Kenza eBookz

Ja'jirtacce complete - Chapter 5

Ja'jirtacce complete - Chapter 5

Ja'jirtacce complete Chapter 5: Ja'jirtacce complete Chapter 5. hatta sarka da yan kunnen ta farare ne haka takalmin kafar ta ma

4,476 words

hatta sarka da yan kunnen ta farare ne haka takalmin kafar ta ma

yarin ya dai ta fito tamkar yar gold sai kyalli da walwali sirrin kyawunta ya kara bayyana

haka shima Amar suite ne farare kal ajikin sa wanda aka siyo mishi iri d'aya dashi da mubarak.

kayan sun zauna d'as a jikin sa kamar dan shi aka yi su, rigar cikin su ja ce haka neck d'in da wuyan hannun shi ma duka ja ne takalmin kafar shi ma jajaye ne.

Sai zuba kamshi suke gaba d'aya mutanen dake d'akin suka zubawa yaran ido domin kasancewar su bakin fuska a gare su.

Ummy kuwa kallon sani take yiwa Safeenah, inda zuciyar ta ta shiga dukan ukuk-uku kwakwalwar ta na son tunano wani abu gameda yarinyar amma ta gagara

sai dai kam ba makawa yarinyar tayi mata kama da yar'ta Yusra,

ganin Alhj ya tsuguna ya rungumi yaran yasa sukayi tunanin ko yaran dangin sa ne.

shi kanshi alhj baisan lokacin da yayi hakan d'in ba, kawai ganin Feenah yayi tamkar wata flower abar so,

ya kuwa rungumeta na tsayin lokaci ji yake ina ma ace yar sa ce baby ta girma haka kuma ake shagalin Birthday d'inta da ita.

Ganin bashida niyyar sakin ta yasa Yusra ta karaso gare su ta kama hannun Amar da Feena taja su zuwa inda Birthday cake d'in yake

ta bawa Feenah wukar tana fad'in

"na manta da na sami sabuwar yarinya, daga yanzu zuwa kowane lokaci Safeenah ita zata rika wakiltar baby"

da harshen larabci tayi maganar wanda yanzu Alh Tijjani ma yanaji sosai da mamaki Ummy ta kalleta

"wacce ce wannan?"

Tai murmushi "zanyi muku bayani daga baya"

safeena kam tsaye tayi da wukar a hannu tana karewa wad'annan fararen mutanen kallo kasancewar su baki a gareta haka Amar ma

Yusra da kanta ta kama hannun Feena ta danna wukar a cake d'in gaba d'aya suka d'auka

_"Happy Birthday to you, happy Birthday baby!_"

nan ne Raudah matar yayan Yusra tayita d'aukar su hotuna da phone d'inta haka dai aka yi murnar harma da su jijjiga lemuna ana watsawa sama

aka gama aka dawo kan shimfid'u inda aka tanadi Alkur'ani irin na d'ibar nan mai peces

Yusra ta kira Aysha mai kula da Feena tace ta tafi da yaran ciki. Taja su suka tafi

suko suka fara karatu dukkan su kowa ya d'ibi dai-dai gwargwadon iyawar shi.

Feena da Amar dai bin Aysha kawai sukayi amma zukatan su basu so barin guri ba, duk da cewa basusan bikin wa akeyi ba.

Haka a d'akin ma suka saka su Aysha gaba da tambayoyi wai bikin wa ake?

Dayake Aysha mai saukin kai ce ita ce ta basu labari tun daga haihuwar baby yar' Yusra har zuwa bacewarta da kuma shekarun da aka d'auka ana gudanar da wannan bikin shekaru takwas kenan.

Dukda kasancewar su kananun yara hakan bai hanasu nuna tausayawar su ga Uwar rainon su Yusra ba.

Safeena hadda kwalla.

Wunin ranar kacokam a d'akin baby suka yishi dasu da bakin nasu, saidai ayi salla a koma aiki (wato karatun Alkur'ani)

duk da cewa suna yi da gaske ne amma sai wuraren karfe goma sha biyun dare sannan suka isar nan kowannan su ya mike suka fara jera nafilfili na tsawon awa d'aya

misalin karfe d'ayan dare suka tsayar da sallar sannan suka hau karanto manya-manyan addu'oi

suka shiga rokon Allah ya kyawawan sunayen sa tsarkaka akan ya bayyana musu wannan yarinyar

indai tana raye Allah ya dawo da ita ga mahimaifiyar ta, inko bata raye Allah yai rahma ga ruhin ta kuma ya bawa iyayenta hakuri da juriyar rashin ta.

in suna da sauran rabon haihuwa Allah ya basu wasu masu albarka.

Haka suka ci daren kaf acikin su ba wanda ya rintsa har sukayi sallar asuba

sannan ne aka fiddo tarkacen kayan abinci da ragowar cake d'innan

aka tsabtace d'akin kamar ba cikin sa akayi shagalin ba.

sannan suka rufo d'akin.

baki suka koma masaukin su,Yusra da Alh kuwa suka koma d'akunan su.

Duk wannan abin da akeyi zuciyar Ummy ta kasa nutsuwa, sai kai'kawo take akan yarinyar data gani Safeenah Allah-Allah take gari ya waye taji

Shin wacce ce wannan Yarinyar mai d'iban kamannin yar'ta Yusra, me kuma yasa suka bata matsayin jikar ta?.

*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:53 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *25* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*

*Ba anan ta tsaya ba, Ku ɗin wani sashe ne na rayuwar Nasmat.*

1, *Queen haucy* 2, *Beauty Queen* 3, *Queen Yar'mama*

*Those are the triple QUEENS of ZAMANI WRITERS*

love all😍😘

Bacci ne mai nauyi ya ɗauke dukkan su, basu suka farka ba sai karfe goma. Nan ma hayaniyar yara ce ta taso su.

Rigima ce ta shiga tsakanin Mubarak na wajen hjy Ummu da Safeena karo na farko da suka fara faɗa tun zuwan su gidan, duk da cewa yana shiga sabgar su su ɗin ne dai basa biye mishi.

Yanzun ma bazata iya hakura bane. Domin yar'babyn ta ce ya kwace, ita kuma yadda take son ta bazata iya bar masa ba.

Sai ta saka kuka shikuwa Amar yana zuwa ya kwace mata abarta ya mayar mata, nan ne fa Mabarak ya nemi yayi faɗa da Amar ɗin dama shi yake nema, shi ya fara kai masa duka shi kuwa ya rama karfi ba ɗaya ba sai ga Mubarak ya hangame baki yana kuka.

Kusan tare suka iso da hjy Ummu wadda ta fito a hassle jin kukan Mubarak data yi, turus tayi ganin duka iyayen sun sauko kuma ta gane faɗa yaran suke yi Amar da Mubarak shiya sai shi kuka.

Salati ta fara yi tana rafka hannaye "me zan gani a gidan nan?, ai wlh baku isa ba kuzo ku sami yaro a gida sannan ku takura shi?, ina ai baza ba sa6u ba wlh"

ta isa gun ta rika hannun Mubarak "wanene ne ya dake ka eye?". cikin kukan da shagwa6a ya nuna Amar da yatsan sa.

Ai kuwa bata jira komai ba ta nufi inda Amar yake da nufin ta dake shi. Hjy Yusra da Alh dake gefe tsaye mamaki ya cika su

Lallai son kai irin na Ummu ya buwaya, haka kurum ba tambayar ba'asi ba komai sai ka yanke hukunci a faɗan yara?.

Abu kaɗan ya rage ta isa ga Amar d'in, Alh ya dakatar da ita da cewa "kar ki kusakura ki ta6a yaron nan Ummu".

wani mugun kallo ta wurgawa Alhjn "kamar ya kar na ta6a shi, shugaban rashin adalci?". Tayi maganar tana kallon inda yake.

Bai damu da kallo da kuma maganar da tayi mishi ba. Ya share ta, ya kalli Amar yace kai mene ne ya had'a ku?".

Amar ya koro masa bayanin abinda ya faru duka. Ya juya ga Mubarak yace "Abinda ya faɗa gaskiya ne?".

ba kunya yace "eh" Alh ya kalli Ummu dake tsaye tana cin ranta yace "to kin ji dai sarkin fushi, Mubarak shine yafara bugun Amar, kuma shine mara gaskiya sai ki kiyaye gaba kirika bincike kafin ki yanke hukunci".

bai jira me zata ce ba ya kama hannun Amar da Feena Yusra ta rufa musu baya suka koma sahen su.

Haka suka bar hjy Ummu tana ta bambami. Alh ya yiwa yaran nasiha akan su daina faɗa su ɗauki Mubarak tamkar ɗan'uwan su.

Suka amsa da "to Abba". "good Allah muku Albarka". Nan suka bar su falon su kuma suka koma ɗaki domin shiryowa su fito kasancewar tashin su kenan.

Ba jimawa suka fito tsaf-tsaf dasu suka ja yaran duka suka tafi gaisa baki ɗakin Ummyn ta suka fara.

Bayan sunyi nocking aka basu iznin shiga suka shiga da sallama, a lokacin Ummy na zaune a kan sallaya tana jan carbi, suka shiga har kasa suka rusuna suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a sa sakin fuska.

Idon ta akan yaran ta kasa jurewa sam bazata iya danne abinda take ji gameda yarinyar ba tace da harshen larabci "Yusra wannan yaran fa, yaran waye?".

Yusra tayi murmushi batare da bata lokaci ba ta kwashe duk yadda ta sami yaran ta gayawa Ummyn ta.

Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Ummy, ta cika da al'ajabi Ummy sam ta kasa 6oye abinda ke ranta tace

"ikon Allah kenan idan aka gan su kamar ya'yan ku, musamman wannan yarinyar dan wlh har kamanni take yi dake Yusra".

Maganar ta Ummy ta fama wa Yusra wani tabo dake kan kirjinta ta kuwa kafe Safeenah da ido ko kiftawa batayi

"tabbas abinda Ummy ta faɗa gaskiya ne, domin kuwa ta daɗe tana kallon yarinyar na mata kama da wata fuska amma sai yau ta fahimta.

Ashe da ita Feena take kama..."

*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 6:53 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *26* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*

A cikin farin ciki nake sadaukar da wannan kawataccen shafin gareka *80k*, domin ka cancanta saboda ɗinbin ko'kari da ɗawainiyar ka garemu *ZAMANI WRITERS* basa raina alkhairi. Allah ya bar tare. muna godiya irin sosai da sosai ɗin nan. 🤝

"ikon Allah kenan" cewar Alh dan yanzu ya tabbatar hakan ɗin ne tabbas suna da kama da yarinyar.

A ranshi yace ba mamaki kamannin ta da matar tashi ne yasa yake matukar son yarinyar

Lura da yayi matar shi ta shiga wani hali na zuzurfan tunani ne yasa ya ɗan girgiza ta tareda ambaton sunan ta a hankali "Yusra" cikin nutsuwa ta juyo da fararen idin ta gareshi waɗanda hawaye suka soma fitowa daga cikin su.

"pls Yusra dont" ya kara faɗa cikin raunin murya da tausayi domin ya hango tunanin ta da inda ta dosa. yasan tunani take akan yar'su Baby tanaji a ranta dama itace wannan.

Ummy ma dai jurewa ne kawai take domin ita ɗin ma ji take inama jikar ta ce wannan saboda haka ne ta kasa furta komai Alh ya mike yana cewa Ummy a huta lfy zai fita. Murmushin yake ta masa tareda addu'ar Allah kare ya fice Yusra ma ta bishi a baya da sauri yaran suka mike dan bin Momyn su wajan rakiyar Abba amma sai Feena taji an riko mata hannu

Dasauri ta juyo idon ta ya sauka akan na Ummy data rike hannun nata duk da cewa ita yarinya ce saida taji wani sauyi a tattare da ita. Ta zubawa dattijuwar ido tana Murmushi domin wani irin son matar da taji ya shigeta a lokaci ɗaya taji tana kaunar Ummy har cikin ranta Ummy ta zaunar da ita bisa cinyar ta har yanzu Murmushin ne a fuskarta.

Cikin wargazajjiyar hausarta tace "baza ku tsaya ku tayani hira ba?" Amar yace "zamu raka Abba ne, muna dawo wa. Zo mu tafi kanwata". Yayi maganar yana kama hannun ta abin mamaki sai yaga Feena ta zame hannun ta tana faɗin "a'a yaya zan taya Ummy hira kai kaje ka raka Abba".

Tsananin mamaki hana Amar magana yayi domin tunda suke da Safeenah bata taba gujewa umarnin sa ba, bata taba son wani abu sabanin wanda yake so ba bai taba cewa ga abu tace a'a ba sai yau.

Bai koma cewa komai ba ya juya ya fice cike da al'ajabi bai kara tsinkewa ba sai sanda yaga har yakai ga barin falon bata fito ta biyo shi ba. Feena kam sakin jikinta tayi sosai tana zubawa Ummy hira haka itama ta biye mata duk da ba gane wata hausar tata take ba, amma tana jin daɗin hira da ita jinta take har cikin ki'kon ranta sonta take ji wanda ko jikokinta ya'yan yayan Yusra bata jin son su kamar yadda take jin na yar'rikon yar'ta yarinya Feena.

To tun daga wannan ranar wata irin soyayya da shakuwa ta ɗinke tsakanin Ummy da Safeenah kullum suna tare dare da rana tun abin na damun Amar har yazo shima ya saba saboda Tsananin son da yakewa farin cikin kanwarshi.

Satin su biyu a Nigeria suka kimtsa suka koma kasar su zuciyar Ummy cike da kewar Safeenah sabanin sauran lokuta da idan suka zo take komawa da tausayin yar'ta Yusra. Haka Safeenah ma tasha kuka ita a dole sai dai Ummy ta tafi da ita dakyar aka riketa suka tafi da zazzabi ta wunin a ranar.

Hankalin Amar yayi masifar tashi shi kan shi yasha kuka yanata rokon Momyn su akan ta bari Ummy ta tafi da su. Wasge garin ranar suka fara zuwa makaranta bayan an kammala musu komai daya dace a IMAN INTERNATIONAL SCHOOLS primary 1 aka saka Feena inda Amar ya sami 3 saboda girman shi.

Ai kuwa sun fara karatu cikin nasara da sa'a sam basu sha wata wahala ba kasancewar sun jima suna ɗaukan lesson a gida.

Rayuwar su gidan Alh Wakkala tamkar farin wata ne a cikin duhun dare basuda wata matsala ko damuwa iyayen na nuna musu soyayya iyaka kulawar uwa suke samu daga Hjy Yusra kamar yadda Alh Wakkala ya maye musu gurbin Uba.

Haka lokuta suka cigaba da shuɗewa wasu na ture wasu suna waya da video call sosai da Ummy haka duk shekara suka ziyarci bikin birthday na Baby kamar yadda ya gabata a farko haka ya cigaba da kasancewa Safeenah ta cigaba da maye gurbin Baby a ranar birthday

tun bata san me ake yiba har ta fara fahimta a ranta tana jinjinawa soyayyar da waɗannan iyayen suke yiwa batacciyar yarinyar tasu.

Tana tausaya musu matuka tareda taya su addu'ar Allah ya banana musu ita a duk likacin da tayi salla bayan ta yiwa Umman ta addu'ar neman rahama kamar yadda malamin islamiyyar su ya koyar da ita.

*************************************

*Bayan shekaru shida*

Shagali na samu anayi sosai a gidan Alh Wakkala murnar kammala makarantar primary ta Safeenah. An kawata gidan ta kowanne fanni musamman bangaren garden ɗin gidan wanda a can aka shirya gudanar da gagarumin bikin

Duk inda ka kyalla idon ka manyan mata ne kawayen Hjy Yusra cikin shiga ta alfarma itama dai ba karya ta caba ado na musamman sai hidima take da baki duk inda ta gifta haske da kyalkyalin zinarin dake sanye a wuya da hannayen ta ke walwali

Komai ya gama tsaruwa su Ummy kawai ake jiran isowar su sai uwar gayyar wadda take can ana tsantsara mata kwalliya. Amar sai kaikawo yake ya rasa abin yi fitowar ta kawai yake jira domin a yau ba wanda ya kai shi farin ciki

Feenanshi ta kammala primary zata zo makarantar su su cigaba da zuwa tare domin shi tuni ya bar bangaren primary yana secondary js2.

Inda rayuwar can ta zame mishi tamkar dole tsawon awannin da yake batare da ita ba jin kanshi yake tamkar a ɗaɗɗaure yake

Yana cikin zariyar ne ta fito cikin wata kiriyar doguwar riga wadda aka ɗinka ta da wani yadi mai shara-shara rigar tabi jikinta cif-cif ga adon stones kota ina a jikin rigar takalmin kamata ma green ne hils masu tudu sai sarka da warwaro na ɗanyen gold da aka zuba mata bakin gashin nan nata yasha gyara sai shaki da walwali yake

Lokacin da ta gama fitowa farfajiyar filin yayi dai-dai da ɗago kanta fuskarta ɗauke da farin ciki mara misaltuwa "masha Allah" iyakan abinda bakina ya iya furtawa kenan saboda tsananin kyau da kwarjinin da Safeenah tayi min sai naga ma kamar sauya min ita aka yi da wata balarabiyar kyakkyawar yarinyar yar shekaru goma sha huɗu wadda makerin budurci ya fara kerawa wato duk wata sura ta ya'mace ta fara bayyana a jikin Safeenah

Babu yadda za'ayi mutum ya iya yi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa ko waye shi kuwa fans bansan yazan kwatanta muku wannan budurwar ba amma gaskiya Safeenah ta gama haɗewa

Shi kanshi Amar bai taba ganin kyawun Safeenah ya bayyana kamar na yau ba. Sam ya gagara raba idon sa da kallon ta Murmushi kawai ya tsinci kansa da yi tareda tunkarar ta da hanzari cikin takunnan nasa na babban yaro.

Murmushinta ta kara faɗaɗawa ta nufe shi da zummar rungume shi yayanta Amar wanda tafi so akan komai da kowa a a cikin mutanen wannan duniyar nan

Abin da ya rage su haɗu kalilan ne hakan yasa Feena ta ware hannayen ta duka tareda lumshe idonta,

Kyakkyawar runguma taji an yi mata tareda manna mata kiss a wuyan ta cikin wani yanayi wanda ya rungume ta ya matsi kuibinta sai a Lokacin hancinta ya bambance mata kamshin turaren Amar da na wanda taji ya rungume ta

Da sauri ta buɗe kwayar idon ta tareda zuba su akan sa cikeda tsantsar mamaki

*Ya Mubbarak* ta faɗa tana ko'karin raba jikinta da nashi

*Afwan my fans, nasan ban kyauta ba dana tsayar da rubutu ba tareda sanar muku ba. Ku sani Nasmat batada burin batawa kowa da niyya kumin afwa hakan ya faru ne bisa wasu dalilai na sirri masoyana Kuna raina much love to you guys* 😍😘

*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/27/2017, 4:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *27* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*

Mubarak ya sake mata wani lallausan murmushi, wanda bai ta6a yi mata irinsa ba tunda Allah ya haɗa zaman su a gidan.

Mamaki ya kara turnuke ta dai-dai lokacin da Amar ya karaso gaban su, su duka biyun ba wanda yayi magana sai dai kallon-kallo da suke wa junansu Mubarak yana yi mata wani kallo ne wanda ta rasa dame zata fassara shi, ita kuwa kallon mamaki da tantama take masa a ranta tana kissima abubuwanda bata tunanin kasancewarsu tsakanin ta da shi.

Duk tarin farin cikin dake cike da zuciyar Amar ya kau, sai ya tsinci kanshi cikin bakin ciki da jin haushin yadda Mubarak ya rungumi kanwar tashi kodan basuda jituwa dashi-dashi ne oho.

Bai jira komai ba ya kama hannun ta, ya jata zuwa wani gefe na 6angaren garden, duk wannan abin da ake yi babu wanda idonsa ya kai garesu saboda abin ya faru ne a kofar shiga main Palo na gidan, su kuwa mutanen da suka halarci bikin suna can tsakiyar gurin kowa da abinda yake yi.

A kan wata kujerar roba ya zaunar da ita ba tareda yace mata komai ba, shima ya zauna yana kallon ɗaya gefen ranshi a 6ace.

Kirjinta ne ya hau dukan uku-uku badan komai ba sai dan tarin 6acin rai da ta hango a cikin kwayar idon yayan nata.

Lokaci mai tsawo ba wanda yayi magana a cikin su, hankalin Safeenah ya koma tashi "me ya 6ata ran Yaya Amar haka?" ta tambayi kanta

Shi kuwa Amar zuciyar shi ce ta kasa nutsuwa "me wannan yake nufi?, a lokacin da Feena ta fito ta nufo shi da murmushi ya ɗauka gunshi ta nufo ashe ba shi ta nufo ba, dama akwai wata alaka ta jituwa tsakanin ta da Mubarak amma take nuna kamar ba ruwanta da shi?".

Sai kuma yaji haushin ta ya kama shi ya kara kama shi, cika yayi bam kamar zai fashe, yayin da yake dukan teburin dake tsakiyar su a hankali da hannunsa daya dunkule.

Feena ta kasa jurewa zafin da zuciyar ta take mata na ganin fushin yayanta, abokin tafiyar da rayuwar ta.

Tafin hannunta ta ɗora akan nashi dake kan table ɗin a hankali ta kira Sunan shi, "Yaya, wai meke faruwa ne ni ban gane makaba waye ya 6ata maka rai, nima kake neman 6ata nawa bayan kasan yau Ranar farin ciki ce a garemu baki ɗaya?.

Nasan ka fiye da kowa, kar kayi tunanin wani shiri ne tsakani na da Ya Mubarak, wlh ko magana baya yi min in ba ta faɗa ko hantara ba, ni kaina ina cike da maimakin abinda ya faru yanzu kuma yaya wlh na ɗauka kaina shiyasa na rike shi".

Ta karashe zancen tana share hawaye domin ganin yadda ɗan'uwan nata ya ɗauki zafi.

Ya yarda da Feena da kuma kalamanta, amma abinda Mubarak ya aikata ya kasa gogewa a zuciya da kuma kwayar idon shi, ganin zai rushe farin cikin da ta daɗe tana gidana ma wannan Ranar yasa ya kakaro murmushi yana faɗin "shikenan ai my Feena, ya wuce amma ki kiyaye domin Mubarak da Mamanshi mugaye ne, a koda yaushe basuda burin da ya wuce su cutar da mu, karki yarda wata alaka ta shiga tsakanin ki da shi kinji kanwata?".

Ya faɗa yana share mata halayen data fara yi, yace "karki yarda ki 6ata adonki, bakiga yadda kika yi kyau ba".

"Allah yaya?, wlh kaima kayi kyau sosai". Ta faɗa cikin sakin fuska da murmushi

Amar ya ciro wayarsa ya fara ɗaukar su hoto suna ta dariya

6angaren Mubarak kuwa daɗi ne ya lullu6e shi ganin yadda ran abokin faɗan shi Amar ya 6aci, koba komai ya sami hanyar da zai rika tusa mishi bakin ciki kamar yadda shima yake ji idan ya ga yadda Dady yake nan-nan da shi.

Tofa🤔

*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/27/2017, 4:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *28* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*

Suna cikin ɗaukar hotunan ne suka ji shigowar motoci a gidan, hakan ne ya tabbatar musu da isowar Ummy Mahaifiyar Hjy Yusra.

Da gudu Feena ta nufi inda aka faka motocin tana tsallen murna, Amar yabita da kallo kafin daga bisani shima ya bi bayan ta, amma shi kam ba gudu yake ba (uhum Amar fa an girma lolz) .

Ummy na fitowa suka rungume juna itada Feena, kowanne su na bayyana irin farin cikin da yake ciki na ganin juna.

Dai-dai nan Hjy Yusra da Amar suka karasa gurin har kasa ta zube ta gaida Mahaifiyar tata, Amar ma haka ya gaisheta, Ummy ta ɗagota tana murmushi "Yusra na same ku lafiya?". Izuwa yanzu bakin Ummy yaji hausa sosai "lafiya lau Alhamdulillahi Ummyna ya hanya?". Haka dai suka shiga gaishe-gaishe wannan karon Ummy ita kaɗai ta zo sai kayan tsarabar ta.

Saboda karancin lokaci ko hutawa Ummy bata yi ba aka fara gudanar da bikin, inda mutane suka fara cike table ɗin dake gaban Feena da kyaututtuka, gaba ɗayan su kawayen Hjy Yusra ne.

Sai ɗaukar hotuna ake ana ajiye gifts, daɗi takeji kamar me, haka taro ya watse bayan anci ansha kuma an nishaɗantu.

Bayan sallar magariba ne suka hallara a babban falon gidan bayan kowa yayi wanka yayi salla, yau wani sakalci Feena take ji saboda ganin Ummy da tayi, kwance take bisa carpet ta ɗora kanta bisa cinyar Ummy tana zuba shagwa6a, wai taron nan duk ya gajiyar da ita.

Ita kuwa Ummy sai sannu take mata, haɗe matsa mata kafafuwanta. Momy Yusra Dady da Amar duka sun zama yan'kallo, a 6angare ɗaya kuma suna jin daɗin yadda Ummyn take tarairayar Feena tana nuna mata so.

Dady yai murmushi kana yayi maganar cikeda tsokana, "Ummy karfa ta karya miki kafa" da sauri Feena ta ɗago "kai Dady dan Allah ka bari, ni ina naga nauyin da zan karya wannan tsohuwar da Kuka riga kuka ginata da beta". Itama dai da tsokanar tayi magana dan sun saba irin wannan da Dad, yanzu sun saba sosai wasa sukeyi tsakanin su da Iyayen, kai ka ce a gidan aka haife su.

Ummy tace "Ke, lallaima Feena baki ganki bane kin girma fa". Ta shagwa6e fuska "amma ai ban yi girman da na wuce hawa cinyarki ba ko?".

Su duka sukayi dariya, Dady ya kawar da zance a lokacin da ya zura hannun shi aljihu ya ciro wani makulli sabo fill, ya kira ta da cikakken sunanta "Safeenah" "na'am Dady" ta amsa tareda tashi zaune tana kallon Dadyn, yace "ga yar karamar Kyautata a gare ku keda yayanki, wannan makullin motor ku ne kwananta biyu da zuwa, tana nan ajiye a parking space wadda kukaga an lullu6eta ɗin nan, kyauta ce dana baku.

Amar yarona ka girma na yarda da nutsuwa da kyan hankalin ka, zan sa Ilu ya koya maka tuki sai kufara kai kanku makaranta, kaga nan gaba kaida Feena zaku rika tafiya".

Safeena ta daka uban tsalle "Wayyo Allah daɗi, kai Dady amma wlh ka gama min komai, Allah dai ya biya ka da Aljannarsa maɗaukakiya". Dady ya amsa da "ameen ameen".

Amar ya kara matsawa dai-dai da kafafuwan Dady ya rusuna, yana daɗa yi mishi godiya, Dady ya shafa kansa "bakomai yarona kai dai ka dage da karatu ka kuma ɗore da kyawawan halayenka dana sanka da su, Allah yayi muku albarka". "Ameen Dady". Suka amsa a tare.

Wannan kyautar ta Alh bakaramin faranta ran Momy Yusra tayi ba, ta daɗe tana yi mishi godiya Ummy na taya ta, yace "haba wannan ai yiwa kai ne, yara namu ne ga baki ɗaya"

Ummy ma kwance Jakarta tayi, inda ta ciro tata kyautar a cikin wani ɗan karamin box ta buɗe

Wata dankariyar sarka ce mai matukar kyau da sheki sai walwali take tana ɗaukar ido, wannan ko ba'a faɗa ba sun san zinari ne. Ta ciro ta tana kallon inda Safeenah take, "zo nan". Ummy tayi maganar a takaice

Feena ta baro gaban Dady ta dawo inda Ummy ta tsuguna zuciyarta cike da farin ciki, Ummy ta kwance sarkar nan ta ɗaurawa Feena a wuya, sannan ta ciro ɗan kunnen ta saka mata bayan ta cire wanda ke sanye a kunnenta.

Feena ta kalli yadda sarkar ta kwanta a wuyanta, da sauri ta rungume Ummy tana yi mata godiya. Iyayen kuwa bakaramin fami ganin wannan sarkar yayi musu ba, sai dukan su sukayi shiru suna tuna wancan lokacin kamar dai haka, haka Ummy ta sakawa Baby sarkar nan da hannun ta.

Amar kanshi bin sarkar yayi da kallo zuciyar shi naso ta zargi wani abu.

Murna da farin ciki sun cika Feena ta rarrafa gaban Momy Yusra tana faɗin "Momy kalla, kalli sarkar da Ummy ta siyo min", Bakina sam yaki rufuwa saboda murna, amma ga maimakin ta sai taji Yusra batace komai ba, hasali ma gaba ɗaya yanayin ta ya sauya.

Ganin yaran zasu fahimci wani abu, Dady yayi saurin dafata "ya dai Yusra?". Ya kalli Amar yace "kuje, kuce Ilu ya nuna muku sabuwar motar ku". Suka mike suka fita cike da murna, a lokacin ne kuma Yusra ta sami damar fashewa da kuka.

Amar kuwa suna fita ya kama hannun Feena zuwa ɗakinshi a madadin inda suka nufa, zuciyar shi cike da tantama, so yake yaje ya tabbatar domin wannan sarkar da Ummy ta sakawa Feena a wuya tayi matukar kama da wadda Ummanshi ta bashi kafin rasuwar ta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull