Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 15
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 15: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 15. Sai dai kafin su ƙara wani abu, sai muka ji ƙarar murya daga bakin…
4,494 words
Sai dai kafin su ƙara wani abu, sai muka ji ƙarar murya daga bakin ƙofa. Abba ne ya shigo cikin hanzari. Idonsa ya sauka a kaina, ya ga kuka nakeyi, sai kuma ya kalli Momy da Bilkisu. “Me ke faruwa nan? Zainabu, me kike yi wa yarinyar nan? Bilkisu, ke ma? Wannan wane irin zalunci ne?” Abba ya faɗa cikin masifa.
Momy ta fara ihu tana cewa “Kai malam har kanada bakin magana? ka bar ni in yi mata duka. Wannan auren da kake so sai an yi a gabana. Na rantse da Allah ba zan yarda ba! Idan har aka yi auren nan, ni ce zan kashe shi. Ba zan bari a yi ba, wallahi ba zan bari ba!”
Sai ta ɗauki gyalenta sannan takara cewa “Idan har za ku daura wannan aure, to wallahi sai na hanashi ko kanaso ko bakaso Sai na tonawa gidan nan asiri. Sai na nuna wa duniya zaluncin da kuke yi min!”
Abba ya kalleta da takaici, ya girgiza kai ya ce “Zainabu, ba ki da imani wallahi. Duk abinda nayi ba ki taɓa godiya ba. Ni bani ne nacewa As'ad ga diyata ba da kansa yace yana sonta ko da akazo da maganar nazata bilkisu ce mai martaba yace ba ita ba ramlatu yake nemawa ɗiyarsa, amma ke kin mayar da shi abin masifa. To ki sani, aure sai an yi, kuma duk ihu da kika yi ba zai hana ba kuma wallahi ƙin bani mamaki munafurci da kike faɗin anyi miki ai kece babbar munafukar kanta..”
Ya juya ya kalle ni, ya ce cikin tausayi “Auta, tashi muje. Ba zan bar ki a hannun wannan matar ba. Tunda ba ta da imani, zata iya cutar da ke. Za mu tafi gidan Hajja Kaltum, can za ki zauna lafiya har sai lokacin aurenki yayi daga can sai gidan mijinki.”
Na yi ƙasa da kai na ce cikin hawaye “Abba, don Allah ka bar ni nan. Ban so in bar gidan nan momy bata fahimta baniba amma zata fahimta .”
Abba ya girgiza kai “A’a, Ramlah. Kin ga halin Zainabu. Ba zan iya barinki a hannunta ba. Ki shirya kawai mu tafi.”
Na share hawayena, na shiga ɗaki na ɗauki hijjab dina da akwati na. Na sanya kayayyakin da na san zan buƙata. Da na fito, sai na ga Abba ya riga ya kwashe kayan da aka kawo a matsayin kayan nagani inaso na aurena.
Ya kalle ni da murmushi mai ƙarfi, amma idanunsa sun nuna baƙin ciki. Ya ce “Auta, shiga motarki ki yi gaba. Zan biyo ki daga baya.”
Na ce “To, Abba.”
Ban kai ga shiga motar ba, sai Momy ta yi wani irin tsalle ta tare ni a ƙofa. Tana ihu tana cewa “Wallahi na rantse, wannan aure ba zai yiwu ba! Ko me za ku yi, ba zan bari ba. Idan kuwa kuka nace, wallahi sai na kawo karshen komai! Wannan aure tsantsar cin amana ne. Cin amana gare ni da diyata Bilkisu! Sai dai ku mutu da bakin cikin ku, amma wallahi ba zan bari ba!”
Abba ya yi kamar bai ji ta ba, ya wuce ya shiga motarsa. Ni ma na shiga tawa, zuciyata tana cike da takaici.
Na kalli Momy a bakin kofar gidan, na ce cikin zuciya “Ya Allah, wannan matar bata tsoronka. Kaine kawai mai iya maganinta wannan kiyayyar da takemun sama da shekaru ka tsareni daga sharrinta. Kaine mai iya bayyana adalci. Kaine mai kare ni daga sharri.”
Na tada motata muka bar gidan. Amma zuciyata ta cika da nauyin bakin ciki da zafin halin Momy, wanda ko kadan bata nuna tana tsoron Allah.
Ko da muka karasa gidan Hajja Kaltum, zuciyata cike da ɗan ƙaramin kwanciyar hankali ne. Ban daƙile hawaye ba, amma na yi ƙoƙarin boye damuwata saboda kar ta fahimci halin da nake ciki.
Na shiga gidan da sallama, sai jina yi an rungumeni Hajja Kaltum ce, mace mai kirki wacce tun ina ƙaramar yarinya ta nuna min ƙauna da tausayi. Na ji jikina ya saki a jikinta kamar uwa da ɗiya.
“Ƴata! Haka kika koma ?. Masha Allah! Kin koma sak mahaifiyarki wallahi kinsan bana kasar sama da shekara 8”
Ta zare hannayenta daga jikina ta kalle ni da murmushi. Amma na ga cikin idanunta akwai tambayoyi da yawa.
Na share idona cikin sanyi, na yi mata gaisuwa yadda ya dace. Ban ce komai ba. Sai kawai na haɗiye damuwata cikin zuciya.
A gefe kuwa sai ga Aliya, ɗiyarta kaɗai, wacce ta girme ni sosai. Ta fito da gudu daga ɗaki tana cewa “Ramlah! Daman kina nan ina tambayar abban ku amma yayi ta shareni 2week kadai mukayi da dawowa mun dawo nan gaba daya yanzu Ai Sannu da zuwa ƙanwata.”
Ta rungume ni kamar wata ‘yar uwa ta jini. Na yi murmushi, na ji nutsuwa. Ko da yake Aliya har yanzu bata yi aure ba, kasancewar tana tsananin karatun boko, amma ita mutum ce mai kirki da natsuwa, kuma yadda tayimun naji dadi sosai.
Bayan dan lokaci sai na ga Abba ya shigo cikin gidan. Ya zauna ya yi sallama da Hajja Kaltum. Bayan sun dan gaisa, sai ya fara magana da ita cikin natsuwa.
“Kaltum, na kawo miki Ramlah saboda ba zan iya barinta a hannun Zainabu ba. Kin san halin matar nan. Tun daga safe tana neman illata yarinyar nan gata nan ki aurar da'ita ki kaimun ita dakinta danAllah komai na barmiki hannunta duk abunda zaku bukata na biki kayan daki da komai da komai zan sakamiki 20m muga yadda zata kasance..”
Hajja ta girgiza kai, ta ce“Kai Yaya Malam, wannan ba sabon abu bane. Kasan tun farko na gaya maka, ka bar wannan yarinya a hannun kakanninta ko kuma a hannuna. Amma ka nace wai ga mahaifiyarta zainabu bayan nasan zainabu bazata taɓa ƙaunarta ba. To yau ga sakamakon banda auren wulakancin da tasanyaka kayiwa yarinyar nan. Wasu matan ai har abada basa son ‘ya’yan kishiyarsu. Zainabu kuma ma haka take.”
Na kalli Abba, na ga yadda ya yi shiru, yana girgiza kai da takaici. Na san maganar Hajja gaskiya ce, amma Abba mutum ne mai haƙuri sosai, shiyasa yake ƙoƙarin daidaita komai da kansa.
“To, Kaltum,” Abba ya ce cikin sauƙin murya, “duk yadda kike so ki rike Ramlah, rike ta. Ni ba na son sake ganin Zainabu ta ci zarafinta. Wannan yarinyar da kike gani tana da daraja sosai. Ina so ta samu kariya.”
Hajja ta ɗaga kai cikin kwarin gwiwa ta ce “Ka bar komai a hannuna, Yaya Malam. Ramlah tamkar jinin jikina ce. Zan rike ta da ƙauna da mutunci. Kuma duk wanda yake son tozarta ta, da yardar Allah ba zai taɓa cin nasara ba.”
Na kasa riƙe kaina, sai na fashe da kuka a jikinta. Ta shafa bayana tana cewa “Ƴata ki yi haƙuri. Wannan rayuwa haka take. Amma ki sani, babu wani abu da ya fi ƙarfin Allah. Ki tsaya da gaskiya, ki zauna da mutunci. Duk wanda ya yi miki sharri, to da yardar Allah sharri zai koma kansa.”
Abba ya yi ajiyar zuciya mai ƙarfi. Ya kalle ni ya ce “Auta, na san wannan abu yana da nauyi a gare ki. Amma ki tsaya da haƙuri. Ki tuna duk abinda Allah ya zaɓa mana shi ne mafi alkhairi. Ni kuma zan tsaya tsayin daka wajen kare ki.”
Na share hawayena, na ce cikin sanyin murya “Na gode, Abba. Allah ya saka da alkhairi.”
Sai Aliya ta taso da dariya ta ce “tashi mutafi dakina.” takira wata yar aikinsu tazo ta kwashe kayana.
Dukkanmu muka yi murmushi, sai na ji zuciyata ta dan lafa da natsuwa.
******
Momy ta zauna tana haki kamar wacce batada lafiya nan tsananin ɓacin rai ne. Idonta ya cika da bacin rai, zuciyarta na kukan baƙin ciki. Sai ta ɗaga wayarta ta kira Yakaka da gaggawa, muryarta cike da masifa.
“Wace irin magana ce kike yi, Yaƙaka?” in ji ta, tana sauke ajiyar zuciya da ƙarfi. “Yanzu kina nufin in kyale yarinyar nan? Wallahi, ko ke ba za ki iya shigar mini malamai ba. Ni zan je da kaina. Kin san wanda zai aure ta kuwa? Kin san kuɗinsa da matsayinsa a ƙasa da duniya? Saboda munafurcin ubanta shi ne zai zagaye ya ba wa danta dama. Ashe Ramlah za a ba, ba Bilkisu ba!”
Ta ƙara da zafi tana magana, kamar zuciyarta za ta fashe. “Yaƙaka, ki saurare ni ki kuma kiyayeni. Kin manta wacece yarinyar ki? Tana da tarihi na shaye-shaye fa. Kina nufin wannan mutumin zai taɓa kaunarta? Ki bar malamai, amma ki ji magana ta. Banda rashin wayo da rashin hankali, idan ni ce ke zan rungumeta, na kaunace ta wannan yarinyar, haihuwarta ne kaɗai ba ki yi ba. Ko da uwarta ta rasu, ke aka dan kawa tun tana tsumma To, menene na damuwa da ita? Na faɗa miki gaskiya ne, wallahi Allah na shiryu. Duk harkar bin malamai da kika ga nasaba to wallahi yanzu bazan kuma ba. Amma ki sani, idan ba ki tsaya kin ji tsoron Allah ba, Bilkisun da kike ɗora a zuciyarki itace za ta lalace saboda sharrin da kike aikawa ramlatu da shi. Nagayamiki gaskiya idan kin saurara kin gyara kanki idan kuma kina ganin hakan baiyi miki ba gaki ga rayuwar ai nidai na shiryu idan nashigo gari zan samu yarinyar nan na bata hakuri nakuma nemi yafiyarta.”
Momy Ta katse wayar a fusace, ta wurgar da ita gefe saboda abin ya ƙona mata rai. jikinta duk jijiyoyi sun tashi, zuciyarta cike da zafi..
Ba tare da ta sake wani tunani ba, ta tashi tsaye cikin hargowa, ta ɗauki mukullin motarta. Tana tsaye a bakin ƙofa ta saki wani irin nishi mai nauyi, sannan ta furta kalmomi da suka nuna bakin cikin da ke cikinta “da dai wani dan iskan ko talaka ramlatu xata aura to zan tsaya mata amma ina ganin zata shiga gidan hutu sosai da arzuki. Bata tsaya ba, ta fice da gaggawa. Da zarar ta isa waje, ta rufe ƙofar motar da ƙarfi, ta kunna injin da wani irin masifa, ta bar gidan tana buga sitiyari da hannu, kamar wacce duniya ta juya mata gaba ɗaya.
Nana hadiza
09030569336
[03/10, 10:17 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ARBA'IN
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Cikin fushi da tsananin hassada Momy tafita daga ciƙin gidan ta hau motarta wani mugun kuka tasaki cike da bakin ciki idan ta tuna ramlah ce zata aure As'ad sai ta sanya kuka sosai har da kara tana duƙan sutiyarin motan cike da bakin ciki da fushi sosai Ba ta koma gida ba sai ta nufi wajen da ta sani gidan boka da ke can cikin ƙauyen , wuri mai inuwa da hista na duhu, cike da hayaki da ƙamshi da mutane suka daina shiga a fili. Amma yau babu abin da zai hana ta tsallaka kowanne ƙofa na gurin.
A gefen titi, gidan bokan yake duk da can cikin kauye ne zata iya tunawa rabonta da zuwa sama da shekara 19 tun lokacin da malam zai auro mata uwar ramlatu bangon da aka sassaƙa da lambobi, ƙofofin itace da suka sha ruwan sama, da ƙananan tukwane a bakin ƙofa. Ta tsaya da motar ta, zuciyarta na bugawa sosai. Ta sauka, ta riƙe jakarta da hannu ɗaya, sai ta gangaro ƙasa ta nufi ƙofar. Cikin zuciyarta akwai tsoro, amma yadda take jinta babu abunda zai iya tsayar da'ita.
Boka ya fito daga cikin dakin bukar, fuskar sa a rufe da gyalle,Ya gaishe ta da salo na daban nasu mashurikai ya ce
“Kinzo lafiya. Me ya kawo ki nan, Zainabu? Shekaru sunja munyi miki aiki sosai.”
Momy ta tsaya a gaban sa, muryarta tana rawa “Boka, akwai babban abu dake shirin faruwa wanda zuciyata daf take fa tarwatsewa Ina bukatar taimakon ka wani abu ke kokarin faruwa. Yarinyar kishiyar nan tawa itace mahaifinta ya dauki wanda ƴata takeso zai bata. Idan ba a hana hakan ba, zuciyoyin mu zasu buga. Ina son ku hana auren ku dakatar da komai. Ku bani mafita.”
Boka ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya miƙa hannu ya taɓa gemunsa, ya duba ta daga kai har ƙasa. A cikin muryar sa mai laushi, ya ce: “Kin zo domin wata bukata mai nauyi sosai Wannan ba magana ce kawai ba aikine mai zaman kansa ko jefa mutum cikin hauka ko azaba. Idan kina so a jefe su dole a bi wata hanya da tabbacin cewa za ki bi sharuddan?
Momy ta kalli boka tare da idanuwan da suka cika da damuwa da masifa tace “Ina son waccan yarinyar tafasa aurensa gaba daya boka idan da hali kada akara maganar aurenta har abada ta mutu batayi aure ba. Ba zan bari a bata farin ciki ba. Ina shirye in yi duk abin da ya dace.”
Boka ya yi murmushi na mugunta, ya ce “Aikin zaizo da sharuda. Ba kowacce hanya ce zamuyi tasiri ba. Akwai hanyoyi da dama, amma abubuwan dana duba kowannen su yanada addu'a suna ambaton Allah suna karanta flaking da nasi ga ayatul kursiyu duk dare babu ta inda zamuyi galaba akansu . Amma akwai hanya guda da zata iya sa abin ya sauya a buƙaci wani abu mai daraja daga jikin wanda za a yi wa asiri. Jinin mutum yana daga cikin abubuwan da ke da ƙarfi sosai a irin wannan aiki. Idan aka kawo shi cikin niyyar hana aure, yana iya haifar da tasiri.”
Momy ta yi saurin ce, muryarta cike da ƙarfi da shirin “Me kake cewa? Jini boka? Yanzu ina zansamu jinin yarinyar nan mijin nawa ma yariga ya dauketa yabar gidan da'ita kuma inda yakaita wallahi bama shiri da matar ko kadan.
Boka ya ɗan gyada kai, idonsa yana zazzarewa. “Bazance miki komai ba ayanzu , Zainabu. Wannan aiki mai haɗari ne. Idan har za ki shiga, to dole ne ki san hadarin. Kuma dole ne ace jinin wanda za a yi wa asiri shi ake amfani da shi. Ba za a iya amfani da wani ko ɓangaren gani ba tana da alaƙa da dangantaka ta zahiri da ruhaniya. Idan ba za ki kawo tsantsar jinin nata ba, wannan aikin ba zai yi tasiri ba. Amma ko da hakan, akwai sauran sharudda ƙudurci, tsarkakewa, da biyan wasu buƙatu da ba zan iya faɗa a fili ba.”
A wannan lokacin, zuciyar Momy ta dinga zugata sosai akan kawai ta yarda duk da hadarin aikin ya gayamata zai iya komawa gurin yarta amma yadda momy take kaunar a nakasa ramlah ya rufe mata idanuwa tunawa da yadda suka kawo dukiya da kuma bakin cikin da bilkisu take ciki da kuma irin arzukin da ramlah zata shiga. Sai kawai tace “To, zan kawo jinin.amma inaso ka tabbatar mun cewa bayan wannan komai zai lallace bazata kuma aure na har abada.
Boka ya jinjina kai, kamar mai sanin abin da zuciyarta “Aiki yana tare da sakamako. Kuma duk abin da ya shafi jinin mutane yana da tsarki da tsanani a fuskar ruhaniya. Zan iya yin aikin, amma ba zan taba ba da tabbacin cewa babu illa ba. Kowanne abu yana da sakamako a duniya da bayan duniya. Ki yi tunani sosai, Zainabu. Ki je gida ki zauna, ki yanke shawara. Idan kika amince, ki dawo da niyyarki sosai, kuma ki kawo abin da ake nema. Ni a matsayina na mai aiki, zan bi sharuddan aikin, amma kin sani abin da ke tafe bayan haka babu ruwana aiki zai iya wadawa ƙanki kokuma diyarki idan bai hau ƙansu ba.”
Momy ta tsaya, zuciyarta cike da rudani. Abu biyu tasanya a gaba daya shi ne damar hana auren da take buri, ɗayan kuma shi ne hadarin jefa kanta da ƴarta Amma ƙishin ganin Burin Bilkisu ya cika ya ci nasara fiye da tsoron illar. Ta ɗan yi shiru, sai ta ce da “To, zan dawo. Zan kawo abin da ka ce. Amma ka tabbatar min ka yi komai cikin sauri. Kada a bari wani abu ya riga mu.”
Ta bar gidan boka tana tafiya cikin dare, motarta tana ƙara gudu a titi. Zuciyarta ciki da damuwa da baƙin ciki.
***
Da daddare muna zaune ni da Yaya Aliya a dining table, muna cin abincin dare cikin natsuwa. Hasken fitilar dakin yana sauka a kan fuskar ta mai cike da fara’a. Da murmushi ta kalle ni tace “Ramlah, gobe fa masu gyaran jiki za su fara zuwa, inji Mom. Ki zama cikin shiri. Amma dai ni ban ga angonki ya kiraki ba har yanzu. Ko kuwa kina boyewa ne bakyason nagani kina waya?”
Na saki murmushi kawai, ban ce komai ba. Ban san yadda zan fara bayanin damuwata gareta ba. Sai kawai na cigaba da wasa da cokali a cikin plate ɗina.
Ta ja numfashi, ta ɗan matsa kusa da ni, ta ce “Haba sis, kidaina min shiru. Ni fa ki ɗaukeni kamar ƴar uwarki, ki bani labarinsa mana. Kinga ni ma fa biki nake shiryawa next month in sha Allah. Ke baki ga yadda nake ta waya da angona ba? Ni ma ina so in ji labarin ki. Ki bani kaɗan, kada ki rufe min zuciyarki ki daukeni tamkara ciki daya muke.”
Na ɗan yi shiru na wani lokaci. Sai na ji zuciyata ta kwanta da'ita kamar ta bani dama ta san damuwata. Na saki ajiyar zuciya sannan na ce “To ai sis, gaskiya bansan shi ba. Ance babansa ne ya nema min aure. Ni kaina, sau biyu kawai na taɓa ganin sa. Kuma ma, ba ni da masaniyar halinsa ko yadda yake. Ga shi kuma Yaya Bilkisu ce take son shi sosai kin ga yadda zuciyarta ke ƙonewa akan shi. Ni kuwa haka kawai aka zabe ni batare da nasan dalili ba ni wallahi tsoro ma nakeji sis gidan sarauta kuma ana ambatar mai kudi nidaman yaya bilkisun aka basa.”
Na yi shiru, zuciyata ta yi nauyi sosai da maganar. Amma Yaya Aliya ta kalle ni da murmushi mai taushi, ta girgiza kai tace “Ramlah, yanzu dai tunda ba ita ya nema ba, ki daina kawo sunanta anan. Ango ke yake so, ke ya nema a gaban iyayensa. Wannan shi ne babban abu. Ki kwantar da hankalinki. Ki saki jikinki. Ki amince kiyiwa kanki fatan alkhairi ko me su bilkisu da momynta zasuyi kada ki damuwa tsananin bakin ciki suke miki wallahi. Soyayya fa da dadi idan kika fara za ki gane.”
Na yi murmushi, amma murmushin da ya fito daga zuciyar da ke cike da tunani. A raina, sai na tuna lokacin Bashari mutumin da ya taɓa cika rayuwata da dariya da motsin zuciya. Mutumin da ya saba kirana ƴar kwalisa duk lokacin da na sa kaya masu kyau. Na tuna murya da idonsa, na ji zuciyata ta yi wani irin nauyi, kamar an cusa min raɗaɗin da bai taɓa wucewa ba.
Na ɗan lumshe ido, na ce a hankali cikin zuciyata “ Ya Allah na, Ka bani ikon karɓar wannan sabon al’amari. Ka bani ƙarfin zuciya in bar baya, in rungumi gaba.”
Yaya Aliya bata lura da tsananin damuwata ba, sai ta ci gaba da cin abinci tana kwasar labarin yadda ta ke shirin bikin nata. Ni kuma sai na zauna ina murmushi, ina amsawa da kai kawai, amma zuciyata na can nesa tsakanin tsohon tarihin Bashari da sabuwar makomar da ake tura ni cikinta.
Nana hadiza
09030569336
[05/10, 8:59 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ARBA'IN DA DAYA
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Bilkisu tana yawo sama da ƙasa, tana tura hanci kamar wacce aka ci amanarta. Idonta ya kumbura saboda kuka, amma duk da haka ta matsa gaban Momy tana wani irin shassheƙar kuka mai ban tausayi.
“Momy, kina kallo za a aurawa Ramlah As’ad? Momy, na dade da keɓe zuciyata da sonshi. Wallahi tun ina ƙuruciya nake zuwa gidansa, nake jin zuciyata ta kamu da shi. Na boye wannan damuwa saboda Nawal da Mamansu nasan bazata taba bari na na auresa ba kuma kema dana gayamiki haka kikace bazaki iya karawa da ayshatu ba , amma yau Momy ace ramlah ce zata aure sa? zuciyata kamar ta fashe. Me yasa Ramlah? Me yasa ita za ta aure shi? Ni ce fa na fi cancanta, ni ce nake mutuwar sonshi. Momy, na dade ina mafarkin wannan rana. Kin ga wannan invitation ɗin da suka rarraba? Wayyo Allah na!”
Sai ta fasa kuka kamar ranta zai fita.
Momy kuwa ta ɗaga kai daga kujerar da take zaune, ta tsaya cak tana kallon Bilkisu sama da ƙasa, kamar tana tantance ta. Hancin ta ya ɗan yi ja ga idanu wanta zun kumbura sosai.
“Au, Bilkisu, ke kinada bakin magana har kike iya zuwa gabana kina cewa kina son As’ad? Dan ubanki, nace kina da bakin magana? Kin manta shaye-shayen da kika ringa yi? Kin manta rayuwarki ta lalace saboda bin kawayen banza da bin malamai? Da baki shiga wannan hanyar banza ba, da kin cancanci kaunarsa. Ai da ke As’ad ya zaba, ba ita ba! Amma yanzu kin zauna kina waƙar soyayya? Ai da nafi sanin kin lalata jikinki fiye da yadda zan iya sake miki magana. Uban wanne mai hankali zai ce yana sonki, bayan duk wannan bala’in da kika jawo? Naga har dan shaye shaye na haɗa ramlatu dashi amma ance bata taba sha ba sai ma sanadiyar shiriyarsa da tazama ke ko kunya bakyaji?.” atake momy tai mata wani irin kallo mai haɗe da ɓacin rai.
“Kin ja min abin kunya, Bilkisu. Kanwarki za ta yi aure a karo na biyu, ke kuma har yanzu kina nan, babu aure, babu mutunci. In banda Allah ya taimake ni na aurar da su Usman da Abbas, ai da bakin cikj dai ya kasusan kasheni. Amma wallahi, duk da wannan ɓacin ran da kika bani, zan sake baki dama. Amma ki sani wannan auren Ramlah ba zai taba tabbata. Yanzu dole ke xakiyi mana aikin.”
Bilkisu ta zabura, tana rarrabe hannu cikin kuka mai tsanani “Momy, ko menene zai faru, koda kashe Ramlah ne, zan yi. Idan har wannan auren za’a fasashi, to na fi son mutuwarta kafin ranar. Momy, wallahi bazan iya jurewa ba. Wannan soyayya ta cika ni har ta wuce ƙima. Na rantse, bazan zauna ba tare da shi ba.”
Sai Momy ta saki wani irin mugun murmushi, ta ɗan ɗaga hannayenta kamar tana jin nasara, ta ce “Shiyasa nake sonki, Bilkisu. Duk da lalacewarki, kina da ƙarfin zuciyar yin duk abin da ake so. Kin san jiya na je wajen boka? Na gaya masa duk wannan magana. Na roƙe shi ya toshe hanyar auren nan. Ya ce za a iya, amma akwai sharadi guda ɗaya. Sai an samu jinin Ramlah. Wannan aikin ba zai yiwu ba sai da jinin jikinta. Kuma kinsan tana cikin al’ada cikin kwana biyu zatayi wanka indai lissafina dai dai ne. Dole ne ki daure, ki yi makirci, ki samu pad ɗinta, mu kai masa. Idan hakan ya tabbata, za mu iya toshe auren nan har abada.”
Momy ta ɗan ja numfashi, ta cigaba da magana cike da makirci “Da ace tana nan gidan nan, ai da duk wannan aikin zai fi sauƙi. Amma yanzu mahaifinki ya mayar da ita wajen Hajja Kaltume. Ba zai yarda ta dawo nan ba. To amma ke Bilkisu, dole ki yi amfani da dabara. Za ki tafi gidan Hajja Kaltume, ki yi kamar baki da wata matsala. Ki yi mata magana mai taushi, ki ce kin yi nadama, ki roƙe ta ta yafemiki. Ki nuna alhini, karki bari ta ji shakku. Idan kika samu wannan damar, ki zauna da ita har dare, idan ya kama ki kwana a can. Sai ki yi amfani da wannan dama ki ɗauko pad ɗinta ki kawo mana. Kin ji ko?”
Bilkisu ta share hawayenta da hannayenta, ta ɗan saki murmushi cikin kuka, tace “Momy, na gode sosai. Na gode wallahi. Anjima zan shirya zan je gidan Hajja Kaltume. Zan yi yadda kika ce. In sha Allah, wannan aure ba zai taba tsayuwa ba. Ni ce kawai zan kasance matar As’ad, ba Ramlah ba. Wallahi, zan ɗauki matakin da ya dace,Momy, na rantse, wannan aikin zan yi shi da hannuna.”
Sai Momy ta matsa kusa da ita, ta dafa kafadarta, ta ce “Haka nake so, Bilkisu. Kada ki sake ki nuna rauni. Kada ki bari zuciyarki ta nuna tsoron abin da za ki aikata. Ki tabbata cewa ke ce mace ta gari idan kika tabbatar kika hana wannan aure. Ni zan tsaya a bayanki, ni zan kula da komai. Idan kika kawo min pad ɗinta, zan tafi da shi wajen boka, a ranar nan nan, sai a rufe dukkan hanyoyin da ke tsakanin Ramlah da As’ad. Wannan aure zai mutu kafin ya rayu.”
Sai ta saki dariya mai ban tsoro, dariya irin ta mai shirin aikata mugun aiki. Bilkisu ta saki ajiyar zuciya, ta share hawayenta gaba ɗaya, ta ce “Momy, ki kwantar da hankalinki. Idan har wannan shine aikin da zai hana Ramlah aure da shi, to zan yi shi. Zan je gidan Hajja Kaltume, zan shiga tsakaninta da ita. Zan yi wasa da ita, zan nuna kamar babu komai. Zan kuma kwana idan ya zama dole. A ƙarshe zan kawo miki abin da kika ce. Ki barni, ni zan gyara miki komai. Ni zan tabbatar da cewa aurenta da As’ad zai zama tarihi mara amfani.” Sai ta nufi ɗakinta, zuciyarta cike da kishi, ƙiyayya da shirin mugunta.
******
Daren nan, bayan mungama girki nida yaya aliya da mom, na fito daga ɗaki zuciyata cike da damuwa. Na zauna a tsakar gida ina kallon sararin sama. Wani sanyi na iska yana kadawa, ga hasken wata yana walwala sama. Duk da wannan natsuwa ta dare, zuciyata ba ta samun kwanciyar hankali. Kalaman momy, zagin Bilkisu, da kuma tarin abubuwan da suka faru cikin ‘yan kwanakin nan sun tattare a kwakwalwata.
Sai kawai naga Hajja Kaltume ta fito daga ɗakinta tana riƙe da tasbihinta. Ta tsaya tana kallona, sai ta yi murmushi wanda yake da cike da tausayawa da kauna. Tana matsowa kusa dani ta ce “Ramlahtu, yarinyata, bar wannan tunanin da kike yi. Kin san ni kam ban fiye son ganin ki cikin damuwa ba. Zo nan, ki zauna kusa da ni.”
Na matsa kusa da ita na zauna, sai na fashe da kuka. Ta riƙe hannuna a nata hannun tana shafa min bayana. “Bar kukan nan Ramlah,” inji Hajja Kaltume cikin sanyin murya. “Na ji dukkan labarin abinda ya faru. Nasan halin Zainabu sosai. Nasan abubuwan da take iya yi da kuma wanda ba ta iya yi, saboda shakuwata da ita tun kafin ma ku girma. Kar ki damu. Wannan shi ne ƙaddarar ki. Wannan shi ne jarabawar ki.”