Kadangarun bariki part 1 complete novel - Chapter 4
Kadangarun bariki part 1 complete novel Chapter 4: Kadangarun bariki part 1 complete novel Chapter 4. Mamu wacce ke kishingiɗe ta amsa sallamar dakyat…
2,261 words
Mamu wacce ke kishingiɗe ta amsa sallamar dakyat saboda ciwon hauren da ta ke,cikin rumfar ya shiga ya gaisheta sannan ya ja kujera ya zauna.Jikinta ya fara tambaya ta amsa "da sauki Ibrahimu ya aiki?" "Alhamdullah"ya amsa a taƙaice ya na ɗan dube-dube ta inda zai ganin ta.
Kamar daga bisa sai ga ta,daga aiken da Mamu tayi mata.Tun daga ƙafafuwan ta uwanda suke sanye cikin takalmi silipas sun ƴar ƙura saboda tafiyar da tayi,har izuwa sama inda ta ke sanye da guntun hijabi iya ƙwabrin hannuwa.Kicin-kicin ya yi da fuska ya na jin kamar zai make ta dan takaici,yi tayi kamar ba ta gansa ba ta durƙusa gaban Mamu tace "ki tashi ki sha ga maganin"karɓa tayi ta na cewa "ba ki ga yayan ki ba?"turo baki tayi kafin ta waigo inda ya ke zaune mamakin yadda tayi banza da shi ya kama sa sosai.
"Ina wuni"ta faɗa can ƙasan maƙoshi,yi yayi kamar bai ji ba sai ma wayar shi da ya fara shafawa ya na murmurshi.
Wani haushi ya luluɓe Mimi haka ta ɗan ƙara ɗaga murya tace "Yaya Himu ina wuni?"wannan karon ɗagowa yayi ya kalleta jin sunan da tayi mashi,sai kuma ya basar ya taɓe baki gami da mayar da hankalin sa kan wayar sa.
"Mamu ina son ta raka ni Kalla Transa ne in kin yarje min"Ibrahim ya faɗa ya na kallon Mamu wacce zuwa yanzu tayi zaune ta na shan magani,kai ta gyaɗa tace "babu damuwa Allah maido ku lafiya"da "amen"ya amsa kafin yayi godiya ya miƙe.
"Tashi ki wanke jiki ki sauya kaya sai ku tafi"Mamu ta faɗa cikin bayar da umarni,Mimi na gunguni ta tashi ta shige ɗaki kayan jikin ta sauya kafin ta fito ba tare da ta wanke jikin ba ta fita fuuu cikin jin haushi.
Ganin bai bakin motar sa yasa ta wuce ciki,a falo ta tarar da shi su na waya da abokin sa sai dariya suke tuntsira su duka biyun.
Cike da gayya Ibrahim yace "gaskiya Waleed yarinyar nan ta ci uwar raina ka yanzu dagaske ƴar talakawan ce tace ta na son ka kuma ko 30years ba ta kai ba?"daga can ɗayan ɓangaren Waleed yace "Allah kuwa abokina in da ma ka gan ta duka-duka nawa ta ke ƙila ma har yanzu ta na fitsarin kwance"Ibrahim yayi dariya yace "Allah sa dai ba ƙazama ba ce ta iya tsarki kar a zo yadda ta ke barin jikinta da dauɗa haka ma can"
"Aboki sai an jima Jumelle ta fara naƙuda gadan-gadan"cewar Waleed ya na mai kashe kiran.
Inda ta ke a tsaye ta na zubar da hawaye ya kalla kafin yace "ya dai lafiya?"jin tambayar ya sa Mimi sake rushewa da kuka,ido ya lumshe ya na jin zuciyar sa na ɗan dokawa da ƙarfi-ƙarfi.....
Yanzu wasar za ta soma ƴar uwa ki mallaki na ki🤪🤪🤪🤪
[06/05 à 10:58] MRS SADAUKI 💫: *ƘADANGARUN BARIKI*💅🏻💅🏻💅🏻
MRS SADAUKI 💫
*Daga wannan page ɗin babu page ɗin zan ƙara fitarwar in shaa Allah 200 ki biya ki karanta hankali kwance duk wacce take buƙata ta yi min magana ta WhatsApp* +22795045822 ,*wacce tayi payement ta ga ban sa ta paid group ba ta min tuni*🥰
19_20
Sam ba ta san da zuwan shi ba sai ji tayi ya rungumota,da sauri ta buɗe ido cike masifa ta ture sa sai dai ko gizau bai yi ba.
Murmurshi ya sake yi kafin yace "Mimina minene?ba ki sona kin tsane ni ko?"baki ta cinno Ibrahim ya sake yin murmushi mai sauti ya cigaba da cewa "ƴar ƙwaila da ke amman kin hana tunanina shaƙat tun ranar da na fara ɗora idona kan ki"ya tsaya da maganar da ya ke ya saki huci ganin ta ƙuresa da ido ta na kallonsa cike da mamaki.
Ƙugunta ya sake riƙewa da kyau hakan ya ƙara kusancin su,murya na ɗan rawa yace "ki yarda da ni,zan mayar da duniyar ki abun kwatance abu biyu kawai na ke so kiyi min,na farko ki tsare min mutumcin ki kar ki bari wani ya illata rayuwar ki ko ta halin ƙaƙa ne ki nuna jajircewa akan tarbiyyar da iyayen ki suka yi maki wajen tseratar da kan ki da darajar ki"ido Mimi ta lumshe a take abun da Daddy yayi mata ya faɗo mata a rai tabbas a ɗan zaman da tayi ta gane Alhaji mutumen banza ne sannan ta lura Ibrahim ya lura da haka shiyasa ya ke mata huɗuba.
Da sauri ta buɗe lumsashun idon ta jin ya cigaba da cewa "abu na biyu shine ki koyi sona ko yaya ne please,rayuwa mai cike da farin ciki da shauƙin soyayya na ke fatan mu yi"jikinta ne duk yayi sanyi,so take ta janye daga gare sa amman sam Ibrahim ya ƙi bata damar yin haka.
Hannu ta ɗora kan ƙirjinsa da zumar ja da baya, sai dai hakan da tayi sai ya ƙara kusancin su ma ta yadda Ibrahim ya ƙara janta jikinsa ya matse.
"Ka sake ni babu kyau fah"ta faɗa kamar za tayi kuka,cikin muryar shi wacce ta fara dishashewa yace "na sani kawai ina ra'ayin hakan ne,am... ni ma ban san mi ke damuna ba kawai kasantuwar mu a haka na ke jin zuciyata na muradi.Ki yarda da ni, Ibrahim ba zai taɓa cutar da ke ba,soyayyar ki da sha'awar ki sun riga sun cika zuciyar sa sannan tausayin ki ba zai bari su rinjaye sa ba har su kai da cutar da ke"
Mimi dai sauraren sa kawai ta ke dan Allah na gani duk a takure ta ke,ga wani irin yanayi da ta ke kamar wacce aka zuba ma ruwan sanyi ƙasanta kuwa har wani abu ta ke ji kamar ya na tafiya yayinda lokaci zuwa lokaci ta kan jin ni'imar ta na zuba kan pant ɗinta wanda kusan dama can ko abu da ya shafi harakar aure ta ji sai ta kwana da ciwon mara .
Ajiyar zuciya ya shiga saukewa a sannu kuma ya fara jin nutsuwarsa na dawowa gare sa,sakin ta yayi sannan yayi baya ya zauna kan kujera.
"Ki shiga toilet ki wanke jikin ki sai ki isko ni mota ina jiran ki"ya faɗa murya a sanyaye,a kunyace Mimi ta nufi toilet ɗin da ke falo ko da ta fito ba ta tarar da shi ba.
Tun da ta fito ya buɗe mata seat ɗin gaba,shiga tayi ta sunne kai shi kuwa yayi ma mota key baba mai gadi wanda ya ke mahaifi ga Halimatu ya buɗe mashi get.
Direct Kalla Transa Mall suka nufa,sayayya yayi sosai kama daga dogayen riguna,riga da sket da kuma bra da pant.
Ita dai Mimi na gefe cike da kunya yadda ya ke wani taɓa bra da pant ya na jinjina su kafin kuma ya juyo ya dube ta dan tantance ko za su yi mata.
Kayan maƙulashe ya saya leda biyu bayan sun gama sayayyar kafin su wuce gida,har ɓangaren su ya rakata yayi ma Mamu godiya kafin ya ƙara da cewa "dan Allah ki rinƙa yi mata faɗa ta bar saka kayan Fulanin nan,ga kaya nan na sawo mata wai ba ta so"yayi maganar ya na hararen Mimi wacce ke kallonsa sake da baki ta na tambayar kanta ko yaushe tace masa ba ta so?Turo baki tayi ta harare sa ai kuwa Mamu ta shiga yi mata faɗa.
A fakaice yayi mata gwalo kafin ya kuma cewa "ga hijabai nan wanda za ta rinƙa sawa in za ta fara aikin gida"ya faɗa ya na fiddo wasu hijabai dogaye kamar wata matar Liman.
Godiya Mamu ta shiga yi masa kafin shi kuma yayi masu sallama ya wuce part ɗin sa.
A can ɓangaren Alhaji kuwa sai da mai gadi ya kira Dr shi ya zo yayi masa allurai haɗi da sa masa magani.
Mai gadi ya dawo inda ya rufe Ameera,ya na shigowa ta tsaya da kukan da take ta na duban sa.Baki ya washe yace "ki bani na baki ƴan mata,in kin yarda ki bani haɗin kai nima na ɗanɗana zumar sai na bar ki kije gida"ɗagowa Ameera tayi ta na kallon tsohon wanda a ƙalla zai girme ma Alhaji,wani abu ta haɗiye muƙut mai ciwo kafin ta gyaɗa kai alamun ta yarda.
Tsohon najadu haka yayi amfani da Ameera har sau biyu kafin ya buɗe mata get ta fita.
Lokacin da ta isa gida ɗan ƙaramin hauka Umma ta ɗora lokacin da ta tabbatar da an yi ta amfani da Ƴar ta,cikin kuka Ameera ta fara bayani "Allah Umma ba su da tausayi haka suke kawo yaran mutane su na ɓatawa,nima Mai gadin gidan ne ya taimake ni ya kawo ni cikin garin"Umma ba ta ce komi ba sai kukan da ta cigaba da rerawa ƴaƴan ta na taya ta.
Bayan sallar Isha'i Baba ya dawo,da Umma ta sanar da shi maimakon ya ji haushi sai cikin Ameera da yayi ya shiga dukan ta "ƙarya kike munafukar banza yawon iskanci kika tafi ke ga karuwa shine da Alhaji ya baki kuɗi ki kawo min sai kika zaɓi zuwa Bariki to Allah ya isa ban yafe maki ba"ya na zaginta ya na dukanta da halbi.
Sai da Umma ta ga zai hallaka mata ƴa sannan ta jaye ta,tace "haba Malam ta yaya za ka rinƙa jifar ƴar cikin ka da mugayen lafuza?"cike da bala'i Baba yace "ƙarya ce nayi ba karuwa ce ba?"cikin jin haushi Umma ta maida martani tace "in karuwa ce mi zai sa ta dawo gida ?"
Baba ya nufi ƙofar fita yace "so ta ke ta zama KARUWAR GIDA ta yadda babu wanda zai tuhumeta a kan karuwancin sai dai ba'a gida na ba ta je can ta ƙarata a duniyar *ƘADANGARUN BARIKI*"
Washegari
Wanka ta kuma yi sannan tayi tsarki da ruwan bagaruwa wanda Umma tace in ta na yin haka kullum tsaf za ta liƙe ta tsuke,ta na cikin banɗaki ta ke jiyo zage-zagen da Baba ke yi ya na aibanta ta.
"Za ki fito ko sai na shigo banɗakin na ci burar ubanki?"ta ji Baba na faɗa ya na jijiga ƙyauren banɗakin kamar zai cire sa,jiki na kyarma ta jawo zane tayi ɗaurin ƙirji sannan ta buɗe ƙyauren.
Naushi ya kai mata a kumci ya na zaginta,Ameera ta fashe da kuka ta nufi ɗaki.
★★★ NIAMEY
Waleed ya karɓi haihuwar Waleedat inda ta haifo kyawawan ƴaƴanta maza masu kama da uban su,tun da aka yi haihuwar Waleed ya kasa tsaye ya kasa zaune kullum cikin zarya ya ke wannan yasa ya mance shaf da batun zuwa dubo Mai Gadi sai yau da ya tuna.
Cikin baƙin rai ya nufi Pays-Bas sai wani gangame fuska ya ke,ya zo daidai inda ya ke parking su Lamira suka fito daga cikin gidan su.
Murmurshi tayi ta na ce ma su Fa'iza "irin waccan motar zan saya in nayi kuɗi"ta faɗa ta na nuni da yatsanta daidai ne Waleed ya fito.
Wani irin ƙuri Lamira ta yi masa ta na jin wani irin sonsa ya shigeta lokaci ɗaya,ba tayi ƙasa da gwiwa ba ta taka gun sa.
"Mai kyawu mi ya kawo quartier ɗin mu?"ta tambaya lokacin da ta zo gat da Waleed wanda ke ƙoƙarin rufe mota,juyowa yayi ya na ƙare ma kyakkyawar fuskarta kallo ganin haka ya sa Lamira sakin murmushi cike da duniyancin da Bibalo ke koya mata tace "gaskiya ba ka kyauta ma kan ka ba da har ka shigo wannan unguwa mai datti haka,am nace amman kai baƙo ne ko?"samun kansa yayi da gyaɗa mata kai ya na mai cigaba da sake kallonta.
Lamira tayi murmurshi tace "ayya shine ka rasa inda za ka sauka sai Pays-Bas unguwar da babu komi sai ƙazanta da sabro?"tayi maganar ta na taɓe baki kafin daga bisani ta ɗauko ƙullin gyaɗa biyu ta miƙa masa.
Karɓa yayi ɗago kansa da zai yi suka haɗa ido da Nabeela wacce ta dawo daga makaranta,juyawa Lamira tayi ganin ya kafe waje guda da ido.Wata muguwar harara ta watsa ma Nabeela kafin tace "ka bar kallonta kar ta ɓata ka duk ƴan ɗakinsu mugun hali ne da su kamar uwar su,am nace mai kyau miye sunan ka?"murmurshin gefen baki yayi yace "ki canka da kan ki"ya na gama faɗa yayi gaba ya na mai zuba gyadar cikin aljihu.
Da sauri Nabeela ta shige gida ta na sharar hawaye kafin kuma ta fito waje inda tun tuni su Lamira sun yi wucewar su.
Marfin motar Waleed ta kama cikin mamakin ta sai kuwa ta ji ta a buɗe,gidan baya ta buda ta shige sai magana ta ke ita ɗaya.
Ta na tsinkayan Waleed tayi sauri ta kwanta ruf ta yadda ba zai ganin ta ba,Waleed kuwa da ya zo sai da ya dubi gidan su Nabeela kafin ya shiga motar shi.
Ƙyaci yayi bayan ya yi ma motar key a fili ya furta "sai na sa ƴar fillo(cewa da Lamira) ta ɗauko min ke ta kawo min ke cikin dubara ba dai kin ce sona kike ba to za ko ki gani yadda zan mayar da ke abar kwatance in rinƙa gana maki azabar da ba ki taɓa sanin akwai kalar ta a duniya ba" gaban Nabeela ne ya faɗi jin abinda Waleed ɗin ke cewa,ta kawo kanta da kanta ga ajalin ta ba ta san lokacin da wani tari ya zo mata ba.Da sauri Waleed ya taka burki ya na mai waiwayo suka haɗa ido biyu da Nabeela wacce tsantsar tsoro ya bayyana ƙarara kan fuskar ta......
*Nan zan tsaya da book one masu son cigaba za ku biya 200₦ ta account ɗin da na bada a waccan page ɗin,ƴan Niger kuma carte airtel ta 300f sai ku turo shaidar biya ta WhatsApp* +22795045822
In an yi payement zan cigaba in shaa Allah