Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 11

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 11

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 11: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 11. “Yes, ranka ya daɗe.”

4,480 words

“Yes, ranka ya daɗe.”

As’ad ya kalle shi cikin nutsuwa, murya mai sanyi amma cike da iko ta fito daga bakinsa

“Ka sanar da Abba. A cikin awa ɗaya za mu fita tare zuwa gidan abokina. Ka tabbatar komai ya shirya yadda ya kamata.”

“To, ranka ya daɗe.” P.A ɗin ya amsa cikin ladabi, sannan ya fice da gaggawa domin shirya motoci, direbobi, da tsaro.

A cikin gidan, masu tsaron lafiyarsa suka fara kai-komo, suna daidaita jerin motocin convoy Range Rover guda biyu a gaba, Mercedes Maybach nasa a tsakiya, sannan G-Wagon guda biyu a baya domin tabbatar da cikakken tsaro.

As’ad ya tsaya a jikin balcony ɗinsa na sama, yana kallon yadda ake shirya komai da tsari, yana ɗan lumshe ido yana shan iska. Fuskar sa ta nuna natsuwa da kwarjini irin yanayin shugabanni da manyan attajirai da kowa ke kallon su da izza.

*******

Wayata ta yi ƙara da notification, na ɗaga idona na kalle ta. Sai ga wani sabon text ya shigo, kalaman soyayya cike da kwarjini da sanyi. Na yi tsaki, na girgiza kai.

“Wayyo Allah, wanene wannan kuma ke ta turo min sakon soyayya haka?” Na furta a zuciyata. Sai kawai na share sakon, ban tsaya karantawa ba.

A gefe kuma, Maryam tana ta dariya kasa-kasa, tana kallona da idanuwa masu cike da zuga.

“Wallahi Ramlah, naga ranar da za ki waye. Nice dai wallahi, nasamu wannan ɗan gayen. Ai shikenan, sai soyayya samarin da duk sun zama ƴan iska.”

harararta nayi “Ke dai babu wani aikin kirki sai soyayya. Ni dai banda lokacin wannan. Kinga tunda mungama lecture, bari in wuce gida.”

Muka fito daga harabar makaranta tare, ita ta nufi hostel ɗinsu, ni kuma na nufi parking lot inda motata take tsaye tana kyalli a ƙarƙashin hasken rana. Na buɗe mota na shiga, hannuna ya faɗa kan sitiyari.

Nan take nashiga tunani yau da safe lokacin da nake fita gida, su Momy sai soye-soye kawai suke yi. Gidan ya cika da ƙamshin albasa da kayan ƙamshi. Ban san ko baki suke jira ba, ko kuma kawai nishaɗin gidan ne.

Na tada motar na nufi gida cikin nutsuwa, tayoyi na murza hanya da laushi. Da na isa bakin gate, na danna horn, masu gadi suka yi saurin buɗe min tare da gaisuwa cikin ladabi. Na shiga cikin gidan na ajiye motar a wajen da aka ware min.

Da sallama na shiga gidan. Sai na ji muryar Momy daga falon ciki, tana magana da ɗan ɗaga murya “Ke Bilkisu, kiyi wanka ki shirya, suna kusa karasowa.”

Sai kuma na ji Billy ta amsa da fara’a “Toh Momy.”

Ni kuwa cikin ladabi na ce “Sannu da gida Momy.” Na wuce kai tsaye ban tsaya bin maganarsu ba.

Na ɗauki Indomie guda biyu na fita kitchen domin dafa wa kaina. Ina tsaka da bude pot sai mai aikinmu ta shigo cikin natsuwa. Ta tsaya tana murmushi sannan ta ce

“Auta, bari na gaya miki. Yau saurayin Bilkisu ne zai zo. Ba ki ga yadda aka yi snacks da abinci ba? Duk don zuwansa.”

Na saki murmushi cikin jin daɗi.

“Kai, Alhamdulillah! Wallahi na ji daɗi sosai. Allah ya sa alheri. To, kuɗi za a kawo kenan?”

Mai aikin ta ɗan kwaɓe fuska ta ce

“Wai Allah, ni ban sani ba. Kinsan halin matar nan dai. Ai sai dai mu jira mu gani.”

Na girgiza kai cikin murmushi..

Nana hadiza

09030569336

[15/09, 10:55 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Na bar wa mai aikin mu kitchen ɗin batare da na ce mata komai ba. Na koma dakina, na baza littafina a gado. Bayan na gama cin indomie ɗin da na dafa, sai na fara karatu sosai, zuciyata a tsare saboda jarabawar da ke tafe.

Lokaci na wucewa, isha’i na ƙara matsowa. A hankali na fara jin ƙarar motoci daga bakin gate, hayaniyar su ya cika gidan. Ban damu da komai ba, domin tun da mai aikin mu ta sanar da ni cewa yau saurayin Yaya Bilkisu zai zo, ba wani sabon abu bane a gare ni.

Na ɗan ɗaga wayata, nayi chatting da Maryam kaɗan kafin naji gajiya. Na rufe chatting ɗin, ina kokarin ajiye wayar sai ga sabon text ya shigo. Da na duba, sai naga daga Malam Fahad ne malaminmu a jami’a.

Na saki murmushi na kaina, ban yi masa reply ba. Na aje wayar gefe, na lumshe ido cikin shirin cigaba da karatu, zuciyata a ɗan nishadantar da sakon.

Na janyo wayata daga gefen gado, na duba notification ɗin da ya shigo. Da na buɗe sai naga daga Malam Fahad ne. Zuciyata ta buga kaɗan, wani irin nishaɗi ya ratsa ni.

Sakon nasa dai ba wani dogo bane, amma kalaman da ya yi sun yi nauyi fiye da rubutun da aka yi

“Ramlah, kina lafiya kuwa? Na dade ban ji muryarki ba. Ina fatan karatun yau ya tafi lafiya.”

Na tsaya na karanta sakon sau biyu, zuciyata ta cika da wani irin sanyi. Wani murmushi ya subuce daga fuskata ba tare da na shirya ba. Duk da haka, ban yi reply ba kawai na aje wayar gefe, amma tunaninsa ya tsaya a zuciyata.

Knocking naji a ƙofar dakina. Yaya Billy ce ta tura ƙofar a hankali, ta leƙa da murmushi.

“Ramlah, kizo inji Abba.”

Na ɗaga kai daga littafina, nace “Toh.” Ban damu ba, saboda na ɗauka baki tuni sun tafi. Don haka sai kawai na ja ɗankwalina, na fice ina danna wayata. Maryam ma nake yiwa reply a chat ɗinmu.

Sai dai tun daga nesa wani ƙamshi mai ƙarfi ya daki hancina ƙamshin turaren alfarma, irin wanda ake yi wa manyan baki. Da na taka harabar palon, sai idona ya sauka a wajen da ya cika da mutane. Fuska masu tsabta, tufafi na alfarma, da dogarai a kowane kusurwa.

Atake kunya ta lullube ni. Na juya da sauri kamar zan koma dakina, amma sai na tuna wannan ba zai yiwu ba. Don haka na sa hijabi cikin hanzari, na fito da natsuwa.

Karaf, sai na ji muryar Momy cikin ɗan tsawa:

“Ke, baki da nutsuwa ne Ramlah? Kina shiga wajen mutane haka?”

Na yi saurin kare kaina cikin ladabi:

“Mumy, bansan da baki ba shi yasa.”

Na ƙarasa cikin ladabi, na zauna ƙasa kusa da Abba. Na ce da muryar biyayya:

“Abba, sannu da dawowa. Ina wuni?”

Sai wasu daga cikin dogarai suka amsa da natsuwa “Yauwa, lafiya lau.”

Idona ya ɗago a hankali ya sauka ga wani mutum mai kyawun fuska da girman hali, yana zaune kusa da Abba suna magana cikin nutsuwa. Kallo ɗaya kaɗai ya isa ya tabbatar da cewa wannan ba mutum na talakawa bane. Sai naji zuciyata ta buga kamar baiji gaisuwata ba ko kuma ya ƙi kulawa.

Na ɗan matsa gefe cikin kunya, sai kuma naji wani matashi daga cikin taron ya ce da fara’a

“Abba Kabiru, wannan ce yarinyar Asubuti ko?”

Sai Abba ya murmusa ya ce:

“Eh, Ramlatu ce. Ga Babanki nan, As’ad. Nasan ke baki sanshi ba, Bilkisu ce ke zuwa gidansa dama.”

Na saki baki cikin gaggawa, na ce da ladabi:

“Ina wuni, Abba.”

Amma sai shiru. Ban ji amsarsa ba, sai ma yadda nake ganin kamar ya yi banza da ni. Hakan ya sa zuciyata ta tsinke, na sadda kai ƙasa na yi shiru.

Abba ya murmusa cikin natsuwa:

“Shi ne wanda ya kula dake a Asubuti.”

Sai na danne zuciyata, ban ce komai ba. Kallo ɗaya kacal na sake yi masa, sai dai na ji kamar ya dizgani da kallo mai ƙarfi, har sai da na juya idona cikin kunya.

A wannan lokacin Momy ta katse shiru, ta ce da ƙarfi

“Bilkisu, zuba musu ruwa mana!”

Sai lokacin na lura da Yaya Bilkisu. Wallahi saura kiris dariya ta kamani, saboda ganin irin shirin da tayi. Wani kwalliya ta zana kanta da foundation mai nauyi, ta yi kwalliya irin ta Instagram slay queens, kamar aljana.

Ta miƙe tana takawa cikin yanga, kamar tana catwalk. Na tsaya shiru ina kallonta, ban ce komai ba, zuciyata na ta yi dariya a ɓoye.

Sai na ɗago kaina a hankali, caraf idona ya haɗu da nasa. Wani irin zafi ya ratsani kamar idon nasa yana shiga zuciyata kai tsaye. Shiru ya biyo baya na daƙiƙu kaɗan kafin ya furta da murya mai nauyi, cikin natsuwar manya:

“Malam, yanzu wannan yarinyar kaiwa aure da wuri haka? I think she is too young.”

Na kasa motsawa. Kalmar tasa ta tsaya a kunne na tana dukan zuciyata.

Abba ya yi murmushi, murmushin wanda ya saba da irin tambayar nan:

“Young? Ai ba a kirga yarinta da aure. Mijin nata nake baka labari, ai ya rasu tun tuni.”

Na lumshe ido, zuciyata ta buga da sauri. Ban ji abin da As’ad ya ce daga baya ba ko dai shiru yayi, ko kuma ya amsa cikin nutsuwa da bashi da yawa. Amma kaina ya riga ya rikice.

Sai kawai na ji Momy ta yi alamar kiran ido, ta na nuna min da hannu cikin sirri in tashi in fita.

Nan take na miƙe tsaye, na gaishe su da murmushi na dole. Ban tsaya jiran wani amsa ba, na fice daga palon cikin natsuwa, zuciyata cike da nauyi.

Kamar iska na ji jikina ya yi sanyi. Na fita daga wajen, zuciyata tana ta dukan tambayoyi da ban iya ba musu amsa ba.

Bayan na fice daga palon, sai na bar su cikin hirar manya. Na shiga dakina, zuciyata na ta tsalle-tsalle saboda kallon da muka haɗa da As’ad.

A palon kuwa, shiru ya ɗan ɗauki wajen na wasu daƙiƙu kafin As’ad ya ɗago idonsa ya kalli Abba. Ya gyara zamansa cikin natsuwa, ya ɗauki kofar ruwa ya sha kaɗan sannan ya ajiye a kan side table.

Sai ya miƙe tsaye cikin mutunci, ya ɗan gyara rigarsa mai kyau. Ya dubi Abba da murmushi mai ɗauke da girmamawa

“ Kabiru, nagode da karɓar da aka yi min yau. Allah ya saka da alheri. Zan koma yanzu saboda akwai wasu meetings da suka jira.”

Abba ya ɗaga kansa cikin farin ciki, ya ce

“Allah ya saka da alheri, As’ad. Ka tafi lafiya. Ka sani gidan nan naka ne. Duk lokacin da kake da lokaci, muna jiran zuwanka.”

As’ad ya ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa. Ya miƙa hannunsa ga Abba suka yi musabaha da natsuwa.

Momy ma ta yi murmushi, ta ce da shi –l “Allah ya tsare hanya, ya ƙara maka lafiya da arziki.”

As’ad ya ɗaga hannunsa cikin ladabi:

“Amin, Nagode.”

Dogarinsa ya buɗe ƙofar, sai As’ad ya fito a hankali. Da ya isa harabar gidan, sai convoy ɗinsa ya ɗauke shi da cikakken tsari motocin tsaro a gaba da baya, sai motar shi a tsakiya.

Abba ya tsaya a window yana kallonsa har sai da suka fita daga gidan, zuciyarsa cike da gamsuwa da irin mutumin da Allah ya haɗa shi da shi.

Bayan As’ad ya fita daga gidan, palon ya ɗan yi shiru. Kowa ya shiga cikin tunaninsa, sai dai Momy ce ta katse wannan shiru da magana mai ƙarfi.

Ta juyo ta kalli Abba, idonta cike da son ganin abin da take mafarki ya tabbata.

“Abban Ramlah, dama zaka haɗa As’ad da Bilkisu. Dan Allah, ya aureta. Ka ga irin mutumin da yake? Allah ya albarkace shi da dukiya da daraja. Wallahi Bilkisu ce ta dace da shi.”

Muryarta ta cika da gamsuwa, tana kallon Abba kamar tana roƙon sa ya amince.

Abba ya kalleta cikin natsuwa, ya yi murmushi mai ɗauke da hikima.

“zainabu, aure ba don arziki da kuɗi kaɗai ake yi ba.dan akwai rabo, to ba za mu iya hana shi ba. Amma idan babu rabo, ba zai tabbata ba, ko da kuwa As’ad ɗin ya mallaki duniya gaba ɗaya.”

Momy ta girgiza kai cikin rashin gamsuwa, ta ce da sauri “To ai Bilkisu ce ta dace. Tunda ta saba zuwa gidansa, to ya kamata kayi masa maganar.”

Abba ya juyo gareta da wani irin kallo na mai

Abba kuwa ya ja numfashi mai nauyi, ya lumshe ido. Zuciyarsa ta cika da tunani mai zurfi musamman tun da ya lura da yadda idon As’ad ya tsaya kan Ramlah fiye da Bilkisu.

Nana hadiza

09030569336

[18/09, 8:03 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ASHIRIN DA TARA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Washegari da safe ban da wani lecture, don haka na yi wanka cikin nutsuwa, na shirya kamar yadda nake so. Na fita zuwa saloon da ke cikin unguwar mu, inda aka yi min wanken kai sosai na ƙwararru, aka bar gashin kaina yana sheƙi. Aka yi min ɗan light lalle a hannuwa da yatsu, wanda ya ƙara ba ni wani fresh look na mace mai tsafta. Duk da cewa lalle ɗin ba na aure bane, amma yayi kyau sosai har yana haskawa a kan fata ta.

Da na dawo gida, sai na zauna na ɗan huta. A wannan lokacin akwai wani series da nake bi sosai a tashar MBC 4, wanda nake ji yana cike da darussa da nishaɗi. Na jingina da matashin kujera a falonmu, ina lumshe ido ina kallon shirin, zuciyata cike da annashuwa.

Lokacin sallar isha’i ya yi. Na miƙe cikin natsuwa na ɗauki alwala, na tsaya a daki nayi salla. Bayan na idar, sai na dawo falon cikin nutsuwa, na ci gaba da kallon series ɗina.

A daren nan, yunwa ta ɗan taso ni saboda ban ci abinci sosai ba tun rana. Na tashi na ɗan fita zuwa wani joint da ke kusa da gidanmu. Na siya shawarma guda biyu wanda yake ɗauke da chicken da salad mai yaji sannan na dawo gida cikin natsuwa. Na shiga kitchen na dafawa kaina tea mai madara, sai na haɗa komai a tray na zauna a falon. Na ɗauki gilashin tea ɗina ina sha a hankali, na cinye ɗaya daga cikin shawarma ɗin. Na ji jikina ya yi sanyi, zuciyata cike da jin dadi. Sai kawai na ji muryar Abba daga falon ƙasa, yana kiran sunana da natsuwa. Da na ji haka, sai na miƙe tsaye da sauri. Na ɗauka yana buƙatar abinci, don haka na nufi kitchen domin dakko masa.

Amma kafin na shiga kitchen ɗin, sai na ji muryarsa daga nesa yana cewa “Ramlah, ba sai kin kawo ba. Zo kawai ki zauna.”

Na tsaya cak, zuciyata ta buga. Da alama yau akwai wani abu da Abba yake so ya yi min magana a kai. Amma kuma da mamaki banji yace komai ba. Ban yi musu ba, sai kawai na dawo cikin falon da shawarmata a hannuna. Amma ganin irin yanayin da yake ciki, sai na ajiye shawarmar gefe na miƙe tsaye da ladabi. A lokacin Momy ce ta fito daga cikin ɗaki cikin nutsuwa, ta ƙaraso inda Abba yake zaune. Ta yi masa sannu da dawowa da murmushi. “Sannu da dawowa Abban Ramlah.” Abba ya amsa da murmushi mai sanyi, sannan ya gyara zamansa a kujerar falon mai yalwa. Momy kuma ta ɗan shige kitchen ɗin ta dawo da tray ɗin abinci mai ɗumi, ta ajiye a gabansa da ladabi. Kamar yadda yaka yace sai munci abincin nan tare kuma bayason wannan shawarmar danake ci dan ba abinci bace ba.

Momy ta ɗan gyara zamanta a gefen Abba, tana kallonsa da wani irin murmushi mai ɗauke da hikimar mata. Sai ta ce da shi cikin sanyi, kamar wacce ke fara magana a hankali don ta ji yadda zai karɓa “Abban Auta, dazu na je family house. Na ji ana ta magana akan batun Ramlah. Wai sai manemani suke fitowa, kowa yana tambaya, kowa yana nema. To me zai hana ka zabar mata ɗaya kawai, ka ɗaura mata aure? Ka huta, ta huta.”

Na ɗago kaina cikin tashin hankali, zuciyata ta doka da ƙarfi. Na kalli Momy da sauri, idona cike da mamaki da shakku. “Ni kuma aure? Wannan magana ta fito haka kawai?” Ban iya cewa komai ba, saboda ganin yadda ta ƙara kallona tana murmushi, kamar wacce ke jin kanta a kan shawarar da ta bayar.

Abba bai ce uffan ba. Sai kawai ya ci gaba da cin abincinsa cikin natsuwa kamar bai ji maganar ba. Wannan shiru nasa ya ƙara tsoratar da ni. Ban san dalilin da yasa zuciyata ke bugawa da sauri haka ba.

Har muka gama cin abincin da aka kawo, Abba bai sake magana kan lamarin ba. Na miƙe cikin ladabi, na kwashe kwanukan na kai kitchen. A can na ɗauki lemo da ruwa, na dawo falon cikin natsuwa.

Na ajiye a gabansa, na koma na zauna a wurina. Sai ga Yaya Bilkisu ta fito daga ɗakinta cikin shigar da ta ɗan yi kyau, tana ɗauke da wayarta a hannu. Ta zauna a gefe cikin izza, kamar wacce ke jiran wani abu.

Cikin natsuwa, Abba ya ɗan gyara murya, ya dubi Momy yana cewa “Zainabu, ai yanzu babu wadda nake so in ga na fara yi mata aure sama da Bilkisu. Auta ai, sai dai idan ita ce ta fito fili ta zaɓo, ta ce tana so. Amma ni da kaina, Bilkisu ce ta fiye min a yanzu.”

Momy ta yi murmushi, tana kallona da ido mai ɗauke da ma’ana. Sai ta ce cikin fara’a “To, Abban Ramlah, kayi masa magana ne?”

Na tsinke ido cikin tashin hankali, zuciyata ta yi wani irin bugu mai ƙarfi. Ban san yadda zan yi ba, balle in furta komai. Na ji jikina ya yi sanyi, kamar ruwa aka zuba min.

Sai kawai Abba ya yi murmushi mai sanyi, ya juyo da kallonsa kaina. Idonsa mai zurfi ya tsaya a cikin nawa.

“Ubansa ne ni da zan yi masa aure? Ke fa Zainabu, wani sa’in kanki baya lissafi. Idan da ace maneman da ake yi akan maganar Ramlah ne suke zuwarwa Bilkisu, da na ce lallai na ji daɗi. Amma yanzu da kaina, babu abin da zan yi mata face in jira ta bayyana ra’ayinta.”

Kalmar tasa ta fito da nauyi. Na ji kamar an sauke dutse daga ƙirjina saboda a lokaci guda ta tabbatar min cewa Abba baya tunanin tursasa ni. Amma kuma ta ƙara bani mamaki “Manema da yawa ne suke fitowa saboda ni? Kuma sai ace sun canza suna zuwa Bilkisu?”

Momy ta yi dariya mai ɗan ƙarfi, tana girgiza kai kamar wacce ke jin kanta “Kai Abban Auta, kai ne da wannan salon natsuwa da sauƙi. To ni dai Allah ya nuna min ranar da zan ga Bilkisu ta zama matar aure a gidan mai daraja. Wannan shi ne burina.”

Abba ya ɗan ɗauki ruwa, ya kurɓa cikin natsuwa. Sai ya kalli Momy cikin ido ya ce da murya mai sanyi amma mai cike da ma’ana “Mijinta? To shi waye mijin nata? Ke dai kina son sauri ne, amma ba saurin nan ake buƙata a rayuwa ba. Allah ne ke tsara aure, ba mu ba. Idan Allah ya ce ga wanda zai zama nata, to babu wanda zai iya hanawa.”

Momy ta yi shiru. Amma na ga yadda ta ɗora hannunta a kirji “Ni dai Allah yasa Bilkisu ce matarsa Wallahi ba zan iya jure ta rasa wannan damar ba akasar nan fa yana cikin manyan masu kudi. To amma Abban Ramlah, naga amininka ne. Ka ga ya dace da Bilkisu.”

Abba ya yi saurin dakatar da ita “Wani irin amini, Zainabu? Dan Allah ki bar wannan maganar. Na gaya miki, ba zai taɓa son Bilkisu ba. Wallahi kinsan halinsa. Wannan magana dai ki bari, kar ta sake fitowa daga bakinki Allah zai kawo wa yarinyata miji na gari.”

Ya ɗan yi shiru, sannan ya ɗaga murya kaɗan cikin gajiya “Ku je ga Isa can. Ya kaiku gidan gaisuwar ko, bani son damuwa yanzu. Auta, tashi ki saka mayafi, ku tafi. Bilkisu ke ma ki shirya.”

Duk muka amsa cikin ladabi“Toh.” Mun tashi muka shirya cikin hanzari. Muka fito waje cikin motar gidan, muka nufi gidan Najeef kanin Abbanmu ne. Shine mahaifin matar da ya rasu, Anty Faiza.

Ko da muka isa, gidan ya cika da jama’a. Ni dai da yake ban fiye shiga cikin harkokin su ba saboda wasu daga cikin dangin Abba basu kaunata sosai, sai kawai nake zama a gefe cikin nutsuwa. Na tsaya har wajen Uncle Hamza, muka gaisa da mutunci. Ya dubeni da murmushi yana tambayata

“Ramlah, ya kike? Yaya zaman ki a gida?”

Na amsa cikin ladabi

“Alhamdulillah, babu komai, komai lafiya lau.”

Ya ɗan jinjina kai sannan ya ce

“Ai yaya Malam yace min yana da magana dani. Yana nemana gobe a office ɗinsa. Bansan kan menene ba, amma zanje naji”

Na yi murmushi na ce “Toh Uncle.” Na kasa tambayar komai, sai kawai na dan yi dariya na bar maganar ta shuɗe.

Daga baya na shiga dakin Anty Faiza, inda na tarar da ita da Momy suna hira cikin natsuwa. Sai kawai na ji tana ce mata da ɗan Masifa “Ke kuwa Zainabu, me yarinyarki zata yi da nakasheshen can? Ko baki san halin sa ba? Ai babu wanda bai san labarinsa ba. Haka nan rabuwarsa da Haneefa ta tabbatar. Ke ma ki kiyaye kuma wannan matar tasa wallahi sai ta sabauta miki yarinyar dan ba imani ne da'ita ba ta mallekeshi gaba daya.”

Na tsaya a gefe kamar mara sauti. Ban fahimci menene suke nufi ba. Kalmar “nakasheshen” da “rabuwarsa da Haneefa” sun tsaya a kunnena, amma zuciyata ta kasa daidaita su da wani mutum na ainihi.

Momy kuwa tayi shiru, bata amsa komai ba. Sai dai ta zauna tana sauraro, ta na kada kai, kamar tana boye wani abu. Anty Faiza kuma ta ci gaba da bata labarin cikin zurfi. Ni dai na tsaya ina sauraronsu a shiru, zuciyata cike da tambayoyi marasa amsa.

Bayan dare yayi, aka gama gaisuwa, muka tattara muka yi sallama muka nufi gida. Zuciyata har yanzu tana juyawa kan maganganun da na ji, amma ban samu ƙwararan amsoshi ba.

Ni dai bayan na karasa gida wanka nayi, sai na nufi gadona cikin natsuwa. Na kwanta da niyyar hutu, domin zuciyata ta gaji da tunanin abubuwan da suka faru a yau. A raina ina ɗan murmushi, saboda tunanin cewa gobe zan je gidan Kakata. Ban ma tabbata ko ta dawo daga tafiyarta ba, amma zuciyata na son na ganta.

A ɗayan ɓangaren gidan, a dakin Abba, Momy ta kalli Abba cikin azahne kamar wacce ke da wani ɓoyayyen labari.

“Abban Ramlah, wata magana na ji akan As’ad. Bansaniba ko kai kasani.”

Abba ya juyo da sauri, idonsa ya tsaya kanta cikin natsuwa da ɗan ɗaga murya

“Zainabu, ba za ki bar ni da maganar As’ad ba ko?”

Momy ta ɗan ɗaga hannunta cikin alamar rantsuwa, muryarta cike da bacin rai “Allah da gaske nake fa, Abban Ramlah. Dazu Faiza ce ta gaya min wai ba shi da lafiya. Kuma labarin nan kowa ya sani, ni kam sai nake gani kamar karyane.”

Abba ya yi shiru na daƙiƙu, sannan murmushi ya subuce masa murmushin wanda ya fi magana nauyi.

“To Allah ya ba shi lafiya. Amma Zainabu, me kike so ki ce da ni? Kin dai san ni bana son surutu da gulma ko.”

Momy ta yi shiru na ɗan lokaci, “Au, kai ma ba ka sani ba kenan, Abban Ramlah?

Abba ya ɗan kalli ƙasa na ɗan lokaci, sannan ya ɗago yana girgiza kai da natsuwa

“Zainabu, kin riga kin fiye tunani. Aure rabo ne, ba tilas bane. Ni dai nace ki kwanta kiyi bacci. Sai da safe, domin gobe ina da aiki tun da sassafe. Kuma banason sake jin wannan maganar nan da dare.”

Ya ɗan jinjina kai ya kwanta, yana rufe ido cikin nutsuwa. Momy ta tsaya tana kallonsa na ɗan lokaci, sannan ta yi shiru. Zuciyarta ba ta gamsu ba, amma bata ƙara cewa komai ba.

Dakin ya kama da shiru, sai ƙarar fitilar AC dake kaɗawa a hankali.

Nana hadiza

09030569336

[21/09, 7:54 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Zaune yake a katafaren sashen nasa, wanda ya sha kawatawa da kayan alfarma daga ko’ina cikin duniya. Persian carpet ya shimfiɗe ƙasa, fitilun crystal chandelier suna walƙiya daga sama, sai ƙamshin oud mai tsada da ya cika falon gaba ɗaya. Gaba ɗaya ransa a ɓace yake, saboda abubuwan da suka wakana cikin ‘yan kwanakin nan. Fuskar sa ta nuna gajiya da damuwa, sai idonsa da ya kasa ɓoye bacin rai.

Ya juyo ya kalli P.A dinsa, wanda ya tsaya a gefe cikin ladabi. Da murya mai nauyi ya ce “Ka shirya komai, gobe zan tafi Dubai. Ina buƙatar in bar nan.”

P.A ɗin ya sunkuyar da kai cikin biyayya, ya ce “To, ranka ya daɗe.” Daga nan ya juya ya fita domin tsara tafiyar.

Bayan mintuna kaɗan, Hajja ta shigo cikin sashen nasa. Kallo ɗaya ga shigarta zai tabbatar maka da cewa ita ba mace ce ta kowa ba mace ce mai tarin mutunci, dattijuwa daga gidan sarauta. Bayan sun gaisa cikin girmamawa, sai ta kalle shi da ido mai nuna damuwa. “As’ad, ya kamata ka tsawatar wa Ayshatu akan wannan yawon da take yi. Ina tunanin ya isa haka. Mace ce ita, kuma mace daga cikin gidan sarauta mai mutunci da kima. Wannan tafiye-tafiye nata suna iya zubar mana da daraja.”

Zuciyar As’ad ta sosu sosai. Ya ɗan jingina da kujerar Italian leather ɗin da yake zaune a kai, ya ɗan rufe idonsa na daƙiƙa kafin ya ce da murya mai sanyi amma cike da nauyi “Inshaa Allahu, Hajja. Zan tsawatar mata. Allah ya ƙara miki lafiya da kwanciyar rai.”

Hajja ta ɗan gyara zamanta, ta ce “To, hakan yayi. Amma ya batun rubutun nan? Kanasha kuwa?”

As’ad ya ɗan murmusa kaɗan, yana nuna girmamawa “Eh, ina sha. Allah ya saka da alheri.”

Hajja ta miƙe tsaye da natsuwa “To Allah ya ƙara maka lafiya. Bari na wuce, Mai Martaba yana jirana.”

As’ad ya rakata da ido har ta fita daga sashen nasa, zuciyarsa cike da nauyin tunani.

Bayan tafiya mai wahala da gajiya, Ayshatu ta dawo gida. Amma duk da gajiyar tafiyar, zuciyarta cike take da missing ɗin Alhaji Muqaddam wanda shi ne yake cike mata rai da shagwaɓa a lokacin tafiye-tafiye. Da murmushi ta nufi wardrobe ɗinta, ta ɗauki wata light riga mai ɗan bayyana ƙirar jikinta. Ta zare ta rolling, ta feshe jikinta da zafafan turaren da aka kawo mata daga France. Duk inda ta tsaya sai ƙamshi ya mamaye wajen.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull