Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 8
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 8: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 8. As’ad ya janye kujerar da yake zaune yana kallon ƙofofin falon,…
4,492 words
As’ad ya janye kujerar da yake zaune yana kallon ƙofofin falon, zuciyarsa cike da ɗimauta. Sai kawai ya ga Nawal da Aminatu 'ya’yansa. Idanunsu duk jajaye ne saboda kuka da tashin hankali, amma duk da haka, sun kwaikwayi ƙarfin hali suka yi murmushi.
Da sauri suka nufi wurinsa, suka rungume shi daga gefe biyu suna fadin
“Dady… Alhamdulillah.”
Sai zuciyar As’ad ta lafa da wani irin sanyi. Ya lumshe idanu, ya rungume su ƙarfaf ba tare da cewa komai na ɗan lokaci ba. Daga bisani sai ya ce da murya mai ƙarfi amma cike da tausayawa “Wannan shi ne amfanin ilimi da nake so ku rike. Kafin jami’an tsaro suyi wani abu, kun riga kun yi amfani da basira da hikima. Allah ya yi muku albarka. Allah ya tsare ku, ya albarkace ku.” Suka ce tare cikin muryoyi masu rawa:
“Amin.” Daga nan Nawal ta ɗago da idonta masu cike da hawaye ta ce “Papa… nasan mamah hankalinta ya tashi sosai ko?”
As’ad ya juyo da kallonsa kan 'yar tasa, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Bai so ya nuna rauninsa a gabansu ba, amma muryarsa ta nuna ƙaunar da ke cike da zuciyarsa “Eh, princess. Hankalinta ya tashi, kamar yadda dukkan zuciyata take a tashe. Sai ya sake rungumarsu yana jinjina kansa cikin shukura.
***
Da ƙyar Ayshatu ta isa hotel ɗin, jikinta na rawa, zuciyarta na ƙaƙarƙarwa. Tana jin kamar numfashinta zai tsaya saboda tashin hankalin da ta shiga masoyinta, Muqaddam, ya shiga wani babban haɗari, kuma ita kaɗai tasan abin da hakan zai iya haifarwa.
Tana kuka sosai ta tura ƙofar presidential suite ɗin ta shige ba tare da ta nemi izini ba. Muqaddam na tsaye, yana sanye cikin farin singlet da wando mai kyau, hannunsa riƙe da gilashin lemo, kamar mai jiran labari.
Cikin masifa, idanunta jajir, Ayshatu ta rufe fuskarta da tafukan hannaye sannan ta fashe da ihu “Muqaddam why??!! Me yasa?? Me yasa zaka saka kanka cikin wannan tashin hankali?! Me yasa zaka je kai tsaye ka tsaya gaban As’ad??! Bakasan karfin ikon sa ba?! Ba kudi kaɗai yake dashi ba yana da kujerar sarauta, yana da suna, yana da jama’a a bayansa! Har yaushe zaka raina shi?! Shine ubangidanka dashi kayi arzuki kamanta shi ke baka kaya?”
Ta rufe fuska tana kuka sosai, muryarta tana rawa. “Wannan ai ba wasa bane! Akan wani dalili zaka saka masa wannan abu a kaya?!! To yanzu ga shi abun ya juye, ba shi aka kama ba… minister Ocho ka tsunduma, kuma dukkan al’amura sun bayyana akan yaranka. An kama yaronka Muqaddam! An kamo shi da hujjoji!!”
Cikin wani irin tashin hankali, Muqaddam ya juyo da sauri, gilashin da ke hannunsa ya kusa zamewa saboda rawar hannunsa. Ya ajiye shi kan counter, idanunsa sun ƙanƙance da fushi da rikicewa.
Ya ɗan yi shiru kamar wanda aka dakile masa tunani, kafin ya buɗe baki a hankali, muryarsa ta yi sanyi amma cike da girgiza kai “Ayshatu… wace irin magana ce wannan? Me yasa kike kuka haka? Kin san me kika faɗa kuwa?”
Yana ƙarewa ya matso kusa da ita, hannunsa ya riƙe kafadarta, idanunsa suka zuba a nata yana neman amsar da zuciyarsa ta kasa haɗawa.
Ayshatu ta kalli Muqaddam da idanuwanta cike da damuwa, numfashinta na nauyi. Tana riƙe hannunsa tana girgiza shi da ƙarfi kamar wacce zuciyarta ta karye.
“Please, Muqaddam, ka kunna TV ka gani da idonka. Idan As’ad ya iya barinka, wallahi mahaifinsa bazai taɓa barinka ba. Kana so ka jawo mana matsala a wannan lokacin ne? muna cikin jin daɗi, sai ka jawo mu cikin tashin hankali.”
Ta ɗan ja numfashi kafin ta ƙara magana da rawar murya
“Ka fahimta sosai… kayan nan ba Nasa baniba! Na san minister ko chairman ne suka saka hannu. Idan suka fara bincike, ka tabbata cewa kai ne farkon wanda za su nemi. Yanzu fa sun fallasa containers, ka san me hakan yake nufi? They are after you, Muqaddam!”
Alhaji Muqaddam ya tsaya kallonta da idanun da suka cika da izza da ƙarfi. Bai ce komai ba sai wani siririn murmushi ya bayyana a fuskarsa.
“Ayshatu…” ya furta a hankali, murya mai ɗauke da natsuwa amma cike da tsoro “Na ɗauki hukunci ne bisa shawarar kaina. Wannan ya zama dole saboda adawar As’ad da ni ta kai matakin da ba za a iya komawa baya ba. Idan ban nuna masa waye Muqaddam ba, zai ɗauka cewa zai iya taka ni kamar ƙaramin yaro. This is power game, baby.”
Ya ɗan matsa kusa da ita yana ɗora hannunsa akan kuncinta.
“Ba wai ban yarda da shawarar ki bane, amma akwai wasu abubuwa da bazan iya bayyana miki ba yanzu. Shawara ko ba shawara… hukuncin nan nawa ne.”
Ayshatu ta fizge jikinta da hawaye tana fadin
“No! Ba haka nake so ba, Muqaddam. Na gaya maka tun farko bana son ka shiga cikin wannan rikicin. Ina jin tsoron cewa ba wai As’ad kaɗai bane zaka yi yaƙi da shi ba yanzu mahaifinsa ma yana cikin lamarin baya ragwantawa akan ƴaƴa. You don’t know what you are up against!”
Ta ɗauki jakarta a hanzarce ta ce cikin kuka
“Am going back! Kada su nemi ni su same ni tare da kai. Please, ka tsaya a hankali ka sake tunani kasan yadda zakayi kafidda kanka nima zanyi nawa kokarin ta bangaren As'ad.”
Ta juya da gaggawa ta nufi ƙofa, zuciyarta na ƙuna, tana jin soyayyarta gareshi ta naƙude da tsoron rikicin da zai iya biyo baya.
Nana hadiza
09030569336
[01/09, 8:30 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ASHIRIN
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Ayshatu tana karasa shigowa private wing ɗin gidan As’ad wani ultra-modern glassy mansion mai dauke da gilasan floor-to-ceiling, ƙamshin turaren oud ya daki hancinta. Bangaren ya cika da soft lights masu launin ja kujerun Italian leather sofas suna kyalli da kyau, sai Persian rugs masu laushi da aka shimfiɗa Akasa gurin sai ɗaukar ido yake basai ankaika da long easy ba kasan wannan rayuwa ce ta multibillionaire.
Sai ta hango unar dake shirin fita sai Nawal da Amina suna gefen As’ad, suna zaune cikin kalar tufafi baki masu sheƙi. Ganin Ayshatu ya sanya su tashi da hanzari, suka rungumeta suka fashe da kuka.
“Allah ya tsare dady mamah kina ganin sharin da akayi masa,” suka maimaita cike da tausayin yadda ake ƙoƙarin yi masa sharri. Ayshatu, duk da ta shiga cikin rungumar su, kukan da take yi ba saboda As’ad bane sai kawai ta kasa jurewa tunanin kamun Alhaji Muqaddam, wanda yanzu labarinsa ya fara cika duniya.
Ta ƙarasa wajen As’ad cikin shashekar kuka,cike da makirci da kissable ta zube a jikinsa tana rungumesa da ƙarfin gaske. “Habibie… please, kayi hakuri. Ka bawa Mai Martaba hakuri, koma wanene ya aikata wannan, ka barshi da Allah. Please Habibie…”
As’ad, cikin nutsuwar gentleman billionaire, wanda ko da yake duniya na kaɗawa yana iya sarrafa motsinsa, sai ya ɗaga hannunsa ya goge mata hawayenta da yatsunsa masu santsi. “Stop crying…” ya faɗa da murya mai nutsuwa, cikin murmushi mai ɗauke da kwarjini. “Komai ya huce. The case is already in the hands of hukumomi. Banda iko da shi yanzu.” Sai Ayshatu ta sake fashewa da kuka, tana furta “Wanda yaso cutarmun dakai bai kyauta ba, habibie…” As’ad ya sake kallonta, idanunsa suka yi laushi amma har yanzu akwai ɗan izgilin sirri a cikinsu. Ya janye jikinsa kaɗan daga nata, yana miƙewa tsaye cikin tsadaddun kayan home-wear nasa custom-made loungewear da aka ɗinka masa daga Silk Armani. “Ki huta. Kibar kuka. Zan fita yanzu. Anjima zamu yi magana.”
Ayshatu, tana share hawaye, ta amsa da “Okay…” cikin murya mai sanyi. Ta fita, su Nawal kuma suka bi bayanta bayan sun sallama da mahaifin nasu sannan suka bi bayanta suna ƙoƙarin rarrashinta. Ko da suka shiga bangaren mata na Ayshatu ce ta fara da murya mai ɗauke da masifa "You’re free to go home, or leave me alone. I just need some peace. Sai ku cigaba da fakewa da ubanku, nasan ke Amina, ke kika shigar da bincike ko?" Amina ta kalleta cikin mamaki tana mai rik’e hannun kanwarta Nawal, murya cike da takaici tace "Yanzu Mama… Daddy yana cikin bala’i, baki ma kallon yadda zuciyarsa ke tafasa ba, amma zaki ce me isa nashiga maganar dadyna fa mahaifina why are you changing mamah muna nan muna tunanin sai kinfi kowa damuwa but..? Wallahi Mama, wannan magana taki ta yi tsauri."
Nawal kuwa ta ja dogon numfashi, ta girgiza kai, tana jin zafi. "Let’s go sis… Mama kamar ma haushinmu take ji. She doesn’t care. We’re just wasting our breath." Mamah ta harare su da idanunta da suka canza saboda kuka, ta dafe hannunta akan sofa mai launin royal blue na Versace design, sannan ta d’aga hannu "Yes, just go! Please I need to rest. Yara sai son ubanku na tsiya. Wani irin abune haka? Haba!"
Da fushi ta nufi bedroom ɗinta, wanda aka kawata da mahogany furniture da chandeliers masu haske irin na Swarovski, ta rufe ƙofar da ƙarfi. Tana jingina da ƙofa tana huci, zuciyarta kamar za ta tarwatse. Da gaggawa ta lalubi Vertu Signature Cobra phone ɗinta, ta danna number. Sai dai kafin ringin ya cika sau biyu, Alhaji Muqaddam ɗin nan da ake magana akansa a duniya akan shine yasanya asaka kwaya ya dauka ya ɗaga.
Ayshatu muryarta cike da kuka "Baby… yaya? Na shiga uku… na rasa me zan yi."
"Calm down, Madarata. Everything will be okay. Ni da kaina zan mika kaina, don wannan case din ba zai taba shafarmu ba. Duk abun da aka hada, zan rufe shi. I have the power, I have the men, kuma ina da manya a hannuna. Trust me."
Sai ta fashe da kuka, muryarta na rawa tana faɗin "Ni fa ina tsoro… wallahi ina tsoro."
Ya yi murmushi cikin taushi amma yana ɗauke da izza irin ta wanda ya saba da karfi da arziki "Don’t cry, my Queen. Ke dai ki nutsu. Dubai ba zata taba cinye ni ba, ina da mutane na. Nan ba da jimawa ba, zaki ga komai ya lafa kamar ba a taɓa samun matsala ba." Sai suka yi shiru na dan lokaci, daga nan ya shiga lallashinta da kalaman soyayya, kafin a karshe ya kashe wayar.
As’ad yana riƙe da sabuwar wayar da yayi kira da ita, ya rufe locker ɗin da ƙarfi, ya ɗauki car key dinsa sannan ya fice daga cikin gidan. Motarsa ce mai baƙi Lamborghini Urus ta jiransa a harabar gidan, driver nasa na tsaye gefe amma da kansa ya shiga ya zauna a sit din direba.
Ya danna starter motar ta yi gurnani mai ƙarfi kafin ta hau hanya da gudu.
Inda ya nufa kuwa ba ko'ina bane illa Private Warehouse dinsa da ke gefen tasha mafi girma ta ruwa a Dubai (Jebel Ali Port). Wannan wuri As’ad ya gina shi musamman don containers dinsa na kasuwanci ciki akwai kayan gini, kayan luxury, har ma da wasu abubuwa na sirri da ba kowa ke da damar shiga ba.
Kafin mintuna 15, security guards na wajen suka bude masa kofa. A ciki akwai CCTV control room da kuma ofishin da ya zuba manyan screens guda shida. Anan ne As’ad zai zauna yana kallon abubuwan da ke faruwa kai tsaye akan dukiyarsa da kuma labaran duniya.
Ya ɗauki numfashi mai nauyi, yana jujjuya pen a hannunsa, zuciyarsa na tafasa da tunanin abunda ya gani a TV.
Da As’ad ya gama magana a waya ya jefa wayar a kan mahogany table din dake dakin. Fuskarshi ta cika da hankali da tunani mai nauyi, zuciyarsa tana tafasa. Kafin ya sake zama kuwa sai ga Umar, ɗansa na farko ya shigo cikin nutsuwa da kamala, yana sanye da farar jalabiya mai ɗinki na alfarma, da sa’fa a hannunsa.
Umar ya tsaya yana kallon mahaifinsa na dan lokaci, kafin ya ƙarasa kusa dashi ya zauna.
“dady,” ya fara cikin ladabi amma da natsuwar mutum mai cikakken hankali, “naji magana daga wajen mutane da yawa. Wallahi lokaci yayi da zaka yanke hukunci. Ayshatu ba ta cancanta da irin kulawa da soyayyar da kake nuna mata ba. Tafi dacewa da a kaita nesa… idan har ma hakan zai shafi mutuncin gidanka, why not? Ka sake ta kawai.”
As’ad ya juyo a hankali, idanunsa suka sauka akan ɗansa, sannan ya ɗan murmusa mai cike da sanyi amma da izza.
“Umar,” ya fada da murya mai nauyi, “kada ka sake magana irin wannan a gaban. Ayshatu… itace farin cikina. Duk wanda ya san As’ad, ya san ni bana wasa da abunda ya shafi rayuwata. Ni ban taba ganin mace da zata iya kawo min kwanciyar hankali kamar ita ba. Kuma duk da shakku, duk da magana… bazai taba yuwuwa na rabu da ita ba.”
Umar ya dan daga gira, yana kallon mahaifinsa cikin mamaki da ɗan takaici.
“Amma Abba… koda kuwa hakan zai cutar da kai? Koda kuwa ta jawo maka abinda kake gujewa tsawon shekaru?”
As’ad ya numfasa mai nauyi, ya ɗan ja doguwar kujera ya jingina, idanunsa suka ɗauki ma’anar jagora mai ƙuduri.
“Ina son ka gane Umar… akwai abubuwa biyu da mutum yake bautawa a rayuwarsa Allah da kuma abin da yake so. Ni Allah ya sani, kuma ya sani zuciyata ta manne da Ayshatu. In kuwa har hakan ya zama cuta a wajenku, to ni zan ɗauki wannan cutar da zuciya ɗaya. Amma ka sani,” ya ɗan ƙanƙance idanunsa, “ba kowanne sirri kuke sani ba. Ni kadai nasan irin rawar da take takawa a rayuwata. Ba rabuwa, ba kuma barinta. That is final.”
Umar ya yi shiru, ya sunkuyar da kai kamar yana tunanin zurfin kalaman mahaifinsa. Sai daga baya ya miƙe tsaye a hankali ya ce
“To Abba, naji. As’ad ya ɗaga kansa ya kalle shi da kallo mai sanyi amma cike da ikon uba.
“Good. Just trust me, Umar. Ba zaku taɓa shan kunya saboda ni ba.”
As’ad yana tsaye bakin glass window na babban falonsa, yana kallon hasken Dubai da dare. Waya ce a kunnensa, a gefe kuwa Umar ɗansa mafi girma wanda yake taimaka masa a harkokin business ya zauna yana duba wasu files a tablet dinsa.
Bayan As’ad ya kammala magana da mutanen tashar jirgin ruwa akan containers dinsa, ya juyo ya kalli Umar.
“Umar, we need to move fast. Zan so ka tabbatar da cewa dukkan kayayyakin da suka shigo sun isa warehouse kafin safe. I don’t trust wannan lokacin da labarai ke ta zuba.”
Umar ya ɗan gyara zama, ya kalli mahaifinsa da ido mai nuni da damuwa.
“Dad… akwai wani abu da nake so na fada maka.”
As’ad ya ɗaga gira.
“What is it?”
Umar ya ɗan ja numfashi, zuciyarsa na bugawa. Tunanin kalmomin da suka iso kunnensa jiya yana ta dawainiya dasu cewa Ayshatu tana soyayya da Alhaji Muqaddam. Amma yadda yake kallon idon mahaifinsa mai cike da izza da ƙarfin hali, sai ya kasa furtawa.
Ya saki numfashi a hankali ya dan murmusa
“Actually… about the new contract da muka samu daga Qatar. Na gama dubawa, akwai wasu clauses da nake ganin ya kamata mu tattauna kafin mu sa hannu gaba ɗaya.”
As’ad ya jinjina kai, bai lura da boyayyar damuwar ɗansa ba. Ya nuna masa kujera kusa da shi, suna ci gaba da tattaunawa akan business.
Amma a zuciyar Umar, kalaman da bai faɗi ba suna ci gaba da yawo kamar ƙaho
“Should I tell him the truth about Ayshatu? Or should I keep it until I’m sure?”
Nana hadiza
09030569336
[02/09, 9:24 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Watanni sun wuce a hankali kamar ruwa mai tafiya cikin kwando, amma Alhamdulillah a kowanne rana ina jin sauƙi da ƙarin ƙarfi. Takaba ta kare, hawayen da nake zubarwa kullum yanzu sun ragu, sai addu’a da godiya nake yiwa Allah saboda ya bani damar tsira daga mummunan hatsarin da ya yi ajalin wasu, amma ya bani rayuwa sabuwa.
Abba kuwa, shi kaɗai ya zama tamkar uwa da uba a gare ni. Shi yake kaini makaranta da kansa, shi yake ɗaukarmun littattafai da sandata, har sanda ɗin da na jiyeta, yanzu babu ita. Zugin kafar ya ragu sosai, na fara tafiya lafiya, babu raunin da zai hanani yin karatun da na jima ina mafarki akai.
Yanzu dai duk inda na shiga ana ganin canjin da Allah yayi min. Na zama sabuwar Ramlah ƴar gayu, mai hankali, mai nutsuwa. Karatu na nake yi da tsantseni, hankalina ya tattaru gaba ɗaya akan littafai da Qur’ani.
A makaranta kuwa, idan banida lecture, maimakon na koma gida in zauna ƙarƙashin tsangwamar Momy ko HarararYaya Billy, sai dai in nufi hostel ɗin Anty Maryam. Gurinta nake zaune, inda muke karatun Qur’ani tare. Ni na riƙa koyamata, ita kuma tana bani ƙarfafawa da kalaman da ke kara min ɗumi a zuciya.
Ina jin daɗin zamana a hostel, saboda can babu rigima, babu ƙiyayya, babu gulma. Zama ne na kwanciyar hankali. Duk da haka, na san cewa Momy ba haka taso ba, saboda a cikin ranta bata so ta ga ni cikin walwala ko cigaba. Amma tunda Abba ya ɗauki alhakin rayuwata gaba ɗaya, sai ya ce “Ramlatu, aikin alheri ne kike yi ai ni bazan hanaki ba kicigaba da koya musu qur'anin.
Wannan kalamai nasa sun kara min ƙarfi sosai. Sai na ce a zuciyata “Eh, lallai watarana sai labari. Watakila Momy da kanta za ta gane cewa baza ta taɓa nasara da mugunta ba.”
Haka rayuwa ta canza a gare ni. Yanzu ko na dawo gida karfe shida na yamma, ba damuwa a zuciyata, saboda na fi sanin cewa akwai gurin da ya fi zama da su Momy saboda yanzu kiyayyar karara take nunamun hatta abinci nataba sai ta yini tana masifa.
Watanni biyu da suka wuce…
Tun bayan mutuwar Bashari da komawata daga asibiti rayuwata ta fara samun sauyi sosai. Mahaifin Bashari da ƴan kauyensu suka zo domin dubani, kowanne daga cikinsu na cike da farin cikin ganin ni da idonsu, musamman ganin cewa na tsira daga hatsarin da ya dauki ɗansu.
Na zauna cikin palon gidan Abba, idanuna na kallon yadda suka shigo da tawali’u da nutsuwa. Duk wanda ya kalle ni sai yayi murmushi ya ɗaga hannu sama yana yi min addu’a.
“Amin Allah ya baki lafiya, ya raba ki da sharrin mutane, ya mayar miki da duk wani hasara da alkhairi.”
“Allah ya baki mijin kirki da zai kula dake, Allah ya daukaka rayuwarki.”
Addu’o’in nasu suna ratsa zuciyata suna sa ni jin sauki, ina jin kamar Allah yana mayar min da martabana a idon mutane bayan tozarcin da na sha.
Ƴan kauyen sun tsaya a gaban Abba suna masa godiya, suna faɗa masa cewa ya rike ni da kyau, su kuma zasu ci gaba da yi min addu’a. Abba ya kallesu da murmushi yace
“Ina godiya sosai, ramlah diyata ce, kuma zan kula da ita fiye da yanda kuke zato. K
Allah ubangiji yajikan bashari ya gafarta masa.”
Duk wannan maganar da addu’o’in nasu, da farin cikin da ake nunawa a fili, sai dai zuciyar Momy tana cike da haushi. Bata iya boyewa sosai, domin wani lokacin idan ta kalle ni sai ta rufe fuskarta da tsaki, ko kuma ta kauda kai gaba ɗaya kamar bata son ganina.
Ni kuma sai inji wani irin sanyi a zuciya, saboda nasan ba kowa bane yake min mugunta kamar yadda take yi. Ga addu’ar mutanen nan na ƙauyen Bashari da ta tsaya min, da kulawar Abba da yake bani kullum.
Yau Friday na farka da sassafe bayan na idar da sallar asuba. Kamar yadda na saba, na nufi bandaki. Na zuba idanu a gaban madubi yanzu jikina ya canza sosai. Tun daga lokacin da na fara amfani da set ɗin Pure & White mai pink colour wanda abba ya siya min, jikina ya fara yin wani irin kyau na daban. Fata ta ta haske, kurajen da suka daɗe suna damuna sun ɓace, warin gaba da kaikayi kuwa duk sun zama tarihi saboda maganin da aka bani a ƙauye. Na tsuraw kaina
kallo a madubi, zuciyata cike da mamaki da godiya. “Subhanallah,” na faɗi ina murmushi Ni ce Ramlah? Wannan kyakkyawar mace da nake gani a madubi wacce ta cika sosai, wacce jikinta ya koma kyakkyawan tsari kamar matar manyan mutane ?
Cikin gaggawa na yi brush sannan na shiga yin wanka. Bayan na gama, na ɗauki light gown fari mai laushi, na sanya rolling a kaina sannan na ɗauki jakata. Duk da irin ƙuncin da na sha a baya, yanzu bana jin komai araina wallahi kwalliya nakeyi nazama ƴar kwalisan da bashari yake kirana hatta maganata da takuna da komai nawa ya canza nayi kiba sosai nayi bul bul. “Yanzu komai ya wuce. Ban sake zama wacce ake tauye mata daraja ba. Ban kuma yarda in ci gaba da ɗaukar cin kashi irin na gidanmu ba.
Na fito falo a hankali, ƙamshi na turaruka na biye da ni. A nan na tarar da momy da yayata Billy suna zaune suna breakfast. Na tsaya na kallesu, sai na ce cikin ladabi
“Ina kwana momy.”
Ta ɗan ɗago kai ta ce da sanyi
“Lafiya.”
Ban tsaya jira ta ƙara magana ba, na wuce inda Billy take. Ta tsaya tana kallona daga sama har ƙasa, sannan ta ce
“Morning, sis.”
Ni kuma da ladabi na ce mata
“Morning.”
Kafin wani lokaci sai naga Abba ya sauko daga saman bene, sanye cikin shigar sa ta office. A hannu rike da jakar aikinsa, sai kamshi yake fidda wa. Kallonsa na yi da farin ciki, sannan cikin rawar murya na ce
“Morning, Abba.”
Ya tsaya yana kallona, sai murmushi ya bayyana a fuskarsa.
“Morning, auta. Mashaa Allah, yau kin fito kamar wata yar sarki. Allah ya ƙara miki kyau da albarka.”
Na ƙarasa kusa da shi da gudu kamar ƙarama, na rungume shi. Wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali na ji a raina. Duk da cewa ban cika da kalaman soyayya da goyon baya daga wajen uwa ba, amma kulawar Abba ta isa ta cike duk wata gibi a zuciyata.
Ina zaune ina kallon su momy suna zubamun ido, amma ni ban damu da hakan ba. Nace cikin taushin murya,
“Abba, fa’ah 10 nake da lecture yau wallahi.”
Ya kalle ni da murmushi mai ɗan ɗauke da izza amma cike da tausayi yace,
“Auta, na hanaki fita Bakiyi breakfast ba ko? Zauna mu karya tare.”
Nayi shiru na ɗan sunkuyar da kai sannan nace,
“To Abba.”
Na mike cikin natsuwa na haɗa masa tea mai kauri, na zuba masa a cikin gilashi mai kyau sannan na kawo masa. Na ɗora masa egg da soyayyen dankali da bread na basa da hannuna.
Abba ya ɗan kalle ni, idanuwansa na nuna farin ciki da yadda na zama mai biyayya. Sai yace,
“Auta ta, Allah ya yi miki albarka.”
Nan take sai momy ta ɗan gyara murya tace,
“Anjima zamuje gidan Hajiya Ayshatu. Muyi mata Allah sanya alkhairi da bikin diyarta, Nawal. Tunda akayi bikin sai jiya suka dawo nan, yanzu dai ya kamata inje ko?”
“ Amma sai hanzu Zainabu? Abba yafaɗa.
“To Abban Ramlah, ai daman bata nan. Saboda haka ne ban samu damar zuwa ba.”
Abba ya ɗan juyo ya kalli Billy da ke zaune gefe. Da kulawa yace,
“Billy, lafiyarki dai kuwa? Naga kamar bakida kuzari sosai.”
Billy ta ɗan gyara zama ta amsa cikin kasaita,
“A’a Abba, lafiya kalau.”
Ni dai da nake zaune ina jinsu bance komai ba. Tunda na dawo gidan nan, maganar minti biyar ma bata haɗa ni da Yaya Billy ba. Sai dai idan ta zubamun harara ko ta kawomun wani irin kallo.
Abba ya ɗan girgiza kai yana nuna damuwarsa, sannan cikin kulawa yace,
“Ki kula sosai Bilkisu. Bana son abunda zai sa kisa kanki cikin damuwa. Kinji ko?”
Na ji kamar zuciyata ta yi sanyi da irin kalaman Abba. Amma ban tsaya ba. Na mike cikin natsuwa, na ɗan gyara hijjab dina sannan na wuce waje. Na nufi wajen motar Abba na tsaya ina jiransa cikin nutsuwa.
Tare da Abba muka bar gida. Cikin nutsuwa yake tuki yana duba ni lokaci-lokaci kamar yadda yake koyaushe idan muna tare. Bayan mun isa bakin department ɗin jami’a ya tsaya ya ja birki sannan ya juyo gare ni
“Auta, ki kula da kanki. Idan kin kammala lectures ɗinki ki kira ni, zan zo na ɗaukeki.”
Kai na girgiza ina murmushi na ce, “To Abba, Allah ya saka maka da alkhairi.”
Na fito daga motar na nufi cikin department ɗin. Tun da na taka ƙasa sai iska mai sanyi ta buge ni, zuciyata ta yi wani irin natsuwa da kwanciyar hankali.
Ko da na shiga, Maryam ta hango ni daga bakin corridor cikin farin ciki ta ruga ta rungume ni tana cewa
“Ramlah, ai ingayamiki? Jiya fa show akayi! Kinsan wanene yake sonki?”
Na janye jikina cikin ɗan bacin rai, na harareta cikin murya mai sanyi na ce
“Maryam, kin san banason irin wannan maganar. Nagayaki bani da tsarin soyayya a gaba yanzu. Kin manta halin da na shiga? Don Allah ki bar maganar nan kawai.”
Amma Maryam ta tabe baki ta ce
“Wai me yasa kike haka ne Ramlah? Wallahi yana sonki sosai, wannan sabon lecturer din namu fa! Bakiga yadda yake ta yimun magiya ba? Haba kawata, ki bude zuciyarki. Ke dai kin manta son da kika rasa...”
Na dakatar da ita cikin tsaki na ce
“Na gaya miki bani da lokacin wannan zancen yanzu. karatune agabana, kuma bana son wani abu ya ruguza hankalina. Please, ki fahimceni.”
Nana hadiza
09030569336
[04/09, 10:06 pm] Deejarh b YCG2: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Na fice daga ajin domin zuwa library. Sai kawai idona ya sauka kansa tsaye a bakin lecture hall ɗinmu sabon lecturer din da Maryam ke nufi. Tsaye yake, dogo, sanye cikin farin shadda mai tsabta da takalmi mai tsada. Idanunsa sun zubawa kaina tamkar yana jira na fito.
Cikin ladabi na kalle shi sau daya kawai, sannan na ɗan sunkuyar da kai na ce
“Good morning, Sir.”
Na juya ina shirin wucewa.
Sai kawai naji muryarsa mai taushi da kwarjini tana kirana
“Ramlah…!”
A hankali na tsaya, zuciyata tana bugawa da sauri, kamar wacce aka cafke cikin wani abu. Na juya a hankali na kallesa, idanuwansa cike da natsuwa da wani abu da ban iya fassara ba.
“Eh Sir?” na ce cikin kunya.