Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 12
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 12: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 12. Cikin izza da salo, ta nufi bangaren As’ad, inda sararin falon ya…
4,495 words
Cikin izza da salo, ta nufi bangaren As’ad, inda sararin falon ya sha kawatuwa da fitilun crystal chandelier da kujerun alfarma na Italian design.
Ko da ta shiga, sai ta tarar da As’ad tsaye a gaban madubi, yana shiryawa cikin nutsuwa. Ta tsaya a bakin ƙofa da murmushi, ta ce cikin ladabi mai ɗauke da shagwaɓa
“Sannu da gida, ranka ya daɗe.”
Ta ƙaraso kusa da shi cikin fara’a, tana ƙoƙarin rungumesa daga baya.
Sai kawai As’ad ya juya da sauri, ya kifar mata da wani mari mai nauyi, da ya sa ta ja da baya tana rik’e kuncinta. Fuskar sa ta nuna tsananin fushi, idonsa ya ƙanƙance da tsawa.
“Me kika ɗauki aure ne, Ayshatu? Me kika ɗauki aure nace?!”
Muryarsa ta cika falon gaba ɗaya da ƙarfi da izza.
“Watan ki uku baki gida! Kullum sunan business trip! Wane irin aure ne wannan, Ayshatu? Kin ɗauka aure wasa ne?”
Ayshatu ta tsaya cak, idonta ya ciko da hawaye. Wani irin kunya da tsoro suka lullube ta. Turaren jikinta ya gauraye da sanyi da ɗumi na damuwa. Ta yi ƙoƙarin buɗe baki ta yi magana, amma harshenta ya tsaya cak saboda ƙarfin kalaman As’ad.
A falon nan mai yalwa, shiru ya kama na daƙiƙu sai numfashin fushi na As’ad da bugun zuciyar Ayshatu da take jin sa cikin kunnuwanta.
Ayshatu ta share hawayenta, zuciyarta ta kulle da masifa. Ta dube shi ido cikin ido, muryarta na rawa amma kalamanta na fitowa da ƙarfin hali
“To menene zan maka in na zauna? Hakkina kake bani ko me? Ko kuma kana da ƙarfin saduwa da mace ne? Ka duba lafiyarka da kyau, As’ad! Idan ba business dina na tafi na yi ba, so kake damuwata ta kashe ni? So kake in mutu a hannunka…”
Bata riga ta karasa ba, As’ad ya kifar mata wani lafiyayyen mari da ya girgiza falon gaba ɗaya. Ƙarar hannunsa a fuskarta ta ji ta fiye mata zafi fiye da kowanne kalma. Sai ta durƙushe ƙasa tana rik’e kuncinta, idanunta sun cicciko da hawaye masu zafi.
As’ad ya tsaya a gabanta, jijiyoyin kansa sun tashi, idonsa ya ƙanƙance da bacin rai. Fuskar sa ta cika da izza da masifa.
“How dare you?! Yau kece da bakin ki kike jifan As’ad da irin waɗannan kalmomin? Kin ce ni ba namiji bane? Kin ce ban iya ba?!”
Ya ƙaraso kusa da ita, muryarsa na karfi, hannunsa na rawar fushi.
“Eh, nace ni ba namiji bane? Ke kike furta hakan a gabana?”
Ayshatu ta fashe da kuka, cikin azaba da tsoro. Amma duk da haka, kalamanta sun fito daga bakin ta cikin rashin nutsuwa “Na jefa ka dasu As’ad! Indai kai ba shege bane, to kasakeni. Ka sakeni! Na gaji da zama da nakasashen namiji da ba shi da komai sai izza da sarauta! Ka sakeni nace! Ka sakeni!!”
Maganarta ta cika falon, hawaye na zuba a fuskarta, muryarta na karyewa da kunci. Sai ta rufe fuskarta da tafin hannunta, jikinta na rawa kamar wanda aka shake.
As’ad ya tsaya cak yana kallonta, zuciyarsa cike da wani irin abu da ba zai iya fassara ba fushi, kaskanci, da ciwon zuciya duk suka haɗu lokaci guda.
Ayshatu ta share hawayenta tana haki, zuciyarta na ƙonewa da masifa. Ta kalle shi da idanu masu cike da tsana, ta ce da ƙarfin murya:
“Ka sakeni nace maka! Ina da kyau, ina da kuɗi, ina da komai da mace zata ji da shi. To stay with you for what? Akwai maza jarumai, waƴanda za su iya bani farin ciki da rayuwa! Kai fa ba komai bane sai izza da sarauta marar amfani!”
As’ad ya yi shiru na daƙiƙu, ya kalle ta da idanu masu cike da dumi da ciwo, zuciyarsa tana tafasa. Sai ya daga hannunsa alamar tsayawa, muryarsa ta fito da sanyi amma cike da nauyi “It’s okay… it’s okay. Ki je. Na sake ki, Ayshatu. Thanks.”
Ya juyo ya juya mata baya, ya tsaya gaban tagar falonsa mai fadi, yana kallon sararin dare. Haske mai sanyi daga chandelier ya haska masa fuskarsa, wanda ya cika da wani irin zafi da shakku.
Ayshatu ta tsaya na ɗan lokaci tana kallonsa, tana jin kamar bata yi tsammanin zai faɗi wannan magana ba. Sai ta juya cikin izza ta nufi ƙofar fita.
Kafin ta kai ƙofar, sai ta tsaya cak, ta juyo da sauri tana dubansa da ido mai ɗauke da ƙiyayya da shaidar raini. Ta ce da ƙarfin murya, muryar da ta amsa cikin dakin alfarma
“Sai ka ji…!”
Maganar ta makale a bakinta saboda tsananin bacin rai, amma duk kalmarta ta ɗauki iska. Ta juya cikin hanzari ta fice, takalman ta suna dukan tiles ɗin falon, turarenta yana bin bayanta.
As’ad ya tsaya a gaban taga, bai juyo ba, amma idonsa ya cicciko da wani yanayi da ba kowa zai gane shi ba fushi, kaskanci, da ciwon zuciya duk sun haɗu lokaci guda.
Har Ayshatu ta fita daga falon cikin izza, sai kuma zuciyarta ta sake tafasa. Ta dawo da mugun hanzari, ta buɗe ƙofar da ƙarfi, tana ihu kamar wacce tayi hauka.
“Naji saki ɗaya? Saki ɗaya fa? That’s not enough! Ina so saki uku! Ta yadda babu wanda zai ƙara tilasta min zama da kai. Zan je wajen masu bani farin ciki, masu lafiya, ba ragwaye ba irin ka!”
Muryarta ta cika falon alfarma, tana rawar zuciya.
As’ad kuwa ya tsaya a bakin tagarsa, jikinsa har rawa yake saboda tsananin fushi. Muryarsa na fita da ƙyar, kamar wacce aka murƙushe a ƙirjinsa. Bai iya kallonta ba, amma kalmarsa ta fito da nauyi
“Kije… na sake ki. Saki uku.”
Shiru ya biyo bayan wannan kalma, shiru mai nauyi da ya cika falon.
Sai Ayshatu ta saki wani murmushi mai cike da raini da izza, ta daga kanta sama tana dariyar mugunta
“Better! Yanzu naji magana. Alhamdulillah! Allah ya raba ni da azzalumi, mugu, kuma mai zuciya marar imani.”
Bata ƙara cewa komai ba. Ta juya cikin izza, ta fice daga falon, turarenta na bin bayanta, takalmanta suna dukan tiles kamar karar ƙarshe na wargajewar aure.
As’ad ya tsaya a inda yake, bai motsa ba. Fuskar sa ta ƙunshi ciwon zuciya da wani irin rashin yarda. Jijiyoyin kansa sun fito, idonsa ya cicciko da wani abu mai kama da hawaye amma ya kasa zubewa.
Ya rufe idanunsa, zuciyarsa na tsalle-tsalle, yana jin nauyin kalmar da ya faɗa “Na sake ki saki uku…”
Nana hadiza
09030569336
[24/09, 4:25 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TALATIN DA DAYA
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, kamar an tsiyaye masa ruwan kankara. As’ad, wanda duniya ta san shi da ƙarfi, izza, da kwarjini, yau ne karo na farko da yake jin kansa tamkar mara kariya. A rayuwarsa ya rabu da mata da dama wasu saboda son kansu, wasu kuma saboda siyasar gidan sarauta. Amma wannan rabuwa daban take.
Ayshatu ce fa matar da ta taɓa kiran kanta da “farin cikinsa”, wacce ta sha maimaita cewa ita ce abokiyar rayuwarsa. Ita ce ta saba zama kusa da shi a kowane lokaci, ta rungume shi da magana mai sanyi a lokutan da zuciyarsa ta gaji da rayuwar duniya. Ita ce mace ɗaya da ya taɓa yarda ta san ɓangarorin rauni a cikin zuciyarsa.
Yanzu ita ce ta tsaya a gabansa ta watsar da shi da kalmomin da suka fi kowanne nauyi Wannan kalma ta fi kowanne mari da aka taba yi masa zafi.
Ya jingina da madubin alfarma da ke cikin falon nasa mai walwalaj. Fitilun chandelier suna walƙiya daga sama suna kyalli, turaren oud ya cika dakin da ƙamshi. Amma duk wannan alfarma ta zama kamar babu komai. Ya ɗaga kansa, zuciyarsa na cike da rudani. Bai san ta yaya ya kai ga wannan hali ba. Bai san ina ya fara kuskure ba. Abin da ya sani kawai shi ne cewa zuciyarsa ta karye a yau fiye da kowanne lokaci a rayuwarsa.
Hawaye suka cicciko masa a idanuwa. Ya manta rabon da ya ji zafin hawaye a fuskarsa tun ranar da haneefah ta tozartashi shekaru da dama da suka gabata. As’ad wanda duniya ta sani da ƙarfin hali, yau hawaye ne suka zubo daga idonsa.
Ya ja numfashi mai nauyi sosai, kamar wanda ke neman ya shaƙe da iska. Amma kafin ya iya daidaita kansa, sai wani irin zazzabi ya rufe shi gaba ɗaya. Jikinsa ya fara karkarwa, hannayensa na rawa, jikinsa na ɗumi tamkar an kunna masa wuta daga ciki.
A cikin dakin alfarma da aka saba jin muryarsa mai ƙarfi tana bayar da umarni, yau sai aka ji shiru mai nauyi. Sai ƙarar numfashinsa mai nauyi da dukan zuciyarsa da ke bugawa cikin azaba.
As’ad ya runtse idanuwansa, yana ƙoƙarin daurewa, amma zuciyarsa ta kasa ɗaukar nauyin kalmomin Ayshatu. Aure da soyayya sun wuce daga zuciyarsa, amma ciwon da ta bar masa ya fi kowanne rauni mai zurfi.
Bayan Ayshatu ta bar bangaren As’ad cikin izza da masifa, zuciyarta cike da naciya, ta nufi sashen Mai Martaba. A ƙofar falonsa masu tsaro suka tsaya daram, amma da ta nemi izini suka aika ciki, aka amince aka bar ta shiga.
Falonnan na Mai Martaba ya bambanta da kowane bangare na gidan sarauta katafaren wuri mai yalwa, bango an kawata da golden frames da hotunan tarihi, ƙasa shimfiɗe da Persian rug mai sheƙi, fitilun chandelier suna walƙiya sama tamkar taurari. Duk wanda ya shiga sai ya ji tsoron darajar wurin.
Ayshatu ta durƙusa a ƙasa cikin girmamawa, ta gaishe shi da muryar ladabi
“Ranka ya daɗe, Allah ya ƙara girma da daraja. Na zo ne da al’amari mai nauyi.”
Mai Martaba ya gyara zamansa cikin izza, ya dubeta da idanu masu nauyin sarauta “Mene ne, Ayshatu? Ki yi magana, muna sauraro.”
Ayshatu ta ɗaga kanta a hankali, idonta cike da ƙarya da naciya. “Ranka ya daɗe, daman na zo in sanar da kai cewa na rabu da As’ad. Na gaji da zama da shi. Ban ga farin ciki a hannunsa ba, balle natsuwa. Ban ga namiji a cikinsa ba. Don haka na ɗauki mataki na barinsa gaba ɗaya.”
Falonnan ya ɗan yi shiru. Mai Martaba ya lumshe idonsa, ya ɗaga kansa sama kamar mai yin tunani. Daga bisani ya ce da murya mai zurfi da ikon sarauta “Hakan yayi kyau. Aure dai rabo ne. Idan kin ga ba ya yi miki, babu laifi ki rabu. Ki nemi farin cikinki. Ni dai a matsayina na uba, ina goyon bayan shawarar ki. Allah yayi miki albarka.”
Kalmar tasa ta bugi zukatan dake wurin tamkar karar ganga.
Sai kawai Uwargidan Sarki ta miƙe tsaye da hanzari, masifa ta cika bakinta. Ta nuna Ayshatu da yatsa, tana kallonta da idanu masu cike da tsana “Butulu! Ashe ke ce kika samu daraja a gidan nan, kin zauna, amma baki iya godiya ba! Ke butuliyar da duniya bata taba gani ba. Aka baki sarauta, aka baki gata amma kika mayar da shi kamar babu komai. Muryarta ta cika falon, tana kakkarwa da fushi.
Ayshatu ta tsaya cikin izza, ta ɗaga kai tana murmushi mai raini, amma bata ce uffan ba.saboda tafi kowa sanin uwargida ta tsani As'ad amma ganin tasamu daukaka yasanya ta manta hakan.
Hajja kuwa, wacce ke zaune a gefe cikin tsantsar nutsuwa, ta kasa cewa komai. Ta rufe bakinta da hijabi, zuciyarta tana cike da damuwa, amma bata iya cewa komai ba saboda tana ganin ayshatu tanada babbam dalilinta tanada kuma gaskiya tunda har As'ad yanada rauni to tabbas rabuwar tafi alkhairi abaya da haneefah tayi haka taji haushi sosai ayanzu kuwa bayajin haushi tana ganin hakan a matsayin adalci.
Shiru mai nauyi ya sake mamaye falon. Mai Martaba ya ɗaga hannunsa alamar kowa ya zauna, yana duban Ayshatu cikin tsantsar girma
“Ki tafi, Ayshatu. Allah yabaki wanda yafi As'ad. Allah ya bashi lafiya shi kuma.”
Uwargidan Sarki ta kasa zama, “Amma Mai Martaba, hakan da kayi bai kyautu ba. Wannan magana da ka goyi bayan Ayshatu kamar ka wulakanta darajar gidan nan ne. Ashe haka za a bar ta ta yi mana rashin kunya?”
Dakin ya ɗan yi shiru kafin Hajja ta ɗago kai cikin nutsuwa. Ta kalli Uwargida da idanu masu cike da tausayi, ta ce da murya mai taushi “Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Shekaru kusan ashirin da biyar da miji, sai yanzu ta rabu da shi. Ai dole ce taja. As’ad fa ba shi da lafiya sosai. Shi ne dalilin da yasa ta yi masa hakan kuma hakan shine adalci ai”
“Hajja, halarci fa kika ce? Wannan yarinyar nan kaskantacciya ce! Yar baiwa ce da aka ɗauka tana mana aiki, aka ɗora mata mutum, aka canza mata rayuwa. Dubeta yanzu, shine take ta yi mana rashin kunya gaban kowa!”
Muryarta ta cika falon sarauta da masifa, tana rawar jiki saboda fushi. Ayshatu kuwa ta tsaya a gefe cikin izza, ba tare da ta nuna kunya ko nadama ba.
Cikin wannan hayaniya, sai Mai Martaba ya ɗan gyara murya, muryarsa mai nauyin iko ta ratsa falon gaba ɗaya.
“Ya isa. Kowa ya tafi. Wannan maganar ta tsaya a nan. Babu wanda zai ƙara tanka mata.”
Shiru ya biyo bayan kalmarsa. Uwargida ta yi tsaki tana jingina da kujerarta, amma ba ta ƙara magana ba. Hajja ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta na addu’a.
Mai Martaba ya ɗago da hannu alamar an rufe zaman, sannan ya rufe idanunsa cikin natsuwar sarauta.
Da Ayshatu ta fito daga sashen Mai Martaba, murmushi mai ɗauke da izza ya bayyana a fuskarta. Tana tafiya tana dariya a hankali, kamar wacce ta ci nasara a wata gasar. Kai tsaye ta nufi harabar gidan, inda hadaddiyar motarta mai ƙyalli ta tsaya a shirye. Direbanta ya buɗe mata ƙofa cikin girmamawa.
Ta shiga motar cikin izza, turarenta mai tsada ya gauraye iska. “Na gama da As’ad. Na rabu da shi gaba ɗaya. Ni ba sai na dogara da dukiyar sa ba. Ina da gidaje, ina da kuɗi, ina da komai a wurare daban-daban. Zan bar wannan ƙasar yau, banajin zan sake juyawa baya.”
Motarta ta ja da sauri ta bar gidan gaba ɗaya, tana barin hayaniya a bayanta.
A cikin gidan, Firdausi kanwar As’ad ta saki dariya cikin raini, tana kallon Hajja da ɗan tsokana “To Hajja, yanzu saboda Ayshatu ta rabu da Yaya, kike nuna takaici? Ai wannan kazamar matar mai cin amanar aure . Ke kika damu da ita? Kina ji ko? Ai abokin Yaya take soyayya da shi tun kwanaki. Ke kike tausayinta.”
Hajja ta ɗago kai a hankali ta kalle ta da idanu masu nuna natsuwa da izza. Murya mai sanyi amma cike da iko ta fito daga bakinta “Firdausi, wannan shi ne karo na ƙarshe da zan ji kin furta irin wannan magana. Kar ki sake kiyi irin wannan kalaman a gabana. Ki tashi yanzu, ki sanar da shi inason ganin As’ad yanzu.”
Firdausi ta yi shiru, ta zumburo baki kamar yarinya, amma bata iya cewa uffan ba. Ta miƙe, ta fice da sauri.
Kafin dare ya rufe wani azababben zazzabi ya kama As’ad. Duk girman jikinsa da ƙarfin da aka saba gani a tare da shi, yau sai jikinsa ya soma rawa kamar ƙaramin yaro. Gabansa ya dinga ɗaukar nauyi, gumi mai zafi yana keto masa daga goshi.
Da ƙyar ya iya tsayawa ya yi sallar isha’i. A kowanne sujuda, kalmomin addu’a suna fita daga bakinsa cikin rauni, kamar zuciyarsa tana neman ta fashe da hawaye. Dukiyar sa, izzar sa, da sarautar sa babu ɗaya daga ciki da ta iya tsare shi daga wannan ciwo.
Bayan ya idar da sallar, ya kwanta a kan kujerar Italian leather a cikin katafaren ɗakinsa, wanda aka kawata da fitilun chandelier masu kyalli da Persian rug mai launin ash. Sai dai alfarma ta koma kamar ba ta da wani amfani, saboda radadin da zuciyarsa take ciki.
Ya jingina kansa, hannunsa na karkarwa, yana maimaita addu’a da muryar da take fita da ƙyar “Ya Allah, ka bani ƙarfin zuciya… kada ka bar ni cikin rauni.”
A hankali aka buɗe ƙofar ɗakin. Hajja ta shigo cikin nutsuwa, hijabinta ya lullube ta gaba ɗaya. Ta tsaya na daƙiƙa tana kallonsa da idanu masu nuna tausayin da zuciyarta ba ta iya ɓoyewa ba.
Sai ta ƙarasa kusa da shi, ta zauna a gefen gadon da ya jingina, ta ce da murya mai taushi amma mai nauyi “Nasan za’ayi haka, As’ad. Nasani tun farko. Ka ga, yau gashi abin da nake tsoro ya faru kayi hakuri nasanka da jarumta nasanka da kokari inshaa Allah Allah zai baka maccen da zata zama sanyin idanuwarka wacce zata kaunace ka fiye da ayshatu.”
As’ad ya ɗan juyo da kallo gare ta, idonsa ya cicciko da hawaye. Amma bai iya magana sosai ba. Sai wasu ’yan surutai marasa ma’ana suka fito daga bakinsa cikin rashin ƙarfi, tamkar mai maganganu da ba a gane gaba ko baya.
Hajja ta ɗan sauke numfashi, zuciyarta ta karye da ganin yadda namijin da duniya ke ɗauka da izza da daraja, yau ya kwanta kamar mara taimako. Ta daga hannunta sama cikin addu’a, tana cewa a ranta “Ya Allah, Ka kawo masa sauƙi.
Nana hadiza
09030569336
[25/09, 6:57 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TALATIN DA BIYU
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Kwana biyun nan muka shiga shirin babban taron da za a yi a makaranta, inda ni ce ke tsara click ɗinmu. Tun daga ƙarfe 9 na safe na isa makaranta, saboda yau abubuwa da yawa ne a gabana.
Da na fito daga gida, sai na ji Momy tana ta habaici iri-iri, tana zubar da maganganu marasa daɗi. Ban damu ba, kawai na bar ta. Ban san ko wane ne take son a haɗa da Yaya Billy ba, amma na tabbata tana da wani nufi a zuciyarta. Da safe ma Abba ya yi mata masifa sosai, har kuka ya taso mata saboda wasu kalaman da suka fito daga bakinsa masu nauyi.
A makaranta kuwa, Maryam da Halifa suka same ni. Sun zauna kusa da ni suna magana kan presentation ɗin da zan gabatar. Lokaci ya yi gaba sosai, saboda karfe uku na rana za a fara taron, kuma an gayyato manyan baki daga ciki har da Gwamna, Sarki, da kuma wasu fitattun masu kuɗi.
Na shiga duba takarduna da aka rubuta min, ina ta gyara a hankali. Gajiya ta lullube ni, zuciyata na cike da tsoro. Na ɗaga kai na dubi Maryam nace “Wallahi Maryam, na gaji. Kuma ina jin tsoro, kada naje na yi wani abu da ba daidai ba a gaban mutane.”
Halifa ya saki dariya yana kallona da nishadi “Haba Ramlah! Kin fiye tsoro fa. Kin san zaki iya sosai. Kidaina damuwa, da ke da Umar ai kowa ya san kunada kwarin gwiwa da himma.”
Na yi murmushi ina kallonsa cikin taushi. Na ce “To shikenan, babu damuwa. Zan ƙara daurewa.”
*****
A babban palon gidan As’ad wanda yakasance ginin dayafi kowanne tsada da kyau acikin gidan sarautar, Mai Martaba tsaye cikin natsuwa, ya dubi As’ad. Gaba ɗaya As’ad ya rame, ya fita hayyacinsa. Kowa ya sani, shi ya fi son Ayshatu fiye da duk wani abu mace mai biyayya ce, mai hankali, wacce ta saba kula da shi a kowane hali. Amma rabuwa ta zo masa tamkar dole, hakan ya jefa shi cikin damuwa da ciwon zuciya.
Mai Martaba ya yi gyaran murya kafin ya ce da shi cikin hikima
“Barka da karasowa. Ai da ka aiko, da na zo. Ranka yadade."
Mai martaba ne yayi murmushi yace " Babu laifi idan nazo naga lafiyarka kwanki sunja kana kwance guri daya hakan kuma baya mun dadi ko ƙadan baya sanyani cikin farinciki Amma yanzu bari in gaya maka wani abu. Ya kamata ka bar komai ya huce. Kada ka bar wannan lamari ya dauke maka hankali daga abin da ya fi muhimmanci. Business dinka, harkokinka duk suna jiran ka. Ka tuna, kai ba yaro bane. Rayuwa jarabawa ce, kuma ba ta karewa sai mutum ya mutu. Wani lokaci daga wanda kake so, sai ka ga ya zama maka makiyi. Don haka ka ajiye batun Ayshatu gefe, ka fuskanci gaba. Kowace yarinya kake so, ko ta wace gida ce, zaka iya samu. Ina fata ka fahimta.”
As’ad ya ɗago kansa, idonsa cike da gajiya, amma zuciyarsa na jin taushin maganganun Sarki. Ya ce cikin ladabi “Na gode sosai, Ranka ya daɗe. Allah ya ƙara maka hikima.”
Mai Martaba ya yi murmushi kaɗan, ya ce “Zaka iya shiryawa yanzu? Cikin mintuna 20 muna da babban taro a jami’a ta wajen gari. Ina so ka halarta.”
As’ad ya miƙe cikin natsuwa, ya gyara rigarsa.
“Angama, Ranka ya daɗe. In shaa Allahu, zan fito yanzu.”
Mai Martaba ya ƙara yin murmushi, sannan ya juya ya fita cikin izzar sarauta. As’ad ya tsaya na ɗan lokaci yana tunanin kalamansa, zuciyarsa na kara samun ɗan nutsuwa.
Bayan fitan Mai Martaba daga falon, As’ad ya tsaya na ɗan lokaci cikin tunani. Kalmomin Sarki sun shiga zuciyarsa sosai “Rayuwa jarabawa ce, ka ajiye batun Ayshatu gefe ka fuskanci gaba.” Wannan magana ta yi masa nauyi, amma kuma ta yi masa amfani.
Ya miƙe tsaye, ya nufi sashen nasa na ciki. A nan P.A dinsa ya riga ya shirya masa kayan sawa farin babban kaya da aka ɗinka da zare, an haɗa da wando da takalman fata na alfarma. Ya zauna aka shirya masa turaren oud da aka kawo daga Dubai, wanda yake da ƙamshi mai tsawo, sannan aka sa masa agogo na Rolex a hannunsa.
Duk da zazzabin da jikinsa ke yi, sai ya yi ƙoƙarin daurewa. Ya duba kansa a madubi, ya ɗan yi murmushi mara daɗi. “As’ad, dole ka dawo da kanka. Rayuwa tana ci gaba, kai ma dole ka ci gaba.”
P.A dinsa ya shigo da hanzari “Ranka ya daɗe, motocin sun shirya. Mai Martaba ya yayi gaba, za a raka ka da convoy.”
As’ad ya ɗaga kai a hankali, ya ce “Toh, mu tafi.”
Tun kafin ƙarfe uku, harabar jami’a ta cika da jama’a. Dalibai suna ta faman jere a gefe, wasu suna ɗaukar hoto da waya, wasu kuma suna ta faɗin magana cikin farin ciki da tsoro. An kawata babban auditorium da banner da rubutun taro, ana ta rera waƙoƙin makaranta da kiɗan band.
Sai ga motocin manyan baki suka shigo a jerin convoy. A gaba akwai motocin jami’an tsaro da siren, sai motocin sarauta da gwamnati suka biyo baya. Nan take jama’a suka fara tafa hannu da sowa:
“Sannu da zuwa! Sannu da zuwa!”
Motar Mai Martaba ce ta fara tsayawa. Da aka buɗe ƙofa, sai dogarawa suka buɗe masa hanya. Ya fito cikin babban riga da rawani, ya ɗaga hannu alamar gaisuwa. Dukan daliban suka yi tsaye suna yi masa “long live Mai Martaba!”
Bayan shi kuma sai aka buɗe ƙofar wata Maybach mai ƙyalli, daga ciki As’ad ya fito. Duk da ya rame, dogayen kaya fari da yake jikin sa sun ƙara haskaka fuskarsa dalibai da lecturer kowa yakafeshi da idanuwansu wasu dalibai ma sunata gulmar dama zai zama nasu.”
Babban Auditorium na jami’ar ya cika da ɗalibai tun kafin ƙarfe uku. A ƙofar shiga, dalibai masu ɗaukar hoto da bidiyo suna ta zagaye, suna ɗaukar dukkan abin da ke faruwa domin tarihin wannan rana. Fitilu masu kyalli suna haskawa sama, banner mai rubutun “Taron Bunkasa Matasa da Cigaban Al’umma” ya rataye a bango, ya kawata dakin sosai.
A gaba, an shirya kujerun baki na musamman wurin da aka kira VIP section. An jera kujeru masu kyau, shimfiɗe da farin table cloth, a gabansu akwai kwalayen ruwa, lemo da kayan ciye-ciye na musamman. An ware wajen ga Mai Martaba, Gwamna, da manyan baki irin su As’ad da sauran fitattun masu kudi.
Dalibai sun zauna cikin tsari, kowanne yana kallo da sa ran ganin yadda komai zai kaya. Zuciyoyinsu cike da farin ciki amma kuma da ɗan tsoro saboda girman taron. Malamai suna ta zagayawa suna tabbatar da komai yana tafiya da tsari.
Sai aka fara da addu’a daga malamin addini. Ya daga hannu sama, dakin ya yi shiru gaba ɗaya, aka rufe idanu aka yi addu’ar neman albarka ga duk wanda ya halarta.
Bayan haka, aka rera waƙar jami’a. Dalibai suka mike tsaye, suka yi waƙar da farin ciki, muryoyinsu suka gauraye da kiɗan band da ke busa a gefe. Dakin ya ɗauka da kida da farin ciki, kowa na jin kamar yana cikin tarihi.
Daga nan sai Shugaban Jami’a ya mike. Ya gabatar da jawabi cikin natsuwa, yana yiwa baki maraba, yana godewa gwamnati da masu kudi da suka goyi bayan makaranta. Dalibai suka yi masa tafi bayan ya gama, sannan aka kira Gwamna ya gabatar da jawabin nasa.
Gwamnan ya tsaya a podium cikin izza, ya yi jawabi kan rawar matasa wajen gina al’umma. Kalaman nasa suka motsa zukata, har dalibai suka fara tafa hannu da shewa cikin farin ciki.
Bayan shi, sai Mai Martaba aka kira. Da ya mike, jama’a suka tashi tsaye da girmamawa. Ya yi magana kan muhimmancin tarbiyya da rikon amana, yana jan hankalin matasa da su rike gaskiya da ilimi a duk inda suka tsinci kansu. Duk kalmarsa tana shiga zukatan jama’a kai tsaye.
Sai aka iso babban ɓangaren da kowa ke jira presentation daga dalibai. Sunan Ramlah da click ɗinta ya fito a kan projector screen. An kira sunanta da ƙarfi, dalibai suka yi mata tafi da shewa.
Numfashinta ya ɗauke, zuciyarta na bugawa. Ta miƙe tsaye cikin nutsuwa, tana kallon gaban inda Mai Martaba, Gwamna, As’ad, da sauran manyan baki suke zaune suna kallonta kai tsaye.
Dakin ya yi shiru, kowa na jiran jin kalamanta.
Ramlah ta tsaya a gaban podium ɗin, hannunta na ɗan karkarwa saboda tsoro. Idanunta suna kan takardarta, amma zuciyarta tana bugawa da ƙarfi. Dakin ya yi shiru, kowa yana jiran jin muryarta.
Amma a gefe guda na VIP section, akwai wani kallo guda ɗaya da ya fi karfin kalmomi kallon As’ad.
Tun lokacin da sunanta ya fito a kan projector, zuciyarsa ta buga tamkar ana dokawa da ganga. Yanzu da ta tsaya a gaban su, ya kasa ɗauke idonsa daga kanta.
Ya ga yadda hasken fitila ya sauka a fuskarta, yana bayyana kyawunta mai tsabta da ba a yi musu da shi ba. Ya lura da yadda ta ke ƙoƙarin boye tsoro, amma duk da haka ta tsaya da wani irin ƙarfi da kwarin gwiwa da ba kasafai ake gani a dalibai mata ba.
Idanunsa sun ƙanƙance, zuciyarsa ta fara faɗi masa kalmomi Yana kallonta tamkar shi kaɗai ne a cikin dakin, har muryar Gwamna da Mai Martaba a gefe sun fara ɓacewa daga kunnensa. Abin da zuciyarsa ta tsunduma ciki shi ne yadda bakinta ya motsa, yadda idonta ke kallo da ladabi, yadda jikin ta ke nuna natsuwa da daraja.