Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 13

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 13

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 13: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 13. Zuciyarsa ta fara ɗan bugawa, yana jin wani abu da bai taɓa ji ba…

4,370 words

Zuciyarsa ta fara ɗan bugawa, yana jin wani abu da bai taɓa ji ba tun rabuwarsa da Ayshatu. Wannan karon ba soyayya ce kawai ba akwai wani irin kasaita da sha’awa da ta haɗu lokaci guda, suna sa shi jin kamar duniya ta tsaya cak.

A hankali ya jingina da kujerarsa, hannunsa ya riƙe carbi da yake yawan murzawa idan yana cikin damuwa. Amma yanzu, ba damuwa ya ji ba wani irin nishaɗi da sanyi da bai san daga ina ya fito ba.

Idonsa bai daina binta ba, yana zagaye da ita gaba ɗaya.

Nana hadiza

09030569336

[26/09, 9:04 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN DA UKU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Dakin ya yi shiru, fitilun spotlight suka sauka a kan Ramlah da ke tsaye a bakin podium. Numfashinta ya yi nauyi a farko, amma sai ta rufe idonta na daƙiƙu biyu, ta ɗan murmusa cikin natsuwa. Lokacin da ta buɗe idonta, ta dubi gaban idanunta suka hango fuskar Mai Martaba, Gwamna, manyan malamai, masu kudi, da kuma… As’ad.

Idanunta sun yi karo da nasa na ɗan lokaci. Wani irin sanyi ya ratsa ta, amma ta ɗauke idonta da sauri ta maida su kan takardunta. Ta yi numfashi mai zurfi, sannan ta fara magana da muryarta mai cike da ƙarfi da kwarjini

“Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. Ina yi muku barka da wannan rana mai albarka, musamman ga Mai Martaba, Mai Girma Gwamna, malamai, dalibai da dukkan baƙi masu daraja da suka halarta. Ni ce Ramlah, ɗalibar wannan jami’a, kuma yau na zo domin gabatar da magana kan taken taronmu ‘Bunkasa Matasa, Ginin Cigaban Al’umma.’”

A dakin aka yi shiru sosai. Muryarta tana fita da daɗi, ba tare da rawa ko tsoro mai yawa ba. “Matasa sune ginshiƙin kowacce al’umma. Idan muka samu matasa nagari, ƙasa zata tashi, al’umma zata bunƙasa. Idan muka rasa su, to muna rasa gaba ɗaya makomar al’umma. Saboda haka, akwai nauyi a kowane matashi da kowane dalibi, ya gane cewa ba wai kawai ya tashi ya yi rayuwa ba ya kamata ya yi rayuwar da zata yi tasiri ga ƙasarsa.”

Ta ɗan ɗaga hannunta alamar nuni da ƙarfi

“Ilmi shi ne makamin farko. Amma ilmi shi kaɗai ba zai wadatar ba. Akwai buƙatar haɗa shi da tarbiyya, da gaskiya, da amana. Akwai buƙatar mu tashi da himma mu kasance matasa masu hangen nesa ba matasa masu bin iska da sha’awa kawai ba.”

Jama’a suka fara jinjina da kai. Malamai suna ta ƙwafa alamar yarda da kalamanta.

A gefe kuwa, As’ad ya jingina da kujerarsa cikin VIP section, amma duk jikinsa ya fara motsawa ba tare da gangan ba. Idonsa bai daina kallonta ba.

Ya lura da yadda ta tsaya da confidence fiye da yadda ya zata. Ta fara da girmama manya, ta zuba kalmomi masu hikima. Yadda ta ɗaga hannunta tana magana, yadda idanunta suke haske da natsuwa duk ya kama zuciyarsa fiye da yadda zai iya buya.

Ya ji zuciyarsa tana tsalle tamkar ana dukan ganga a ƙirjinsa. Ya ce a zuciyarsa “Wannan ba kawai presentation ba ce. Wannan magana ce da ta fito daga zuciyar mace mai daraja.”

“Mai Martaba, Mai Girma Gwamna, da dukkan masu daraja. Idan muna so mu gina al’umma, sai mun fara da kanmu. Mu matasa, mu daina tunanin cewa komai gwamnati zata yi mana. Mu ne gwamnati ta gobe. Mu ne shugabanni, mu ne malamai, mu ne masu kuɗi na gaba. Idan muka tashi da gaskiya, zamu bar tarihi mai kyau. Idan muka tashi da rashin gaskiya, zamu bar tarihi mai duhu.”

Muryarta ta ɗan yi nauyi, tana jan hankalin kowa “Ina roƙon kowane ɗalibi a nan ku bar daurewa da ƙaramin buri. Ku yi mafarki mai girma, amma ku haɗa shi da aiki tukuru. Ku guji sata, ku guji cin amana, ku guji bin hanya mai sauƙi wacce zata lalata rayuwarku. Domin ƙasar nan tana da albarka, kuma albarkar nan ta rataya ne a wuyanmu matasa.”

Sai ta ɗan yi murmushi kaɗan, ta ce “Na gode da wannan dama, kuma ina fatan kalamaina zasu taɓa zuciyar duk wanda ya saurare ni.”

Da ta sauka daga podium, aka yi mata tafi sosai. Dalibai suka yi ihu da farin ciki, wasu ma suna kiran sunanta. Amma a zuciyar As’ad, abin da ya ji ya fi kowanne tafi da ihu.

Ya ji kamar zuciyarsa ta rushe gaba ɗaya. Wani abu mai nauyi ya tsaya masa a ƙirji. Idonsa ya rufe na daƙiƙu, yana jin muryarta tana maimaituwa a cikin kunnensa.

“Mu matasa… mu gina al’umma… ku guji bin hanyar sauƙi…”

Sai ya ɗan lumshe ido, ya riƙe hannunsa daidai ƙirji, zuciyarsa tana ta bugawa da ƙarfi. Idonsa bai daina bin ta da kallo ba, har ta koma kujerarta. Zuciyarsa ta riga ta rikice gaba ɗaya.

Taron ya kusa zuwa ƙarshe. An yi jawabin Gwamna, Mai Martaba ya yi kalmomin hikima, sannan aka kira babban ɗan kasuwa As’ad Kabir domin ya yi nasa jawabin.

Dakin ya yi tsit. Dalibai suka zuba idanu, malamai suka lumshe ido suna jiran jin kalaman sa. Duk da cewa an saba jin shi a wuraren taro, yau akwai wani sabon yanayi a jikinsa zuciyarsa tana ta bugawa saboda fuskar da yake gani a cikin ɗalibai.

Ya tashi tsaye cikin dogon farin babban kaya da aka ɗinka da zare agogon Rolex yana kyalli a hannunsa. Ya ɗauki microphone a hankali, ya ɗan murmusa kadan sannan ya fara “Assalamu Alaikum warahmatullah. Na fara da godiya ga Mai Martaba, Mai Girma Gwamna, da dukkan malamai da ɗalibai. Na kasance a wurare da dama, amma wannan taro ya daɗa bani kwarin gwiwa saboda abin da na gani a yau matasa masu ilimi da hangen nesa.”

Sai ya ɗan tsaya, ya kalli dalibai gaba ɗaya. Amma a zuciyarsa, idonsa yana neman fuska ɗaya Ramlah. Da ya hango tana zaune da takardunta a gefe, zuciyarsa ta sake yin tsalle, amma ya ɓoye wannan da murmushi.

Ya ci gaba: “Ni As’ad na tashi daga cikin al’umma kamar kowa. Ban samu dukiya a sauƙaƙe ba. Na san darajar ilimi, kuma na san wahalar neman rayuwa. Saboda haka, duk inda na samu damar taimakawa ilimi, sai na yi shi da zuciya ɗaya.”

Ya ɗan lumshe ido, sannan ya ce cikin murya mai nauyi “Ina bada gudummawar gina cibiyar kimiyya da fasaha (ICT Centre) a wannan jami’a, domin ɗalibai su koyi zamani da yadda duniya take tafiya. Ina kuma bayar da motocin bas guda uku domin sauƙaƙa musu zirga-zirga daga gida zuwa jami’a.”

Dakin ya fashe da tafi da ihu. Dalibai suka tashi tsaye suna yi masa “thank you! thank you!”, wasu suna yi masa kirari. Malamai suka yi dariya suna tafa hannu, Gwamna ya ɗaga kai cikin jin daɗi, Mai Martaba kuma ya ce da ƙarfi “Allah ya saka da alkhairi, As’ad!”

Sai As’ad ya ƙara cewa “Amma gudummawa mafi girma da zan iya bayarwa, ita ce shawara. Ina so ku daina tsoron ku. Ku tsaya da gaskiya kamar yadda na gani a hannun ɗaliba guda a yau wacce ta nuna cewa ilimi da tarbiyya idan suka haɗu, suna haifar da tasiri mai girma.”

Yana magana haka, ya kalli Ramlah kai tsaye. Idonsa ya tsaya a kanta tamkar babu wani a cikin dakin. Zuciyarta ta buga sosai, hannunta ya yi sanyi. Ta sunkuyar da kai cikin kunya, amma zuciyarta tana tsalle.

Ya ƙarasa da cewa “Ina fatan za mu samu dalibai da yawa kamar haka, wadanda za su zama gado ga ƙasa. Na gode.”

An sake fashewa da tafi. Dalibai suna kiran sunansa, malamai suna jinjina da kai. Amma a zuciyarsa, bai ji komai ba sai sunanta Ramlah.

*****

Na dawo gida da jiki a gajiye, zuciyata cike da rudani. Yau fa na yi abin da ban taɓa yi ba tsayawa gaban manyan baki, ina magana, kowa yana kallona. Amma duk da haka, zuciyata ba ta yi sanyi ba. Na ji dalibai da yawa suna jin haushina saboda ganin ni kaɗai aka baiwa damar yin jawabi. Wasu ma suna kallona da idon hassada.

Sai kuma malam Fahad… tun daga makaranta yake turomin text ɗin masifa

“Ke Ramlah, kina ta murmushi a gaban masu kuɗi kina neman suji da ke ko? Na gaya miki ki kiyaye, ni ba zan lamunta ba. Idan wani acikinsu ya nuna yana kaunarki fa?!”

Na ji haushinsa sosai. Ban taɓa son irin wannan sarƙaƙiyar kulawa ba, sai kawai na kashe wayata.

Na shiga mota na nufi gida cikin natsuwa, amma zuciyata cike da gajiya. Da na isa bakin gate, sai na yi horn, masu gadi suka buɗe min. Na karasa cikin gidan na ajiye motata, ina jin yunwa sosai.

Da na shiga falo, na yi sallama, na ce “Sannu da gida Momy. Don Allah, akwai abinci? Yunwa nake ji sosai.”

Sai na ji Momy ta kalle ni da wani irin kallo, ta ce cikin wata murya mai cike da zafi “Uwarki tasanya, ni na dafa miki abinci? Shigiyar yarinya mara mutunci! Kin zo kin hana ni zaman lafiya da mijina, mara kirki kawai. Dallah ki huce ki bani guri.”

Na tsaya cak, zuciyata ta buga. haka kawai saboda na tambayi abinci? Sai hawaye suka cika idona, amma na ce cikin muryar da ta karye “Momy… me nayi miki? Me yasa kike zagi na haka? Na tambayi abinci ne kawai fa.”

Sai Momy ta mike da hanzari, ta fara tafka masifa tana huci “Dukana zakiyi ne? Shigiyar yarinya mara tarbiyya! Ai yau sai na nuna miki wacece ni.”

Na ja da baya, na girgiza kai cikin kuka “Ni zan dake ki Momy? Ni fa kawaii tambaya nayi. Kinsan yunwa nake ji.”

Amma sai ta fara masifa “Mara mutunci! Kin haifeni ne? Ko ni ƴar aikin ki ce?. Naga mijin da zai kwasheki ai munafuka Zuciyata ta fashe da radadi. Ban san abin da nayi mata ba da har kalmomin da suka fi wuƙa soka take jefomin a kai.

Na juya na nufi dakina da kuka..

*****

Daren ya yi nisa. Gidan ya lulluɓe da shiru, amma zuciyar As’ad ba ta samun nutsuwa. Ya tsaya a bakin taga yana kallon taurari, hannunsa riƙe da gilashin ruwa amma bai sha ba. Zuciyarsa tana tafasa tamkar ana hura wuta a cikinta.

“Ramlah…”

Sunanta kawai ke yawo a kwakwalwarsa. Yadda ta tsaya gaban dakin taro, dukkan haske ya sauka kanta, tamkar duniya ta tsaya cak saboda ita. Yadda ta yi magana da hikima kalmomi masu sauƙi amma masu nauyin gaske, sun faɗi kai tsaye cikin zuciyarsa.

Ya rufe idonsa ya tuna lokacin da suka haɗa ido. Idon nan nata mai sanyi amma mai ƙarfi ya tsinke shi har cikin zuciya. Bai taɓa jin irin wannan ba tun rabuwarsa da Ayshatu.

“Ayshatu ta bar ni… na rantse ban ƙara son mace. Amma yau, me yasa wannan yarinyar ta karya alkawarin da na ɗaura a zuciyata? Me yasa kallo guda ɗaya daga gareta ya fi duk kalmomin soyayya da na taɓa ji?”

Ya ja numfashi mai nauyi, zuciyarsa ta yi masa zafi.

“Wata yarinya ce, ɗaliba, mai tarbiyya, mai natsuwa. Amma akwai wani abu fiye da haka a cikinta. Abin da na gani a cikin idanunta shi ne gaskiya wacce ban taɓa gani ba kwanan nan. Wani haske ne, wani tsarki ne da ya shige ni.”

Ya jingina da bango, zuciyarsa tana tsalle.

“Idan ina tare da Ayshatu, na saba jin izza da lalata. Amma idan ina tunanin Ramlah… ina jin nutsuwa. Ina jin wani abu mai tsarki, mai kyau, wanda ya fi ƙarfin ni. Wataƙila wannan shi ne abin da ake kira da soyayyar gaskiya? Amma As’ad… kai ba yaro bane. Ka tabbata zaka iya jurewa hakan?”

Ya ƙara lumshe ido, sai ya ji kalamanta suna dawo masa “Matasa su ne ginshiƙin al’umma… Ku bar daurewa da ƙaramin buri… Ku yi mafarki mai girma…”

Ya murmusa da wani irin radadi, hawaye suka taru a idonsa.

“Ke yarinya ce mai hankali. Kin fado zuciyata ba tare da izini ba. Kuma duk da nake so in gudu daga hakan, zuciyata ta ce min: As’ad, wannan karon ka tsaya. Wannan karon, ka saurari zuciyarka.”

Sai ya juya daga taga, ya nufi gadonsa. Ya kwanta….

Nana hadiza

09030569336

[27/09, 8:45 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN DA HUDU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Ofishin Abba katafaren wuri ne mai ɗauke da alfarma. An kawata bangon da hotunan manyan sarakuna da dattawan gida. A gefe kuwa akwai shelves ɗin littattafai masu daraja, waɗanda suka cika da littafai. Ofishin yana cike da kamshi mai daɗi daga turaren itace da aka saka a cikin burner. Fitilar chandelier ta rataye a tsakiyar ofishin, tana haskawa da wani irin sanyi wanda ke bada kamshin dadi.

A kujera Abba ya zauna, cikin farin shadda da hula ruwan madara. A gabansa tebur mai kyau ne da aka jera kwalayen ruwa, kayan rubutu, da laptop nasa. Yana duba wasu takardu ne, fuskar sa cike da nutsuwa da kwarjini, lokacin da aka sanar masa da zuwan Hamza.

“Barka da warhaka Baba Malam, nadanyi busy ne jiya naso nashigo bansamu dama ba sai yau,” in ji Hamza da sallama, yana shiga cikin ofishin.

Abba ya ɗan gyara zamansa, ya ɗaga kai yana murmushi. “Sannu da zuwa Hamza. Yaya ofishin? Yaya mutanen gidan?”

Hamza ya gyara zamansa a kujerar da aka tanadar masa. Wani nutsattsen murmushi ya bayyana a fuskarsa. “Alhamdulillah, duk suna lafiya Abba.”

“Magana nake son yi maka akan ‘yarka.”

Uncle hamzq ya ɗan daga gira cikin mamaki.

“Ɗiyata? Wacce kenan, Hamza?”

Abba ya ce a hankal “Ramlatu ce.”

Zuciyar hamza ta ɗan buga, amma bai nuna ba. Ya yi tambaya cikin nutsuwa “To, lafiya dai ko? Menene ya faru?”

Abba ya yi murmushi mai sanyi, ya gyara zaman rigarsa sannan ya ce “To , magana ce mai girma. Jiya mun yi zama tare da Mai Martaba. A cikin tattaunawar mu, sai ya kawo maganar cewa yana sha’awar samun ɗiyarka a gidan sa. Na tambaye shi, wacce daga ciki? Sai ya bayyana min a fili cewa Ramlatu ce yake so ya bawa ɗansa.”

Shiru ya cika ofishin na ƴan daƙiƙu. Abba ya jingina baya a kujerar tasa, ya rufe littafin da yake karantawa ya ajiye gefe. Ya yi dogon numfashi, sannan ya saki murmushi mai ɗauke da nauyi.

“Masha Allah. Alhamdulillah. Wannan babban alheri ne. Gaskiya wannan abinda muka dade muna fata ne gidan mutunci da daraja. Ai abin godewa Allah ne.” Hamza ya ɗan ɗaga kansa da murmushi, yana ganin farin ciki a fuskar ɗan uwansa. “ yaya malam. Wannan dama ce babba, kuma abinda kowanne uba ke fata ne ganin yarinyarsa ta shiga gidan da zai ƙara mata daraja da alfahari. Ai gidan sarauta ne, gidan mutunci, gidan da kowa zai yi alfahari idan ya shiga.”

Sai Abba ya yi shiru na ɗan lokaci, ya ɗan lumshe idonsa kafin ya ce “Hakane Hamza. Amma akwai abu guda da nake jin tsoro a raina. Na rantse tsakanina da kaina cewa ba zan taɓa tilasta ‘ya ta akan zabin miji ba. Komai daraja, komai alheri, dole in saurari zabinta. Idan itace ta kawo min da kanta, zan yi murna. Idan ba haka ba, to Hamza, ina tsoron kada in zalunce ta.”

Hamza ya ɗan yi dariya, ya ɗora hannunsa a kan teburin yana kallon Abba kai tsaye.

Yaya malam, ka kwantar da hankalinka. Ka bar wannan magana a hannuna. In shaa Allahu ba za ka ji kunya ba. Auta tana da biyayya, tana da hankali, kuma mun san cewa ita ba ta da matsalar bin umarni. Wannan shi ne gidan da muke mata fatan shiga tun farko. Gashi yanzu dama ta zo. Ai ita kanta zata fahimci wannan babban arziki ne.”

Abba ya saki wani irin murmushi mai ɗauke da nauyi. Ya jingina hannunsa a kan kujerar, yana tunanin abin da zuciyarsa take gaya masa.

Sai ya ce cikin muryar dattijo mai hikima

“To, Hamza. Na ji maganarka. Allah ya sanya alheri. Amma ni dai burina na farko shi ne farin cikin Ramlatu. Idan ta ce eh, zan yi murna. Idan ta ce a’a, zan bar maganar.”

Hamza ya gyara zamansa, yana murmushi cikin natsuwa. “In shaa Allahu, yaya malam. Ka bar wannan a hannuna. Zan yi magana da ita da hikima. Ba za ka ji kunya ba, wallahi.”

Sai aka yi shiru na ƴan daƙiƙu, ofishin ya cika da kamshin turaren da ke ƙonewa. A gefe kuma aka ji karar agogon bango yana taƙawa.

***

Yau na dawo gida a mugun gajiye. Jarabawar da muka yi ta tsotse min ƙarfina gaba ɗaya. Wasa wasa, ga shi har mun kusa kammala wannan zangon karatu, amma duk da haka nauyin karatu da gwaje-gwajen da malamai suke ɗorawa a kaina sun fi ƙarfin da kowa zai ɗauka. Da na tsaya na yi tunani, sai na ce a zuciyata “Kai, abin nan da gaske da wahala sosai karatu babu sauki ko kadan Amma in shaa Allah za mu iya zakuma mu jure dan nasan watarana sai labari.”

Da na karaso gidan, ban tarar da kowa ba. Da alama Momy ta fita unguwa, domin gidan ya yi shiru, babu muryarta ko motsinta yar aikinmu kuma ba kwana takeyi ba tana zuwa ne kullum tatafi. Ban tsaya yin tambaya ba, kawai na tura kaina cikin dakina.

Na tsaya cak! A kan gadona, Yaya Bilkisu na kwance tana hutawa, idonta a rufe. Ɗan wani abu ya motsa a zuciyata, wani abu da ban iya fassara ba kwanaki har kayana naga ta sanya danayi magana momy ta rufenu da masifa. Amma sai na yi shiru kawai, na share tunanin, ban ce mata komai ba na ajiye jakata da takalmina sannan na cire kayan jikina na zura hijjab.

Na nufi bathroom, na yi wanka da ruwan sanyi duba da garin zafi ake domin in wanke gajiyar da nake ji. Bayan na fito, na sa kayana masu sauƙi na zauna ina shirin ɗan hutawa, sai ga wayata ta fara ringing a hankali.

Na ɗauka cikin kasala, ina kallo naga lecturer ɗin mu ne Malam Fahad.

Cikin rashin natsuwa, na ɗaga. Sai kawai na ji muryarsa ta cika kunne na da masifa

“Wai me ke faruwa ne da ke? Ina ta kiran ki baki ɗauka ba. Haka ake soyayya ne? Kin raina ni kenan ko?”

Wani numfashi na takaici na ja. Kai malam din nan da gaske yana bani haushi. Kullum sai masifa, ko kadan ya ga kuskure, sai ya yi kamar shi ne mai ikona.

Sai kuma ya ɗora da cewa “Wai ba magana nake miki bane? Ban son ana min banza. Ni ba sa’an ki bane, ki sani. Ke dai yarinya ce, ni ba irin mutanen da kike wasa da su bane. Kina ji ko?”

Na dafe kaina cikin takaici. “Ni? Soyayya da kai? Ni ba na buƙatar soyayyar da ke cike da masifa da zagi, kamar dai na yi aure da mutum mara tausayi.”

Ban san me zan ce masa ba. Zuciyata ta yi nauyi, zuciyata ta ƙi amincewa da irin wannan dangantaka. Na ce kawai “Na gaji, malam shiyasa.” Kafin ya ƙara magana, na kashe wayar gaba ɗaya na ajiye ta a gefe. Na lumshe ido ina jin jikina na rawa saboda takaici.

A lokacin ne na ji wata muryar ta fito daga kan gadona. Yaya Bilkisu ta buɗe idonta a hankali, ta yi dariya kaɗan sannan ta ce “Toh, kin dawo kenan gadonki inajin dadin bacci idan nasamu dama nan daƙin zandawo?”

Na juya ina kallonta. Fuskar ta nuna tsantsar gaskiyarta har tana faɗin gadon da abba yasanya miki yafi nawa tsada shiyasa.Amma ni ban daɗe da fita daga masifar malam ba,zuciyata har yanzu cike da takaici.

Na ce mata da gajiyawar murya” Au”

Ban ƙara cewa komai ba. Na miƙe na bar ɗakin, na bar mata gurin gaba ɗaya.

Na fita zuwa falo, zuciyata cike da tunani da bacin rai. Na ce a zuciyata:

“Ko da rayuwa ta yi wuya, zan daure. Amma wallahi ba zan lamunci a saka ni cikin soyayya ta ƙarfin tsiya ba. Na fi jin daɗin zaman lafiya da zuciya ta, fiye da a saka ni cikin wani da kullum masifa yakemin tun ban aureshi ba ya canza faɗa da mita kullum.”

Na jingina da kujera a falo, na rufe ido. Amma duk da gajiyar jarabawa, zuciyata ba ta samu nutsuwa ba saboda masifar Malam Fahad.

*****

Hajja na zaune a gaban Mai Martaba cikin natsuwa da girmamawa. Zauren fada ya cika da sanyi, turaren itace na tashi a gefe,Ita kuwa Hajja ta jingina da kujerar tana cikin shiga mai kyau ta alkyabba, tana sauraron maganar da ke fita daga bakin Mai Martaba.

“Ranka ya daɗe, shi As’ad din ne yace yana son yarinyar?”

Muryarta ta fito da nutsuwa, amma a zuciyarta akwai nauyi da kuma mamaki.

Mai Martaba ya yi murmushi mai zurfi, yana kallon Hajja cikin idanuwa. “Kwarai kuwa, Hajja. Shine wanda ya nemi aurenta. Yau da asuba ma, bayan mun haɗu a masallaci, sai ya sake tambayata akan yana so a je a nema masa auren kawai.”

Ya yi shiru, ya jingina da kujerarsa mai dauke da zinariya, yana mai jan numfashi.

Hajja ta dafe ƙirjinta da hankali, ta ja dogon numfashi, sannan ta ce “Banki maganarka ba, Ranka ya daɗe. Amma fa ina ganin wannan auren yanzu kamar zaluntar mata ne. Kaga ai As’ad yanzu bashida cikakkiyar lafiya. Wannan matsalar da zaka tuna ita ce ta faru da Haneefah, ta jawo rabuwarsu. Yanzu kuma ga Ayshatu ta gudu daga gidan aure saboda larurarsa. To Ranka ya daɗe, ina ganin a kawo wata yarinya ƙarama kuma a ɗora mata wannan nauyin, gaskiya kamar babu adalci.”

Nana hadiza

09030569336

[28/09, 8:19 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN DA BIYAR

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Hajja ta yi shiru, idonta na kan ƙasa, tana nuna gaskiyar damuwarta. Ita uwa ce da ta tsani ganin an zalunci mace da aure da wahala.

Mai Martaba ya ɗan dafe gemunsa cikin tunani, ya ɗauki shiru na ƴan daƙiƙu. Daga baya sai ya ce a hankali “Maganarki abar dubawa ce, Hajja. Hakika, akwai gaskiya a ciki. Amma kuma wannan lamari dole ne mu yi shi da hikima. Ni dai abin da nake gani shi ne zan yi magana da As’ad din da kaina tukunna. Zan ji dalilinsa, zan ji natsuwarsa. Idan kuwa ya tsaya kan lallai yana so, sai mu ɗauki mataki na gaba nasan As'ad bazai taɓayin abunda zai cutawa yarinyar ba.”

Ya ɗan gyara zamansa, ya ɗora hannunsa kan armrest ɗin kujerar, yana mai nuna da cewa shi ne na ƙarshe a zance. “Inaso ne, Hajja, ki zama cikin shiri. Saboda gobe nake so a fara isar da gaisuwa ga iyayen yarinyar. Duk wasu hidindimun da za a yi, sai a tsara su a hankali. Na san za ki iya kula da komai yadda ya kamata.”

Hajja ta sunkuyar da kai cikin girmamawa. Tana jin nauyin magana, saboda tunda Mai Martaba ya yi hukunci, ita aikin ta kawai shi ne ta biya bukata. Amma zuciyarta har yanzu ba ta kwanta ba.

Ta ce cikin nutsuwa “To, Ranka ya daɗe.”

Sai ta yi shiru, ba ta ƙara cewa komai ba. Zuciyarta tana cike da tunani “Shin wannan aure zai kawo farin ciki ko kuma zai sake kawo wani bala’in?”

Da ta bar gaban Mai Martaba, Hajja ta zauna a ɗakinta tana tunani sosai. Ta tuna rayuwar As’ad da yadda ya tashi da matsaloli rashin lafiya, damuwa, da kuma rabuwa da mata kala kala Ta tuna yadda Haneefah ta yi kuka a lokacin rabuwarsu, sannan Ayshatu ta gudu da zuciya cike da ƙiyayya.

“Yanzu kuma a kawo wata yarinya ƙaramar mace? Wata ɗiya mai fara rayuwa a saka ta cikin irin wannan masifa? Wannan ba adalci bane.”

Hajja ta girgiza kai cikin zuci. Amma kuma ta san shi As’ad mutum ne mai daraja a gidan sarauta, kuma duk wanda yake so ya aure to babu makawa fa sai anyi auren nan. Amma ita dai zuciyarta tana tsoron abunda zaije yadawo.

“Allah ka tsare. Allah ka tabbatar da alheri. kada a zalunci yarinyar nan.”

******

Shi kuma Mai Martaba bayan tafiyar Hajja, ya zauna shi kaɗai a falonsa. Ya jingina da kujera, yana jujjuya carbi a hannunsa.

“As’ad ya zo da kansa ya nemi wannan aure. Ban taɓa ganin shi cikin irin wannan natsuwar ba tun bayan rabuwa da Ayshatu. Shin hakan yana nufin zuciyarsa ta sake buɗewa? Ko kuwa wani abu daban yake nema? Nasha yimasa aure kala kala baitaɓa musantamun ba hakan na nuna wannan yarinyar itace hakikanin zabinsa”

Ya ɗan murmusa, ya ce a ransa “Ni zan tsaya masa dan nasan wanene ɗana bazai taba zaluntar ƴar mutane ba dan haka babu yadda za a yi sai a na tsaya masa akan al’amarinsa.”

Sai ya rufe idonsa yana mai ambaton addu’a cikin zuciya.

Bayan an idar da sallar Magrib, As’ad ya nufi bangaren Hajja domin gaisuwa. A babbar fadar ta ya same ta zaune bisa kujerar dogo tana lazumi, hannunta riƙe da carbi baki tana lazumi. Ac din cikin falon suna bada sanyi, kamshin turaren itace yana tashi a hankali..

Da ya shiga, sai ya tsaya a gefe, ya duƙa da ladabi ya gaishe ta. Hajja ta ɗaga kai ta dubesa, sannan ta amsa cikin natsuwa.

Ya zauna a ƙasa, yana sauraron Firdausi wacce take ba shi labari. Amma shi dai ba ya iya ce mata komai, sai kawai kallon ƙasa yake yi cikin natsuwa. Sai da Hajja ta gama lazuminta sannan ta kalle shi kai tsaye.

“As’ad, Yaya kake ya aiki? Nayi tunanin ai baka kasar ma ina fatan babu wata matsala ko?” ta tambaya.

Ya ɗaga kai cikin ladabi, ya ce “ Eh yau dai nake kokarin shirya tafiyan spain akwai aikin da zanyi acan matsala kuma Babu, Hajja. Allah ya ƙara miki lafiya.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull