Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 17

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 17

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 17: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 17. Amma zuciyarsa ta ƙi yarda ta zauna.

4,433 words

Amma zuciyarsa ta ƙi yarda ta zauna.

“Zan sake kira,” ya faɗa a hankali.

Ya sake danna redial cikin hanzari kamar wanda baya son bata lokaci.

Yana sa ran ko da taji muryarsa, zata fahimci shi wannan karo na biyu, wayar ta shiga ringing, yana sauraro a hankali, numfashinsa na fita a hankali Bai kai ƙarshe ba, sai ya ji “click” alamar an ɗaga.

Da farko, shiru ne.

Sautin numfashi kawai yake ji daga ɗayan ɓangaren. Zuciyarsa ta tsaya cak, yana jin bugun zuciyarsa kamar ana harbi a ƙirji.

Sai kawai wata murya ta fito

“Assalamu alaikum…”

Wani irin sanyi ya ratsashi a lokaci guda.

Tsigar jikinsa ta miƙe, numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci. Muryarta ce.

Wata murya mai sanyi, mai natsuwa, wacce take da daɗin ji a kunne kamar ruwan sanyi a cikin zafi. A hankali, yana mai janye numfashi ya amsa, “Wa alaikumus salam…”

Sai shiru ya biyo. Ya kasa cewa komai.

Zuciyarsa ta cika da motsi, harshensa kamar ya makale.

Ta ɗanyi shiru na seconds kafin tace cikin ladabi, “Ina wuni.”

Sai kamar daga sama, kalmar ta buɗe masa zuciya, amma har yanzu muryarsa ta kasa fita da kyau. Da ƙyar, cikin rauni da nutsuwa, ya furta “Lafiya lau… kina lafiya?”

Cikin mamaki ta ce, “Bangane mai magana ba…”

Wannan kalmar tata ta dawo masa da hankalinsa. As’ad ya yi shiru. Sai kuma ya lumshe idonsa, yana jin muryarta tana yawo a cikin kunnensa.

Yana so ya ce, “Ni ne As’ad, wanda zaki aura, wanda yake tunaninki kullum,” amma sai ya kasa.

Zuciyarsa ta buge sosai, kamar tana cewa, ka yi shiru kawai. Sai kawai ya katse kiran.

Wayar ta mutu da sautin click.

Ya jingina bayansa da matashin kai, yana kallon sama. Numfashinsa yana fita a hankali, zuciyarsa tana bugawa kamar ana busa ƙaho.

A hankali, ya furta a hankali cikin murmushi, “Ko muryarki kadai, ta isa ta kwantar min da hankali.”

Ya ajiye wayar a gefe, hannunsa ya rufe fuskarsa. Wani murmushi ya subuce masa, wanda yake nuna nutsuwa da jin daɗi da kuma ɗan shauƙi.

Yaji kamar yana so ya sake kiran ta, amma zuciyarsa tace “a’a, ka tsaya, ya isa haka yau.”

Sai ya ɗauki wayar, ya sake kallon sunanta a screen ɗin, yana murmushi.

Wannan karon, murmushin ya zama daɗi mai yawa kamar wanda ya ci nasarar samun abin da yake nema tun da daɗewa.

Ya ɗaga kansa sama, yana faɗin a hankali

“Allah ka bani ikon kula da wannan yarinyar da zuciyata ta amince da ita.”

Ya kwanta yana kallon gilashin taga, fitilun birnin suna haskawa kamar taurari.

Zuciyarsa ta ragu daga tashin hankali zuwa nutsuwa.

Nana hadiza

09030569336

[11/10, 8:26 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA BIYAR

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Ina kwance a kan gado tare da yaya Aliya ita dai tanata faman danna waya idanuwana na fara rufewa saboda bacci yana neman ɗaukata. Sai kawai na ji muryar Yaya Aliya tana faɗin cikin mamaki “Wai Auta, wa ne yake kiranki haka? Yanata kiran waya baki daga ba. Ko da yake naga kin daga na karshe kina tambayar wai wanene Ramlah, to idan mijinki ne fa?”

Na buɗe ido a hankali, na kalleta da murmushi mara ƙarfi. Na yi ajiyar zuciya sannan nace “To ai bansan shi ba. Ko shi ne, ban tabbatar ba. Muryar babba ce fa, Yaya Aliya.”

Ta juyo jikinta gaba ɗaya tana kallona, sai ta haɗe gira ta ce da ɗan dariya amma da fada “Ke dai kina kama da wacce bata waye ba. Wata kila shi ne mijinki, amma kika ki daga masa waya? Ai kin san irin waɗannan mazan basuda wannan lokacin na kiraye kiraye kamar sabbin balaga bafa yaro baniba babba ne idan kika yi wasa, sai su tsere. Yanzu kin san ko kina da kishiya kuwa? Irin waɗannan, ana rikesu hannu bibbiyu wallahi.”

Sai ta ɗan ja numfashi tana kallona da wasa, tace “Amma bari kawai, zan faɗa wa Mom ta san da kirar nan.”

A firgice na zauna, zuciyata ta buga. Na kama hannunta nace cikin sauri “Ayya Yaya Aliya, dan Allah kada ki faɗa mata! Wallahi bansan shi ba, shiyasa ban amsa ba ba da gangan nayi ba. Bansan ko shi ne ba.”

Ta yi dariya ta ɗan bubbuga kafadata tace “To ai ba komai, amma ya kamata ki kira shi yanzu, ki tabbatar masa cewa kina da tarbiya, baki gane baniba yasan eh kinada nutsuwa da sanin yakamata”

Na yi shiru, na ɗauki wayata a hankali. Numbar da aka kirani da ita a baya na lalubo, na danna redial a hankali. Sai kawai na ji “The number you have dialed is switched off.”

Na tsaya na kalli wayar kamar mai jiran ta yi magana. Sai kawai na maida ta gefe, na juya gefe ɗaya, na kwantar da kaina a jikin matashin kai.

Cikin zuciyata sai na fara jin wata irin rauni da ba zan iya fassarawa ba. Ban san dalili ba amma duk lokacin da nake jin sunan shi, zuciyata tana bugawa da wani irin yanayi.

Na lumshe ido ina tunani “Ni dai basu san ba son mutumin nan nakeyi ba kawai biyayyar iyaye nayi. Amma me yasa zuciyata take irin wannan yanayin duk lokacin da na ji muryarsa ko sunansa?

Na sake juyawa gefe, na lullube jikina da bargo. A hankali idanuwana suka fara rufewa, amma zuciyata bata natsu ba tana tafarfasa da tunanin yaya aliya datace inada kishiya a haka dai nayi addua na komawa baccina.

*****.

Washegari da safe, tun kafin gari ya waye, masu gyaran jiki suka iso gidan. Suna shigowa, suka cika gidan da ƙamshin turare da hayakin turaruka. Cikin nutsuwa suka fara gyaran jiki, suna goga mana kayan gargajiya kamar kurkum, lalle, dasu kurkum. Jikina har yana wani sanyi saboda laushin da yayi.

Ina tsaka da gyara, sai na ji muryar Mom daga falo tana faɗin “Ramlah, zan je unguwa, ku dora min pepper soup, zan sha idan na dawo.”

Na ɗaga kai cikin ladabi nace, “To, Mom, shikenan adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya.”

Tace, “Kuyi hankali da shigowar kowa.”

Ta fice tana tafiya da ƙamshin turarenta, har sai da motarta ta bar harabar gidan. Bayan ta tafi, Yaya Aliya ta juya ta kalle ni da murmushi. Tace “Ramlah, kin kirashi kuwa nifa banason haka dakikeyi haba sai kace ba wayayyiya ba.”

Na saki dariya kadan, nace mata “Ni kuwa ban ga kiransa ba tun jiyan da yakira shiyasa nima ban kara kira ba.”

Ta zaro ido tace “To, ki kirashi ke da kanki! Haba, ai ba za ki jira kullum shi zai kira ba.

Na girgiza kai nace “Ai bana son yaji kamar ina binsa. Tunda ba ni da tabbacin shi ne ma.”

Yaya Aliya ta harare ni tace “Ke kin fiye jan aji! Wayar da miji ce kike wa wannan wasa? Ki daina wallahi. Idan kika yi wasa da irin wannan namiji, wata za ta tafi da shi.”

Na tura baki a shagwaɓe nace “to ni na barmata tatafi dashi daman ni ba so nake ba lika mun akayi ai.

Sai muka yi dariya gaba ɗaya da masu gyaran jikin, har mai gyaran ta ce kadafa kixo kina cemana idan bashi ba sai rijiya.

Na saki murmushi kawai, ban ce komai ba.

Na kasa faɗa musu cewa ni dai har yanzu ba na sonsa ko kadan bam sansa ba bansan halinsa ba sannan mai kudi kuma mai sarauta abubuwan sai naga kamar sunyi mun yawa. Masu gyaran suka ci gaba da aikinsu, suna shafa min kurkum da madarar gari, suna cewa “Wannan zai sanya laushin fata, kuma ya fidda haske.

Suna ta bani shawara kala-kala yadda zan kula da fata, yadda zan yi matsi, da yadda ake gyaran jiki kafin aure. Duk da dariyarsu,zuciyata cike take da tunani.

Na ɗan sauke numfashi, na maida kai saman matashin kujera, na rufe idona inajiran abun da suka shafamun ya bushe zan shiga wanka sosai tsigogin jikina suke tashi yanzu saboda abubuwan da ake bani gaba daya mom ta canza abincin gidan daga ni har yaya aliyah gyaramu takeyi sosai.

*****

Sallamar Hajja Kaltume ce ta cika harabar gidan Abba, bayan ta fito daga cikin babbar Mercedes dinta mai sheƙin silver. Tun daga bakin ƙofar gidan take kwalla kira da ƙarfi “Zainabu! Zainabu! Ki fito nan gurina kafin in shigo da kaina!” Muryarta ta cika gidan, har ma’aikata suka tsaya suna kallon kofar.

Momy, wato Zainabu, wacce ke kwance a kan gadonta tana dan danna waya, da sauri ta tashi. Ta saka gyalenta a wuyanta, ta fito zuwa balcony, ta tsaya tana murmushi irin nata na tsiya da izza.

“Aa Hajja Kaltume, yau kece tafe agidan namu? Barka da zuwa, wallahi, barka! To, kishigo cikin gida mana.”

Sai Hajja Kaltume ta tsaya cak a tsakar gida, ta buga mata wani kallo mai cike da bacin rai da raini. Ta ɗaga hannu tace “In shiga? In shiga gidan ki? Ai ban manta ba lokacin da nake zuwa, ke kike barina tsaye a rana kina yin kasaita kamar wata sarauniya. Amma yau kin ga Allah ya nuna miki bambanci nafi mijin naki dan uwana wadata ko kinzata zan manta sanda zanzo ganin yaya kibarni anan?” Ta gyara tsayuwarta, ta ci gaba da magana cikin zafi “To ba wannan ya kawo ni ba, Zainabu. Na zo ne yau saboda inyi miki kashedi inyimiki gargadi da jan kunne saboda wannan auren Ramla. Wallahil azeem, ki ji maganata, idan wannan yarinya ta sami ciwon kai ne ma saboda sharrinki, sai na kulleki da kaina. Na rantse da Allah tunda ke bakisan Allah ba bakida tsoron Allah ko ciwon kai tayi sai munyi shara’a dani dake!”

Mom ta saki murmushi mai ɗan ɗaci tace “To Hajja, me yasa har kike wannan faɗan? Ni menayi to? Ni me na yi?”

Hajja Kaltume ta taka gaba da ƙarfin hali ta nuna ta da yatsa “Ke menene bakiyi ba? Ba wannan ne yakawoni ba nazo ne in tuna miki ! Ke ba imani ba tsoron Allah. Kin dade kina cusa ƙiyayya a zuciyarki ga Ramlah, don kawai kin fi son Bilkisu. Amma ki sani, aure za a yi! Ko kin so, ko baki so wannan auren sai an yi shi! Ko ma ki mutu ko kiyi rai aure dai babu fashi.”

Momy ta dan girgiza kai tana murmushin raini. “To Hajja Kaltume, ai aure ba dole ba ne. Idan As’ad din da kike ta faɗa zai auri Ramlah ne, ai sai mu gani. Kuma ni fa, ban ga dalilin da yasa sai ku yi ta saka baki ba aure ne nace ayi magani ko an munafurce ni an bawa yar kishiyata mai kudi an bar tawa yarinyar.”

Sai Hajja ta ɗaga murya sosai ta ce “Zainabu! Kin ji ni da kyau! Idan kina ganin hakan ba zai faru ba, to sai mu gani Idan kin ce baki son zaman lafiya, to ki shirya. Ni da ke sai dai a gaban kuliya mu sake haduwa. Bazan bata bakina akanki.”

Daga nan ta juya da izza ta nufi mota tana huci. Tana shiga motarta ta rufe murfin da ƙarfi, tayoyin suka murɗa ƙasa suka bar gidan da ƙura.

Mom ta tsaya daga balcony ɗin tana kallon bayan motar, fuska cike da fushi da kunar rai. Sai ta furta a hankali “Hmm... tun ina amarya kece matsalata kaltume kinsan ni fiye da kowa amma nasan me zanyi.” Sai ta juya ta koma cikin gida da sauri, zuciyarta cike da tsanar Ramlah da haushinta.

Samun guri Mom tayi ta zauna, gaba ɗaya zuciyarta ta ɓaci. Tunani ya fara yi mata yawa, komai ya rikice a kanta. “To yanzu ai aikin boka ya lalace,” ta faɗa a ranta. “Dole in kira Yakaka, inji shawarar da zata bani.”

Ta ɗauki wayarta cikin hanzari, ta shiga kiran Yakaka. Sai dai har ta kira sau biyar kafin daga ƙarshe ta ɗaga wayar “Lafiya kuwa, Zainabu? Me ya sa kike ta kirana haka?”

Momy ta daidaita muryarta, ta dan sauke numfashi kafin ta ce “Dan Allah, Yakaka, ki taimake ni. Na rasa yadda zan yi. Batun auren nan na Ramlah yana neman ya zama gaskiya, ni kuma wallahi ba zan yarda ba.”

Yakaka ta yi shiru na wasu sakanni, sai kuma ta ce da murya mai natsuwa “Zainabu, yanzu kin shirya sauraron gaskiya kenan? Domin maganar da zan gaya miki ba itace gaskiyar.”

Mom ta ce da sauri “Ina saurarenki, Yakaka. Kawai ki taimake ni.” “To, ki ji ni da kyau,” in ji Yakaka. “Na faɗa miki tun farko malamai ko bokaye babu abin da za su ba ki sai danasani da mummunan ƙarshe. Zainabu, idan har kika daina bin zuciyar kiyayya, wallahi sai kin ci arziki ta hanyar yarinyar nan. Ramlah fa alheri ce gare ki, amma zuciyarki bata taɓa yarda ta gani hakan ba. Kiyayyarki gare ta ta yi yawa sosai.”

Momy ta yi shiru tana sauraro, idonta cike da hawaye, amma zuciyarta har yanzu ba ta sauka ba. Yakaka ta ci gaba da magana cikin nutsuwa “Yanzu dai ki fara da saita kanki. Ki dawo da hankalinki. Idan Abban yarinyar ya dawo daga tafiyarsa, ki nemi yafiyarsa, ki yi masa magana da kuka da lallashi kamar yadda kika saba. Ki nuna kamar kin canza, kina son zaman lafiya.”

Ta dan yi shiru kadan sannan ta kara da cewa “Amma tunda auren nan baki so, ai akwai wata hanya. Kina da numbar mijin yarinyar, ko ba haka ba?”

Momy ta ce “Eh, tana tana wayar abbansu bazatayimun wahalar cirewa ba.”

“To, sai ki nemi sabon layi, ki yi masa text message. Ki rubuta masa cewa Ramlah ba ta da tarbiyya, ba ta da kamun kai, har ki ce masa ai karuwa ce wadda bata dace da shi ba. Idan ya karanta wannan, tabbas hankalinsa zai rikice, aure kuma ya afasa.”

Hankalin Mom ya fara dawowa a hankali, sai ta dan murmusa cikin muryar shaidanci ta ce “Yakaka... sai da ke! Gaskiya kin bani shawara mai kyau. Na gode sosai.”

Yakaka ta ce “Ai ni ban fi ki wayo ba, sai dai na fi ki gaskiya. Ki kula da abin da kike aikatawa, saboda Allah yana ganin zuciyar dan Adam.”

Mom ta share gefen idonta da tissue, sannan tace cikin ɗan murmushi “Nagode Yakaka... yanzu na san abinda zan yi.” Ta katse wayar a hankali, tana murmushi mai cike da mugunta, zuciyarta na tunzura ta kamar wuta.b “To wannan karon, Ramlah, sai na tabbatar kin rasa komai aure, mutunci, da farin ciki.”

Nana hadiza

09030569336

[13/10, 10:24 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA SHIDA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

*********

Tunda Alhaji Muqaddam ya shigo falon, Ayshatu ke ta harararsa, tana ƙoƙarin guje wa kallonsa. Kunnuwanta sun yi ja, idanunta kuma na cike da tsoro da bacin rai. Ita dai tuni ta tsani yadda yake nuna mata kamar ba ta da muhimmanci, duk da kuwa tana ganin kanta mace ce mai kyau da aji tana ganin tafi matansa komai tundaga kyau aji har dukiya.

Alhaji Muqaddam ya tsaya yana kallonta, sai kuma ya saki ƙaramin murmushi. Dama shi mutum ne mai saukin kai sosai amma a zuciyarsa, gaskiya yana sonta sai dai halinta na rigima da son faɗa yana tsananta masa gajiya.

A hankali ya ƙarasa inda take zaune ya ce da ita cikin salo na lallashi “Ayshatu na... ni dai ban taɓa ganin rigimammiya kamar ke ba. Kin san fa ina son ki, amma ki rage wannan halin naki. Na fa gaya miki, zan baki ₦50 million, amma sai na siyar da kayan nan da na samo daga waje.”

Ayshatu ta tashi tsaye kamar wacce aka zuga, ta ce cikin fushi “Wallahi, Alhaji, kai kullum dai haka kake! Asad ma ina tambayarsa abu, nan take yake bani baya tsayawa jayayya dani. Kai kuwa, har mako biyu yanzu, ka kasa bani kuɗin da ka alkawarta! Wannan wani kalar tsiyace nagayamaka shago zan bude inason saro kayayyaki sosai kana gani dai asarar shaguna na duk kaine ka jawomun.” takarasa idonta yana ciccikowa da hawaye tuna irin iftilin yan fashi da suka shiga shagunanta sukayimata sace sace manya.

Da zarar ta ambaci sunan Asad, sai jinin Alhaji Muqaddam ya hau. Cikin bacin rai yake tsananin tsananin kiyayya da Asad, saboda yana ganin shi ne wanda ke janyo masa rashin mutunci da Ayshatu take masa yau kusan watanni da aure amma babu ranar da bazata ambace shi.

Kafin ta gama maganar, sai kawai ya ɗauketa da mari mai zafi Ƙarar muryarta ta cika falon. Hannunsa ya nuna mata cikin tsananin ɓacin rai, ya ce da murya mai cike da iko “Ki saurare ni da kyau, Ayshatu. Wannan shine karon ƙarshe da zaki sake ambatamin sunan Asad! Karki kuskura ki sake! Wace irin mace ce ke? Kina mantawa ni mijinki ne? Kokuma angayamiki asad mijinki ne yanzu? Ya janyo numfashi, yana ƙoƙarin danne fushinsa, sannan ya ci gaba da magana da muryar da ta nuna tsantsar izza “Ai ni ba ke kaɗai nake aure ba! Inada mata biyu kafin ke tsarkakku, masu kamun kai, waɗanda ban yi abin kunya a waje ba dasu ba. Amma ke, kina yawo kina cika kunne da maganganun banza! Ko zaki komawa asad dinne da aurenki to kijini da kyau wallahi bazantaba sakin ba har abada munatare.”

Ayshatu ta tsayar da hawaye a idanunta, amma har yanzu zuciyarta tana tafarfasa da tsanar shi. Sai dai bata iya cewa komai ba, saboda ganin yadda zuciyar sa ta ɓaci sosai.

Alhaji Muqaddam ya juya yana nuna mata ƙofa da yatsa, ya ce cikin murya mai karfi “Kuma ki sani daga yau ban yarda ki fita ko’ina ba! Wallahi, idan kika sake fita ba tare da iznina ba, sai na nuna miki ni Alhaji Muqaddam ɗin da kike rainawa ne.”

Ya juya ya fice daga falon, yana huci kamar wuta. Ayshatu kuwa ta tsaya cak, tana riƙe da fuskarta da ya yi wa mari. Hawaye na zuba a hankali, zuciyarta na tafasa da wani irin baƙin ciki da kunar rai. “Da gaske ne Asad ya fi shi komai,” ta faɗa a ranta, tana jin wani sabon ƙuduri yana taso mata ta rama, ta nuna masa ita ce mace, ba zai taka ta ba.

Ayshatu ta kasa cewa komai. Wani kuka mai raɗaɗi ne ya kufce mata kuka mai cike da tausayin kai da baƙin cikin rayuwa.

Tunda suka yi aure, ta tabbata Alhaji Muqaddam yana sonta amma soyayyar da take ganin tana da daraja a farko, yanzu ta koma tamkar daurin rai da rai. Duk wani abu a gidansa, sai ya nuna mata cewa ita ce ta “tarar” da sauran matan, ita ce ƙarama, ita ce dole ta yi haƙuri.

Idan aka yi wani abu da bai faranta masa rai ba, sai ya ɗaga murya yacce “Ayshatu, banda yawo fa! Ba a son mace ta rika fita kamar ba ta da gida!”

Da farko kalamansa suna mata ciwo a zuciya, amma ta kan danne saboda tana sonsa. Har ta kai ga ta fara jin tsoron maganar saboda duk lokacin da ta yi ƙoƙarin bayyana ra’ayinta, sai ya katse ta da zargi ko faɗa.

Tun da dadewa tana jin hasashen cewa bai yarda da ita ba, amma yau ta tabbatar. “Shi kenan,” ta faɗa a hankali, hawaye na zuba daga idanunta, “ba ya sona da gaske. So daya ne kawai na gani a rayuwata agurin Asad.”

Zuciyarta ta matse da ƙuna, tunani akan Asad ya cika kwakwalwarta gaba ɗaya. Tun lokacin da suka rabu bata taɓa samun nutsuwa ba. Duk da cewa tana da numbar sa, amma duk lokacin da ta kira, baya ɗauka. Wani lokaci ma, sai ta ji muryar kamfani ta ce “number not reachable.”

Kowane irin yunkuri da ta yi domin ta ji muryarsa, yakan kare da faduwar gaba da kuka.

Ta ɗauki wayarta tana kallonta sai ta ji kamar wayar ma ta zama abokin damuwarta. Ta lumshe idanu tana murmushi mai ciwo, tana faɗin a hankali “Toh, gaskiya dai Asad ya fi Muqaddam komai. Ba wai saboda kudi ba, amma saboda hali, saboda yadda yake girmama mace...”

Sai kuma ta kifa kanta a kan pillow tana kuka sosai. Kukan ya haɗu da nadama da raɗaɗi. A hankali ta shiga dakinta, ta rufo ƙofa, ta kwanta tana kukan da ya fito daga zuciya.

Kowane numfashi da take fitarwa sai ta ji kamar wani dutse ne yake matsa mata kirji.b“Da na san haka rayuwa zata juya, da ban taɓa rabuwa da shi ba...”

**

Washegari da sassafe na farka da jin hayaniya daga ƙasa. Na leƙa ta window na ɗakin, sai naga gidan Mom ya cika da jama’a. gidan ya cika da annashuwa. Kowa na ta faman hidima ana share-share, ana gyara falon baki da na ciki. Wani kamshi mai daɗi na turaren wuta ya lullube gidan gaba ɗaya.

an uwanmu suna ta hada-hada kamar ana bikin yau. Matar Yaya Abbas tana gyaran falo, yaronta na kai kaya daga mota, matar Uncle Hamza kuma tana ɗaura abinci a kicin. Wasu kuma suna shirya kujeru.

Dakayar dai na iya sakkowa nashiga gaida yan uwa haka na karasa kitchen na zuba abinci sannan nafito kowa sai tsokanata yakeyi amarya amarya Ban iya cewa komai ba, sai na dan sunkuyar da kai cikin kunya. Kwana biyu kenan da na lura kamar jikina ya sauya na ƙara haske, kuma zuciyata ta cika da kwanciyar hankali. Tunda Mom bata gidan yanzu bana tare daita duk wani baccin rai ko damuwa ban dashi gashi muna hutun makaranta kusan 1month kamin mu koma inda nakejin dadi ma final year nake yanzu.

Ina cikin duba wayata ne sai naga Yaya Aliya da Hamdiyya sun shigo dakin sunata tsokanata kowa da abunda yake cewa nikam ban iya cemusu komai ba “Ranki ya dade!”

Daya daga cikinsu tafaɗa na kalleta ina harararta

Da misalin ƙarfe goma na safe, sai ga manyan motoci sun fara shigowa cikin layin. Wata babbar Prado ce, sai wata Hilux mai cike da akwatuna, sannan wasu motoci uku masu ɗauke da manyan akwatuna.

Mutane suka fara taruwa a bakin ƙofar gidan suna kallo, yara suna ihu, manyan mata kowa yafito ganin manyan motoci wasu ma baka taba gani arayuwarka ba kwatakwata. Kowa mamaki ya rufe masa baki da fatan alkhairi.

Babbar motar da aka buɗe wasu matane kyawawa suka fito sauran motocin kuma bayin gidan sarki ne sunata ahiri hiri da ihu sosai da murna maganganu dai da ko baa gayamaka ba kasan ahalin gidan sarki ne.

Gaba ɗaya gidan ya kaure da hayaniya! Kowa ya fito,ana murna. Akwatuna masu sheƙi iri daban-daban ake saukewa daga motoci, ana jera su a falo cikin tsari. Kowane akwatin yana ɗauke da wani abu ajiki ga sunan Ramlatu ajiki. Haka aka shiga gaishe gaishe da mutunta juna ashe abba ya gasa raguna kusan hudu banda snacks da katan katan din lemoka da aka ajiye musu sai tukwuicin kusan million 3 akai sukuma suka bada million 7 akai. Kowanne acikin yan uwa sun rikice wasu suna fatan ina ma nasu ne wasu kuma yaransu wasuma tambaya suka dinga yi wanene zai aureta ayaran sarkin amma mom babu wanda tabawa amsa dan dayawa daga cikin dangi dun nuna baƙin cikin karara..

Ganin bacci nakeji yasanyani kashe light din dakin nayi saurin kwanciya zuciyata cike da tsoro da tunani gani nakeyi akwai tazarar dake tsakani yafi karfina yafini komai gani nakeyi ban kai ba sannan hankalina gaba daya atashe yake bansan yaya ahalin suke ba kuma naji yaya aliya na fadan kamar inada kishiya gabadaya zuciyata babu dadi dannewa kawai nakeyi wallahi. Bansan lokacin da bacci yakwasheni ba dan jiya da daddare mom tahadamun kankana da kaninfari da dabino da madara tunda nadawo gidanta kullum sai nasha da daddre da waji turare danake tsugunnawa akai iccen gab gab ne da habbatussauda da bagaruwa da kaninfari da ganyen magarya aka daka aka zuba miski da perfume oil kullum shima sai na tsugunna akai. Kullum faɗanta tunda bataɓa aure dole ta dage gurin kulawa dani.

Nana hadiza

09030569336

[13/10, 10:24 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA BAKWAI

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewapen @nanadiso10

*********

Abba na zaune a falonsa yana duba wasu takardu, sai momy ta shigo cikin natsuwa amma fuskarta cike da nadama duk da duk plan ne amma tayi kalar tausayi sosai Ta durƙusa a gabansa cikin kuka tace, “Abban Ramlah, dan Allah ka yafemun. Na san nayi kuskure, ban kyauta ba. Sharrin shaidan ne da kuma zugar kawaye suka sa haka. Don Allah ka yafemun, bazan sake ba.”

Abba ya ɗan kalleta na wani lokaci, sannan ya sauke numfashi yace da tausayi, “Bakomai Zainabu. Allah Ya shirye ki. Abun da ya wuce ya wuce. Ki tashi ki shirya, ki je ki ga lefen yar taki, ai yanzu an kawo.”

Gaban momy ne ya faɗi da sauri ta ɗago tana tambaya cikin firgici, “An kawo lefen ne?” Abba ya ɗan gyara murya yace, “Eh, sunkawo dazu. Har da tukwuicin mota, sannan da tukwuici na miliyan biyar (5M).” Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci momy. Ta haɗiye miyau tana faɗin,

“Akwati nawa suka kawo?”

Abba ya kalleta da sakon da dan mamaki yace “Ni ban je ba, ban san adadinsu ba. Amma ki shirya, ki tafi ki gani da idonki.”

Momy ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta dan share hawayenta tace, “ Yau gashi ina kukan farin ciki Allah alhamdulilahi Allah Ya sa alkhairi, Ya ba su zaman lafiya, insha Allahu. Zan je in gani, ko gobe, yau dai jikina ba daɗi.

Da ta juya ta nufi dakinta, hawaye suka fara zubo mata. Ta zauna a gefen gado tana kuka cikin sirri, tana faɗin, “Me nayi haka? Rayuwata ta rikice saboda kishin banza. Na rasa komai, na rasa kowa.”

Bilkisu ta shigo dakin momy cikin kuka sosai, tana share hawaye tana magana da muryar ta tana rawa “Momy… kin ga lefen Ramlah kuwa? Momy wallahi kayan sun hadu! Akwatuna ne har dozen hudu, duk an yi musu ado da zinariya, an kawo nata babbar mota sabuwa. Gaba ɗaya mutane suna magana akai, har a Instagram bloggers suna dora hotunansu mommy ni yakamata nasamu ba ramlah ba momy..!”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull