Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 10

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 10

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 10: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 10. Sai naci gaba da karanta Hasbunallahu wa ni’imal wakil har sau 450…

4,499 words

Sai naci gaba da karanta Hasbunallahu wa ni’imal wakil har sau 450 kamar yadda malamai suka koyar. Duk karan da nake maimaitawa sai in ji kamar wani nauyi na sauka daga zuciyata, sai in ji wani sanyi na shige ni.

Na fara tuna rayuwata ta baya da Bashari. Nace a zuciyata “Inama yana nan, inama ba hatsari ya dauke shi ba, da yanzu shine yana nan yana rungumeni, yana sumbatata, yana kirana yar kwalisa. Amma shikenan babu shi.”

Na share hawayen da suka zubo, na daga hannuna sama n na fara karanta Ayatul Kursiyyu sau uku,Suratul Falaq sau uku,Suratun Nas sau uku,Suratul Ikhlas sau goma. Na hura a hannuna na shafa jikina gaba daya. Na cigaba da karatun tasbihi har wani bacci mai dadi ya daukeni.

A cikin wannan baccin ban sake ganin duhu ba, ban sake ganin wanda ke shashafani ba. Sai kawai na ga kaina cikin wani fili mai haske, inda yara kanana ke wasa suna dariya suna gudu suna kirana!” naji sanyi a zuciyata sosai.

Da safe lokacin rana bata gama haskawa ba,ban nayi wanka nazauna nayi azkar sannan na tashi da niyyar shiga kitchen domin in hada abunda zan karya dashi na breakfast. Kafin na kai bakin kofa, sai na tsaya cak saboda jin muryar Yakaka a cikin parlor. Hankalina ya tsaya cak, zuciyata ta fara bugawa da karfi kamar zata fito waje. Sai na dan matsa gefe don jin abinda take fada sosai. “Zainabu, wannan shine garin da malamin ya bani. Ki tabbata yau da kanki kin zubawa Ramlah acikin abincinta. Idan har taci, to wallahi za’a nemeta a rasa. Wannan shi ne matakin karshe. Malamin yace idan kika yi sakaci to shikenan, burinmu ya tashi.”

Nana hadiza

09030569336

[08/09, 6:50 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Ko da naji abunda momy take furtawa game da ni, sai jikina ya dauki rawa na koma dakina zuciyata cike da tsoro da tambayoyi marasa amsa. “Subhanallah,” nace a zuciyata, “wace irin kiyayya ce wannan? Me yasa momy ta daukeni a matsayin abokiyar gaba alhali kuwa ni ba laifina ba ne?”

Akwai lokacin da abba yake bani labari, bayan haihuwata da wata guda mahaifiyata ta rasu, momy ce ta ɗauki nauyina. Ita ce ta raineni, ta ciyar da ni, ta kula da ni. Amma me ya kawo wannan kiyayya yanzu? Shin saboda na rayu, ko kuma saboda wata zuciya ce ke neman ta cinye ta?

Ina cikin wannan tunanin sai naji muryar abba daga waje ya kwalamun kira cikin kulawa yana cewa “Ramlatu, fito mu karya, yau ina da meeting.”

Na gyara jikina cikin nutsuwa, na fito. A palon gidan na tarar da Yakaka, wacce take hira da abba. Bayan na gaida ta, sai ta juyo da murmushi tana cewa “Ramlatu, kin fito makaranta . Allah ya bada sa’a.”

Cikin jin kunya da jin daɗin addu’arta nace “Ameen, Yakaka. Nagode sosai.”

Na juya na gaida momy da yaya Billy, kowa ya amsa cikin salon nasa. Abba ya miko min kofin shayi (tea) da ya hada min da kansa, ya ce “Auta, ga shi, sha kafin mu fita.”

Na ɗan yi murmushi nace “Abba, azumi nakeyi.”

Ya girgiza kai cikin nutsuwa ya ce “To shikenan, babu damuwa. Ki ci gaba da azuminki. Amma tashi muje kafin lokaci ya kure mini.”

Na mike cikin ladabi muka fito tare. Mumy ta biyomu da kallon da ban iya fassarawa ba. Ko da muka isa bakin mota har ta kawo karshen magana tana faɗin “Adawo lafiya Abban Ramlah. Allah ya kiyaye hanya.”

Bayan abba ya amsa, sai ta juyo kaina cikin murmushi na karfin hali tace “Ramlah, me kike so na dafa miki yau?”

Duk da naji kalamanta a matsayin wata dabara, ban nuna hakan ba. Cikin ladabi nace “Jallof macaroni, Mumy.”

Ta ɗan ɗaga kai tace “To, shikenan. Zan dafa miki.”

Na amsa da “Nagode” na koma cikin mota tare da abba, amma zuciyata ta cika da al’ajabi. Wannan mace wacce ta raineni kamar ‘ya, ita ce yanzu take nuna kiyayya ta ban mamaki. Na iso makaranta cikin hanzari zuciyata na bugawa saboda latti da nayi. Har lokacin dai lecture dinmu ya fara amma na tsaya a bakin kofa ban iya shiga ba. Na kasa shiga saboda kunyar yadda dukan idanu zasu sauka kaina idan na shiga cikin ajin kuma tsaf zai iya dizgani wallahi yace nafita shiyasa nakama kaina.

Ina tsaye a bakin kofa sai ga lecturer Fahad wanda yake ɗaya daga cikin sababbin malamai da aka kawo mana kuma yafara nuna yana sona ya iso. Yana tafiya da kwarjini yana tattaunawa da lecturer dake ciki. Idanunsa suka sauka kaina na kasa ɗaga kaina sosai.

Sai kawai cikin murya mai nutsuwa da izza yace “Shiga mana, kar ki tsaya a waje haka.”

Na ɗaga kaina a hankali nace, “Nagode, Malam.”

Na shiga cikin aji zuciyata na harbawa kamar zata fito saboda yadda yake kallona lokacin da nake shiga. Sai kawai naji kamar akwai wani abu daban a idanuwansa.

Ina samun wuri na zauna sai Maryam, kawata, ta matsa kusa dani tana dariya kasa-kasa tana cewa“Kin ga ko? Wannan fa shine ranar masoyi gashi har yasanya an barki kinshigo. i kinga yadda yake kallonki kamar zai cinye ki da ido.”

Na daka mata harara amma ba tabar min magana ba.

Tun daga safe zuwa ƙarfe shida na yamma, ina cikin lecture ɗinmu da sauran abokan aji. Malamanmu suna da irin wannan salon koyarwa da yake sanya ka ji kana son ka zauna ka saurara, koda kuwa kana gajiya. A lokacin, zuciyata tana kallo zuwa gaba, tana tunanin yadda rayuwata zata kasance bayan duk waɗannan karatu da wahalar da nake sha.

Lecture ɗin farko da muka fara shine Political Science, inda Malam Ado ya tsaya tsawon awa ɗaya yana magana kan tsarin mulki da rawar da ɗalibai zasu taka a gobe mai zuwa. Wannan darasin ya tsaya min sosai, saboda yana da alaƙa da rayuwa gaba ɗaya. Bayan nan muka shiga English Literature, inda muka tattauna game da “Shakespearean Drama.” Duk da na kasance cikin lecture ɗin, hankalina a wani lokacin yana waje, yana kiran sunan da zuciyata ta saba Bashari.

Bayan kammala lecture na ƙarfe uku, muka sami ɗan hutu. Abokiyata Maryam ta matsa kusa dani tana fadin,

“Ramlah yau kinyi shiru sosai. Kina lafiya kuwa?”

Na ɗan murmusa, duk da gajiyata, nace,

“Eh Maryam, lafiyata kalau. Kawai dai tunani ne ya ɗaukeni.”

Ta girgiza kai tana dariya, tace,

“Tunani kuma? Ke dai ki kula da kanki. Kin san rayuwa sai a hankali.”

Mun ci gaba da lecture har zuwa ƙarfe shida na yamma, lokacin da muka sallami darasi na ƙarshe. Zuciyata cike da gajiya amma har yanzu akwai ƙaramin farin ciki a zuciyata. Na juyo na kalli Maryam nace,

“DanAllah ki rakani zuwa restaurant ɗin da ke kusa da faculty. Ina so nasiyo abinci kafin na tafi gida.”

Mun nufi restaurant ɗin, inda iska mai ɗan ɗumi ke kadawa, sai ƙamshin nama da soyayyen abinci yana gauraye da ƙanshin kayan ƙamshi. Na shiga ciki, na yi order na rice da chicken, sai na saka a jaka saboda ban jin yunwar ci a wurin. Sai da muka fito waje na yi godiya ga Maryam, sannan na ce,

“Zan hau napep na tafi gida. Gobe sai mu haɗu insha Allah.”

Na hau napep ɗin da sallama a bakina, zuciyata na sake daɗi saboda na hango gajiyar yau zata ƙare ne da nutsuwa a gida.

Na koma gidan ainda na tarar da su Khairiyya da Ummi yaran unclen hamza abokan wasana tun muna yara. Duk da cewa shekaru sun shige, har yanzu sa’annina ne, kuma ganin juna ya dawo da duk wata soyayya ta da. Muna ganin juna kawai muka rungume juna kamar mun dade ba mu hadu ba.

Khairiyya ce ta fara magana, kamar yadda take da hali na magana da nishadi

“kai Ramlah, kece kika zama yar lukuta haka? Tabdi’ah, gaskiya kin canza sosai, kin kara kyau fiye da da!”

Na harare ta da wasa, sannan nace da dariya “Yason ranki dai, amma tabarakallah, ni dai ban ga canjin ba. Ke dai kinfiso kiganni kamar da.”

Momy ta shigo falo a lokacin. Na kalle ta nace “Momy, sannu da gida.”

Sai dai bata amsa da murmushi ba. A maimakon sai tace “Abincinki na kitchen.”

Na dan yi shiru sannan nace “To Momy.”

Na mike zuwa kitchen na dauki abinci nawa. Na tafi dakina, inda su Khairiyya da Ummi suke jiran. Daga nan muka fara hira irin ta mata da dade ba su hadu ba. Na kawo musu abinci, nace“Ku ci naku, nawa kuma zan ci daga baya.”

Suka fara ci suna dariya, mu kuma mun ci gaba da hira. Sai dai zuciyata bata cikin natsuwa ba. Na lura da rashin halin Momy. Tun da na dawo bata taba nuna min kulawa sosai ba. Duk da haka, na daure na boye a zuciya.

A gefe guda kuma,Abincin da momy tabani nakeso naje na zubar dashi dan kuwa naji yakaka tana gayamata na 3days zata samun idan nazubar dana yau ai saura 2days kenan, dayake su khairiyya kwanaki zasuyi sai na gyaramana gadona suka kwata munata hira, muna tunawa da abubuwan baya, muna kwasar dariya.

Har mun kwanta, sai ga Momy ta turo ƙofar dakin da sauƙin murya tace

“Ramlah, zo. Abbanki yana palour, yana son ganinki.”

Na dago da sauri, zuciyata ta buga kamar kararrawa. Na amsa cikin ladabi

“To, Momy.”

Na ɗauki hijjab dina cikin natsuwa, na saka, sannan na fito zuwa falo inda Abba yake zaune a kujera Falon ya cika da ƙamshin turaren “Oud Mood” da shi kansa Abba ya fi so. Idanunsa masu nutsuwa suka juyo a kaina, sannan ya yi murmushi irin nasa wanda yake sanyaya zuciya.

“Auta, kin ci abinci?” shi ne abu na farko da ya tambaye ni.

Na yi murmushi a hankali na girgiza kai cikin ladabi.

“Eh Abba, naci.”

Sai ya jingina da kujera, ya kamo wata leda a gefensa ya miko min.

“Ga wannan, ki buɗe ki gani.”

Na amsa da hannu biyu, zuciyata na rawa. Cikin ledar na ji nauyi. Na buɗe a hankali sai naga sabuwar waya ce Samsung Galaxy S24, black colour.

Na kalle shi cikin mamaki da murmushi, idona na cike da farin ciki.

“Abba, wannan tawa ce?”

Ya yi dariya mai sauti, yana kallona da kauna

“Eh Auta.”

Na sake kallon wayar a hannuna, zuciyata ta cika da godiya. Amma kafin in gama magana sai na zura hannuna cikin ledar gaba ɗaya, na jiyo wani ƙaramin abu.

Sai ga mukullin mota a ciki. Na zaro shi da sauri, idona suka faɗaɗa.

“Abba, ga mukullinka.”

Na miƙa masa kamar na yi kuskure. Amma sai ya yi murmushi ya girgiza kai “Ba mukullina bane, Auta. Naki ne. Motarki ce na siya miki.”

Na tsaya cak kamar an dora dutse a kirjina.

“Motata? Abba, ni fa?”

Kafin ya amsa, sai ga Momy ta fito daga ɗaki tana daɗa kallonmu da mamaki, ta ce cikin ƙarfin murya:

“Mota fa? Abba, me kake nufi?”

Abba ya juyo gareta da nutsuwa.

“Eh, ita. Na sayawa Auta mota. Ai ga ziryar makaranta. Tunda yanzu ta girma, ya kamata ta dinga tafiya da kanta. Ba ita kaɗai ba, har Bilkisu ma na saya mata ai itama waccan lokacin.”

Momy ta ja numfashi da ƙarfi, fuskar ta ɗauki alamar rashin jin daɗi. Amma Abba bai kula ba, sai ya ɗan yi murmushi yana kallona.

Ni kuwa na kasa magana. Na ji zuciyata ta cika da farin ciki har sai da hawaye suka cika idona. Na ce cikin ladabi

“Abba, nagode sosai. Allah ya saka maka da alkhairi.”

“Ameen, Auta.”

Sai ya kira mai gadi, Malam Yakubu, wanda tun shekaru yake tare da mu a gidan. Mutum ne mai haƙuri da natsuwa.

“Malam Yakubu, gobe sai ka fara koyawa Auta tuki. Ita ce mai motar yanzu.”

Malam Yakubu ya murmusa yana kallona da girmamawa “Insha Allah, Alhaji. Zamu fara tun safe.”

Na ji wani irin daɗi ya ratsa zuciyata. Na miƙe da hanzari na fita zuwa wajen.

A can bakin harabar gidan, motar sabuwa ce Toyota Corolla 2024, baki kal tayi kyau sosai Na ɗaga hannuna sama cikin farin ciki na ce “Ya Subhanallah!”

Nana hadiza

09030569336

[10/09, 3:31 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

A cikin Penthouse ɗin Alhaji Muqaddam dake Burj Khalifa Dubai, ɗaya daga cikin manyan gidajen da suka fi tsada a duniya, komai cike yake da walwala da salo na masu kuɗi.ƙamshin turaren Oud da Musk na tashi a cikin iska, yana haɗuwa da ƙamshin ruwan wankan da suka fito dashi.

Ayshatu kwance take kan kujerar fata mai taushi daga Italy, jikinta a kwance saman faffadan kirjinsa, tana wasa da hannunsa tana shafa shi sosai.

Alhaji Muqaddam ya ɗan matsa ya ɗauki rigar silk ɗinsa yana kokarin sanya ta. Ayshatu ta rikoshi da murmushi mai cike da salo tace

“Baby… meye haka? Muna cikin farinciki ka tashi? Wani abu ne ya dameka?”

Ya kalleta da idanuwan da suke nuna ƙwazo da izza, sannan cikin murya mai cike da nauyi da girman kai yace

“Ya kamata mu daina ɓata lokaci da juna. Ni ina sonki sosai Ayshatu. Amma ina jin ke kin kasa cire As’ad daga zuciyarki. Abin da nake so daga gareki shi ne ki daina zama tamkar kina wasa da ni. Ki rabu da shi gaba ɗaya. End this marriage. Nina gaji da ganin ki tare da shi.”

Ayshatu ta yi wani murmushi mai cike da dabara, ta jawo kansa ta jingina a kanta. Tana shafa fuskarsa cikin salo tace

“Haba love… shine ka shiga wannan fushin? Ka daina. To ka saurara, gaskiya na gaya maka na daina sonsa tun tuni. Tunanina da zuciyata duk suna tare da kai. Abinda kake jira kawai shine lokaci. Zan gama da shi cikin natsuwa da salo, saboda bana so na nuna wani abin da zai tona asiri. Ka kwantar da hankalinka.”

Idanunsa suka sauko kanta sannan yayi murmushi, ya rungumeta jikinsa yana jin ƙamshinta. A hankali ya ɗaga hannayensa biyu ya rufe fuskarta da sumbata masu tsawo. Ayshatu ta mayar masa da martani cikin ƙwarewa kamar yadda tasaba.

Nan da nan yanayin dakin ya canza. Ƙarar ƙamshin turaren Oud ya gauraye da na Chanel No.5 da take fesawa. Wani irin yanayi ya lullube su, suka tsunduma cikin sabuwar duniyar su ta boyayyar soyayya wacce take tafiyar da su daga hankali zuwa wani yanayi na biyan sha’awa da jin daɗi na masu kuɗi.

Daga nesa, tagogin gilashin Burj Khalifa suna kallon ƙasar Dubai da hasken tituna da motocin alfarma masu launuka masu kyalli suna wucewa. Sai ƙarar Rolex ɗin Muqaddam da agogon Cartier da ke gefen gadon da suka ajiye suna haskawa a ƙarƙashin fitilon.

Ayshatu tana narkewa a jikinsa tana faɗin cikin shagwaɓa “Ni kai nake so, kai ka fi komai a wurina… Habibie na, ka kwantar da hankalinka. Ka gani nan gaba As’ad zai zama tarihi kawai.”

Alhaji Muqaddam ya ɗan dariya cikin izza, ya lumshe idanu yana rungumeta sosai sannan yace “Wannan ce kalmar da nake son jin kin faɗa min kullum… Madarata ta, kai na, soyayyata ta gaskiya. Yanzu zan nuna miki ƙauna fiye da duk wani da kika taɓa gani.”

Nan fa suka shige cikin duniyar alfasharsu mai ɗauke da kazanta, da rashin tsoron Allah da cin amana.

Bayan sun fito daga wanka, Ayshatu ta ɗauki lokaci mai tsawo tana shiryawa cikin kaya masu tsada Kaya ne na alfarma, farar riga mai walƙiya da siket, sai turaren da ya cika ɗakin da ƙamshi mai sanyi. Tana kallon madubi tana murmushi, zuciyarta cike da alfahari. Bayan ta gama, ta ɗauki wayarta ta fita daga gidan kai tsaye zuwa babban wuri da aka yi musu alƙawari da kawarta.

Da ta isa wajen, sai ta hango Fatima tuni ta iso. A take suka rungume juna da ƙarfi. Fatima ce ta fara magana cikin nishaɗi “Kawata! Ke fa ba yanzu ba wannan ƙasar, ba wancan ƙasar. Yanzu kuma kina dubai? Me kuma kikeyi anan bangaren bayan nasan yaranki basa nan bangaren?”

Ayshatu ta saki murmushi mai ɗaukar hankali, ta ɗan ɗaga gira alamar izza. “Fatima kenan! Ina naga zama a wuri guda? Ina tare da sugar dady na. Duk inda ya je, to nan nima zanje. Rayuwar masu kuɗi kenan, ba ta da daidaito.”

Fatima ta dan yi shiru tana kallonta da mamaki, sannan ta girgiza kai. “Ayshatu, baki da hankali wallahi. Har yanzu baki nutsu ba? Har yanzu baki gane duniya ba? Wallahi bana son ki rasa As’ad. Wannan daman daya ne.”

Maganar ta fito ne daga zuciya, da gaske take yi mata nasiha.

Sai Ayshatu ta ɗan buge baki, ta harareta da kallo mai ɗauke da raini. “Fatima, ban gane me kike nufi ba. Wayagamiki? Son As’ad nake! Ki ji tsaf mahaifiyata baiwa ce a cikin gidansu, wacce aka ‘yantata kafin ta mutu. Ni kuma ta barni hannun uwargidan sarki, wacce na tashi a gidanta ina mata aiki, komai nata sai ni. Amma tun ina ƙarama zuciyata na cike da kaunar As’ad. Mahaifiyarsa ma ta san halin mahaifiyata wajen rashin kyan hali. Saboda haka ita tafara hana auren alokacin dataji suka nuna sai dai ƴar aikin As'ad badai mata ba.”

Ta dan ja numfashi sannan ta cigaba da magana cikin izza “Na shiga malamai, na mallaki zuciyar mutanen gidan tas. Har sai da na zame musu abin dogaro. Sai na auri As’ad. Da gaske na aure shi ba don komai ba sai don in tabbatar da matsayina a duniya. Fatima, na dade ina mafarkin zama wata mace mai izza, mace da ake kallo a cikin al’umma. Yanzu na samu, nayi ilimi, nayi kuɗi, na shahara da manyan mutane. Gayamin, menene ban samu ba?”

Fatima ta kalleta da ido jajayen hawaye, ta girgiza kai cikin damuwa. “Ayshatu, kina ganin kuɗi da matsayi shi ne komai? Ba kya tunanin wata rana za ki rasa duk wannan ki koma ba komai? Wallahi zuciyarki tana taurin kai. Allah dai ya shiryar dake.”

Ayshatu ta yi dariya mai sauti, wacce ke nuna girman kai da isa. “Fatima, ki bar wannan tunanin talakawa. Ni yanzu ba a irin wannan tunanin nake ba. Ni ina rayuwa irin ta masu kuɗi. Villas a Paris, otal-otal a Dubai, motoci masu tsada, da turaren da ko a kasuwannin duniya ba a samu. Fatima, na wuce wannan matakin.”

Sai ta zaro wayarta mai walƙiya ta nuna wa Fatima hotunan da take ɗauka a wurare daban-daban na duniya tare da As’ad, cikin kayan alfarma.

Fatima ta kalleta da mamaki da kuma tausayin zuciya. “Ayshatu, wallahi zuciya ba ta huta da irin wannan. Karki manta da tushe. Kuɗi ba sa kawo salama, suna iya ɓata mutum idan bai kiyaye ba. Karki bari son sugar dadynki da son kuɗi su rufe miki ido gaskiya nake gayamiki idan kika rasa As'ad wallahi Allah kin cuci kanki ko bashida lafiya bai cancanci haka ba .”

Fatima ta kalli Ayshatu cike da mamaki, idonta kamar zai faso hawaye. Ta ce cikin rawar murya

“Ayshatu, kece baki son As’ad? Wallahi karya kike! Kowa yasan ke majanunuwa ce akan mijinki. Duk rayuwarki As’ad kike bugawa da shi.”

Ayshatu kuwa ta saki wata dariya ta classy, dariyar da ke cike da izza da alfahari, kamar wata sarauniya.

“Fatima, ina son As’ad ne domin na zama wata. Ina son sa ne domin na mallaki kuɗi. Kuma yanzu nasamu! Ba kawai kuɗi ba yanzu nasamu abin da ake kira true love.”

Fatima ta kasa yarda da abin da ta ji. Sai ta kama hannun kawarta da tausayawa, tana ƙoƙarin nuna mata gaskiya.

“Kawata, please ki yi tunani kafin ki ɗauki kowanne mataki. Kada ki faɗa cikin tarkon zuciyarki. Ki sani, ba kowane namiji ne zai kaunace ki da gaske bayan As’ad ba. Kuma wannan da kike kira true love ɗin ki, ki fahimci cewa As’ad ɗin nan shi ne kaunarki ta gaskiya. Kin riga kin same shi, me kike nema bayan haka?”

Ayshatu ta ja hannunta daga na Fatima da ƙarfin zuciya, ta ɗan ja tsaki. “Fatima, baki da right na bani shawara a kan rayuwata. Ni na fi kowa sanin abin da ya dace da ni. Wannan rayuwata ce, kuma zan tafiyar da ita yadda nake so. A yanzu, ina da flight ɗin da zan bi. See you next time.”

Fatima ta tsaya cak tana kallonta, ta kasa cewa uffan. Idonta kawai ya cika da hawaye. Ta ɗaga kai alamar yarda, koda kuwa zuciyarta ta tsinke da tsoro da damuwa.

Ayshatu ta janye jikinta, ta nufi motarta direba ya buɗe mata ƙofa. Fatima ta tsaya a wajen tana kallo, zuciyarta cike da tunani.

“Allah ka shiryar da ita, kafin ta kai kanta wajen halaka.”

Nana hadiza

09030569336

[12/09, 3:18 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Kwanakin nan As’ad bai samun hutawa kwata-kwata. Rayuwarsa ta cika da tarurruka da shirin buɗe sabuwar kamfani a ƙarƙashin empire ɗinsa. Tun kwanaki biyu da dawowarsa daga Switzerland, inda ya je kan harkokin kasuwanci da masu hannun jari, bai huta da aiki ba. Amma duk da haka, zuciyarsa na cike da rashin kwanciyar hankali domin Ayshatu, matar da ya fi kauna, har yanzu bata dawo ba.

Ta ce masa za ta tafi wani important meeting, daga nan kuma ta nufi Dubai. Amma lokacin da ya kira Nawal domin tabbatarwa, sai ta ce masa Ayshatu bata zo Dubai ba kwata-kwata. Wannan rashin gaskiyar nata ne ya shiga ran As’ad.

Cikin nutsuwa ya shiga ɗakin sa mai yalwa, gadon king-size ɗin da aka yi da kayan alfarma na Italian design. Ya zauna a gefen gadon yana dan zura ido cikin system ɗin sa da ke gefensa, yana bin wasu bayanan kasuwanci. A gefe kuma an aje masa gilashin green tea mai ɗumi, yana ɗan sha sannu a hankali, kamar wanda ke so ya takaita damuwa.

Sai kawai wayarsa ta fara ƙara. Ba kowa bane P.A ɗinsa ne. A ko da yaushe P.A ɗinsa yana magana da ladabi, yana kiran sa cikin tsananin girmamawa “Baraka da yanzu, ranka ya daɗe. Mai martaba ya ce ka shirya domin akwai wani mutum da ka taɓa yiwa alheri, tun dazu yake cewa yana so ya sadu da kai. Yanzu dai an turosu, yana babban palour yana jiranka.”

As’ad bai yi wani dogon bayani ba, bai ɗaga murya ba. Ya amsa cikin takatsantsan kamar yadda yake yi idan baya son ɓata lokaci “Okay.”

Ya kashe wayar, ya jingina da kujerar gefen gado na ɗan lokaci, yana mai saƙa tunani. A duk inda yake, komai nashi yana tafiya da tsari daga tsarin isowar baki har zuwa yadda ake gabatar musu da shi. Mutane sun saba cewa, a gidan As’ad babu wanda zai shigo babban palour sai da dalili mai muhimmanci.

Bayan mintuna kaɗan, an sanar da shi mutumin da ya taɓa taimakawa tun da dadewa yanzu yana jira a babban palour.

As’ad ya miƙe tsaye cikin natsuwa, ya ɗauki agogon hannunsa mai tsada Rolex Platinum, ya daidaita rigarsa mai alfarma, sannan ya nufi ƙofar ɗakin. Hanya daga ɗakinsa zuwa babban palour ɗinsa tana nuna irin darajar rayuwar da yake yi fitilun chandelier masu walƙiya daga sama da ƙamshi na oud da aka fesa dukkan gidan.

Daga nesa kallo ɗaya, mutum zai fahimci cewa As’ad ba ƙaramin mutum ba ne mutum ne da duniya ke ɗaukaka sunansa.

Da As’ad ya fito daga ɗakinsa cikin nutsuwa, ya nufi babban palour ɗinsa wanda ya sha kayan alfarma. Kallo ɗaya kacal zai tabbatar maka wannan ba gidan kowa bane gidan mutum ne da duniya ta ɗauka a matsayin multibillionaire.

Mutumin da aka kawo ya miƙe da girmamawa da ganin shi. Tuni ya yiwa As’ad gaisuwa da ladabi kamar yadda ake yi wa manya “Ranka ya daɗe, nagode! Nagode da alherin da kayi min. Jindadin da muka yi lokacin nan yasa na ce ba zan bar haka ba, sai na zo nan gida nayi godiya da kaina. Allah ya sani, naji daɗin irin yadda aka karrama ni.”

As’ad ya tsaya yana sauraro cikin nutsuwa, bai yi gaggawar amsawa ba. Murmushi mai ɗauke da hikima ya bayyana a fuskarsa. Mutane sun saba da irin wannan nutsuwar tasa wanda ya saba da mulki da kuɗi baya taɓa gaggawa wajen magana.

Sai mutumin ya zaro small parcel daga jaka, ya mika da hannunsa yana cewa

“Ranka ya daɗe, wannan rubutu ne na kawo maka. Natsari ne ana sha, ana kuma shafe jiki da shi. Na kawo shi da zuciya ɗaya saboda sharrin masu sharri. Dan Allah ka amshi wannan ƙaramin kyauta daga gare ni.”

As’ad ya amsa da murmushi, ya ɗan ɗaga hannunsa alamar karɓa.

“Nagode, Baba. Allah ya saka da alheri.”

Ya karɓi natsarin da ladabi, sannan ya yi alamar ajiye shi a gefe. Irin nutsuwarsa da salon magana tasa ya sa duk wanda ke kallonsa ya fahimci cewa wannan mutum ba mai ƙi kyauta bane, amma kuma baya nuna wata alama ta buƙata komai nasa yana tafiya da izza.

P.a da ke gefe ya karɓi kyautar cikin girmamawa, ya ajiye a kan teburin da aka kawata da gilashin crystal.

As’ad ya zauna a kujera mai faɗi da aka yi masa musamman daga Milan design house. Ya ɗan gyara agogon hannunsa Rolex Platinum, yana kallon mutumin da nutsuwa.

“Duniya dai tana tafiya da kyakkyawan zuciya, Baba. Allah ya saka maka da alheri da albarka. Kuma kada ka damu babu wanda zai iya shafar abin da Allah ya kare.”

Mutumin ya sadda kai ƙasa cikin godiya. A zuciyarsa, ya ƙara tabbatar da cewa As’ad mutum ne da ba a samu irinsa da sauƙi ba ba kawai mai kuɗi bane, mai kirki ne wanda ya san darajar mutane.

Bayan As’ad ya gama gaisawa da mutumin, ya koma ɗakinsa cikin nutsuwa. A can ya ɗan zauna na ɗan lokaci, sannan ya miƙe tsaye da cikakken shiri.

Ya shiga cikin wardrobe ɗinsa mai yalwa, inda riguna da kaya masu tsada daga ƙasashen duniya suke a tsare. A hankali ya zabi ɗaya daga cikin manyan traditional attires ɗinsa na alfarma, wanda aka dinka masa musamman daga Dubai da handmade embroidery. Ya sanya rigar tare da rawani mai kyau, ya kammala shirin da agogon hannunsa mai daraja Patek Philippe da takalman Italian leather. Duk wanda ya ganshi a wannan lokacin zai fahimci cewa As’ad mutum ne da yake da daraja ta daban.

Da ya fito daga ɗakin, P.A ɗinsa ya yi saurin mikewa tsaye da girmamawa, ya ɗan sunkuyar da kai yana jiran umarni.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull