Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 16

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 16

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 16: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 16. Na share hawayena da bayan hannuna, amma zuciyata har yanzu cike…

4,500 words

Na share hawayena da bayan hannuna, amma zuciyata har yanzu cike take da tambayoyi. “Hajja, me yasa duk wannan ke faruwa da ni? Me yasa momy ta tsane ni haka, har ta ke mun fatan mutuwa banyi aure ba? Me na yi mata?”

Hajja ta yi murmushi ta girgiza kai.

“Ki saurare ni yarinyata. Allah yana jarabar wanda yake so. Ki tuna, duk wata jarabawa da take zuwa ga bawa, idan ya yi hakuri to lada mai yawa ne yake jira a gaban Ubangiji. Ke dai ki yi hakuri. Ki san ko waccan auren da suka yi miki ba da yardarki ba? Kin ga yadda Allah ya juya miki shi ya zama alheri. Kin samu darasi, kin samu nutsuwa, kin kuma fahimci rayuwa sosai. Wannan shi ne alamar cewa Allah yana tare da ke.”

Na sunkuyar da kaina ina share hawayena. Hajja ta cigaba “Na san halin Zainabu sosai. Idan ta tafi wajen malaman ta, zata kara karasowa kokuma zata kara zuwa zance miki ko ta turo yarinyarta, kada ki damu. Duk maganganunsu na banza ne. Abinda ya kamata ki yi shi ne ki dage da addu’a. Kada ki yi kasa a gwiwa. Ki zauna dakinki da addu’a. Karki sake ki fadi sirrinki. Kin ji? Inshaa Allahu, babu abin da zai same ki illa alheri.”

Na ce mata cikin murya mai rauni “To Hajja, amma ina jin tsoro sosai. Ga Bilkisu tana zagina kullum. Ga momy tana yi min kallon tsana duk soyayyar danake ganjn tabani jna karama ashe kiyayyace. Na rasa yadda zan yi.”

Ta ɗan yi dariya ta ce “Ke dai ki saki jikinki. Kada ki bari tsoron su ya cinye ki. Aurenki yana gab da faruwa, ki mai da hankali wajen addu’a da kuma shirye-shiryenki. Kin san fa auren nan mai daraja ne, kuma kin san shi aure ne gatan macce. Ki godewa Allah da wannan dama da kika samu. Kada ki dubi Bilkisu. Zagin ta ba zai rage miki daraja ba. A zahiri, zagin da suke yi miki na nuna cewa sun kasa daurewa ganin irin alherin da Allah yake yi miki.”

Na ɗan yi shiru ina jin kalamanta suna shiga zuciyata. Wani natsuwa na fara shiga jikina, kamar ana cire wani nauyi daga zuciyata.

“Hajja, na gode. Kalaman ki sun sanyaya min rai sosai. Allah ya saka da alheri.”

Ta riƙe hannuna sosai ta ce “Ki dai dage da addu’a. Kin san addu’a ita ce makamin musulmi. Ki karanta Al-Falaq, An-Nas, Ayatul Kursiyyu, ki ringa shafesu kafin bacci. Kuma kikara rike zikirin safiya da yamma inshaa Allahu bazaki taɓa danasani ba. Ki riƙa roƙon Allah ya kare ki daga sharrin makiya. Inshaa Allahu, zaki ga yadda Allah zaiyi dasu babban gida xaki shiga bakisan yanayin tsarin ba gidan sarauta akwai fitintinu kala kala dole sai kin dage wanda zaki aura ba karamun mutum baniba.”

Nana hadiza

09030569336

[07/10, 8:21 am] Deejarh b YCG2: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

wasu manyan mata suka shigo da kayan su cikin ɗakin da jakunkuna, ƙananan kwanduna da aka cika da turare, wasu na sansu wasu kuma ban sansu ba Sun yi sallama fuskarsu cike da murmushi sunata kallona samun guri sukayi suka zauna suna gaisawa da mom bayan sungama sukace “ a’a hajjaju daman yaran naki guda biyu ne?” Mom ce tayi dariya tace kunga muna kama ko? Itama yarinya tace.” kai mashaa Allah hajjaju yarinki so mashaa Allah kuma sai yanzu naga kamarsu da Aliya.bari mufara ko

Yau zamu fara da tsaftar jiki gaba ɗaya. Wannan gyara na gargajiya ne domin ki samu haske, kuma jikinki yakara laushi kikara kyau.”

“Yanzu zamu fara da haɗa Wankan kurkum.”

Ina daga gefe ina kallon su Suka fara hada kurkum da ruwan zuma da madara. An nannade ni da wannan hadin, suka shafa a dukkan jikina. Naji tana cewa shi wannan Kurkum din yana tsabtace fata, yana cire datti, ya kuma sa fata ta yi sheki sosai

Na zauna taɗe cikin ɗan mayafi, har sai ya bushe, sannan suka wanke ni da ruwan ɗumi mai ƙamshin ganyen magarya. Wannan ruwan ya ƙara tsaftace fata ya sa ni jin sanyi a jiki sosai ni tunda nake bantaba kokarin gyara jikina ba. Sannan tacemun mamanki tacemun ƙintaba aure dan haka dole ne kisha wannan matsin ta mikomun ruwan da aka dafa kanunfari da habbatussauda. Tace shi zantasha har tsahon sati. Sun ce wannan yana ƙara ƙarfi ga mace, yana kuma taimaka wajen tsaftar ciki. An ba ni na sha kadan, sannan suka ba ni na tsugunna kan tururin ruwan. Wannan tururi ya shiga jikina, ya ba ni nutsuwa da sauƙin numfashi sai naji har wani sakayau naji ajikina. Daga nan suka kawo ƙaramin roba mai ɗauke da humra suka shafa a saman fata, musamman a wuraren da aka fi buƙata (hannuwa, wuya, kafaɗa). Sun gauraya shi da ɗan subulussalam domin ƙarin ƙanshi mai ɗaukar hankali. Jikina ya cika da ƙamshi mai laushi, wanda yake shiga zuciya har sai na ji ina dadi da kaina. Bayan turaren, suka ɗauko man zaitun da man hulba.

Suka yi min tausa a hannu da ƙafa, har zuwa baya. Wannan tausa ta sa na ji ƙashin jikina sun sake, Fata ta kuma tayi sheki da laushi fiye da da.

Sai suka ɗauko ƙananan leda tace mun

“Wannan gyara ne na musamman ga amarya.” A ciki akwai hadin ganyen hulba, man habbatussauda da garin citta. Sun ce ana shan ɗan ƙaramin cokali da ruwan zafi da safe. Murmushi nadinga yi dan duk yadda nake ganin inada kyau yanzu gyaran nan da akayimun sai naga nakara kyau sosai. Yaya Aliya da take gefe ta ce “Wallahi Ramlah, kin canza gaba ɗaya. Idan As’ad ya ganki haka, sai ya rude.” Na yi murmushi kawai na sunkuyar da kai, zuciyata na bugawa cikin jin kunya, ni wallahi tsoron Auren nan mutumin da bansan shi ba dan sarauta mai kudi ina ni inashi kallo su kawai nakeyi wallahi amma am afraid wallahi.

*****

Zuciyar Abba cike take da tunani. Bai taɓa zaton matar da ya ɗauka da soyayya da amana zata nuna irin wannan hali ba. Duk da haka, sai ya zauna a falonsa yana kallon jaridar hannunsa, zuciyarsa na dudduba abubuwa.

Cikin hanzari sai ga Momy ta sauko daga sama, fuskarta a kumbure saboda kuka. Da ƙarfi ta ce “Yanzu, Abban Ramlah, wannan uwar dukiyar zaka kashewa Ramlah? Dukiya da aka tara da wuya? Ina Usman? Ina Abbas? Su kabasu su ja jari mana ace har gida biyu zaka cikawa yarinya tun yanzu zaka fara nuna musu rashin adalci?”

Abba ya ɗago idonsa a hankali, ya kalleta cike da mamaki da takaici. Sai kawai ya sakar mata murmushi mai ɗauke da zafi da rashin yarda. “Zainabu,” ya ce cikin nutsuwa, “kin san ba don halinki Allah ya bayyana mun ba da sai nace bantaba ganin macce mai sharri makira kuma mara imani irinki ba okay dayake ba diyarki bace ba, to banda abunki ke kike nemar mun kudin? Amma bari na faɗa miki gaskiya Ba ni kaɗai ba na hada wannan kuɗin. Gudummawar yara nake haɗawa. Usman ya ba ni miliyan 7, Abbas miliyan 5, ƙannina kuma miliyan 10. Su kaɗai suka ɗauki nauyin wannan shagalin. Hamza ma yace shi zai kula da gidan a babban birni. Sun riga sun bamu mukullin bangaren da ake kammalawa cikin kwanaki uku. Zuwa jibi za mu tafi mu duba komai.”

Ya lumshe idonsa yana sauke numfashi, sai ya ci gaba “Kin gani? Ba wai dukiya ta kaɗai ba ko duk abunda na mallaka ce zan kashe mata ba ni da haufi akan aura.” Momy ta zuba masa ido, jikinta na rawa saboda takaici. Wani irin bakin ciki ya lullube ta, zuciyarta kamar za ta fashe. Sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin

“Amma Abban auta… ka cutar da ni! Wallahi ka zalunce ni! Ga Bilkisu nan, ga yarinyata nan tana mutuwar son As’ad, amma ka mayar da hankali kan Ramlah. Naga tawa yarinyar itace babba ita yakamata ka aura mata shi. Wannan ai cuta ce da zalunci! Wallahi an zalunci ne!”

Ta rufe fuskarta da hannu tana rusa kuka.

Abba ya kalleta da wani irin kallo na takaici. Idanunsa sun nuna alamar haƙuri ya ƙare, zuciyarsa ta gaji da fitinarta. Sai ya miƙe a hankali, ya ɗaga yatsarsa yana nuna mata, sannan ya ce da ƙarfi cikin murya mai nauyi

“Zainabu! Ki saurare ni da kyau. Idan baki gyara bakinki ba, idan baki koyi mutunci da kunya ba, wallahi sai na hukuntaki sha sha. Na gaji da halinki nayi haƙuri da halinki tsawon shekaru, amma yanzu kina kai ni bango zan hukunta ki wallahi, ke wai bakya tsoron Allah ne? Ke ko kunya bakyaji? To ki kiyaye! Wani abu ɗaya ne zai hanani rabuwa dake yaran da muka haifa tare. Amma idan kika kai ni bango, wallahi wallahi sai kin gane baki da wayo.”

Ya tsaya yana huci, yana kallonta da idanun da suka cika da bacin rai.

Momy ta saki hannayenta daga fuskarta tana kallonsa da wani irin yanayi. Tana son magana amma harshenta ya tsaya cak saboda tsoron kalamansa. Idanunta suka ƙara cika da hawaye, sai ta fashe da kuka mai ƙarfi, tana jijjiga jikinta.

Abba bai sake ce mata komai ba. Ya ɗauki mukullin motarsa ya nufi waje. A zuciyarsa ya ce “Ni fa bana jin tsoron komai sai Allah. Amma matar nan zata iya haddasa fitinar da bazan iya kashewa ba kwata kwata zainabu bata tsoron Allah son zuciyar da daban yake.”

Momy ta bishi da kallo har ya fice. Sai kawai ta nufi sama da sauri, tana tafe tana huci, tana jin kamar zuciyarta zata buga saboda ɓacin rai. A cikin ɗakinta ta jefa kanta kan gado, ta rufe kanta da bargo, tana kuka cike da ƙiyayya da kishi. “Wallahi,” tace a ranta, “ba zan taɓa barin wannan aure ya tafi lafiya ba. In dai ni ce Zainabu, sai na tabbatar Ramlah ta fuskanci abin da bata taɓa zato ba. Koda kuwa zan zubar da hawaye, zan je wurin boka, zan nemi malamai, zan tafi ko ina.!”

Sai ta sake fashewa da kuka, tana jijjiga kanta kamar wacce ta rasa hankali.

A can gefe kuma, Abba yana mota yana tafiya cikin dare, zuciyarsa cike da tunani. Amma duk da haka, ya san Allah ne ke tsara komai. Ya san shi dai ya ɗauki matsayin adalci, bai cutar da kowa ba. Sai ya furta da zuciyarsa “Ya Allah ka rufa asiri, ka kare Ramlah da duk yaran nan. Ka sa zaman lafiya ya zauna a gidan nan. Ka kawar da sharrin zuciya da hassada.”

Cikin masifa momy ta faɗa dakin bilkisu tana kwance ta bararraje “ Dan ubanki shige kije ki samomana abunda muke bukata kamin zuciyata ta buga bilkisu da itama idonta ya kumbura tace mata to ta fita.zuwa gidan hajja kaltum domin samo jinin ramlah na al'ada.

*****

Muna zaune a babban palon gidan, lokacin da muka ji ƙarar ƙofa sai ga Bilkisu ta shigo tana kuka tun daga bakin ƙofa. Koda ta shigo, tana ta faman ihu kamar ranta zai fita. Ni kuwa ban ma kalle ta ba saboda zuciyata cike take da abin da ya faru a kwanakin baya.

Mom ta ɗaga kai ta kalle ta, idanuwanta sun kan kance sabida fushin ganin bilkisu ta mike ta nunata da hannu tace

Nana hadiza

09030569336

[09/10, 7:36 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA UKU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

“Kada ki soma shigomun cikin gidana ki koma inda kika fito fitsararriya ko kin manta rashin kunyar da kikayimun da dadewa? Kin manta cin mutuncin da kuka yi mini ni ke da uwarki?”

Bilkisu ta tsaya a bakin ƙofa tana cigaba da kuka sosai ga rawa a muryarta. Ta ƙwantar da numfashi, ta miƙa hannu tana roƙon yafiya kamar yadda yan india suke “Yaya, Mom, na tuba. Don Allah ki yafe min, na zo ne in nemi yafiyar ƙanwata. Na yi kuskure, na tuba.”

Momy ta ɗaga murya cikin tsawa “Ko ki fita ko in kori ki! Ke har kinsan haka?, mara tarbiya! Wannan gidan nawa ba gidan ku baniba da zakizo kiyimun rashin kumya nagayamiki maza mazq ki barmun gida kamin na saɓa miki.”

Bilkisu ta fusata sannan sai ta juya ta fita daga gidan da kuka. Momy tace da ni da Aliya” kuyi maza ku tashi, Aliya, ku bita da sauri kada tazo ta zazzaga mana wani tsafin nasu nasan halin uwarta wallahi ba dan Allah taxo gidan nan ba tanada manufarta.”

Muka tashi muka bi bayan ta, Amma bamu ganta ba muka kalli baba mai gadi muke tambayarsa ina bilkisu take yake gayamana bata fito ba hakan ya sanya yaya aliya hanzarin yin bayan gidan ai kuwa muka tarar da ita ta zazzage shara gaba daya akasa tasanya leda a hannunta tanata faman tonewa. Na tsaya cikin mamaki, zuciyata cike da tsoto Wacce irin masifa ce wannan? Wacce irin ƙiyayya suke nunawa haka?

Tana ganin mu yaya aliya tace mata mekikeyi a sharar mu sai ta sanya gudu tabar gate din aguje muka bi bayanta.

Mumy dataji muna salati ta fito tace “Na san halin Zainabu sosai wannan kadan daga aikinta ilau wani abun boka ya bukata shine tazo zata dauka yanzu da ace na barta ta zauna sai kunyi miki illar da Allah kadai yasan lokacin da zata tsaya ubangiji Allah yakareki Ramlah ko dan waƴannan da sabuwar rayuwar da zaki shiga ai kimga babu ke babu wasa da addua.”

Ina kallon momy ta kira masu gadi ta gargade su “Ku sani, duk wacce za ta shigo sai ansanar dani kada akara barin wani ko wata tashigo bada izinina ba.”

Masu gadin suka amsa cikin ladabi “To, Hajiya.”

Ina kokarin fashewa da kuka sai mom ta kalleni tace kada ki soma kukan nan ramlatu dole kizama jaruma ba komai ne ake kuka ba dole ki iya dakiya da dauriya kizama jarumar gaske kinjini amma kuka baya magani sai dai yasanya ciwo ki dage da addu’a dai babu wasa kinji shige muke yarinyar kirki yar albarkat tagama nasara akanki inshaa Allahu.

*****

Zaune yake a babban ofishinsa mai kyan gaske daya daga ciƙin office din dake kasar da yafi gudanar da kasuwancin sa wato dubai kallon bangon kadai ya isa ka fahimci attajirinr na gaske wasu haɗaddun gilashin tagogi na kewayen ɗakin suna haskawa da hasken rana, wata kujera ce yake zaune datake motsawa dashina hankali a gaban teburin As’ad an baza wasu takardu masu muhimmanci kwangiloli, yarjejeniyoyi da suka shafi kamfaninsa. Hannunsa ɗaya ya daura a kan tebur, ɗayan kuma yana juyawa da alƙalami yana sa hannu a jere, cikin salo irin na mutum mai natsuwa da kamun kai.

Kallonsa Alhaji Osama yake yana murmushi ɗaya daga cikin manyan abokansa kuma abokin hulɗa a kasuwanci, ya gyara zamansa a kan kujera yana kallon sa. Sai ya ɗan yi gyaran murya ya ce

“Young billionaire… kana ganin wannan yarinyar da ka ɗauko don aure babu wata matsala kuwa? Kasan irin yaran zamani. Ka gani dai yadda Ayshatu ta auri Alhaji Muqaddam, wanda hakan bakaramun taɓa ka yayi ba harma damu . Kai dai san na sanka, baka da ra’ayin bin mata ko shiga harkokin banza, kai mutum ne mai natsuwa tun muna yara ka bambanta da mutane dayawa wanda zan iya cewa Allah ne yake tsare maka imaninka Amma nasan kai ba kasan abubuwan da ke gudana yanzu a tsakanin matan zamani ba. Wasu har bin ‘yan uwansu mata suke yi, wasu kuma suna shaye-shaye. Shi yasa nake son ka kula sosai. Ka bincika yarinyar kafin ka yi babban kuskure nasan gidan sarauta suna bincike sosai kuma kaima mai arzuki ne da kome zaka iya sani kanta.”

As’ad ya ɗaga kai daga rubutunsa ya kalli Alhaji Osama da idanuwansa masu zurfi. A fuskar sa babu wata alamar damuwa, sai murmushi mai sanyi wanda yake da wani irin ƙarfin hali.

—“Aboki,” in ji shi cikin muryarsa mai nutsuwa, “ka kwantar da hankalinka. Nariga na bincika yarinyar. Na san asalinta. Na san tarbiyyarta. Na san darajar mahaifinta. Na kuma san inda take tafiya da inda bata tafiya. Babu wata damuwa, maganar ayshatu kuma nagayamaka bana son ko sunanta gurina please take note.”

Alhaji Osama ya ɗan ɗaga gira cikin shakku ya ce “Ni kuwa nake da damuwa. Indai yar gidan Kabiru ce kamar yadda ka faɗa min, to ka sani yarinya ce mai shaye-shaye. Na san labarinta tun can baya, tana bin maza, tana fita da ‘yan iska. Ni da kaina nasan irin halayenta. Na santa farin sani da kake ji da ba tataba zama gidanka ba? amma…”

Kafin ya ƙarasa, As’ad ya ɗan ɗaga hannunsa alamar ya isa. Wani murmushi mai ɗauke da ƙarfin zuciya ya bayyana a fuskar sa.

“Osama… kada ka dogara da jita-jita. Duniya ce mai cike da maganganu. Duk lokacin da Allah Ya so ya ɗaukaka bawa, mutane za su fito da ƙarya da sharri. Na gwada ta. Na saurari zuciyata. Na kuma gayawa Allah. Wacce kasani ba ita bace ba Abinda nake fata shi ne Allah Ya shiryar da ita, Ya kuma tabbatar mana da zuri’ar mu kan daidai osama komai dabarar bawa bayayiwa Allah wayo Ina rokon Allah yabani maccen kwarai.”

Ya ɗan lumshe idanu yana sauke numfashi a hankali, sannan ya buɗe su da murmushi. “Ni ban taba tsoron aure ba, aboki. Tsoron da nake dashi shi ne na rasa mace da take da gaskiya a zuciyarta. Wannan yarinyar, na yarda da ita. Kuma zan riƙe ta a matsayin amana.”

Alhaji Osama ya jingina da kujera, ya girgiza kai alamar mamaki. Sai ya ce “Wallahi kai ba ka canzawa. Ko da yake na yarda kai mutum ne mai hangen nesa. Allah ya tabbatar maka da alkhairi, As’ad. Lamarin matan ne sai addua.”

As’ad ya ɗaga kai sama, idanuwansa suka tsaya a gilashin taga inda ake iya ganin birnin gaba ɗaya. “Eh, duniya ba ta da sauƙi. Amma zuciyar mutum idan ta tsarkaka, duk tsananin duniya, Allah yana sauƙaƙa masa. Ni ban dogara da mutane ba, Osama. Na dogara ga Allah. Kuma na san wannan zabin shine alkhairi gare ni inshaa Allahu.”

Ƙarshe, ya sanya hannu a kan kwangilar da ke gabansa cikin salo, ya miƙa ta ga Osama.

“Yanzu ka kwantar da hankalinka. Ka ga aikin nan mun kammala. Aure kuwa… abinda Allah ya rubuta, babu mai iya hanawa.”

Alhaji Osama bai daina magana ba sai ya ce “To amma duk da haka, ranka ya daɗe, ya kamata ka ƙara bincike akanta sosai. Komai nata sai ka tabbatar. Idan ma za a yi, ayi mata ƙarin tambayoyi, ko a yi hang-out ɗin waya. Kai ka san yanzu, matan sai an kula da su sosai. Wallahi idan ba haka ba, akwai matsala.”

As’ad ya jingina da kujerarsa, ya sauke numfashi a hankali. Sai kawai ya ce “Okay.”

Bai ƙara cewa komai ba, sai wayarsa ta fara ƙara a hankali. Ya ɗan kalli screen ɗin wayar, sai ya ga sunan mai kiran. Wannan yasa ya ɗauki wayar cikin ladabi ya ɗora a kunnensa.

Muryar mai martaba ce ta cika kunnensa cikin natsuwa da ladabi “Asalamu alaikum, As’ad. Allah ya ƙara maka lafiya. Barka da dare.”

As’ad ya yi murmushi yana amsawa cikin ladabi “Wa alaikumus salam, ranka ya daɗe. Allah ya saka da alheri. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana.”

Mai martaba ya ɗan yi shiru na sakanni kafin ya ce cikin lallashi “Yanzu kai As’ad, yaro ne kai da sai na gaya maka abu kafin ka yi? Tunda dai ana magana akan aure, bai kamata ba ace har biki ya kusanto amma ba ka taɓa zama da yarinyar nan ka tattauna ba. kaima kasan ba daidai bane. Idan har tana da wata bukata fa? Ko tana da wani ra’ayi da baka sani ba? Ka manta da umarnina ne, As’ad? Kai ka sani ni ban daure ka ba, amma tunda kai ne ka nuna wannan zabin, ya kamata ka nuna kulawa sosai.”

Muryar mai martaba ta fito cike da hikima da girman daraja, tana da wani irin salo da yake sa zuciya yin natsuwa.

As’ad ya sauke wani dogon numfashi mai nauyi, alamar tunani ya cika masa zuciya. Sai yace cikin ladabi “Allah ya huce zuciyarka, ranka ya daɗe. Na ji duk abin da ka faɗa, kuma gaskiya ne. In shaa Allahu zuwa gobe ko jibi zan dawo gida. Yanzu ina tsakiyar wasu manyan taruka ne na meeting, shiyasa na ɗan jinkirta. Amma in shaa Allahu zan yi abin da ya dace. Na gode da shawarar ka.”

Mai martaba ya yi murmushi a can ɓangaren ya ce “To babu damuwa, As’ad. In shaa Allahu Allah zai taimaka. Amma ka tabbatar, kafin lokacin biki ya iso, ku zanta da juna. Ko a waya ne, don ku fahimci juna sosai. Wannan shi ne alkhairi.” “In shaa Allahu, ranka ya daɗe.” As’ad ya amsa cikin ladabi.

Wayar ta katse, sai As’ad ya jingina da kujerarsa ya rufe idanuwansa na ɗan lokaci, zuciyarsa tana shawagi tsakanin maganganun mai martaba da na Alhaji Osama.

Nana hadiza

09030569336

[11/10, 8:25 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA HUDU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

“Wajen ƙarfe shida na yamma As’ad ya fito daga babban taron meeting dinsa na yau, wanda suka shafe sa’o’i suna tattaunawa da manyan ‘yan kasuwa. Yana tafiya a hankali cikin dogon corridor na ofishinsa, hannunsa ɗauke da takardu, kamshinsa yana gauraye da sanyin iska mai ƙamshi.

Bayan ya kammala komai, sai ya nufi gidansa dake cikin ɗayan manyan unguwannin Dubai, wani gida ne mai kyan gaske da tsari irin na zamani. Bayan ya shiga falon, yaronsa P.A, wanda shi ne Babban yaronsa ya shigo cikin girmamawa yana gaishe shi.

“Ranka ya daɗe,”ya faɗa cikin natsuwa, “na tura maka lambar wayarta tun dazu ta text, amma har yanzu bata gida. An ce tun da ta fita kwana biyu kenan bata dawo ba. Sun ce kamar gidan yar uwarta ta koma. Kuma dazun an gansu sun fita tare, sun je wajen masu furniture, amma basu dade ba suka koma gida.”

As’ad ya ɗaga kai kawai, fuska cike da natsuwa kamar wanda ya fahimci komai amma bai damu ba. Ya gyara zaman kujerarsa, hannunsa ya ɗora a gefen kujerar mai launin baki, ya ɗan lumshe idanu. Wannan alamace ga p.a cewa maganar ta ƙare, ya juya ya fita da girmamawa.

Ya zauna na ɗan lokaci yana kallon gilas ɗin da ke gabansa. Ruwa mai sanyi ne a ciki, amma hankalinsa ba a wurin yake ba. Tunani yake yi tunani mai zurfi game da ita...Ramlah daman haka soyayyar take ciƙin kankanin lokaci gaba daya ta rikirkitasa.

Yadda yake jin sunanta kawai, sai zuciyarsa ta buga. Duk da bai taɓa magana da ita kai tsaye ba, akwai wani irin jan hankali da bai taɓa ji ba a rayuwarsa.

Ya miƙe tsaye da cikakkiyar izza, yana tafiya a hankali kamar sarkin da ya saba da mulki. Ya nufi cikin ɗakin wankansa, wanda yake cike da wani kalar kamshi.

A hankali ya kunna ruwan zafi, yana jin ƙarar ruwan Ya cire rigarsa ya shiga ƙarƙashin ruwan, yana barin ruwan zafi ya gangaro a jikinsa. A lokacin da ruwan ya fara tafiya a kansa, sai yaji kamar an kunna wani wutar sha’awa a zuciyarsa. Ba wai sha’awa ta jiki kawai ba a’a, wutar da take hade da tunani, da so, da jan hankali.

Yana ganin fuskar Ramlah, yadda take tafiya cikin nutsuwa, tana sanye da doguwar riga mai launin ja tana dariya kaɗan Sai ya ga bakinta, wanda idan ta yi magana yana motsawa da salo, kamar yana kiransa cikin natsuwa.

Numfashi ya sauke a hankali, hannunsa yana biye da ruwan zafi, sai ya furta cikin sanyi, “Ramlah…”

Cikin mintuna kaɗan, ya gama wanka. Ya ɗauki tawul mai laushi ya goge jikinsa. Sai ya ɗebo mai mai ƙamshi ya shafa a jikinsa a hankali, yana kallon kansa a madubi.

Jikinsa mai lafiyayyen tsari, idanunsa kuwa suna da wani irin natsuwa da tsoro a lokaci ɗaya irin idon mutum mai iko amma mai sirri.

Ya nufi ɗakin kwanciyarsa wanda ke cike da kamshin Oud da Amber, haske mai launin rawaya yana kunne daga gefe.

Ya ɗauki rigar bacci mai laushi mai launin toka, ya sanya, sannan ya ɗauki remote ya danne maɓalli ɗaya. Cikin lokaci kaɗan fitilun ɗakin suka mutu.ya taka a hankali ya haye gadonsa mai launin fari, wanda gado ne irin na manya, Ya jingina kansa a matashin kai, ya lumshe idanu, numfashinsa yana fita a hankali.

Duk da kowane abin alatu na duniya yana hannunsa, amma yau zuciyarsa tana cike da abu guda tunanin yarinyar da ta siye komai na zuciyarsa shi tund yake bai taba jin haka cikin ransa ba.Hotonta ya ci gaba da yawo a cikin tunaninsa.Yana iya ganin murmushinta, yadda idanunta ke juyawa cikin sanyi, da yadda fatar fuskarta take da haske kamar ta jaririya.

Sai ya murmusa, yana faɗi a hankali

“Idan Allah ya yarda, gobe sai naji muryarta…”

Ya ɗan ɗaga wayarsa, ya buɗe gallery, yana kallon hotonta da aka turo masa hoton da aka ɗauka batare da ta sani ba.

Ta saka hijabi mai haske, fuskar nan cike da kamala da nutsuwa.

Yana kallon hoton, sai wani irin nutsuwa ya sauka a zuciyarsa. Ya ji kamar yana so ya rungumeta, ya ce mata ta kwantar da hankalinta, babu abinda zai taɓa ta muddin yana numfashi.

Sai ya lumshe idanu, yana murmushi. Yana ambaton sunanta a hankali cikin numfashinsa.

“Ramlah…” yana ambaton sunan Allah.

Numfashinsa ya yi sanyi, yana kallon sama, yana jin zuciyarsa tana bugawa a hankali kamar ana buga ganga cikin ruwan sanyi. ya kasa samun bacci Yayi ta juyawa a kan gadonsa Numfashi yake saukewa a hankali. Sai kawai ya miƙa hannu ya ɗauki wayarsa dake gefen gadon.

Yayi shiru yana kallonta.

“Indai ban ji muryarta ba yau, bazan taɓa samun nutsuwa ba,” ya faɗa cikin ransa a hankali, kamar yana magana da zuciyarsa.

Yana kallon sunanta a saman screen ɗin, sai wani murmushi mai taushi ya bayyana a fuskarsa. Murmushin da bai saba yi ba, wanda ke fitowa daga zurfin zuciya.

Ya ji wani abu mai kama da farin ciki yana ratsa shi daga kai har ƙafa, kamar ruwan sanyi da aka zuba masa a zuciya.

Sai kawai ya danna call ɗin.

Wayar ta shiga kiran ta a hankali, yana jin ringing ɗinta kamar kiɗan soyayya a kunnensa.

Sai kiran ya ƙare bata ɗaga ba.

Ya lumshe ido, ya dafa kansa, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull