Ja'jirtacce complete - Chapter 6
Ja'jirtacce complete Chapter 6: Ja'jirtacce complete Chapter 6. Wadda tace masa da ita aka tsinci Safeenah, kuma ta umarce shi da ya rike sarkar da aminci,…
4,398 words
Wadda tace masa da ita aka tsinci Safeenah, kuma ta umarce shi da ya rike sarkar da aminci, ya kula da ita sosai domin tabbas sarkar ta musamman ce, dukda batasan takamaiman matsayin sarkar ba, amma tunda take bata ta6a ganin sarka mai kyau kamar ta ba.
kuma tana tunanin ko da ita za'a iya gano asalin Safeenah.
Wardrobe ɗinsa ya buɗe, kana ya sunkuya can kasanta ya ɗauko ɗaurin ledar ya fara kwancewa yana kallon Safeenah,
wadda har yanzu bata sami damar yi mishi magana ko tambayar abinda hakan yake nufi ba.
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/28/2017, 9:59 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *29* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Bayan ya sami nasarar kwance kullin ledar ne ya zaro sarkar dake cikin ta, naɗe a cikin wata takarda. Safeenah kanta data kalli sarkar saida ta koma kallon ta wuyan ta, wadda Ummy ta saka mata yanzun nan. "Yayana wannan fa?" a ina ka samu?"
Baisamu nutsuwar bata amsa ba har saida ya karaso gabanta, yasa hannunsa ya ɗago sarkar da aka sa matan yana kare mata kallo, domin tantance bambancinta da wannan wadda Ummansa ta bashi.
Ya kuwa gano bambancin domin wannan tata ta jaranta karma ce, kuma zagayayya kamar sifar kwallo. Bayan wannan ma da rubutun larabci a jikinta wanda a yanzu zai iya karantawa, (Marhaba) haka aka tubuta ajikin wancan karamar. Sa6anin wannan da aka rubuta Sunan Safeenah da manyan haruffa na larabci.
Ya kara duban sarkokin ya cika da mamaki, ganin duk irin daɗewar da wannan karamar tayi haskenta da shekinta suna nan kamar na wannan wadda aka bawa Feena yanzu. Hakan ya daɗa tabbabar wa Amar cewa lallai maganar Ummanshi ta tabbata akan cewa wannan sarkar ta musamman ce.
Ya rumtse idonshi tareda damke sarkar a tafin hannunshi, yana tunano maganganun Ummanshi akan Safeenah, "Abinda yaya Larai take faɗa akan Safeenah gaskiya ne Amar, tabbas ita yar'tsintuwa ce. Sai dai hakan bai isa yasa akirata da shegiya ba, kai inma hakan ɗin ne meye laifin yarinya?". Maganar ta dawo raɗau a kunnen sa, tamkar a lokacin take gaya mishi ita.
"Babu Umma, wlh bata da laifi" ya faɗa cikin rauni kamar mai shirin fashewa da kuka Safeenah ce yaji ta dafa kafaɗarshi tana faɗin "Yaya, wacce ce batada laifin?"
Da sauri ya juyo ya kalleta, a lokacin idon shi sun fara kawo kwalla. Ganin zata gane kuka yake, yasa yayi saurin rungume ta dai-dai lokacin da halayen ke fitowa daga idonsa.
Tausayin rayuwar Feena ya kara lullu6eshi. A wani 6angaren na zuciyarshi kuma godewa Allah yake daɗa yi, akan taimakon da yayi musu ya inganta rayuwarsu ta hanyar haɗa su da waɗanan bayin nashi Momy Yusra da Dadynsu Alh Wakkala.
Cikin dabara ya kai hannunshi bisa kumatunsa ya goge hawayen fuskarshi, domin yasan da zarar ta gani yanzu itama zata saka kukan.
A sannan ne ya raba jikinshi da nata ya ɗagota suka fuskanci juna. "Kanwata Feena kinsan ina kaunar ki, Umma ma tana sonki sosai, ita ce ta bayar da wannan tace na baki, kuma tace taki ce tun kina jinjira". Ya faɗa yana nuna mata sarkar, lallausan murmushin nan nata ta sake mishi, alamun farin ciki ne suka bayyana karara a fuskarta. Ta kar6i sarkar "Allah sarki Ummana, ina kaunar ki Umma. Allah ya kai rahma kabarinki". Da sauri ta fara kiciniyar cire sarkar da Ummy ta saka mata domin maye gurbin ta da wannan wadda Umma ta bayar a ajiye mata.
"a'a kanwata, kar kiyi haka". Amar ya yayi maganar yana janye hannuta ga barin abinda take ko'karin yi. "me yasa?". Ta tambaye shi fuskarta cike da damuwa.
"Feena Umma tamu ce a kowane lokaci zamu iya amfani da abinda ta bamu, waɗannan bayin Allah kuma sune suka ɗauke mu a matsayin nasu, irin Soyayya da kulawar da suke nuna mana ko a gurin Iyaye sunada wahalar samu Safeenah. "Kiyi hakuri da wannan ta Umma har zuwa wani lokacin, yanzu ki zauna da ta Ummy idan kika cireta sam bazata ji daɗi ba". Shiru tayi na ɗan lokaci tana nazarin kalaman sa, tabbas abinda ya faɗa gaskiya ne.
"Shikenan Yaya, amma zuwa yaushe zan saka ta Ummana?". Tayi tambayar cikin sanyin jiki, da alama hakura kawai tayi amma tana muradin sarkar.
Yai murmushi "bafa ta Umma bace, taki ce". Ta kalle shi "to ai itace ta bani". Shiru kawai yayi dan bazai iya gaya mata yanda abin yake ba. Hannu ya zira ya kar6i sarkar ya maida ta cikin takardar nan ya ninketa, sannan ya saka a leda ya maidata inda ya ɗauko ta. Ya juyo ya kama hannunta suka fice.
Direct compound ɗin gidan suka nufa inda ake ajiye motocin gidan, Feena ce mai kwallawa Ilu direban gidan nasu kira. Cike da murna da farin ciki. Da hanzarin sa ya taso yana faɗin "Uwar ɗaki fita zamu yi?" Sunan da duka ma'aikatan gidan suke Kiran ta da shi kenan. "A'a Ilu, Dady ne yace ka nuna mana sabuwar motar da tazo jiya tamu ce, mu aka siyawa". Tayi maganar da yanayin nan nata na yaranta. Ilu ya hangame baki yana kallon Amar "gaskiya na taya ku murna domin ko Alhaji bai ta6a hawa motar da takai kuɗi da kyawun wannan ba". Ya karashe maganar lokacin da yake yayewa motar rufin da akaimata.
"wow" Safeenah ta faɗa cikin kwalalo ido waje. Amar kansa ya jinjinawa kyau da girman motar daɗi ne ya lullu6e zukatan matasan biyu. Tayi tsalle ta rungume yayanta "wayyo Allah yaya, daɗi zai kashe ni". Tare suka karasa gaban motor key ɗin ta saka ta buɗe kofar ta shiga shima ta buɗe mishi 6angaren driver ya shiga ya zauna yana karewa cikin motar kallo.
Wannan karon kasa 6oyewa yayi, hawayen farin cikin da suka gangaro daga idanun shi. Feena tayi saurin kai hannunta ta share mishi. "Meye haka kuma yaya?, me ya saka ka Kuka?". Shiru yayi na wasu dakiku yana kissima yadda rayuwa take tafiya da tsare-tsaren ta.
"Kinga rayuwa ko kanwata?, kinga yadda abubuwa suka canza daga tsanani zuwa daɗi ko?, shin ke baki ji wani iri ba Safeenah?". Ita ɗinma hawayen ne shar a fuskarta. "na gani yaya wannan duka ikon Allah ne, shi ne mai maida zafi sanyi ya kuma juyar da sanyi ya koma zafi, babu abinda ya gagari Ubangiji haka malamin islamiyyar mu yake gaya mana".
Ta matsa daf da shi ta kwantar da kanta bisa kafaɗarshi "haka Allah ya tsara mana tamu rayuwar Yayana, mu godewa Allah dan na tabbatar wannan shi ne Alkhairi akan zaman mu kauye". Ya share mata hawayen yana faɗin "Allah ya jikan Umma yayi mata rahma". tace "ameen ya Allah".
Makullin ta mika masa ungo yaya tayar mu tafi, Dady fa bai san mun iya mota ba" tayi maganar tana dariya. Amar ya kare mata kallo daga ita sai kayan jikinta riga da siket, ko ɗankwali batada shi balle mayafi. Ya harare ta "waye zai fita dake haka?".
*Yar'muta Arkilla* ✍ [11/29/2017, 10:01 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*......... *30* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Shigar jikinta ta kalla cikin shagwa6a "kai Yaya Allah wani lokacin ka fiya takura, yanzu meye illar fita na haka?". "hmm bazaki gane ba Feena, idan baki koya yanzu ba to yaushe kike so ki koyi suturta jikinki idan zaki fita?". Tayi shiru tana zun6oro baki. Yai murmushi sannan ya buɗe murfin motar ya fito, ya zagayo ta gefen ta dan ya lura da abinda take son yi wato fushi.
Ya buɗe kofar gefen ta ya janyo hannunta, ba musu ta fito maimakon ya ja hannun nata su tafi sai ma ya janyo ta ya kwantar da ita a gefen jikin shi suka nufi cikin gidan, suna tafe tana dire-diren kafa tana tittirjewa tareda guna-guni. Shi dai ba abinda yake sai lallashi da ban baki. Ilu da Mudi mai gadi kuwa me zasuyi inba dariya ba domin su sun saba ganin irin wannan shagwa6ar ta Uwarɗakin su ba adadi, tana juyowa suka gimtse dariyar, suka cigaba da hirar da suke.
Amar kamar yayi dariya haka dai ya lalla6ata suka shiga gidan, haka wajen saka mata hijabi ma yasha fama, dan a cewar ta karamin mayafi take son yafawa, dakyar da lallashi dai ya samu ta yarda ta sako ɗaya daga cikin hijabanta.
Ya kalli fuskarta wadda ta haɗe ta guri ɗaya, ta cakuɗe kamar mai shirin fashewa da kuka. "Haba dan Allah Feena, so kike kisa ni kuka?". Yayi maganar kamar da gaske shima kukan zai yi, da sauri ta harare shi "wlh kar kayi Kuka, kaji na rantse ko?". Yayi dariya saboda yadda tayi maganar "to naji bazan yi ba, amma kema ki daina wannan fushin da kike Allah sai kika ɗebe kyawu kamar ba ke bace". Tayi saurin kallon shi "da gaske?". "da gaske kuwa, zo ki gani".
Ya kama hannunta ya kai ta gaban madubin ɗakin nata "kalla". Ya nuna mata madubin ta kuwa duba, sai taga ashe da gaske ne sam batayi kyau da fushin ba. Sai ta fara murmushi.
"Lah! Yaya kalli nayi kyau sosai da nayi murmushi". ta faɗa tana dariya. "Sosai ma kuwa, ai ke ɗin kyakkyawar gaske ce, kawai kiyi ta murmushi, kiga yadda kyawunki zai daɗa yin yawa".
Tafukan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta wai kunya taji, Amar yayi dariya a ranshi yana jinjina yadda yake tsintar kansa cikin farin ciki idan yaga kawar tashi tana murmushi ko dariya.
Haka suka fito suna ta kyalkyala dariya, suka shiga motar, Mudi ne ya buɗe musu gate suka fice cikin farin ciki, yana ɗaga musu hannu. Ma'akatan dake zaune a harabar gidan suka bisu da kallon sha'awa, yaran sun yi a rayuwa suna burge kowa.
Ummy ta kalli yar'ta Yusra da fuskarta tayi sharkaf da hawaye tace "kiyi hakuri Yusra, nasan abinda kike tunawa, kuma ni kaina inajin wannan zafin. Amma ki sani wlh har ga Allah yaran nan da kike gani rahma ne a gare mu". Ta tsaiga tana duban yar'tata da surikin ta, kafin ta cigaba "ni kaina da kike gani har yau ina jin zafi da kunan rashin haihuwar ki da kuma 6atan yariyar nan Baby, amma abin mamaki sai zuwan bakin yaran nan ya rage kusan kaso arba'in a cikin ɗari na tarin damuwar. Kuma nasan kema dole taki ta rugu dukda zamomar ki Uwa, kodai har yanzu kina fushi da ikon Allah ne dukda kyautar ta ya koma yi miki?".
Yusra ta share hawayen ta, ta ɗago kai ta kalli Ummy cikin sanyin murya tace "Ummy bawai ina fushi da ikon Allah bane, wallahi ko ɗaya. Tsakani na da Allah sai godiya, bisa kyaututtuka da ya wanzar da rahmarsa da yayi gareni". Ta ɗan yi shiru kafin ta ɗora da cewa "ya'mace na rasa kwaya ɗaya jal, yau gashi na wayi gari da ya'ya biyu mace da namiji. Duk da cewa su ba ya'yana bane amma na tabbatar zasu min rana koma ince suna kan yimim ɗin, suna cire min kewa suna saka ni farin ciki, duk abinda nake so shi suke yi, koda wasa basa kusantar abinda bana so. Ummy nifa ganin sarkar nan ne ya saka ni kuka, in baki manta ba irinta kika sa aka yowa Baby a lokacin da aka haife ta. Ranar da kuka diro Nigeria a ranar kika saka mata ita, haka kuma a ranar aka ɗauke yarinyar".
Sai ta fashe da kuka mai tsanani "ɗa' na jini daban ne Ummy, soyayyar da nake ji ina yiwa Baby ta daban ce abinda na tuna ya saka ni Kuka kenan". Ta faɗa cikin kuka. Tausayin ta ya kara kama Ummy da Alh Tijjani, wanda su dukan su hawayen suke yi, jin bazai iya kallon Yusrar shi tana wannan kukan ba yasa ya tashi tsaye yayi taku zuwa kujerar da take kai itama ya mikar da ita. Sannan ya kama hannunta suka fice daga ɗakin.
Ummy ta bi bayan su da kallo, sai bayan fitar su ta kai hannu ta share nata zafafan hawayen. Ita kanta kukan take domin rashin Baby ba nasu bane su kadai, hadda ita ya shafi zuciyarta.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/25/2017, 3:09 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *31* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Yau kam Amar da Safeenah sun kasa kididdige adadin farin cikin da suke ji a zukatan su, yawo sukayi sosai a cikin garin Kano (ta dabo tumbin giwa) sun zaga guraren hutu da shakatawa bila adadin. Daga karshe suka juya akalar sabuwar motor tasu zuwa Gida cike da farin ciki.
Karfe ɗaya saura suka shiga gidan, dai-dai lokacin da shi kuma Dady yake shirin fita, cike da mamaki ya bisu da kallo har Amar ya daidaitawa motar tsayuwa ya fito, Feena ma fitowar tayi hannunta rike da robar ice cream babba.
"Lah Dady fita zaka yi?" ta tambaye shi baki a washe, kai da ganin ta kasan tana cikin farin ciki. Bai amsa mata ba, sai dai hankalinsa na gareta, na lura kallon da yake mata na nazari da kididdiga ne, Alh Tijjani ya gamsu da gulmar da zuciyarsa ke yawan kawo masa ya yarda ɗari bisa ɗari Feena tayi kama da matarsa Yusra bama kaɗan ba, musamman yanzu da yariyar ta fara girma sai kamanninta da Hjy Yusra suka kara bayyana.
Amar ne ya katsewa Alh tunani da cewa "barka da fitowa Dady" ya faɗi hakan ne bayan ya rusuna gaban sa. "Yauwa barka dai Amar, dama ka iya tuki ban sani ba, yaushe ka koya?". Kafin ya amsa tambayar tayi caraf "hhhh Dady ai tun yana primary 6 Ilu yake koya mishi mota, nima fa yanzu na fara iyawa". Ta karkare da dariyar nan tata mai ɗaukar hankali.
"Kai gaskiya na yaba, madalla da aikin Ilu, naji daɗi sosai, sai ku shiga ciki Momyn ku tana ta neman ku". "Shikenan Dady, a dawo lafiya". Suka faɗa a tare, ya amsa musu yana murmushi, sannan ya shige mota driver ya ja suka fita.
Amar yayi gaba ta ruwa masa baya tana ta zuba mishi surutun ta,suka yi sallama a falon. "Amar ina Kuka tafi?" Momy Yusra ta tambaya tana kallon su. Saida suka kalli juna sannan Feena tayi zaraf "kai Momy shine kika 6ata rai kamar 6ata muka yi?" da sauri Hjy Yusra ta ɗago manyan idonta ta sauke su a kan Feena, zuciyarta na mata wani zafi da raɗaɗi wanda kalaman Feena suka haifar mata. "Ke! Feena are you mad?, did you ever know what you are saying?, pls live this room live me alone". ta faɗa a tsawace irin tsawar da bata ta6a yi musu ba, saida ta dafe kirkira kafin ta nuna musu hanyar ɗakunansu alamar su wuce.
Feena ta fashe da kuka ta ruga ta fice da gudu ta nufi ɗakin ta, hankali tashe Amar ya ruga mata baya. Hjy Yusra kuwa komawa tayi ta zube kan kujerar dake kusa da ita tana maida numfashi, yayinda zuciyarta ke mata Kuna, kalaman Safeenah na neman fasa kwanyar kanta. Da sauri ta mike ta shiga ɗakin ta, toilet ta wuce kai tsaye ta sakarwa kanta ruwa tareda lumshe fararen idonta da sukayi jajur tana tuna halin da ta shiga ɗazu da bata ga su Amar da kanwarsa Safeenah ba.
Wato bayan da Dady gama rarrashin ta ne, sai taji tana son ganin Feena kafin tayi bacci, hannunta ta kai ta danna kararrawar kiran sashen ma'aikatan gidan, mintuna kaɗan Iya ta bayyana a ɗakin, nan tasa Iya ta kira mata Feena a waje ko a sashen su, ta amsa da "to" ta fita. Jimawa kaɗan ta dawo nan take shaidawa Hjyr cewa Amar da Feena basa gidan. Nan da nan hankalita ya tashi, ta mike da kanta ta fito saida ta zaga duka 6angarorin gidan amma bata gansu ba, tun tana yi da karfinta har sassan jikinta suka sanyaye saboda turawa da yadda tayi irin wannan zagayen na nema lokacin da baby ta 6ata.
Sai daga bisani Ilu da Mudi suke gaya mata ai sun fita da sabuwar motarsu, sannan ne ta sami nutsuwa nan ma ba sosai ba, zuciyarta na ta zarya da zullumin kar wani abu ya same su, sai gashi kuma Feena tazo tana sinfonia kansu da kalmar da ba zata ta6a mantawa da ita ba, wato *6ata*.
Towel ta ɗauro ta fito bayan ta tabbabar ruwan sun gama ratsa jikinta, doguwar riga ta zira bayan ta gama tsane jikinta. Ta koma ta baje bisa lallausan gadonta, tana tuna yadda Feena ta bar falonta da gudu tana kuka saboda yadda ta mata magana, sai taji bata kyauta ba, saboda yariyar bata San komai dangane da abinda ke ranta ba.
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/25/2017, 5:33 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *32* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Bangaren Feena kuwa Da zuwa ɗakinta sai ta afka bisa lallausan gadonta tana karawa kukanta sauti, Amar da ke biye da bayanta duk nutsuwarsa ta fara kwacewa, dan duk fad'in duniya babu abinda ya tsana bisa yaga Feenar sa cikin halin damuwa balle ma ta kaita ga kuka tana zubda gwalagwalan hawayenta.
Gefen gadon ya zauna dai-dai kanta, shiru yayi na lokaci mai tsayi yana kallon ta, yayin da sautin kukan nata ke masa yawo a zuci yana ji kamar kankarar kirjinsa ake da wuka ko wani abu mai kaifi. "Feena, ya kira Sunan lokacin da ya kai hannunsa bisa kanta, "dan Allah kiyi shiru kanwata da gaske kukan ki ciwo yake min a nan". Ya faɗa yana nuna kirjinsa da ɗaya hannunsa, Safeenah juyar da kanta gefe tana sheshshekar kuka "Feena pls" ya koma faɗa a tausashe, "kanwata zaki sakani a wani hali, ki sani Momy batai miki tsawa dan tsana ko jin haushin ki ba, hasali ma tayi miki tsawa ne dan tana kaunar ki tsakanin ta Da Allah".
Dara-daran idon nan nata ta ɗago ta sauke su fes a kan sa, tana nazarin abinda ya fito bakin sa. "me kake so kace min? Did I do something wrong da za'ayimin tsawa a kai?". "for her understand u do Feena".
Tashi tayi ta zauna da kyau tana kallon shi "meye wannan abin, me nayiwa Momy da zata min tsawa yaya?". Cikin tausayin ta da kuma jinjinawa yarantar ta yasa hannu ya goge mata hawaye yana faɗin "me yasa bakya son faɗa Feena?". Ta yatsina fuska "ni kawai bana so ne, ai waɗanda aka tsana ne kawai ake yiwa faɗa". Ta karashe maganar cikeda yaranta "hmm Feena ho, to bari kiji in gaya miki duk wanda kika ga ana yi mishi faɗa akan abinda bai dace ba to shine asalin wanda ake so, kuma wannan shine mai gata...
Ya cigaba da cewa "Momy tana son mu sosai ta damu da rayuwar mu, adalcinta ne yasa ta dai-daita soyayyar da take mana da wadda takewa yar'da ta haifa, Momy tayi miki tsawa ne saboda maganar *6ata* da kika danganta da mu, kin san meyasa?". Ta girgiza kai tana kallon sa, murmushi yayi mata kafin yace "saboda kaunar da take mana bata so mu *6ata* ta rasa mu kamar yadda ta rasa yar'ta Baby".
Shiru ya ratsa ɗakin Amar ya zubawa kanwarsa ido, yana kallon yadda ta dage tana nazarin maganganun sa, "lallai Feena akwai kuruciya" ya ayyana a ransa
A hankali ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga ciki, idanuwanta kyar akan su, sannan ta tako cikin sanyain jiki ta isa garesu. Hjy Yusra kenan wadda ta kasa jure zogin da cuciyarta ke yi mata akan halin 6acin ran da ta jefa Feena ciki, dukkanin su ita suke kallo cikeda tausayin ta har Safeenar domin zuwa yanzu ta fahimci dalilin Hjyr na yi mata tsawa.
Da sauri ta mike ta rungume Momyn itama sai ta rungume ta, kusan a tare suka sauke numfashi mai kunshe da abubuwa daban-daban, "Momy pls forgive me, I don't really understand how it's feel, I know it's hurt, and I know you are doing all this for us just because you love us, you are different Momy na, we love you too". Duk wannan maganganun tayi su ne tana kankame da Momy, wadda take jin kalaman yarinyar kamar ana yafawa zuciyarta ruwan sanyi, soyayyar ta Da kaunar ta na data ninkuwa a ranta cikin sautin kuka ta fara magana.
"Thank God you understand me Feena, I don't want to lose you as I lose her, kiyi ko'kari ki fahimce ni ina matukar kaunar ku keda yayanki, Kun kasance min tamkar ya'yan cikina". Hawaye ne suka gangaro daga idon Amar, tausayin baiwar Allah nan ya lullu6e shi, sosai kalamanta suka kara narkar da zuciyar matasa, a 6angare ɗaya kuma soyayyar da suke mata ta kara ha6aka.
Nan da nan Feena ta warware su duka suka ɗunguma sashen da Ummy ta sauka, a nan aka ci dare ana hira kafin daga bisani suka yi mata sallama suka fita, Amar ya nufi ɗakin sa Feena da Momy kuwa ɗakinta suka wuce dan yau Hjy Babba ce da girki a can Dady yake, (Hjyr Mubarak kenan Hjy Ummu). Dama duk ranar girkin ta Feena a ɗakin Momy take kwana, wannan ne ya kara musu shakuwa da kusanci, domin a can ma wata sabuwar hirar suke kullawa su yita yi har sai Feena tayi bacci, sannan Momy ta mata addu'a ta rufe ta da blanket itama ta kwanta daf da ita.
Haka rayuwa tayi gaba da tafiya cikin farin ciki da annashuwa, inda lokaci ya ke ta kwararawa, watanni biyu Feena tayi tana hutar kafin daga bisani results ɗin su ya fito, jarrabawa tayi kyau Alhamdulillah, Safeenah Wakkala taci exam 100%. Ba jimawa aka kammala mata komai ta koma fannin Secondary duk a cikin Makarantar, wai a ranar Amar ji yayi tamkar an maklakar masa duka garin Kano saboda murna, da yawan ɗalibai da Malamai sun yita mamaki, yadda nutsatstsen yaron ya sauya a wuni ɗaya da zuwan wata yarinya, suka yita ce-ce kace kafin su san takamaiman matsayin Safeenah a gurin Amar Wakkala, gwarzo kuma jarumi ɗalibi na farko wajen ko'karin cin jarrabawa, sai dai tarin miskilanci da kyale mutane.
Tunda ya fara zuwa school ɗin bai yi aboki ba, dukda tarin sa'anninsa masu neman cusa kansu gare shi, shi kam sam baya saurarar su. Baya magana da kowa inba ta kama dole ba, sai gashi yau sun gashi da wata yarinya tanata juya shi, kamar remote control, haka yake bin duk wani umarninta, haka a filin makaranta lokacin break, suka kafa dandalin wasar su gefe, daga ita sai shi suke wasan ball abinda bai ta6a yi ba koda da maza yan'uwansa balle da mace.
Sai gaba ɗaya hankulan ɗaliban suka dawo kansu, bayan burgewa akwai alamun mamaki karara a fuskar ɗaliban.
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/25/2017, 7:30 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *33* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Haka suka cigaba da tafiyar da rayuwar su a makarantar ganin sha'awa, suna burge kowa a school ɗin tun ba'a san su waye ba har ɗalibai da malaman suka fahimci yaya da kanwa ne, sun gane hakan ne a lokacin taron Yara da Iyayensu wanda hukumar gudanarwar makarantar ta shirya, inda suka ga Iyayen Amar sune Iyayen Feena wato dai Iyayensu ɗaya.
To da haka dai sukayi ta mulmula rayuwa tana mulmula su, kwanci tashi, da daɗi da ba daɗi Momy da Dady na iya ko'karin su wajen kula da yaran da faranta musu, 6angaren Hjy Ummu kuwa zaman nan nasu na doya da manja yana nan itada abokiyar zamanta Yusra, wadda sam bata kulata, bata shiga sabgar ta, hasalima kullum cikin gargaɗin su Feena take akan su yiwa Hjy biyayya kamar yadda suke mata, Mubarak kuma su rike shi a matsayin ɗan'uwa.
Ita kuwa Hjy Ummu a kullum cikin jin zafi da takaicin Yusra take, tareda hura wutar gaba tsakanin yaron wajenta Mubarak da su Amar, kullum nuna mishi take Dady yafi son su akan sa shi da suka zo suka samu a gidan, hatta motar da aka saya musu saida shima aka siya masa iri ɗaya kala ce kawai ta bambanta, amma saida tayita zugashi akan wai ta su Feena tafi tashi kyawu.
Rayuwa kenan mai hali baya canjawa, ta sakanta yaronta Mubarak ta nuna mishi jin daɗin duniya tun bai tauna ba balle ya haɗa, yaro ɗan 22years yasa yayi shaye-shaye, ya nemi mata, ya saci kuɗin Dady idan ya gani, kasancewar yana gaban su a karatu yanzu haka yana jami'a matakin farko, Sam babu jituwa tsakanin sa da Amar domin ko wannen su kallon tsana yake yiwa ɗan'uwan sa, dambe suke yi sosai, domin wasu lokutan ma idan yana neman Amar da rigima ta kan Safeenah yake farawa wadda yasan muddin ya ta6ata to dole Amar zai kula shi.
Yau ranar girkin Hjy Babba ne, saboda haka bayan sun kammala hira Hjy Yusra da Feena suka nufi ɗakinta, Amar kuma ya nufi nasa ɗakin. Bayan yar hirar da suke yi a ɗakin sai ta kwanta tayi shiru tana nazarin sabon al'anarin da take ji a jikinta yau, tax juyin duniyar nan tana neman bacci ya ɗauke ta amma bata samu ba, zogi da raɗaɗin da take ji a mararta sai kara yawa yake yi, tun tana iya jurewa har ta fara kuka kasa-kasa.
Momy Yusra dake gefenta tayi zaraf ta tashi zaune, Safeenah? Lafiyar ki kuwa? me yake damun ki?". Ta jero mata tambayoyin lokacin da take ɗago ta, ta mikar da ita zaune tana nazarin fuskar ta, wadda duk ta kumbura kana idanunta sukayi jajir.
"Safeenah lfy? What's wrong with you?" cikin kukan ta nunawa Momy mararta da yatsa, alamar a nan take jin ciwon, hankalin Momy yayi matukar tashi, da sauri ta mike tsaye tareda mikar da Safeenah da nufin ta kaita asibiti.