Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 3
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 3: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 3. Cikin shagwaba da tsantsar shagaltuwa, Ayshatu tace, “Are you sure?…
4,496 words
Cikin shagwaba da tsantsar shagaltuwa, Ayshatu tace, “Are you sure? Ka tabbatar? Kayi min video call, let me see you.”
A take ya canza kiran zuwa video call. Fuskar sa cikin tsabta da tsafta irin ta manyan attajirai masu hutawa a manyan villas na Dubai ta bayyana. Shima yana sanye da doguwar riga ta alfarma mai launin ivory da zane na ja. Fuskarsa na bayyana damuwarsa gareta da yadda zuciyarsa ke tafarfasa da son ta.
Ta dafa kirjinta tana kallo, tana murmushi cikin hawayenta, tana fadin, “I miss you more, kaɗan ne nake bukata daga gareka kaɗan daga kulawarka ina bukatarka, Mukaddam.”
Ya gyara zama, yana duba ta daga allon wayar, sannan yace, “Ki kwanta ki huta, my queen. Raina na a kanki, zuciyata ke karaya idan kina kuka. Wallahi bazan bari kiyi kuka ba, komai sai nayi. I’ll make sure As’ad ya gane kuskurensa.”
Soyayyar su taci gaba suna musayar kalmomi masu daɗi, kamar a cikin fim. Wayar ta shiga salo na soyayya mai kauri, tana ɗebe Ayshatu daga zafin da take ciki. Da wannan ta samu natsuwa, ta lumshe idanu tana jin zuciyarta na saukar nauyi, tana godewa kasancewar Alhaji Mukaddam a rayuwarta.
*******
Tunda na bude idanuwana wani ƙamshi ya bugi hancina, cikin wata irin firgita na saki ƙara mai ƙarfi ina fadin “Ga Bashari! Bashari ne! Ku Rikeshi dan Allah, rikemun hannu, I want to live my life with you! Wayyo Bashari, karka tafi...!”
Ihun da nayi ne ya sanya likitoci da nurses suka shigo da sauri cikin ɗakin. Cikin firgici da kulawa Dr. Maryam ta iso da sauri, ta rungumeni tana sauke addu’a da karatu a kunne na. Tana dafa ni, tana shafa jikina a hankali, tana tausayawa irin halin da na shiga.
“Lafiya Ramlah! Lafiya... kin dawo da cikakken numfashi, alhamdulillah. Amma ya kamata a sake dubaki. Nurse, a kira team ɗin X-ray yanzu-nan,” in ji Dr. Maryam da gaggawa.
Nurses biyu suka fito daga ɗakin cikin hanzari. Daya ta kama hannuna da tausayawa tana cewa, “Ramlah ki kwantar da hankalinki, komai zai daidaita, muna tare da ke.”
An shiryani cikin mintuna kaɗan. Aka saka ni a kan gado mai ƙafafun tuƙi, aka ɗaura ni da belin lafiya don kar in motsa ƙafata. Aka sanya min allurar rage ciwo cikin hannu na dama, yayin da wata nurse ke riƙe da oxygen tube kusa da hancina. Likitan X-ray ya iso da kayan aikin sa, yana duba takardun cikakken bayani da ke fayil dina.
Aka tura ni har zuwa babban dakin X-ray. Cikin kankanin lokaci aka tabbatar da cewa akwai wasu kayan ƙarfe da aka manta dasu a aikin tiyata na baya, kuma sun matse wani jijiyar ƙafa ta hagu. Cikin sauri aka shirya komai don a sake yin karamin aikin cire kayan.
Dr. Maryam ta sanya hannu cikin bayani, ta ce, “Mu haɗu da Dr. Kabir, specialist orthopedic surgeon, domin gudanar da wannan aiki cikin sauri. Wannan ƙaramin aiki ne amma yana bukatar kulawa ta musamman.”
A cikin wannan yanayi aka kwantar da ni da kulawa, yayin da zuciyata ke bugawa da sauri, amma Dr. Maryam na rike da hannuna, tana ba ni karfin gwiwa. “Zaki warke, Ramlah. Zaki warke, in sha Allah. Ki amince da ikon Allah.”
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
Nana hadiza
09030569336
[17/08, 6:03 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA BAKWAI
Bayan sun ƙara fito da ni daga aikin, wani irin tsananin zafi ya mamaye jikina gaba ɗaya. Cikin raɗaɗin da nake ji, sai na fara birgima a gadon, ina kuka mai ƙara kamar mai cikin maƙiyaya. Na dinga roƙon ruwa da ƙarfi, na dinga fadin 'Dan Allah ku bani ruwa, zan mutu!' Amma suka hana ni. Wani daga cikinsu yace, 'Patient bai kamata ya sha ruwa ba sai bayan awanni, don lafiyarsa.' Amma ni kuwa ban fahimta ba ciwo ya gagare ni, makogwarona ya bushe, jikina ya karye. Na dinga ihu, na dinga kiran sunan Allah 'Wayyo Allah! Ya Allah ka taimakeni, Zan mutu kubani ruwa kafata zata cire wayoo Allah Na ' Na kuma fara kiran sunan Bashari da karfi 'Bashari... Bashari dan Allah kazo ka ceci matarka!' Amma babu wanda ya amsa sai karar na’ura da sautina atake likitan yace 'BP ɗinta yana sauka sosai, a ɗauki mataki yanzu!'
Dr. Maryam ce ta matso kusa da ni da sauri, tana rike hannuna, tana karanta addu’o’i cikin sassanyar murya. 'Ki kwantar da hankali Ramlah,' ta fada cikin tausayi. 'Kin fito lafiya, sai dai kisa zuciyarki cikin nutsuwa domin ki murmure. Ki tuna da Allah, ki bar kuka haka.' Amma kuka ya ƙi dena zuwa gareni, domin raɗaɗi da rashin samun abinda nake nema suka mayar da zuciyata kamar an huda da wuka.
Ana cikin haka, aka ɗauke ni aka sake maidani ɗakin kulawa na musamman, inda injin numfashi da na’urorin duba jini suka cigaba da aiki a kaina. Daga can nake jin Dr. Maryam tana bada umarni 'A ajiye ta cikin kwanciyar hankali. A saka ta cikin fluid IV, sannan ku sanya mata pain reliever. Daga nan sai mu jira a duba X-ray ɗin ƙafarta da aka yi kafin mu ci gaba da kulawa.'
Duk da yadda nake cikin jiri da azabar zuciya bayan aikin tiyata.
***
Wani bawan Allah dake gefen vip daƙin danake ciki ne ya kalli nurse din da suke gaisawa yace “Lafiyar yarinyar nan kuwa? Haihuwa zata yi ne? Ko…?”
Cikin girmamawa da tausayi, nurse ɗin tace
“A’a Alhaji, ba haihuwa ba. Accident tayi very serious. Aiki sau uku aka mata. Kafarta ta tsage, har yanzu ba a san kowa nata ba Akallah zatayi 3weeks , ba a san iyayenta ko danginta ba. Yanzu haka da nake maka magana, basu dade da fito da ita daga theatre ba.”
“Allah sarki… Allah sarki… this is punishment. No family for her…?”
Nurse ta kalle shi tace
“Eh, ainihin gaskiya. Ko ID bata da ita. Kuma har yanzu bata iya magana… tana cikin unconscious state. Bai kamata a bar ta a irin wannan halin ba.”
Na tausayamata wallahi but bari nagama da doctor zan shiga in dubata.
Bacci nayi sosai a ranar, sai wajen ƙarfe sha biyu na rana sannan na farka. Doctor Maryam ce ta zo ta bani abinci tare da ruwa sannan ta bani magani. Wani allura ce ta sake yi min, hakan yasa bacci ya sake daukeni. Ban tashi ba sai bayan gari ya waye. Lokacin da na buɗe idona, na nemi alfarmar Dr. Maryam da ta taimaka mini da alwala domin in sauke sallolina. Cike da kulawa ta taimaka ta yi mini brush, ta wanke fuska ta kuma yi mini alwala. Sai da na idar da sallata a kwance, bacci ya sake kwasata.
A gefe guda kuma, kamar yadda yayi alkawari, Alhaji Hamza ya dawo domin ganin yarinyar da aka ce tana ihu jiya. Da ya iso asibitin, kai tsaye ya wuce VIP ward inda aka kwantar da ita. Ya tambayi wata nurse dake bakin kofa inda dakin marar lafiyar yake, nan take ta nuna masa. A hankali ya murɗa kofar, yana mai sallama cikin ladabi da nutsuwa. Aka amsa masa da "come in."
Da farko bai lura da fuskar yarinyar ba saboda ganin nurses biyu a tsaye, sai ya ce, "Sorry, I will come back later." Yana juyawa zai fita kenan, sai kallon fuskarta ya kama shi. Ramlah shine kalmar daya faɗa atake Tsayawa yayi cak! Kirjinsa ya fara bugawa da ƙarfi, yana cigaba da matsowa cikin dakin. A cikin magagin bacci, Ramlah ta buɗe idonta, tana ganin hazo-hazo ne. Tace da rauni, "Bashari... gani nan... Bashari ka zo ka ɗaukeni... jikina ciwo... zafi Bashari..."
Dr. Maryam ce ta matso da sauri ta ɗan ruɗe, tace, "Bawan Allah, kasanta ne?" "Sannu doctor," ya faɗa cikin sanyin murya. "Tun yaushe take nan? Ni kawunta ne. Jiya naji ihu a asibitin nan shine nace sai na shigo in ga marar lafiyar nan in yimata Addu'a ."
Dr. Maryam ta yi ajiyar zuciya, tace, "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Ramlah ke nan... Amma bawan Allah, don Allah mu fita waje muyi magana. Yanzu haka tana cikin trauma ne sosai, gaskiya ba zata gane komai ba."
Bayan sun fito daga dakin suka zauna a wani ofis din asibitin, Dr. Maryam ta kalli Uncle Hamza da kulawa, tace
"Alhamdulillah, naji daɗin ganin ku wallahi. Gaskiya wannan yarinya ta sha wahala. Sunyi accident ne kusan sati uku da suka wuce. Dukkan mutanen cikin motar sun rasu, ita kaɗai ce ta tsira. Itama fa ba a ce tayi tsira gaba ɗaya ba, domin jiki da ruhi duk sun ji rauni sosai. Mai martaba Sarki ne da kansa ya bada umarnin a kula da ita, tun daga ranar da aka kawo ta aka tsare ta a VIP."
Ta ɗan ja numfashi, sannan tace: "Mun gano cewa kafarta kwalabe sun shiga. An yi mata aiki har sau uku kafin ta samu sauƙi. Har yanzu tana buƙatar kulawa ta musamman saboda tana fama da mantuwa, da ruɗani. Idan ta farka, ba ta iya tuna iyayenta ba, sai dai tana kiran sunaye da ba mu san su wanene ba. A gaskiya muna buƙatarku kusa da ita wani daga cikin danginta domin taimakon jin daɗin zuciyarta."
Uncle Hamza ya dafe kansa, cikin wani yanayi mai raɗaɗi, yace: "Ya Allah, Ramlah... wannan yarinyar bata da laifi. Tun tana ƙarama take fama da rayuwa mai wahala. Allah ya saka da alheri ga mai martaba da ya ɗauki nauyinta. Yanzu da kika ce tana cikin ruɗani, akwai yiwuwar wannan damuwa da taji ta wuce ƙima ne. Insha Allah zan nemi babanta da gaggawa, mu zo mu tsaya mata."
Suka miƙe tsaye, kowa cikin yanayi na tausayawa da fatan alheri. Cikin zuciyar Uncle Hamza, addu'o'i da damuwa suka cika.
Hawayen dake fuskarsa ya goge, yace, “bari na kira babanta yanzu.” Doctor Maryam ta saki murmushi tana kallonsu cike da jin tausayin yadda zuciyar wannan saurayi ke nuna damuwa da ƙauna ba tare da shakku ba. “Doctor, mungode sosai. Allah ya saka miki da alkhairi.”
“Ba komai, wannan aikina ne,” ta amsa tana mai haɗe hannuwanta a kirji.
Wayar dake hannunsa tafara ringing. Bai tsaya tunani ba ya dannan kira. Cikin wani irin sauri da tashin hankali ya ɗaga wayar yana cewa, “Yaya malam, dan Allah duk inda kake kazo nan babban asibitin birni yanzu, dan Allah.”
A cikin wayar, muryar malam ɗinsa ta amsa da nutsuwa, “Lafiya dai, Hamza?”
“A’a yaya malam, ba lafiya ba. Kazo dan Allah yanzu yanzu, yanzu ne kawai,” ya maimaita yana kallon ƙofar dakin da Ramlah ke kwance.
“To ganinan inshaa Allahu. Dama mun fito da Zainabu gaisuwa,” ya ce a cikin wayar yana nuni da cewa tuni ya shiga hanya.
Uncle Hamza ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya. Kamar zuciyarsa zata fashe saboda yadda yake jin zafin halin da Ramlah ta tsinci kanta ciki.
A cikin zuciyarsa, yana jin kaunar Ramlah kamar yadda mahaifi ke jin ta ga ɗiyarsa. Kuma a yanzu, ya fara ganin alamar cewa akwai buƙatar karɓa da dagewa wajen neman mafita da kawo karshen wannan baƙin labarin.
Likita Maryam na tsaye a gefe, tana karanta fuskarsa da zuciyarsa. Daga kallo daya, zaka gane tana jin tausayinsa sosai. Amma da kwarewar aiki ta san cewa dole ne a ci gaba da kula da Ramlah har sai ta dawo daidai, ba kawai lafiyar jiki ba, har ma da na zuciya da tunani.
Uncle Hamza ya ja kujera ya zauna bakin gado, yana kallon Ramlah da wani irin kallo na tsantsar tausayi da kauna. Ya dafa hannunta a hankali ya furta, “Allah ya baki lafiya, Ramlah.”
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
Nana hadiza
09030569336
[19/08, 8:05 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TAKWAS
Abban Ramlah ina kakeyi damu haka? Nazata gida zamu wuce ai?.
"Eh, Hamza ne ya kirani akan nazo Asubuti, babu lafiya," cewar Abba.
Abbas dake gefen Abba yace, "Subhanallah, Allah yasa dai lafiya."
Mumy dake baya tace, "Wanne irin lafiya kanaji ana ambatar Asubuti?"
Cikin hanzari sosai Abba ke tokin mota har suka karasa babban General Hospital.
A hankali yayi parking motar yana dannawa Hamza kira.
"Yaya, ku karaso bangaren VIP, muna nan."
"Okay, tohm ga mu nan."
Suka karasa har babban gini na VIP sannan suka fito.
A tsaye suka tarar da Hamza, idonsa duk ya canza yayi jajir.
"Lafiya kuwa, Uncle?" Abbas ya fada yana kallonsa.
Kumuje ku gani, in ji Hamza, yana ja gaba cikin hanzari. Har suka hadu da Dr. Maryam a hanyar da ta nufi bangaren VIP. A nan ne Hamza ya nuna mata ga mahaifinta yana tsaye, ta gaidashi cikin ladabi, shi kuma Abba ya amsa da murmushi mai sanyi.
Suna shiga dakin da Ramlah ke ciki suka tarar da ita kwance a gado, kafarta gabadaya anannade da bandeji. Fuskarta ba komai face raɗaɗi, amma har yanzu akwai haske mai ban tausayi a cikinta. Tana kallon dayan gefenta, kamar bata ankara da zuwansu ba.
Sai da Mumy ta furta da kakkausar murya, "Wacece nake gani kamar Ramlah? Wato guduwa kikayi kenan?" Kalaman nata sun cika da wulaƙanci da rashin tausayi, kamar yadda aka saba daga gareta.
Abba kuwa kafin ma ya iya furta komai, idonsa ya kai ga halin da 'yarsa ke ciki, ya saki wani irin numfashi mai nauyi. Sai kawai jikinshi ya saki, ya fadi kasa warwas. Wannan lamari ya girgiza likitocin da ke kusa, suka ruga da gaggawa suka tallafe shi, tare da kiran karin taimako. Har sai da aka kwantar da shi a wani gado kusa, domin sauke nauyin da zuciyarsa ke ɗauka.
Uncle Hamza kuwa ya samu damarsa ya matsa kusa da Mumy yana kokarin yi mata nasiha cikin natsuwa. Amma ita ko ajikinta, sai ƙara zazzaga maganganun da suka cika da zargi da rashin imani. "Wayasani ma ko Ramlah ce ta kashe mijin nata ta gudu," in ji ta tana kwaɓe fuska.
Dr. Maryam da ke tsaye gefe ta girgiza kai cikin tausayi, tana kallon yadda ake wulakanta marar lafiya maimakon a kwantar mata da hankali.
Mumy ta tsaya gaban gadon Ramlah, ta danyi kallonta sama da ƙasa. Sai da ta tsaya cak, zuciyarta ta buga. Ganin yadda Ramlah ta ƙara kyau, ta ƙara kiba, jikinta ya murje kamar wanda ke samun gata da kulawa ta musamman ba yadda take fata ta ganta ba, ba a wulakance, ba a lalace.
Wani malalo ya tsaya mata a cikin wuya. Jin bakin ciki da kishin ganin wadda take fata ta rushe, ta dawo da kuzari. Wannan abu ya cika mata zuciya da takaici da kuma haushi.
Amma Ramlah ko a jikinta. Idonta a rufe, numfashinta na tafiya a hankali, jikinta cikin natsuwa kamar mai barci. Wani salo na natsuwa da kwanciyar hankali ke yawo daga gareta salon da ya fi komai ciwo a zuciyar Mumy.
Daga can nesa, muryar Dr. Maryam tana ba da umarni ga nurses da su kara kula da marar lafiya da ke cikin wannan daki, tare da tabbatar da cewa an dakile duk wani abu da zai kawo cikas ga murmurewarta.
Wani mugun kallo mumy tayiwa doctor maryam tana fita domin in tacigaba da kallon ramlah to tabbas zata rufeta da duka wallahi tsabagen baƙin Cikin da zuciyarta takeyi da hassada to make faruwa taji dai ana cewa hatsari, kenan bashari ya mutu tafaɗa tana dafe kirjinta da bakin ciki shikenan abunda ta kullah ya warware shikenan an ruguza mata komai kuma yadda ma take kallon Ramlah fari taga tayi sosai da kiba tacika tayi wani kalar bul bul da ita Innalillahi wa inna ilaihi raji’un tafaɗa tana dafa kujerar reception tana zama.
Uncle Hamza dake kusa da gadon da Yaya Malam ke kwance ya kalli ɗan uwansa da damuwa a fuskarsa. A hankali ya ce, “Abban Ramlah, ka dubi yarinyar nan a wannan ƙaron don Allah. Ka dubi halin da take ciki, ka saurari zuciyarta da idon tausayi kada ka manta yarinyar nan amanace gareka marainiya ce wallahi wallahi auren yaron nan da akayimata an zulunci ta amma yadda likitan ta sanar dani yadda take ambatar sunansa hakan ya nuna ya kuka da'ita yadda ya kamata.”
Cike da gajiya da kunya, Abban Ramlah ya juyo ya kallesa. Ya saki wata doguwar ajiyar zuciya kafin ya ce, “I learn from my mistake, Hamza. Na fahimci kuskurena. Nayi kuskure, nayi babban kuskure amma yanzu zan gyara. Nagane wacece Zainabu tun kwanakin da suka wuce. Zainabu da zugarta ta ɓatamun zuciya. Wannan karon zan tsaya na duba gaskiya zan kula da diyata zan kuma tsaya mata Inshaa Allahu.”
Hamza ya dan murmusa, idonsa ya cika da hawaye. Ya ce, “Alhamdulillah. Allah nagode maka da wannan rana. Ka san Ramlah tayi hatsari fiye da sati huɗu yanzu? Kuma ba kowa ne zai rayu a irin wannan hatsari ba. Ita ce kadai ta tsira cikin motar, sauran duk sun rasu. Kafarta ce kawai ta samu rauni, amma likitoci sun tabbatar da cewa zata warke da izinin Allah.”
Yaya Malam ya kada kai, zuciyarsa cike da nadama. “Muje naganta Hamza. Naganta, ɗiyata. Diyar albarka. Nagane gaskiya yanzu. Kana ganin yadda Bilkisu ta ɓatamun suna? Kana ganin yadda ta lalata rayuwarta? Ko?”
Hamza ya kamo hannunsa yana dariyar tausayi. “Koma menene, yanzu lokaci ne na gyara. Abinda ya rage garemu shine addu’a da kula. Ka shiga ka duba ta, ka nunawa zuciyarta cewa tana da iyaye.”
Yaya Malam ya gyara zamansa, zuciyarsa cike da kishi da ƙauna ga ‘yarsa da a baya ya yi watsi da ita. Yanzu lokaci ne da zai gyara kuskuren da rayuwa ta watsar masa da mafita.
Haka Uncle Hamza ya riko Yaya Malam suka nufi ɗakin da Ramlah take kwance, likitanta na tsaye a kanta yana duba ta. Mumy kuwa, saboda bakin ciki da haushin abin da ke faruwa, ta kasa ma komawa ɗakin gaba ɗaya. Zuciyarta tana mata zafi sosai ga tata yarinyar can ta zama ƴar maye cikakkiya ga wacce takai gidan ɗan shaye shayen ko alamun shaye shaye babu atattare da'ita.Tashiga tashin hankali matuƙaganin duk wata dabararta ta rushe, asirin da ta kulla yana ta watsewa tamkar garwashin toka a iska. Ita kam sai ta ga Ramlah ta lalace sosai, ta zube, ta lalata kanta. Amma abin mamaki, yau idonta ke hango wata siffa ta daban Ramlah ta yi kyau, ta yi fari, ta ƙara kiba. Babu ko ɗan alamar lalacewa ko shaye-shaye a fuskarta, balle warin sigari ko giya. Zuciyar Mumy ta cika da mamaki, takaici da kuma tsananin kishi.
Tana ganin Abban Ramlah ya shigo, sai ta yi saurin shigowa ita ma, tana kwaɓe fuska, ta riƙe kanta.
“Haba, Abban Ramlah! Ka zo da kanka bayan kai ma jikinka ba daɗi. Wallahi wannan labari bai yi min daɗi ba… Allah dai ya sa ba wani abu ta aikata ba ne har ta gudu zuwa nan,” ta faɗa cikin murya mai cike da kwaɗayi na neman amsa.
Abba ya juyo a hankali, idanunsa suka ɗan ƙanƙance, sannan cikin muryarsa mai nauyi amma mai ƙarfi yace “Zaki iya yi min shiru, Zainabu?”
Kalmar ta doki zuciyar Mumy tamkar wuka. Likita ta kawo wa Abba kujera, ya zauna a hankali, yana kallon Ramlah da ta kwanta cikin rauni. A hankali ya kama hannunta, yana shafa shi cikin tausayi. Nan take, kamar wanda aka ja daga zurfin mafarki, ta buɗe idanunta a hankali.
Ganin Abba a gefen gadonta ya sa zuciyarta ta karye, idanuwanta suka cika da hawaye, sai ta fashe da kuka mai tsuma rai.
Cikin muryarsa mai sanyi, Abba ya ce
“Kiyi hakuri, Ramlahtu… ki yi shiru, komai zai wuce.”
Amma cikin rawar murya ta faɗa da sauri
“Bashari… Bashari bai nan… Bashari yaki zuwa… wai Bashari ya tafi, Abba… Bashari ne kaɗai yake sona Abba danAllah kace yadawo zamuje sabon gidanmu ”
Kamar yadda kalamanta suka rikita zuciyar kowa a ɗakin, haka suka tayar da damuwa a zuciyar mahaifinta. Likita Maryam ta matso, ta dubi Abba sannan cikin muryarta mai taushi ta ce “Kayi hakuri, Alhaji… ta shiga halin unconscious sosai tun lokacin da aka kawo ta. Wannan muryar da kake ji yanzu na cikin rudani ce. In shaa Allah, da izinin Allah, zata dawo daidai.”
Abba ya lumshe ido, yana share hawayen da suka taru masa a fuska, zuciyarsa cike da nadama, tausayin ’yarsa, da kuma ciwon ganin irin wannan hali da take ciki…
Na fashe da kuka tamkar zan suma, hawayen suka zubo min ba tare da tsayawa ba. Cikin rawar murya nace,
“Abba… Bashari nake so… na je wajensa… kai zaka kaini ko?”
Yaya Abbas ya matso kusa da gadona, ya riƙo hannuna yana mai shafa shi da taushi.
“Kiyi hakuri, Ramlah,” ya ce cikin muryar tausasawa. “Ki dage da addu’a ga Bashari… Allah ya kyautata makwancinsa.”
Na girgiza kai da ƙarfi, idanuna cike da hawaye.
“Abba, wallahi bai mutu ba… kuma ba zai mutu ba!”
Abba ya kasa jurewa, zuciyarsa ta karye da jin irin nadamar da ke cikin maganata. Ya matso sosai, ya rungume ni tamkar kar ya sake ni. Hannayensa masu ƙarfi amma masu dumi suka lullube ni gaba ɗaya, yana shafa bayana a hankali.
“Ramlahtu,” ya furta cikin muryar da take girgiza zuciya. “Ki kwantar da hankalinki… Bashari yana hannun Allah. Idan Allah ya rubuta zai dawo, babu mai hana hakan. Amma ki kula da kanki yanzu, don ni ina buƙatar ki fiye da kowane lokaci. Ke ce ƙawata, ke ce farin cikin raina. Bana so in kara ganin hawayenki… idan zan iya, da zan kwashe duk ciwonki in ɗora a kaina. Ki bar wannan kuka, kinji?”
Ya ɗaga hannuna ya manna shi a ƙirjinsa.
“Kin ji yadda zuciyata ke bugawa? Kowanne bugun zuciyata yana faɗin addu’a ne saboda ke. Idan kika kasance cikin lafiya, wallahi komai zai dawo daidai. Ki yi mini alƙawari, Ramlahtu, zaki tsayar da damuwar nan kinji saboda ni.”
Muryarsa ta cika da taushi amma tana ɗauke da wani nauyin soyayya da kulawa da ko a mafarki ban taba tsammanin zan ji daga gare shi ba.
A gefe kuma, Mumy tana tsaye tana kallon wannan yanayin, zuciyarta na tafarfasa da haushi da kishi, ganin yadda Abba ke rungumeni tamkar wata ƙaramar sarauniya. Amma Abba bai ma kalleta ba duk hankalinsa na kaina….
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
Nana hadiza
09030569336
[19/08, 8:05 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TARA
Fati ta zuba mata ido tana kallon Ayshatu kamar wadda bata yarda da abinda ta ji ba. Tana zaune kan kujera mai launin zinariya, falon yana sheƙi da hasken fitila mai ƙyalli. Ƙamshin turare mai tsada ya cika dakin.
“Ban gane ba Ayshatu,” ta fara magana a hankali amma muryarta na ɗauke da izza. “Ke baki san wanene As’ad ba ko? Wannan ba saurayi irin na titi bane. As’ad ɗan gidan sarauta ne, kokuma nace miki ɗan sarki ne mai kuɗi fiye da tunaninki. Ke ce kika gaya min cewa zaki rufe duk wata kafa da zai iya samun zargi a kanki. To yanzu me yasa zaki nuna masa wani abu da zai fara tunanin akwai matsala? Idan ya fara zargi, kinsan wallahi zai gano komai.”
Ayshatu ta ja dogon numfashi, ta ɗan ɗaga gira, ta ce “Kin san me yayi min kuwa, Fati? Ya mare ni! Abhnda bai taba ba kome nayi ai bai kamata yayimun haka ba”
Fati ta ɗan girgiza kai tana murmushi mara annuri. “To gaskiya Ayshatu, na yarda kin canza. Wannan soyayyar ta rufe miki ido sosai. Har kin manta wacece ke. Shi As’ad ne fa… namijin da mata ke mafarkin samu. Idan kika rasa wannan damar, zaki yi nadama har abada. Idan bazaki iya zama dashi ba to kawai ki nemi takardarki agurinsa kamin ki tonawa kanki asirin.”
Ayshatu ta ɗan matsa kusa da ita, ta ce
“Takarda kike cewa in nema? Tayaya zan iya rabuwa dashi? Ni fa ina son duk abin da yake da shi. Gidaje, motoci, kuɗi, darajar zama uwargida. Abinda nake jin haushi kawai marin da yayi min ne.”
Fati ta saki wani murmushi mai kaifin ma’ana, ta ce “To shikenan. Ki je ki lallabashi, ki dawo yadda kika saba masa kafin ya fara bincike ya gano sirrinki. Idan kika bari ya fita daga hannunki, wannan saurayin da kike ɓoye a gefe bazai iya baki wannan rayuwar ba. Ki bar shi kawai a gefe kina ɗebe kewa, amma kar ki kuskura ki saki As’ad.”
Ayshatu ta ɗaga ido tana mamaki.
“Kina nufin bayan ya mare ni, na je na bashi hakuri? Haba Fati!”
Fati ta tsareta da ido ta ce
“Ayshatu, ki saurare ni da kyau. Ki yi hakuri, ki lallabashi. Wannan dama bata zuwa sau biyu. Wannan sabuwar motar da kike mafarki, kin san tayaya kawai za ki mallaketa? Idan kika tabbatar kin dawo masa da kaunarsa. Ki yi tunanin mace mai daraja, ki yi aikinta kamar mace mai daraja.”
A zuciyar Ayshatu, ta riga ta yanke shawara
“Zan koma masa da fara’a, zan ba shi soyayya fiye da da. Zan sa shi ya ji ni ce rayuwarsa. Amma a zuciya ta, zan riƙe wannan marin a matsayin kalubale. Zan rama… a hanya da ba zai taɓa zato ba.”
*******
A cikin babban falon gidan Alhaji Mukaddam, bangon gilashi mai tsawo yana nuna hasken fitilun gari daga nesa. Kujerun leather na launin baki da ja sun cika falon, ƙamshin turaren Oud na yawo a iskar ac, yayin da ƙarar ƙaramar kiɗa daga sound system ke lullube wajen.
Alhaji Mukaddam yana zaune a kujerar executive, kafarsa ɗaya a ɗora kan ɗaya, hannunsa riƙe da coffee mug fari. Idonsa yana ɗauke da nutsuwa irin ta wanda ya saba da yin manyan cinikayya.
A gabansa, Samuel ne babban yaron da ya fi yawan shigar masa da kuɗaɗen kasuwanci yana tsaye da murmushi a fuskarsa, sanye cikin designer suit mai kyau.
Alhaji Mukaddam ya ɗan jinjina kai, yana magana cikin murya mai ƙarfi amma ba da ihu ba “Samuel, wannan aikin bana so a yi shi da wasa. Ina so ka shigar da wannan kwayar cikin kayan As’ad… yadda zai ɗauka babu hatsari. Ba na son shakku ko alamar komai. Na fi son a yi shi da hikima… ka san ni bana son yin abu da zai ja min magana kuma kasan hatsarin da as'ad yake dashi.”
Samuel ya ɗan matsa kusa da teburin, yana ɗora ƙafarsa ɗaya saman kujera “Oga, idan game da wannan aikin ne, ka barshi a hannuna. Zan saka mutanenmu a wajen da ake haɗa container din . Za a saka kwayar a tsakiyar kayayyakin, sannan mu tabbata an samu hotuna da videos. Bayan haka… duniya ta gama gane shi a matsayin wanda ke cutar al ‘umma.”