Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 5

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 5

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 5: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 5. “Ina zaki haka, Haneefa?” Ta tambaya da kalar murya mai kwaikwayon…

4,497 words

“Ina zaki haka, Haneefa?” Ta tambaya da kalar murya mai kwaikwayon kulawa amma da ƙunshe da wata dabara.

Haneefah ta bata amsa cikin ɗan haushi amma da murmushi a fuskarta

“Gurin su Nawal zan je mana.”

“Yauwa, to.” Mama ta ce, tana matsowa kusa. Ta saka hannu cikin jakarta ta fito da wata ƙaramar kwalban mai kamar turare . “Karbi wannan ki shafa mata a jikinta, kinji? Zai yi miki kyau sosai.”

Haneefah ta kalli kwalbar, zuciyarta ta buga. Duk da cewa bata da tabbacin abun, tana da kyakkyawar fahimtar muguwar siyasar uwar.

“Mama…” Ta fara cewa da shakku.

“Karbi mana, kiyi mata amfani dashi mana.” Mama ta dage.

Haneefah ta karba a hankali, ta ce, “To.” Amma zuciyarta na cewa wallahi ba zan saka mata ba.

Sai da ta bari Mama ta juya ta nufi hanyar sashenta, sannan Haneefah ta yi saurin komawa bakin dustbin dake gefe, ta cilla kwalbar tana furtawa cikin ƙasa-ƙasa

“Allah wadai da mugun hali irin na uwata mai haɗa yaranta cikin sharri.”

Ta ja tsaki, ta ci gaba da tafiya, zuciyarta na ƙara harbawa da niyyar ganin As’ad a yau ko da da sunan hoton biki ne.

Tana yin sallama, ƙofar royal wing ta buɗu da ƙara mai sanyi, wata baiwa cikin riga mai ɗauke da tambarin gidan sarauta ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa ta ce,

“Maraba da Haneefah, ranki ya daɗe.”

Tana shiga, iska mai ɗauke da ƙamshin oud, amber, da sandalwood ya daki hancinta. Falon ya cika da walƙiya fitilun chandelier masu siffar lu’ulu’u suna haskakawa sama da kan zinariya mai sheƙi. A gefe guda, ƙafafun kujerun fata na musamman suna sheƙa haske, ƙasa kuwa an shimfiɗa Persian rug mai ƙirar musamman daga Iran.

Cikin tsakar falon, ‘yan uwa da dangin mai martaba suna ta bushe-bushe, murmushi da gaisuwa na ta yawo, ana ɗaukar hotuna da cameras masu ruwan zinariya. Angwaye cikin shigar alfarma, iyayen ango cikin kayan gargajiya masu walƙiya.

Haneefah ta zuba ido, zuciyarta na bugawa kamar ana busa gangar fada. Idonta ya sauka a can gaban babban falon As’ad, ɗan sarki, cikin custom-made royal agbada mai launin farin zinariya da dinkin Italian gold embroidery, hannunsa ɗauke da cane na sarauta da aka haɗa da platinum. Fuskarsa cike da izza, murmushinsa kuwa na da wani irin sanyi mai haɗa zafi murmushin wanda ya saba da samun duk abin da yake so.

Zuciyar Haneefah tayu wani narkewa, hannayenta suka yi sanyi. Rabon da na tsaya haka kusa da shi... na manta.

Amma shi ko inda take bai kalla ba.

Ayshatu kuwa da ta fi kowa daukaka a wajen dangin mai martaba ta tsaya kusa da shi cikin gown mai launin champagne da aka yi masa ado da Swarovski crystals, hannunta a kafaɗarsa, murmushi na soyayya a fuska.

Ta ce cikin muryar da duk suka ji

“A’a, Haneefah! Zo mana, ayi hotunan dake!”

Kafin Haneefah ta iya cewa komai, Amina ta taho da gudu, ta kama hannunta, tana ji kamar zata ja ta a hanzari.

“Zo ki shiga, kiyi hoton zumunci!”

Amma zuciyar Haneefah tana ƙuna. Idonta na satar kallon As’ad, amma har yanzu bai ma motsa kai ya kalle ta ba.

Sai Ayshatu ta matsa gaba, ta rungume As’ad da cikakkiyar nutsuwa , ta ɗan jingina kanta a kansa, kyamarori suka ɗauki hoton walƙiya ta haska fuskokinsu, ta kuma ƙona zuciyar Haneefah da kishi.

A zuciyarta, Haneefah ta ji tamkar an cusa mata wuka mai sanyi, wadda take huda zuciya a hankali tana barin ciwo mai ɗaci. Duk da haka, ta ɗan murmusa cikin dole, tana kokarin ɓoye rawar zuciyarta, amma idonta ya kasa sauka daga kan As’ad ta ɗan matsa gaba, zuciyarta cike da begen cewa aƙalla sai ta tsaya a kusa da shi a hoton, koda kuwa bai kalle ni ba.

Amma kafin ta iso gaban kyamarorin, Ayshatu ta yi wani ɗan murmushi mai ɗauke da zaki da zafi a lokaci guda, ta kamo hannun Amina tana faɗin

“Amina, zo mu fara hotonmu na mata uku na gidan nan, kamin sauran su shigo.”

Amina ta amsa da,

Sai Ayshatu ta matsa kusa da As’ad, ta ɗan juya jikinta ta rufe ƙaramin sararin da Haneefah zata iya shiga, tana ci gaba da zuba murmushin da kamarar ta ke.

Nana hadiza

09030569336

[21/08, 10:39 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SHA BIYU

Duk yadda aka yi da Abba a daren nan akan ya tafi gida ya huta, sai ya girgiza kai cikin ladabi ya ce, “Ku tafi kawai, zan kwana tare da ita.”

Wannan maganar tasa ta cika zuciyata da wani irin dadi da ba zan iya fassara shi ba. Amma a gefe guda na lura da yadda hakan bai yi wa mumy ba ko kaɗan Dr. Maryam dadi taji, domin itama ranar tanada wani aiki awani asubutin. Duk motsina a gadon, idanunsa suna kan nawa. Shi ma ba cikakken lafiya yake ba, amma hakan bai hana shi kulawa da ni ba.

Har alwalar sallar dare shi ne ya yi min da kansa. Bayan haka, ya cire min ledar fitsarin da aka rataya, ya rage min fitsarin da hannunsa cikin kulawa. Ya bani abincin da Yaya Abbas ya kawo, ya tabbatar na ci kadan-kadan. Daga nan ya bani magunguna, sannan sai da nurse ta shigo ta yi min allura kafin na samu bacci.

Cikin dare na sake farkawa, sai na same shi yana nan a kujerar, hannunsa har yanzu cikin nawa, yana shafa min yatsa da natsuwa. Idanunsa sun nuna gajiya, amma a cikin su akwai irin wancan kulawar da ban taba gani ba. A zuciyata na ce Allah na, me yasa ma duk irin kuncin da nake ciki yanzu, ina jin kamar ina cikin aminci idan yana kusa?

Hawayena suka cicciko, ba saboda ciwo ba, amma saboda jin dadi da mamakin irin kulawar da yake nuna min. Duk yadda na so na tuna bakin cikin da nake ciki a baya cin zarafi, azaba, da kunci sai kawai na kasa. Soyayyar da yake nuna min ta mamaye zuciyata ta hana ni tuna munanan abubuwa.

Washegari da sassafe sai ga Mumy ta shigo da tray, ta ajiye kan karamar tebura. A ciki akwai tea mai kauri, kwai da aka soyawa, da bread Da murmushi mai sanyi ta ce,

“Abban Ramlah, ka tashi mu koma gida. Za mu nemi mai kula da ita a gida ko amma bai kamata ace kai kana kwana da'ita ba ga aikinka ga kuma yanayin jikinka.”

Abba ya kalleta yama kasa magana, sai kawai ya daga gira cikin mamaki.

Mumy ta kara cewa “Ni gaskiya ba zan iya kula da ita ba. Kai ma ka san ba lafiya ce ta isheni. Kuma ma, ka tabbata ba wannan yarinyar ce ta kashe yaron nan ba? Ni fa ban yarda da ita ba, asararriyar yarinya ce kawai tunda har yanzu danginsa basu zo ba.”

Kafin ta karasa, sai kawai na ji karar mari mai karfi ya doki kunnena. Tsayawa tayi cak tana kallon Abba, idonta cike da mamaki.

“Zainabu!” Abba ya fada cikin murya mai nauyi, amma cike da fushi. “Duk ranar da kika kara batawa yarinyata suna, wallahi sai na saba miki! Wacce irin mara imani ce ke? Kina kallon irin halin da take ciki, amma bakya jin tausayinta. Idan ba ni ba, wa zai tsaya mata? Ki sani, Ramlah ba ‘yar da za a ci zarafinta a gabana ba ce.”

Shiru ya ratsa dakin, sai karar zuciyata da take bugawa. Kallon Abba nake yi tamkar ban taba sanin shi a baya ba.

Abba ya kalleta da idanu masu cike da takaici, sannan ya ce da ita cikin kakkausar murya “Me tayi miki a rayuwa ne da kika tsaneta haka, Zainabu? Wace irin mugunta ta taba yi miki da har kika kasa sonta? Wannan yarinya fa bata taba cutar da ke ba, balle ma wani daga cikin ahalinki. Har sai kinyi mata sharri akan ta kashe mijinta bayan ke kanki kincemun kinji wata mota tayi hatsari babu wanda yayi rai sai wata yarinya?

Me ya rage daga zuciyarki haka? Mijinta ya mutu fa?, bayan ke kika dinga rura wuta na aura mata shi. Yanzu kuma da ita ta rasu, Zainabu, me kike so in ce? In yi yaya da hakkinta? Nayi yaya? Me ya sa kika koma haka alhali ba haka kike ba a baya?

Ki tafi kawai idan bazaki iya kula da yarinyata ba. Ni zan iya, ubanta ne kuma uwarta nake. Halaccin da mahaifiyarta ta yi miki a rayuwa bai kamata ki saka mata da wannan sharrin ba. Fita!”

Muryarsa ta cika da zafi, kalamansa suka daki zuciyata. Na kasa boye damuwata, sai kawai na furta cikin muryar da take rawa “Abba… kaina.” Da sauri ya nufo inda nake, ya kamo hannuna yana rarrashina “Sannu Ramlatu… bari akawo miki abinci ki ci, sai ki sha magani.”

Na juyo da idona na bi Mumy da kallo, ganin yadda jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi. Ta juya ta fita ba tare da ta ce komai ba, alamun kamar hawaye ne ke shirin zubowa daga idonta.

Ko da ta fita, Abba ya rike hannuna gam, yana kallona cikin idanuwa “Kiyi hakuri da dukkan halinta, Ramlatu. Kinji? Watarana sai labari.”

Murmushi kawai na yi, na ce masa cikin tausayi “Abba, dan Allah ka tafi office, kada ka zauna a nan.”

Ya yi murmushi, ya shafa min kai a hankali, ya ce “Karki damu, Ramlatu. Ni da kaina zan yi miki jinya. Hakan ba zai hana komai a office ba. Kin ji? Kuma yayanki ma ya ce yau zai sauka.”

Har bai gama maganar ba sai ga Doctor Maryam ta shigo da sallama. Ta fara gaida Abba sannan ta ajiye flask ɗin abinci a gefe. Abba ya kalleta, ya ce “Me yasa ba ki gajiya, Maryam? Dan Allah a barshi haka, kada nauyin ya yi miki yawa.”

Ta yi murmushi cikin ladabi ta ce “Ai babu komai, Abba. Ni diyata ce. Yaya, kafar taki tana zafi har yanzu?” Na girgiza kai cikin jin kunya, na ce “Aa, ba ta yi min komai yanzu, Doctor.” “Allah ya ƙara miki lafiya bari zanje yanzu akwai aikin da zamuyi wasu .” abba yayi mata fatan nasara sannan tafita.

Yinin ranar kuwa, ‘yan uwa da abokan arzikin Abba suka dinga zuwa dubani kowanne da sallama, da mamaki, da addu’a. A haka ne ma har yaya Abba da matarsa suka zauna a can, suna tare da ni har yamm Sai da yamma, lokacin da Anty matar yaya Abbas ta shigo, Abba ya kalleta ya ce “Anty, ki zauna tare da ita, ni zan wuce gida na yi wanka.” Ta ce “To, Abba.” Da zarar suka fita, Anty ta fara bani labarai iri-iri. A tsakiyar zancen na tsinci kaina da tambayar “Anty, wai ina Ya Billy ne? Ban ganta ba.”

Anty ta riƙe baki, idonta ya faɗaɗa, ta ce “Au! Ke ba ki san abin da Bilkisu ta jefa kanta ba? Shaye-shaye take yi wallahi. Ta ɓata rayuwarta gabaki ɗaya. Ai yanzu babu inda take zuwa. Usman ma sai da ya zo, suka yi wata biyu, aka kaita rehabilitation kafin aka samu ɗan sauƙi. Amma har ta taɓa hauka saboda kwaya.” Ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da cewa “Ai na faɗa wa Mom ɗita Wallahi hakkinki ne ke bin Mumy.”

Ni dai na yi shiru, na kasa cewa uffan saboda wani irin kuka mai nauyi da ya cika makogwarona. Sai kawai hawaye suka dinga silalowa. Anty ta ce cikin tausayi “Ai ma da sauƙi tunda ba ki ganta ba. Idan kika ga yadda ta dawo, wallahi sai kin yi mata kuka.”

Da Mumy ta dawo gida, ta tura ƙofar falon cikin hanzari, idanuwanta suka sauka akan Bilkisu wacce ke zaune a gefen kujera, tamkar mai jiran hukunci. Ba ko sallama, sai wutar masifa ta tashi daga bakinta. “Dan ubanki! Dan uwarki! Shaye-shaye kike yi? Kin lalata rayuwarki da kanki?!”

Bilkisu ta zabura, jikinta yana rawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Ta kalli Mumy cikin tsoro, muryarta na rawa kamar wacce aka kama da laifi “Wallahi, Mumy, babu abinda nasha. Ban shan komai ba… Allah ya sani.”

Amma Mumy bata saurare ta ba, tamkar ba ta jin komai sai bugun zuciyarta da tashin hankali. Ta yi tsalle kamar wacce ake hura wa wuta “Ki daina mjn ƙarya, Bilkisu! Wallahi kin cutar da ni. Kin tona min asiri. Kin ci amanata. Ki tashi ki je ki kalli Ramlah ta koma kamar yarinyar labarawa, ga kumari, ga kyan jiki sai ki rantse ba a kauye akayi mata aure ba. Ita nake so ta shiga cikin masifa, sai ke kika tsunduma kanki a ciki! Ni da kaina nake so in ga ta wahala, amma ke kika fi kanta shiga ƙangin sharrin duniya!”

Bilkisu ta rushe da kuka, hawaye na gangarowa ba tare da tsayawa ba. Tana girgiza kai cikin nadama, muryarta na karkarwa “Mumy, wallahi na daina. Ba zan sake ba. Na tuba, na yi nadama. Amma… bikin Nawal fa akayi yau…”

Wannan maganar ta kara hura wutar da ke cikin Mumy. “Bikin Nawal sai uban me?! A haka za ki je wajen jama’a? Kowa ya ganki ya ce ga ‘yar shaye-shaye, ga mai lalata kanta! Kina so ki zubar min da mutunci gaba ɗaya? Kin lalata rayuwarki, Bilkisu! Dallah tashi ki bani wuri kafin in karya miki ƙafafu. Yar iska kawai! Wallahi babu abinda kika haifar min face masifa da kunya!”

Bilkisu ta matso baya, tana jan hanci da tafin hannu. Maganganun Mumy na dukan kunnuwanta kamar tsintsiyar ƙarfe. Cikin zuciyarta, tana jin raɗaɗin kalmomin da suka fi dukkan duka zafi.

Sai ta juya a hankali ta nufi ɗakinta, tana jin kowane mataki tamkar yana kara nauyin zuciyarta. A ƙasan ƙirjinta, wani irin kunci ya tsaya mata. Ta san Mumy bata yarda da ita ba, kuma bata da hujjar da zata tabbatar mata cewa ta daina shaye-shaye.

Mumy kuwa ta zauna a kan kujera tana huci, hannayenta na rawa saboda fushi. A zuciyarta, tana tunanin yadda komai ya ɓaci. A maimakon ta ga Bilkisu cikin tsari da kwarjini, ta ga ta karkace zuwa halaye marasa kyau. Duk wani tunanin alfahari da ta taba yi da ita ya watse.

Hankalin Mumy ya sake dawowa kan Ramlah. Wata zuciya tana cewa ta je ta ganta a asibiti, amma wani bangare na zuciyar ta na son ta yi watsi da ita gaba ɗaya. Duk da haka, tunanin yadda Ramlah ta tsinci kanta a cikin wannan hali ya cigaba da mamaye kwakwalwarta.

A ɗaki, Bilkisu ta jingina da bango tana kallon sama. Tunaninta ya tafi baya lokacin da rayuwarta bata da wannan duhu. Tana tuna shekarun baya, lokacin da Mumy ke kallonta da alfahari, tana yabawa kyan halinta. Amma duk wannan ya canza a cikin kankanin lokaci, saboda kuskuren da ta bari ta fada.

Sai ta rushe da kuka mai ƙarfi, tana jin zuciyarta na bugawa da wani irin kunci. Duk wani alƙawarin da ta taba yi wa kanta, kamar an watsar da shi. Duk da ta ce ta daina, har yanzu alamar laifi na manne mata a idanun kowa.

Mumy daga falon ta ji wannan kukan, amma bata motsa ba. A ranta, tana cewa “Haka rayuwa take. Idan ka lalata sunanka…

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[23/08, 7:47 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SHA UKU

Mumy na shiga ɗaki, ta zura hannu cikin jaka tana lalubar wayarta. Cikin hanzari ta kira Yakaka. Kiran farko bai shiga ba, ta sake kira karo na biyu shiru. Ta sake karo na uku bata ɗauka ba. Mumy ta saki wayar a fusace, tana maida numfashi a hanzarce. Kafin ta kai ga ajiye ta gaba ɗaya, sai ga kira ya dawo mata. Ta ɗaga wayar da sauri, muryarta ta riga hawayen da suka cika mata ido “Yakaka, na shiga uku! Asirina ya tonu! Abban Ramlah ya gane halina yau… akan Ramlah! Har marina yayi, kinga kuwa? Da kansa yake zaune yana jinyarta a asibiti!” Ta yi maganar cikin kuka mai ƙarfi, muryarta na rawa, numfashinta na kaɗuwa. Yakaka ta yi tsaki tana faɗi cikin mamaki “Ni dai, dan Allah, ki bar wannan kukan! Kin saka ni cikin duhu. Wacce irin magana ce haka kike yi? Ramlahtu kuma? Yarinyar da mu ka riga mu ka gama da ita da babanta?” Mumy ta shasheƙe kafin ta amsa cikin masifa “Yakaka, Ramlah ta dawo! Mijinta ya mutu! Sun yi haɗari! Ni komai nawa ya jagwalgwale gaba ɗaya! Kin ga yadda Bilkisu ta koma saboda shaye-shaye, ai yanzu ma haka ta ke…” Yakaka ta yi tsaki mai ƙarfi

“Ke har yanzu baki hana ta shaye-shaye ba?”

Mumy ta yi dariyar takaici, ta share hawayenta “kema ai kinsan alkawarin ‘yan shaye-shaye alkawari ne! Nidai yanzu gani nake kamar ta rage, amma har yanzu ba ta dawo hayyacinta sosai ba.”

Yakaka ta dan yi shiru kafin ta sauke ajiyar zuciya “To ki yi hakuri. Komai mubishi a hankali. Zan san yadda za mu yi. Zan shigo garin nan ko zuwa mako mai zuwa. Sannan ke ki je ki ba mijinki hakuri… ai idan kika yi hakan, za ki iya jawo mana komai ya koma dai-dai.” Mumy ta lumshe ido tana sauraron muryar Yakaka, amma zuciyarta cike take da tunanin yadda abubuwa suka rikice fiye da tsammaninta.

Kusan sati uku kenan muna asibiti. duk wannan lokacin, Abba ne ya ɗauki nauyin jinyata gaba ɗaya. Shi yake kwans dani safe da dare yana tsayawa a kaina kamar wanda yake kula da ƙaramin jariri. Komai kamin na bukata yayimun, yana yawan tambayata babu inda yake miki ciwo babu inda yake miki zafi? ”

Wannan kulawa tasa tana ratsa zuciyata. Na ji wani sabon yanayi a raina yanayin da ban saba ji daga Abba ba. Mun fara shakuwa da shi sosai, har na fara kallonsa da wani sabon ido, ido na godiya da ƙauna irin ta ‘ya da uba. Wani lokaci idan ya zauna gefen gadona, muna yin hira mai daɗi, yana ba ni labarin ofis ko wani abin ban dariya da ya faru a hanya.

Sai dai wannan shakuwa tsakaninmu tana ƙona zuciyar Mumy fiye da tunani. Kullum idan ta shigo ɗakin asibiti, fuskarta cike da haushina take kallon yadda Abba yake bani kulawa. Na lura da yadda idan Abba yana bani abinci a baki Mumy sai ta ƙanƙance ido kamar wacce take so ta ce wani abu, amma ta danne. Duk da haka, maganarta tana fitowa cikin tsami kamar ɗaci a baki.

Karshe dai, wata rana bayan tazo bayan ta ɗan zauna tace wai ita wanne irin dangi ne da bashari da har yanzu basu so ba, Abba ya kalle ta cikin nutsuwa, sannan ya ce da'ita

"Zainabi, ki daina zuwa asibitin nan. Na riga na yafe miki, amma bana son ki ƙara shiga abunda bai shafeki. Ki huta a gida kawai."

Maganar ta yi mata zafi sosai. Na gani a fuskarta idanunta sun yi jajir, leɓenta na rawa kamar mai shirin yin magana amma ta kasa. Sai kawai ta tashi ta fice ba tare da ta ce komai ba.

Na tsaya nayi shiru, zuciyata na bugawa da sauri. Ban san ko farin ciki nake yi ko kuma fargaba ba. Na san wannan magana ta Abba zata shiga zuciyar Mumy ta yi masifa a bayan fage. Saboda na san halinta ba ta son a raina ta balle har a hana ta shiga inda take so ta yi tasiri.

Bayan ta fita, na tambayi Abba cikin rawar murya "Abba, me yasa ka ce haka?"

Ya yi murmushi mai ɗan ɗaci, sannan ya ce:

"Saboda bana son ki ƙara shiga damuwa. Idan akwai wanda zai kawo miki damuwa a lokacin da kike bukatar natsuwa, to zai fi kyau a cire shi daga kusa da ke."

Wannan maganar tasa ta shiga zuciyata sosai. Na ji kamar an cire wani nauyi daga kaina. Amma kuma na san ba zata tsaya haka kawai ba. Na san Mumy idan ta ji haushi irin wannan, to akwai abin da zata yi domin ta rama.

A cikin wadannan kwanaki, na ga yadda Abba ya mayar da kansa tamkar uba da uwa a lokaci guda. Shi yake tabbatar da cewa ban rasa magani ba, shi yake sa ido kan likitoci idan suna duba ni, har ma yana taimaka min wajen motsa jikina idan likita ta bada umarni. Sau da yawa idan dare ya yi, maimakon yayi bacci sai ya tsaya har na yi bacci sannan ya tafi.

Wasu lokuta idan ya fita ɗan shan iska, nakan zauna ina tunanin rayuwata gaba ɗaya. Ina tuna lokutan baya da na yi kuka saboda rashin kulawarsa, da yadda yanzu yake biyayya ga duk wata bukatata.

Yau Jumma’a, rana mai albarka, kamar yadda na jiyo suke ta faɗa a masallacin asibiti da ke kusa. Ina zaune a gefen gadona, kafata tuni ta fara samun sauƙi, amma har yanzu sai na jingina da sanda idan zan tashi ko tafiya, kamar yadda likitoci suka ce. Duk da haka, zuciyata tana cikin natsuwa saboda na ji lafiya ta na ƙara dawowa a hankali.

Abba ya shigo da murmushinsa na kullum, ya ajiye ledar abinci a kan teburi, sannan ya zuba min a faranti. A hankali ya soma bani, kamar yadda uwa ke baiwa ɗanta jariri. Idan na ɗauki loma, sai ya tsaya yana kallona har sai na haɗiye kafin ya saka min wata. Wannan kulawa tasa tana saka zuciyata ta yi wani irin sanyi mai daɗi.

Na ɗan ja numfashi, sannan na ce

"Abba, kasan me?"

Ya ɗan kalle ni da mamaki, yana murmushi:

"Aa, auta, sai kin faɗa."

Na kalli farantin hannuna, sai kuma na ɗago ina dubansa cikin ido na gaskiya:

"Wallahi Abba, Bashari ya zama mutumin kirki. Yadaina shaye-shaye, Abba. Yana sona, kuma kaga yadda yake kula dani. Har ya siya mana gida a Kano, muna shirin komawa... sai kawai yayi hatsari."

Na yi shiru, idona ya cika da ɗan hazo. Wani ɓangare na zuciyata yana cikin farin ciki saboda canjin da na gani a wurin Bashari kafin hatsarin, wani ɓangaren kuma yana cike da raɗaɗin rashin sa.

Abba ya yi murmushi mai ɗauke da tausayawa, sannan ya ce cikin nutsuwa:

"Allah ya jikansa, Ramlah. Kin ji? Ki yi hakuri, duk wani abu da ya faru, Allah ya riga ya tsara shi. Ki kwantar da hankalinki. Bari na je na gama abinda nake yi a ofis, sai na dawo wajenki daga baya."

Na ji muryarsa tana kwantar min da hankali, amma zuciyata ta cigaba da tunani kala-kala. Wani lokacin na rufe ido ina tuno lokacin da Bashari ya rungume ni yana shakar kamshina yana faɗin ƴar kwalisa sai asabon gidan mu sai ki haifamun yara kyawawa masu hankali irin ki ko?"

Amma kafin wannan.., kaddara ta riga ta katse mana hanya. Na san ba zan iya maida lokaci baya ba, amma maganganun Abba sun sa na ji wani sabon ƙarfin zuciya cewa watakila rayuwata zata iya samun sabon shafi, duk da komai.

Ko da fitarsa kenan daga ɗakin, sai ga Dr. Maryam ta shigo. Kyakkyawar murmushinta ya riga ya cika dakin kafin ta ƙaraso kusa da gadona. Ni ma na yi saurin gyara zamana na ce mata "Assalamu Alaikum, Doctor ina wuni."

Ta amsa da kulawa "Wa’alaikumus salam, beauty lafiya kalou yaya karfin jinkin naki?. Kinga yadda kika ƙara kyau? Mashaa Allah. Hatta launin fuskarki ya dawo kamar da, sai dai kafar nan, a hankali ne zata warware."

Na yi murmushi kadan, zuciyata na jin sanyi saboda irin kalaman kwantar da hankali da take fada min kullum. Ta zauna a gefen gadon, ta ɗan gyara hijabinta sannan ta ce cikin kulawa "Inason na baki shawara, Ramlah. Duk wani abu da ya huce a baya, ki ajiye shi a baya. Kada ki sake barin abubuwan da suka faru su ci gaba da damunki. Yanzu ki zama sabuwar Ramlah wacce ta tsai da kanta, wacce ba ta bari kowa ya maida ta marar ƙima ba mutuwa rigar kowa ce danAllah ya dauke miki abu mai mahimmacin ba hakan ne zaisa kiyi tunanin rayuwarki ta kareba har sai kwananki kema ya kare."

Ta ɗan kama hannuna tana mai ƙarfafa gwiwa "Ki zama yar gayu mai kima, amma mai hankali. Ki tsaya sosai akan dukkan abin da zai inganta rayuwarki. Ki ci gaba da karatunki, kada ki bari komai ya katse miki gaba. Kuma, matar babanki ki girmamata, amma ki canza yadda kike zama da ita. Ki rike mutuncinki, ki kama kanki. Bashari kuma ki yi masa addu’a. Muma a nan muna masa addu’a, Allah ya yafe masa."

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[25/08, 11:17 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SHA HUDU

Dr. Maryam ta yi shiru na ƴan dakiku tana kallona kai tsaye, kamar tana karanta zuciyata. Sai kuma ta ɗan gyara zamanta ta ce cikin nutsuwa "Ramlah, zan gaya miki wani abu mai muhimmanci da na koya a rayuwa, musamman game da maza. Maza suna son mace mai kunya, mai kama kanta, wacce ba kowa bane zai iya kaiwa gare ta. Ba wai sai kin yi tsaurin fuska ko kin yi ta yin magana ba, a’a kawai ki kasance mai kiyaye martabarki."

Ta ɗan murmusa, tana kallona cikin ido

"Ki rike kanki kamar zinariya. Idan kika kasance mai kyawun hali, mai tsafta, mai kula da kanki, maza za su ganeki a matsayin wacce ta dace da su, ba wacce za su yi wasa da ita ba. Ki guji zama a wuraren da za su sa a raina ki. Ki koyi cewa shiru da natsuwa suna ƙara darajar mace." Sai ta ɗan matsa kusa da ni ta ce da ƙarfi kadan "Maza suna son yarinya mai gaskiya, amma kuma mai iya saka kima a jikinta. Yar gayu ce mai tsafta, mai kamshi, mai kula da jikinta da suturarta. Amma duk wannan bai isa ba idan bata da kunya da tarbiyya. Ki tuna, ki zama mai kaifin hankali wajen fahimtar magana, amma kar ki zama mai buda baki da zance mara amfani."

Ta ɗan yi dariya kadan "Kin san menene sirrin mace? Sirrinta shi ne ta kasance kamar littafi mai kyau ana ganin murfin sa kyakkyawa, amma ba kowa ke samun damar budewa ba. Idan kika kare kanki, kika kama kanki, ko wane namiji zai girmama ki."

Daga nan sai ta ɗora hannunta akan hannuna ta ce "Ki tabbata kina da manufar rayuwa. Kada ki yi rayuwa kawai don ki burge mutane. Ki yi rayuwa don ki gina kanki, ki kai ga inda kike so. Mace mai burin kaiwa wani matsayi tana da daraja a idanun kowa, musamman maza."

Na yi shiru ina sauraren ta, zuciyata tana karɓar kowace kalma kamar ana ɗora min ɗigon zuma a hankali. Kalmar “sabuwar Ramlah” ta tsaya sosai a zuciyata. A zuciyata na fara hango wani sabon shafi na rayuwata, shafi da babu tsoro ko durkushewa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull