Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 6

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 6

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 6: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 6. Dr. Maryam ta cigaba "Yanzu ma za a sallame ki, inshaa Allahu. Kafin…

4,495 words

Dr. Maryam ta cigaba "Yanzu ma za a sallame ki, inshaa Allahu. Kafin na tafi UK, zan zo har gidanku in same ki. Ina son ganin yadda kike karɓar sabuwar rayuwa da hannunki."

Na kalle ta da idanu masu cike da jin daɗi, na ce cikin nutsuwa "Nagode sosai, Doctor. Ubangiji Allah ya saka miki da alkhairi, ya biyaki da mafificin lada."

Ta yi murmushi mai ɗauke da gaskiya "Amin, Ramlah. Ki tsaya da addu’a. Kada ki manta, ƙarfinki yana hannunki."

Daga nan ta miƙe tsaye, ta karɓi wayar Abba daga kan teburi. Ta ce tana son ta kira ni idan ta fita daga asibiti don jin ko na isa lafiya. Ni kuma kafin na yi mata waya daga baya, sai na sake mata godiya "To, nagode, Doctor. Allah ya kiyaye hanya."

Ta yi murmushi ta ce "Amin, auta. Sai mun haɗu.”

Bayan fitan Dr. Maryam, sai nayi shiru na ɗan jim kaɗan, zuciyata tana taɗa da kalmomin da ta bar min. Da kyar na tashi daga gadon, na ɗan jingina hannuna a bango har na isa bandakin ɗakin.

Lokacin da na shiga na jingina a ƙofar na saki dogon numfashi. Na ɗauki cup din na fara zuba ruwan zafi da na roƙi nurses ɗin su kawo min tun da safe. Ruwa mai ɗumi ya fara haɗuwa da ruwan sanyi har ya zama dai-dai. Na zuba ruwa a jikina tun daga ƙafa zuwa kai.

Sai na rufe idona na saki numfashi mai zurfi. Ji nayi kamar kowanne ɗigon ruwa da ke sauka a jikina yana wanke duk wani baƙin ciki da ya manne a zuciyata tun watanni da suka wuce. Duk da cewa kwana uku kenan da fara taɓa ruwa yau kamar sabon numfashi nake karɓa.

Na ɗan jingina da bango ina shafa jikina a hankali. Hannuwana suna jin santsi da natsuwa, zuciyata kuma tana ƙara cika da kwanciyar hankali. Na ji dadi fiye da tunani.

Bayan na gama, na ɗaure kaina da tawul, na fito daga bandaki a hankali. A gefen gadona na hango sabon hijabi mai launin milk white da Abba ya kawomun jiya. Nace a raina

"Lallai Abbana ya canza yana kulawa dani sosai yanzu bakamar da ba Allah ya saka masa da alkhairi."

Na ɗaura hijabin a kaina, na kalli madubin ƙaramin ƙofa. Nayi murmushi ina kallon kaina ban da ɗan raunin da ya rage a fuskata, sai na ga sabuwar ni. Idanun nawa sun ɗauki wani irin annuri daban, kumatuna sun ciko sosai sunyi bul bul nadai kara kiba dan jinyar nan danayi a asubuti kokuma harda ruwan dana sha?

Sai na ɗauki sabuwar abaya mai launin black da fari da Abba ya kawo min daga kasuwa. Abayar ta zauna jikina sosai, ta fito da cikakkiyar mace a cikina. Na ɗaure rigar sosai sannan na saka ɗan sure ajikina sannan nasaka turare a wuyana wanda yake da ƙamshi mai taushi amma mai ɗaukar hankali.

Wannan karon ban ga kaina kamar marar galihu ba. Na ga kaina kamar wacce aka haifa sabuwa, wacce ta tashi daga cikin ƙunci da tsananin jarabawa.

Na fito daga gefen gado na zauna a ƙaramar kujerar ƙarfe da ke gefen window. Wani iskar safe mai ɗauke da sanyi ta shigo daga cikin window, ta taɓa fuskata a hankali. Na runtse ido ina shakar wannan iska mai tsabta kamar wacce take wanke zuciyata da hanci lokaci guda.

Cikin raina nayi shiru ina jin daɗin zaman. Na ji kamar zuciyata tana furta addu’a "Ya Allah, ka bani ƙarfin zuciya, ka bani ikon gina sabuwar rayuwata. Kada ka barni in koma baya Allah kajikan Bashari kayi masa rahama."

Kamar na ji muryar Dr. Maryam a cikin kunnuwana tana cewa "Ki zama mace mai kima, ki zama mace mai kunya da tarbiyya." Sai na ɗan murmusa a raina. Na riga na yanke shawara cewa daga yau zan zama fiye da tunanin duk mai tunani.

Na yi shiru ina kallon ƙofar ɗakin asibitin. Nurses suna wucewa suna dariya, wasu suna ɗauke da files. Bayan na zauna, sai na ɗauki Qur’ani ƙarami da yake gefen gadona, na buɗe Suratul Rahman. Na fara karantawa a hankali, muryata tana rawa kaɗan saboda farin ciki. Kowanne ayar da nake karantawa kamar tana magana da ni kai tsaye. Lokacin da na zo wurin “Fabi ayyi aalaaa’i rabbikumaa tukaththibaan” sai na fashe da dariya mai ɗan ɗaci.

Na ɗaga hannuwana sama nace "Ya Allah, wallahi babu wata ni’ima da zan ƙaryata. Ko da yake rayuwata ta cika da wahala, amma har yanzu ina da iyaye, ina da lafiya, kuma ina da damar sake gina kaina."

Idanuna suka ɗan cika da hawaye, amma ban bari suka zubo ba. Na share su da gefen hijabina, na miƙe tsaye a hankali.

Na taka ƙafata a hankali, har na ji ciwon ya rage. Likitocin sun ce a hankali zan rika tafiya har ƙafar ta saba. Wannan karon ban ji tsoron fadowa ba, sai na ji ƙarfin zuciya ya shiga cikina.

Na dawo kan kujerata na zauna, na jingina bayana, na kalli sama. Rana ta fara haskawa daga window ɗin asibitin, hasken safe ya ratsa fuskata.

Bayan na gama karatun da nake yi ina zaune kusa da window, kwatsam na ji sallama ta cika cikin dakin da sauti mai cike da ƙauna da farin ciki. “Assalamu Alaikum…”

Na ɗago da sauri, murmushi ya bayyana a fuskata lokacin da na hango Abba ya shigo tare da wasu daga cikin ‘yan uwansa. Ba shi kaɗai ba ne yau, sai ga Uncle Hamza da sauran kanin Abba guda biyu da na daɗe ban gansu ba. Fuskar kowa cike take da annuri da murmushi, alamun farin cikin ganin an sallame ni daga asibiti.

Suka shigo ɗakin ɗaya bayan ɗaya suna ce min “Sannu auta, Allah ya ƙara miki lafiya, Allah ya baki cikakkiyar sauƙi.”

Wani irin natsuwa na ji zuciyata ta cika da shi. Har na ji hawaye na son zubowa saboda wannan kulawa da ƙauna da suke nuna min. Duk da duk wahalar da ta ratsa ni. Abba ya ƙaraso kusa da ni ya zauna, ya yi murmushi yace “Ramlah, yau an sallame mu. Ki shirya mu tafi gida.”

Uncle Hamza ya ɗan yi dariya yana juyawa yana kallona yace “Auta, anya kuwa ba gidana zaki dawo ba ko? Kin dai san gidan Hamza dai babu hantara babu takura babu.., ba a rasa dariya da annashuwa.”

Kafin inyi magana, Abba ya ɗaga ido ya kalleshi da wata irin nutsuwa “Hamza, menene ya samu gidan ubanta da zaka dinga yi mata tayin gidanka? Ko kai basan babanta ya canza ba?.”

Da sauri sauran ‘yan uwansa suka sanya dariya, suna kallon juna cike da annashuwa.

Uncle Hamza ya ɗan gyara zamansa, yana kallona da murmushi kamar yana son ya ɓoye jin haushinsa, yace “To yaya, ai dai magana ce kawai. Ke ma kin sani auta, ai duk diyar yaya ɗiyata ce. Ban ga laifi ba idan na nuna kulawa ko in yi dariya da ke. Menene na ɓatan baki?”

Abba ya girgiza kai a hankali yana kallon ƙasa, sannan ya ɗaga kai ya sake dubansa yace “Haka ne Hamza, amma akwai iyaka a cikin kulawa. Ni ban yarda da wannan maganar taka ba, kuma kar na sake jin irin wannan. Auta zata koma gidana babu accent data isa ta takura mata. Kar ka sake yin wasa da irin wannan magana, domin bana so.”

Na kalli Abba zuciyata ta cika da alfahari da shi. Wannan kulawa da tsare mutuncina da yake yi ya ƙara tabbatar min cewa shi fa ba uba kawai ba ne, uba ne mai cike da adalci da tsantsar kulawa.

Na ji Uncle Hamza yana murmushi yana cewa “To yaya, Allah ya baka hakuri ya kuma yi mata albarka. Ni dai gaskiya ne kawai nafaɗa, amma tunda ka ce haka, babu matsala. Amma fa Ramlah kinsan nima ina ɗaukar ki tamkar diyata, haka ma sauran ‘yan uwa. Kada ki ji komai.”

Na ɗan yi murmushi cikin ladabi nace “Na sani Uncle, nagode da kulawar ku. Allah ya saka da alkhairi.”

Na ji Abba ya sake murmushi yace “Wannan yarinyar fa jini na ce. Kuma daga yau tana da sabon shafi a rayuwarta. Ni dai na yanke hukunci babu inda zata je, gida zata koma.”

Dukkanmu muka yi shiru na ɗan lokaci. Sai murmushi ya bazu tsakanin su Uncle, kowa yana dariya da annashuwa. Amma ni a raina na ji wani irin farin ciki mai zurfi, kamar an ciro wani dutse daga zuciyata. Na ji kwanciyar hankali kamar ba a taɓa yi min irin wannan kariya ba a baya.

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

Nana hadiza

09030569336

[26/08, 7:29 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SHA BIYAR

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Sallamar “Assalamu Alaikum” ta katse tattaunawar da ake yi, sai muka juyo gaba ɗaya muka ga Yaya Abbas ne ya shigo da murmushin annuri a fuskarsa. Ya ƙaraso kusa da Abba da sauran ‘yan uwansa, suka gaisa da shi. Ni ma na ɗago da murmushi, na ce cikin ladabi “Sannu da zuwa Yaya Abbas.”

Ya kalle ni da nutsuwa, yana murmushi yace

“Ramlah, ya jikin naki? Kin fara jin sauƙi kuwa?”

Na amsa “Alhamdulillah Yaya, yanzu dai da sauƙi sosai. Na warke kusan gaba ɗaya, kawai dai a hankali nake farfaɗowa.”

Ya girgiza kai da murmushi ya ce

“Allah ya ƙara miki lafiya Auta. Wannan jarrabawar ta zo ne a matsayin darasi, amma in sha Allahu Zaki samu lafiya shi kuma bashari Allah yajiƙansa.”

Daga nan ya juya ya kalli Abba yana mai cewa “Abba, ya kamata mu shirya muje mu yiwa Mai Martaba godiya. Tunda kowa ya sani cewa shi ne ya ɗauki nauyi ya yi komai a wannan lamari. Ko ba haka kake gani ba?”

Abba ya yi ajiyar zuciya, sannan ya girgiza kai a hankali ya ce “Hakane Abbas. Ni kaina wallahi har na sha’afa naso tun jiya munje.”

Amma Yaya Abbas ya gyara zamansa, yana mai ɗaga murya cikin natsuwa yace “Eh Yaya, amma ka sani ai na riga da na isar masa da sakonmu. Na gaya masa cewa za mu zo, amma ya ce a wancan lokacin su na wajen bikin jikarsa a waje. Shiyasa bai ce mu zo ba. Amma yanzu sun dawo daga ƙasashen wajen, Yanzu ne ma lokacin da ya dace muje domin nuna girmamawa da godiya.”

Abba ya yi murmushi cikin gamsuwa ya ce “Tabbas kuwa, dan ni kuwa sai sha’afa nake. Bari mu shirya mu tafi.

A wannan lokacin na ji wani irin kwanciyar hankali a zuciyata. Na tuna irin jinyar da nayi tsawon kwanaki, da irin kulawar da nake samu daga Abba da likitoci. Amma yanzu da maganar godiya ta taso, sai na ji cewa lallai akwai darasi a ciki idan mutum ya yi maka alheri, wajibi ne ka gode masa kafin ma ka nema daga Allah ya saka masa saboda bada ban mai martaba ba tabbas datuni an ciremun kafata ta dalilinsa nasamu kulawa tun farko.

Da su Abba, Yaya Abbas, da sauran dangin suka isa ƙofar fadar, sai masu gadi suka tsaya da ƙwazon tsarewa cikin kayan sarauta, hannayensu da sanduna na alfarma. Daga nesa aka tambaye su “Su waye? Kuma daga ina?” Abba ya gyara hularsa ya ce “Mu ne iyalan Malam Kabir, mun zo wajen Mai Martaba domin yin godiya bisa alherin da ya nuna mana.”

Da wannan aka buɗe ƙofar, masu gadi suka miƙa hannu suna nuna musu hanyar shiga. Harabar fadar cike take da ƙayatarwa fitilu na gilashi suna haskawa, ƙasa an shimfiɗa farin tabarma mai tsabta, sai ƙamshi na turaren Oud da Amber dake tashi ko’ina.

A ƙasan babban zauren, fadawa suna tsaye cikin kaya masu ɗaukar ido, kowanne cikin rawani da babbar riga. Duk wanda ya gan su, sai ya fahimci izzar sarauta da ɗaukakar fada.

Da aka shigar da su ciki, sai aka kawo musu ruwan sanyi da lemoka acikin robobi masu sheƙi tare da kofi na glass aka ajiye a gabansu, aka miƙa musu da ladabi.

Mai Martaba ya fito cikin nutsuwa, yana sanye da hula mai launin fari, babbar riga farar gaske da aka yi da zare mai tsada, fuskar nan tasa cike da annuri da izza. Da suka gan shi gaba ɗaya suka miƙe tsaye suka rusuna suna gaishe shi “Assalamu Alaikum Ya Mai Martaba.” Ya amsa cikin muryar dattako “Wa’alaikumus Salam. Sannu da zuwa, ku zauna.”

Aka nuna musu kujeru masu ƙyau aka zaunar da su. Nan Abba ya miƙe da ladabi, ya ɗan sunkuyar da kansa kafin ya fara magana da murya mai cike da girmamawa “Ya Mai Martaba, mun zo gareka ne don nuna godiya bisa alherin da ka yi mana, musamman lokacin da Ramlah ke cikin mawuyacin hali. Kai ka ɗauki nauyin duk abin da ya kamata a lokacin, ka tsare mana mutunci, ka tsaya mana tamkar uba nagari. Wannan alheri ba zai taɓa gushewa daga zuciyoyinmu ba.”

Sai ya ɗan tsaya ya shafa hula ya ce “Mai Martaba, muna addu’a Allah ya saka maka da alheri, ya ƙara maka daraja da nisan kwana. Mun gode sosai.”

Abba ya tsaya da girmamawa, yayin da Ramlah zaune kusa dashi cikin natsuwa da kunya.

Mai Martaba ya ɗago ido ya kalli Ramlah, ya ce cikin murya mai daɗi wacce take da nauyin sarauta “jikata Ramlah, zo mu gaisa. Yar albarka, kinsha jinya sosai Allah yasanya kaffarace tabbas jini baya buya ina kallonta naga kamar nasan fuskar ashe diyar kabiru ce. Wato Kabiru, wannan ’yar taka ba ƙaramin juriya tayi ba. Ni fa tun a kallon farko na ji kamar nasan fuskarta, ashe kuwa na sani.”

Zaure ya ɗauki nutsuwa, kowa ya yi shiru. Cikin kunya da natsuwa, Ramlah ta tashi a hankali. Ta ɗan dafa sandar hannunta, tana tafiya a hankali, jikinta yana nuna ladabi da kamala. Idanun mutane sun bita har ta ƙarasa gaban Mai Martaba, ta tsugunna a ƙasa, ta ce cikin siririyar murya“Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da daraja. Na gode ƙwarai da wannan kulawa.”

Mai Martaba ya yi murmushi mai cike da ƙauna, ya ce “Allah ya ƙara miki lafiya, diyata. Yaya kafar taki? Ko dai sai an fita da ita waje ne naga kina dogarawa da sanda?”

Kafin ta ba da amsa, sai Yaya Hamza ya yi saurin tunkarar magana cikin ladabi “A’a, Ranka ya daɗe. Tasamu sauki sosai. Likitoci sun ce kawai sanda ce har yanzu saboda ƙarfin ƙafarta bai dawo sosai ba. Amma a yanzu tana kara samunlafiya cikin sauri.”

Mai Martaba ya ɗan gyara zamansa, ya kalli fadawa ya ce “Alhamdulillah. To yanzu, ku sanar da As’ad ya fito, yana da baki a wajenmu yau.”

Zaure ya ɗauki wani irin motsi, kowa ya kalli ƙofa inda fadawa suka nufi wajen kiran shi.

Wajen ya ɗauki shiru na ɗan lokaci, sai ga Bafade cikin shigar sarauta, ya shigo da ladabi yana tsugunnawa kafin ya yi magana.

Da murya mai ƙasaita amma cikin ladabi, ya ce “Ranka ya daɗe, ina sanar da kai cewa As’ad bai nan cikin ƙasar tun jiya da daddare. Ya tashi da jirgi zuwa waje, amma ana tsammanin zai dawo Abuja a yau ɗin, In shaa Allah.”

Mai Martaba ya ɗaga kai da nutsuwar shugaba, ya kalli Abba da sauran jama’a da suka zo tare da shi. Murmushi ya bayyana a fuskarsa, sai ya ce “Allah ya dawo da shi lafiya. Kabiru, wannan zuwanku dai alheri ne. Allah yasa duk abin da kuka zo da shi ya zamto albarka a gare ku. Na yarda da ku kuma na karɓi godiyarku. Ku kuma, Allah ya saka muku da alkhairi.”

Sai ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya cigaba “Ku yi hakuri da rashin ganin Hajja. Tana Dubai yanzu, ba ta dawo ba. Amma zan isar mata da gaisuwarku. Kuma in Allah ya yarda, idan na sami lokacin, zan kawo ziyara gidan ku domin nuna farin ciki da wannan haɗin zumunci da ke tsakanina da ku.”

Abba da sauran su suka yi gaisuwar ladabi, suka ce “Amin.

Daga gidan Mai Martaba muka nufi gida. A hanya na kasa rike tunanin irin karamcin da akai mana, na kasa mantawa da yadda suka tarbe mu cikin girmamawa. Hakan ya ƙara mini kaunar Abba da godiya ga Allah da Ya bani wannan dama.

Ko da muka iso gida, na tsaya cak a bakin ƙofar falon. Na zuba ido ina kallon cikin gidan, sai na ji zuciyata ta buga da sauri. Gidan ya sauya gaba ɗaya! Abba ya yi masa gyare-gyare sosai.

Abba ya riƙe hannuna a hankali ya ce da ni “Auta, ki shigo. Na san kin gaji sosai. Wannan gidan mahaifinki ne kidaina damuwa da komai kinji bakida inda yafi nan.”

Na ɗan lumshe idona cikin jin daɗi, na ce cikin zuciyata Lallai Abba ya yi mini uwa, ya kuma yi mini uba. Ubangiji Allah ka saka masa da mafi alkhairi. Muka shiga cikin falon. Na hango Momy tana zaune a kan kujera tana kallon talabijin. Tana ganinmu ta miƙe tsaye da murmushi a fuskarta. “Sannu da dawowa Abban Ramlah. Sannu Ramlah, ya jikinki yanzu?” Na sunkuyar da kai cikin ladabi da kunya, na ce “Lafiya kalau Momy, na gode. Ina yini?” Abba ya taimaka ya zaunar da ni akan kujera kusa da shi, sannan ya saki hannuna cikin kulawa. Na ji wani irin farin ciki ya ratsa zuciyata, saboda kulawar da yake nuna min tana da nauyi sosai a raina.

Sauran ‘yan uwan Abba da suka raka mu suka shiga gaisawa da Momy, kowanne yana yi mata sannu da gida da fatan alkhairi. Ita kuma tana amsawa da murmushi da fara’a, sai dai na lura idanunta sun fi tsayawa a kaina. Kamar tana nazarin sabon ni’imar da Allah Ya bani. Bayan ɗan hira, kowanne daga cikinsu ya fara tashi ɗaya bayan ɗaya, suna cewa “Yaya malam, mun wuce gida. Allah ya ƙara lafiya.” Sai falon ya rage mu uku kacal ni, Abba, da Momy.

Abba ya kalli Momy, ya ce “ Zainabu, ga Auta nan. Ki kula da ita sosai. Ta sha jinya sosai danAllah ki kula da amana ki ajiye kiyayya agefe haihuwar ramlah ne kawai bakiyi ba amma tundaga tsummanta ke kika kasance uwa gareta bayan marigaya. Ina so ki dinga nuna mata kulawa sosai.” Na ji maganar Abba ta kama zuciyata gaba ɗaya. Hawaye suka cika idona, amma sai na rufe fuskata da murmushi na ƙasa-ƙasa. Momy kuwa ta saki wani murmushi “Ai dama haka nake yi. Ita fa yarinyarmu ce gaba ɗaya.” Na sunkuyar da kai cikin kunya da ladabi, na ce “Na gode Momy.” Sai dai, duk da murmushin da Momy ta yi, zuciyata ta ji kamar akwai wani abu da take ɓoyewa a ranta. Idonta ya ci gaba da kallona da wani irin yanayi da ban iya fassara ba.

Na sunkuyar da kai ina wasa da hannuna a jiki, zuciyata kuwa tana ta bugawa saboda mamakin yadda rayuwata ta fara sauyawa cikin ɗan gajeren lokaci.

Abba ya kalle ni cikin kulawa, ya ce “Auta, ki tashi ki je ɗakin da aka tanada miki ki huta. Sannu a hankali dai, kiyi amfani da sandar. Daga yau ni zan kasance a tare da ke har sai kin murmure gaba ɗaya.” Na ce masa cikin sanyin murya “Na gode Abba. Allah ya saka maka da alkhairi.” Na miƙe a hankali cikin ladabi na baro falon, zuciyata na cike da godiya da kuma ɗan tsoro saboda idon Momy da nake ji a kaina.

Da na shiga ɗakin komai sabone hatta wardrobe din an sakamun kaya duk da basuda yawa na rufe ƙofa, sai na jingina da bango na sauke ajiyar zuciya. Na ji hawayena na neman zuba saboda farin ciki da kuma ruɗani. Na tuna kalaman Doctor Maryam, na tuna irin kulawar Abba, na kuma tuna yadda Momy take kallona.

A falon kuwa, bayan na fice, Momy ta juyo ta kalli Abba da murmushi mai ɗauke da ɓoyayyen bakin ciki “Abba, gaskiya Ramlah ta yi kyau kamar ba jinya takeyi ba. Sai kuma tace yanzu, wannan kulawa da kake nuna mata batayi yawa ba Ba ka tsoron mutane su fara magana?”

Abba yace “zainabu, ki saurara. Wannan yarinyata ce fa . Ita ce farin cikina, kuma na ɗauki nauyinta gaba ɗaya. Ba zan bari wani ya cutar da ita ba. Idan na nuna mata kulawa, wannan kulawar ce zata faranta mata rai ta dawo da ƙarfinta.”

Momy ta ɗan yi shiru, ta ɗora hannunta kan kugu ta ce cikin taushin murya “To Allah ya sa haka. Ni dai bana son komai ya sa a dinga kallona tamkar bana son.”

Nana hadiza

09030569336

[27/08, 9:48 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SHA SHIDA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Da Abba ya bar falon, Momy ta yi wani nishi mai nauyi kamar wadda aka zuba wa dutse a ƙirji. Jikinta ya yi sanyi, zuciyarta kuwa ta ƙara tsananta tafarfasa. Ba ta iya jurewa ba, ta nufi bene tana dingishi cikin takaici.

Da ta shiga ɗaki, ta faɗa kan gado kamar wadda aka fatattaka, ta rufe fuskarta da hannu. Sai hawaye suka fara zubo mata, zuciyarta na jijjiga da kalaman da ta kasa faɗa a fili.

Cikin rawar jiki ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta, ta lalubo lambar Yakaka. Tana danna kira zuciyarta na dukan uku-uku, kamar wadda aka cafke a faɗa.

Cikin sa’a kuwa, bayan ɗan lokaci an ɗaga wayar. Muryar Yakaka “Zainabu… lafiya? Me ya faru da ke haka cikin dare?”

Momy ta share hawaye da sauri amma zuciyarta na tsuma, ta ce cikin muryar kuka “Yakaka! Na shiga uku wallahi. Kinga yadda Ramlah ta dawo gida kuwa? Idan kika ganta sai ki ɗauka wata hamshakiya ce, cike da kwarjini da izza. Kin ga gatanan ta dawo gidanmu, kuma Kabiru… wallahi kulawa yake nuna mata fiye da yadda na zata. Nayi tsammanin zai nemi kakaninta ya ba su ita, amma sai ya dawo da ita har cikin gidana! Yakaka, na rasa yaya zan yi. Idan na kalli Bilkisu, zuciyata na fashewa da kuka. Sai na ji kamar Ramlah zata ɗauke mata komai daga zuciyar mahaifinsu.”

Yakaka ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta yi gyaran murya cikin nutsuwa mai cike da izza “Zainabu, ki kwantar da hankalinki. Kin san irin rayuwar da kika shiga tun farko gidan Kabiru ba gidan da ake nuna son zuciya ba ne. Amma ki ji wannan shawarar tawa ki cigaba da dannewa. Kada ki sake nuna kiyayyarki akanta a gaban mutane, musamman a gaban Kabiru. Idan kika yi haka, sai ki bayar da dama ya fahimci asalin zuciyarki. Ki yi haƙuri. Zuwa jibi zan karaso. Zamu zauna mu tsara yadda za mu tafiyar da lamarin nan. Amma ki tabbata, ki rike zuciyarki a boye.”

Momy ta goge hawayenta da sauri, ta daure murya kamar wadda aka sake mata ƙarfin guiwa “To Yakaka, zan gwada in ga yadda zai kasance. Amma wallahi zuciyata ta ƙi yin sanyi. Idan na ga Kabiru yana nuna mata kulawa, sai na ji wuta ta sake hura a ƙirjina. Zan danne, amma ba zan taɓa bari Ramlah ta mamaye ransa ba ko gurin malamin nan ne akoma.”

Yakaka ta yi ƙaramin nishi, sannan ta ce “Shi kenan, ki tsaya kiyi shiru har sai na dawo. Idan muka haɗu, zamusan abun yi.”

Da ta katse wayar, Momy ta jingina da gado, tana huci da zuciya mai ƙuna. A zuciyarta kuwa ta ɗaura alwashin cewa wannan dawowar Ramlah, ba zata taɓa zama santsi ba a rayuwarta.

Bayan an idar da sallar isha’i, gidan yakasance shiru sosai. Kowa ya koma dakinsa, sai hasken fitilu masu launin fari da suka barbaje a falo.

Abba ne ya dawo daga masallaci, fuskar nan tasa cike da kwarjini ya shiga falon. Momy ta fito da abinci tana ajiye masa a gabansa.

Sai Abba ya ɗauki wayarsa ya tsaya, ya kalleta cikin nutsuwa yace “Zainabu, ki ɗauki wannan abincin ki kai min ɗakin Ramlah. Daga yau tare za mu riƙa ci. Ba zan so autata ta zauna ita kaɗai ba sannan ina bilkisu tashiga ban ganta ba tunda nadawo yau nafa gayamiki banason yawon nan datakeyi bana jin dadi kiga yadda yarinya ta koma.”

Nan take fuskar Momy ta sauya, ta dan saki dariyar raini da ɓacin rai a ranta. “Ranka ya daɗe, ai Abbas ya shigo dazu ya ɗauki Bilkisu zuwa gidansa da ita. Gobe zata dawo. Shi yasa baka ganta ba.”

Abba ya ɗaga kai ya kalleta da ido mai nuna izza da gargad. “To shikenan, ba matsala. Amma ki ɗauki wannan abincin ki kai wa Ramlah yanzu.”

Momy ta runtse ido kamar zata fashe da kuka, ta ce da ɗan harara “Haba Abban Ramlah! Abincin ma sai ka shiga kunci da autarka? Nace maka na zuba mata nata a ɗakinta. Wannan naka ne kaɗai.”

Sai Abba ya ajiye waya ɗin hannunsa ya ɗan lumshe ido, sannan ya buɗe su ya kalleta da izza, muryarsa cike da ƙarfi da umarni ya ce

“Na gaya miki bana son haka, Zainabu. Ramlah ɗin nan diyata ce, . Kada ki ƙara yin magana kamar ba ƴar gidan nan ba. Ki ji tsoron Allah wajen nuna bambanci tsakanin ’ya’ya. Ki taimaka min da gaskiya, kada ki ƙara canzawa.” Momy ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗan girgiza kai da rauni tana share hawayen da ya cicciko a idonta.

Sai Abba ya ɗaga hannunsa cikin natsuwa ya ƙara cewa “Barshi ma, Zainabu. Zauna ki ci. Ni da kaina zan kai mata.”

Nan take ya miƙe da tray ɗin hannunsa, tafiyarsa cike da izza da girma, ya nufi ɗakin.

***

Bayan na idar da sallar Isha’i, ban tashi ba nan take daga dardumata. Na zauna na jingina da bango, zuciyata na cike da tunani iri-iri. Sai na fara lazumin “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”. Na maimaita kalmar sau da dama har sai da ta kai kusan sau 450, kowanne maimaitawa yana sanyawa zuciyata ta ji nutsuwa da kwanciyar hankali.

A yayin da nake maimaita ta, nake tuna kalmomin malamaina na addini

Idan mutum ya dage da wannan kalma, tana zama katanga tsakanin shi da kowanne sharri. Ita ce addu’ar Annabi Ibrahim (AS) lokacin da aka jefa shi cikin wuta, Allah ya mayar masa da ita sanyi da salama.

Ita ce addu’ar da Annabi Muhammad (SAW) ya yawaita lokacin da makiya suka kewaye shi a yaƙi, Allah ya tsare shi.

Hakan yasa na ji zuciyata tana samun nutsuwa da kwanciyar hankali, kamar an ɗauke mini nauyin damuwa daga kafada ta.

Bayan haka kuma na ɗauki littafin addu’o’ina, na karanta wasu sirrikan addu’o’in da malamai suka ce idan mace ta dage da su

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull