Idan kaya ya gaji part 2 - Chapter 5
Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 5: Idan kaya ya gaji part 2 Chapter 5. Asibiti:. Tun sassafe Yar shuwa ta kasance a asibiti. Hamida kuma taje raka…
4,344 words
Asibiti:. Tun sassafe Yar shuwa ta kasance a asibiti. Hamida kuma taje raka iyayenta tasha zasu ɗauki hanya. Tana zaune a doguwar kujerar dake ɗakin da Babangida yake kwance tanata tunani a ranta so take tasan menene yake faruwane taga tamkar dangin Babangida da akwai abinda suke ɓoyewa dai. "Amman koma menene in tayi wari maji" Ta faɗi hakan a zuchiyarta. A hankali Babangida ya buɗe idanunshi ya kalli sama, ya dawo da kallonshi wajen Ƴar Shuwa da Ramadan dake zaune a kujerar roba yana gyangyaɗi. "Ramadan ka kira mun Mustapha a waya inason ganinshi" Ya faɗa yana nishi irinna jiki yayi tsanani. Saida Ramadan ya garzaya ya kirawo ma'aikatan jinya kafin ya isarma da Mustapha saƙon Babangida. Mustapha yace dama suna hanya shi da matanshi gashi nan ƙarasowa " Likita na tsaye a kanshi yana aunashi, ga nurse a tsaye da kwando ɗauke da takaddu da magungunan marasa lafiya" "Malam Babangida ka daure ka rage ma kanka damuwa sabida jininka ya samu ya sakko. Kaga jinin bai sauka yadda ya kamata ba. Tunda dai kai musulmine dole ka yarda da kaddara me kyau ko akasin hakan. Ka duba iyalinka da iyayenka karka kashe kanka a banza yaranka suna buƙatarka a raye" Dr ya dinga mishi nasiha tare da bashi musalai masu yawa, har da jawo mishi hadisai da ayoyin Qur'ani mai girma. "Nagode sosai Dr. Komai zai daidaita in sha Allah." Idanunshi ya runtse zuchiyarshi ke tuka mishi. Har aka gama wanke mishi ciwon aka sake yima wajen dressing Babangida idanunshi arufe sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Bawai baya jin zafin ciwon bane har cikin ranshi yake jin motsin zafin. Amman zafin da zuchiyarshi take ɗauke dashi ya doke zafin ciwon zafi. "Yanzu ka samu kaci abinci kasha magangunanka, sai ka daure kayi wanka. Amman sai dai a goge maka jiki da tawul kada a kwara maka ruwa a jikinka. Magungunan ya mika ma Ramadan, yayi musu sallama ya fita. "Ramadan taimaka mun in soma watsa ruwan tukunna, ji nake kamar na shekara babu wanka. Ramadan ya taimaka mishi suka shiga bayan gida, shi ya goge mishi jiki da tawul, ya buɗe mishi sabon brush yayi. Alwala ya ɗauro mishi ta hanyar shasshafa mishi ruwa ya kuma taimaka mishi suka fito. Saida yaci abinci, yasha tea, ya haɗiyi magungunanshi kafin daga gadon ya soma rama sallolin da ake binshi. Duk wannan bidirin bakin Ƴar Shuwa bai rabu dayi mishi sannu ba. Daidai da sannunta sau ɗaya bai amsa ba, inda take ma bai kalla ba. Mustapha da iyalanshi ne suka turo ƙofar suka shigo suma niƙi_niƙi da kayan abinci a basket. Daga me ciki, sai me goyo, sai me jego a matan Mustapha. Gaggaisawa akayi kafin Mustapha yace Dukkanku ku bamu waje zamu tattauna in mun kammala kwa dawo" Matan Mustapha da Ramadan suka fice, Ƴar Shuwa kuma ta gyara zama ita a tunaninta ai duk abinda za'a tauna yana da alaƙa dasu. "Ke me kike nufi da ba zaki fice ki bama mutane waje ba?" Babangida ya faɗa da ɗaga murya yana zare idanu tamkar zai cinyeta. "Kayi haƙuri jannaty da bata maka rai da nayi natuba. Amman kaga yanzu haka daga gida aka turo mun hoton Sabuwa ita da wani a zaune" A razane ya kalleta yana son ya furta kalma harshenshi ya gaza haɗa kalmomin da za'a fahimta. "Ya haka baiwar Allah, ya ina ganinki da hankalinki zaki faɗa ma mara lafiya irin wannan maganar kuma?" Cewar Mustapha kenan. "Ka kyaleta wallahi so take zuchiyata ta buga in mutu a raba musu gadon dukiyata ki fice a ɗakinnan" Cikin fushi tayi ficewarta asibitin ma ta bari baki ɗaya dan ji take da badan Babangida jinya yake yi ba bai isa ya daka mata tsawa bata mayar mishi ba. "Mustapha yaya kuka ƙare dasu Sumy ne da Ramatu, wayata na hannunka ko?" "Tana wajena dukkansu so suke dole sai sun zo asibitinnan sun duba ka. Kasan Allah da ace dukkansu sunsan a wanne asibitin kake kwance da tuni sun ɓaro maka aiki. Amman ni ba wannan ba batun Alhaji Abubakar Baban Bola shi yafi ɗaga mun hankalina in fa bawan Allahnnan kudinshi za'a biya shi Babangida wallahi dukiyar daka tara kab sai ta ƙare kuma bata kai ka biya shi kuɗinshi ba. Nace kenan asirin rufin bakin da akayi mishi tsawon shekaru shine ya karye? Cewa nayi ko zan kuma komawa Inugun ne in samu malamin a sake rufe bakin shi Alhaji Abubakar Baban Bolan?" Kai Babangida ya shiga girgizawa tunda Mustapha ya soma magana, saida ya jefo mishi tambayar ƙarshe ya samu zarafin cewa. "Kaiya Mustapha bakin alkalami ya bushe. Ai tunda Alhaji Abubakar Baban Bola ya samu baki ya fallasa wannan maganar taje har kunnen Kawu Manga da Wawo kaima kasan tabbas Baba Malam yasan da maganar. To shi in an rufe bakinshi su iyayena da ƴan uwana yaya zanyi dasu? Asirina ya riga daya fallasu" Mustapha ya busar da iska daga bakinshi yace. "A_a Babangida kacigari karka sare. Har su Baba Malam ɗin ba sai a sa a rufe musu bakinsu ba? Talauci da tsiyane fa suke shirin tukaroka. Ka bari a sake sabgarnan kaci gaba da dama dukiya" Hannu ya ɗaga mishi hakan ya tilastama Mustapha yin shiru. "Mustapha ba zaka gane bane. Mu ajjiye wannan maganar a gefe ta riga tazo ƙarshe mu dawo maganar Sabuwa zuchiyata jinta nake tamkar zata tarwatse Mustapha. Kai a tunaninka wanne matakin ya cancanta in ɗauka wanne hukunci zata karɓa ita Lolon?" "Hmm ni a nawa muguntar duk runtsi kada ka saketa tunda abinda take so kenan. Kaga duk bala'i dole ta haƙura da wannan ɗan iskan. Ai tunda takai ƙara kotu kada ka sake ka saketa. Sannan in ka saketa Malama fa sakinta Baba Malam zaiyi" Dafe kai Babangida yayi yana kallon Mustapha. "Kotu ta kaini akan me wai?" Nan Mustapha ya bashi labari. Dariyar da tafi kuka zafi da ƙuna yayi. "Zata ga sharri. Lolo zata gane kuranta sai tayi nadamar shigar da wannan ƙara, kazalika sai tayi nadamar tunzurani da tayi. Zata ga makircin lauyoyi kuwa shi kuma farkanta zai sha mamaki wallahi" Sun daɗe sunata tattaunawa da Mustapha kan yadda zasu ɓullo ma lamarin. "Kaga fa wayarta na hannuna amman babu ma chaji farkan nata yaita kiranta tare da tura mata kalmomi daɗaɗa akan ta kwantar da hankalinta. Tana fitowa daga gidanka zasu yi aure. Duk iyakar runtsi kada ka sake a rabu da'ita wallahi" Tari Babangida ya soma babu shiri Mustapha yayi shiru da bakinshi. Babangida yayi juyin duniya Mustapha ya bashi wayar Lolo amman yaƙi fur ya kaɗa ya raya fur Mustapha ya hana wayarnan. Mikewa yayi yai mishi sallama ya fita akan da yamma inya taso aiki zai zo. Yana fita Hamida ta shigo ta nemi waje ta zauna a farar kujerar dake gefen gadon. Babangida kuma yana jingine shiru yanata lissafin halin da zai shiga in Alhaji Abubakar Baban Bola ya ƙwace dukiyarshi, ga shariar sabuwa dole tana buƙatar makiran lauyoyi masu yima mutum sharrin da sai ya tsani shari'a. To su kuma ba ƙaramin kuɗi suke buƙata ba. Wani ɓangare na zuchiyarshi yanata jaddada mishi ya saki Sabuwa kawai ya huta tunda ba sonta dama yake yi ba. Wani shashe na zuchiyarshi kuma sai yaji yayi nauyi. Sosai da sosai MRS BUKHARI
Ina manyan mata masu capacityn suke? ku fito lambarku ce ta fito. Ƴar uwa turaren wuta kike nema nau'ika daban_daban masu musulmin ƙamshi da kama muhallu? Ba itacen banza masu sanya gida ƙauri da hayaki kamar an kunna taohuwar bespa ba. Matso gasu MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI nazo miki da duk abinda kike buƙata na ƙamshi. Kama daga turarukan wuta irin na gidan alfarma. Zuwa humrori iri daban daban masu musulmin ƙamshi da riƙe jiki. Bugu da ƙari muna da turarukan kaya, na fesawa dana turara kaya. Muna da kulaccam nau'i daban daban masu gyara jiki da lausasa fata mata, ga kuma ƙamshi mai inganci. Muna da turarukan tsugunno na musamman masu sirri Hajiyata Muna da room freshener iri_iri Muna da mopping mix masu kama waje. Akwai turarukan kafet dana kujeru. Sannan akwai box _ box setika na Hajiyoyi masu ƙyallin goshi. Muna da Amarya package. Muna da uwargida package Muna da maijego package Muna bayar da sari ko a ƙasar waje kike, muna tura kaya Saudiyya Nijar Ghana Camaron A duk ƙasar da kike kayanmu zai iso miki cikin aminci da yardar Allah. Hajiya akwai Humrar matan aure wannan ta musamman ce. Duk wani abu da kika sani na ƙamshi babu irin wanda bamu dashi a kamfaninmu. Muna da turaruka designer na maza da mata wanda kamfaninmu ke bugawa Hajiya babu inda zaki je ki ci karo da mai irin ƙamshinki. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI TAZO MUKU DA DUK ABINDA KUKE SO NA ƘAMSHI HAJIYA. KUNSAN KANURI MUNE ƘAMSHI DAMU AKE KOYI SIYAN NAGARI MAIDA KUDI MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAYA KO SARI. LAMBAR DA ZA'A SAMENI KAI TSAYE ITACE. Wa.me/2348179523215 SAI NA JIKU IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA BIYAR BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
INA MIƘA SAƘON GODIYA GA ƊAUKACIN MASOYANA NA FAƊIN DUNIYA. MRS BUKHARI TAKU CE.
Sabuwa:. Bani na farka ba sai ukun rana. Da hanzari na miƙe amman jiri sai ya mayar dani na koma kan kujera. Kasancewar yau alhamis yaran suna gida babu islamiyya. "Sannu ummi kin tashi. Ya jikin?" Mardiyya ta faɗa da salon tausayawa. Su Adama ina jiyosu a kitchen kamar ba basu biyu bane. Jiki da sauƙi Mardiyya ina Aɗɗa'u naga kowa shi banda shi?" Sadiya ta fito daga kitchen tace. "Gaskiya Lolo yaranki na da shegen yawo. Yau mune har kogi ammman babu shi babu dalilinshi. Muka dinga zagaye gidajen abokanshi wallahi suma abokan basa nan" Take na sake shiga sabuwar damuwa dan na lura Aɗɗa'u yana da rashin ji sosai kuma yaron bashi da tsoro sam. Ni dai ko da nayi wanka nayi Sallah Allah na roƙa akan Allah ya shirya mun Aɗɗa'u ina roƙon Allah kada Aɗɗa'u ya ɗebo halina ko halin mahaifinshi na sa iyaye a cikin magana " Kafinma in fito Labbai ta biyo ni da jallof ɗin taliyar Hausa taji attaruhu da albasa ga kifi an warwatsa. "Lolo yaya ƙarfin jikin naki? Ki samu ki daure kici abinci zuwa yamma mu leƙa Ƴan asibiti. Naga waccan baƙar kadarar ta dawo daga asibitin mun haɗu da'ita a tsakar gida kinga kallon banzan da take yi mun kuwa? Taci sa'a yau aka sakeni jikina da sanyi da sai naci abu ta kazan ubanta" Adama ce muka jiyo tana rangaɗa mana kira da ji ba lafiya ba, babu shiri na tsallake abincin na fito da sauri. Na'ila na gani shaƙe da wuyan Aɗɗa'u ga bakinshi na fitar da jini. Lafiya meya faru Na'ila. Kai kuma meya same ka sarkin yawo?" Tana jijjiga tace. "Ai dole kice haka kin koya ma yaro sata. Kamar wannan yaron ace har ya iya shigowa ɗakin mutane saɗab saɗab ya yi sata?" Da mamaki na kalleta na dawo da kallona gun Aɗɗa'u. Tabbas ya sata ga rashin gaskiya ɓaro_ ɓaro tattare dashi na gani. Dama bai dena satar ba kenan? "Baiwar Allah ai nutsuwa zaki yi ki mana bayani a tsanake ba kizo kina jijjiga ba. In hau kike ji dashi iyayenki ne a gabanki. Ki sake yaron mutane ko?" Adama tana ƙarashe maganarta ta fincike Aɗɗa'u a hannunta. Ni dai numfashi kawai nake ja da fesarwa. Kudina gasu ya shiga ya satan mun daga shiga banɗaki. Allah yasa yana ƙoƙarin guduwa ni kuma na shigo. Narantse da Allah in ya kuma shiga yayi mun sata na lahira sai ya fishi jin daɗi. Ko da yake tarbiyyar da aka koya mishi kenan. Uwarshi ma da ranar Allah aka kamata a mota" Tana faɗin haka naji wani abu ya tsirgamun Ga yara duk suna wajen sunyi cirko _ cirko. "Ke dakata ƙaramar ƴar balaja'u mai tafe da wando. Ya zaki shigo har ɗakin mata kina faɗa mata magana. Sata dai ai ba a kanshi aka soma ba. Kuma da kike cewa an kamata a mota ke a kamaki mana. Ya yi satan kuma ya saci banza" Ai Labbai bata rufe baki ba Na'ila ta shiga ɗaga murya tana kwaroroto dan mutane suji dama nasan da biyu, amman ɗan kuka shi ke jama uwarshi jifa. Na'ila kowa yasanta ba ƙatamar munafuka bace ita da ƙawarta Hamida. A guje Ƴar Shuwa ta leƙo tana tambayar meke faruwa ai kuwa Na'ila ta faɗa mata. A lokacin har Maman Safara,u ta shigo. "Uhm Allah ya kyauta. Sata yaro kamar wannan? Ashe duk ƴan canjinan da muke ajjiyewa mu rasa shine yake sacewa. "Ya sata dan uwarki kiyi abinda zaki yi in baki bar wajennan ba zaki sha mamaki" Inji Adama. "Hehehe me zanyi kuwa. Kuji da sakin duk da akai muku itama Lolo tana hanya dan baku isa kun tare mana a gida ba" Nayi mamakin yadda akayi Ƴar Shuwa tasan auren Adama ya mutu, gara ma na Labbai tunda anyi rikici harda motar ƴan sanda. "Ayi haƙuri Labbai dan Allah kada ku sake cewa uffan. Ke kuma maman Fatima ki koma ɓarayinki. Na'ila tunda dai kinga kuɗinki sai kiyi haƙuri duk a taru ayi haƙuri " Tsaki yar shuwa tayi ta wuce fuu. Adama ta tasanma zagi Na'ila kuwa saida ta dinga zage_zage tukunna. Ni tana zage_zagenma na zame na shiga ciki na dira a wuyan Aɗɗa'u kamar Allah ne ya aikoni har gwara kanshi a bango nake yi. A tunanina ya dena sata tunda muka baro tsohon gidanmu. Sata babu irin wacce Aɗɗa'u bayayi har atampa ya sata ya siyar ya kashe kuɗin. Nasan jarabawace tunda guda nawa yaron ma yake. Su Maman Safara,u ne suka kwaceshi a hannuna duk goshinshi ya fashe, ni kuma sai haki nake yi Maman Safara,u da Labbai ne suka garzaya dashi kemis ni ko dana shiga ɗaki sai kuka, na daɗe ina rera baitukan kuka kafin nayi shiru. Adama na zaune tana cewa in gode Allah a hakanma, Su Mardiyya kuwa kowa ya shiga taitayinshi, ban fiye dukansu ba amman inna tashi dukan yaro ni saina fitar mai da jini hankalina yake kwanciya. Da sallama Labbai ta shigo. "Lolo ki daure kici abincin ki tuttura nasa Mardiyya ta kawo miki tea wancan yayi sanyi. Kinga biyar har tayi mu samu muje asibitinnan ko?" Ko magana na kasa yi, ina gani sukai wanka duk suka saka suturuna. Da ƙyar nayi ma abincin loma uku tean ne ma na rufe ido na shanye na tashi. Sallah nayi na sake kayana muka nufi asibiti harda yaran duka, Aɗɗa'u naso barinshi a gida amman da nai wani tunanin dole na ja hannunshi muka tafi asibitin. Hamida na ciki tana ba Babangida tea muka shigo. Haɗa idanu muka yi dashi na wani haɗe girar sama data ƙasa na nemi waje na zauna. Su Adama ma da suke yi mishi ya jiki babu na wacce ya amsa. Yara dai sun yi mishi ya jiki ya amsa musu ciki _ ciki. Hamida bata kula kowa ba, babu wanda yabi takanta in banda yara da suka gaisheta. Jigum_jigum muka zauna na kusan minti talatin. To Labbai ku taso muje ko magriba har tayi" Mun tashi kenan muka ga an turo ƙofar an shigo Mustapha ne ya soma shigowa abokanshi suka mara mishi baya. Suna ƙarasa shigowa nayi ficewata su Adama ne suka tsaya aka gaisa kafin suka fito suka same ni muka wuce gida. Sai bayan isha muka shiga gidan. A tsakar gidan muka tarar da Kawu Manga da Wawo, da Ƴar Shuwa a tsaye tana miƙa ma Wawo key kamar dai na mota ne. Ƙarasawa mukayi aka gaisa. Kawu Manga yake tambayar meya samu Aɗɗa'u. Kafin in yi Magana mandiya tace. "Sata ya shiga yayi a maƙota shine matar tai mishi irin wannan dukan." Jim yayi muma duk mu kai shiru kamar ruwa ya cinyemu. "Allah shi kyauta. Ai sai a ci gaba da bashi rubutu yana sha ko Allah zaisa ya dena" Wawo kuwa girgiza kai kawai yake yi. A sanyaye mukai musu sallama muka shige ɓarayina. Duk bamu zauna ba Alwala kowa ya shiga yi, saida akayi Sallah suka soma kiciniyar cin abinci kuma. Ana gamawa yara suka tafi ɗakinsu, muma muka kwanta Ni dai juyi kawai na dingayi har iya awannin da ban isa sani ba.
Washegari:. Bayan hantsi muka shirya ni da Labbai Adama yaranta sunzo wajenta dama tace ita ba zata je wani asibiti ba. A can muka tarar da ƴar Shuwa da Hamida, Kawu Manga da Wawo ma suna ɗakin muka shigo. Ba'a ko gaisa ba wasu mata su su biyu suka shigo da ganin kamanninsu uwa da Ƴa ne, ga yarinya da bata wuce Ƴar wata takwas ba a riƙe a kafaɗar wannan dattijuwar, wata kyakkyawar matashiya na biye da'ita "Ohh Babangida ashe haka jiki ya tsananta ji hannunka yadda ya aune" Inji wannan dattijuwar. Ni yaron dake riƙe da hannunta ma nake kallo yaro mai kama da Babangida tamkar an tsaga kara. To su kuma suwaye waɗannan na faɗa a raina Bani kaɗai ba harsu Hamida wannan ɗan yaro suke kallo. A murya kawai na fahimci Babangida bashi da gaskiya yadda duk ya daburce yana zare idanu. "Bayin Allah ina wuninku, yaya kuma me jikin?" "Jiki da sauƙi gashi nan" Hamida ta ba dattijuwar amsa a yatsine. "Baby yaya ƙarfin jikin naka kaga yadda ka rame kuwa? Na kira Mustapha sai yi mun hanya hanya yake yi. Ni kuma ina ganin lokaci yayi da zan bayyana kaina ga iyalinka sabida tsoron halin mutuwa ko dan sabida wannan yaron" Inji wannan matashiya. Mu dai duk munyi tsit muna sauraren ikon Allah Dattijuwa tace. "Gaskiya ne kam. Ni kaina sai bayan kwanciyarka a asibiti nayi nadamar biye muku da nayi a matsayina na uwa. Yarinyarnan tun sanda labarin rashin lafiyarka ya sameta take cikin damuwa sabida abokanka kab sun kasa faɗa mata a wanne asibitin kake." Babangida ya kalli su Kawu Manga da sukai tsuru_tsuru ya dawo da idanunshi kanmu kafin ya runtse idanunshi tare da dafe kanshi da hannunshi mai lafiyar" "Hajiya mu bamu gane ba fa. Ku ɗin su waye ne daga ina?" Cewar Wawo da kanshi yafi na Kawu Manga daurewa. Ni kam tuni na gane matarshi ce tabbas ko kaffara babu. "Bawan Allah ka tambayeshi waƙa a bakin me ita yafi daɗi ai. Ke Ramatu jeki ki zauna acan baki fiye juran tsaiwa ba." Kusa dani da Ƴar shuwa tazo ta zauna tace. "Sannunku" Tana mana kallon banza. Yauwa sannu" Na amsa mata. "Kai Babangida su waye waɗannan matan, menene alaƙarka da me kiranka Baby?" Ya daɗe sosai yana tauna maganar kafin a sanyaye yace. "Matatace Kawu kayi haƙuri " Salati su Hamida suka shiga yi tare da tafa hannaye. Ni kuwa sai murmusawa nake yi. Ba ƙaramin tashin hankali da damuwa Ƴar Shuwa ta shiga ba. "Matarka, yaronma da cikin duk naka ne kenan naga kamar ciki ne da'ita ai?" Kai kawai ya ɗaga ma Kawu Manga. Shiru yayi yana nazari kafin yace. "To ai Shikenan babu damuwa tunda dai aure kuka yi. Waye maɗaurin auren to?" "Baba na shago ne" Kawu Manga yayi shiru ya kasa cewa komai Wawo kuwa inya kalli Babangida sai ya kalli Kawu Manga. "Hajiya gara da Allah yasa ku kai tunanin zuwa tun wuri ba har saida lokaci ya ƙure muku ba." Wannan dattijuwar tace. "Hala mahaifinshi ne kai ko?" "E uba nake a wajenshi" Sai tace. "Alhamdulillah ga Ramatu itama a bata ɗaki a gidan mijinsu ta zauna a haɗu ayi jinyar Babangida tare da'ita. Gidan da suke ciki ma Wanta ya karɓe har ya siyar sakamakon wani iftila'in daya afka mishi. Ni kuma bazai yiwu taci gaba da zama a gidana ba tunda dai mijinta yana da gida. Dama kuma ba da son ran dangin mahaifinta aka yi auren ba. Ganinta a gida da akeyi sai aka soma tsogumin ko aurenne ya mutu" Kawu Manga yace. "To yayi. Ke Sabuwa in zaki tafi ki tafi da wannan baiwar Allahn ta zauna a turakar Babangida tunda a halin yanzu babu inda zata zauna zuwa a sallamoshi" To Kawu in sha Allah" Na faɗa da ƙarfin guiwata. "Keyn turakar a hannun wacce matar taka yake?" Babangida tsabar kunya ne, ko meye yama kasa ɗagowa ya kalli kowa yace. "A hannun Maman Fatima na barshi" Kawu ya dubi Ƴar shuwa yace. "Kin yana tare dake ne, ko yana gida?" A kumbure tace. "Yana gida" Bai damu da kumburinta ba yace. "In kin koma sai ki ba Sabuwa keyn. Wawo da Ramadan ku taso muje. Matanshi zasui jinyarshi su dinga yin kama_kama" Ai kuwa suka haɗu su uku suka fice, da gani a ƙule Wawo yake ainun dama gashi da faɗa. "To Ramatu da Alkhairi in kin isa gidanki mayi waya ki mana kwatance ko. Babangida Allah ya ƙara sauƙi" "Ameen nagode Mama" Wannan dattijuwa ta fita Amarya ta bita a baya. Yaro kuma yana wajen Babangida a yanata mishi kwarance "Hmmmm. Hmmmmm. Hmmmm" Shine abinda Ƴar Shuwa take ta nanatawa idanunta sunyi jawur dasu. Wallahi ni kuwa raina fes tamkar audiga. Labbai muje masallaci muyi Sallah sai mu ɗau haramar gida ko?" Na faɗa tare da miƙewa. Kafin mu fita Amarya ta dawo, mu kuma muka fice. "Lolo haka mijinku yake kamar bunsuru wajen son mace?" Haba Labbai ai sai dai ki kirashi Ayu baban bunsurun kenan. Ni wallahi abun yayi mun daɗi. Ƴar Shuwa ai gani take ta mallake Babangida sai yadda tayi dashi. Bata san ya fita cin kai ba, a tafin hannunshi take. Ya kika ga Amarya kyakkyawa da'ita gashi a doke ba dokuwa zata yi ba ba" Dariya muka saka. Har muka isa masallaci bamu dena dariyar ba. Ko da muka idar da Sallah a hanyarmu ta komawa cikin asibiti zancan dai muke yi. Muna tura ƙofa muka tarar ana gurmi, wai damme Amarya da zuwanta zata shiga tattaɓa Babangida a gaban matan gaban goshi. Ita kuma Amarya tace ai mijinta ne itama. "Ya isheku haka ko, kasheni kuke so kuyi ne kome. Ke Maman Fati me yasa bakya son a zauna lafiya ne?" Ƴar dariya ce ta subuce mun da naji yau babu Habibaty sai Maman Fati "Maman Fati ka kirani yau gatsau Jannaty sabida wannan abun?" "Wacece Abu? Ai wallahi nafi ƙarfin abu ke da gani kinsan ni dake babu haɗi" Da ƙyar dai sukai shiru sai da ya daka musu tsawa sannan suka nutsu. Amarya mu zamu tafi, kin shirya tafiya ne yanzu?" A wulaƙance tace. "Ni anan zan kwana kije kawai" Tana faɗin haka ni da Labbai muka juya muka fice abinmu. Ya suka ƙare ohon musu dai.
Baba Malam: Yana zaune a zaure gashi ga Malama Babba da Malama ƙarama da Wawo, da Kawu Manga. Kawu Manga ya kwashe komai ya faɗa musu ya ɗaura da cewa. "Kai tsaye wajen shi Baba na shago muka je. Ya tabbatar mana shekara ɗaya da kusan rabi kenan da ɗaura auren Wannan shine abinda yake faruwa a gaskiya na kusan cire hannuna akan Babangida koma ince na cire hannun nawa. Shi wanne irin yarone?" Malama Babba dake ta faman salati sai ta sau kuka. "Yanzu ashe a duniya akwai abinda Babangida zaiyi ba tare da ya shawarceni ni mahaifiyarshi ba? Wannan yaro ina zansa baƙin cikinshi?" "Ai tukunna ma Babba. Ba dai kina bayan rashin gaskiya ba, in dai kuka ne ai bakiyi ba. A baya irin kunyar da Babangida ya saka mu ta wasa ce. Bari in faɗa miki ki kuma sani batun Sabuwa data maka ku a kotu. Kisa a ranki muddin alƙali ya saki Sabuwa tamkar ke ya saka in baki sani ba ki sani igiyar auren Sabuwa a ƙulle suke tare suke tafiya da igiyar taki auren. Ai sanan kinsan da zaman wannan sharaɗin Kuma daga yau ban amince Babangida ya sake tako ƙafarshi ya shigarmun gidana ba. Na zame shi daga cikin jerin Ƴaƴana ko mutuwa nayi kada yazo kan gawata." Salati Kawu Manga ya shiga yi ganin yadda Malama Babba take shiɗewa. "Kawu mu kaita asibiti kada ta mutu. Malama Babba" Wawo ya shiga kiran sunanta. Babu shiri suka kwasheta zuwa asibiti cikin rashin hayyaci. Malam ya runtse idanunshi wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mishi. Ya lura Babangida shine zaiyi ajalinshi da baƙin cikinshi. Sai kace shi kaɗai aka haifa duk yabi ya fitineshi, bashi da aiki sai jaye_jayen magana tun yana ƙarami. A daddafe ya rarrafa ya shige turakarshi ko gani bayayi. Jin har an kira Sallah a masallaci Baba malam bai fito bane Idirisa ya shiga turakar ya samu Baba malam a ƙasa babu yadda yake. Kan kace me mazan gidan suka rufu a kanshi. Su Wawo suna asibiti aka bugo musu waya ana sanar dasu halin da Malam yake ciki. Babu shiri Wawo ya baro asibitin ya bar Malama ƙarama acan da Sa'a da bata jima da zuwa ba. Malam dai anyi juyin duniya a kaishi asibiti yaƙi fur. Dole sai likita aka kira mishi har gida yazo ya duba shi. Jininshi ne ya hau sosai da sosai. A wannan rana iyalan gidan Malam Baba basu runtsaba a cikin wannan dare da ya shiga tarihin daren da Babangida ya tashi hankalin kab ahalin gidan. Gashi a wannan karonma silar Babangidan ne.
Babangida:.
Shima yana asibiti jikinshi ya tashi sakamakon fargabar abinda kaje yazo. Yasan matsawar Baba Malam yaji abinda ya aikata tamkar sake rura wutar ƙiyayyarshi yayi a zuchiyar Baba Malam. Hatta Malama Babba da a kullum burinta ta kareshi yasan in taji wannan labarin zai ruguza mata zuchiya. Wannan abunne duk suka taru suka haɗe mishi. Gashi da ƙyar ya kori Ƴar Shuwa da Hamida a asibitin suka bar Ramatu ta yi zaman jinyarshi na kwana ɗaya. "Baby jikinne yake damunkane? Wai garinma yaya kaji irin wannan ciwon ne?" "Kar ki damu. Ki daure ki kiramun likita hannuna tsami yake yi mun" Miƙewa tayi ta fita, yabi bayanta da ido kawai. Takamaimai ya rasa tunanin me zaiyi ma zuchiyarshi a cunkushe take sosai. Haka dai wannan daren ya kasance musu dare dubu da ɗaya 🤣🤣
MRS BUKHARI Babangida yana ruwa
IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU SHAFI NA SHIDA BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GA ƘARIN SHAFI ALLAH YASA ZUKATANKU SUYI SANYI.
SABUWA:.