Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 1

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 1

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 1: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 1. [08/08, 11:54 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

4,456 words

[08/08, 11:54 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA DAYA

Ina cikin duhu. Ba haske, ba sauti, sai ƙarar numfashi na da yafi kama da kuka. Sai wani zafi da ke ratsani daga ƙafata har zuciyata. Idanuwana sun kasa buɗewa gaba ɗaya, zuciyata na bugu kamar ana dukan ganga a kunne na. Amma inajin motsin rayuwa, kuma inajin ciwo... mai muni.

Cikin tsananin ƙara, jijjiga da motsi, na buɗe idona. Komai a kusa da ni ya kasance duhu ne, cike da ƙura da warin jini da hayaƙin injin. Idanuna suka ci karo da motar da ta ragargaje ta murɗe gaba da baya, ta lanƙwashe kamar takarda. Gaba ɗaya mutane cikin motar ba wanda ya motsa.Sai ni kaɗai. Sai ni kaɗai ce nake numfashi. A jiki na, jini yana kwaranya. Amma ba haka ya fi bani tsoro ba. Kwalban gilashi da ya shiga cikin kafata ne ya fi mini zafi. Cikin sautin azaba nake fadin “Wayyo Allah na… Bashari!!!” Sai na jiyo muryar wani mutum daga gefe, yana tawowa cikin ƙoƙari da jin tsoro. “Subhanallah! Ga wata tana numfashi! Don Allah ki daure... ki daure.” Ya matsa kusa da ni. Da alama ba daga cikin fasinjojin motar ba ne mai tuka mashin ne da ya tsaya a gefe lokacin da hatsarin ya faru. Ya fashe da kuka yana fadin “An kife motar gaba ɗaya. Ba wanda ya motsa sai ke. Ya Allah… wayyo wannan ƙaddara!” Na shure, na rarrafa ina kuka kamar sabuwar haihuwa, ina nuna masa kafata “Don Allah ciremin… Don Allah ciremin kwalban nan… Bashari fa?! Ina Bashari?! Ya shiga ina?!” Mutumin ya karasa da gudu, yana riƙe da wata bakar jakarsa, ya ce “Na kira asibiti, amma sun ce babu space, kuma ba ambulance. Ki daure, sai mu tafi babban asibitin birni. Ina da mota. Ba zan bar ki nan ba.” Na fashe da kuka cikin murya mai cike da raɗaɗi “Ka taimake ni, don Allah. Ka duba… Ka bincika Bashari…!” Mutumin ya juya ya duba ragowar mutanen motar. Ya ce “Na shiga motar nan. Gaba ɗaya sun mutu. Kinsan me ke nuni da rai? Kai kaɗai ke motsi, kuma ke kaɗai nake jiyo ihu daga nesa.” Sai na fashe da wani sabon kuka, zuciyata kamar ta fasa ƙirji. Idanuna na nemansa Bashari, amma babu shi. Babu kansa. Babu kalamansa. Babu dariyarsa da zai ce "ƴar kwalisa, ke kika shafamin farin, kinji." Mutumin, ya ɗauke ni daga ƙasa kamar jaririya. Gilashin da ke cikin kafata yana barin jini, amma ina jin ƙarfin hannunsa kamar uba. Sai ya saka ni a cikin motarsa. Ya ce“Ki daure. Inkai ki babban asibitin birni. Wannan kafar taki da wuya idan nasai an mata aiki ba kwalabe sun shiga ciki ki daure kiyi hakuri kinji.” Na lumshe idona cikin ciwo, numfashina yana tafiya sannu a hankali. Na ce cikin kuka mai zurfi “Bashari... ba za ka tafi ka barni ba, ko? Ka ce ba ka so mu rabu… don Allah... Ka ce mu za mu yi rayuwa tare…” Mutumin ya shiga mota da hanzari, ya tada injin, sannan ya bar wurin cikin gaggawa. Jini na zuba daga kafata. Hawaye na kwaranya. Amma zuciyata ta mutu fiye da kafata.

Ina kwance ne a kan kujerar bakin asibitin garin. Ba ruwan jikina da motsi. Daga ƙafa har kai babu wani sashi da ke iya amsa sakon da kwakwalwata ke aikawa. Sai dai ina raye. A’a… Ina numfashi numfashin da ke fita da wuya kamar wanda aka jingine tsakaninsa da mutuwa.

Zafi nake ji a kafata. Kamar ana hura wuta a cikin jinina. Idanuwana sun lumshe amma hawaye ke zuba kamar ruwan famfo. Cikin ƙasan zuciyata, ina ta faɗin sunan da ya kasa fita daga zuciyata

“Bashari… Kai kada ka mutu… Kai kada ka barni… Don Allah… Bashari ka tashi…”

Wani dattijo ne ya tsaya a kaina. Shi ne wanda ya cece ni daga ragargazawar motar da ta lashe rayuka. Har yanzu yana tsaye, yana magana da nurse da likitoci da suka fito daga ginin asibitin.

"Don Allah ku taimaka! Kalli yadda kafarta ke zubar da jini! Ba ku ganin kwalban da ya shiga ƙafarta?! Motarsu ta yi hatsari ne daga can wajen gari. Mutane da dama sun rasu! Ita ce kawai da rai a cikin su!"

Sai nurse ɗin, wata mace mai fuskar sanyi amma zuciya mai duhu, ta ce da shi cikin rashin kulawa

"Baba mun ce ba za mu iya karɓar patient ba sai an kawo police report. Wannan doka ce. Muna buƙatar sahihin bayani daga ƴan sanda kafin mu yi admission!"

Na buɗe idona da ƙyar. Cikin hazo, na hangosu suna tsaye kamar duwatsu masu murya. Dattijon yana roƙo kamar wanda yake neman rai daga hannun makaho.

“Dan Allah! Mutum ce fa wannan! Shin kun yarda ku kalli mutum na mutuwa saboda babu takarda? Ina rahama? Ina tausayi?!”

Amma basu saurareshi ba. Babu motsi a fuskokinsu. Sun juya kamar babu abinda ya dame su.

Ni kuwa... ina jin numfashina na kara rauni. Jikina ya daina amsa. Kwalban da ke cikin ƙafata ya jike da jini, yana zubar da zafin da ba a iya misaltawa.

Sai kawai na saki kuka cikin wahala da azaba.

“Wayyo Allahna! Bashari! Kai ne kadai nake da kai! Kada ka mutu wallahi… Bashari! Ka tashi ka ce musu ni matarka ce!”

Kamar kowa a wurin ya tsinke kunnen sa daga ihuna. Sai wani ɗan juyi suka bani a kujerar da ke wajen ginin, suka ce da malam ɗin “Kaita wani asibiti. Ba za mu karɓa ba.”

Wani matsanancin kuka ya fito daga cikin zuciyata, yana neman karairaya makoshina. Na fashe da ihu ina ƙwala kiran sunan mijina

“Bashari! Ka dawo! Don Allah kada ka barni!”

Dattijon ya durƙusa ya duba kafata, yana girgiza kai da hawaye a idonsa. Amma yasan bazai iya tsayawa da karfi ba. Yace da nurses

“Kuji tausayin dan Adam. Bama tambayar magani yanzu. Ku taimaka ku cire mata wannan kwalban cikin ƙafarta kawai!”

Sai wani daga ciki yace

“Muna aikine, ba mu da hurumin karya doka. Ita kuma sai an samo police report!”

Cikin waɗannan kalmomi ne zuciyata ta fara bushewa da fatan taimako. Hannuna ya saki, hawaye na shudewa, numfashi ya soma tsayawa sannu a hankali.

Kafin na fitar da wata kalma ta ƙarshe, sai naji idanuwana sun soma yin duhu. Na soma jin kamar ni kaɗai nake cikin duniya, ba mai amsa kuka na. Na soma zamewa… hankali na ya daina iya tunanin komai.

Shiru… Sai duhu…

Ina kwance akan tile mai sanyi, cikin jini da gumi, na kasa ko motsi da kyau. Na kankame ƙafata da hannu ɗaya, duk da azabar da ke ratsa gangar jikina. Ina jin kwalban da ya huda mini ƙafa yana ci gaba da barin jini kamar famfo, amma hakan bai hana kaina ci gaba da ƙaƙƙame murya ba.

"Bashari... Kai kadai nake da kai... Ka dawo, don Allah kada ka barni... kafata... kafata tana huda min...!"

Na dinga rerawa kamar mai hauka. Na ci gaba da kuka, kuka mai zafi da na’amani, kamar wanda zuciyarta za ta fashe.

Wanda ya kawoni... ya riga ya kau. Na ji dai wani mutum yana fadin "To ni na kawo ta nan fa. Amma ba zan iya jira ba, idan kun gaji ku duba ta, ku duba. Idan ba haka ba, ni na tafi."

Wani nurse ya ce da shi da ƙarfin murya "To ai ka fiye magana. Idan ka kawo ta ba tare da police report ba, ai ba za mu karɓeta ba. Doka ce haka. Je ka samo police."

Na ji ƙafarsa yana nisa, sai shiru… yana barina a nan… a zube… kamar itace da aka jefa daga bene.

"Wayyo ni Ramlah... Wayyo kafata... Bashari ka dawo ka ce musu matarka ce ni... kada ka barni a haka!"

Duk da na san cewa kalmomina sun zube a kunne kurame, ban daina ambata sunansa ba. Cikin azaba da ciwo, cikin kukan da ya cika zuciyata, na dinga ja da ƙyar ina kai ihu. Nurse ɗin da ke tsaye gefe sai ta kwabe ni

"Ke! Me ke damunki ne haka da ihu kamar yarinya? Idan za a karɓeki to a kawo takarda daga police."

Na saki kuka sosai, ina jijjiga ƙafata, wanda hakan ya ƙara haddasa ciwo. Fuskata cike da zufa da hawaye, jikina yana rawa, zuciyata kamar ta fita daga kirjina.

Wani mara lafiya da ke gefe ya yi ƙoƙarin tashi, ya kalli nurse ɗin da ta ce haka, yace da ita "Ku duba wannan yarinyar danAllah. Ai wannan jini da ke fita daga ƙafarta sai ta mutu kafin ku gane!"

Wata mata mai ciki ta ce "Subhanallah! Ku taimaka, kallo ɗaya zai nuna cewa wannan yarinyar tana buƙatar agaji!"

Sai dai su ma’aikatan ko kallona batayi ba

"Doka ce, ba za mu iya duba ta ba. Idan wani abu ya faru fa? Ku da kuke cewar agaji, idan aka tambaye mu, wa zai tsaya mana wayasani ko yar kidnapping ce?"

Na ƙara fashewa da kuka. "Don Allah... kafata tana ciwo... Bashari ka dawo... Ka ce musu matarka ce ni... Wallahi zan mutu...! Ya Allah ka karɓi raina tunda babu mai tausayi..."

Na soma jijjiga jikina cikin tsoro da fargaba, zuciyata ta cika da raɗaɗi da tsananin wahala. Wasu daga cikin marasa lafiya sai da suka juya kai domin basu iya kallona ba.

"Ai wallahi wannan zalunci ne. Mutane sun manta da imani," wani dattijo ya fadi da mamaki da takaici.

A ƙarshe, wani cikin patients ya kalli nurse da ƙarfi ya ce "Idan wannan yarinyar ta mutu fa? Wannan jinin fa yana gangarowa, kuna kallo kuna dariya?!"

Sai kawai wata nurse ta daka masa tsawa "Kai da kake magana kamar kai ne shugaban asibiti! A doka fa muke! Ba a karɓar patient ba tare da police report ba."

Na ƙara miƙewa da ƙarfin da ban sani ba daga ina, na ɗaga hannuwa zuwa sama cikin kuka da raunana murya

"Ya Allah, idan mutane sun yi watsi da ni, ka karɓi raina cikin rahama. Ka kaini inda babu ciwo, babu tausayi, babu wulaƙanci..."

Ban san lokacin da na sume ba.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[10/08, 8:25 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA BIYU

Babban Cambo ne na motocin sarki suka shigo cikin harabar babban asibitin birni. Motoci masu alfarma, masu ƙayatarwa, masu tsada irin waɗanda ba kowa ke gani da idanu ba, balle har ya taɓa su. An jero su cikin tsari, kowane yana dauke da tambarin fadar mai martaba, kuma an lullube su da launin zinariya da baƙi, alamun iko da ƙima. Sai wani siririn hayaƙi mai ƙamshi ke tashi daga tayoyin motocin da suka ratsa cikin farin tiles ɗin harabar asibitin kamar taurari a cikin dare.

Wani daga cikin motocin gaba gaba limousine mai ƙafa takwas shine yake ɗauke da mai martaba. A cikin motar kuwa, an zauna kamar a cikin masarauta kujerune masu kyau da alfarma, silin da aka yi masa ado da furanni na murjani, Da wata ƙaramar fitila mai launin shudi tana walƙiya a saman dashboard. A can gefe As'ad ke zaune, yana sanye da shadda mai launin toka, hula doguwa da aka ɗinka da dinkin fadawa, da takalmi.

Kallo ɗaya zaka masa ka gane asalin jinin sarauta ne tsayayye, ba ya yawan motsi, Tunda suka shigo harabar asibitin, mutane ke tsayawa, suna kallon motocin da shauƙi da mamaki. Sai da suka tsaya a gaban babban ward ɗin emergency kafin ‘yan tsaron fadar suka fito suka bude kofar motar da take dauke da mai martaba.

“Gaisuwa gareka ya mai martaba! Sarkin mu! Ruwan zinari! Gwarzon sarauta!” suka rinka faɗa da ƙwazo.

Mai martaba ya sanya kafarsa a ƙasa. Kafin ƙafarsa ta taɓa tiles ɗin asibitin, wasu ma’aikatan tsaro sun riga sun baza kilishi mai tsabta wanda yake ɗauke da tambarin fadar su. Da zarar kafar As'ad ta sauka, sai ya ɗan runtse ido, kansa na sarawa kamar yana jin wani abu da ba shi da fassara.

Ya ɗan ciza labbansa da natsuwa, sannan ya cigaba da tafiya cikin kasaita, yana bin mahaifinsa da ya riga ya shige ciki.,yana tafiya da ƙarfi, kallo ɗaya zaka masa ka gane ba karamin tashin hankali ya shiga ba. Fuskar nan tasa mai cike da kwarjini ta sauya, tana ɗauke da bayyananniyar damuwa game da marasa lafiya da suke zaune a yashe a emergency din.

Yayin da suka shigo babban ward ɗin, jikin As'ad sai rawa yake kamar mara lafiya. Wani numfashi mai nauyi ya sauke, ya dubi mahaifinsa cikin ƙwalla tausayin irin mutanen da yagani duk yacika ransa. Mai martaba ya tsaya cak, ya juyo gare shi, ya dafa kafadarsa da karfi yana cewa

“Dole ne mu kasance masu haƙuri As'ad. Shiyasa ziyartar Asubuti yana karawa bawa imani zaiga Abubuwa Dayawa da Allah yabashi kyautarsu.”

Sai dai As’ad bai iya ce masa komai ba. Idanunsa sun cika da hawaye, numfashinsa yana k’aruwa. Ya k’ara takawa da ƙarfi, yana tafe da wata nutsuwa wacce ke ɗauke da radadi. Kamar ya fashe da kuka, amma girman sarauta ya hana shi.

Likitoci na babban asibitin suka fito cikin gaggawa da girmamawa, duk suna darje gwiwa cikin ladabi da tsoro. Ko wanne likita yana gaishe su da kyau yana sunkuyar da kai cikin nauyin alhaki da darajar manyan da suka iso. Wasu daga cikinsu har da farin hula, wasu kuma cikin fararen labcoat masu ɗauke da alamomin matsayinsu, sun tsaya cikin layi suna jiran umarni daga masu tsaron mai martaba kafin su matsa gaba.

As’ad ya tsaya gefe yana bin kowane motsi da idanu kamar na zaki mai nazarin farauta. Bai ce komai ba, amma kallo guda daga gare shi ya ishi mutum ya gane cewa ba shi cikin walwala. Mai martaba kuwa yana ɗan lumshe ido kamar wanda ke adana ƙwallar da ke dab da zubowa. Yana daure fuskarsa cikin yanayi na haƙuri da nauyin duniya, yana tafiya kamar wanda ke keta wani tsattsauran lokaci da ya shaƙe numfashinsa.

Da suka iso gaban ɗakin da aka ajiye wanda aka ce shi ne kanin mai martaba, wata babbar likita mai suna Dr. Nasreen ta fito tana tattare da takardu da kwayar nutsuwa a idonta. Sai ta sunkuya da girmamawa ta ce

"Mai martaba, muna taya ku jimamin haɗarin da ya faru. Muna godiya da kasancewarku da wuri. Yaron yana cikin kulawa ta musamman yanzu, amma halin da yake ciki…"

Ta dan tsaya, idonta ya haɗu da na As’ad wanda ganinsa na farko taji Inama ace mijinta ne ko saurayinta.

Mai martaba ya ɗan yi ajiyar zuciya, sannan ya ce da murya mai nutsuwa amma mai nauyi "Zamu iya shiga mu gan shi?"

Dr. Nasreen ta gyada kai cikin girmamawa. "Eh mai martaba. Amma... ku kasance cikin shiru domin halin da yake ciki ba ƙaramin abu bane."

Kafafunsu suka shiga motsi kamar ba da niyyar tafiya ba, amma ba su da zaɓi. As’ad ya tsaya kafin shiga, ya kalli mahaifinsa, sannan ya ce cikin wata murya da ke ɗauke da haɗaɗɗen tausayi da firgita “ Allah yakara maka lafiyar ina tunanin fitar dashi waje shine abunda yakamata.

Mai martaba bai ce komai ba. Ya bude kofar ɗakin, sai wani irin ƙamshi mai tsami ya daki hancinsu ƙamshin magunguna da jinin da aka kwana ana gogewa daga cikin numfashin marasa lafiya. A can cikin hasken ɗakin, aka hango gadon da Yusuf ke kwance kai bandage, jikin sa cike da tubo da allura. Fuskarsa tayi jajir, numfashinsa na tafiya da kyar. Mai martaba ya nufi gaban gadon, ya durƙusa da ƙyar, yana kallon fuskarsa kamar yana nazarin tarihin da bai fahimta ba.

"Yusuf.." ya furta cikin sanyi. "Na zo... Qllah ya kiyaye gaba yabada lafiyai."

As’ad ya tsaya a bayansa, hannunsa a aljihunsa, zuciyarsa na tafasa kamar ruwan da ya kaure. A karo na farko cikin dogon lokaci, ya kasa boye raunin zuciyarsa. Ya fuskanci cewa dangi, kudi, da matsayi ba sa hana bala’i. Ba sa hana mutuwa shigowa kai tsaye.

Wata kwalla ta zubo daga idon mai martaba. Sai ya mike, ya juya yana fadin

"Kira min babban likita. Kuma ku duba ko akwai bukatar a mayar da shi kasar waje nan take. Ko meye za a yi... A nema masa visa nan da 1days..."

Atake aka amsawa mai martaba, kamar yadda aka saba da martabar gidan sarauta. Fadawa biyu suka ruga a guje suka bude masa gaban emergency ward, tare da sara da girmamawa. Mai martaba yana sanye cikin riga mai launin zinariya da hula mai ado da zaruruwa. Kallon idonsa kadai ya isa ya haddasa tsoro a zuciyar marasa gaskiya, amma yau zuciyarsa cike take da tausayi da damuwa.

A bayansa ne Yarima As’ad ke takowa a natse kamar wanda ke biyayya ga uba, fuskarsa cike da tsanani da damuwa, zuciyarsa kuwa tana tafarfasa da ruɗani da bakin ciki. Kafarsa na dukan tiles ɗin asibitin a hankali, sai hayaniyar fadawa ke bin sawunsu da gaisuwa da kuma jagorancin su zuwa babban ward din gaggawa. Kowa yana basu hanya, masu lafiya da mara lafiya, ma’aikatan jinya da masu tsaro, kowa na girgiza kai cikin mamaki da girmamawa.

Da suka karasa harabar babban ward ɗin, sai suka tsaya cak ihu ne kawai ke tashi daga cikin ɗakin. Murya ce ta mace karama, amma mai raɗaɗi da ƙunci, tana kururuwar ciwo kamar wadda ake yanka da reza

“Wayyooo Bashari... zan mutu! Bashari, gwara na mutu! Wayyo Allah na... ku ciremin kafata ku ciremin in huta! Wayyo Allah... wayyo mijina...!”

Mai martaba ya tsaya cak, jikinsa yayi wani irin sanyi. Idonsa ya zuba a cikin ɗakin, amma zuciyarsa ta ɓaci, saboda ba a cikin kukan ba ne kawai, a’a, sai da jin haushin yadda aka bar yarinya tana ihu haka cikin wahala ba tare da taimako ba. Sai ya juya yana duban fadawa da likitocin da suka raka shi, ya ce da wata murya mai cike da iko da girmamawa

“Ya zaku bar yarinya cikin wannan halin? Ina likita mai kula da wannan sashen? Ina matakin gaggawa akan wannan?”

Nan da nan suka rikice! Likitoci suka ruga ciki da sauri, wasu suna ɗaukar wayarsu suna kiran karin ma’aikata, wasu kuma suna gaishe da mai martaba suna ba da hakuri. Yarima As’ad kuwa ya tsaya yana kallon yaddan halin da yarinyar ke ciki ya dame shi matuka. Fuskar yarinyar kamar ta rusa da kuka, jini ya wanke gefen kafarta, kwalba ce ta shiga kusa da kashin kafarta yana daddare. Ta gigice ta galabaita.

Ban san me ke faruwa ba. Ban gane waɗanda ke kaina ba. Amma naji kamar duniya ta narke. Ban gane shigarsu ba, ban san wanene mai martaba ba, amma naji wani na faɗin cikin girmamawa Cike da tausayi mai martaba yace ina iyayen yarinyar nan ina mijin nata da kuke magana akai? Nurse tayi saurin fadi. Hatsari sukayi wanda yakawota ya gudu ya zaku bar yarinya cikin wannan halin ai kuwa suka rikici gaba daya aka shiga daukar ramlah zuwa daƙin da za'a dubata

“Kidaina kuka, kinji. Zaki samu lafiya, zaki rayu… inshaa Allahu”

Na kama hannunsa cikin tsoro, kamar jaririya wacce ta rasa uwa. Amma kafin inyi magana wani daga cikin hadiman da ke tsaye kusa da shi ya kwace hannuna da karfi yana faɗin

“Ke yarinya, kula da taɓa ɗan sarki! Wannan cikakken Yarima ne, ragowar kasar nan. Ki rike nutsuwarki.”

Na fashe da kuka mai ƙarfi, na dinga kiran Bashari da karfi, “Wayyo mijina! Bashari ka zo! Ka taimaka min…!”

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[11/08, 2:24 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA UKU

Mai martaba ya juyo da sauri cikin damuwa ya ce, “Ku ɗauketa! Ku kai ta dakin kulawa ta musamman. Ku sanar da Dr. Hamid ya taho yanzu! Duk abinda ake bukata, ku dora a kan file dina. Wannan yarinyar za a kula da ita kamar ‘yata ce.”

Wani dagawa hannu da yayi ya sa duka fadawa suka shiga motsi, kamar wani yaki ne aka bada umarni. Likitoci biyu da nurses suka ɗaukeni a hankali cikin girmamawa da tausayi. Fuskokin su na nuna damuwa. Mai martaba ya kalli hannunsa inda na daƙumo shi da tsoro, ya ga inda na bar alamar jijiyata a jikinsa. Ya lumshe ido yana girgiza kansa cikin tausayi, sannan ya juya yana kallo likitocin da ke fita da ni daga cikin emergency ward din.

As’ad kuwa ya biyo su da kallo har suka bace. Sai ya tsaya yana kallon mahaifinsa, zuciyarsa cike da raɗaɗi da wani abu da ba zai iya fassara ba.

As’ad ya ɗan sosa kansa. Ya kasa cewa komai. Sai da suka fita daga emergency ɗin suka dawo wajen motocinsu da sauran fadawa, ana cigaba da juyawa da bada umarni domin a tabbatar da Ramlah ta samu kulawar da ta dace.

Kamar haka rayuwata ta sake juyawa... a gaban manyan mutane, a gaban sarki da yarimansa. Maganar masu matsayi ba kala daya bace data talakawa domin naga ƙarfin iko sosai..

Wani zazzafan ajiyar zuciya As'ad ya sauke, Yarinya ƙarama haka me ya kai ta ga auren da ya jefar da ita cikin wannan halin? Sai wani mugun sarawa ya ratsa kansa, yana dafe goshinsa da hannayensa biyu, yana ambaton sunan Allah cikin kaɗuwa. Idanunsa suka lumshe, amma sautinta ihun azaba da kiraye-kirayen da take yi suna ci gaba da dukan kunnensa..

Da zarar aka tura gadon da Ramlah ke kai zuwa cikin babban dakin gaggawa (ER Ward A1), kukan siririnta da ajiyarta mai sarkakiya ya cika sararin asibitin. Kamar mai neman taimako daga sama, tana kara ihu tana kiran

"Wayyoo kafata! Wayyo Allah na, ku ciremin wannan kwalbar... wayyo mijina... Bashari!"

An hanzarta sanya gadon Emergency stretcher akan babban teburi mai duhu da gilashi. An kewaye ta da manyan likitoci guda uku tare da nurses biyu da suka shigo cikin kalar uniform ja da fari. A jikin rigar Dr. Na’ima Musa akwai “Consultant Trauma Surgeon,” sannan Dr. Abdulmu’az Muhammad kuma yana riƙe da “Ortho Specialist.” Har ila yau, wani babban likita Dr. Joseph Adewale wanda shine Chief Medical Director a asibitin ya shigo da kansa domin tabbatar da an ceto lafiyar Ramlah kamar yadda aka umarcesu daga ofishin sarki.

“Vitals please!” cewar Nurse Hafsah tana duba numfashinta da Pulse oximeter. “BP 82/50. Pulse 122bpm. Respiration 26. Saturation 91%. She's going into shock!”

"Get me 1L of normal saline, warm, and hang it now!" Dr. Na’ima ta umarta cikin sauri.

Nurse Farida ta riga ta shinfida cannula #18G a hannun hagu. Har cikin mintuna biyu an fara zuba ruwan jiki cikin sauri. Kallon jikin Ramlah da kwalbar gilashi da ta faɗa gefen kafarta yana sake kara tayar da hankali.

“Dr. Abdulmu’az, we may need imaging, but there’s no time. There’s active bleeding. The glass is embedded deep in her medial malleolus. We must remove it now before sepsis or nerve damage!” cewar Dr. Na’ima.

“Let’s sedate her slightly first. She’s still screaming in pain,” ya ce yana duba allurar Midazolam da Nurse Farida ta riga ta kawo. An haɗa da Fentanyl domin rage mata zafi kafin fara aikin.

A take aka fesa Lidocaine Spray akan yankin kafar domin rage jin zafi a waje. Sannan aka sanya suturar sterile a duk inda gilashin ya shiga. Aka buɗe kayan aiki masu tsabta scalpel, forceps, artery clamp, gauze pads, iodine swabs, da suction machine aka shirya da kyau.

Dr. Joseph Adewale ya matsa kusa da gadon, yana kallon yadda duk ke tafiya.

“Ina son sauri amma da tsari. Kar ku bar ciwon ya baza,” ya faɗa cikin murya mai nutsuwa da karfi.

Sai aka fara aikin cire kwalbar.

Dr. Na’ima tana tafiya a hankali tana amfani da scalpel wajen buɗe wajen da kwalbar ta lullube. Ta ce, “Apply suction... gently now.” Nurse Hafsah ta taimaka da suction domin zubar da jini.

“Clamp the bleeder!” Dr. Abdulmu’az ya ce yana nuna wata tashar jini. An kamo da artery clamp sannan aka saka gauze pads da sauri.

“Wannan glass din ya karya a ciki,” cewar Dr. Na’ima. “We need the magnetic tip forceps.” Aka kawo, sai ta lallaba tana cire kashi-kashin da ke ciki.

Ramlah na karkarwa duk da sedation, zuciyarta na bugawa da karfi.

“Is she stable?” Dr. Joseph ya tambaya.

“Yes sir. BP rising to 90/60. Pulse dropping to 110,” Nurse Farida ta amsa.

“Good. We’re almost done.”

Kusan mintuna ashirin suka ɗauka kafin a kammala cire kwalbar gaba ɗaya, sannan aka wanke gurin da sterile saline, aka saka dressing mai kariya. Aka rubuta mata antibiotics da painkillers.

Bayan komai ya lafa, Dr. Na’ima ta ce

“Prepare her for X-ray. We need to confirm there’s no residual fragments.”

Nurse Hafsah ta gyada kai sannan suka fitar da Ramlah zuwa bangaren radiology.

Manyan yaran fada suna tsaye baƙin kofa suna ganin duk abunda akeyi domin umarnine daga sarki..

Asibitin ya dauki shiru yayin da aka ci gaba da bawa Ramlah kulawa, gado na musamman aka tanada mata.

Bayan an shigar da Ramlah cikin dakin X-ray, likitoci suka tabbatar da cewa akwai wani babban kwalban gilashi da ya shiga tsakiyar kasan kafarta har yana harbawa zuwa kashin sarkar ƙafarta. Wannan bayanin ya firgita ƙwararrun da ke aikin kula da'ita, kasancewar yana buƙatar aikin gaggawa tare da kulawa ta musamman.

Dr. Saleem Muhammad, ƙwararren likita a fannin orthopedic, shine ya karɓi alhakin jagorancin aikin. Yana tare da Dr. Halima Yusuf (anesthesiologist), da Dr. Khalid Bello (surgeon assistant), da nurse Maryam Bello wadda ke da kwarewa wajen kula da marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta musamman.

Dr. Saleem ya kalli hoton X-ray din, ya sake zurfafa gani cikin tsanaki sannan yace, “Nan take za mu shiga theatre. Kwalban ya shiga kusan rabin zurfin kashin kafarta. Dole mu cire shi cikin kulawa domin kada ya karye a ciki.”

An fara da shigar da ita cikin sterilized surgical ward, inda suka tanadi komai. An fara da tsaftace kafarta da sterilized iodine, sannan aka ɗaura drape mai tsafta. Nurse Maryam ta tabbatar da dukkan kayayyaki na aiki suna shirye scalpel, forceps, surgical scissors, retractor, da syringe masu magani

Dr. Halima ta gabatar da anesthesia cikin IV, har Ramlah ta fara jin sanyi yana ratsa jikinta. Ta rufe idonta a hankali, numfashinta yana sauka daidai. Sai aka shigar da oxygen cannula domin kula da numfashinta.

Dr. Saleem ya fara da buɗe gefen da aka hango kwalban a cikin X-ray. A hankali, da kulawa, ya kama gefen da gilashin ya keta fata. Gilashin yana kusa da nerve ɗin kafarta, don haka sai Dr. Khalid ya taimaka wajen jan gefe da retractor. A hankali Dr. Saleem ya fara jan kwalban da forceps, yana dubawa ko akwai sauran tarkace.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull