Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 14

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 14

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 14: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 14. Sai ta ɗan yi shiru, ta gyara zama, ta dubesa da ido. “Nikuma anan…

4,462 words

Sai ta ɗan yi shiru, ta gyara zama, ta dubesa da ido. “Nikuma anan ina da Babbar matsala kuwa, As’ad. Dazu mai martaba yasameni akan maganar da kayi dashi ina ganin babu adalci azancen nan nasan mai martaba bazai taba hanaka auren wacce ka neme ma ba saboda yana ganin ai ka kasance mai biyayya gareshi a kowanne lokaci dan haka a yarda ya nunamun ma maganar tariga ta tabbata.Na ga kana da imani da kyakkyawar zuciya. Amma tayaya zaka je ka ce kana son wata yarinya yanzu? Kana fi kowa sanin halinka, kana da matsalar lafiya. Mata nawa suka rabu da kai? Ina tunanin sun fi bakwai. Yanzu itama zaka jawo ta har ƙasa? Bayan ka cuta mata ka rabu da'ita ko da matsalar ayshatu nata nuna maka karabu da'ita amma sai soyayya ta rufe maka idanuwa ko? Inada tabbacin kai ba yaro baniba As'ad sannan kanada saninka na addini ban kasance uwa mai danne son yaranta dan ayi zalunci ba”

Muryarta ta cika da damuwa da tausayawa hade da faɗa.

As’ad ya sunkuyar da kai, ya yi shiru na ɗan lokaci. Sai daga baya ya ce cikin ladabi da murya mai sanyi da kuma girmamawa “Allah ya ƙara miki lafiya, Hajja. Dan Allah ki yi hakuri. Nasan ban da cikakkiyar lafiya, amma yanzu ina kan magani, ina samun sauƙi sosai. Kuma gaskiya Hajja… yarinyar ina jinta sosai a raina. Bantaba jin wata kamarta.”

Hajja ta girgiza kai, ta dafe hancinta.

“As’ad, kai musulmi ne. Kada ka manta dukiyar ka da sarautarka ba za su baka ikon taka duk wanda kake so ba. Aure amana ne, ba wasa ba. Idan ka tafi haka kana ɗaukar yara kamar kaya, wallahi kana shiga cikin abin da Allah ba zai yarda ba.”

As’ad ya lumshe idonsa, zuciyarsa na buga. Ya ce da nutsuwa “Hajja, ban ɗauki aure da wasa ba. Duk abubuwan da suka faru abaya jarabawa ce hajja wacce banda ikon rabuwa da'ita bankuma da ikon tsallake su. Ban kuma ɗauki mace a matsayin abin kwaikwayo ba. Amma wannan karon, zuciyata ta sha bamban. Ba wai kawai saboda daraja ko sarauta ba, Hajja. Amma ina jin ta sosai. Ina ganin in Allah ya yarda, ita ce zata bani nutsuwar da ban samu ba a baya.”

Sai ya ɗan yi shiru, ya zuba mata ido.

“Dan Allah, Hajja… ki bani damar wannan aure. Zan kiyaye, zan yi gaskiya. Ina roƙonki da addu’arki.”

Shirunsu ya cika fadar. Hajja ta jingina, tana kallonsa da ido mai zurfi. Ta ga gaskiya a cikin murya da fuskarsa, amma zuciyarta har yanzu na da nauyi. Sai kawai ta sauke ajiyar zuciya, ta ce a hankali “Allah ya tabbatar da alheri, As’ad. Amma ni zan ci gaba da addu’a. Ka sani, ba zan taɓa ƙarfafa ka wajen zaluntar wata yarinya ba.”

As’ad ya tsugunna sosai yayi murmushi “Nagode Hajja. Allah ya saka miki da alheri.”

Tunda ya bar sashen Hajja, jikinsa gaba ɗaya ya saki kamar wanda aka cirewa ƙarfi. Wannan sauyin bai zo masa da sauƙi ba. Kwana biyu kenan As’ad yana fama da wani mugun zazzabi mai rikitarwa. Bai ji daɗi ko kadan ba, sai dai nauyin jiki, ciwon ƙashi, da kuma sanyi mai sosa shi tamkar ana zuba kankara a cikin jininsa.

A da can, irin wannan zazzabi ya saba dashi. Amma yau daban yake. Domin duk lokacin da idonsa ya rufe, fuskar Ramlah ce ke bayyana a cikin zuciyarsa, tana yi masa gizo-gizo kamar hoton da aka lulluɓe da haske. Idanun ta masu launin sanyi suna zuba masa kallo, muryarta tana ƙara komawa kunnuwansa kamar waƙar da ta zame masa magani.

Nana hadiza

09030569336

[29/09, 4:22 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN DA SHIDA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

As’ad ya taɓa soyayya da mata da dama. A gaskiya ya san ya fi son Ayshatu a wancan lokacin fiye da kowace mace, amma wannan abin da yake ji yanzu ba kama-karya bane. Bai taɓa jin irin wannan nauyi da tsananin sha’awa ba. Bai taɓa jin mace ta shiga zuciyarsa cikin irin wannan ƙarfin da ba zai iya kwacewa ba.

Ya jingina a jikin kujerar da aka zana da hannun kwararru daga Italiya, jikin nasa yana rawa saboda zazzabi. Tsigar jikinsa tana tashi, hakoransa suna datsewa da ƙarfi. Amma duk da wannan raɗaɗi, zuciyarsa ta ji daɗi mai ban mamaki. Kamar dai wannan zazzabi ya haɗu da wani irin motsi na sha’awa da yake ƙonewa a zuciyarsa.

“Ya Allah, Ya Kareem, menene nakeji haka yafaɗa cike da mamaki” ya furta cikin kunci, yana rufe bakinsa saboda tsananin rawar da jikinsa yake yi.

Wayarsa tana kara a gefe, kiran da ba ya iya amsawa saboda hannunsa ya yi nauyi kamar an ɗora masa duwatsu. Amma zuciyarsa ta kasa tsayawa wuri ɗaya. Kullum fuskar Ramlah take dawowa.

Ya tuna lokacin da suka haɗa ido a taron jami’a, yadda idanunta suka tsaya cikin nasa na daƙiƙu kaɗan. Wannan kallo ɗaya ya fi masa duk wata soyayya da ya taɓa rayuwa da ita. Wani irin sanyi ya ratsa shi, zuciyarsa ta ce masa

“Wannan ce soyayyar da ake faɗa. Wannan ce mace ɗaya da zata iya sa rayuwarka ta dawo haka kaunar take.”

Jikinsa yana girgiza saboda zazzabi, amma a zuciyarsa wani irin sha’awa ta kama shi. Sha’awar rungumarta, sha’awar jin muryarta a kusa da kunnensa, sha’awar kallon idanunta da tsawon lokaci. Yarasa gane wannan lamari yasamu lafiya ne kokuma dai yana bacci ne?

As’ad ya rufe idonsa, yana jin kamar hannunsa na taɓa gashin kanta. Sai ya buɗe ido cikin mamaki, amma babu kowa. Wani murmushi mai taushi ya subuce a bakinsa.

“Ramlah… ko kin sani? Ke ce kika sa zuciyata ta fara motsi. Ko jikina da aka ce ya mutu, yau ya fara jin wani sabon motsi saboda ke.”

Ya ja numfashi mai zafi, yana jin yadda zafin zazzabi ke ƙone shi daga ciki. Amma a lokaci guda, wannan ƙonewar ta koma daɗin soyayya. Tsiririyar zufa ta ratsa goshinsa, ta gangaro kan kumatunsa. Ya rufe idonsa, yana jin kamar yana jin muryarta a kusa da shi tana faɗin “Matasa su ne ginshiƙin al’umma…”

Sai bugun zuciyarsa ya ƙara tsananta, jikinsa yana amsawa da wani irin zafi mai radadi.

Ya nufi gadonsa da ƙyar, ya zauna a kan shimfiɗar mai taushi. Fitila na saman kai tana bada wani haske switch ya kunna ya kashe Ya dafe ƙirjinsa, yana jin zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi kamar zata tsage.

“Ramlah…” ya kira cikin muryar da ta cika da ƙauna da sha’awa.

Ya jingina da pillow, jikinsa yana rawa saboda zazzabi, amma zuciyarsa ta gama yanke hukunci gobe yakeso aje anema masa izini baijin zai iya daukar lokaci batare da takasance tasa ba. Yes mai martaba yasanar dashi tataba aure wannan kuma ba matsalarsa bace ba ko aurenta goma yana kaunarta ahaka. As’ad ya kasa tsayawa da tunanin irin yadda zai kasance idan ya sake ganinta. Fuskar ta ce ke masa magani, idanunta ke rarrashin zuciyarsa. Duk cikin zazzabi da damuwa, ya ji natsuwa. ya rufe idonsa, ya yi addu’a “Ya Allah, idan wannan ce soyayya ta gaskiya, ka tabbatar min da ita. Ka haɗa ni da ita cikin alheri.”

Ya lumshe ido, ya bar kansa cikin haduwar zafin jiki da daɗin zuciya. A hankali kuma yafara karanto addu'a a hankali.

***

Ruwan sama ne ya tashe mu tun da safe, iska mai sanyi tana busowa ta taga, tana cike da ɗanɗanon ƙasa da ƙamshin ruwa. Ni kuwa na tashi cikin farin ciki saboda mun gama jarabawa, duk da gajiyar da nake ji.

Na yi wanka, na ɗan gyara gidan sama sama, sannan na sanya light gown mai sauƙi amma ya fito da ƙibata, domin yanzu na ciko sosai. Na tsaya gaban madubi ina kallon kaina, sai hawaye suka cicciko min. Na furta a zuciya

“Allah ka jikansa… Bashari Allah kabashi Aljanna.”

Ban gama tunanin ba sai naji an turo kofar daƙin nawa. Momy ce ta leƙo, ta ce cikin yatsine fuska “Ramlah, zo. Abba na kiran ki.”

Na ce “Ganinan, Momy. Bari in gama.”

Na ɗan ɗora lipstick, na fesa turare kadan, sannan na fito zuwa falo.

Abba na zaune cikin shadda mai kyau, alamarsa ma fita zai yi. Da na ganshi sai na tsugunna har ƙasa na gaisheshi da ladabi. Ya amsa da murmushi, sannan ya ce “Ramlah, angama jarabawa ko?”

Na ce cikin ladabi “Eh Abba. Munyi hutu sai next month.”

Sai ya ɗaga hannu sama, ya ce “Ubangiji Allah ya baku sa’a.”

Na amsa da “Ameen.”

Abba ya ɗan gyara zama sannan ya ce “Uncle dinki Hamza yana son ganin ki. Yana jiranki yanzu, sai ki tafi.”

Momy kuwa ta yi saurin tsoma baki tana kallon Abba “Abban Ramlah, dan Allah ka dinga haɗata da yar uwarta. Su dinga zuwa ko’ina tare banajin dadin yadda kake wari bilkisu.”

Abba ya dubeta da ido mai nuni, ya ce “To ai, Zainabu, ke ce baki son ta rabe diyarki. Amma Ramlah tana son yar uwarta sosai.”

Sai Momy ta yi shiru, saboda ba haka take so a ce ba. Da alama taso ace Abba ya rufeni da masifa.

Ni kuwa na ji daɗi a zuciyata. Domin don na nuna mata cewa korafinta bai karbu ba, sai na ce “Yaya Billy, kitawo mu tafi.”

Ta dubeni ta ce “Toh.”

Tana kallon Momy, ni kuma na wuce na ɗauko hijjabina na lullube jikina gaba ɗaya.

Sai muka fito ni da Yaya Bilkisu tare, muka nufi hanyar gidan Uncle Hamza, zuciyata cike da tambayoyi “Me yasa yake son ganina yanzu haka? Menene zai ce min?”

Tun daga cikin mota, Yaya Bilkisu bata bari na samu nutsuwa ba. Tana ta kwarmamin labari kan yadda take son aure, amma kash! duk samarin da suka zo wajenta, ba wanda ya tsaya har zuwa ƙarshe. Na ji muryarta kamar tayi kuka. Ni dai shiru nayi, ban ce mata uffan ba. Amma saboda kada ta ɗauka kamar ban ji ta ba, sai kawai nace mata “Allah ya kawo miki na gari, Yaya.”

Ta yi shiru, tana kallon titi da idonta cike da tunani. Ni kuwa zuciyata ta fara damuwa da dalilin kiran da uncle yakemun

Muka karasa gidan Uncle Hamza, gida mai tsari da kyau, an kawata shi da shuke-shuke a harabar, da fitilu masu haske Muka yi sallama, aka karɓe mu da fara’a. Mami, matar Uncle, ta fito ta tarbe mu da murmushi, tana cewa “Sannunku da zuwa ƴaƴana ku shiga ciki ku huta.”

Muka gaisa da ita, sannan muka nufi sama zuwa dakin Uncle Hamza. babban ɗaki ne mai ɗauke da carpet mai laushi, shelves ɗin littattafai, da tebur mai cike da takardu da kwalayen ruwa.

Da muka shiga, sai na tsugunna da ladabi na ce “Uncle, Abba ne yace kana nemana. Allah yasa ba laifi nayi ba.”

Na ɗago kaina cikin sanyi, zuciyata cike da ɗan tsoro.

Uncle ya yi murmushi, ya girgiza kai cikin natsuwa. “Babu ko ɗaya, Auta. Kin yi abin da ya dace.”

Na zauna a kasan carpet cikin ladabi, Yaya Bilkisu kuma ta zauna a gefe tana kallona. Na ji zuciyata na dukan tamkar ana kaɗa ganga.

Uncle ya ɗan gyara zamansa, ya ce da muryar dattijo mai tausayi “Ramlah, akwai wani bawan Allah da ya ganki ya ce yana sonki. Harma yana shirye-shiryen turo iyayensa. To sun samu Abbanku, amma Abba ya ce bazai taɓa tirsasa ki ba. Indai akan mijin aure ne, sai ke kanki kika faɗi ra’ayin ki.”

Na runtse idona, numfashina na sarkewa. Hannuna na fara karkarwa a hankali. Amma Uncle bai tsaya ba, ya ci gaba da magana cikin natsuwa “Mun yi magana sosai da Mai Martaba kan wannan lamari. Har ya tabbatar min cewa shi da kansa ne ya nemi wannan aure. Amma na ce masa ‘Ni ba zan taɓa turasa Ramlah ba, sai na ji daga bakinta.’”

Zuciyata ta sake tsalle tamkar wuta. Sunan Mai Martaba ya girgiza ni. Na kalli Yaya Bilkisu, fuskar ta canza, kamar an zuba mata ruwan zafi. Shiru tayi, ta kasa cewa komai.

Uncle Hamza ya ci gaba da maganar sa cikin ladabi da kwantar da hankali “Ramlah, kar ki ji tsoro. Idan baki amince ba, babu wanda zai matsa miki. Amma ki sani babu wata daraja da kimar diya mace sama da aure. Ki guji kallon baya, ki tuna cewa baya ya riga ya wuce. Rayuwa gaba ce. Kuma wannan gidan da kike ji, gidan mutunci ne da alkhairi. Idan kika shiga, ki tabbata babu wanda zai taba cewa ki yi nadama.”

Hawayena suka cicciko. Na kasa magana na ɗan lokaci. Na ji zuciyata tana rawar jiki, na ce a raina: “Ya Hayyu Ya Qayyum… menene wannan jarabawar? Aure kuma? Dawa to?”

Na tuna ni mace ce, ƙarama, mai ɗan ƙwarewa a karatu amma ba ta taɓa yin tunanin cewa zata shiga cikin gidan sarauta irin wannan ba. Tsoro ya mamaye ni, amma lokaci guda na ji wani irin nauyi da biyayya.

Na share hawayena da hannuna, cikin muryar kuka nace “Uncle… indai hakan yayi muku kuma kun amince, to nima na amince. Ni mai biyayya ce gareku. Duk inda kuka sa ni, zan tsaya. Amma na faɗa muku gaskiya, ban taɓa tsammanin haka ba.”

Na fashe da kuka sosai. Kukan da ya haɗa fargaba, biyayya da kuma tsoro na gaba.

Uncle Hamza ya yi murmushi cikin tausayi, ya ɗaga hannunsa yana kallona da ido mai cike da jinƙai. “Na sani, Ramlah. Na sani sosai. Amma nasan daman bazaki taɓa bamu kunya ba. Allah ya albarkace ki. Ki kwantar da hankalinki. Insha Allahu alkhairi ne.”

Na ji muryar sa ta shige zuciyata. Amma zuciyata ta kasa tsayawa wuri guda. Tana tambayar kanta: “Shin wannan aure zai kawo farin ciki gare ni? Ko kuwa wata jarabawa ce mai girma take tunkarata?”

Na sunkuyar da kai, hawaye suna zuba, amma kalmomin Uncle suna kara sa zuciyata ta aminci “Allah ya zaba min abunda yafi alkhairi dan bazan taɓa iya bijirewa iyayena ba.”

Nana hadiza

09030569336

[30/09, 10:00 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Na ɗan samu natsuwa a zuciyata bayan dawowa daga gidan Uncle Hamza duk da ni ban shirya aure yanzu ba bama na marmari ko kadan Allah yasani inata kau da kaina daga samarin danake samu ko malam fahad ban boye masa ba nagayamasa gaskiya bana sonsa amma kuma bazan iya jayayya dasu abba ba duk da zuciyata bata so ko kaɗan. Duk da nauyin maganar uncle hamza nadai dage da addu'a idan babu alkhairi ubangiji ya lallata abun.

Na yi ƙoƙarin mayar da hankali na ga wayata ina kallon YouTube saboda damuwar danaga ina kokarin shiga Na ɗan samu farin ciki acikin zuciyata saboda inason series din danake kallah ina ganin kiran malam fahad haka na share ban dauka ba dan ni yanzu bana kaunarsa ko ƙadan tunda baisan darajar mace ba ko kadan daga zagi sai fada wayasani ma ko irinsu ne masu dukan mata.

Bayan kwana biyu sai na fara jin maganganu. Da farko na ɗauka kamar almara ce banyi tunanin maganar zata dauki dangin abba ba Amma sai labarin ya fara shiga kunnuwana daga wurare daban-daban.

Da farko wata bahijja yar kanin su abba ta kira ni da daddare, tana dariya. Ta ce “Ramlah, wai daman soyayya kike duk kin boye mana sirri ko? An ce wani babban mutum daga gidan sarauta yana sonki. Ashe har kin samu wannan alfarma baki gaya mana ba? Haba auta bakyaso mu tayaki murna”

Na yi shiru, jikina ya yi wani irin sanyi. Banyi mamakin zancen ya yaɗu ba tunda daman nasan mami matar uncle hamza taji to tabbas sai ta sanar da kowa lamarin macece mai shegen surutu da magana Na ce mata cikin muryar dake rawa “Wallahi ni ban san komai ba. Maganar aure kawai Uncle ya yi da Abba, amma ban ji sunan kowa ba. Kema kin san ban taɓa ɓoye muku komai ba ai.”

Sai ta yi dariya ta ce “Ai kuwa family house anata maganganu. An ce daga gidan sarki ne, kuma babban mutum ne sosai. Nikam nayi miki murna sosai..”

Na kashe wayar zuciyata cike da rudani. Na ji kalmarta ta tsaya min a zuciya tamkar ƙaya. “Daga gidan sarauta? Babban mutum? To wanene haka?”

Ban daɗe da ajiye wayata ba, sai wata kawar Yaya Bilkisu ta shigo gidan. Ina jin ta tana hira da ita a tsakar gida. Billy, kin ji labari kuwa? Ana cewa kanwarki ta samu alfarma. Gidan sarauta suna neman aurenta. Lallai wannan kanwar taki tanada kashin arzuki sha hararren mai kudi ne fa duk da dai dattijo ne.”

Na ji jikina ya ɗauki rawa. Na ji Yaya Bilkisu tayi shiru ta kasa magana, sai ta ce cikin murya kasa kasa “ kinji sunansa?” Sai kawar tace a'a gaskiya banjiba nima fa a family house dinku nakeji.

Da ta shigo ɗaki bayan kawar tata tatafi, idonta ya cika da wani irin hawaye. Ta kalle ni sama da ƙasa sannan ta ce “Ramlah, kinji ko? Ana cewa gidan sarauta suke sonki. Ashe ke kina da sa’a kika samu wannan dama? To ni dai zan tsaya naga yadda za ki yi dan wallahi kowa yasan ke ba kalar gidan sarauta bace ba ni nafi dacewa da gidan.”

Na ji kamar ta soki zuciyata da wuka. Amma ban ce mata komai ba, sai kawai na sunkuyar da kaina hawaye suka zubo a hankali. Wai nice ba kalar gidan sarauta ba bayan yaya Billy gaba daya ta lallace tafita hankalinta tarame tayi baki ni auren ma baya gabana wallahi da zasu bata mijin danaji dadi.

Momy tana zaune a falo tana waya da wata kawarta. Sai kawai na ji tana cewa cikin masifa “Ai duk ƙarya suke yi. Uban wa zai aureta? Su dai suna ta ɓata lokaci ne amma duk karya ne. Wallahi babu gaskiya a ciki duk karyane fa munafurcin hamza ne.”

Na tsaya a bakin ƙofa ina jin kalamanta. Idona ya cicciko da hawaye, na juya na koma dakina. Na fada kan gadona, na rufe kaina da bargo. Zuciyata ta yi wani irin nauyi tamkar dutse aka ɗora min.

“Allah na, me yasa komai nawa yake zama kamar jarabawa? Me yasa duk lokacin da na ji wani abu mai daɗi, sai a juya shi ya zama masifa? Ni kadai nasan radadin da nake ji.”

Na jawo littafi na ce in karanta don na manta, amma babu abin da yake shiga cikin raina. Sai kuka kawai nake yi cikin raina.

Wannan magana ta ci gaba da yawo daga gida zuwa waje munatane sunata munafurci.

****

Zaune bilkisu take akan gadonta abun duniya ya isheta yanzu ma kenan ramlah aure zatayi ta barta sosai zuciyarta take konewa ko ba'a faɗa mata ba tunda taji ance gidan sarauta ai wannan shine gidan manyan mutane cikin zuciyarta tafara maganganu na na tabbatar maganar da ake ta yawo ba ƙarya bace, zuciyata ta ƙone da bakin ciki. ji nakeyi kamar duniya ta tsaya cak a gabana. Duk abinda na dade ina mafarkin samu aure mai daraja, mutunci, shiga gidan sarauta yanzu an ɗauke shi aka ba Ramlah.

INa zaune a dakina na dinga kallon madubi, idona cike da hawaye amma zuciyata tana tafasa. “Ni ce babba, ni ce na fi cancanta. Ni ce na fi kowa shiryawa. Amma me ya sa ni aka wuce aka bawa ita? Ni da nayi shekaru ina mafarkin in zama matar mutum mai daraja, ni da na sha zancen samari da yawa amma suka guje ni. Sai ita, ita da bata ma san darajar aure ba, ita aka bawa wannan sa’a?”

Ji nakeyi kamar zuciyata ta fashe da wuta. Na rasa yadda zan zauna da ita cikin gida ɗaya. Idan na ga fuskarta, sai zuciyata ta ƙara tafasa.”

tashi nayi n shiga dakin Momy. Na zauna kusa da ita na fara kuka tamkar wacce aka zalunta. Na ce “Momy, kin ji abin da ake cewa kuwa? Ashe Ramlah ce ake nema daga gidan sarauta. Ni fa Momy, ni fa na rasa sa’a. Ni fa kullum sai dai ace na tsaya gefe, ana ɗaukar duk abin kirki a bawa ita. Momy, me yasa haka?”

Momy ta tsaya ta kalleni, idonta ya nuna haushin magana. Ta ce da zafin rai “Ke ki kwantar da hankalinki Bilkisu. Wallahi wannan magana ƙarya ce kawai. Ba gaskiya bace. Ai babu wanda zai aure ta. Nagayamiki har yanzu abbanku bai mun magana ba idan da gaske ne ai kinga abbanku zai fara sanar dani ko? Ke da nake tayiwa kokari ki auri As’ad ai kowanne miji xata samu bazai taɓa kaiwa kamar naki ba.”

Maganar Momy ta ɗan sanyaya ni, amma zuciyata bata huce ba. Na ji kishi da bakin ciki sun mamaye ni gaba ɗaya. Na ce a raina “Ko gaskiya ce, sai na yi duk abinda ya kamata domin na lalata wannan aure. Ba zan taɓa bari Ramlah ta shiga inda ni na dade ina mafarki ba.”

Na kwanta a kan gadona da idanuwa cike da hawaye, amma zuciya cike da ƙuduri.

Washegari bayan la’asar, muna zaune a falon gidanmu. Abba yana zaune akan kujera yana duba jarida. Momy kuwa tana gefe da fuskarta cike da damuwa sosai dan sai magana takeyiwa Abba amma bai kulata ba. Yaya Bilkisu tana can cikin dakinta amma ina jin shigowar sautin kukan kiɗa daga wayarta. Ni kuma ina kusa da Abba, ina karanta littafina a hankali.

Sai kawai aka ji karar motoci a bakin gate. Mumy ce ta lika ta window tace kai, motoci guda uku masu shegen kyau suka shigo harabar gidan namu fa atake Fuskata ta ɗauki zafi, zuciyata ta fara dukan ban tsoro. Na ce a raina “Subhanallah, wa zai zo da wannan motocin ga momy sai faɗa takeyi ita bata taɓa ganin irin motocin nan ba ko daman kasan da bakin abban auta?” banji abba ya amsa mata ba sai natashi nashiga dakina na lika ta window nima Sai ga masu tafiya cikin nutsuwa suka fito daga motoci. Sanye suke da dogayen kaya na alfarma, hannunsu riƙe da akwatuna da jakunkuna masu shegen kyau dan zan iya rantsewa bantaɓa ganinsu ba. A gabansu akwai wani dattijo mai fara’a wanda kallo ɗaya za ka yi masa ka san daga gidan sarauta yake.

Masu gadi suka shigo dasu da girmamawa, aka yi musu iso zuwa cikin falon. Na tsaya gefe jikina na rawa.

Abba ya miƙe cikin fara’a, ya tarbe su da murmushi “Sannunku da zuwa, Allah ya kawo ku lafiya maraba maraba ban san da zuwan ba agafarceni.”

Suka amsa cikin girmamawa, suka zauna a kujerun da aka tanada musu. Na lura Momy ta miƙe bayan ta gaidasu sannan ta koma gefe tana kallo da mamaki, fuskar ta ta cika da rashin jin daɗi da kuma tsananin mamaki da tambaya.

Wannan dattijon da ya jagoranci tawagar ya gyara zama, ya kalli Abba cikin ladabi ya ce

“Alhamdulillah. Malam mun zo ne da gaisuwa daga gidan Mai Martaba. Mai Martaba ya turo mu domin mu gabatar da muradinsa a gaban ku.”

Falon ya ɗauki shiru. Na ji kamar zuciyata ta tsaya cak. Idona ya sauka ƙasa, hannuna suka fara karkarwa.

Dattijon ya ci gaba “Mai Martaba ya bayyana cewa ɗansa As’ad yana neman aure. Ya kuma zaɓi ‘yarku, Ramlatu, a matsayin matar da yake so a ba shi. Mun zo ne da wannan magana, da kayan tambaya na al’ada, domin ku duba, kuyi shawara, sannan ku ba mu amsa.”

Na ji duniya ta juya a kaina. Sunan As’ad ya doki kunnena kamar ana buga ganga. Na ji hawaye sun cika idona, amma na runtse su na ƙi bari su zubo shine fa wanda yaya

Abba ya yi murmushi, ya gyara zamansa. Ya ce cikin ladabi “Alhamdulillah. Gaskiya wannan babbar alfarma ce gare mu. Amma kamar yadda na saba faɗi, ni bazan tursasa ‘ya ta akan aure ba. Zan kira ta, ta zauna da ku, ku ji kanta. Idan ta amince, to shikenan. Idan kuma ba ta so ba, to ba zan iya hanata ba.”

Duk mutanen falon suka kalli Abba da girmamawa. Dattijon ya ce “Malam wannan abin godiya ne. Mun san kai mutum ne mai mutunfi. Mu dai mun kawo gaisuwa, sauran naku ne.”

Na ji jikina na rawa. Sai kawai Abba ya dubeni ya ce “Ramlah, tashi ki gaishe da baki.”

Na tashi jikina kamar maraƙi, na rufe jikina da hijjabi, na tsugunna har kasa na yi musu sallama. Sun amsa da murmushi, sannan suka ce “Allah ya yi miki albarka, Insha Allahu wannan aure zai zama alheri gare ki.”

Na kasa magana, sai hawaye suka zubo min a hankali. Na sunkuyar da kai, na ce cikin raina “Ya Allah, kai kadai ka sani. Idan wannan aure alheri ne, ka tabbatar min da shi. Amma idan jarabawa ce, Allah ka tsare ni.”. Na koma dakina, na zauna na fashe da kuka. Na ce cikin raina “Allah na, wannan aure na As’ad ya zama mafarkin kowa. Amma me yasa aka kawo shi a kaina? Shin wannan ƙaddarata ne ko jarabawa ce? Ni kadai nasan zafin da zuciyata ke ji.”

Nana hadiza

09030569336

[01/10, 6:56 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA TALATIN DA TARA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Da sassafe na tashi na gyara dakina ina addu’a cikin zuciya, don na ji jikina yana nauyi saboda abubuwan da suka faru jiya. Ban gama komai ba sai kawai na ji ƙarar ƙofa ta buɗe da ƙarfi. Sai ga Momy da Bilkisu sun shigo cikin masifa. Fuskar su a turbune “Yau sai mun koya miki hankali! Sai mun nuna miki baki da mutunci munafukar yarinya wato kun haɗa baki da ubanki dan kiyi aure agidan kudi’ Momy ta faɗa tana nuna ni da hannunta.

Na tsaya ina kallonsu, ban motsa ba, ban kuma yi magana ba. Naui tunani nace “Idan kika yi magana yanzu, za su samu damar rufeki da duka da zagi.” Sai na yi shiru kawai.

Momy ta ƙaraso da sauri ta ɗauke ni da mari mai zafi. Kuncina ya ɗauki zafi wasu hawaye suka fara fitowa daga idanuna amma na share kawai ban yi magana ba. Zagin da suka dinga yimun bashida iyaka. Suka fara kirana da kalmomi marasa dadi harda karuwa harda wacce taci amanar ƴar uwarta.

Ban ɗaga baki na ce komai ba. Na tsaya ina share hawayena da hannu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull