Kenza eBookz

Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 24

Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 24

Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 24: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 24. Wasu hawayen takaicine suka gangaro Mata tana sake qanqanmesa tana…

4,476 words

Wasu hawayen takaicine suka gangaro Mata tana sake qanqanmesa tana hanasa dagowar dayekeson yin sbd kada yagane Mata jiki..

Kuka Mara sauti tafara sbd tun farko batasan abinda ya rabata da rigar jikintaba, Yariga yagantama kila.

Kuka Mara sauti takeyi tana Jin zafin haduwar jikin nasa da nata Amma bazata iya barin yagantaba ko yayane.

Rigarsa yasaka hannu daya ya fara balle maballanta Yana yiwa Amal din wani kallon daya sata sake Shiga tashin hankali da firgici da mamaki.

Yana Gama balle maballan ya zare ahankali take murdadden lafiyayyan jikinsa ya bayyana batareda ya zare hannu dayanba sbd anan ta manne Masa ya kalleta ganin hawayenta na tsananta gudu Ya sake Kai bakinsa kunnenta ahankali yace,

"Kinafa sukarmun jiki da......da Ido ya nuna Mata kirjinta Yana Mata wani shegen kallo......

Da sauri ta qarasa fizge rigar jikinsa ta rufawa jikinta tana tashi jikinsa da sauri wata irin kunya da baqin ciki na cikata.

Wani qayataccen murmushi yasake Mata a karo na farko sbd yanda tayi din kamar ba wadda tagama manna Masa su a Daren ba batareda tasaniba.

Saukowa yai daga gadon Yana kallon time ya wuce toilet ba Riga ajikinsa dagashi Sai dogon wandon kayan baccin.

Brush yayi da sauran abubuwanda zaiyi kafin yayi wanka yafito daureda towel ash a qugu jikinsa na bayyanarda ruwan wankan dayayi.

Qin juyowa tayi ta kallesa tunda taji fitowarsa tareda sanyin qamshin Aesop dinsa na wanka daya gauraya dakin.

Tanajin ya nufo inda take tayi saurin saukowa gadon ahankali batada wani qarfi ta zagaya ta daya bangaren ta shige toilet ta rufo kofar.

Shiryawa yayi cikin navy blue Armani's da sai tsadaddun takarminsa da agogunansa masu tsadar gaske yayi order na plain tea da shuga free cookies sbd bayason zaki sosai.

Sama sama yaci ya kunna wayarsa yakira al'amin ya fice daga dakin bayan yasaka daga babban boutique din Echelon din su Kira bayan mintina idan ta fito toilet tafada musu kayan datake buqata akawo Mata.

Ficewa yayi ya nufi inda su al'amin ke jiransa.

Tunda ya fito lifter Al-Amin yayi Masa kallo daya ya sauke Kansa ganin yanda komai nasa yake a kame da ajinsa kamar yanda yake Amma idanuwansa sun Dan sauya alamar rashin isashen bacci kokuma wani aikin daban.

Barka da fitowa yai Masa Yana Masa Ina kwana tareda fara Koro Masa bayanin andawo da meeting din cikin hotel din sbd rashin time da Kuma rashin jinsa.

**Ta Jima cikin toilet din tana gasa jikinta yadan sake Mata marar ma sbd magani dakuma tasamu yafara zubowa sosai sai ta Dan sake mata.

Tun acan ta sako pad dinta ta fito sanyeda wata qatuwar bathrobe din daban ta Dan fara fitowa ahankali ganin baya dakin saita qarasa fitowa cikin sanyi da nutsuwa tazo gaban mirror ta zauna tana kallon fuskarta datayi fayau.

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali jikinta ba qarfi ta dauko handbag dinta da batasan waye ya dauko Mata ba ta bude ta dauko wayarta dake kashe ta kunna ahankali.

Kafin tafara Kiran kowa Bilkisu tafara Kira tana dauka ahankali murya ba qarfi tace,

Bilkisu mommy ta kiraki?

Eh takira jiya tace Bata samun wayarki.

Wani numfashin takaici ta sake tace,

"Me Kika ce Mata to?

Dan Sosa Kai Bilkisun tayi tace,

"Cewa nayi Kun tafi asibiti tareda Sir.

Wani qaramin tsoki takuma sakewa a ahankali kafin tace,

"Idan tasake kiranki karki fadawa kowa baa gida na kwana ba, Kuma karki fadawa kowa shine ya daukeni din, Kinji??

Eh"tace tana sake tambayarta jikin nata.

Naji sauki Zan dawo yau, Kosu mommy sundawa fa karki fadawa kowa nafada Miki.

Insha Allah naji,Allah ya dawo daku lfy.

Kashe wayar tayi tana cewa,

"Nida waye?bayan nace kada kisake fadan Ina guri daya dashi.

Bata rasa Turarenta Daman koyaushe a handbag dinta Dan haka nata Turaren tayi amfani dashi ta kasa Sha ko Mai.

Boutique Suma sun Kira tace kawai su kawo mata dogayen riguna idan akwai,

Akwai din Amma basuda tsayi half ne hakama masu tsayin yawanci basuda hannuwa Dan Haka Dole tasa aka kawo Mata Riga da wando masu fadi sai doguwar Rigar daya mai tsayi har qasa Amma batada hannu.

Riga da wandon ta saka taci cookies itama da tea Mai kauri Babu shuga itama.

Tana gamaw tash magani takira su mommy wainda basusan inda take dinba sbd tafiyarta da AQEEL ASAD wani tunani ne da Basu taba kawowa ko kusaba.

Sama sama dukkaninsu sukai magana da ita sukayi Mata sannu kafin sukai sallama.

Id card dinta tayita dubawa cikin Jakarta bata ganiba sbd siyan ticket taso Yi ta waya ta tafiyarta sbd takasa yarda da itace ta kwana a guri daya da Wanda bazata taba iya karban aurensaba.

Bacci tafara dan Yi daga zaune guraren 3 sai gashi yadawo a Dan gajiye Dan Haka taqi bude idanuwanta tana jinsa Dan bata buqatan magana dashi.

Kallo daya yayi Mata ya fahimci idonta biyu sbd yanda ta Kama jikinta.

Tubewa yayi yayo wanka ya fito daureda towel ya shafa duk abinda zai shafa ya saka milk Riga da wandon Prada shima masu Fadi da kauri Ba zato taji qamshinsa yashiga hancinta ahankali,

Qin bude idanuwanta tayi Sai Jin fuskarsa tayi ta shafi wuyanta Da qarfi ta sake rintse idanuwana tana qin budesu.

"Yaya jikin?? "Ya Dena Miki ciwo?

Kasawa tayi ta bude idanuwanta tareda janyewa daga inda yake din batareda ta juyoba ta kallesa qamshinsa kawai neman yagama cika kanta da hancinta.

Tashi tayi zata bar gurin ya dawo da ita ta fada kan qafafunsa ya zira Kansa cikin wuyanta ya shaqi qamshinta ya lumshe fararen idanuwansa a hankali yace,

"Kinsan meyene matsalan ciwonki??

Shiru tayi Masa tana son tashi daga qafafun nasa Ya riqe hannuwanta biyu cikin nasa ya sake miqa Kansa cikin kafadun wuyanta yace,

"Kinason maganin wannan wahalan da kikesha kike wahalarmun da Mamina gurin neman magani????

Juyowa tayi ta kallesa batareda tasan tayi hakanba sbd ciwonta wani babban lamarine datake neman warakarsa idan har yasan inda zai samo Mata magani zataso hakan Ita kadai tasan azabar datakeji Duk Mai ganinta saidai ya tausaya Mata Amma basa gane abinda takeji din.

Ahankali cikin kunnenta Yakuma furta,

" kinaso???

Jikinta na mutuwa batareda tasan abinda yake nufiba ta daga Kai ahankali tana Dan rintse Idon fuskarsa dake cikin wuyanta.

Juyo da fuskarta yayi suka fuskanci juna yana matse fuskokinsu ahankali yasake cewa,

"Kin tabbata Yar Uncle??

Gyada Kai tayi ahankali itama tana sake rintse ido sbd idanuwansa dake yawo Akan fuskarta.

Wani lalataccen murmushi yasake yana zura hannayensa ya zagayota yana Dora goshinsa akan nata dogayen hancinsu na gogar juna qasa qasa da wata muryar data sakata bude idanuwanta akansa yace,

"Namiki Alqawarin Baki ko ayau Kika Gama wannan din,tunda kedai kikace kina buqatan Mijinki.........

Zaro idanuwanta tayi cikin mummunan tashin hankalin abinda ta fahimci Yana nufi.,

Da sauri cikin zafi ta miqe wata irin kunya da haushin kanta na rufeta..

Tana jinsa Yana cewa,

"Kinfasa ne? Kokuwa zuwa can din ya Miki nisa......

Kukan da batasan na meneneba ta fashe dashi tana jefa Masa pillow din dake dayar kujerar dakin sbd kunya da takaici.

Riqe pillow din yai tareda hannunta Yana wani shegen murmushi mai nutsuwa yace,

"Bazaki jira Mami tadawoba kikeson maganin????

Wani kukan tasake fashewa dashi tana kokawa qwace hannunta Dan yagama Kasheta da ranta da wannan maganar tasa.

Ganin da gaske takeyin kukan ya janyota zaiyi magana ta qwace ya nufi toilet ta shige tana tunanin bazata iya sake kwanaba agurin yau wlh gida takeso Dole ya maidata bama tareda kowa yasan sunyi tafiya tareba har musamman su mommynta bazata taba son wani yasan da hakanba. ##MAMUH#

MASU FIDDAMUN BOOK DAGA AREWABOOKS KUNYIMUN NE SBD CUTATARWA DAN HAKA BABU ABINDA ZANCE MUKU SAI ALLAH YA YAYE MUKU QYASHIN CIGABAN WANI YAKUMA SHIRYAKU IDAN KUNADA RABO YASA KU GANE KU DENA.

INTRODUCING UNIQUE AND AFFORDABLE PART-TIME DIPLOMA AND DEGREE PROGRAMMES IN HEALTH RELATED COURSES.

The Directorate for Consultancy Services and Continuous Education of the Kazaure School of Health Technology, Kazaure, Jigawa State, Nigeria wishes to inform the general public that it now offers the underlisted Health courses at its Kazaure centre.

DIPLOMA

1. Dental Surgery Technician

2. Medical X- Ray Technician

3. Health Information Technician

4. National Diploma Biomedical Engineering

5. Public Health Technician

6. Junior Community Health Extension Worker (J-CHEW)

7. Community Health Extension Worker (RE-TRAINEE)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Interested applicants can call the following phone Numbers for the application forms.(WhatsApp) 08035298851, Calls Only 07066542055

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥 Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma

*KI KULANI*🔥 Miss xoxo

Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171 Maryam sani Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 51 Tana Shigewa toilet din ya saki wani boyayan murmushi wayarsa ta nuno haske Alamar shogowar sako ko Kira,

Juyowa yayi ahankali ya kalli wayar yaga sunan Al-Amin ne Dan Haka ya dauka tareda miqewa tsaye yaje bakin Makeken window dayake dakin Yana amsa wayar cikin nutsuwa.

Bayani ne akan angama komai sun saka hannu dayan kamfanin akan kasuwancin da sukazo Akan kullasa.

Ajiyar zuciya ya sauke Mara karfi Yana cigaba da magana..

Bude kofar toilet din datayi ne yasashi Dan kallon kofar ya kalleta Da alamar kukan datayo duk a fuskarta datayi ja.

Cigaba yayi da wayar Yana kallonta ta nufi inda handbag dinta take ta bude ta dauko hanbag dinta tana sake duba id card dinta Ticket zata siya gida zata tafi.

Gama wayar yayi ya tsaya Yana kallonta cikin mamaki batareda yayi magana ba yakoma kan kujera ya zauna ya Dora kafa daya kan daya Yana kallonta.

Duk tagama duba jakar batagansaba Dan Haka ta rintse Ido tana danne zuciyarta ta juyo ta fuskancesa batareda ta kallesaba ahankali tace,

"Id card Dina fa??

Bakin da yayi maganar ya maida idanuwansa akai ya kalla kafin ya maida akan idanuwanta daseke qin kallonsa.

"Gashi zo ki karba abinki" yafada yana kallonta.

Batareda ta kallesaba ta nufosa ta miqa hannu ya Bata,

Hannunsa ya miqa ya kamo hannunta yasake janyota jikinsa ya zaunar kan qafarsa Yana shinshinata kamar wani maye ya lumshe fararen idanuwansa ahankali cikin kunnenta yace,

"Duk zafin kan Nan naki bakida wayo?? Shikenan daga nace ungo saikizo batareda kin duboba.

Janye kunnenta tayi sbd lips dinsa dake taba fatar kunnenta gurin maganar Gashi riqo me kyau yamata takasa qwacewa.

Sake dora lips dinsa yayi kan kunnen nata Wani masifaffen shock yashigeta ta rintse idanuwanta ahankali da qarfi,

Cikin Yar rawar murya Mara sauti sosai tace,

"Ni id card Dina nakeson kabani.

Da wata irin murya qasa qasa yace,

"Nine id card din, Yanzu kinada wani id dinne bayan ni?

Gani Me zakiyi da Id din?

Rawa jikinta yafara yi tana sake rintse idanuwanta tareda motsin qwacewa daga jikinsa Amma ya zagayeta da hannuwansa ne gabaki daya akan qafafun nasa tareda manneta da jikinsa ta bayanta ya saka Kai cikin wuyanta acan ya Dora bakinsa kan kunnenta.

Ahankali Yana sake zagayota da kyau tareda hade tannayensa da nata saida yasake shafar kunnanta da lips dinsa ya lumshe Ido can qasa yace,

"Me zakiyi da Id din uhmmm??

Batasan ya akai ta basa amsa idanuwanta a rufeba da cewa,

"Gida Zan koma.

Muryarta tasashi Dora lips dinsa kan kunnenta ya sakar Mata wani kiss daya sata qanqame hannunsa dake cikin nata ta sake rintse Ido.

Qamshinta ya sake cusa Kansa cikin wuyanta ya shaqa Yana narkewa jikinta yace,

"Mami Bata Nan bazan bar uwar babies Dina taje tayi zaman kadaiciba Ko gidana kike nufin Zaki koma ne???

Bude idanuwanta tayi cikin sauri tareda juyowa gabaki daya tana kallonsa da mamaki da fushin abinda ya fada harma da kunya" Wai uwar babies dinsa,Kuma gidan take son zuwa"

Wlh yana cutarta.,dauke idanuwanta take neman Yi daga Kansa ya matsota jikinsa kirjinsu ya manne yayi wani irin lumshe Ido Yana saukar da ajiyar zuciya Mai sanyi kafin ya bude idanuwan nasa Yana shafa wuyanta da hannunsa 'daya, 'dayan Kuma ya manneta jikinsa dashi.

Wani irin kallo yake Mata Yana shafa wuyanta Yasake Kai Kansa cikin wuyan ya shago tareda goga Mata fuskarsa a fatar wuyan Ta hadiye wani numfashi Mai zafi tana motsawa ahankali...

Kirjinta ya dago ya kalla ahankali yace,

"Kece dai Kika juyo da kanki kika....

Batasan lokacinda ta daga hannuwanta duka biyu ba ta rufe Masa Baki Wanda hakan ya sake bawa kirjinsu hadewa dakyau..

Wani kallo yasake jefa Mata bakinsa na rufe da hannuwanta masu taushi da Ido yace Mata,

"Kashewa Mami 'da zakiyi??

Jin tayi kanta na namen bugawa da maganganunsa Bata San me zatayiba sai kawai tasake fashe Masa da kuka tana janye hannuwanta daga bakinsa...Bata Gama aje hannunba ya kamo fuskarta da hannuwansa biyu ya Dora bakinsa kan nata tareda zura harshensa Kai tsaye cikin bakinta ya fara laso yawunta ya hadiye cikin bakinsa Yana lumshe Ido kafin yafara kissing dinta cikin wani irin sanyin salo Yana sake manneta da jikinsa.

Kamar mutuwar zaune tayi daga farkon Jin bakinsa Anata Saidataji yanda yaka kissing Yana Shan bakin nata yasata fita hayyacinta cikin tsoro,fargaba,tashin hankali da fushin ba zata.

Ta bangare daya kasa motsawa tayi bare ta qwace kanta sbd wani abune yake faruwa da ita Wanda Bata taba yiba a rayuwarta, Ita namiji ba gabaki daya rayuwarta jikinsa Bai taba ta'ba nataba.

Hawayane suka gangaro Mata daidai lokacin Kuma Kira yashigo wayarsa wadda take cikinsu Dan Haka vibrating dinsa yasashi sakinta ahankali Yana kallon fuskarta datai ja sbd kunya da kuka.

Numfashi ya sauke ahankali Mai sanyi kafin ya juya ya dauki wayar yaga sunan Maminsa.

Ajiyar zuciya yasake saukewa tareda Dan gyara muryansa dayasan Dole ta sauya kafin ya daga wayar a hankali cikin nutsuwa yakira sunanta Yana cewa,

"Aslm alakm Mami barka da dare..

Da sauri Amal ta dago ta kalli wayar kafin tadan kallesa shima ita yake kalla Yana cigaba da wayar.

Haj Zainab amsa gaisuwarsa tayi tareda tambayarsa aiki da tafiyan dayace Mata yayi tace,

"Tun dazu Ina Kiran wayar Bilkisu Bata Shiga na Amal ma yanzu inata Kira Bata daukaba Daman zatayi magana ne da likita anjima zai Dan Mata tambayoyi idan Babu matsala.

Ajiyar zuciya ya sauke Yana kallon Amal din datayi raurau da fuska tana hawayen kada yafadawa mommyn tana taredashi Dan Allah.

Nutsar da muryarsa yayi cikin kwanciyar hankali da nutsuwar dayansaba magana da ita yace,

"Karki damu Mami basai tayi magana dashiba insha Allah zaa Samar Mata magank idan baiyiba zataje taga likatan daga baya.

Ajiyar zuciya Haj Zainab tayi cikin Dan Jin Dadi tace,

"Allah yasa adace da Wanda zaka bincika din Idan baiyiba nafison zuwanta din Daman akan wayar sbd ba komai zaa ganeba.

Jinjina Kai yayi ahankali Yana kallon Matarsa dake kan jikinsa yace,

"Hakane Mami insha Allah zaa Dace ma.

Cikin Jin Dadin zancensa da yanda ya shiga zancen tayi sallama dashi tana Jin hankalinta na kwanciya da zuwan da zai bar Amal din tayi taga likita.

Yana Gama wayar ya ajiye Yana kallonta hawayenta na sake gangarowa Tama rasa ya zatayi da rayuwarta.

"Kinji Mami ma tanason ki warke Dan Haka ki.......

Tashi tayi daga jikinsa da sauri batareda tabari taji qarshen abinda zaiceba Kunnuwanta bazasu iya sauraran abubuwansaba.

Toilet take kokarin komawa batareda tasan me zatayoba Tana Dora hannunta kan kofar toilet din yafada Mata abinda yasata fasa shiga toilet din ta juya ta nufi window ta tsaya tana kokarin dedeta numfashinta dake fita da sauri.

Alwala yayo yafito sbd lokacin sallar magrib dayayi Yana fitowa ya fice dakin ya nufi inda zasuyi sallah dasu Al-Amin.

Bayan sallar magrib Bai dawoba Saida yai sallar ishai daganan suka fita wani gurin shida Al-Amin.

Itama ganin Bai dawowab tanata jiran dawowarsa ta tabbatar Masa da gida takeso su Bata id card nata Amma Bai dawoba.

Qarfe Tara tashiga toilet tayi wanka da ruwan zafi ta fito ta shirya sharp sharp cikin Riga da wando na bacci masu tsantsi data saka aka kawo Mata daga boutique din cikin gurin sbd Bata iya bacci da Kaya masu nauyi sosai.

Noodle tayi order taci tasake Shan magani da plain tea tayi brush tazo tazauna kan sofa tareda rufe jikinta da abin rufa tafara gyangyadi a zaune sbd maganinta akwai Mai Dan saka bacci Bata jimaba agurin bacci ya dauketa.

Sai after 10 yashigo bayan sun qarasa kammala duk abinda sukazo Yi.

Kallonta yayi yaga yanda ta takure tana bacci sbd kada tahau gadon yazo ya hau.

Toilet ya wuce Saida yayi wanka dasu brush yafito ya shirya shima cikin Riga da wandon bacci masu santsi black Kamar nata yaso tada ita taci abinci saiyaga alamar taci sbd cup din daya gani ajiye na tea datasha bayan Gama cin abinci.

Daukanta yayi ahankali ya nufi gadon da ita ya kwantar kafin shima ya hau ya kashe musu wuta tareda addua ya shige jikinta kaman baby ya kwanta shima ba jimawa baccin ya daukesa.

Bacci tayi sosai Bata farkaba Ko asuba Shi kadaine ya farka yayi sallah da adhkars dinsa yagama yadawo ya kwanta tareda sake Shigewa jikinta.

Qarfe tara da mintina ta farka tajisa cikin jikinta ya lafe Yana bacci hankalinsa kwance.,

Mamakin ganinta kan gadon yasata saurin duba jikinta taga rigarta tana jikinta Ta saki wani boyayyan numfashi tareda janye jikinta ta sauko gadon ta nufi toilet tayi brush da wanka ta sako pad ta fito da bathrobe ta nufi mirror Sharp sharp tashirya sbd kada ya farfka ya ganta ahakan.

Riga da wando ta saka tareda saka qatuwar jacket akai sbd akwai sanyi tana gamawa Yana farkawa shima.

Time yakalla yaga 10 harta wuce gashi jirgin 12 zasubi Dan Haka ya tashi ya nufi toilet yayo wanka dasu brush yafito daureda towel ash ya nufo gaban mirror din Yana kallonta tana tsaye tana hada kayan handbag dinta Dan yau ko Babu id saita tafi gida.

Ba zato ya rungumeta ta baya cikin kunnenta ya furta,

"Good morning Amal Sanda" ahankali qasa qasa kaman wanda baccin Bai ishesaba.

Shiru tayi Masa tana zamewa tace,

"Tafiya zanyi.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna Yana kallon kayan jikinta da Basu fitar da jikinta tako inaba ya shaqi qamshinta Yana dago fuskarta yace,

"Wa Zaki barwa Mijin idan kin tafi??

Qin kallon idonsa tayi ta janye tana cewa,

"Banda miji n....." Bata qarasa ba ya jefata da wani kallo wani lafiyayyan murmushi na sauka kan fuskarsa ya sake janyota ya shaqi qamshinta Yana zura hannunsa cikin rigarta ya shafo cibiyarta... Numfashinta yakusa fizgewa daga kirjinta tayi saurin bude idanuwanta akansa tana kallonsa.

Sake shafa cibiyarta yayi Yana lasar wuyanta da harshensa A wahalce ta fizgo magana daga bakinta tace,

"Stop please.."

Cikin kunnenta yace,

"Duk duniya waye ya Isa yayi Miki hakan idan ba Mijinkiba???

Bata San lokacinda ta gyada Masa kaiba qafafuwanta na rawa.

Wani murmushin Yakuma saki ya saketa tabar gurin da sauri.

Shiryawa yayi a natse yayi musu ordern breakfast Ita tea da cake Tasha Shikuma yaci fries da black tea suna gamawa Suka fito hannunsa na riqe da nata dukkaninsu cikin qananun Kaya kwarjininsa sai sake bayyana yakeyi Suka nufi inda al'amin ke jiransu tun dazu.

Bude mata mota yayi da Kansa tashiga kafin shikuma Al-Amin ya bude Masa yashiga Shikuma Al-Amin yadawo yashiga gaban motar driver yaja suka wuce.

Sai a airport tagano id card dintama Yana hannun Al-Amin Ashe Aka miqa Mata suka wuce.

Tunda suka shiga jirgi har lokacin hannunta na cikin nasa Kuma komai nasa a kame cikin nutsuwa kaman Wanda baya magana kwata kwata saima yadawo yana Bata mamaki.

Suna sauka Kai tsaye IDON NERA Rs suka fara Isa securities na ganinsa suka Masa barka da zuwa cikin girmamawa

Har sama ya rakata taqi barinsa shiga bedroom dinta tashige ta rufe Ya juya ya tafi Bilkisu na Masa a sauka lfy. ##MAMUH#

INTRODUCING UNIQUE AND AFFORDABLE PART-TIME DIPLOMA AND DEGREE PROGRAMMES IN HEALTH RELATED COURSES.

The Directorate for Consultancy Services and Continuous Education of the Kazaure School of Health Technology, Kazaure, Jigawa State, Nigeria wishes to inform the general public that it now offers the underlisted Health courses at its Kazaure centre.

DIPLOMA

1. Dental Surgery Technician

2. Medical X- Ray Technician

3. Health Information Technician

4. National Diploma Biomedical Engineering

5. Public Health Technician

6. Junior Community Health Extension Worker (J-CHEW)

7. Community Health Extension Worker (RE-TRAINEE)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Interested applicants can call the following phone Numbers for the application forms.(WhatsApp) 08035298851, Calls Only 07066542055

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥 Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma

*KI KULANI*🔥 Miss xoxo

Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171 Maryam sani Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA! *Thanks for choosing us*🔥 *_Arewabook@Mamuhgee_* 52 Yana barin gidan Kai tsaye gidansa aka wuce dashi Daman Al-Amin qaninsa yazo daukansa airport shikuma malam Rabiu ne.

Suna Isa gida Yana fitowa mota Kai tsaye sashen ummansa yafara wucewa.

A Palo ya taddasu zaune itada umman Cameroon suna magana suna ganinsa sukai shiru suna amsa gaisuwarsa Kai tsaye fuskokinsu a Dan sake da kulawa ba kaman kwanaki ba Da alama sun sauko tunda dai fushin Babu abinda zai qara ko ragewa saima sake nesantasu dashi Zainab din ta qarasa samunsa a bagas tunda suna fushi dashi,

Umman Cameroon ce tace gwara su sauya taku tunda masifa da balain ya kasa kwato musu shi daga hannun Zainab gwara Suma su koma Masa abin tausayi ta yanda Suma zai mutu akansu.

Barka da dawowa umma tayi Masa tana Dan tambayarsa ya hanya,

Amsawa yayi da dan mamaki kafin ya maida kallonsa kan mahaifiyarsa Yana karantar yanayinta cikin kulawa yace,

"Umma kina lafiya dai right??

Gyada Masa Kai tayi tana danne zuciyarta daga duk wani fushi da bacin ran rabata da akai dashi ta Dan saki fuskarta tana cewa,

"Lfy kalau alhmdllh, Ya hanya?

Wani sanyayyan numfashi Mai sanyi ya saki a boye cikeda tausayin mahaifiyarsa da Koda yaushe take ganin kamar baya Sonta.

Cikin kulawa yace,

"Alhmdllh.

Umman Cameroon ya kalla itama shi tadan kalla din cikin kulawa itama yace Mata,

"Mutan Cameroon ya naki jikin???

Dan washe Baki tayi na farin cikin zancenaa tana Kuma son Hana sake Masa fuska sosai tace,

"Lafiyata kalau bazan mutu ba saina sake ganin sauran 'yayanka duk da so kake ka aikani da wuri akan rigimarka.

Dan gajeran murmushi kawai ya sake tareda miqewa ya fice Bayan yasake musu sallama.

Yana Isa sashensa tun a babban palon farko mufeeda ta tarbesa fuskarta ba Yar sakewa sosai tayi Masa barka da zuwa tana kallon ummenta data fito daga bedroom dinta itama ta nufosa tana zuwa tayi hugging dinsa tana Masa barka da dawowa cikeda so.

Amsawa yayi Yana dauke kallonsa daga kanta Dan baiga bacin ran fushin abinda tayiba.

Sama suka wuce tare tana riqeda hannunsa suna shiga bedroom dinsa tabarsa yayi shirin wanka ko sallah da lokacinta yayi ta sauko zuwa kitchen Dan bada umarnin abinda zaa dafa Masa tinda ya dawo.

Bai jimaba yafito ya nufi masallaci yayi sallah yadawo yakoma ya huta sosai sai laasar ya fito yaci abinci tareda Bilkees da mufeeda.

Bai bar gidansaba sai bayan sallar ishai da yayi yaja mota da Kansa ya wuce gidan Maminsa.

Yana Isa Kai tsaye ya shigo tun a palan qasa daya kusanto saman hancinta yajiyo Mata kusancinsa dasu

Ta juyo da kanta kadan ta kalli kofar shigowa saman Daidai shigowarsa din sanyeda qananun kayan Nike masu kauri fuskarsa fresh kaman Wanda ya taso daga bacci lokacin.

Shima ita ya kalla tana zaune tareda Bilkisu tana cin white rice da egg sauce cikin Dan qaramin plate Bilkisu Kuma kallo takeyi tana Taya Amal din zama.

Miqewa Bilkisu tayi ganinsa Cikin girmamawa ta gaidasa tareda sulalewa tafice daga palon.

Dauke kanta tayi daga bangarensa taci gaba da cin abincinta ahankali cikin nutsuwa tana Hana kanta sake waiwayowa.

Ahankali ya qaraso ya durkuso kadan ba zato yayi kissing kumatunta tareda furta Mata Saida safe ya juya ya fice sbd Idan yayi Wasa zai iya raba dare a gidan baisaniba.

Harya fice Bata dagoba Bata Dena cin abincinta ba.

Dawowar Bilkisu ce ta tabbatar Mata daya bar gidan gabaki daya Dan Haka tana gamawa batai wani doguwar firaba ta shige ta kwanta.

Washe gari Kiran Ahmed tayi qarfe goma ya iso Suka wuce makaranta.

Acan ta wuni sai yamma sosai ta dawo Shima ranar wani irin busy ya zama Dan Haka Bai samu zuwa gidanba saida daddare bayan harta kwanta yashiga har dakinta yayi kissing goshinta tana jinsa harya fice tukuna bacci ya dauketa.

Washe gari ma Haka ta wuni makaranta sbd zaman gida Babu Dadi tunda Babu kowa,

Haka ta ringa rayuwar kadaici agidan Babu kowa shiyasa take wuni makaranta sai yamma ta dawo,

Shima ayyukane masu zafi suka Sha Kansa shiyasa iyakacinsa yazo da safe yaganta kokuma da daddare,

Su Haj Maryamah kuwa ganin sun nuna Masa tuba da sallamawa akan komai Yana nuna Mata kauna da kulawa fiyeda kowane lokaci Dan tausayinta yakeji yanda ta Hana kanta sukuni, Ita kanta umma Cameroon yanzu ne suke gane Masa sai suka gano masifar wani lokaci batayi,

Da wannan Haj Maryamah ta ringa lafewa yau ciwo go lafiya ta ringa cinye lokacinsa tana hanasa zuwa gidan Zainab batareda ma sunsan Bata qasar ba.

Ita kanta Bilkisu ganin yanda yake da iyayensa sun shirya sosai taga hankalinsu kaman ya kwanta saita hau murya Dan kuwa tasan warwarewarsa dasu Zainab ne kawai zaisa su umman su sake Haka Dan Haka itama saita kwantar da hankalinta ta ringa zuba Masa iyayi da kissa kala kala duk da Bai dawo yanda yake a baya da itaba sbd zuciyarsa dake shakkar kishinta ysata fidda zancen nan Amma dai duk da hakan lafiya kalau suke zamansu Babu tauyewa ko wani dogon sauyin.

Sanin ya Saba zuwa duk dare yasa yanzu tasamu kanta da Bata shigewa sa wuri bacci saiyazo sbd batason Yana shiga dakinta Dan Bilkisu dake iya gani karta fadawa mommy kosu Anty Fareedah da Siddi ayi tinanin wani abin.

Yana wucewa take Shigewa ta kwanta Kuma har wannan lokacin magana dai bata hadata dashi Dan haryanxu Bata karbi auren nasaba.

Satinsu Haj Zainab biyi da kwanaki suka dawo Tayi farin ciki da murnan dawowarsu sbd Ba'a taba tafiya batareda Babu dayansuba acikinsu sai a wannan karon Kuma Suma sunyi kewarta.

Ranar dasuka dawo baizoba sbd tafiyar Rana daya dashima yayi.

Jikin mommynta ta lafe tana zuba Mata shagwaban barinta dasukai.

Readers Also Read