Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 9

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 9

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 9: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 9. Ya dan murmusa, yana kallona da ido kai tsaye, wanda yasa naji…

4,500 words

Ya dan murmusa, yana kallona da ido kai tsaye, wanda yasa naji zuciyata ta kara dukan da ban taba ji ba.

Na tsaya cak a wurin, tamkar ƙafafuwana sun kulle. Na kasa motsi sai bugun zuciya kawai da yake ƙara karfi, tamkar zata fito ta hanyar kirji. Idanunsa na kallo tamkar wani abu ne da ya haɗa ni da shi, wani yanayi da ban saba da shi ba.

Ya ɗan gyara tsayuwarsa, sannan cikin ladabi da tausasa murya ya ce:

“Banason na dame ki, amma akwai wani abu da nakeso mu tattauna. Za ki iya zuwa office ɗina bayan lecture?”

Na yi shiru, na sunkuyar da kai, jikina na rawa. Na kasa cewa komai sai da nayi ajiyar zuciya sannan nace a hankali

“Yes, Sir.”

Murmushi ya yi wanda ya bayyana wani salo na kwarjini da nutsuwa. Sai ya ɗan ɗaga hannunsa kamar mai sallama, sannan ya ce

“Thank you, Ramlah. Zan jira ki.”

Na juya cikin sauri, ina jin yadda idanuwan sa suka bini har na ɓace cikin hallway ɗin library.

A lokacin da na isa library, ba littafin da nake kallo na gani. Hankalina gaba ɗaya ya tattare kan maganar da ya faɗa. Wane irin magana ne yake so muyi? Kuma ya akayi ya san sunana tun kafin na gaisa da shi? Ko dayake maryam zata iya gayamasa nasan halinta.

Na jingina da kujerar karatu na, zuciyata na cike da tambayoyi kala-kala ahaka nayi karatu sama sama sannan nafita na bar gurin.

Bayan mun gama lecture ɗinmu kenan, ina shirin tafiya sai naji Maryam tana cewa

“Ramlah, kiyi hakuri ki saurare shi mana, yanada kirki ne wallahi, kinga tun jiya yake tambayata akan ki.”

Na ɗan ja tsaki cikin zuciyata nace, "wai meye dalilin da zai sa ya nace haka? Ni dai bana son hayaniyar soyayya yanzu, banda lokacinta nagaymike."

Sai dai saboda kada ace na raina shi ko na nuna isa, da ƙyar na juya na nufi office ɗinsa. Yana ganina ya miƙe da fara’a, murmushi mai nuna jindaɗi ya bayyana a fuskarsa.

Ya nuna min kujera da girmamawa ya ce “Please ki zauna Ramlah, ba zanyi miki dogon jawabi ba.”

Na zauna cikin natsuwa, sai na kalli agogon hannu na saboda bana so lokaci ya ɓaci.

Cikin nutsuwa ya fara magana, yana mai daidaita muryarsa “Na san baki da lokaci sosai, amma ina so ki fahimci cewa abin da nake ji gare ki gaskiya ne. Ni ba irin samarin banza bane masu wasa da zuciya. Ni na fuskanci kaina, ina son ki da gaske.”

Zuciyata ta buga, amma ban nuna komai ba. Na saki numfashi a hankali sannan nace cikin murya mai nutsuwa

“Nagode sosai da wannan kalma taka. Amma dan Allah ka fahimce ni ni yanzu karatu ne a gabana, ba soyayya ba. Ba wai bana daraja abin da kace ba, amma bana da lokacin soyayya yanzu. Dan Allah kayi hakuri, idan wannan ne dalilin da yasa ka kirani, to na fi son ka fahimci matsayina.”

Na miƙe da sauri kafin ya ƙara wani abu. Yana kallo na har na kai bakin ƙofa ya ce cikin murya mai taushi

“Ramlah… koda kuwa na jira har ki gama karatun?.”

Na tsaya na ɗan juyo, na kalle shi a hankali nace “Allah ya sa ka samu tagari. Amma don Allah kada ka ɓata lokacinka akaina yanzu.”

Na juya na fice cikin natsuwa, zuciyata cike da wani irin nauyi.

Maryam kuwa murna tayi sosai ganin na saurari malaminmu, wanda ake kira Haneef Idris. Kyakkyawa ne baki fari mai kyau, kana kallonsa kawai kaga ɗan masu kuɗi ne. A ranar kuma jikina ba daɗi yake yi ba

kaina na ciwo sosai hakan yasa ban karɓi wayar maryam nakira abba ba Maimakon hakan sai kawai na ɗauki jakata na fita na samu napep na koma gida cikin gaggawa.

Na isa gidanmu cikin gajiya da jin yunwa. Da sallama na shiga babban palour, na tarar da Yakaka tana zaune tare da Mumy da yayata Billy. Na gaishe su cikin ladabi kamar yadda aka koya min. Yakaka ta dan jinjina kai, tana mai cewa “Zainabu, lallai babu shakkah, kada kucemun ramlah ce wannan? Wallahi idan aka kalle ta sai ka ɗauka yarinya ce daga larabawa, ba wannan wacce kuke tsangwama ba. Tabbas abban nata ya canza mata rayuwa.”

Sai naji zuciyata ta yi sanyi, amma kafin in amsa ko na ji daɗin kalaman Yakaka, sai Mumy ta buɗe baki da gubar kalmarta “Wallahi abun nan na damuna. Kin ga yadda uban ke ji da ita? Kin ga yadda yake nuna bambanci tsakaninta da Billy? Wannan fa abun kunyace, kirki kiri ya nuna yafisonta akan diyata can wannan kwayoyin take sha tayi kiba haka.”

Billy kuwa ta ɗaga murya cikin izza “Ai nagaya miki tun farko, Mumy, ki sa abba ya aura mata Yunus ɗan Uncle mamman kawai. Ni kaina yadda nake ganinta cikin walwala ba na jin daɗi. Idan kika bar ta, nan gaba zata hau kanmu gaba ɗaya.”

Na tsaya ina sauraro cikin mamaki. Na fahimci kalmomin da suke furtawa ba wai tattaunawa ba bace, makircinsu ne da tsantsar kiyayya. Amma ban furta komai ba, na wuce dakina, na yi wanka, na fito da kayana nasaka , sannan na shiga kitchen dan neman wani abinci domin yunwa ta takura min.Sai dai kafin in karasa , sai naji muryar Mumy tana kwala min kira da ƙarfi. Na fito cikin ladabi nace “Na’am Mumy.”

Sai kawai ta harare ni da wani kallo mai haɗe da tsanar zuciya “Banason irin wannan shigar a gidana. Wannan ba gidan mijinki ba ne! Ke baki jin kunya ne? Wannan ba gidan dan iska Basharin nan bane,ba gidan Asararriya bane, gidanane”

Kalmar “dan iska” ta daki zuciyata kamar kibau. Na tsaya cak ina kallonta, hawaye na cikamun ido nace cikin raunin murya “Mumy, me yasa? Menene da shigar da nayi? Kuma Bashari ba dan iska bane, Allah ya gafarta masa. Bai cancanci ki ce masa haka ba.”

Sai Yakaka ta ɗan girgiza kai tana cewa “Eh gaskiya, Ramlah ta fara samun karfi yanzu. Lallai zainabu, yaushe kika yi sake haka? Wannan yarinya ta tashi da tsari, me yasa baku gane ba?”

Na juya na koma kitchen domin na kauce rikici, amma Mumy tazo ta fizge ni da ƙarfi daga hannun kwanon da nake riƙe dashi. Tana zuba mun masifa da bala’i tana fadin “Ni zakiyiwa magana haka dan uwarki? Ni? Wato ni zaki mayar yar iska? Kin rasa wa zakiyiwa iskancinki da fitsararki saini? To wallahi daga yau ni bazan taɓa yarda ki shigarmun kitchen ba sai abunda naga damar baki daga abincin Fita! Kar na kara ganinki a kitchen ɗina!”

Na sauke hannunta daga kafaɗata cikin karyewar zuciya, nace cikin raunanniyar murya “Okay Mumy. Amma ki sani yunwa nake ji.”

Sai ta ɗaga hannu tana bubbuga ƙasa da ƙafarta cikin fushi “Tafi! Banason ganinki! Ke ba ƴata bace, yar iskar yarinya kawai!”

Na juya na koma dakina, hawaye suna zubo min. A zuciyata nake tunani “Mene na yi musu? Me yasa suka tsane ni haka?”

Jakata na buɗe a hankali na zaro ATM card ɗina, na saka a aljihuna, sannan na fice zuwa harabar gidanmu. Zuciyata cike da nauyi, amma sai na daure don kar wani ya hango fargabar da ke lulluɓe da zuciyata.

Tun ina saukowa daga saman matakala naji muryar Momy tana cike da masifa da tsinuwa, tana zagina da kalmomin da ko kowa ya ji sai ya tausaya. Na dan tsaya na huci, amma ban ce mata komai ba. Ban iya maido mata da amsa ba, saboda bana son ƙara jin haushinta a zuciyata.

A bakin ƙofar gidanmu na hango almajirin mu wanda kullum yake kaiwa da kamowa, na kira shi a hankali na ba shi kwatancen wata eatry na kusa da gidan. Na zaro masa kudi, nace masa,

“Ka siyo mun fried rice da pepper chicken, sannan ka ɗauko min lemon guda. Ga Kudin nan na 4k ne, ka tabbatar da da ka dawo da wuri.”

Ya ɗan yi murmushi da sallama yace,

“Toh Hajiya Ramlah, bari na tafi yanzu.”

Na zauna a gefen harabar gidan ina jiransa. Iskar dare tana kadawa tana kadawa tana busa hijjab dina a hankali. Idanuna suna kaiwa sama kamar ina neman hasken wata ya rage min radadin zuciya.

Bayan kusan minti ashirin sai ga almajirin ya dawo da ledar. Na karɓa da godiya, na mike cikin sauri na shige ɗaki.

Cikin shigata har ban ma kulawa da abinda Momy take yi ba. Amma daga ɗan nesa naji ƙarar yaya Billy tana kara zagina da bakin ciki.

Ban tanka musu ba, ban ma waiwaya ba. Ledar abincin kawai na runguma na nufi ɗakina kai tsaye.

A zuciyata dai abu ɗaya kawai ke yawo “Ina jiran Abba…

Nana hadiza

09030569336

[04/09, 10:06 pm] Deejarh b YCG2: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Na shige ɗakina ba tare da na ce musu uffan ba. Na rufe ƙofa da kyau sannan na zauna kan carpet. Na ɗauki take away ɗin abinci da abba ya kawo min, na buɗe, nayi bismillah sannan na fara ci. Duk da rashin ƙarfina, na ci sosai saboda yunwar da nakeji, har sai da na cinye tas. Na ɗauki lemo na sha, sai na sauke ajiyar zuciya.

Amma kafin na kai nesa, tunanin Bashari ya dawo da ƙarfin gaske a cikin zuciyata. Wani irin hoto na sautin muryarsa ya tsaya mani a kunne. Yadda yake yawan cewa "Yar kwalisa kici abinci, zomuci abinci tare. Banason wasa da abinci."

Kafin na ankara sai hawaye suka cika idona, na soma wani marayan kuka ina faɗin

“Ya Allah, ka gafarta masa, ka jikansa, ka yafe kurakuransa.”

A hankali na share hawayena, amma zuciyata bata daina bugawa da ƙarfi ba. Wani irin yanayi daban ya lullubeni, na ji jikina yana amsawa da wani abu da banyi tsammani ba. Wani irin zafi mai daɗi ya ratsa ƙirjina.

Na tuna yadda Bashari yake rungumeni da ƙarfi, yadda yake shinshinar jikina kamar baya son ya sake ni. Tsigar jikina ta mike gabaki ɗaya, naji kamar wutar sha’awa ta ƙone ni daga ciki. Wani kalar rashin natsuwa ne ya saukar min, zuciyata na faɗin

“Da ace har yanzu yana raye, da wannan kewar bata addabeni haka ba.”

Na rusuna da hawayen ƙauna da kewarshi, na rasa yadda zan kwantar da zuciyata.

Ganin ina shiga wani yanayi na zuciya da ban iya kwantarwa ba, sai na miƙe a hankali, na nufi bandaki nayi tsarki sannan nayi alwala. Cikin kwanciyar hankali na shimfiɗa sallaya, nayi raka’o’in sallar isha’i. Bayan na idar, na ɗauki carbi na, na fara istigfari cikin nutsuwa, “Astaghfirullah… Astaghfirullah…” sai kuma nayi salati ga Annabi (SAW) sau da dama. A haka naji zuciyata tana sauka kadan, amma har yanzu damuwa bata barni gaba ɗaya ba.

Na ɗauki ƙaramar ƙur’ani na, na buɗe na fara karatu, da niyyar neman nutsuwa daga cikin kalamun Allah. A hankali kalmomin suna ratsa zuciyata, suna sanyamun rai. Bayan wani lokaci, na rufe littafin na, na mayar da shi inda yake, sannan na ɗauki mayafina na rufe jikina.

Da na ga bacci baya zuwa idona, sai na yanke shawarar na fita zuwa palour domin na ɗan huta ko na samu canjin yanayi. Ko da na shiga, na tarar babu kowa face Yakaka da alama ta kwanta, tana juyi a kan kujerarta. A gefe kuma, ya Billy na zaune akan kujera yana kallo, Chinese series ke tafe a talabijin.

Ban yi magana ba, na zauna a gefe cikin nutsuwa. Duk da ban shirya tattaunawa ba, idona ya bi fuskar ya Billy cike da tausayin yadda ta lalace. Wani irin baƙin ciki ya cikeni, na tuna yadda ta kasance yarinya kyakkyawa, mai fara’a, mai cike da kuzari. Amma yanzu, duk ta lalace sakamakon shaye-shaye.

Jikinta ya rame ƙwarai, idonta sun fita daga kaho, fatar jikinta ta yi baki, kuma idan ka kalleta sai ka fahimci baƙin cikin rayuwa ya mamaye ta. Tabbas ta jefa kanta cikin ƙarya da shaye-shaye, wanda ya rushe mata komai. Ban iya jurewa ba, sai na kalli ƙasa, ina addu’a Allah ya shiryar da ita.

Ban ankara ba, sai naji ihun momy daga gefentamin ihu

"Mayya! Diyar mayu! Ramlah, wallahi kina cinyemun ƴa ta da ido. Kika kafa mata ido haka ta lalace. Wayasani ma ko Ke kika yi mata sihiri kika lalatamin rayuwarta!"

Na ɗaga kaina a hankali, na dubi momy. Zuciyata ta yi wani irin kakkarwa saboda zargin da take yi. Na ji ciwo sosai a zuciyata.

Na girgiza kaina a hankali, ban ce mata komai ba. A zuciyata nace “Ya Allah, kai shaida, ban taɓa yiwa wannan matar mugunta ba, balle in yiwa ƴarta asiri. Idan akwai wani alheri cikin rayuwarta, Allah ka dawo mata da shi. Amma idan wannan ne sakamakon sharrinta da zaluncinta, to kai ne mai hukunci.”

Sai kawai na juyo tana faɗin "To wallahi baki isa ba. Ko maita kika ɗauka daga kauye, wallahi Allah ya fi ƙarfinki. Ba zaki taɓa cinye mu ba Ramlah."

Na lura da yadda idon ya Billy yake tsaye a kaina, kamar tana son faɗin wani abu amma tana jin tsoro. Ta ɗan janye idanunta gefe, sai kuma ta sake kallona cikin wani yanayi mai cike da ƙorafi da shiru. Na ji tausayinta sosai.

Daga ƙarshe ta tashi, ta ja tsaki mai ƙarfi sannan ta fice daga palon ba tare da ta ce komai ba.

Ni kuwa na zauna a wurin, zuciyata cike da tarin damuwa. Na ji hawaye suna taruwa a idona, amma na ƙi barin su zubo. Na dafa kirjina nace “Ya Allah, kai kadai ne na dogara gareka. Ka tsare ni daga sharrin zuciya da sharrin waɗanda ke yi min hassada. Ka tsare abinda ka bani, ka tsare mutuncina, ka tsare ni daga zargi mara tushe.”

Ina zaune akan kujera cikin nutsuwa ina kallo a television, duk da cewa zuciyata ta cika da tunani iri-iri da ba zan iya fassarawa ba. Kallon kawai nake tamkar wanda ya manta da kansa. Sai kawai naji sallamar Abba a bakin ƙofa. Atake na tashi da sauri saboda farinciki da girmamawa da nake masa nace,

“Sannu da zuwa Abba.”

Ya murmusa cikin yanayin kulawa da ƙauna yace,

“Yauwa auta, Allah ya kara lafiya naji dadi danaga kinfito kina kallo.”

Momy kuwa tana gefensa tana karbar jakarsa da kulawa, kai tsaye ta shige dakinsu da ita, kamar wacce bata son tsayawa sosai a wancan lokacin. Ni kuma sai naga kallon da Abba ke min, wani kallo mai ɗauke da tambaya da soyayya a lokaci guda.

“Kallo ake yi auta?”

Ya tambaya cikin dariya.

Na gyara zama a kan kujerar nace,

“Eh Abba, kallo nake yi kawai.”

Sai yaja numfashi yana sakin murmushi, kamar wanda ya sami nutsuwa daga ganin yarinyarsa cikin kwanciyar hankali.

Bayan ya zauna a kasa saman carpet yadda ya saba, sai ya kira momy daga daki da cewa,

“Zainabu kiyi sauri ki zuba min abinci, yunwa nake ji sosai.”

Ni kuma sai naga kamar ba zan bar shi cikin shirun nan ba. Na sauka daga kan kujera na zauna kusa da shi saman carpet ɗin, na jingina gefe ɗaya ina kallonsa.

“Abba kasan me? Munkusa fara jarabawar mu a makaranta. Lecture ɗin mu na yau ma yayi nisa sosai, Malami yana ta mana nasiha akan mu dage da karatu, saboda shi jarabawa kowane ɗalibi sai ya nuna irin ƙoƙarinsa.”

Na tsaya na ja numfashi sannan nace,

“Shiyasa nake jin tsoro sosai, amma kuma ina ƙoƙari. Insha Allahu zan yi kokari na samu result mai kyau, saboda kai da kanka kullum kana min addu’a.”

Abba ya kalle ni da murmushi, ya ɗaga hannunsa sama kamar yana yi min addu’a sannan ya ce “Allah ya taimake ki, auta ta. Allah ya buda miki basira, ya baki sa’a da rabo mai kyau. Na yarda dake, nasan baki da raini, baki da wasa da ilimi. Kuma abinda ya fi komai, nasan baki da son cin amanar iyaye. Allah ya sanya iliminki ya amfanar dake, ya amfanar da al’umma.”

Idanuna suka cika da hawaye saboda jin kalaman sa. Na kalleshi da murmushi nace,

“Amin Abba. Kai kullum kana bani kwarin gwiwa. Da ace ba kai ba, da na dade ina jin tsoro ko karatun ma bazan iya dauka sosai ba.”

Sai yace “Auta, rayuwa ba zata taba zama daidai ba idan bamu dage ba. Kullum akwai kalubale, akwai jarabawa, akwai masu son ganin kin fadi. Amma ki tuna da addu’a, addu’a ita ce makamin mumini. Ki dage da sallah, ki dage da karatun Alqur’ani. Idan kika rungumi Allah da gaskiya, babu wanda zai cutar dake.”

Nayi shiru cikin natsuwa ina jin kamar zuciyata ta kara nutsuwa. A hankali na ce masa “Abba, zan yi kokari sosai. Na dauki alkawari a raina cewa bana son ka shiga damuwa saboda ni.”

Ya murmusa ya shafa kaina yace “Na sani, auta.”

Momy ce ta shigo hannunta dauke da tray mai ɗauke da tuwo da miyar taushe, a gefe kuma kwalban zobo da ruwan sanyi. Ta aje a kan table tana murmushi tana fadin

“Abban Ramlah, ga abincin ka.”

Abba ya amsa da murmushi yana duban tray ɗin “Kai, Zainabu, yau ma kin sha aiki Allah ya saka da alkhairi. To Auta, zo muci tare.”

Ni kuma da ke zaune a gefe cikin zuciyata sai naji wani irin haushi ya turnike ni. Na daure fuska na ɗago kaina cikin rashin kuzari nace

“Abba, nasiyo abinci fa, naci.”

Da mamaki abba ya juyo yana dubana sosai:

“Bangane ba, kinsiyo abinci? Ke kanki baki iya sa kisa yar aikin nan ta dafa miki abinda kikeso ba? Kuma kinsan yanzu ke marar lafiya ce, yaushe kika fara siyan abinci a waje?”

Na sauke ajiyar zuciya, idona cike da hawaye, amma na daure nace cikin wata murya mai nuna ƙunci “To ai Abba, Momy ce tace min kar na kuskura na shiga kitchen ɗinta. Kuma tace ban isa ta dafa min abinci ba, tunda gidan ba nawa bane. Haka kawai ban taɓa samun abin da nakeso a hannunta ba. Don haka dole nayi niyyar siyo naci idan yunwa ta isheni.”

Dakin yayi shiru na ɗan lokaci. Abba ya juyo da fuska cike da mamaki yana kallon momy, wanda ita kuwa ta zabura. Da sauri ta ɗan gyara zama ta ce cikin dariyar da ta keƙashe da fushi a ciki “Subhanallah! Ramlah, wannan wane irin magana ce haka? Ai ni ina tausayinki har nayi wannan miyar taushe don nayi tunanin abinci irin wannan za ki iya ci. Amma sai ki zauna kina cewa wai ban yarda ki shiga kitchen ba. Wallahi abban Ramlah, wannan yarinya bata son na yamzu shi ya sa take kera maganganu don ta bata mini suna.”

Na fashe da kuka “Abba, wallahi ba karya nake ba. Tun lokacin da aka kawo ni nan bata taba bari na shiga kitchen ba. Bata taba dafa min abinci ba sai dai in kai kace muzo naci Kullum sai ta nuna cewa bani da wani matsayi a wannan gida.”

Momy ta harare ni sosai cikin bacin rai ta ce “Ke! Kar ki kuskura ki hadamin ƙarya gaban mijina. Kin ji ni? kawai ki zo ki ringa ƙirƙira abubuwa saboda a tausaya miki. To wallahi baki isa ba”

Abba ya mike tsaye, fuskar nan tasa ta cika da fushi, ya daka mata tsawa “Zainabu! Ya isa haka! Duk ranar da kika sake ɓata wa Ramlah wallahi sai na nuna miki ke baki da wayo karamar yarinya ki dauki kiyayya ki aza mata idan bilkisu ce zaki hanata shiga kitchen? Wannan yarinyar da kike ƙoƙarin wulakantawa itama jini na ce, Kina ji na ko? Ni dai na riga na yanke hukunci, daga yau idan Ramlah ta nemi abinci, za a dafa mata abinda takeso, ko da ace shi kaɗai take so. Kuma idan kika sake cewa ba za ta shiga kitchen ba, wallahi sai dai ki bar min wannan gidan gaba ɗaya!”

Jikina ya karye cikin kuka sosai na sunkuyar da kai na. Sai dai zuciyata ta cika da wata irin jin daɗi saboda abba ya tsaya tsayin daka akan gaskiya. Na kalli momy a hankali na ga yadda ta yi ja a fuska, kamar wacce zata hadiye zuciyarta saboda haushi.

Nana hadiza

09030569336

[05/09, 10:56 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA HUDU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Ina zaune a gefen kujera cikin ɗakin, zuciyata cike da damuwa da wani irin raɗaɗin da ban san sunansa ba. A hankali na natsu na kalli fuskar Abba, wanda yake zaune a gabana yana tsare ni da idonsa masu cike da ƙauna. Da rauni na fara magana cikin muryar da take rawa saboda hawaye da suka taru a idona.

“Abba… danAllah kadaina mata faɗa. Ni bance ayi mata faɗa ba, dan kayi mata faɗa. Mumy uwata ce, tanada haƙƙin ta yimun faɗa idan taga banyi dai dai ba DanAllah Abba ka bata hakuri. Ni kuwa… idan har Mumy bata sona, idan har Yaya Billy bata kulani, to Abba, ina ne zan samu farin ciki idan ba a wajen iyayena ba? DanAllah abba kabasu hakuri ifan fushi suke dani”

Kukan da na danne tun farko ya kufce, hawaye suka gangaro bisa kumatuna. Abba ya dan ɗaga hannunsa alamar ya isa. Muryarsa ta tsananta, amma har yanzu akwai nutsuwa da lallashi a cikinta.

“Zainabu,” ya kira sunan Mumy da kakkausar murya. “Kin manta ke uwa ce. Uwa ba ta cika rantsuwa akan yarta da mugun hali ba. Idan baki iya mata uzuri ba, to ki koyi hakuri. Na gaya miki tun farko, duk wanda ya bata wa Ramlah rai, to ni kaina ya batawa rai. Ni dai ina roƙonki ki gyara halinki, kada ki ci gaba da nuna mata ƙiyayya.”

Ni kuma cikin zuciyata, wani irin daɗi ya lullube ni. Na kasa boyewa sai dai na cigaba da hawaye, zuciyata na murna da siyasar da nakewa Abba A hankali Abba ya juya ya ɗauki wayarsa, sannan ya kira Yaya Billy cikin ƙarfin murya.

“Bilkisu! Bilkisu! Zo nan!”

Bilkisu ta fito daga ɗakinta cikin kasala, kamar wacce aka tura dole. Da zarar ta tsaya a gabansa sai ta sunkuyar da kai tana cewa

“Sannu da zuwa Abba.”

Ni kuwa cikin gaggawa na miƙe daga inda nake zaune, na nufi Yaya Billy da hawaye a idona. Na kamo hannunta na ce

“DanAllah Yaya Billy kiyi hakuri idan wani laifi nayi miki. DanAllah ki yafe min. Tun da na dawo gida ban ji wani farin ciki daga wajenki ba, ko hira bakya yi dani. DanAllah ki yafe min idan na bata miki rai.”

Na sake fashewa da kuka. Abba ya daga hannunsa ya dakatar dani.

“Ya isa, Auta. Ki zauna.”

Sannan ya juya ya kalli Bilkisu da idanuwan nan nasa masu cike da natsuwa amma suka ɗauke da izza.

“Bilkisu, kinfi kowa sanin ba ki da wata ƙanwarki sai Ramlah. Idan ke kika watsar da ita, waye zai rungumeta? Me tayi miki da bakya kulawa da ita? Ina tambayarki!”

Shiru Bilkisu tayi, ta ƙara sunkuyar da kanta. Abba ya ƙara danna mata tambayar da ƙarfin murya.

“Bilkisu, ba magana nake miki ba ne? Kina jina ko baki jina? Me yasa kika bar kanwarki tana rayuwa a cikin kewar iyaye, alhali ke kina nan da rai?”

Da kyar ta bude baki, muryarta kamar wacce ake murɗawa tace

“Abba… babu komai.”

Abba ya ɗan jinjina kai, sannan ya ce da ƙarfi

“Idan babu komai, to Daga yau, duk inda kika shiga sai da Ramlah. Har abinci, sai ku zauna tare ku ci. Bilkisu, ke ce babba, ita kuma Ramlah kanwarki ce. Ko kinason ta shiga cikin damuwa ne? Kinason ta shiga depression saboda babu wanda yake kula da ita a gidan? Wallahi ba zan lamunta ba. Duk wanda ya nuna mata wariya daga yau, to ni da shi.”

Na ji jikina ya saki da murna da farin ciki, zuciyata kamar zata fito ta bugawa Abba godiya. A hankali ya sauke murya ya ce

“Bilkisu, danAllah ki gyara halinki. Banason fitina a cikin gidan nan. Ni ina so ku kasance tamkar jini guda. DanAllah ki zama uwa ga kanwarki.”

Bilkisu ta zumbura baki, kamar wacce aka tilasta, amma da ganin yadda Abba ya tsaya da gaske akan maganarsa sai tace da ƙyar

“To… Abba. Zan gyara. Na ji.”

Abba ya ɗan gyara zama “Alhamdulillah. Allah yayi muku albarka. Allah ya sanya zumunci tsakaninku ya zauna. Ku zama masu ƙaunar juna, ku zama gata ga junanku. Ni kuma zan ci gaba da saka muku ido.”

Bayan haka ya kalleta da tsantsar tausayi ya ce

“Ku tafi ku kwanta. Ku kwantar da hankalinku, ku zama ƴaƴa nagari.”

Bayan na fito daga bandaki nayi alwala, na koma kan gadona da sanyin zuciya. Na kwanta a hankali saboda zafin da kafata ke bani amma zuciyata cike take da murna. Na tuna yadda abba yake tsayawa a kaina kullum, yadda yake kula dani kamar karamar yarinya, har yau naga ya rike momy da magana saboda ni. A zuciyata nace “Alhamdulillah yau naga adalcin mahaifi, yau naji dadi, yau naji na samu gata.”

Na janyo bargo na lullube jikina ina jin dumin soyayyar abba a kaina. Wannan karon banji nauyin zuciya irin na baya ba, naji kamar wata sabuwar ni’imar Allah ya budemin.

Na rufe idona cikin natsuwa amma kwatsam sai nashiga wani yanayi. A mafarkin naga kaina a wani fili mai duhu, babu haske sai kalar hayaki mai sanyi. Na ji kamar akwai wanda yake takowa kusa dani, kamar ana bugun ƙafafuwa da ƙasa a hankali. Cikin firgici na dinga juyawa ina kallon ɓangare, sai kuwa naga wani mutum yana nufomun.

Mutumin yana matsowa yana shashafani, hannunsa yana kokarin taba ni cikin wani yanayi na sha’awa. Idona suka firfito saboda tsoro, bakina ya bude na fara ihu ina kiran “Abba! Abba!” amma babu wanda ya amsa. Wani irin ƙarfi nake ji a jikinsa da kuma nauyin da yake kokarin dora min, na fara kukan tsoro kamar na samu numfashina ya tsaya.

Da karfi na rarrafa ina neman gudu amma babu inda zani, sai na fashe da ihu sosai. Wannan ihu din ne ya farkar dani daga baccin mafarkin. Na bude idona naji gumi ya lullube jikina kamar na fito daga wanka. Zuciyata sai bugawa take kamar ana busa ganguna.

Atake na sauka daga gadona duk da zafin kafa, na je ban daki na kara alwala, hannuna sai rawa yake amma nace “Na tashi don neman tsari a wurin Ubangiji.”

Na dawo na shimfida sallaya, na dauki carbi na fara tasbihi. Kalmar da na fara furta ita ce “Hasbunallahu wa ni’imal wakil”. Na maimaita ta sau goma, sau hamsin, sau ɗari, har sai da na ji zuciyata ta fara samun natsuwa. Na tuna darasin da Doctor Maryam ta bani “Ki rike addu’a, ki rike kunya, ki rike nutsuwa, ki rike kanki.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull