na jss 3 Adda'u za'a shiga jss 1 Malama kuma aji huɗu zata shiga. Har titi na rakasu saida suka shiga abun hawa sannan na dawo bayan na jaddadama Mardiyya kada fa ta mance sunan layin. Dariya tayi tace. "Ai Ummi akwai ƴan makarantarmu da yawa a layinnan. Mum ma taɓa zuwa gaisuwar rasuwar yarinyar ajinmu a layin dake bayan namu" Sannan hankalina ya kwanta A hanyar komawata gida kuwa naita cin karo da ƴan makarantar tasu. Ina shiga gidan na tarar matan gidan ko wacce tana bakin ƙofarta tana haɗa abun kari. Sai ƙamshin toye_toye ke tashi abunma kamar gasa a yadda na fahimta. Matan dake cikin lungummu na tsaya duk aka gaggaisa da fara,a na gabatar musu da kaina. "Ayya sannu da dawowa Maman Mardiyya. Aini da naga an tashi su Maman ummi nayi mamaki, sai daga baya ne muka ji labarin wai matan ƙanin abokin me gidanne zasu dawo su huɗu" Murmushi kawai nayi mata na wuce ciki. Labbai na tsaye tana toya ƙwai, Adama na haɗa tea a ƙaramar robar fenti. Sai kwatsam muka jiyo muryar Maigogul yana gaisawa da matan lungun. "Sannunku fa. Nine mahaifin Sabuwa uwargidan Babangida wanda suka dawo jiya. Ga mahaifiyarta nan, wannan kuma yarta ce" Nan suka shiga rige_rigen gaishesu, sai washe bakinsu suke yi. "Masha Allah Allah ya baku zaman lafiya. Megidan nasu yana kwance a asibiti ne, amman yauma za'a sallamoshi daga asibitin muke anata ƙoƙarin biyan kuɗaɗen jinya ma, dake ya jima a asibitin. Ai faɗane..." "Maigogul dan Allah ku shigo daga ciki, Rakiya ku karaso" Cewar Adama data katse hanzarin Maigogul danta fahimci so yake daga zuwa ya watsarmun da mutuncina a idanun matan gidan ga gida gidan yawa. Ƙarasowa suka yi. "Ahh Adama anata haɗa haɗin murtuk an baro gidan miji an rabu da dumamen tuwo. In sha Allah aurenku sai masu arziki a wannan karon. Sai ku ƙara sanwa dan ko ruwa bamu kurɓa ba." Maigogul yana gama magana ya tsallake ya shigewarshi ciki. Babu mamaki matan lungunmu sunji sak abinda maigogul yace, tunda ko wacce tana bakin aikinta. Tattare kayan karyawan muka yi zuwa cikin falon. Adama ta zuzzuba ma kowa muka zauna zaman karyawa tare da tattaunawa. Maganar dai ɗaya tak. Ni dai in yi haƙuri in zauna a ɗakina in janye ƙara akwai alƙawari mai tsoka da Malama Babba tayi musu muddin na jaye wannan ƙarar. Wasu zafafan hawayen baƙin cikine ya zubo mun. Shikenan mu iyayenmu a kullum sunfi fifita abin duniya sama da farin cikinmu. Wato Malama Babba ta hanyar su Maigogul ta bullo? Wallahi koma menene ƙudurinta sai dai ta mutu wallahi sai Babangida ya sake ni ko sama da ƙasa zata haɗe. Nasan sabida kada aurenta ya mutu ne take son lallai saina janye ƙarar dana shigar. In zauna suci gaba da tsangwamamun. A fili nace da Rakiya da Maigogul. Ni wallahi bazan taɓa iya janyewa ba. Maigogul nifa sai Babangida ya sakeni, wallahi na fishi taurin kai a wannan karon ni ku ƙyaleni kawai ni kaɗai nasan halin da nake ciki" Duka Rakiya ta kawo mun. Maigogul kuma ya sauke murya. "A_a Lolo cewa fa tayi zata iya bamu gida. Kar muyi haka dake, ina laifin me sonka da ɗanshi. Shifa Malam da kike ji da gani ingiza mai kantu ruwa yake yi miki. Babu ƙauna a tsakaninku, in kin mance badaƙalar data faru a baya da irin matsananciyar ƙiyayyar da yake yi miki a baya sai mu tuna miki dan ubanki. Harni zaki ma baƙin ciki tun tasowarku a ɗaki ɗaya kuke rayuwa ku da uwarku ya yau ance za'a bani gida Lolo kina son kawo mana cikas. So kike in bi malamai a kanki a juya miki kai. Ko ko a_a so kike in kwaso tsofaffin kayan tsubbuna in soma turo miki aljanu baƙaƙene su birkita miki lissafinki bafa tsoronki muke ji ba. Malama Babba har mun faɗa mata kin janye ma kin gama shine kike wannan maganar" Miƙewa nayi na shige uwar ɗaki a guje na faɗa gaɗo dan baƙin ciki da takaicin dake shirin ƙarashe rayuwata. Su Adama ne sukai mun tsaye a kaina sai faɗa suke yi mun akan in daure ko ba dan komai ba in zauna a ɗakina dan yarana. Ni dai nasan a musulunci babu wani zaman yara da hausawanmu suke yi. Kaga mace ma an saketa kamar tsohuwar maiya tace ba zata tafi ba zatai zaman ƴaƴanta. Maigogul har uwarɗakin ya shigo yace. "Ku barni da'ita dan ubanta nace. Zata gane kurenta inna dinga yi mata ture ba zata ji da daɗi ba. Wai ya zaka haifi yaro ya zama baya jin maganarka Rakiya tawo muje. Kuma duk ku bar mata gidanta taci kanta" Ai kuwa ilai suka tarkace komatsensu suka tafi sai ni kaɗai. Na jima ina kukan baƙin ciki can baccin wahala da gajiya ya debeni bani na farka ba sai azahar shima jiyo kiran Sallah nayi rangaɗaɗau a kunnena kamar a cikin gidan da muke. Babu shiri na duro, shi ciwon hawan jini muddin kana cikin ƙunci, musamman haɗi da ciwon damuwa baka taɓa rabo dashi. A zaune nayi Sallah na ɗaga hannu na dinga roƙon Allah akan ya bani sa'a da nasara akan shari'ar da zamu zauna gobe. Ya kuma kareni daga sharrin lafuzzan Maigogul dan wabillahillazi la'ilaha, illahuwa akan gidannan da Malama tace zata bashi, zai iya mun shige shigen malamai dan a rikirkitamun ƙwaƙwalwata, hmm ku dai a gaba akwai labarai da dama da muka tsallakesu dole zamu ɗakkosu daga tushe. Kuma komawa gado nayi na duƙunƙuna, zuchiyata ta shiga aikin tunanin son gano meye manufar Malama Babba akan wannan shari'ar da take so in janye tunda ai dama tasan igiyoyin aurenmu a sarƙe suke Nasan koma menene zata yi ne dan kawai tafi son a kullum taga ina kuka Babangida yana jana a ƙasa. Ni kuma na lashi takobin ja ya ƙare a tsakanina da kowa. Dole a sake mu ni in bar gidan mijina in kama haya. Ita kuma ta koma ƙauye ko hannun ƴaƴa. Sallama naji anata dokawa a falo dole haka na fito kaina na sarawa. Maƙotane suka shigo ganin waje, tare da matan gidan. Wasu ma a tsaye suka tsaya suna yaba kyan wajen, sune harda leƙa uwar ɗaki. Wata zabiya ce tace. "Waje yayi kyau komai nason gyara ji waje yadda ya sha fenti da tsadaddun kaya kamar ba ɗakin maman ummi mai kitso ba." Sai suka saka dariya. Wata ƴar ƙawutar mata da zata yi Amina madaki a ƙiba da duhun fata mai sheƙi tace. "Ashe an sallamo mijin naku, ai ɗazu ƴan uwanshi suka wuce dashi ɗakin ɗaya daga cikin abokan zamsn naki. Ni da nama ɗauka a ɗakinki zai zauna yayi jinyar har sai ya warke. Maman Bello naga sanda Baban Bello mota ta bijeshi a ɗakinta ya zauna yayi jinya" To ni bamma san sun dawo ba, ina ruwana da dawowarshi mutumin da in ina ƙaunar mutuwata to ina ƙaunarshi. Ɗan murmushi kawai nayi musu, sukaita hira a tsakaninsu daga ƙarshe suka fice. Ajjiyar zuchiya na sauke, na shiga kaye_kaye nice harda shara. Kitchen na fito dan in ɗan samu ruwan zafi in kurɓa. Sai ko ga Sa,a a ƙofar ɗakina. "Wai ke Sabuwa me kike ji dashi, da me kike taƙama da har zamu fi awa biyu da shigowa gidannan an dawo da Babangida amman ba zaki zo ki duba jikinshi ki gaishe mu ba?". Wuƙar dake hannuna da na ɗauka zan yanka albasa na kalla, take bakina naga ya soma cijewa da kanshi tsumin dabancina nason ya tashi. Abinda kike ji shi nake ji Sa'a. In ke kina jin mara ji ce ki shigo daga ciki in ban faffarɗeki ba kice ba Sabuwa bace" Zaburowa nayi ina shirin buɗe ƙofar. Wallahi saita danna a guje ta bar lungun, a yadda taji ina magana ma kaɗai ya isa yasa ta tsorata, kuma a baya tasan waye Sabuwa. Ba kince bakya ji ba, dana koya miki ji, inda aka fito da ɗan uwan naki ke ki maye gurbinshi." Dariya na saka dana tuno yadda ta saka gudu ɓakatar_ɓakatar ga sifukun zama kamar na masoyiya maidoki sai sama da ƙasa suke yi. Ƙwai na soya na dafa indommie guda ɗaya, na haɗa tea nayi komawata ciki. Inaci kamar magani nake ci haka nake ji, bana jin daɗin komai Haka naita turawa har yamma lis yara suka dawo makaranta, sai dai daf magriba suka dawo sakamakon nisa da muka ƙara yi. Dole na kira Malam a waya nake sanar mishi sai yace daga makarantar zai sa a dinga haɗosu da yaran Wawo ana wucewa dasu can gidan in yaso in aka tashi makarantar islamiyya Ramadan ya kawo su gida. "Amman Sabuwa kin shiga kin duba Babangida da jikin kuwa naji labarin an sallamoshi ko?" Kai na girgiza kamar yana gabana kafin nace. E an sallamoshi, amman banje ba" "Assha Sabuwa a dinga daurewa yaci albarkacin haihuwa. Ki taimaka mishi yaranshi suga darajarshi. Ki kama hannunsu kuje zuwa bayan isha ku duba shi ƙila ma akwai ƙarin bayanin da zai zaunar daku yayi muku" A sanyaye nace. To in sha Allah zamu je nagode" "To mu kwana lafiya sai Allah ya kaimu jibin in mun haɗu a kotu" Ajjiye wayar nayi naci gaba da tuƙa tuwona. Mardiyya ku samu kuje kuyi wanka ayi Sallah sai azo aci tuwo ko?" Malama nan tahau bori ita ba zata ci tuwo ba abinci take son taci. Maƙociyarmu tana ji maman Sa'idu tayi dariya tace. "Zo ki karɓi abinci to. Yarinya fa da gaskiyarta Maman Mardiyya wanne tuwone za'a tareta dashi." Dariya kawai nayi, banso ba amman bana so tayi tunanin wani abun. Taci kwalliya ta gani a faɗe, matan gidan gaskiya ƴan gayune sosai, dukkansu kayan kantine a jikinsu, daga masu riga da wando sai masu dogayen riguna, ga abinci na alfarma ko wacce tana yi. Kwano ta ciko ma malama da lafiyayyar shinkafa da miya, ga ƙatuwar kaza a saman abincin, ga ko slow harda ɗaɗɗaran zoɓo da samosa guda ɗaya. Da kanta ta ƙaraso ta miƙo mata lokacin ina juya miyar zogalena da taji gandar naman kan saniya da dama yake tafashe a firiza tuntuni. Ah angode sosai. Wannan ai yayi mata ma yawa." Dariya tayi tana ta sake leƙa mun miya tana. "Ahh babu komai wallahi saci da yayyenta" Ana kiran sallar magriba ina gama kwashe tuwona na saka a filas na tuwo da miya Mardiyya ta shigarmun dashi ciki. Saida mukai sallah mu matan kafin muka zauna, mazan masallaci suka tafi, saida na haɗa Adda'u da Allah akan ya rufamun asiri da an idar ya biyo Aminu su dawo. Ai kuwa ana idarwa sai gasu sun shigo. Malama da Aɗɗa'u suka ci shinkafar da Maman Sa'idu ta basu. Mu kuma na zuba mana tuwo a faranti dukkanmu muka sa hannu muna ci. Daurewa kawai nake ina wurga loma dan yaushe ma rabon da muci abinci a kwano ɗaya. Harsu Malama bayan sun gama cin shinkafarsu saida suka saka hannu akaci tuwon tare dasu. Rabon da inci abinci mai yawan wanda naci yau tare da yarana harna mance. Wanka na shiga nayi a ciki na ɗan shafa maina sama sama, na ɗauki doguwar rigar atampa na zura na saka hijabina kalar atampar na tada Sallah. Na jima a zaune a sallaya ina roƙon Allah nasara. Dan gabana sai naji yanata faɗuwa. Mardiyya ce ta shigo da sallama. "Ummi wai Baba yana nemanki inji Maman Usama." Kallonta nayi, itama ni take kallo sai naga ta nemi waje ta zauna. "Ummi da gaske jibi zaku shiga kotu ke da Baba wai akan ya sakeki?" Idanuna na lumshe kafin nace mata. Tabbas hakane jibi zamu soma zaman kotun. Kuyi haƙuri kunji, ke kinfi kowa sanin halin da nake ciki a gidan mahaifinki. Mardiyya nasan ke da kanki ba zaki so inci gaba da zama cikin ƙasƙanci ba. Abinda nake so dake shine ki nutsu ki kama mutuncin kanki, da kin samu miji kiyi aurenki ya fiye miki" Saita sauke kanta naga tana ɗan murmushi sabida na ambaci mijin Aure. "Ummi amman a wajen wa zaki tafi ki barmu, ko damu zaki tafi? Ummi da zan baki haƙuri ki haƙura da nace kiyi haƙuri dan Allah " Sai kuma ta soma tsiyayar hawaye shiru nayi ina kallonta ina nazari. Ta daɗe tana rera kuka bance mata uffan ba. Da dai naga kukanta na neman kassara kuzarina saina jawota kusa dani. Dena kuka uhm Mardiyya ke da zaki yi aurenki ki tafi naki gidan mijin ma uhm ai na lura kamar kin samu saurayin da kike so ko?" Kanta ta sunne sai mukai ɗan dariya. "E Ummi akwai wani mutum da muka haɗu dashi shekaran jiya, yaso karɓar lambata nace mishi Babanmu yace har sai nayi aure zan riƙe waya. Yauma mun haɗu dashi a hanyar makaranta" A_a Mardiyya me yasa baki kwatanta mishi gidanku ba sai a waje zaku dinga haɗuwa? Kema kinsan duk randa Babanku yaji ko ya ganki zaki ɗanɗana kuɗarki. In kuka haɗu ki kwatanta mishi gidanku yazo ya samu Babanku ya nemi izini. In Allah ya dedetaku shikenan kinga ɗan gidan Sa'a ya huta duk da shima fitinace kawai" Dariya ta saka naga jin daɗi sosai a tattare daita. To muje ku gaishe da Babanku da jiki. In mun dawo a bani labarin me sunan sirikin nawa" Gaba tayi tana dariya. Ni kuma na sharce wata ƙwalla mai ɗumi. Hmmm miƙewa nayi ni da yara muka je ƙofar ɗakin Hamida muka yi sallama, daga ciki ta amsa tare da bada izinin shigowa. MRS BUKHARI
Ga masu son shiga group https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=r_t IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA BAKWAI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
INA SONKU WALLAHI MASOYANA SON SO SAI DA KU ƳAN AMANANA.