Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 4
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 4: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 4. Alhaji Mukaddam ya ɗan murmusa, yana zuba cream a cikin coffee
4,491 words
Alhaji Mukaddam ya ɗan murmusa, yana zuba cream a cikin coffee
“Shi As’ad yana ganin kansa ya wuce kowa a kasuwanci. Yana kawo min cikas a wasu harkoki da suka kamata su rufe min kasuwa. Wannan dama ce ta rusa shi daga tushe… ba sai na shiga gaban kotu ko gasa da shi a kasuwa ba. Wannan shi ne wasa da hankali, Samuel, ba da makami ba.”
Samuel ya ɗaga kai yana murmushin mugunta
“Na fahimta oga. Idan na gama, kowa zai ɗauka As’ad ya lalata kansa da kansa. Za ka zauna ka sha iska ka kalle shi yana faɗuwa daga sama… ba tare da ka motsa yatsa ba.”
Alhaji Mukaddam ya ɗauki briefcase ɗin kuɗi daga ƙasan tebur ya miƙa masa
“Ga ₦10 million. Ka yi amfani da shi don ganin komai ya tafi daidai. Ba na son wata gaggawa mara tsari ka yi abu cikin natsuwa, kamar yadda muke yi a harkokinmu.”
Samuel ya karɓa yana dariya
“Oga, wannan aikin ka ɗauka an gama. Zan yi shi da tsabta, babu wata shaida, babu wani da zai danganta da kai.”
Alhaji Mukaddam ya miƙe daga kujerarsa, yana kallon waje ta bangon gilashi
“As’ad… kai dai kana ganin kana kan sama. Amma a kasuwanci, wanda yake ƙasa yana iya janyo wanda yake sama ya faɗo, idan yana da isasshen kuɗi da hankali.”
*****
Ayshatu ta ɗan lumshe ido tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, zuciyarta na ta harbawa da hanzari. Duk da fushin da ke ranta, ta danne komai ta tashi da nufin aiwatar da abin da zuciyarta ta ɗauka. Da natsuwa ta shiga bathroom ta yi wanka mai ɗauke da ƙamshin turaren rose water, ta shafa body oil mai ɗanɗanon vanilla, jikinta na sheƙi tamkar an shafa masa zinariya.
Ta fito ta ɗauko wasu fitinannun kayan bacci masu laushi irin na silk masu launin emerald green da suka amsa launin fatarta, sannan ta zuba turaren Baccarat Rouge da ƙamshinsa ke dawwama. A hankali ta ɗora abaya mai launin ruwan toka wacce ta yi mata kyau fiye da yadda ta zata, sannan ta ɗauki golden clutch a hannunta.
Daidai lokacin agogon bango na falonta ya nuna ƙarfe 12:55 na dare. Ta san idan ta je yanzu, As’ad zai kasance yana cikin lokacin da yake mafi yawan natsuwa.
Ko da ta isa ƙofar babban bangaren As’ad, ta san idan ta bi hanyar babban falon za a iya tsayar da ita da masu tsaro. Don haka, ba tare da wata jinkiri ba, ta bi ƙofar sirri da ke haɗa ɓangarorinsu guda biyu.
Ta shiga cikin babban palon sirrin As’ad wani falo mai faɗi sosai, bangon gilashi yana nuna hasken dare daga cikin gidan mai manyan fitilu na zinariya, kafet ɗin Persian mai launin ja da zinariya yana shimfiɗe ƙasa, ƙamshin oud da sandalwood na yawo a iska. Amma babu kowa a ciki, sai shiru mai cike da izza da tsari.
Ayshatu ta ɗan lumshe ido tana shakar ƙamshin, sannan ta ɗaga kayan abayarta ta fara hawa spiral staircase zuwa bene na sama.
Da ta ƙarasa, ta ji muryar addu’a daga ɗayan ɗakunan muryar As’ad. Ta tsaya cak a bakin ƙofa tana kallon sa… yana tsaye a kan dadduma mai launin ruwan sama, ya na sallah cikin nutsuwa, fitilar ɗakin mai ɗan duhu ta haskaka ƙirar jikinsa. Tsarin sa da kyan halitta sun haɗu tamkar an ƙera shi da hannu.
Ayshatu ta daɗe rabonta da ganin shi cikin irin wannan tsantsar ibada, har sai ta manta cewa wannan ma As’ad ɗin ne mai kyan fuska da salo, wanda a yau ke tsaye yana roƙon Ubangiji. Wannan yanayin ya girgiza zuciyarta fiye da yadda ta zata.
Ta shiga ɗakin a hankali, ta cire abayarta ta ajiye a gefen kujera, tana barin kayan baccin silk ɗinta su bayyana. Sai ta zauna gefen gadon king size mai lulluɓe da farin zanen Egyptian cotton, sannan ta kwanta a kanta, tana jiran lokacin da zai kammala sallarsa.
Bacci yana ƙoƙarin ɗaukarta, zuciyarta kuma tana sake tunanin duk yadda kyan As’ad ya kasance irin kyan nan da yake haɗa kyakkyawan sura na Allah da kuma ganiyar kulawa ta masu kuɗi.
As’ad bai kalli inda Ayshatu take kwance ba, ya nufi babban bathroom ɗinsa mai bango fari, bene mai sheƙi kamar madubi, fitilu masu sanyi suna walƙiya daga saman chandelier ɗin da aka kawo daga Italy.
Cikin ‘yan mintuna ya fito, jikinsa fes da ruwa, white Egyptian towel ɗaura a kugunsa. Ya tsaya gaban madubin bango mai fadin kusan rabin ɗakin, gefen madubin an jera kwalaben turare masu tsadar gaske Clive Christian No.1, Roja Dove, Creed Aventus waɗanda farashinsu kaɗai zai iya siyan gida a cikin birnin.
Ya ɗauki sure mai ɗauke da ɗan ƙaramin zoben zinariya a murfin sa, ya shafa a jikinsa cikin natsuwa kamar wanda yake da lokaci mai tsawo. Ƙamshin oud da saffron ya gauraye cikin ɗakin, yana haɗuwa da sanyi mai fita daga air condition na musamman.
Daga gefe, tagogin gilashi masu tsayin sama da mutum biyu suna kallon waje, inda ake iya ganin hasken birnin yana kyalli kamar taurari a ƙasa. Daga can ana iya hangen rukunin motocin As’ad Rolls Royce Phantom, Bentley Mulsanne, kowacce na sheƙa a ƙarƙashin hasken wuta.
Kafin ya saka rigarsa ta silk da aka yi masa musamman daga Paris, Ayshatu wacce zuciyarta ke tafarfasa ta tashi daga kan gadon, wanda kansa aka lulluɓe da headboard na zinariya mai sassaƙen royal emblem. Ta iso gare shi a hankali, ta rungume shi daga baya, tana jin zafin jikinsa da ƙamshin turarensa sun yi mata wani irin shigar zuciya.
"Dan Allah… dan Allah jarumina, Habibie na…" ta fara magana da muryar da ke da sanyi, tana ƙara matsowa kusa da shi.
"Ka yi hakuri… am sorry. Na yi kuskure… amma fushinka bana iya ɗauka, As’ad."
Ta ɗaga kanta, idonta cike da hawaye.
"Please… am sorry babyna. Ka yafe min."
Amma As’ad ɗan sarki, mai daraja, wanda kalmar sa take da nauyi fiye da zinariya bai yi saurin amsawa ba. Fuskar sa cike da izza, idanunsa suna kallonta kamar suna karanta ranta. A hankali ya ja hannunsa daga nata, yana tafiya zuwa babban gadonsa na king size, wanda zanen silk duvet ɗin shi kaɗai farashinsa ya kai sama da dubban kuɗaɗe.
Ayshatu ta biyo shi cikin rawar murya, ta riƙo hannunsa, tana jin idan ta bari ya kwanta haka, zuciyarsa ba za ta huce ba. Amma ko a wannan yanayin, iko da mulkin sa sun fito fili ba kawai saboda shi ɗan sarki ne ba, amma saboda shi mutum ne da idan ya so, zai iya mayar da rayuwar mace aljanna ko wuta cikin dare ɗaya.
Ayshatu ta matsa kusa da shi, idonta cike da hawaye, muryarta tana rawa.
"Nasan na yi kuskure… nasan ban kyauta ba… please Habibie…"
Kafin ya ce komai, ta kwanta a ƙirjinsa, ta ɗora kanta saman ƙafadar sa kamar yarinya tana neman kariya daga maigida. Hannunta ya hau wuyansa a hankali, sannan ta ɗora bakinta cikin nasa wani sumbata mai cike da nadama da roƙo.
As’ad wanda zuciyarsa a lokacin take cike da tunani mai nauyi ya sauke wata ajiyar zuciya mai zurfi, ƙamshin oud ɗinsa ya gauraye da nata perfume mai daɗin ƙanshi. Sanyi ya ratsa shi kamar an zuba masa ruwan sanyi a zuciya, nauyin fushinsa ya fara raguwa, amma har yanzu izzar sa ta fito fili.
Cikin murya mai rauni amma tana da ƙarfin iko, ya ce mata
"Ayshatu… kina wasa da zuciyata, kina wasa da amana…"
Sai ta ɗago da idanunta, ta runtse su a hankali, muryarta ta koma kamar mai rarrashi
"Please… romance me, Habibie…"
As’ad ya tsaya kallonta na ɗan lokaci kallon ɗan sarki wanda idanunsa ke iya yanke hukunci kafin harshe ya furta shi. Sannan ya kama hannunta da natsuwa, ya ja ta zuwa gefen babban gadon royal bed ɗinsa wanda aka lullube da zanen silk mai launin zinariya. Fitilar chandelier da ke sama ta haska launin fatare tasu kamar madubi mai walƙiya.
Ya zaunar da ita a hankali, hannunsa na shafa bayanta, amma har yanzu kallonsa na nuna shi ne mai iko a wannan lokaci, ba ita ba.
"Ki sani, Ayshatu… soyayyata tana da daraja. Ba kowace mace ce ke samun taba."
Kalmarsa ta ƙarshe ta faɗi kamar satar zuciya, sannan ya matsa kusa da ita, hannunsa ya tafi ƙasan ƙugunta, yana jawo ta kusa da shi. Kallon shi ya cika da haɗin kauna, izza, da mulki, irin na ɗan sarki wanda komai nasa na musamman ne har ma da yadda yake nuna soyayya.
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
Nana hadiza
09030569336
[20/08, 9:32 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA GOMA
Ayshatu ta zuba masa ido tana kallonsa kamar macijiya da ta hango ganima. Zuciyarta na bugawa, amma duk da haka ta lumshe idanu tana mayar da murya cikin salo.
“Habibie… ka yafemun. Don Allah, kar fushin ka ya hau kaina. My love… ni nake roƙonka, ka rungumeni… kayi romancing dina.”
As’ad, wanda ke zaune gefan gado mai faɗin gaske, ya kalleta da idanun da suka haɗa tsananin iko. Ya matso a hankali, yana tafiya kamar wanda yake da dokin zuciya amma yana iya sarrafa shi salon da yake sa zuciyar mace ta narke. Ya tsaya gabanta, ya zare hannuwansa ya riƙe fuskarta cikin natsuwa. Idanunsa sun yi zurfi cikin nata, yana kallon ta kamar yana karanta littafin da babu wanda ya taba buɗewa sai shi.
A hankali ya ja numfashi ya sauke, yana jin duk wani ƙunci ya fara raguwa.
“Ayshatu…” ya kira sunanta cikin sautin da ya kama tsakanin umarni da salo.
Hannunsa daya ya zame zuwa bayanta, ya rungume ta sosai, ya ɗora goshinsa akan nata.
A hankali, ya fara sarrafa jikinta da salon da kowa zai gane ba namiji talaka bane kowane motsi yana da daraja, yana da natsuwa, kamar yadda ya koya daga rayuwar manya masu mulki. Yatsunsa suna tafiya a hankali a bayan wuyanta zuwa ƙasan bayanta, yana jin yadda jikinta ke amsawa cikin nutsuwa.
Ayshatu kuwa ta rasa natsuwa, zuciyarta na bugawa kamar ganga, ta rufe idanunta tana shakar ƙamshin jikinsa da kamshin gadon zinariya da yake ɗauke da shi. Gadon kuwa an lullube shi da zanen siliki mai kauri, launin fari da ja, fitilun gefen gado suna bayar da wani laushi na haske da ke ƙara sa komai ya zama romantic sosai.
“Habibie… kai kaɗai ne zan iya bari ka mallake ni haka,” ta furta cikin rauni, tana kama hannunsa da ke kan bayanta, tana matsa jikinta ƙara kusanci da shi.
As’ad ya murmusa a hankali, murmushin wanda ya san ikon sa a kan mace. Ya ɗan ɗaga ta kaɗan, ya zaunar da ita a gefen gadon kamar sarauta ce ta dawo wurin da ta dace. Sannan ya ci gaba da sarrafa jikinta cikin natsuwa, kamar yana tsara kowanne motsi don ya tabbatar ta manta duk wata damuwa ko zargi da yake zuciyarta.
Ayshatu tana kwance a gefen gadon, tana jin nauyin sarrafawar jikinta da ya fara shigar mata a hankali. Duk haushin da ta ji a ranta saboda yadda yake tafiyar da lamarin da kansa, ba tare da bin layin da take so ba, sai jikinta ya fara amsawa da sanyi. Ta runtse ido, ta furta a hankali, muryarta tana rawa
"Habibiee, ba zan taɓa cin amanarka ba har abada. Zan kasance mai biyayya gare ka… nakasarka bakomai bace a gare ni. Domin ada, kai ne kake faranta min a kan gado… har yanzu kai ne masoyin zuciyata."
As’ad ya tsaya yana kallonta, idanuwansa sun yi zurfi kamar yana duban ƙasan zuciyarta. Ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarsa ta fito da ƙarfin namijin zaki, tana da tsantsar gaskiya da izza
"Ayshatu… kidaina wasa da zuciya ta. Kidaina, please. Ina miki wani irin so da ba zan iya fassara shi ba. Amma wannan canjawarki a kaina wallahi kamar ɗandanawar azaba ce a raina. Na roƙe ki da girman Allah, idan har ba za ki iya zama da ni ba… idan har ina cutar miki, Ayshatu… to kiyi haƙuri mu rabu tun kafin mu cinye juna. Duk da soyayyar da ke tsakaninmu, nasan yanzu… ba ni da ƙarfin da nake da shi a baya."
Ya ɗan ja numfashi, ya ɗauke kallonsa daga idonta na ɗan lokaci, sannan ya sake dubanta da tsantsar damuwa da aminci "Na san… yanzu ban kasance cikakken namiji ba. Na san… gabana baya aiki kamar da. Na san kinada lafiya sosai, kinada ƙarfi, kinada sha’awa… kuma ba kullum zan iya gamsar da ke ahaka ba. Amma Ayshatu, ina so ki sani… ba ƙasawa nake yi don raina ki ba zuciyata tana tare dake, ko jikina ya kasa."
Ya matsa kusa da ita, yana sanya hannunsa a kan kuncinta cikin salo wanda baya buƙatar hayaniya domin nuna iko. Idanunsa suna da wani irin natsuwa.
"Idan so kike mu nema magani, Na kashe dukiya ta… idan so kike mu bi duniya neman mafita, zan rufe duniya domin ke. Amma kiyi haƙuri… ki kasance min tsintacciya ba mai jefa ni cikin ƙarin zargi ba."
Cikin ranta Ayshatu tana zagin As’ad, tana jin tsantsar takaici kamar ta ce masa duk abin da zuciyarta ke ɓoye. Amma a fuskarta kuwa, kyakyawan murmushi ne mai ɗan ɗanƙon hawaye, cikin bariki da siyasa.
Tana jan numfashi a hankali ta fashe da kuka mai sauti, tana ɗan bubbuga kirjin As’ad wanda ya sha kaya masu tsada da ƙamshin Oud Royal. "No… a’a, Habibiee… bana son wannan maganar, wallahi bana so. Yaranmu biyu dakai, mun daɗe tare… bana son rabuwa da kai. Zan rayu har na mutu tare da kai. Weakness ɗinka? Ba komai ba ne a wurina. Dan Allah kada ka sake mun irin wannan maganar, tana saka ni cikin damuwa.
Habibiee, ni ina son ka a yadda kake yanzu, kuma ba ka cutar da ni. Sha’awa? Ni ban da ita yanzu… so na kawai nake ji."
As’ad ya yi murmushi mai ɗan nauyi, ya ja ta zuwa jikinsa cikin salo na soyayya yana rufe ta da hannayensa kamar yana kare wani zinariya mai daraja. Yana jin zafin kalamanta, amma a ganinsa kalaman gaskiya ne suka fito daga zuciyarta.
Ayshatu kuwa, duk da irin rungumar da ta ji, zuciyarta ta ƙara cika da haushi. Tana ji a ranta "Inama Alhaji Muqaddam ne yake kusa da ni yanzu… namiji mai cika duk buƙata, mai ɗaukar mace kamar sarauniya… ba irin wannan namiji da bashida karfin gaba bashida mamaro ko kadan sai dai ma ya riketata kawai."
Sai kawai ta ƙara lumshe ido, ta sanya kanta ƙirjinsa, tana kwaikwayon mace mai natsuwa, amma zuciyarta tana tafasa da mugun tunani.
****
Washegari, gari bai gama wayewa ba aka riga aka shiga cikin wani irin yanayi na shirye-shiryen biki da kowa a gidan mai martaba ke ji a zuciya. Ba wani maganar kuɗi ake yi ba, domin an san idan As’ad ya ce biki, to kuwa kudi zai nuna ƙansa sosai da sosai dan kuwa mai ƙudin da kasarsa take alfahari dashi ne kuma wanda duniya ma tasansa to kuwa komai zai kasance cikin alfahari, kyan gani, da izza ta masarauta.
Ana ta shirin manyan abubuwan da suka haɗa da event guda biyar uku a nan ƙasar, biyu kuma a waje. A nan gida, za a yi taro a babban masarautar Kano, wani a Abuja, sannan wani exclusive dinner a Legas. Sauran biyun kuwa a wajen ƙasa ne, babban ɗaurin aure a cikin masarauta tare da manyan baki daga ko’ina cikin duniya.
Duk inda za a gudanar da taro, ana tura ƙungiyoyin masu shirya abubuwan alfarma daga manyan event planners na ƙasar zuwa fitattun masu kawata wurare daga ƙasashen waje.
A gidan mai martaba kuwa, fitowar manyan motocin Rolls-Royce Phantom, Bentley Mulsanne, da Maybach ta cika harabar. Fitattun masu rike da sarauta, manyan ‘yan kasuwa, da VIP guests na duniya sun fara sauka. Babban ɗan As’ad, Umar, ya sauka da matarsa mai kyan hali tare da ‘ya’yansu guda uku, duk cikin shigar da ke bayyana matsayin royal family.
Harabar gidan ta cika da ƙamshin Oud da Ambergris, tare da sautin kidan gargajiya da na zamani suna haɗuwa cikin natsuwa. Ma’aikata cikin shigar masarauta ke yi wa baki tarba da lemo masu tsada da kayan marmari.
A ɓangaren mata kuwa, zoben lu’ulu’u, kayan ado na zinari, da silk sun mamaye ɗakin shan shayi. An fara tattaunawa kan guest list, menu, da kuma kyaututtukan da za a rabawa baki a kowane taron.
Uwargida Hauwah, matar farko a gidan mai martaba, tana zaune a cikin babban royal sitting room ɗinta wani falo mai yalwa, an kawata shi da Persian rugs, kujerun velvet masu zare na zinariya, da fitilu masu sheƙi daga Swarovski. Kamshin oud da bakhoor na musamman ya lullube dakin, yana ƙara masa kamshin alfarma.
A gefe, baiwar amintacciyarta, Halima, na zaune a ƙasa da ladabi tana yi mata gulma cikin muryar da take nuna tsoron abin da ta ke faɗa.
“Ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya,” Halima ta fara, tana ɗan sunkuyar da kanta. “Game da umarninki na a saka maganin nan ashashen As’ad cikin shirinmu… wallahi duk wata dabararmu ta kasa. Tsaro a bangaren nasa yana nan 24 hours, babu mai shiga babu mai fita sai da izini.”
Hauwah ta kalleta da idanun da suka cika da ƙyamar abin da ta ji, tana tura numfashi da karfi.
“Tsaro kika ce?” ta maimaita, tana jin zafin kalmar a kunnuwanta. “Kin san wacece ni kuwa, Halima? Ni ce uwa a wannan gida, ni ce ginshiƙin mulkin nan, amma wannan yaro ya zama min ciwon ido! Tsaro?
Tace ranki yadade Wallahi ko matarsa ce, sarkin ƙofa ya ce bai ga ta shiga ba har yanzu.”
Ta miƙe tsaye, ta fara tafiya cikin dakin, ƙafafuwanta suna bugawa a marble floor mai santsi.
“Halima,” ta ci gaba, muryarta na nuna haɗuwar takaici da ƙuduri, “na rasa yadda zan kassara shi. Na rasa yadda zan salwantar da shi daga wannan gidan. Idan ban gama aikin nan ba, bokana ya ce dole in manta da ganin duk wani nasara ta a rayuwa.”
Ta tsaya a tsakiyar dakin, ta juyo da kallon da yake cike da makirci.
“Idan bokana ya tabbatar min cewa nasarar wannan yaro ita ce tushen hasken gidan nan, to wallahi wannan haske zan kashe shi da kaina… da hannuna… ko da kuwa zan dauki matakin da zai girgiza sarautar nan.”
Halima ta sunkuyar da kai, zuciyarta na bugawa, tana jin nauyin shaidar da ta bayar. Amma a zuciyarta ta san wannan magana bata tsaya kan raini ba akwai wani babban abu da uwargida Hauwah ke shirin yi, abu da zai iya sauya tsarin gidan sarautar gaba ɗaya.
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
Nana hadiza
09030569336
[21/08, 10:38 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SHA DAYA
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Sashen Hajja mahaifiyar As’ad ya cika da jama’a. Dangin sarauta da ‘yan uwa daga ko’ina suka hallara, kowanne cikin shigar da ta dace da matsayin gidan mai martaba.
Kamshin turaren da aka kunna a oud burner ya lullube ko’ina, yana haɗuwa da ƙamshin fresh roses da aka yi wa falon ado, ya sa dakin ya cika da wani irin yanayi na alfahari da daraja. A gefe, mawaƙa na mata suna rera wakokin aure na gargajiya cikin muryar da ke motsa zuciya, ana busa algaita da gangar aure.
Hawaye da dariya suka gauraya a tsakanin ‘yan uwa, kasancewar yanzun nan aka gama daura auren Nawal. A gefe guda, ana bushe-bushe na farin ciki, ana yi mata addu’o’in samun zaman lafiya da albarka.
Nawal ta shigo sanye da shigar Hausa-Fulani ta alfarma zani na indigo mai zane-zanen gold embroidery, blouse ɗin da aka yi masa aiki da zaren azurfa, da mayafi mai launin royal blue da aka ɗora a kan kanta cikin salo. Zinare ya lullube hannunta da wuyanta, daga golden bangles har zuwa long necklace mai kyalli.
A bayanta, ‘yan uwanta mata suna tare da ita, kowacce cikin shigar da ta nuna asalin sarautarsu. Fuskar Nawal ta cika da annuri, kwalliyarta ta yi dai-dai da matsayin matar da za ta zauna a gidan mai kuɗi da sarauta.
Sai ga mijinta ya shigo cikin doguwar farar babban riga ta zare, da red cap na alfarma, kyawunsa da tsayinsa sun sa kowa ya ɗan tsaya yana kallonsa. Ya ƙarasa gare ta, suka yi murmushi mai cike da alamar fahimta a tsakaninsu, sannan suka tsaya tare aka yi musu hotuna na royal couple da za su yi armashi a duk fadin gari.
A wannan lokacin, kowa na cikin fargabar ganin irin kasaitaccen biki da za a ci gaba da yi domin an riga an shirya events guda biyar uku anan cikin gida, biyu kuma a Abuja, sannan da taron musamman a Dubai, inda Nawal za ta fara rayuwarta ta aure a can.
Tunda daga nesa, Nawal ta hango Umar babban yayanta, wanda ya taso musu matsayin uba da uwa a lokaci guda. Fuskar ta cika da farin ciki, ta yi gudu cikin sauri har ta faɗa jikinsa tana rungume shi da ƙarfi, kamar yarinya ƙarama.
“Papa!” ta furta cikin muryar soyayya. “Yaushe kuka iso?”
Ya yi murmushi, yana ɗan ja mata hancinta cikin shagwaɓa.
“Dazu muka shigo, princess,” ya amsa a cikin yaren Turanci, muryarsa cike da ƙauna. “Sannu ku da zuwa. Bari na wuce gurin su Nazrah in gaishe su.”
Sai kuma ya kama hannunta cikin tsananin kulawa, yana kallon idonta
“Ki kula da kanki sosai, kinji? Duk wanda zai taɓa ki, ko ya kawo miki abu koda ruwan sha ne ki tabbatar kin san shi sosai kafin ki ɗauka. Kin fahimta?”
Nawal ta yi dariya mai sauƙi, tana ɗaga kai.
“Tohm, Papa.”
Amma sai ya sake jaddada mata maganar da ɗan kakkausar murya.
“Ki tuna da maganata, Nawal. Wannan gidan, rigimarsu sai su. Don haka ki kiyaye kanki sosai.”
Ta sake murmushi cikin ladabi, tana tabbatar masa da cewa zata kula, hakan yasa ya saki hannunta ya tafi.
A gefe guda kuma, Ayshatu tana can a babban royal hall na fadar, tana kula da al’amuran hidimar biki. A yau, ta zama tamkar zinariya a tsakiyar zinariya kamshinta, kwalliyarta, da yadda take tafiya cikin nutsuwa sun sa kowa ya sake kallonta sau biyu.
Daga cikin ‘ya’yan gidan mai martaba, babu wanda ke da daraja da daukaka a cikin jama’a irin ta Ayshatu. Uwargida tana yi mata kallon girmamawa, ‘yan uwan mijinta suna yi mata koyi, ma’aikata kuma suna ta faman hidima gare ta kamar sarauniya.
A cikin zuciyarta, Ayshatu ta san wannan matsayi nata ne zai iya ja mata kishiya ko abokin gaba idan bata taka tsantsan ba. Don haka, ta ɗora murmushi a fuska, amma cikin zuciya ta ƙuduri cewa dole ta ƙara kulawa sosai, ta rike martabarta da takunta sosai yanzu ne ma zata zauna da As’ad dan ta tabbatar mijin nata zaki ne kuma billionaire ne.
Haneefah ta yi kuka kamar zuciyarta za ta fito, idanuwanta sun kumbura, kumatunta sun yi ja. Tana zaune gefen gado, hannunta rike da zani tana share hawayenta. Sai jin ƙarar ƙofa ta banko, yayarta ta shigo cikin hanzari, kamar wacce aka kira domin ceton rai.
Ta ƙarasa gare ta da sauri, ta kama hannunta cikin kulawa.
“Haneefah, lafiya? Menene yake faruwa?”
Cikin rawar murya, Haneefah ta ce
“Yaya… wallahi inason As’ad. Ina jin shi har cikin ƙashi na. Zan koma gare shi, koda kuwa bashida kuzarin biyan bukatata. Yaya, zuciyata tana mani zafi. Na je wurin Mama, nace mata zan koma, amma tace in na sake zance, sai ta zanine.”
Yayarta ta tsaya tana kallonta cikin mamaki, idonta cike da tambayoyi.
“Haneefah, ki rufawa kanki asiri ki bar wannan maganar. Kinsan ko Mai Martaba kansa bazai yarda ba. Ke da kanki kika roki a raba ku.”
“To yaya, yanzu me zanyi? Me zanyi?” Haneefah ta sake maimaitawa, kuka na neman karya muryarta. “Dazu na ganshi a sama suna daukar hoto da matarsa… kamar na mutu saboda son da nake masa.”
Yayarta ta girgiza kai cikin tausayi.
“Nidai shawara ta gare ki, ki yi ta addu’a har Allah ya cire miki sonsa. Kin san daman na gaya miki, biyewa Mama da shiga gurin bokaye ba alheri bane. Watarana zatazo, sai kinyi kuka da idonki.”
Ta kalli Haneefah da kalar tausayi
“Gashi yanzu, cikin maza biyar da kika aura, ga guda daya nan da soyayyarsa ta koma wahala a gare ki duk da irin bata masa suna da kika yi. Yanzu, ke baki ga anty Ayshatu ba? Bata burge ki? Kin ga yadda kowa ya maidata kwal a gidan nan saboda mijinta koda kuwa shi ba cikakken namiji bane ya fiki daraja yanzu auren ne dake? . Kin ga yaransa yadda suke, kamar ka ga yaran turawa.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana jan numfashi.
“Ni ma, da ace Umar zai yarda ya aureni, da nayi murna. Amma nasan mugun halin uwata da irin yadda suka san halinta bama umar ba zai taba kulani ba.”
“Kitashi ki wanke fuskarki, ki shiga a yi hotuna da ke.” Yayarta ta ce da murya mai sanyi. “Kiyi hakuri, shine abunda zan iya gaya miki. Zama kina kukan Yarima ba zai miki alheri ba. Ki shiga cikinsu, kema ayi bikin da ke a cikin hoton.”
Haneefah ta share hawayenta da bayan tafin hannunta, tana jin nauyin zuciya, amma maganar yayarta ta yi tasiri a kanta. Tana cikin jin haushin kaddararta, amma ta tashi, ta nufi bandaki.
A hankali ta wanke fuskarta da ruwan sanyi, ta goge da tawul mai laushi, ta sa ruwan turare mai kamshin da zai iya jawo hankali daga nisan ƙofa. Ta zabi wani fitted gown ja mai haske, wanda ya bayyana ƙirarta cikin kalar sarauta, ya bayyana siririyar kugunta, ya kuma dace da launin fatarta. Tayi kwalliya sosai launin jan baki da shimmer eyeshadow wanda ke kama hasken fitila, har sai da ta kalli kanta a madubi ta ji kamar mafarin shirin mata manyan kuɗi na Netflix.
Sai ta ɗauki wayarta a hannu, ta fito daga sashenta tana tafiya da salon mace mai cikakken kwarin gwiwa, tana jan numfashi daidai da tafiyarta.
A zuciyarta kuwa, ba wai son hotuna ne yasa ta shirya haka ba, son ganin As’ad ne yasa ta yi wannan shirin. Ta ɗauki matakin da zata iya don aƙalla idan taga shi, ya hango kyawunta ya tuna irin tsohuwar soyayyar da ta taɓa ratsa tsakanin su.
Kafin ta isa bangaren Hajja, sai ta ci karo da Mama a tsakar gida. Mama ta tsaya, ta zuba mata ido tun daga ƙasa har sama.