Ja'jirtacce complete - Chapter 7
Ja'jirtacce complete Chapter 7: Ja'jirtacce complete Chapter 7. Abinda ta gani a jikin bedsheet ɗinta ne ya ganar da ita matsalar Feena, sai jikinta yayi…
4,428 words
Abinda ta gani a jikin bedsheet ɗinta ne ya ganar da ita matsalar Feena, sai jikinta yayi sanyi, hankalinta ya ɗan kwanta. Feena kam idonta a rufe sai Kuka take tana gimtse fuska, lebenta har ja yayi saboda cizon da take masa. Jin Momy ta tashe ta tsaye kuma tayi shiru yasa ta buɗe idonta ta sauke su kan Momy, fuska a marairaice tace "Momy marata, wlh ciwo take min sosai, ganin kan Momy na kallon gadon yasa itama tayi can da idonta, ai kuwa karaf suka sauka akan jinin da ya fara fitar mata a jiki har ya 6atawa Momy zanin gado, cikin rashin fahimta ta kalli Momy "na shiga uku na yau me zan gani, Momy mutuwa zanyi?, yan'ciki na ne suka fashe ko me wlh ina zubar da jini". Sai kuma ta fashe da Kuka ta kankame Momy, kuka take sosai tana jerowa Momy tambayoyi waɗanda Momy ta rasa yadda zata amsa mata su.
A madadin haka sai ta kama hannun ta suka shiga toilet ta cire mata kayan jikin ta, sannan ta tsabtace mata shi ta nayi tana mata sannu, ita kuwa ta gama tsurewa, gaba ɗaya tunanin ta ya bata yan'cikinta ne suka fashe kuma babu makawa mutuwa za'ayi, wannan tunanin yana cikin abinda ya hanata tsagaita kukan da take.
Sabon pad da pant Hjy ta ɗauko ta haɗa mata, da kanta ta manna mata always ɗin a jikin pant sannan ta bata tace ta saka, ba musu ta kar6a ta saka, sai dai har yanzu bata daina kukan ba.
Hjy Yusra kuwa banda rarrashinta ba abinda take, saida ta tabbatar ta kimtsa ta Da wasu kayan sannan ta riko hannunta zuwa ɗakin ta yake bedsheet ɗinanan ta shimfiɗa wani, ta zaunar da Feena gefen gadon sannan ita kuma ta koma toilet, ta kama zanin gadon nan dai-dai inda ya 6aci ta wanke shi tas, abinda bata ta6a yi ba a rayuwar ta, sannan ta dawo ta zauna gefen Feena wadda har yanzu Kuka take, tana ganin ta ta fara rokon ta akan ta barta ta tafi gun Yayanta ta ganshi kafin ta mutu.
Momy ta tattara nutsuwarta ta fuskanci Safeenah, tace "Feena ina son ki saurare ni da kunnen basira, kuma kiyi amfani da duk wani abu da zan gaya miki".
Safeenah tayi zuru tana kallon Momy, cikin yanayin damuwa da tashin hankali.
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 8:10 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *34* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Cikin sanyi da lalkausar murya, ta fara yiwa Safeenah bayanin wannan hali da ta tsinci kanta a ciki, ta tabbatar mata da cewa al'ada ta fara (haila) wato menstruation a turance, sosai ta wayar mata kai akan messes, kuma ta fahimta domin an jima ana yi musu bayanin lalurar a islamiyya, tasan abubuwa da yawa akan sa, kamar barin salla da mai lalurar zai yi har zuwa ranar da zai yanke, da yadda zai tsabtace jikinsa ya koma salla a lokacin da ya yanke, da nisantar ta6a alkur'ani mai tsarki da dai sauran su.
Sai taji kunyar Momy ta kama ta, ta rufe fuska da tafukan hannayen ta, na gane Momy Malaman makarantar mu suna yawan gaya mana wannan abin da hukunce-hukuncen sa, kuma duka na sani in Allah ya yarda zan zamo mai kiyayewa. Momy taji daɗin yadda yarinyar ta fahimta, tayi murmushi tana faɗin gud girl, dare sosai suka kai suna hira Momy na kara wayar mata kai akan abinda ya shafi al'ada, ta tabbatar mata da dole ne mai wannan abin ya zama cikakken mai tsabta, baya ga wanna ta nusar da ita abubuwa masu yawan gaske, daga karshe ta rufe da nasihohi masu sanyi da ratsa jiki.
Duka dai Safeenah ta fahimce ta, magunguna Momy ta haɗo mata tasha sannan ta kwanta bayan tayi filo da cinyar Momy dake kwance, wai a haka zatafi jin daɗin kwanciya, Momy dai bata ce komai ba, saima shafa kanta da ta shiga yi, a hankali kuwa bacci yayi kasa da ita.
Saida ta tabbatar tayi baccin sannan ta ɗaga ta ta gyara mata kwanciyar ta, ta rufe ta Da mayafi, sannan itama ta kwanta tana mai cigaba da kallon fuskar Safeenah, fuskar da tafi soyuwa a cikin zuciyarta.
Washe gari suka tashi kamar yadda suka saba, da asuba kenan Momy ta ɗauro alwala ta tashi salla, Feena kuwa toilet ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi tayi wanka, ta fito lokacin Momy ta idar da salla tana addu'a, hakan yasa Feena ta fara tsane jikin ta tukunna, sannan ta fara shafa lafiyayyun lotions ɗin su, bayan ta kammala ne ta ɗauko wata doguwar riga ta saka, kasancewar da yawa kayan ta a ɗakin suke, sai da Momy ta shafa addu'a sannan ta tashi, ta ninke sallaya ta mayar, a wardrobe ɗin ta koma ɗaukowa Feena wani sabon pad da wani pant ta bata, ita ta koya mata yadda zata rika haɗa su, ta kuwa iya duk da tana jin kunyar Momy sosai.
Lafiyar gado ta koma bi ta lafe saida gari ya waye, sannan ta farka a lokacin Momy ta fita kitchen, ganin haka yasa ta shige toilet wani wankan ta kuma yi sannan ta fito ta shirya, cikin wata atamfa super yar' asali, kalar light green, ɗinkin riga da sket, kayan sun mata kyawu matuka, ta taje lafiyayyen gashin kanta, ya kwanta ya luf-luf, ta ɗaure shi da ribbon kalar kayan jikinta, ta naɗa ɗankwalin tayi kyakkyawan ɗauri ɗan yayi, yarinya ta fito fes da ita.
Suna zaune a kan dinning suna cin abinci, Momy da Amar wanda duk hankalin shi na kan kanwarsa, wadda tun ɗazu yaso yaje ya taso ta Momy tace ya barta tukunna tunda bata jin daɗin jikin ta, sai yayi duk hankalin sa ya tashi, abincin ma sakawa kawai yake ba tareda gane takamaiman ɗanɗanon sa ba. Momy ta lura da yadda yake kimsa abincin tamkar wanda aka yiwa dole, sai ta basar ta kyale shi, domin tasan damuwar sa Feena ce.
Tare suka juyo lokacin da suka jiyo takun takalmin ta, tana sakkowa daga kan benen, Amar kam kasa hakura yayi, da sauri mike yayo kanta, "Safeenah kanwata, ya jikin naki?". Yayi maganar lokacin da ya riko hannunta, murmushin nan nata ta sake mishi, kafin tace "lau nake Yayana, fatan kaima haka, barka da safiya".
Ta shafi kumatun ta yana faɗin, "na shiga uku Momy, Feena ta fara 6oye min damuwar ta, kinga wai bata gaya min batada lafiya ba". Momy tayi dariya tana cewa "nima ai ba gaya maka nayi ba kawai dai cewa nayi karka taso ta saboda bata jin daɗi". Ajiyar zuciya ta saki jin Momy bata gayawa yayan nata abinda ya faru da ita a daren jiya ba, "bana son damuwar ka ne Yayana, tunda na riga naji sauki to miye na gaya maka?". "Shikenan amma kin tabbata kin ji sauki ko?". Ta gyaɗa kai "sosai ma kuwa, kaikam zo mu ci abinci". Ta kama hannun sa suka isa gun dinning, ta ja mishi kujera shima ya janyo mata suka zauna fuskoki da zukatan su tas da farinciki. Momy kam nata ido ne, domin ta riga ta saba, tunda take a duniyar nan bata ta6a ganin soyayyar yaya da kanwa kamar irin ta su Feena da Amar ba.
Sai a lokacin ya ware, ya saki jiki ya ci abincin sosai, haka itama, sai watanni suke da labarun raha, Yusra kam banda dariya ba abinda take, haka Dady ya fito ya same su, sosai zuciyarsa tayi fari, soyayyar yaran ta kara samun muhalli a rayuwar sa, domin ya yarda a yanzu yaran sune farin cikin Matarsa da shi kan shi ma.
Tare suka mike suka taro shi, Amar ya kar6i jakar shi Feena kuma ta riko hannun shi suna mishi ina kwana, ya amsa cikin fara'ar nan tashi da sakin fuska, idon sa akan Matarsa yace "Maman yara, a nata hira ko?" "barka da safiya, an tashi lafiya". Ta gaishe shi kicin fara'a, ya amsa mata cikeda jin daɗi, Mubarak dake bayan shi sai hararar Hjyr da yaranta yake, Dady ya kalle shi "boy ba zaka gaida Maman ka ba?", ya kara tamke fuska, ya kalle ta kasa-kasa "ina kwana" Yusra tayi murmushi "lafiya lau Mubarak, ka tashi lafiya?" bai koma tanka mata ba ya fice daga falon yayi waje. Dady ya girgiza kai, ya kalli Yusra "ki kara hakuri da halayyar Ummu da yaron nan Mubarak, dan Allah Yusra kar ki yarda kisa wata damuwar a ranki kinyi?". Yana gama faɗin haka ya juya "ni Na fita" "a dawo lafiya Alh, Ubangiji Allah ya tsare ka, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah ya bada sa'a da rabo mai albarka ". "ameen Yusra nagode da addu'a Allah ya albarkaci rayuwar ki da ta yaran ki". Ya fice yaran suka rufa masa baya dan yi masa rakiya.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah. Rayuwa ta nisa lokuta sun shuɗe, abubuwa da yawa sun faru, an rasa da yawa kuma an sami da yawa, Amar da Safeenah an girma, ya kammala secondary har ya sami gurbin karatu a jami'a, Safeenah ma ta kammala secondary tana jiran sakamakon jarrabawa.
Suna sami kulawa sosai, sam basu ta6a tunanin samun irin wannan gatan ba a rayuwar su, sau da yawa sukan ke6e wasu lokuta domin yin addu'oi ga Iyayen rokon su Alh Wakkala da Hjy Yusra, alkhairin waɗannan mutanen a gare su abu ne mai wahalar samu a wannan rayuwar
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/26/2017, 9:59 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *35* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Safeenah yan'mata jarrabawa ta fito harma an sama mata gurbin karatu a jami'ar bayero inda Amar yake level 1, yau itace rana ta farko da zata fara shiga jami'a, ta riga kowa farkawa a gidan, tunda tayi salla ta nufi kitchen, ta samu ma'aikatan nata kiciniyar harhaɗa break, ta saka hannun ta suka cigaba da aikin tare, kamar yadda Momy Yusra take yi.
Shida da rabi Yusra ta iso kitchen, sosai try mamakin ganin Feena da yadda ta zage take aiki, "Feena dear, ya akayi yau kika rigani tashi?" murmushi tayi tareda juyowa ta kalli Momy, tana sosa kyeya "uhum, ba komai Momyna kin san yau ne zan fara zuwa school, kuma da lecture karfe takwas zan fara, shiyasa na tashi da wuri". Dariya sosai Momy tayi "Feena ho, yarinya ta ba dai zumuɗi ba, to kawo aikin maza kije ki fara shiri dan nasan yau wankan ma na musamman za'ayi". Kunya ce ta kama ta, sumi-sumi ta ra6a Momy ta wuce, ta shiga ɗakinta kai tsaye toilet ta nufa, ta haɗa ruwan ɗumi ta shige cikin su, mintuna goma tayi tana wankan sannan ta fito, tabbas maganar Momy tayi fari domin yau komai na musamman tayi, bayan kwalliyar ma takai mintuna talatin tana canje-canjen kaya duk wanda ta saka sai taga kamar basu mata kyau ba ta cire, haka Momy ta shigo ta same ta duk ta cika gadonta da kaya, "ikon Allah". Momy ta faɗa tana kallon Safeenah, "wannan kuma miye Feena?" "yauwa Momy pls zo ki taya ni za6a, na rasa kalar kayan da zan saka, pls Mom". Momy tayi murmushi "lallai yau naga yar jami'a, Feena tun ba'a shiga ba?" tayi dariya ta rufe fuskar ta da tafukan hannunta "Momy bazaki gane ba, kin san ina bin yaya wasu lokutan, wlh baki gani ba yadda yan'jami'a suke kure wanka".
"To naji zo ki gani" ta kama hannun ta ta zaunar da ita tukunna, sannan ta shiga duba kayan dake baje bisa gadon, can ta hango wani swiesless red colour, mai kananan flowers, masu kalar milk ta ɗauko shi ta bata, "ki saka wannan na tabbatar zai amshi jikinki". Ta kar6a da sauri tana godiya, "thanks Mom" ta manna mata kiss a kumatu, Yusra tayi dariya tana girgiza kai. Da kanta ta ninke ragowar kayan da Feena ta fitar ta mayar dasu cikin wardrobe ta rufe, ta bar ta nan tana saka kaya.
Saida suka kusa kammala break sannan ta fito, cikin takun nan nata na kasaita ta sakko daga upstairs, tare suka maida hankalin su gareta, Amar da Momy kenan, suka zuba mata ido kamar yau suka fara ganin ta, saida ita iso inda suke sannan suka iya ɗauke mata ido, kowannen su da abinda yake ji a ransa. Ita dai Yusra kallon tsaf takewa Feena dan ganin yau ta fito ita sak, a lokacin da take budurwa kamar haka take ba ba wani bambanci. Shi kuwa Amar kallon da yake mata na daban ne dan tunda take ado bata ta6a yin wanda ya fitar da ita kamar wannan ba, kayan sun kama jikinta sosai sannan sun bayyana kuruciyar ta ainun, tsayayyar budurwa yar shekaru ashirin cif-cif, fuskar nan tata ta shimfiɗu da rantsattsiyar kwalliyar ta, kayan jikinta ɗinkin doguwar riga ne fited gown sai takalmi da hand bag ɗinta milk colour haka siririn mayafinta ma, ɗaurin ɗankwalin ya zauna ɗan tamkar anan aka halicce shi.
Ji yayi sassan jikin sa sun yi sanyi, zuciyar sa ta dugunzuma, ya rasa gane gabanta dangane da kwalliyar Safeenah, shin daɗin ganinta yaji ko akasin hakan?. Ita ce ta katse masa tuna ni da zankaɗeɗiyar muryar ta, tana faɗin "badai har Dady ya fita ba?". "hmm Feena manya, kin kuwa san lokacin da kika 6ata kina shiri?". Momy ta tambaye ta, sai taji kunya ta kama ta. Amar kam bai sami damar yin magana ba sam ya kasa gano yanayin da yake ciki.
Zungurar shi tayi bayan ta zauna, tana faɗin "barka da safiya Yaya" "yauwa barka dai Feena kin tashi lafiya?" tayi murmushi "lafiya lau, amma Yaya baka ce nayi kyau ba" tayi maganar tana zun6uro baki, "ni na isa, ai dama jira nake ki zauna in tambaya any ba canjin fuska kika yi ba?" yayi maganar yana murmushi. Momy ta ka6i maganar sosai kuwa Amar ni kaina ina tantama, yau sai naga fuskar kamar tawa. Dukkan su suka yi dariya
Sama-sama tayi break ɗin, cike da zumuɗin zuwa makarantar tana yi suna mata dariya, da haka har ta kammala ta kira Uwani mai dafa musu abinci tace ta kawo mata abinda suka yi, ba jimawa ta dawo ɗauke da leda babba a hannunta ta bawa Safeenah, ta kar6a tayi godiya suka mike, suka yiwa Momy sallama suka fita, ta bisu da kallo cike da sha'awa.
Tafe suke tana zuba masa hira da tambayoyi, waɗanda ya kasa amsa mata ko ɗaya, saboda tsantsar takaicin da ya tsinci kansa daji gameda shigar da tayi, shi kansa ya kasa gane kansa yau ne rana ta farko da ya fara jin ciwon kar wasu su kalleta, saboda tsantsar kyawun da tayi, musamman a sanin da ya yiwa jami'a akwai da yawa waɗanda basuda aiki sai kallon kyawawa irinta, wasun ma har da tanka musu suke.
Dogon tsaki ya ja lokacin ya dai-daita tsayuwar motar a harabar makarantar, da sauri ta kalle shi "Yaya lafiya?" saida yayi ko'karin dai-daita nutduwar sa sannan ya kakaro wani murmushi da bai wuce le6en shi ba, yace "ba komai, wani malami na tuna ɗan tsurku ne, shi zai ɗauke mu anjima". Tayi dariya "lallai Yaya an zama yan gari, a malaman ma har da yan tsurku".
Bai tanka mata ba, sai dai dariyar yaken da yayi mata, suka buɗe kifofin motar suka fito, fuskokin su ɗauke da yalwataccen murmushi, ita dai Safeenah murmushin farin ciki take da murnar ranar ta ta farko a jami'a, shi kuwa Amar yana yi ne dan karta gano halin damuwar da yake ciki.
Haka suka tsatsa cikin makarantar hannayen su sarke da na juna, suna tafe tana zuba shiko yana binta da murmushi. Sannu a hankali yan'matan dake kai koma a tsakiyar makarantar suka fara maida hankalin su akan kyawawan matasan, yayinda da yawa daga cikin su suka raina kansu, suka kuma tabbatar da dalilin Amar na rashin sake fuska gare su. Wata ɗaya daga cikin tawagar kawayen Jidda tace "wai zankaɗi, wanda yake da wannan santaleliyar budurwar dama yaushe zai tsaya ta kan mu.
Jidda wata department met ɗinsa dake zaune da kawayen nata, ta kura musu ido, zuciyarta na tafarfasa, nan take tsanar Safeenah ta tsargu a cikin zuciyarta, ji tayi kamar ta tashi taje ta shake yarinyar har sai ta mutu.
Tofa🤔 Wace ce Jidda?, me kuma Feena ta kashe mata da shigowar ta jami'a?.
Ku biyo ni domin jin dalilin, yanzu ne wasar zata fara 😎.
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [11/27/2017, 8:10 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *36* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Har kofar ɗakin karatun su ya raka ta tareda, bayan ya nuna mata inda zata same shi idan ta fito. Duk zumuɗin da take saida ya kau, lokacin da taga Amar zai tafi ya bar ta, shiru tayi tana kallon shi kafin kace me sai hawaye shar a fuskar ta. Nan da nan hanklin sa ya tashi, ya kama hannunta suka kauce daga kofar ajin saboda masu shiga, "haba Feena, haba mana kanwata, so kika karatun yau ya wuce ni?". Ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in haka ne meyasa kike kuka dan zan tafi"? Cikin shagwa6a da yaranta ta fara magana" Yaya ni bana so ka barni ne, bansan kowa a nan ba, nidai zan bika naku ajin". Kusan dariya maganar ta'ta ta bashi, sai ya daure yace "Feena manya, ta ya zaki bini ajin mu bacin kema ga naku ajin nan, kuma fa zaman na ɗan lokaci ne da zarar kuka gama wannan lecture ai muna tare ko". Yayi maganar da sigar rarrashi. "To shikenan ka tafi karka makara, da zarar na fito zan same ka acan" "yauwa Feena na, sai mun fito ko" ya faɗa yana share mata hawaye da handkerchief ɗan dake hannun sa, saida ya manna mata kiss a gashi sannan ya kama hannunta ya shigar da ita cikin class ɗin, a kujerar gaba ya zaunar da ita kusa da wata ɗaliba, sannan ya juya ya fice yana yi mata murmushi.
Ta bishi da kallo sai da ya kurewa ganin ta, sannan ta sauke numfashi ta kira kanta bisa table. Amar kuwa yana fita ya nufi department ɗin su, sauri-sauri yake tafiyar saboda lokaci baya so ya haɗu da fushin fitinannen Malamin nan nasu.
Abu kaɗan ya rage ya kaureta saboda yadda ta tari gaban shi bada sanin sa ba, yaja ya tsaya yana kare mata kallo cikeda mamaki. Duk da yau ya fara ganin ta hakan bai hana shi gano tana cikin 6acin rai ba, ya tambayi kansa a ran sa yace "wannan kuma me na mata?" Jidda kuwa sai cika take tana batsewa akan dalilin da bai sani ba, "Ke lafiya, kika zo kika tare min hanya?" yayi mata tambayar a tsawace. Amma ga mamakin sa sai ta tintsire da dariya a madadin amsa tambayar shi, abinda ya kara harzuka Amar kenan. Ya canza hanya zuwa gefen ta ya cigaba da tafiya "dakata Amar" yaji ta faɗa cikin tsawa, sai yaji yana son sanin dalilin da yasa ta tsayar da ɗin, cak! yaja ya tsaya ba tareda ya juyo ba, hakan bai dame ta ba, ta fara magana cikin 6acin rai,
"yau shekara ɗaya kenan ido na yana kan ka, tun randa na fara ganin ka naji ina kaunar ka, ina ta fara da soyayyar ka tsayin lokacin nan, ganin baka kula ko wacce mace yasa nake shayin tunkarar ka, amma yau sai gashi ka bayyana da wata mace a gabana, wannan yana nufin kana soyayya, kana kula mata, amma sai ka nuna kamar baka San komai ba"
Tayi shiru sannan tayi taku ta isa gaban sa, Amar wanda yayi tsaye tamkar wanda aka dasa kallon ta yaci gaba da yi ba tareda ya iya ɗaga harshe ya mata magana ba, Jidda ta sauke numfashi sannan ta kwantar da murya lokacin da hawaye suka fara bin kuncin ta.
"Amar ina son ka, ina maka son da ban ta6a yiwa wani irin sa ba, a baya na zata baka kula ko wacce mace ashe hauka nake kana da wacce kake so, kar ka yi min haka Amar, idan ka su6ucemin zan rasa rai na, shekara ɗaya nayi ina renon son ka, na roke ka karka nisanta tsakanina da kai". Ta karashe maganar cikin kuka tareda durkushewa gaban sa, hanklin sa ya kara tashi, ganin yadda mutane ke kallon su yasa dole ya sassauta zuciyar sa, yace "naji, duk naji abinda kika faɗa, amma dan Allah ki tashi kinga mutane sai kallon ki suke, ba a haka ya kamata muyi maganar ba".
Jidda ta tashi tsaye tana sharar kwalla, ta kalle shi "ya kake so nayi?, haka zan cigaba da zama muddin baka saurare ni ba". Yayi ajiyar zuciya sannan ya kwatanta mata inda zasu zauna bayan lecture, yace ta same shi can. A kan haka suka raba zuciyar sa cunkus da mamaki da kuma tsoron abinda ke shirin faruwa da shi...
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [12/6/2017, 5:40 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *37* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*
A ɗakin karatun ma haka ya kasance sama-sama yake jin abinda ake yi. Har aka kammala kwakwalwar sa bata ɗauki komai ba. (Allah sarki Amar)
To haka ma 6angaren karatun su Feena ɗaliban sun yaba sosai da irin son da wannan da ya kawo ta yake mata, a tunanin su Amar saurayin ta ne.
Maryam wadda ke zaune a kusa da ita, ita ce ta fara yi mata magana "sannu frnd suna na Maryam Muktar, da fatan zamu zama abokai". Murmushi kawai ta mata ba tareda tace komai ba ta koma kifa kanta da table. bata koma ɗagowa ba sai lokacin da ta ji shigowar Malamin da zai ɗauke su lacture.
Mintuna biyar da zaman shi sai gata ta iso, Feena ita ce wadda ta fara zuwa bayan fitar Malamin su. Amar na zaune yana nazarin abin yi, saka yake yana warwarewa tunda yake bai ta6a Soyayya ba, yau da rana tsaka wannan ta bijiro masa da ita. Tambayar kansa yake anya kuwa zai iya?, to inma zai iya ta ina zai fara?". Yana cikin wannan yanayin ne ya ji an rufe masa ido ta baya, kamshin turaren da yaji ne ya tabbatar masa Safeenah ce. Dan haka yasa nashi hannayen ya janyo ta, ya zagayo da ita gaban sa kana yayi ko'karin danne damuwarsa yana faɗin "barka da fitowa yar' jami'a". dariya tayi sosai saboda yadda yayi maganar. "Allah yaya yau ina cikin farin ciki".
"Naga alama ai" ya faɗa yana murmushi. Duk wannan abin da suke yi akan idon Jidda, tana kallon su kasancewar itama fitowar ta kenan daga class, ta nufo inda ya kwatanta matan.
Tun daga nesa idanuwanta suka yi tozali da tauraron nata, duk da cewa babu wata fara'a ko murmushi akan fuskar tashi ita ganin kyanshi take tamkar sabon wata tsayuwar yau. Sai murmushi take, tana ji a ranta ta sami shiga ganin yadda ya bawa ganawa da ita muhimmanci har ma ya rigata zuwa wajen. Ganin Feena tayi kamar wadda aka jeho daga sama ta nufi inda Amar ɗin yake zaune. Hakan ne yasa dole taja ta tsaya tana kare musu kallo, a take zuciyar ta ta ɗauki zafi, wani kululun bakin ciki ya tokare mata a makogwaro, "dama ya kira ta nan ne dan ya ci mata mutunci?". Ta tambayi kanta, tambayar da batada amsar ta
Ta kasa karasawa gurin, ta kuma kasa juyawa ta koma cikin Makaranta. A gaban idon ta Feena ta fito musu da kayan abinci, a plate ɗaya ta zuba musu, dambun nama ne wanda yaji haɗi yasha kaya, sai robar ruwa ɗaya da ta lemun fanta, nan ma kofi ɗaya ta dire a tsakiyar su. Abinda ya daɗa tunzura zuciyar Jidda kenan. Wato komai ma ɗaya suke amfani da shi. Ta jinjina lamarin a ranta, tareda kissimawa tana so ta tantance irin soyayyar dake tsakanin su.
Can taji zuciyarta na gargaɗin ta akan ta hakura da wannan guy ɗin, tunda har ta ga da wadda yake so kuma ta tabbata wannan ta fita da komai da ɗa namiji zai so a jikin mace, Sai dai ita ta girme ta da shekaru wata zuciyar ta ce mata "a kul karki yarda ki sadaukar da soyayyar ki saboda wata macen, kamata yayi ki dage kema ki nemi soyayyar sa kamar yadda ta nema ta samu. Namiji ai tsamiya ne ki tsotsa ki bani in tsotsa.
Hannun ta tasa ta share zafafan hawayen da suka fara jerin gwano bisa kumatunta. Igiyar so na janta, zuciyarta na dad'a yin nutso a tafkin kaunar sa. Saida ta danni zuciyarta sosai sannan ta iya takawa ta isa inda suke zaune. Dakyar harshenta ya iya dai-daita kalmomin Sallamar da tayi musu. Tare suka amsa Sallamar kamar yadda suka ɗago kai tare suna rige-rigen ganin wadda ke musu Sallamar. Wani irin faɗuwar gaba ne ya riske shi a sakamakon ganin wadda ke tsaye a gaban sa. Feena kuwa murmushi ta koma saki ganin bakuwar fuskar da bata sani ba, "sannun ku da hutawa, Amar gunka na zo". Ta faɗa kanta na kasa tana ko'karin danne damuwar ta. "Bismilla zauna" ya faɗa yana nuna mata wani 6angare na lallausar grass carpet ɗinda yake zaune akai.
Zuba mishi ido tayi tana mishi kallon tuhuma, ganin duk yadda ta kai ga dannar fusatacciyar zuciyar ta Amar yana son yaga ya kular da ita. "inba haka ba Akan me zata ce tana son magana da shi sannan yace wai ta zauna a nan, yana nufin a gaban budurwar sa zasu yi maganar?" ta koma tambayar kanta. A fusace ta ɗago kai tareda zarewa bakinta sakatar da tasa masa tace...
*Yar'mutan Arkilla* ✍ [12/8/2017, 7:41 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *38* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
........... *JA'JIRTACCE*....... *25* 👇🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na* Nasmatu Muhammad *(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:* ---- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* ↓↓ *Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION* ---- *CHECK OUR BLOG'S* ↓↓ *Zamaniwriters.blogspot.com* ---- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* ↓↓ *Zamaniwritersassociation@gmail.com*