Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 7
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 7: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 7. “Ya Allah, ka sa albarka a jikina, ka tsarkake zuciyata, ka shiryar…
4,478 words
“Ya Allah, ka sa albarka a jikina, ka tsarkake zuciyata, ka shiryar da tafarkina.”
Addu’ar neman sauƙi da lafiyar kai da zuciya.
Addu’ar neman kariya daga hassada da makiya.
Daga nan sai na rufe littafin na ɗaga hannuwa sama cikin kuka na ce “Ya Allah, idan wannan dawowata gida alheri ne, ka sanya min albarka a ciki. Ka bani kariya daga duk wani sharri, ka sanya ni cikin amincinka da rahamarka.”
Lokacin da na kammala addu’a sai na ji wani sanyi ya ratsa zuciyata, na kasa ma gane ko nafi jin daɗin addu’ar ko nutsuwar da take kawo min.
Daga baya kuma na koma banɗaki nayi wanka, na ji jikina ya ɗan lafa. A cikin wardrobe na hango wata Morocco light yard mai kyau, sai na sanya ta. Bayan haka na koma gadona na kwanta, saboda yunwa na fara ji sosai. Lokaci kuwa ya ja, tuni karfe tara ta wuce.
Cikin nutsuwa sai na ji an kwankwasa ƙofar ɗakin. Da sauri na ɗaga kai, sai naga Abba ya shigo hannunsa riƙe da flask ɗin abinci. Na yi yunƙurin tashi daga gadon, sai ya ɗaga min hannu cikin kulawa ya ce “Zauna kawai, autata. Kada ki matsa wa kafarki, kinga tana buƙatar sauki. A hankali ne komai zai daidaita. Bari na shirya miki abinci mu ci tare.”
Na lumshe ido na ce “To Abba.” Cikin kulawa ya buɗe flask ɗin ya zuba min abinci a plate, sannan ya zauna kusa da ni muka fara ci tare. Abincin yayi daɗi sosai, kuma zuciyata ta cika da farin ciki da wannan kulawar tasa.
Da muka kammala, Abba ya tattara kwanukan ya fita da su, daga nan ya dawo ya tsaya a gefen gadona yana murmushi ya ce “Auta, gobe zan aika tailor ya zo ya ɗinka miki sabbin kaya. Ina so ki gayamun komai dakike bukata. Na kasa boye farin cikina, sai na ce cikin jin daɗi “Na gode sosai Abba, Allah ya saka da alheri.” Sai ya ɗan shafa kaina cikin tausayawa, sannan ya ce “Sai da safe auta, ki kwanta ki huta. Allah ya kare ki.” Da haka ya juya ya fita cikin natsuwa, ya barni cike da farin ciki da nutsuwa.
Bayan fitar Abba daga ɗakin, sai wata kewar Bashari ta cika zuciyata tamkar an shigar min da wuta mai ƙona rai. Na lumshe idanu, hoton yadda yake rungumeni yana tsaye a cikin tunanina. Wani lokacin sai in ji kamar hannunsa ya zagaye ƙirjina yana kwantar da ni a bisa kirjinsa. Na tuna yadda yake sumbatata cikin kauna, har sai da numfashinsa ya gauraye da nawa.
Muryarsa da ke kira na da kalmar da ya fi so
“Yar kwalisa ta…” ta dawo min da ƙarfi a kunnuwana. Sai hawaye suka zubo ba tare da na iya tsayar da su ba. Na fashe da kuka mai ƙarfi, zuciyata na tafkawa da nauyin tunaninsa.
A wannan daren ban yi ƙoƙarin mantuwa ba, sai dai na zauna ina yi masa addu’a “Ya Allah ka yafe wa Bashari, ka sanya kabarinsa haske, ka bashi hutun da babu damuwa ko ciwo. Ka yafe masa laifukansa, ka kuma saka masa da aljanna domin kaunar da muka yi a duniya.” Na ji kamar zuciyata na karyewa idan na tuna da irin soyayyar da muka gina tare. Ina ji a zuciyata tamkar da ace yana nan raye, duk wahalar rayuwa zata yi sauƙi a gabana.
Sai kawai wani sabon tunani ya taso a raina yaya babansa zai ji idan har ya sani cewa ya mutu? Wannan tambayar ta ƙara zubar min da hawaye, zuciyata na bugawa da sauri kamar zata fito daga ƙirji.
Abba bai ce min an zo daga garinsu ba, bai kuma ambaci sunan babansa ba, hakan ya sa har yanzu zuciyata tana cike da fargaba da tambayoyi da ban samu amsar su ba.
Nana hadiza
09030569336
[28/08, 2:27 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SHA BAKWAI
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Dubai
A cikin Burj Al Arab Jumeirah, ɗaya daga cikin manyan hotel ɗin da suka fi tsada a duniya, inda ɗaki ɗaya yake kai wa dubban dirhams a daren guda, Ayshatu ta shigo. Haske mai walƙiya daga fitilun ya cika babban falon hotel ɗin, ga ƙamshin turaren ƙasaita na Oud & Amber da aka watsa.
Tana cikin shigar alfarma mai ɗauke da kaya na designers daga Milan, fuskarta a rufe da niqab, a hankali ta murɗa ƙofar ɗakin presidential suite ta shige ciki. Duk wata alama da zata iya nuna wucewar ta ta toshe, domin babu wanda ya kamata ya san inda take.
Tana bude daƙin Alhaji Muqaddam ya fizgota da sauri, kamar mai jiran ta tsahon shekaru. Ya aza mata wasu lafiyayyun sumbata masu ɗauke da sha’awa, itama tana mayar masa da su da ƙarfi. "Am missing you sosai," ta faɗa da wani salo mai sanyi. Shi kuma cikin murya mai izza ya ce "Na fi missing dinki, madarata. Kin ƙara kyau sosai, kin zama princess ɗin Dubai." Ta saki murmushi tana ce masa
"Kai ma kayi kyau sosai, kai ne kadai kake ƙara tabbatar min da darajar mace a idona." Sannan ta rungume shi sosai kamar wacce ta rasa mafaka. A cikin ɗakin Presidential Suite na Burj Al Arab, suka nutsa cikin duniyar alfasha, suna mantawa da aure, da Allah, da darajar rayuwa.
Bayan sun fito daga wanka, dakin ya cika da ƙamshin sabulun Dior Sauvage da turaren Chanel No.5 da Ayshatu ta shafa. Jikinsu har yanzu yana ɗauke da dumin ruwa da shauƙin kusanci.
Alhaji Muqaddam ya tsaya yana kallonta da wata irin sha’awa da alfahari. Hannunsa ya kamo kugu nata, ya matso kusa sosai, ya saki wata ƙaramar muryar izza
"Madarata... kin yi fresh sosai. Kin ƙara kyau, kin ƙara kiba. Wallahi kin zama cikakkiyar sarauniya."
Ayshatu ta ji zuciyarta ta ƙara narkewa da wannan yabo. A hankali ta juyo gaba ɗaya, ta zame kanta cikin ƙirjinsa, ta rungume shi da ƙarfin gaske tana furta "Mine... kasan me? So nake kawai mu kasance tare har abada. Kai ne farin cikina, kai ne duk abunda zuciyata ke nema."
Sai ya saki murmushi mai cike da izza, yana kara murɗe kanta cikin ƙirjinsa, sannan ya ce da murya mai cike da ƙuduri "Ki kwantar da hankalinki Aysha. Kwanan nan zakiga yadda As’ad zai dawo ƙasa. Ba zan barshi ya mareki ba tare da fansa ba. Yau dinnan zan rama miki marin da ya yi miki."
Cikin murmushi mai cike da jin daɗin ƙauna da shauƙi, Ayshatu ta ɗaga kai tana kallonsa idanuwa cikin idanuwa, tace:
"Me zakayi masa? Kasancewar kai da abokai ɗaya fa..."
Kafin ta ƙarashe, sai ya sa yatsansa a labbanta cikin salo, ya ce "Shhh... karkice komai babyna. Kin ji? Abun da zan yi masa sai ki gani da idonki. Ni ban yafe wa wanda ya taba ki ba, kuma As’ad zai gane darajar ki ta fi wacce ya taɓa zato."
Sai ya sumbaci gashinta, yana ƙara murɗe jikinta a jikinsa, zuciyarta kuma cike da jin daɗin samun wani namiji da ke nuna darajarta fiye da komai.
A gaggauce Ayshatu ta nufi wardrobe ta zaro rigarta ta fara shiryawa cikin hanzari, tana gyara mayafinta da niqab ɗinta ta kalli Muqaddam da murmushi mai ɗauke da ɗan tsoro.
"Babyna, bari na wuce yanzu kafin As’ad ya zargi wani abu, kin san shi ba ya yarda da jinkiri," ta faɗa a hankali tana ƙoƙarin shawo kansa.
Cikin ɓacin rai ya nufi gaban madubi ya zuba mata ido, sannan ya ɗauki glass ya kurɓi ruwan juice mai sanyi. Ya ce da wata murya mai nauyi:
"Madarata, every time kina barina haka da gaggawa, kina barni da jin babu ke a jikina. Yanzu ma sai kice As’ad… wane As’ad? Me ya isa yake yanke miki hukunci a kaina?"
Ta ƙarasota kusa da shi ta rungume hannunsa, ta tura kanta a ƙirjinsa tana ɗan murmushi:
"Ka kwantar da hankalinka babyna. Kai ne zuciyata gaba ɗaya, kai ne komai na. Amma in na yi jinkiri, zai fara tambaya, kuma banason ya fara zargi."
Ya ɗan saki ajiyar zuciya, ya rungumeta da ƙarfi kamar bai son sakinta. Sai da ta lallaɓe shi da kalamai masu taushi, tana sumbatar hannunsa da kuma lallaba harshensa da murya mai laushi.
"Ka yi haƙuri babyna, zan dawo very soon. Just wait for me."
Daga ƙarshe ya ɗan murmusa ya ce:
"Okay, amma wallahi Aysha, ba zan bari wannan mutumin ya yi wasa da soyayyarmu ba. Zan nuna masa waye ni. Kin ji?"
Ta ɗaga kai cikin lallashi:
"Na ji Babyna, amma don Allah ka bari komai ya kasance a hankali. Ka san bana son tashin hankali."
Sai ta saki jikinsa da kyar, tana kalle-kalle cikin fargaba, sannan ta fice daga ɗakin cikin gaggawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi.
Shi kuwa Muqaddam ya tsaya da hannunsa a aljihunsa yana kallon ƙofar da ta rufe, murmushin mugunta ya bayyana a fuskarsa:
"As’ad… kai kaɗai nake jira. Zan nuna maka cewa akwai wani da ya fi ka iko, kudi, da soyayya.”
Ɗaya daga cikin manyan gidajen As’ad Babangida dake cikin Emirates Hills, Dubai wuri ne da ake kira “Beverly Hills of Dubai”, inda manyan attajirai da shugabannin kasashe ke da gidaje. Gidan As’ad katafaren palatial mansion ne mai hawa uku Private swimming pool mai nisan mita 25 da ke kallon Burj Khalifa daga nesa. Helipad a saman rufin gidan, inda private helicopter dinsa ke sauka daga Dubai International. Babban garage ɗin da ke ɗauke da manyan motoci irin su Rolls Royce Phantom, Lamborghini Aventador, Bugatti Chiron, da kuma Maybach S680.
A cikin gida kuma akwai cinema hall mai kujeru 20, indoor gym & spa, da kuma art gallery cike da zane-zanen Picasso da Da Vinci originals. Yau dai dawowarsa kenan daga wani babban meeting da ya shiga da board of directors a Dubai Financial Centre, wanda ya shafe tsawon sa’o’i yana tattaunawa akan multi-billion dollar oil deal.
Yagaji , ya watsa ruwa a bathroom nasa da aka yi da Italian marble & gold finishing, sannan ya fito yana goge jikinsa da fararen tawul masu ɗan ƙamshi.
Ya sanya designer robe daga Versace, sannan ya nufi private wardrobe room nasa wanda ya cika da kayan Armani, Louis Vuitton, da Tom Ford suits.
A karo na uku ya duba Patek Philippe Grandmaster Chime agogon hannunsa mai daraja yana tsaki saboda Ayshatu bata shigo ba har yanzu.
Zuciyarsa na raya masa, “Ko dai ta je wajen ƙawarta kamar yadda ta gaya? Ko akwai wani abu da bata faɗa min ba? Kuma me yasa zuciyata ke cike da rashin kwanciyar hankali yau?”
Ya janyo gilashin w decanter nasa wanda aka yi da crystal Swarovski, ya zuba sparkling grape juice yana juyawa a hankali, idanuwansa na kallon hasken birnin Dubai ta cikin gilashin window mai girma wanda ya mamaye fuskar bedroom ɗin.
Ƙarar wayar As’ad ce ta cika ɗakin. Ya ɗaga kansa ya kalli golden Vertu phone ɗinsa da yake kan mahogany side table. Sunan PA dinsa ne ya bayyana. A hankali ya ɗaga wayar.
“Sir, Doctor Ibrahim is on the line, he wants to do a video call with you immediately,” cewar PA cikin ladabi.
As’ad ya kalli agogon hannunsa mai darajar miliyoyin daloli, ya ɗan jinjina kai sannan yace, “Okay, patch him through.”
Nan take screen ɗin wayar ya sauya zuwa video call. Fuskar Doctor Ibrahim, babban consultant daga asibitin da As’ad ke kula da lafiyarsa a London, ta bayyana. Bayan gaisawa cikin ladabi da mutunci, Doctor ya fara magana cikin yanayi na professionalism.
“Alhaji As’ad, mun sake nazari akan gwajin da muka ɗauka kwanan nan. Binciken ya nuna cewa gaba ɗaya lafiyar jikinka kalau ce. Dukkanin results ɗin sun fito normal. Ba mu ga wata matsala ko ɗaya ba.”
As’ad ya jingina da kujerar Italian leather armchair ɗinsa, idonsa ya kankance. Ya ɗan yi shiru kafin ya amsa da ƙasƙantar murya:
“Doctor, how come? Kusan shekara guda kenan gabana is not working. Duk yadda na gwada, babu wani alamar normality. How do you explain that?”
Doctor ya ɗan gyara glasses dinsa, yana sauke ajiyar zuciya.
“Wallahi gaskiya, Alhaji, babu wani medical cause da muka gano. Duk tests sun nuna everything is fine. A ganina wannan al’amari zai iya zama ne daga psychological blockage, ba daga lafiya ba. Maybe stress, maybe emotional factor. Amma medically, kalau kake.”
Ƙasan zuciyar As’ad ta buga. Ya ɗauki gilashin nasa ya juya sparkling juice ɗin da ke ciki, ya ɗan ɗaga idonsa sama kamar yana tattaunawa da kansa.
“Ina nufin for a whole year… na rayu da wannan disgrace, kuma ku kuka ce lafiya kalau?”
Doctor ya sake jaddadawa cikin nutsuwa
“Yes, medically, you are healthy. Ba mu ga wata matsala ba.”
As’ad ya numfasa sosai, ya murɗa cufflinks dinsa masu lu’ulu’u kafin yace cikin salo na karfin hali “Alright, Doctor. Thank you. Just keep monitoring. Zamu sake magana soon.”
“Of course, sir. Allah ya kara lafiya.”
Suka yi sallama. Wayar na kashewa, As’ad ya jingina da kujerar, idanuwansa suka zame masu nauyi.
Nana hadiza
09030569336
[30/08, 7:17 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SHA TAKWAS
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
As’ad yana zaune a cikin babban mahogany office desk ɗinsa, MacBook Pro a gabansa yana danna wasu confidential emails na kasuwanci. Idanunsa na cikin sharp focus, hannunsa ɗauke da Montblanc pen, glass ɗin sparkling water yana gefe.Sai kawai ƙarar Louboutin heels ɗin Ayshatu ta fara ratsawa a cikin babban ɗakin, tana takawa cikin classic elegance. Da zarar ta buɗe ƙofar, ƙamshin turarenta ya cika sararin, yana haɗuwa
da ƙamshin oud da As’ad ya saba amfani da shi. As’ad ya ɗago kai daga system ɗinsa, idanunsa suka sauka kanta kai tsaye.
Ya bita da kallo tun daga sanda ta fara takowa har ta ƙaraso. Wani abu ya tsaya masa a rai ƙamshin turaren. Ba irin wanda ya saba ji a jikin Ayshatu ba. Wannan yana da ƙarfin gaske, mai ɗaukar hankalin maza,
kuma idan ƙwaƙwalwarsa bata masa karya ba, wannan kamshi for men exclusive collection ne daga Tom Ford.
Ya jingina da kujera, yana ci gaba da kallonta cike da izza, da nutsuwar mutumin da yake da
dukiya da iko amma yana da doubts a zuciyarsa. Ayshatu ta yi murmushin da ke ƙoƙarin narkar da shakku, ta ce cikin sanyi
“Habibie… dan Allah ka yi hakuri. Mun je kallo ne a cikin Dubai mall, nasan kanata jirana… kawai wanka nayi na shigo.”
As’ad ya ɗaga gira daya, idonsa na zare mata a hankali cikin suspicious charm. “Did you… change your perfume ne?” Ayshatu ta ɗan gyara tsayuwa, zuciyarta na bugawa da sauri kamar tana ji da kansa zai iya karanta ranta. “No… ban canza ba. Kawai na friend dina ne na fesa.”
Shiru ya biyo baya. As’ad ya ɗan ƙurawa idanunsa a kanta, ya ɗauke idanu kamar wanda bai damu ba. Sai kawai ya maida kallonsa kan screen ɗinsa, ya lumshe ido da ƙaramin murmushin da ba zai fassaru ba.
“Okay…”
Amma a zuciyarsa, wani tunani ya tsaya “Friend? Wacce irin abokiyar da zata fesa turaren maza? Kuma ita Ayshatu, wacce bata son turare mai ƙarfi…” Ya ci gaba da danna system ɗinsa, amma zuciyarsa tana ta ƙirƙira tambayoyi masu nauyi, yayin da Ayshatu ta zauna kusa da shi tana ƙoƙarin nuna kulawa, tana son ta ɓoye raunin sirrin da take ɗauke da shi. Ayshatu ta takarƙare kafarta ta haye gefen kujera, ta jingina da As’ad cikin salo na romantic petting.
Hannunta mai taushi ta shimfiɗa akan kafadarsa, sannan ta ƙara kusanto shi, tana shakar ƙamshin turarensa da murmushi
“Habibie… baƙin cikin ka yana sa zuciyata ta tsinke. Na fi son ganin ka cikin farin ciki.” Ta furta cikin rauni, tana lumshe idanunta tana manne kanta a ƙirjinsa.
As’ad ya dan lumshe ido, yana jin ƙamshin nata da ya gauraye da nasa, amma zuciyarsa bata daina yi masa tambayoyi ba. Duk da haka, sai kawai ya ɗan janyo ta da hannunsa guda, ya kwantar da ita jikinsa, yana shafa gashinta a hankali. “Ki kwantar da hankalinki Aysha…” Ya furta cikin murya mai nutsuwa. “Ni fa bana so kina ɓata min rai da waɗannan tafiyoyi naki. Kin san bana son jiran ki ba tare da dalili ba.”
Ayshatu ta ɗan tura bakinta kamar yarinya tana romantic complain “Wlh ban yi nufin ɓata maka rai ba Habibie… kai ka sani, komai naka nake so. Kai ne nake so in gani kullum… Kai ne zuciyata ta ɗaure da kai.” Sai ta ɗago kanta ta ɗan zuba masa ido, kamar yarinya mai neman assurance. “Ka yafe min, please?”
As’ad ya yi shiru na ɗan lokaci, yana kallon idanunta. Yasan kalamanta suna da saukin narkar da zuciya, amma suspicion ɗinsa bai shuɗe ba. Sai kawai ya ɗan yi murmushi, ya ce “Hmm…kin iya lallashi sosai Aysha.”
Ta yi dariya kaɗan ta sake rungumesa tana masa wasa da wuyan rigarsa “Babu wani taimako da nake buƙata sai daga gareka. You’re my everything.” Ya juyo ya kalleta sosai, kamar yana so ya karanta zuciyarta. Amma daga karshe sai ya ɗan janye kai, ya ce cikin murya mai sanyi “Good. Amma ki sani duk wani abu da zai kawo cikas tsakanina da ke… bana son shi, Aysha.” Cikin sauri ta ɗora yatsanta a bakinsa tana cewa “Shhhh… babu wanda zai iya rabani da kai. Wallahi.” Sai ta yi kissing lips ɗinsa a hankali, tana ƙoƙarin narkar da duk wani shakku da zai iya kasancewa aransa.
hannunsa kan laptop yana tura wasu emails. Sai wayoyinsa gaba ɗaya suka fara ringing lokaci ɗaya daga landline, daga iPhone, da kuma daga kan work phone nasa.
Ayshatu ta juyo daga gefe tana kallonsa, zuciyarta na matuƙar bugawa. Ta daɗe tana saurarawa kafin ta furta da lallashi “Please Habibie… ka ɗauka mana, watakila abu ne mai muhimmanci.”
As’ad ya ɗan harareta da ido mai nauyi, amma yana ganin cewa kira na ta maimaituwa, sai ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyin. Ganin lambar Hajja ce ya dan saki numfashi mai nauyi, sannan ya ɗaga.
“Assalamu Alaikum Hajja, Allah ya ƙara miki lafiya. Aiki ne ya ɗan tsayar dani…”
Muryar Hajja ta fito daga wayar, cike da gaggawa da ɗan rawar murya
“As’ad, ka dubi labarai yanzu, ka tabbatar min da abinda ke faruwa. Wannan al’amarin ya shafi gida sosai.”
As’ad ya ɗan ja numfashi, zuciyarsa na bugu da ƙarfin gaske. Ya danna mute a wayar sannan ya kalli Ayshatu, idonsa ya ƙanƙance.
“Ayshatu… On the TV. Right now.”
Ayshatu bata yi wata-wata ba ta miƙe da gaggawa, zuciyarta kamar ana murƙushe ta. Ta ɗauki remote ta kunna TV plasma ɗin dake bango. Nan take tashar Al Jazeera News ta bayyana da rubutun ja mai girma
🔴 Breaking News
Ayshatu ta tsaya cak, hannunta na rawa, idonta akan screen ɗin. As’ad kuwa ya jingina da kujerarsa, idanunsa suka cika da zafi da tambaya.
“US AUTHORITIES SEIZE DRUG CARGO LINKED TO BILLIONAIRE BUSINESSMAN, AS’AD BABANGIDA.”
Camera ta nuna babban tashar jirgin ruwa ta Amurka inda aka jibge manyan containers guda uku da aka cike da kayan As’ad na kasuwanci. A cikin rahoton an ce Kayan an nuna cewa furniture da luxury cods ne daga Dubai → USA. Amma binciken US DEA (Drug Enforcement Agency) ya gano akwai manyan miyagun ƙwayoyi (cocaine da heroin) a cikin wasu akwatunan. Sun bayyana cewa shipping documents da company seal ɗin As’ad ne ke jikin containers ɗin.
Ayshatu ta firgita, jikinta ya yi sanyi. Ta zuba ido cikin tashin hankali tana kallon As’ad.
As’ad ya mike tsaye da karfi, zuciyarsa ta yi wani irin bugu. Murya na rawa yace
“This is impossible… this is not my cargo! How dare they put my name in this mess?”
Ya ɗauki wayarsa ya kira lawyer dinsa kai tsaye, yana huci da fushi.
Lawyer ɗin “Sir, calm down. This looks like a serious frame-up. The documents were hacked somebody altered your shipping line code. We have to move fast, otherwise the US government will press charges.”
Ayshatu ta matso kusa da shi da rawar murya “Habibie… wannan fa babban abu ne. Idan Amurka ta tabbatar, ba wai kuɗi kaɗai ba, rayuwarka gaba ɗaya zata shiga haɗari. Wane yayi maka wannan mugunta?”
As’ad ya runtse idanu, zuciyarsa ta soma cike da tuhuma. A ransa ya fara zargin wani daga cikin manyan abokan kasuwancinsa.
“Wallahi duk wanda ya shigo cikin harkata ya yi min wannan setup, zan tona masa asiri. I’m As’ad Babangida I don’t fall that easily.”
Wayar As’ad ce ta shiga ringing babu kakkautawa babban layin da ke da taken Private Line Royal.
Ya ɗan kalli screen ɗin, zuciyarsa ta ɗan tsinke da dukan da bai saba da shi ba Mai Martaba ne ke kira. Idanunsa suka yi jajir, ya haɗiye wani irin zafi a makogwaro saboda ciwon kai da ke masa illa tun tunanin labaran da ya gani a TV.
Cikin ladabi da girma, ya ɗaga wayar ya ɗora a kunnena. “Assalamu alaikum Mai Martaba.”
Mai Martaba yace
“As’ad, how true are these rumours? Labaran da ke yaduwa yanzu suna iya illata martabar mu gaba ɗaya.”
As’ad ya runtse ido, ya daure fuskarsa kamar jarumi.
“Mai Martaba, wannan ma ba kayana bane. Just a setup ne kawai. Somebody is working against me.”
An ɗan yi shiru, sai murya mai nauyi da izza ta dawo daga wayar “Then work for it right away. Na baka lokaci As’ad. Do not fail me. You understand?”
“Yes, Mai Martaba. I promise. Insha Allah zan warware wannan cikin gaggawa.”
“Good. Be strong, my son. Ka tuna, ba kai kaɗai kake da alhakin wannan ba – akwai tarihi, akwai mutunci da ake karewa. Do not let me down.”
Sai kiran ya katse. As’ad ya jingina da kujerarsa, idonsa ya ɗaure kamar wanda ke shirin shiga yaƙin duniya. Hannunsa ya ɗan goge gumi daga goshinsa sannan ya kalli Ayshatu da ta kasa zaune ta kasa tsaye, jikinta har rawa yake.
Nana hadiza
09030569336
[30/08, 7:17 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA SHA TARA
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
As’ad ya miƙe da ɗan sauri, ƙirjinsa yana ɗauke da nauyin tunani. Ayshatu dai tana zaune tana kallonsa, idanuwanta cike da hawayen da suka ki zuba.
Ya isa gaban locker ɗin ƙarfe mai ƙirar zamani, ya murɗa code ɗin tsaro sannan ya buɗe shi. Wata sabon waya mai tsada wacce har yanzu ba a cire lakabin gilashinta ba ya ɗauko.
A sanyaye ya kunna wayar, ya rubuta wani lamba da hannunsa mai sanyi amma cike da izza. Da aka ɗaga kiran, muryarsa ta fito da ƙarfi, babu wata alamar tausayawa “Ina so cikin mintuna goma sha biyar a haɗa mun meeting , inda aka ajiye containers ɗina yanzu haka. Kuma ku tabbatar da an yi connecting da dukkan tashoshin labarai na duniya kafin na iso. I need the truth live.”
Ya kashe wayar da ƙarfin gaske, ya jefa ta saman teburin mahogany ɗinsa mai sheƙi, sannan ya jawo dogon numfashi kansa na mugun sarawa.
Ayshatu na jin waɗannan kalamai, jikinta ya yi sanyi sosai. Zuciyarta ta buga, hawaye suka fara zuba da sauri. Bata iya cewa komai ba sai kuka mai sauti, sannan ta mike a guje ta fita daga ɗakin.
As’ad ya bita da idanu masu zurfi, ya dafe gashin kansa, zuciyarsa na karanto alamu da dama tsakanin soyayya da shakku, tsakanin ikonsa na duniya da raunin zuciyarsa ga ita.
Tana fita da hawayenta, ƙamshin turarenta na nan yana ratsa dakin, Umar ɗan As’ad, ya shigo hannunsa riƙe da iPad ɗin nan mai sirri. Fuskar sa ɗauke da damuwa amma a lokaci guda akwai nasara a idanunsa.
“Dad,” Umar ya kira shi cikin murya mai nauyi, yana mikar da iPad ɗin, “nayi bincike a kan CCTV footage ɗin da aka nuna a TV. Wannan mutumin da aka gani yana shiga hotel ɗin… shine wanda ya saka kayanka cikin container. Amma gaskiyar ita ce”
Ya ɗan dakata, ya shaki numfashi sannan ya ci gaba “ba naka kayan bane Dad. Yanzu haka an tabbatar a news platform cewa kayan babban Minister na USA ne aka shirya a saka maka, domin a jefa ka cikin international scandal.”
Jikin As’ad ya tsaya cak, ya ɗaga kansa ya kalli ɗansa. Numfashinsa ya yi nauyi, amma zuciyarsa ta fara samun wani sanyi na relief. Ya jingina da kujerarsa, hannunsa ɗaya ya rufe gashinsa kamar wanda aka sauke dutse daga zuciyarsa.
“Alhamdulillah…” ya furta a hankali.
Sai kuma ya ɗaga ido cikin izza ya kalli Umar:
“Good job, son. Wannan shine dalilin da yasa nake son ka kasance kusa da ni. You’re sharper than half of my security team.”
Umar ya dan murmusa kadan, amma cikin seriousness yace “Dad, wannan magana ba tq wasa bace. Mutumin da ya shirya hakan ya shiga kai tsaye cikin Muqaddam ne. Dukkan alamu suna nuna shi ne mastermind. Kuma yanzu haka kafafen yada labarai suna kan haka cctv footage.”
As’ad ya yi shiru na dan lokaci, idanunsa suka koma kan wall-sized window da ke fadin dakin, yana kallon yadda Dubai skyline ke kyalli da fitilu. Ya ji zuciyarsa ta kara tafarfasa.
“Muqaddam…” ya furta cikin sanyin murya amma cike da zafi, “Yayi kuskuren da bai kamata ya taba yi ba. Ya dauka zan zuba ido in bar shi ya bata sunana? No… yanzu zan koya masa me ake nufi da shahara da iko.”
Umar ya dan gyara tsayuwa yana kallon mahaifinsa da girmamawa, amma ya lura da wani abu.
As’ad ya tsaya kallon su ta hanyar hologram connection, ya ɗaga hannunsa alamar jin daɗi. “Kun bani hujja ta gaskiya. Yanzu case ɗin gaba ɗaya ya juye. Daga kaina ya koma ga minister ɗin da suke yi min adawa. CCTV ɗin da aka fitar ta nuna a fili cewa ba ni bane kayansu ne suka saka min a boye. Aljazeera ma ta gyara rahotonsu yanzu.”
Sai aka sauya camera zuwa tashar TV da ke nuna sabon breaking news
“Hukumar tsaro ta tabbatar cewa an samu kuskurin bayanai a rahoton farko. Bincike na nuna kayan ba na Alhaji As’ad bane, sai dai na wani daga cikin ministocin gwamnati da ke cikin jerin masu adawa da shi. CCTV footage ya nuna cewa sun shirya shigar masa da kayan don bata masa suna.”
Umar ya jingina da kujerarsa yana murmushi.
As’ad ya janye hannunsa daga kan table ɗin, ya ɗan ɗaga glass ɗinsa mai cike da ruwan sanyi, idanuwansa suna haskawa da nasara.
“Game over. This is my empire, and nobody can break it.Allah baya bacci and addu'ar uwa ba karya bace ba.”