Kenza eBookz

Ina tare da ita novel - Chapter 8

Ina tare da ita novel - Chapter 8

Ina tare da ita novel Chapter 8: Ina tare da ita novel Chapter 8. ********** Yah Suleiman ne dasu abbu da Ummi yaje gaidasu da safe ,suna gaisawa suna…

3,246 words

********** Yah Suleiman ne dasu abbu da Ummi yaje gaidasu da safe ,suna gaisawa suna kallon TV dke kunne ,kawai sukaga anhasko pic na baby da Mlm Haruna tana kua tana cigiyarta..

Zumbur yah Suleiman yamik'ec tsaye hade da cewa...

Share

📚📚mmn fareesa ce

AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

INA TARE DA ITA! 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 (bansan ita bace) 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story &written by mmn fareesa

🅿55&56

NOT EDITED

Zumbur yah Suleiman ya mike tsaye had'e da cewa me nake gani haka abbu ?"kuduba anya mahaifinta ne?"

Abbu yace ah ah dakata ,aibazaiyi karya ba!kuma ai Dr yace indai taga Wanda tasani ko shakuwa da shi zata iya komawa normal...

"Ahankali yace eh yafadi haka"

Amma gsky bazamu je da ita ko inaba ,mujedai mutaho da shi ta gansa k'ila tadawo hayyacinta.

Abbu yace to bbu damuwa muje ma yanxun gdn TV dinko?"

Yah Suleiman yace ,amma gsky inhar karya yamana zan hukuntashi!

Harararsa abbu yyi yace banason raini fa dg gani mlm ne ,karyar me zaiyi? "

Kuma ko munje nizanyi mgn bakaiba.....Ummi ta karbe zance da cewa eh alh tunda dai kayi alwarin ya aureta ,inya gaya masa mgn marar dadi zai iya fasa basa ita!

Yah Suleiman kuwa yacika yyi FAM"besake mgn ba ,abbu yace suje yanxun bbu musu yyi gaba ,byn abbu yyi sallama da Ummi yabiyosa.

Koda ya fito parking space yanufa ,kafin ya isa.....baby data hangosa da gudu ta biyosa bbu Dan kwali akanta tana cewa yah ileeeeeeeeeeee!

"Cak yaja ya tsaya dan yasan itace"

Kokarin fadawa jikinsa take da sauri yarik'e mata hannuwa had'e da hararanta"ahankali yace ke ko?"bakyajin mgn nahanaki gudu da yawo bbu Dan kwali ,amma bakya bari ko?"

Murmushi tayi tana kallon sa, hancinta yaja yace to kiyi mgn manah!"

Turo baki tayi had'e da mik'e hannunta dan ta ja hancinsa ,wato ta rama amma bata kaiwa yafita tsawo,murmushi yyi dan sai yatuna da iftihal ,in yaja mata hanci tasa rigimar sai ta rama dagata yake sama saita rama...

Shikuwa koda yaga takasa ,kwalo yyimata tana y'ar dariya...adedenan abbu ya iso...dab Sosa kai yah Suleiman yyi had'e da bude mota zai shiga iftihal ta biyosa.

Abbu yace ikon ALLAH insha ALLAH tafiyarnan alkhairi ce gareni.....Fatima daya hango yakwalawa Kira tana zuwa yace tatafi da ita ciki.

Bayan ta tafi da ita abbu yashiga motar yah Suleiman yaja motar suka bar gdn .

Bayan isarsu bbu bata lokaci abbu yagabatar dasu atake aka kira number ayuba (Wanda sukazo tare da mlm)

Akace suxo yanxun angano yarinyar. "

Mlm da zumudi had'e da murna ,suka iso gdn TV din.

Bayan sun gama gaisawa da juna ,abbu yasanar dashi inda aka tsintseta da lalurarta,data samu da fad'ar Dr duk yasanar da Mlm..

Salati kawai mlm keyi ,yana hawaye had'e da mmkin taya hakan yafaru?"

Abbu yace suje yanxun in ALLAH yasa yasamu lfy zaiji komai dg bakinta...

Yah Suleiman da tunda suka gaida baiyi mgn ba sai yanxun yace amma taya kayi sakaci da ita har aka mata irin wannan dukan ?"tana mace....

Mlm yace ah ah d'an nan lbrin da tsawo ne ,mujedai naganta...

Nan suka fito bayan yah Suleiman da abbu sunyi signing a wani file .

Mlm da ayuba na gdn bays ,abbu da yah Suleiman na gaba da haka suka iso gdn ...

Suna fitowa dg motar ,byn yyi parking mlm yace oh allahu akhbar nah nah wai tana gdn nan..

Azuciyar yah Suleiman ya maimaita sunan yace nah nah kuma?"

Tun kan su ida isowa parlourn Ummi ,abbu yakirata yace tafito d baby nan gasunan zasu shigo...

Yah Suleiman ne gaba ,sai abbu yyinda mlm na bayansa sai ayuba karshe.

Iftihal najin kamshin turaren yah Suleiman zumbur ta mike tsaye had'e da nufaso.....saidai me ?"

Kawai taga mlm yyi tsaye had'e da kureta da ido....kallonsa take kuri zuwa can tadafe kanta dake juyawa ta kwallah wata razanan nar k'ara .

Tayi luuuuuuuzata fadi ,cikin zafin nama yah Suleiman yatarota ta fad'a jikinsa.....

Kuyi hkuri da wannan.🙏🏻🙏🏻

Share..

📚📚mmn fareesa ce✍🏻✍🏻

AWESOME WRITER 'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

INA TARE DA ITA ! 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 (bansan ita bace) 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿57&58

NOT EDITED

Tayi luuuuuuuuu zata fadi,cikin zafin nama yah Suleiman yatarota ta fad'a jikinsa...

Gaba daya yan cikin parlourn kallonta sukeyi"ahankali yah Suleiman yaduba yaga ta suma....wayarsa yafito yakira Dr jabeer ,yyinda yasanar da shi komai. "

Cewa yyi ayayyafa mata ruwa yanxun.

Bbu musu yah Suleiman yafada musu aka kawo ruwa acup mlm yyi addua had'e da watsamata afuska.

Wata nauyayyar ajiyar zuciya tasaki had'e da dafe kanta ,ta ware manyan idanunta farare Ta's a silin dakin.

Zuwa can tafara kallon dakin da mutanen dke cikin sa,mlm kuwa yyimata kuri da ido yanata adduar ALLAH yasa tawarke."

Juyowa tayi jinta jikin mutum...caraf sukayi 4eyes da yah Suleiman ..... "Ahankali komai yadawo mata nadukanta da baffa habu yyi da muciya .

Da azama tajanye jikinta dg jikin sa ,azuciyarta tana cewa ko wanene wannan?" Har Abba yabarni jikinsa...muryar mlm taji yace nah nah ta kiyi mgn dan ALLAH..

Saurin matsawa tayi had'e da kallon su abbu "ahankali tace Abba!inane nan?" Kuma suwanene waddannan?"ina baffa habu da inna delu?"

Yah Suleiman daya tsintsi kansa da jin fad'uwar gaba sakamakon jin muryarta azuciyarsa yace tacika tambaya."

Mlm yyi ajiyar zuciya yace to masha ALLAH Alhmdllh muna godiya ga ALLAH dayabaki lfy..

Abinda nike so kigane,kuma ki fahimta shine ki k'ara yadda da ikon ALLAH kikuma kara imani!wasu yan satittika dasuka wuce antsintseki abakin fita dg kauyenmu kamar matatta.

Jina jina ,wannan bawan ALLAH ne yyimiki komai yakaiki asibiti yamaidoki gdn iyayansa ,byn suntabbatar da kinyi loosing na memory dinki.

Kinzama tamkar yarinyar goye, sai yadda akayi dke,yafada had'e da nuna mata yah Suleiman dsu ummmi..

Hawaye kawai nah nah keyi ....yyinda Ummi keta kallonta tana son tagano dawa take mata kama?"

"Ahankali nah nah talabarta musu tun dg farkon haduwarta da mai gari da zuwa dukan da baffa yyi mata..

Mlm yyi ajiyar zuciya afili yace biri yyi kama da mutum ,dama shine silar jefaki a wannan lalurar?

Zan koma gd kotuce zata rabamu ,wato shine azatonsa mutuwa kikayi yakaki ya yar.."

Duk su abbu sun tausaya mata ganin yar yarinya da ita tashiga halin kuncin rayuwa.,,,,

Mlm yalabartamusu baya gd hakan ta faru,byn yadawo yasamu labarin ba'a gantaba shine yajiyo xuwa dawowa nemanta.

Nah nah ta dago kai da niyar mgn caraf suka had'a ido da yah Suleiman azuciyarta tace masha ALLAH amma afili saita bankomasa harara,had'e da murguda masa baki...

Cikin shagwaba tace to nidai Abba alokacin dabana lfiyar badai shine ke mun komai ba?"kamarsu wanka ....mlm yyi murmushi yace eh mana shike miki harda tsarki ma,yafada cikin sigar tsokana.

Turo baki tayi ,kamar zatayi kuka..Ummi ta karbe zancen da cewa ah ah y'ata wasa abbanki yake miki nike kula dake...

Murmushi nah nah tayi tace to mama nagode sosae ALLAH yabamu ladar...suka AMSA bakidaya.

Yah Suleiman kuwa ya cika yyi FAM tamkar yafashe ,azuciyarsa jin haushin nah nah yake kan tace waibashine ke kula da itaba sadda bata lfy ,amma yasha alwashin zata gane kiranta zai mata hankali ,harwanima harararsa take ,haba zai kamata.

Yatsina fuska yyi had'e da tashi tsaye ...abbu yace ah ah kajira mana agama mgn agabanka"ahankali yace pls abbu zanje na watso ruwa ne ..

Abbu yace to jeka ....Dede gun datake yabi had'e da fakar idanunsu yataka mata kafa....iya k'arfinsa yyi saurin ficewa dan yaga ma yadda shagwababbiya ce ita!

Abbu yace to masha ALLAH mlm ina Neman alfarma biyu agunka !

"Mlm yace haba alh aibabu ita atsakanunmu "

Abbu yace inason da farko kabawa Dana auren yarinyar nan inba'a mata mijiba"sannan inaso kabarta anan bazai ta koma kauyeba ta ida warwarewa ..

Mlm yyi ajiyar zuciya yace kafin k'arfin komai alh aguna nabaki auren ta Amma inaso kuje har kauye kuyi bincike akanmu sannan kuje can kunemi auren ta.

Nima gobe zan koma insanar dasu ko hankali nasu ya kwanta.

Barinta kuma shima na yarda ,dg baya nazo da mai dakina da yar uwarta suganta..

Abbu yace masha ALLAH gsky mungode sosai da halarcin dakamana wlh...mlm yace bbu komai kuncancanci fiye da haka aguna..

Nah nah kuwa haushi taji na badata d mlm yyi bacin yasan Abbas ta keso tuni hawaye suka cika idonta..

Ummi kuwa kiranta tayi tadawo kusada ita ,tafara bata labarin Fatima da Rukayya alokacin da bata lfy sun shaky da juna..

Cikin farin ciki tace suna INA?"

Ummi tace suna dakin yara!

Murmushi tayi tace to nima zanje...abbune yakatse su da cewa , to bara mlm akaina sashen baki ka huta ko?"

Mlm yace ah ah abarshi wucewa zanyi masaukina....nah nah tace Abba nidai um um natsaya anan d'in.... Kafin mlm yyi mgn yah Suleiman yyi sallama yashigo cikin shirinsa da kakinsa ajikinsa yyi masifar yin kyawu ..suna had'a ido da nah nah yabankomata harara saurin dauke kanta tayi dan takatan da yyi dazun taji jiki."

Azuciyarta tace oh Ashe sojane ,nikadama yaharbeni da bindiga ,amma yanada kyau aradu...

Jin datayi mlm na cewa to bara naje can din ,had'e bin bayan yah Suleiman dke kokarin fita ,da sauri tace Abba nah ina yah Abbas yake?"

Wani irin haushi yah Suleiman yaji da tambayar datayi ,to wanene Abbas yafada azuciyarsa ?"

Wata zuciyar tace oho me ruwanka tunda basonta kakeba..waigowa yyi yanadon suhada ido da ita amma taki yarda..gaba yyi ganin tana mgn da Mlm ..

Har masaukin baki yah Suleiman yakaishi sannan yashiga mota yabar gdn..

Ummi kuwa kiransu Fatima tayi ,suka hada break mai nice aka kaiwa mlm ..

Sai nan nan suke da nah nah wacce ita tunda tagansu take k'aunarsu ...

Tuni suka wuce dakin gara suka Shiva bata Latin yah Suleiman da irin kulawar daya bata sadda bata lfy ,sun kuma gaya mata bayason raini ko kadan.

Itadai jinsu take dan said taji ita bata sani tsoronsa .

Break sukayi sunanta bata labarin gdn harda batan iftihal da tafiyarsu momi amma basu sanar da ita yadda yah Suleiman keni da iftinsaba..

Bayan sun gama Fatima ta sa ta ta yi wanka had'e da wanke kanta ,suka mata meke up ,tasaka doguwar Riga gown pink ,masha ALLAH tayi bala'in kyau.

Fitowa sukayi suka rakata gunda mlm yake,sannan suka koma cikin gd.

Azaune tasamesa ,nan suka sake gaisawa yashiga yima ta nasiha da tuni akan rayuwa had'e da hakurin zama da mutane.

Ahankali tace wai Abba d gske nan zakabarni?"

"yace eh gsky" sbd banaso kisake komawa kauyen nan gsky kuma dan ALLAH kuyimun biyayya dukda ke yarinyace dudu shekarunki 15 ne amma musulunci ya yarda namiki aure..

Hawaye takayi ,mlm yace kiyi hkri kinji?"insha ALLAH auren nan alkhairi ne gareki..

Mutanan nan sun mana komai arayuwa basu nuns komai garemu ba ko San in suwanene mu sukace inba dansu aurenki ,aiko sunyi ,kuma nafahimci sunada kirki da daraja dan Adam tun dg kanki,shiyasa nabasuke ,duk da haka nima zanyi istihara nanemi zabin ALLAH nakumasa ayuba dke d'an gari yyimun bincike dukda na yarda dasu ..

Ahankali tace to Abba !amma naso inkoma gd wlh yace bbu damuwa zanxo miki dasu su ganki insha ALLAH..

Firar su suke ta yi gwanin shawa'a ,batabar dakinba saidai aka kira azhar tukum sukayi sallama ta nufo sashen Ummi..

Samun Ummi tayi tana share parlour ,ga dining table nan anshirya abinci samansa..

Da sauri ta karbi sharar ,Ummi na cewa ki bari kinji ,amma ta Karba ta share Ta's tayi mopping ,sai sannu Ummi ke mata azuciyarta tana yana tarbiyyarta.

Tambayarsu Fatima tayi Ummi tace suna dakinsu suna bacci..

Murmushi tayi tace bara natadasu muyi sallah,Ummi tace eh dakin kyauta dan lokaci yyi,nan ta nufi dakin yaran yyinda Ummi ta wuce dan yin tata sallar.

Tana sjiga ta tarasu ,duk sukayi arwallah suka yi sallar ,suna gamawa ,nah nah tafara karatun alkur'ani mai girma cikin sweet voice dinta mai zaki tana fidda hartufa cikin hafshar Wanda ke waiting parlour yanaji..

Su Fatima sukayi mata kuri da ido ganin duk karatun nan datake dakane bbu littafi ,azuciyarsu sun yaba da iliminta..

Yah Suleiman da shigowarsa kenan ,kunnensa yajiyomasa zazzak'ar muryarta tana rera karatun alkur ani mai girma..

Ummi ya kalla had'e da cewa Ummi wake kara tun nan cikin yaran nan ?"

Ummi tace hmmm baby ce fan"

Yatsina fuska yyi .had'e da cewa ina daki akaimun abincina acan".

Ummi tace to ,nan yafice yana mamakin baby azuciyarsa ..

Baby nah nah bata ida karatunba saidai takai aya ganin yadda su Fatima ke santin muryarta.",,,

Fitowa sukayi parlour ,Ummi ta mikowa baby basket had'e da cewa ungo kikaiwa yayanku yana dakinsa...

Jikinta na rawa ta Karb'a dan batasan yin musu da Ummi ,"ahankali tace inane dakin.?"

Fatima tace muje narakaki.

Jikinta sai rawa yake ga fad'uwar gaba yanaji ,suna fita tace amma dan ALLAH ki kaimasa sai najiraki ko?"

Fatima tace um um bbu ruwana wollah ,kadai kijamun yatattakani ,tunda ke aka aika kije wlh zaifi sauki .

Adede nan suka iso d'akunan samarin gidan ,ta nuna mata dakin farko tace nan ne nasa..

Gabanta na dukan Tara Tara tanufi k'ofar had'e da murdawa.

Tashiga tayi sallama..

Share

📚📚mmn fareesa ce ✍🏻✍🏻

AWESOME WRITER'S ASSO..🏮

(palace of excitation and pleasant writer's)

INA TARE DA ITA! 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 (bansan ita bace) 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story &written by mmn fareesa

Wannan page din nakine beauty baby kiyi yadda kike so da shi inaji dake irin totally dinnan😍😍

🅿59&60

NOT EDITED

Tashiga tayi sallama amma tanajin tsoro azuciyarta!

Karewa parlourn kallo tayi ta hango sa kan 3 seeter ya kishingid'a yana karanta jarida,sanye yake da farar jallabiyya ,azuciyarta tace oh mutumin nan akwai jinkai kodan yaga yanada kyau !oho..

Sake maimaita sallamar tayi..can ciki ciki ya amsa yana wani had'e rai.

Ajiye masa basket d'in tayi gabansa"ahankali tace gashi inji Ummi! Beyi mgn ba ita kuma ta juya dan tafiya...keeeeeeeee!baby xonan"yafada tamkar bashi yyi maganarba.

Tunani take azuciyarta wacece baby ?"ko watace me suna hakan adakin ,tafiyarta tacigaba da yi hartakusa kaiwa k'ofar fita atsawace yace kikasake kika fita bada izinina ba zaki gane kuranki...

Turo baki tayi cikin shagwaba tace Toni ai basunana baby ba ,nah nah nisunana .

Tsaki yyi yace da hakan kowa ke kiranki agidan nan ,dakuma hakan zaacigaba da kiranki ,kuma kik'i amsawa kiga yadda zanyi dke yar kauye kawai da ita kazama me kashin kwance....

Ai tuni baby ta fashe da kuka da dire dire ita wlh batasonson tunda yake cemata mai kashin kwance.

Dariyar data taso masa yadanne yace eh ance me kashin kwance kije ki tambaya kiji aikinayi kullum sai na wanke miki kashi da asubar fari shine dankin samu lfy kike wani iyayi ko?"

Harararsa tayi had'e da murguda masa baki tace eh d'in aidai konayi ba ahaiyacina ne ba ko?"kuma ni bansanka yah Abbas nikeso yafika s....tsawar dayyimata ne yasata yin tsit.

Cikin kakkausar murya yace keeee!dakata inkika sake maganar wannan dan kauyen me yellow d'in hakoran nan xanbaki mamaki sokuwa dke nima ai basonki nikeba dazaki birgeni ,shine kicewa mlm bakyason auren dazanyi farin ciki da hakan,Dan inba my angel d'ina ba bbu wata macen dazanso har abada koda zanso wata toko Rabin son danikewa iftina bazata samu ba.

Batayi mgn ba amma tatsintsi kanta daji n haushinsa ,juyawa tayi dan tafiya ta murda k'ofar... Wani Jan kwata kwaren kadangare yyi saurin shigowa kafin ta fita...

Kara tasaki had'e da juyowa da gudu ta fada jikin yah Suleiman tana cewa wayyo zanmutu dan ALLAH yaya kada kabari yayimun wani abu....da sauri yace ke ki nutsu ki dagani Nina fitar dashi sai sani ihu kike mana!

Cikin shagwaba ta ce to kaini ciki ko gurinsu Fatima dan ALLAH kaji?"

Lumshe ido yyi dan saita tuna masa da iftinsa itama tsoron kadangare take yi sosai.

Hannunsa data girgiza yadawo da shi tunaninsa ,cikin kuka tace kayi wani abu yanafa cikin dakin nan!

Cikin mutuwar jiki yace ke baby ki cikani ko!cikashi tayi tana hawaye sai kuma yaji tausayinta..

Cikin rarrashi yace bazaimiki komaiba !make kafada tayi tace um um nikafitar dashi yanxun pls.

Nuna mata wata k'ofar yyi yace kishiga na koresa inba hakaba kekika sani..

Bb musu ta Shiga ciki,Ashe bed room d'in sa ne ,azuciyarta ta yaba da tsabbartasa ,zama tayi ko ina sai kamshi yake ita kanta jikinta kamshin turaren sa yake.

tafi minti 15zaune kan bed din sa...yashigo da sallama yace oya matsoraciyya kifitomun adaki kin wani zaunamun a saman bed .

Bata ce komaiba ta fito gun basket d'in ta nufa tayi serving nashi..yanata mamakin ta tana yar kauye harta iya serving d'in mutum inzaici abinci..

Zama yyi kan carpet ta ajiye masa gabansa had'e da zama kusa da shi sai sukayi tamkar mata da miji...

"Ahankali yace ke kinci abincin?"

Bata kallesaba tace ah ah"

Yace to muci tare kinjiko?"

Ba musu ta jawo spoon suka fara cin abincin ,sai tsakura take ,yyinda yaketa cin abincin sa hankali kwance .

Can tace yayaaaaaa!

Kallonta yyi ,"ahankali tace nakoshi!had'e rai yyi yace ah ah tare zamucinyesa dama bakison cin abinci ko?

Cikin shagwaba tace dan ALLAH kayi hkuri wlh na koshi kuma zantafi gun su Fatima ...

Beyi mgn ba yaci gaba da cin abincin sa.

Har yagama sai turo baki take ,tashi yyi yace ki gyara gurin yanxun kigyaramun dakin...

"Ahankali tace to amma inna gama zantafi " had'e rai yyi yace oh baby kin rainaniko?"

Cikin kukan shagwaba ta ce ah ah yaya kadafa anemeni,juyawa yyi yana tafiya yace Toni na rikeki ne?"

Batayi mgn ba yyi ficewarsa ,tashi tayi ta gyara parlourn da bed room d'in, byn tagama ta kwaso kayan abincin ta nufo part din Ummi ta zauna anata fira da ita...

Bayan an gama sallarla'asar ta fito gun mlm dketa tunanin koya fadawa su abbu wacece nah nah ko yayi shiru.

Abinda yake gudu shine kada suce sun FASA auren sannan ita nah nah tashiga damuwa intagano ko ita wacece...muryarta yaji ,yyi ajiyar zuciya suka k'ara gaisawa.

Bata jimaba ta fito ,tana fitowa tahangi yah Suleiman yashigo gidan cikin shigar kananun kaya yyi masifar kyau da gudu ta nufesa.

Daure fusaka yyi had'e da cewa wai miyasa baby bakyajin mgn?"

Ahankali tace oh yaya menayi kuma?"

Harararta yyi yace ban hanaki guduna! Cikin yarinta tace to aibansan kahananiba sai yanxun ,amma nadena.

Yace yanxun ina zaki?

Tace baby,dama kaina hango nazo inma oyoyo, murmushi yasubuce masa yace hmmm abinda ke sannu d zuwan nan baki iyaba balle gaisuwa sai rashin kunya ni munbata dake..

Cikin shagwaba ta ce to ai zandunga gaidakai,kuma bakaine ke tsokanata ba ,amma bazan koma yimaka rashin kunyaba!

Yatsina fuska yyi yace hmmm kima sake kiga yadda zanyi dke oya muje kinwani tsaya haka!

Batace komai ba sukajera suna tafiya "murya qasa qasa tace yaya ina wayarka?"

Beyi mgn ba yafito da ita dg aljihu yace gata.

Murmushi tayi had'e da karba tace game zaka sa mun nayi!

Kallon ta yyi yace ina kika kiyi game ?"tace yo yah Abbas yanada waya yana samun nayi tun....katseta yyi da Jan doguwar tsuka dan besan daliliba inta ambaci Abbas yakejin haushi.

Fuska daure yace bani wayata"sannan kika koma fadar Abbas gabana wlh xanbaki mamaki.....yafada yana huci.

Ita kuwa harta fara hawaye ,cikin kuka tace to ga wayarka kuma insha ALLAH bazan koma cewa kabaniba ,tana fadin hakan da sauri ta tafi tabarsa tsaye gurin.

Gaba daya saiyaji tabasa tausayi wato fushi tayi da shi kenan.

Duk sai yaji bbu dadi danko ifti baya bari tayi fushi da shi,gashi harda kuka take ALLH yasa kada ta fadawa su ummi .

Part din sa yanufa ransa fal da damuwa sbd baby nafushi dashi .,

Bangaren mm zulai kuwa...

Share..

📚📚 mmn fareesa ce✍🏻✍🏻

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull