Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 2

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 2

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 2: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 2. Kamar wasa, gilashin ya fara motsi. Sai ga kwalban ya fito da duka ba…

4,491 words

Kamar wasa, gilashin ya fara motsi. Sai ga kwalban ya fito da duka ba tare da ya karye ba. Sai suka sauke ajiyar zuciya gaba ɗaya. Nurse Maryam ta sa turaren disinfectant, suka fara sutura da surgical suture, sannan aka daura bandage da rigar gyaran kafa.

Dr. Saleem ya ɗan juyawa manyan fada wanda ke tsaye daga nesa da gilashi yana kallo. Ya ɗaga hannunsa alamar komai ya tafi lafiya.

Ramlah har yanzu ba ta farka ba. Amma sun fitar da kwalban, sun gyara kashin, kuma sun tanadi duk wani magani da zai hana kamuwa da cuta.

Dr. Halima ta ɗora mata IV fluid da antibiotics. Likitoci suka fice daga dakin da nutsuwa, har sun bada tabbacin komai zai tafi lafiya.

Wannan aiki ya dauki kusan awa guda da rabi.

Bayan wani dogon barci da ban san yaushe ya daukeni ba, na farka da kyar. Idanuwana suka buɗe da nauyi kamar an auna su da baƙin dutse. Sai dai ba na cikin rami ko cikin gari ba dakin asibiti ne, shiru kamar makabarta, sai sanyi da ƙamshin disinfectant ke yawo.

Nayi ƙoƙarin motsa ƙafata... sai azaba ta ratsa jiki na, na sake lumshe idanu ina mai rintse gumi. A lokacin naji motsin wata mace kusa da gadona, tana fadin, “Alhamdulillah kin farka. Ki kwantar da hankalinki, An gama aikin lafiya. An cire kwalbar da ta tsaya a kashinki.

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[12/08, 7:11 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HUDU

Na buɗe idanu a hankali. Likita ce kyakkyawa, tsaftatacciya, fuska cike da tausayi. Sunanta Dr. Maryam Khalid. Sai ta ɗan dafa hannuna da kulawa, ta ce, “Na kawo miki abinci daga gidan mai martaba. Gashi nan. Ki ci ko kaɗan don lafiyar jikinki.”

Na kai ido a abincin da aka kawo shinkafa ce miyan farfesun kaza, da dafaffiyar dankali. Amma zuciyata bata son cin komai. Cikin muryar da ke ɓoye kuka na tambaye ta, “Likita... ina Bashari?”

Ta kalle ni da mamaki, kamar bata san sunan ba. “Bashari?” ta maimaita kamar tana nazari. “Ni ban san wani Bashari ba, gaskiya. Wanene?”

Sai hawaye suka gangaro a fuska ta, na ce da ita cikin ƙunci, “Mijina ne... shine muka taho tare... shine... shine suka ce...”

Ban iya ƙarewa ba, kuka ya mamaye ni. Na lulluɓe kaina da bargo na. Likita Maryam ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta zauna a gefen gadona.

Ta ce, “ki saurare ni. Kin tsira daga wani babban hatsari da mutane da dama basu rayu ba. Wannan ba ƙaramin alheri bane daga Allah. Kin tashi lafiya bayan babban aiki da muka yi domin cire kwalbar da ta shiga cikin kashinki.”

Ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba, “Yanzu aikin da ya rage a gabanmu shine ki karɓi kaddara ki yarda da cewa Allah yana tare da mai haƙuri. Ki ƙara ƙarfin zuciya. Duniya cike take da jarabawa, amma fa Allah baya barin bawansa har abada cikin wahala.”

Na share hawayena da bayan hannuna na dan sha ruwa. Duk da ba na jin daɗi, sai kalamanta suka kara sanyayamun rai.

“Ki ci wannan abincin, na tabbata zai taimaka miki,” ta ƙara nanatawa, tana kallona da tausayi. Kuka kawai na fashe dashi nakasa cin abincin tanata lallashina cike da tausayi sai kuma bacci yaƙara kwasheni saboda Allurar Da akayimun..

Cikin rauni da rawar murya na dago idanuna, har yanzu hawaye na gangarowa kamar famfo da aka bude. Na kalli likitar nan mai tausayi wadda ta tsaya kusa dani kamar uwa ga ɗiyarta. Ta ce da ita, “Don Allah… bani lambar iyayena. in kirasu, ko ki bani wayarki in kira su.”

Ta gyara zaman rigarta, sannan ta durƙusa kusa da gadon da nake kwance, ta kamo hannuna da wata irin kulawa da ta karya min zuciya. “Yaya sunanki?” ta tambaye ni cikin kulawa.

Na ce mata da hawaye, “Ramlah…”

Ta numfasa tana dafe kirjinta. “To Ramlah, ki bani lambar iyayenki, kinji ko ta wani ɗan uwan naki kuma agarin nan kike daga ina kuka tawo?”

Na lumshe idanu cikin zafi, na ɗauki lokaci ina tunani kamar raina zai fita saboda ta tunomun da bashari kalmar sa ta ƴar kwalisa da yake gayamun. Nace Mata “Nakasa tuna lambar kowa… kai na zafi… zuciyata na wani irin yanka… Doctor… Allah ya ɗauke min mamata yanzu kuma ya ɗauke Bashari Abbana baya sona bashari yana kaunata yana sona Doctor mumy batasona yanzu wanene zai soni doctor?…” Sai na fashe da kuka mai tsuma zuciya, na shiga fizge-fizge ina ƙara cewa, “Me yasa ni mutuwar bata kasheni ba ?! Me yasa Na rayu? Dama na mutu nima?

Doctor ta zaro idanu cikin tashin hankali, ta kamo hannuna tana shafawa cikin kulawa tana cewa, “A’uzubillahi Ramlah. Babu kyau irin wannan maganar. Allah baya azabtar da bawanSa fiye da ƙarfinSa. Ki yi haƙuri.”

Na ce mata cikin murya mai rauni, “Doctor… idan ba zai barni da mahaifiyata ba… idan ba zai barni da Bashari ba… toh me nake yi a duniya? Wannan duniya ai ba tawa bace… na gaji da numfashi!”

Doctor Maryam ta share hawaye daga fuskar ta, sannan ta ce, “Ke karamar yarinya ce mai dauriya. Kin tsira daga hatsari da babu wanda ya rayu a cikinsa sai ke. Wannan ba ƙarya ba ce alama ce cewa Allah yana tare dake kuma yana kaunarki fiye da dukkan wanda kike ambata. Ki daure. Ki karɓi wannan jarabawa da zuciya mai imani.”

Na kalleta, zuciyata cike da raɗaɗi. “Kina jin zuciyata kamar ana nika ta da dutse? Kina jin yadda jikina ke rawa? Kin san yadda kafata ke min ciwo kamar za ta cire kanta daga jikina? Kin san… Bashari ya tafi…”

Ta girgiza kai tana murmushin tausayi. “Bazan ce na fahimta sosai ba, amma ina tare da ke. Kuma Allah yana tare da ke. Ki karɓi abincin nan, kin ji. Ki ci ko ɗan kadan. Sai ki sha magani, domin kafarki na bukatar kariya sosai.”

Na ce mata, “Bazanci ba har sai kin fada min ina Bashari. Da gaske ya mutu? Da gaske ya barni?”

Ta zauna a gefen gadon, ta kamo hannuna da duka hannayenta. “Wallahi ban san shi ba. Ban san ko wanene ba. Amma naji ana cewa ke kadai kika tsira daga cikin motar. Ki yarda da kaddara, ki cigaba da rayuwa domin rayuwar nan wata rana zata saka ki murmushi.”

Na fashe da kuka sosai, ina kiran sunan Bashari. Sai Doctor Maryam ta rungume ni kamar uwa, tana jera min kalmomi masu daɗi da lallashi.

Bayan sati guda da na kwana a babban asibitin birni, na fara samun sauƙi sannu a hankali. Duk da cewa har yanzu jikina ba wani ƙarfi yake da shi ba, amma numfashi ya dan saki. Doctor maryam tasiyomun kaya kala uku harda brush da su maclean bana zama har yanzu sai dai komai adan dagani nayi tazame mun kamar uwa mijinta da yayarta duk sunzo sun dubani daga gidanta ake mun girki.Likitoci da nas-nas suna ta yawo a kaina, amma cikin su duk babu wanda ya ja hankalina kamar Dr. Maryam mace mai kamala da tausayi, wadda take mu'amala da ni tamkar uwa da ɗiya.

Tun daga lokacin da na buɗe idanuwa a dakin jinya, Dr. Maryam ce ke kula da ni da kanta. Ita ce ke tabbatarwa na ci abinci, ta duba kafata.Tana ƙoƙarin bani kwarin gwiwa a kowane lokaci, har ta kai matakin cewa idan ba tana aiki ba, to tana zaune a kusa da gadona tana sauraron numfashina. Wayarta ma tana bani in dinga kallon fina-finai ko kuma na saurari karatun Qur’ani duk domin in manta da zafin jiki da kuma zafin zuciyar da nake ciki.

Ina yawan mafarki, mafarkai masu nauyi da suka cika da tsoro, da kuka. A mafi yawan lokuta sai in farka da zufa tana keto kamar an watsa ruwa a kaina. Da safe Dr. Maryam zata zo, ta zauna gefen gadona tace “Ramlah, yau ma an yi mafarkin?” Idan na ce mata eh, sai ta sauke ajiyar zuciya cikin tausayi, sannan tace min, “Yakamata mu ga likitan kwakwalwa, domin mafarkanki na iya nuna alamomin rauni a zuciya ko kwakwalwa.”

Haka ta kawomun abinci ranan nan tacemun in zauna inci abincin nan saboda kwana biyu zazzabi yana takuramun da daddare har takai takan kira yayarta ta zauna dani. Na zubawa abincin ido, ba don ina jin yunwa ba, sai don na san tana son in samu lafiya. Ta zuba mani shinkafa da miya da salad , ta ce in sha juice din da aka kawo min. Duk abincin da nake ci yanzu, Dr. Maryam ce ke kawowa. Tana siyo kayan wanka, tana kawo min sabbin riguna, tana kuma kulawa da kayan tsaftatawa na mace. A wani lokaci sai in zauna in kalle ta, hawaye na gangarowa a idanuna. Sai in ce mata, “Dr. Maryam, Allah ya saka da alheri, kin zamo uwa a wurina.”

Ta murmusa, ta ce, “Ramlah, ke kamar ‘yata ce. Allah ya bani ke a lokacin da kowa ya juya miki baya.”

Wani lokaci sai in fara kuka, ba don ciwon jikina ba, sai don ganin Allah yabani kyautar uwa lokaci guda, ko Na kasa tuna komai. Na sha tambayar kaina “Shin ni ‘yar wace unguwa ce? Wane gari muke ciki ma?” Lokacin da Dr. Maryam ta tambaye ni ina gidanmu, sai nace mata, “Ban sani ba, bana iya kwatantawa.”

Ta tsaya ta kalleni sosai, ta ce, “Yakamata mu samu bayanan danginki Ramlah. Amma naga kamar akwai matsala acikin kwakwalwarki.”

Wata rana ina zaune a gado, na tambaye ta“Dokta, me yasa kike min wannan kulawa haka? Me yasa ba ki gaji da ni ba?”

Ta zauna gefena, ta dafa hannuna, tace, “Saboda ina jin zafin dake ciki kamar nawa ne. Kuma saboda Allah ya ce mu kula da marasa lafiya da kulawa da tausayi. Ramlah, kin tsallake mutuwa ne dole ki godewa Allah, domin akwai wanda bai farka daga motar nan ba.”

Na fashe da kuka, nace, “To me yasa Allah bai ɗaukeni ba? Me yasa ni nake rayuwa cikin raɗaɗi?”

Ta sanya ni jiki, ta share hawayena da tissue sannan tace, “Domin Allah yana da babban sirri a rayuwarki. Ina rokonki, kada ki yanke ƙauna da rayuwa. Ki ci abinci, ki sha magani, mu ci gaba da addu’a. Allah zai bayyana komai.”

Wannan kalmomi nata sun shiga raina sosai, kamar ruwa mai sanyi da aka watsa a zuciyata. Na fara ɗan ƙoƙari, ko ba don komai ba, don Dr. Maryam. Ta zamo mai ƙarfafa zuciya a kowane lokaci. Komai nake so, ita ce ke bani. Ta fitar da kudi, ta siyo min turare, ta kawo min gyale mai laushi, tace, “Na san zaki fara fita nan gaba, ki zama mai tsabta da ƙamshi.”

Kullum da safe sai ta shigo da murmushi a fuska, tace min, “Yau kin dan ƙara kyau Ramlah.”

Sai in ce, “Dokta, me yasa kike so na haka?”

Ta ce, “Saboda ke na gani kamar diyata ce. Kuma na sha wahala a rayuwa na rasa mahaifiya tun ina ‘yar shekara goma. Dole na rayu da juriya. Zanyi iya ƙoƙarina ki dawo rayuwa cikin natsuwa.”

Har yanzu mafarkai na bani tsoro, sai dai kulawar Dr. Maryam na hana ni firgita. Kullum da dare, tana sanar da Nurse su tabbatar da cewa ba zan kwana ni kaɗai ba.

Bayan kwana biyu, muka shiga gaban likitan kwakwalwa, inda aka duba lafiyata. Bayan gwaje-gwaje, ya ce, “Ramlah, akwai trauma da kika fuskanta. Amma da kulawa da addu’a zaki warke.”

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[14/08, 11:46 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA BIYAR

Rungume suke da juna, zuciyarsu na bugawa da sauri kamar ruwan sama da ke sauka a lokacin damina. Wani irin yanayi na ƙauna da jin daɗi ne ya lullube su, tamkar ba duniya suke ba. Ayshatu ta ɗago idanunta tana kallon Alhaji Muqaddam cikin wani yanayi na taushin rai. Hannuwanta na cikin nashi, suka manne juna kamar su kaɗai aka halitta don juna.

Alhaji Muqaddam ya lumshe idanunsa, yana shakar ƙamshin turarenta mai daɗin gaske wanda ke tunzura zuciyarsa. Sai da ya janye da ɗan sanyi, sannan ya ce da ita cikin murya mai rauni, "Zanyi missing ɗinki Ayshatu... bana gajiya dake ko kadan. Amma banda yadda zanyi, tunda kince As'ad ya damu, ki koma. Nafiso ki kasance tawa ni ƙadai Wallahi ina mutukar bakin cikin cewa kina tare da As’ad."

Ayshatu tayi murmushi mai cike da wayo da ƙayatarwa. Tace, "So kakeyi asirinmu ya tonu? Kasan dai duk ƙasar da nake, akwai private jet ɗin As'ad."

Alhaji Muqaddam ya dafe fuskar Ayshatu yana kallon cikin idanunta. "Nima I'm going to miss you. Amma karki damu. Da zarar an gama biki, zan sameka. Ka sa ranka cikin sanyi."

Ayshatu ta sumbaci goshinsa, sannan ta janye cikin nutsuwa. Ta wani yatsine fuska mai ƙayatarwa, sannan ta juya cikin salo na Manyan mata. Abaya ce jikinta, mai tsadar gaske daga wani sanannen designer na ƙasar Paris, an ƙawata ta da adon zinariya da dinkin hannu. Takalminta na Loubs yana yi mata ratsa da kowace ƙafa ta taka.

Koda ta isa filin jirgi, wasu matan kamfanonin jirgin da suke cikin kayan uniform masu kyau suka tarbeta. Aka budewa Ayshatu wata babbar mota wadda za ta kai ta har gaban jirgin da ke jiranta. Jirgin kuwa ba karamin jirgi ba ne private jet mai suna *AL-AMIR ROYALE* wanda mallakin gidan As’ad ne gaba ɗaya. Komai yana cikin shirin karɓarta kamar yadda aka saba.

Ayshatu ta kalli sararin samaniya da nutsuwa. "Zan tafi amma bazan daina kaunarka ba, AlhajiMuqaddam ," ta furta a ranta.

A ɓangaren AlhajiMuqaddam, yana tsaye a bakin tagar babban hotel ɗinsa mai hawa goma sha biyu da ke tsakiyar birnin Dubai. Yana kallon yadda jirgin ke shawagi cikin sararin samaniya. Yayi ajiyar zuciya mai nauyi, yana tuna yadda suka shafe kwanaki suna soyayya da motsin rai ba tare da kowa ya gane ba.

Sanye yake cikin shiga ta alfarma. Yau aka kawo lefen Nawal, komai ya gudana kamar yadda al'ada ta tanadar an kashe kuɗi sosai, an cika harabar fada da motoci, hayaniya da busar kaho na annashuwa. Amma duk da wannan shagalin, ransa aɓace yake. Ba komai ke damunsa kamar yadda Ayshatu, matarsa, har yanzu bata dawo gida ba.

Idan yayi lissafi daidai, yau fa kwana sittin kenan rabonsa da ita. Ta masa magana kullum cewa business ne ya riketa a ƙasar waje. Tunaninsa ya zurfafa har sai da ya kasa zaune.

Sanar da shi aka yi cewa ga Hajja nan shigowa. A razane ya ɗan daidaita, ya samu guri ya zauna. Da girmamawa ya tashi ya tarbeta, gaisuwa ya mata na gaske. Hajja ta zauna tana kallonsa, fuskarta cike da damuwa da ɓacin rai.

"As'ad," ta fara da murya mai sanyi amma mai nauyin nuni, "Bansan irin zaman da kuke yi da Ayshatu ba. Shin kun rabu ne? Me yasa zata banzatar da yaranta haka? Yau ana batun fara biki, amma uwarsu tana can wai kasuwanci? Kusan watanni 2 fa, Kana ganin wannan daidai ne? Yara sun kwallafa rai akan uwarsu."

Ta daure fuska, sai ta cigaba, "Idan ba ka da lafiyar zama da ita, As'ad, karabu da ita ka sawwaka mata. Kada ka shiga hakkinta. Na gaya maka gaskiya."

Tunda Hajja ta fara magana, As'ad bai ce komai ba. Har sai da ta gama, sannan ya ɗago idonsa yana kallonta da damuwa.

"Inshaa Allah Hajja, zan ɗauki mataki. Ni ma abin yana taɓani sosai," ya amsa da ladabi.

Hajja ta miƙe tsaye. "Tun kafin Mai Martaba ya shiga cikin wannan lamari, ya kamata kai da kanka ka ɗauki mataki. Ka duba fa, idon mutane da yawa na kanka."

Ta fice cikin natsuwa kamar yadda ta shigo.

Bayan tafiyarta, As'ad ya kira PA dinsa da sauri. "Zan fita yanzu. Amma wannan fita sirri ce. Ka tabbatar ba wanda yasan inda nake."

PA din ya girgiza kai, "Ba damuwa ranka ya daɗe."

Bayan sun fito da mota, As'ad ya zauna a bayan motar yana duba agogo. Sai suka hau hanya cikin natsuwa da tsari. A titi, ya ɗago kai yace, "Ka kaini General Hospital. Maganar yarinyar nan fa?"

PA din ya juyo, "Ranka ya daɗe, tana samun sauƙi sosai. Likitan dake kula da ita na wajen ne kullum yana dubata. Idan kana so, zan kira shi ya zo yanzu."

As'ad ya girgiza kai, "A’a, inason naje da kaina. Inason ganin yarinyar da kaina. Inason jin komai daga bakin likitan da ke kula da ita."

Motar ta cigaba da tafiya cikin sauri amma natsuwa, har suka doshi babban ƙofar asibitin.

Cikin wata irin alfarma da ƙima da ta dace da gidan sarauta, aka turo wata fitacciyar motar Maybach s600 Guard mai cikakken kariya da aminci zuwa babban harabar asibitin na kasa. Yana fitowa daga cikin motar, ya sanya takalman "Oxford handmade" masu ɗauke da zinariya a gefuna, sanye da babban riga na zare mai ɗinki irin na Morocco, wanda aka kawata da zinariya ta dabam.

Kafin ya kai matakin ƙofar shiga asibitin, likitoci da jami'an lafiya suka rinka fitowa suna durƙusawa da cewa, “Ranka ya daɗe!” Sannu a hankali ya amsa tare da ɗan ɗaga hannunsa alamar girmamawa. Mamaki ya kama wasu daga cikin likitoci, musamman Dr. Bako, wanda ya san cewa yusuf an turashi india kusan kwanaki yanzu ma.

“Ina marar lafiyar da aka kawo daga haɗarin mota?” Ya tambayi babban jami’in asibitin.

“Ranka ya daɗe, tana cikin VIP suite ɗin da aka tanadar musamman bisa umarnin mai martaba.”

Suka nufo wing ɗin VIP ɗakin da aka ƙawata da gilashi mai sheƙi, labulaye masu lulluɓin ƙanshi irin na turaren oud da lavender. Lokacin da suka isa cikin babban daki mai lambar V-03, aka ce masa "ga yarinyar".

As’ad ya shiga cikin natsuwa, yana tafiya kamar sarkin wata, cikin kyakkyawan shimfiɗar gado mai dauke da tsarin hydraulic orthopedic mattress, da pillow mai aromatherapy. Ramlah na kwance cikin nutsuwa, tana bacci mai cike da gajiya da jin zafi. Jikinta a lullube da rigar asibiti mai launin "mint green," fuskarta kuwa cike da bayyanar raɗaɗi.

Dr. Maryam ce ke kula da ita babbar likita ce da ke da digiri daga Oxford Medical College, ta shigo cikin natsuwa bayan da aka kirata. Bayan gaisawa, As’ad ya ce

“Yaya jikin ta?”

“Tana samun sauki sosai, ranka ya daɗe. Sai dai matsalar ta da mantuwa tana kasa tuna komai game da iyayenta, ko sunayen nasu.”

As’ad ya ɗan lumshe ido, yace, “Kafarta fa?”

“Mun cire kwalbar da ta shiga kashin, mun saka titanium internal fixator. Har yanzu muna duba kar ta samu matsalar 'infection' amma ana recovery sosai.”

Yayi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce “Ki kula da ita sosai. Ina buƙatar every movement update komai da za kiyi ki sanar da ni.”

“Zan kula da ita tamkar diyata, ranka ya daɗe,” ta amsa tana sunkuyar da kai.

Ya juya cikin izza da salo, ya fice daga dakin yana barin ƙanshi mai ɗaukar hankali. Dr. Maryam ta tsaya tana kallonsa har ya ɓace daga gani.

Yana karasowa harabar gidan cikin wata motar alfarma dogaransa na biye da shi kamar zoben hannu. Cikin nutsuwa da izza ya taka matattakalar falonsa, sai wani babban mai gadin gida ya sunkuya yana kwasar gaisuwa. Bai ce komai ba, sai dai kallon daki-daki da ya aika masa kafin ya shiga cikin gidan.

“Mai girma, Hajiya Ayshatu ta dawo,” wata hadima ta shaida masa da ladabi.

Idanunsa suka yi ja, zuciyarsa ta kara tafarfasa da ƙiyayya da ɓacin rai. Lokacin da ya shigo, ya hangi Ayshatu zaune tana rungume da Nawal wacce ke sheƙe da murna. “Maamah I missed you sosai!” Nawal ta faɗa tana ƙara shigewa jikin Ayshatu.

Sai dai ba tare da ya ce uffan ba, As’ad ya wuce ya shige dakinsa, ya bar su a tsaye da mamaki da shiru.

Ayshatu wacce ta fahimci fushinsa ta saki dan murmushi, murmurshin mace mai kuzari da kwarjini, sannan ta kalli Nawal tana cewa, “Nawal, bari naji da daddynki zan shigo bangarenku.”

“Okay maamah,” Nawal ta amsa da murna.

Da kyar Ayshatu ta buɗe ƙofar dakinsa, kafin ta ce komai, sai kawai ya jiyo da fuska cike da ɗaci, a karo na farko tun aure ya ɗaga hannu ya kifa mata mari a kuncinta.

“How dare you!” Ya daka murya, kamar sarki na ba da umarni a majalisar fadawa.

“Kina da guts na banzatar da yara na da sunam business? Wani irin business ne da ba za’a iya yi a gida ba? Ayshatu! I’m tired. Idan har kin gaji, let’s be apart. Kowa ya kama gabansa. Please, just go.

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[17/08, 1:02 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SHIDA

Tunda ta fice daga dakin cikin ɓacin rai, As'ad ya bita da ido cikin mamaki da ɓoyayyen ciwo. Bai taɓa tunanin wata rana Ayshatu zata iya juya masa baya haka ba. Wannan ba ita bace ba irin matar da ya aura ba. Aysha da ya sani mace ce mai kunya, mai ladabi, mai mutunta miji da kulawa da gidan aurenta. Amma yanzu? Komai ya sauya. Abubuwan da suke faruwa sun wuce fahimtarsa.

"Subhanallah..." ya faɗi a hankali, yana jan numfashi. "Me ke faruwa da rayuwata haka?"

Ya zauna gefen gado yana shafa kansa da hannunsa mai santsi. Zuciyarsa na masa wani irin nauyi kamar an daura dutse a kanta. Wani abu kamar hawayen takaici ne ya taru a cikin idanunsa, sai dai ya ƙi barinsu su zubo. As'ad ba irin mutanen nan bane masu nuna rauni, duk da cewa zuciyarsa tana kuka fiye da yadda idonsa zai iya nunawa.

Bayan da ya ɗan nutsu, sai wayarsa ta ɗauki ƙara. Sakon daga masarauta ne sakon mai martaba kai tsaye yana nemansa. Ya miƙe da hanzari, ya saka babban jallabiyarsa na fitar gida irin wanda aka ƙera daga zaruruka masu tsada masu yalwa, ado a gefe da kuma tambarin masarautar da aka ɗinke a kafaɗa. Hanyar da ya fita ta babban ƙofar falo ce, wacce ke da tsawo da silin din tagulla, fitilu masu siffar lu'u-lu'u suna ta sheƙi.

Yana fitowa, direbansa ya buɗe masa kofar motar Range Rover Ko a hanya, idonsa na kallon nesa amma zuciyarsa na nan cikin rikici. Me ya faru da soyayyar da suka gina? Me yasa Aysha ta zama haka?

"Ko akwai wanda ke yaudararta?" Zuciyarsa ta tambaya. "Ko dai tana da wani sirri da bani da masaniya a kai?"

Motar na tafiya a hankali, gaban fadar sarki suka nufa. Yana isa aka buda masa kofar masarauta cikin girmamawa. Bayin fada suka durƙusa suna kwarara gaisuwa, kowanne yana cewa

"Ranka ya daɗe! Allah ya ƙara daraja!"

As'ad ya gaishe su da ido kawai. Bai da natsuwar yin magana da kowa. Har ya iso dakin mai martaba ya shiga ciki. Kamar kullum, fadar na sheƙi da alfarm bulo-bulo na marmara, labule na siffar alkyabba, kujeru masu ɗinke da zinariya. Mai martaba yana zaune yana karanta wata takarda lokacin da As'ad ya shigo. Ya ɗago kai ya kalleshi.

"As'ad ɗana, me nake ji game da Ayshatu da Nawal?"

Ya ɗan sunkuyar da kai. "Mai martaba, abubuwa sun rikice. Ayshatu ta zama tamkar ba ita ba, kwata-kwata ta canza."

Mai martaba ya lumshe ido. "Ina matuƙar son zaman lafiya a tsakanin ku. Ku mutane ne masu daraja a idon jama’a. Idan aure ya gaza, sai a sawwaka shi da sauƙi. Amma kada ku banzatar da shi."

As'ad ya gyada kai da ladabi. "Na gode mai martaba. Zan yi iyakar ƙoƙarina."

"Ya maganar yarinyar danace kaje ka dubamun ita da kanka?" ya tambaya cikin murya mai ƙaifi , yana mai turo hanci cikin ikon mulki.

As'ad ya rusuna kadan yana cewa, "Ranka ya dade, naje kamar yadda ka umurce ni. Na gan ta da idona a VIP ward, tana samun kulawa sosai daga likitocin babban asibiti."

Sarki ya ɗan juya kansa kadan, yana duba cikin idon As’ad. “Kaje ko ka dubata As'ad? Idan ka dubata, shin ba ka ji wani abu a zuciyarka ba? Yarinyar nan bata da kowa yanzu.”

As’ad ya sunkuyar da kai yana jan numfashi. Mai martaba ya ci gaba, "Yakamata ka dinga girmama maganata. Yakamata ka nemi iyayenta, As’ad, at least ayi bincike. Idan ya kama, a fidda ta waje. Mu kasance masu tausayi mana a cikin zukatanmu. Yaranmu zasu iya kasancewa a halinta."

"Na fahimta, ranka ya dade. Zan dauki alhakin binciken iyayenta. In shaa Allah zan kula," cewar As’ad, yana zubda idanunsa a kasa.

Sarki ya dafa hancinsa cikin alamar gajiya. "Kuma maganar komawarka Paris da zama, banyi izini ba As’ad. Ya kamata kazama jarumi sosai. Ka tsaya kamar namiji. Watakila wata rana kai ne sarkin wannan garin gaba daya. Haka zakai ta guje-guje saboda wata magana mara tushe? Ba haka ake shugabanci ba."

Waziri ya gyara zama yana cewa, "Ayi hakuri, ranka ya dade. Zai gyara, zai kula da dukkanin abubuwan da suka kamata, In shaa Allahu."

Mai martaba ya kada kansa a hankali, yana juyawa gefe cikin halin duba nagarta da jagoranci.

*****

Tunda takarasa dakinta ta banko kofar da ta amsa gaba daya, wani marayan kuka ne ya kufce mata. Tabbas bai taɓa ko yimata ihu ba, balle dukanta ko marinta. Wannan shine karon farko daya daga hannunsa fuskarta a rayuwar aurensu. Wani irin tsaki ta ja, zuciyarta cike da kunya da ɓacin rai, zuciyar da tayi kaca-kaca da kalmomin da ba zata iya furtawa ba. Sai ta dakko wayarta cikin rawar hannaye, ta shiga dialing number ɗin Alhaji Mukaddam.

Bugu biyu kacal ya ɗauka, kamar dai ya rigada ya san damuwarta. Sai ta fashe masa da kuka, tana fadin, “As’ad ne ya mare ni... he slap me, my love...” Muryarta cike da hawayen da ke fita da wahala, zuciyarta na kuna da zafi mai haɗe da raɗaɗin raini.

Cikin wata irin masifa mai sa zuciya rawar jiki, Alhaji Mukaddam yace, “Akan wani dalili?! Kibarni na illata mutumin nan Ayshatu! Bai san darajarki ba! Mugu ne! Kina dai gani gabansa baya aiki amma yakasa rabuwa dake dan yanaso ki kasance cikin kunci!”

Cikin daki mai walwali, dauke da fitilun Swarovski da falsar turaren oud mai kamshi, Alhaji Mukaddam yana kwance a saman gadon na musamman, yana magana da ita kamar mijin aure da matarsa.

Ya ci gaba da cewa, “Akwai aikin da zan yi akansa cikin week ɗin nan. Fansar marin nan naki... ki yi hakuri, I love you. Ni missing ɗinki nake sosai wallahi. Soyayyarki ta riketa ni, babyna. Kinji? Jikina har ya mike... ki daina kuka. I will do something.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull