Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 18
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 18: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 18. Cikin zafin rai momy ta ɗago kai ta kalleta da wani irin kallo mai…
4,491 words
Cikin zafin rai momy ta ɗago kai ta kalleta da wani irin kallo mai cike da takaici da haushi, ta daga hannu ta harareta sosai, sannan ta ɗan ɗaga murya tace “Ke! Bilkisu, ki kama min wawan bakinki ki yi shiru dan ubanki! Me yasa kike kara tunzura min rai? Kin manta abun da ke gabanki ne? Ko dai baki gane halin da muke ciki ba? Ina ruwanki da lefen Ramlah? Ai duk wannan bakin cikin nali zai sa kowa ya gane abunda kike ciki.”
Ta turo baki, ta ɗan gyara zamanta sannan tace da karfi “Ki saurara da kyau wallahi da bakin cikin haka azahiri ki daina nunawa kowa ki kau da kanki ki nutsu amma dole sai mun hana wannan auren. Dole sai mun yi amfani da siyasa da makirci, mu tursasa kanmu da son abun kada mutane su gane. Idan ba haka ba, to ki sani, auren nan babu fashi.”
Bilkisu ta tsaya tana kallonta, idanuwanta sun rine saboda kuka da haushi. Ta haɗiye miyau ta juya ta bar dakin, zuciyarta cike da zafi da baƙin ciki. Tana fita ta jingina da bango tana tunani, tana ji kamar zuciyarta zata tarwatse.
“Ni Bilkisu... har Ramlah ta rigani aure?” ta faɗa cikin raɗa. “Kawayena duk suna ta dora lefen su a Instagram, yanzu itama ta zama abin kallo? Sai trending takeyi kowa sai dorata yakeyi yana mata addua ni yakamara nasamu wannan gatan dole nasan abunyi dole.?”
Ta share hawayenta da ƙarfi, ta fisge jakarta tana faɗin cikin takaici “Wallahi ba zan zauna ina kallo auren nan ya tabbata ba. Komai zai faru, sai nayi wani abu!” Ta fice daga gidan da sauri, zuciyarta tana tururi, tana da tabbacin cewa zata yi komai domin ganin wannan aure bai tabbata ba.
*********
Ayshatu ta fizgo wayarta da karfi, ta jefar da ita ƙasa, tana rike kirjinta da hannuwa biyu, tana saki wani irin kuka mai ciwo da radadi. Ta buga wayar akan gado tana faɗin “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Asad zai yi aure? Ashe da gaske ne? Ashe ba wasa bane?”
Kukanta ya ƙara ƙaruwa, hawayenta na gangarowa kamar ruwan sama. Zuciyarta tana bugawa kamar zata fito daga ƙirjinta.
Ta zauna tana sheshshekar kuka, tana magana kamar wacce ta haukace.
“Ni nayi zaton idan na bar shi, zai haukace! Na zaci bazai iya rayuwa ba tare da ni ba. Na zaci ni ce farin cikinsa, ni ce komai nasa! Amma yau, yau Asad zai yi aure? Me ya same shi? Tayaya haka ta faru?”
Ta dafe kanta tana jijjiga jikinta, zuciyarta kamar zata fashe.
“Mutumin da gabansa baya aiki fa idan yana tare da ni! Mutumin da yake sona fiye da kowa! To tayaya zai iya aure? Wani irin abu ne wannan Ya Allah?”
Ta fashe da wani sabon kuka, tana rera kukan cikin tsananin baƙin ciki “Ya Allah, don girman ka... kada ka bari wannan aure ya tabbata. Kada ka bari Asad ya aure wata mace... ba zai yiwu ba!”
Cikin hargowa ta ɗauki wayarta, tana share hawayenta da sauri ta danna numbar Nawal, ɗiyarta kuma itace cikin yaran take kusa da Asad. Sai dai kiran farko bai shiga ba, haka ta kira sau biyar kafin na shida ta daga.
Muryar Nawal mai sanyi da girmamawa ta amsa “Mamaah, lafiya? Wannan kiran haka da safe?”
Ayshatu ta ɗaga murya cikin fushi “You’re stupid, Nawal! Are you seriously asking me that? Dan ubanki aure babanku zai yi, kuna zaune kuna kallo kamar ’yan banza? Kuna nufin baku da hankali ne? Shine zaku barshi haka kawai yayi aure tsofai tsofai dashi ko ku bazaku hanashi ba nawal amina daman tadaina daukar wayata ma saboda nayi aure ko?”
Nawal ta ɗan yi shiru tana mamaki sannan tace cikin ladabi “Mamaah, wacce magana ce haka? Ki natsu mana, please. Ki gaya min me ke faruwa ne?”
Ayshatu tana huci, tana kuka da fushi lokaci guda “Bazan natsu ba! Ku tashi ku hanzarta ku hana shi aure! Kin bar babanku ya fita da girmansa wai xaiyi aure yanzu zai aure wata karamar yarinya! Nawal, wallahi nagayamaki, idan wannan aure ya tabbata, sai na tabbatar da cewa babu wanda zai zauna lafiya!”
Nawal ta girgiza kai tana jin nauyin maganganun takarasa tana dariya “Mamaah, don Allah ki dena wannan maganar. Ba mu hana ki aure ba, amma wannan lamarin babu ruwanki kiji da aurenki danAllah kada kisaka kanki arigima danAllah…”
Ayshatu ta katse ta cikin ihu “Nawal! Ni kike gayawa haka? Ni kike gayawa magana da wannan murya? Kamar Wacce kika haifa? Kuma yarinyar ma yar gidan uban wanene…”
Kafin ta karasa, Nawal ta katse ta “Sorry Mamaah, sai anjima please dan Allah ki kama kanki kada kikara saka kanki cikin wani bala’in. Wallahi banyiwa dady magana.”
Sai da taji “beep-beep” na wayar ya tsaya sannan Ayshatu ta zube a gadon tana rusa kuka kamar ranta zai fita.
“Asad… me yasa zaka min haka? Tayaya zaka manta da ni haka?” Tana kuka tana bugun kirjinta, tana jin kamar duniya ta tsaya cak. Duk duniya babu wanda yake jin zafin zuciyar Ayshatu kamar ita kanta mace da take da komai, amma yanzu ta rasa mutum daya da zuciyarta ke so da gaske.
****
Cikin bacci nake jin ana tashina a hankali, kamar daga nesa nake jin muryar da ke kirana. Na buɗe idanuwa a hankali, sai naga Yaya Usman ne tsaye a gabana. Ai bansan sanda na zabura na tashi daga gadon ba, na rungumeshi da farin ciki har da dariya.
Cikin magagin bacci nace masa “Yaya... kaine kuwa? Ko mafarki nake?”
Ya yi murmushi yana kallona da idanuwansa masu taushi, yace “Nine fa, Auta. Kin girma, kin kara kyau sosai. Allah yajikan Manny, yanzu kamarku daya da ita. Har kinfi ta kyau.”
Na murmusa ina dariya kadan nace v“To yanzu Yaya shine kaje kayi zamanka a India har tsawon lokaci, ko tunawa dani bakayi?”
Ya girgiza kai yana murmushi, yace “A’a Auta, kiyi hakuri. Ba wai na manta dake bane. Ina dai gujewa bacin ran Momy ne, itace tace kar na dinga zuwa saboda wasu dalilai nata. Amma yanzu da komai ya lafa, gashi na dawo, kuma kin ga nazo da iyalina.”
Cike da murna nace “Yaya, da gaske? Ina matarka take?”
Yace “Tana kasa ne, tare muka zo har da yaran. Sun ce sai sun ganki saboda sun dade suna tambayata ke.”
Na murmusa cikin farin ciki, zuciyata ta cika da soyayyar ɗan uwan da na dade ban gani ba.
Sai ya kalleta da fara’a yace “Auta, wai saraki kika dakko mana haka? Tun dazu ake ta shigowa ana kallo kayan lefe, har yanzu ba a gama ba. Kowa sai murna yake da fadin alkhairi, babu wanda yake maganar sharri. Wallahi kowa yana yabon shi, kinga ribar hakuri komai wannan rayuwar komai yayi farko to tabbas zaiyi karshe babu wani.”
Na saki murmushi ina jin zuciyata cike da tsoro Yace “Na yi matukar farin ciki Auta. Kin ga, aure babban abu ne. Kuma kin samu miji mai mutunci, wanda mutane ke girmamawa ga sarauta ga kudi. Ki godewa Allah, ki dage da addu’a. Ki girmama shi, ki nuna masa biyayya da ladabi. Kin san rayuwar aure sai da hakuri, kinji?”
Na gyada kai a hankali nace “In shaa Allahu, Yaya. Zan kula, zan kuma kiyaye abin da ka fada min.”
Ya shafi kaina yana murmushi yace “Haka nake so, Auta. Allah ya saka miki da alkhairi, ya ba ku zaman lafiya da yasanya albarka acikin aurenku.”
Na ce masa cikin natsuwa “Amin Yaya. Na gode sosai.”
Sai muka yi dariya kadan, muka ci gaba da hira cikin nishadi da kauna.
Nana hadiza
09030569336
[15/10, 11:16 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
*********
Bayan tafiyar mutanen gidan Mai Martaba, falon gidanmu ya cika da wani irin shiru mai nauyi. Sai shashekar kukan yaya billy dake tashi aciƙin palon Abba yana zaune yana murmushi, Shi ɗin fa har dariya yake yi kadan-kadan, yana faɗin “Alhamdulillah, wannan babbar ni’ima ce daga Allah. Bayan wahalar da kikasha da kuma azabar da akasa nasanyaki na auramiki ɗan daba gashi Allah yayi miki tukwuici yayi miki gata baɗan karami ba Nagodewa Allah sosai ubangiji Allah yasanya albarka acikin auren nan naki.”
Ni kuwa zuciyata ta yi wani irin nauyi. Kuka ya subuce min, hawaye suka zubo daga idona ba tare da sanina ba. Ban san mijin da za a bani ba. Ban san ko wane ne, ko yadda yake ba. Duk da na ji an ambaci sunansa a taron makaranta, amma zuciyata ba ta gama fahimtar abin da ke faruwa ba. Na ce cikin raina
“ wayyo Allah na, me yasa ni? Idan na fahimta yaya bilkisu ke son as'ad?”
Ban gama rufe bakina ba, sai kawai na ji Momy ta fasa kuka sosai kamar karamar yarinya. Ta miƙe da sauri ta shiga masifa tana faɗin “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ashe haka ake shirya aure a bayan idona? Ashe haka ake kawo akwatuna guda goma sha biyar cikin gidan nan? Wannan uban kayan duk kudin nagani inaso ne?! Ga kudi, ga tsadaddun kaya! Amma ban san komai ba! Na raini yarinya na tsahon shekaru da kaina? Ashe haka za a raina ni a gaban ‘ya’yana?!”
Ta juyo ta kalli Abba da idanuwanta masu cike da ƙiyayya da mamaki “Abba, ban gane ba. Me ya kawo mutanen nan? Na ji kuna magana akan Ramlah, na ji kuma suna As’ad. Kai, me kake nufi da wannan? Wato Ramlah kake nema wa aure ga As’ad ba Bilkisu ba? Kai kuwa wani irin uba ne kai? Wane irin zalunci ne wannan?”
Na ji jikina ya ɗauki rawa, zuciyata ta tsinke kamar ana yage ta da wuƙa. Na rasa abin da zan ce. Na tsaya tsaye kamar gawa.
Abba ya ɗago daga inda yake zaune, ya kalle ta da ido mai cike da ɓacin rai. Bai yi magana nan take ba, sai da ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce da murya mai natsuwa “Zainabu, ki sani, wannan ba shawarar kaina bace. Mai Martaba ne da kansa ya aiko. Sun zo neman auren Ramlatu ga ɗansa As’ad. Ni dai na karɓi gaisuwarsu. Kuma kin sani, bana taɓa tursasa ‘ya ta akan aure. Amma wannan dama da Allah ya kawo ba zan taɓa hana ta ba kuma kisani ni ba uban as'ad bani ba da zan tursasa shi yaso bilkisu ke bari ma na fito miki a mutum ban isa na sanyashi ba ba saa na baniba ya nuna wacce yakeso kuma nima na bashi.”
Momy ta kara fashewa da wani wahalallen kuka ta ce cikin huci “Wato kai Ramlah zaka ba As’ad? As’ad ɗin da Bilkisu take mutuwar so? Kai kuwa mugun uba ne, kai baka da adalci, kai ka ci amanata! Ashe haka zaka hallaka min farin cikina?!”
Kafin ta ƙarasa maganar, sai kawai muka ji Abba ya miƙe tsaye cikin masifa ya ɗaga hannu ya kifa mata mari mai ƙarfi. Sautin marin yacika daƙin.
Ya ce da murya mai kaifi “Eh! Ita zan aura masa! Ita Ramlah ce na yarda zan ba As’ad! Zainabu, idan kina da abin da zakiyi wallahi kiyi! Amma ki sani wannan aure sai ya tabbata. Ba zan bari a afasa shi ba!”
Momy ta riƙe kuncinta tana ihu “Wayyo Allah na! ka ci amanata! ka ɗauke min dukkan farin cikina aka ba wannan yarinyar! aka zalunce ni ni da diyata Bilkisu!”
Kafin ta ƙare, sai muka ji wani kukan da ya fito daga ɗakin Yaya Bilkisu. Da gudu ta fito, fuskarta cike da hawaye, idonta ya kumbura.
Tana sharɓar kuka tana kallon Abba ta ce “Abba, me nayi maka da zaka hanani dadyn su nawal abba tun ina zuwa gidansa nake sonsa abba? Ashe haka zaka wulakanta ni? Ashe haka zaka ɗaga ni ka jefa ni a ƙasa? As’ad da na dade ina mafarkin aure dashi, wanda kowa ya san shi ne burina, kai ka ɗauke min shi ka ba Ramlah? Ashe haka za a yi min? Abba… bata karasa ba itama abba yaɗauketa da mari mai zafi.
Ta juyo ta kalle ni da idanuwa masu cike da hawaye da ƙiyayya “Ramlah! Kin ci amanata! Ashe ke ba ‘yar uwata bace! Ashe ke muguwar munafuka ce! Kin ɗauke min burina, kin ɗauke min farin cikina. Allah zai saka da ke!”
Maganarta ta daki zuciyata kamar wuka. Na fashe da kuka cikin tsananin zafi. Na ce cikin kuka “Wallahi ban san komai ba! Ban taɓa neman wannan aure ba! Ban taɓa faɗa wa kowa cewa ina so ba. Don Allah ku kyale ni. Ku daina zargina.”
Momy tace “Ƙarya kike yi! Kin san komai. Ke kika shirya wannan komai. Kin lalata min rayuwa! Wallahi wannan aure ba zai taɓa tabbata ba!”
Kukan Bilkisu ya ƙara ƙaruwa. Ta riƙe kanta tana faɗin “Allah ya isa tsakanina da ke! Daga yau ni da ke mun rabu. Ba za ki taɓa zama kanwata ba. Na tsane ki har abada.”
Na kasa jurewa. Na juya da gudu na nufi dakina. Na rufe ƙofa da ƙarfi na faɗa kan gadona. Na rufe fuskata da bargo na cigaba da kuka mai tsanani.
A waje ina jin Momy tana ihu tana cewa “Ba zan bari ba! Wallahi ba zan bari ba! Wannan aure ba zai tabbata ba. Ba zan taɓa bari ba!”
Ina jin Bilkisu tana kuka tana faɗin “ na rasa komai! na rasa farin ciki! rayuwata ta kare.”
Abba kuwa na ji ya bar falon da ƙarfi. Motarsa ta tashi da sauri, ya bar musu gidan cikin masifa.
Na ci gaba da kuka a dakina. Zuciyata tana bugawa kamar ana dukan ganga. Na ce cikin raina:
“Ya Allah, me yasa ni? Ban taɓa neman wannan aure ba. Ban taɓa neman wannan soyayya ba. Amma me yasa aka jefa ni cikin wannan bala’i? Allah ka taimake ni. Allah ka tsare ni daga wannan jarabawa.”
Na ci gaba da kuka har sai da dare ya yi. Idona ya kumbura, zuciyata ta karye. Na kwanta ina kuka har barci ya ɗauke ni.
********
Da safe garin Spain ya waye cikin sanyi da iska mai daɗi. Fitilu na kan tituna suna haskawa, mutane suna ta hargitsi da ayyukansu. As’ad kuwa, duk da zazzabin da yake ji tun jiya, ya yi nufin tafiya ya ga likita idan ya isa.
Tun da ya sauka daga jirgi, ya nufi babban hotel ɗinsa na alfarma wanda ya saba sauka a duk lokacin da ya zo ƙasar. Hotel ɗin kuwa ya kasance mai katafaren tsari, ɗaki mai girma, gadon alfarma, fitilu masu kyau, da kuma taga dake fuskantar kogin da ke gefen birnin.
Bayan ya huta na ɗan lokaci, sai ya nufi wuraren da ya saba zuwa wajen business dinsa. As’ad mutum ne mai daidaita lokaci, duk inda ya shiga komai sai ya tafi da tsari. Kafin awa 24 ta cika, ya riga ya gama dukkan harkokin da ya kawo shi ƙasar domin su.
Sai ya ɗauki lokaci ya nufi asibitin manya domin ganin likita. Bayan an karɓe shi da girmamawa, aka gudanar da cikakken bincike akansa.
Likitan ya kalleshi cikin murmushi, ya ce “Mr. As’ad, babu abin da mukagani Zazzabin da kake ji alamar jiki yana murmurewa ne. A gaskiya, dukkan gwaje-gwajen sun nuna cewa kana samun ƙarin lafiya a jiki. Amma duk da haka zan baka wasu ƙananan magunguna don ka gwada, idan Allah ya so zaka ji sauƙi fiye da haka.”
As’ad ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi. Ya yi murmushi mai taushi ya ce “Alhamdulillah. Na gode sosai, doctor.”
Bayan ya karɓi magungunan, ya dawo hotel ɗinsa cikin nutsuwa. Zuciyarsa tana ta duba abubuwa da yawa na rayuwa, na aure, da kuma ƙaddarar da take jiran sa.
Daren ranar As’ad ya kasa rintsawa. Duk yadda ya juya kan gadon hotel ɗinsa, bacci ya ƙi zuwa. Sai zuciyarsa ta kasa nutsuwa, tana ta bugawa tamkar ana buga ganga.
A hankali ya ɗauki wayarsa, ya buɗe gallery, sai hoton Ramlah ya bayyana. Hoton da aka ɗauka ba tare da saninta ba lokacin da take shiga hall din jami’a. Yadda ta ɗaga ƙafarta cikin natsuwa, yadda hijjabinta ya lulluɓe ta da kwarjini, duk ya sa numfashinsa ya tsinke.
Ya kalli hoton nata sosai, yana jin wani irin sanyi ya ratsa jikinsa. Ya sauke wani nauyayyen numfashi haɗe da dukan zuciya mai daɗi. Tsigar jikinsa ta tashi, murmushi ya subuce masa.
“Ramlah…” ya faɗa cikin sanyi, yana jin sunanta ya kwanta masa tamkar zuma.
Idonsa ya tsaya kan bakinta. Kadan ne daga cikin hoton, amma ya ishe shi ya haddasa masa rudani. Sai ya yi tunanin yadda zata yi idan ta yi murmushi kusa da shi, ko idan bakinta ya furta sunansa cikin sirri. Sai zuciyarsa ta tsinke da wani irin farin ciki mai ban mamaki.
Ya ɗaga hannunsa kamar yana son taɓa hoton, yana jin tamkar tana tsaye a gabansa.
“Na tabbata wannan ba al’ada bace. Wannan soyayya ce ta gaskiya…”
Ya lumshe idanuwansa ya tuna yadda Mai Martaba ya gaya masa cewa sati mai zuwa za a kai sadaki, kuma a daura auren su. Zuciyarsa ta cika da farin ciki, ya ji tamkar ranar bata da nisa.
“Ni da ita a matsayin miji da mata. Ni da ita tare da ni a gidana, a kusa da zuciyata.”
Ya lumshe idanu yana jin yadda zuciyarsa ke kiran ta. Duk da shi babban mutum ne, mai daraja da iko, a wannan lokacin ya zama tamkar ƙaramin yaro da aka bawa abin da yake mafarki.
Cikin zuciya ya yi addu’a “Ya Allah, ka tabbatar min da ita cikin alkhairi. Ka sanya ta zama farin cikina, abokiyar rayuwata, kuma ka tsare mu daga duk sharri.”
Ya sake murmushi mai cike da kauna, ya rufe wayarsa ya rungume ta a ƙirjinsa tamkar yana rungumar ita kanta…
Nana hadiza
09030569336
[15/10, 3:25 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
*********
Zaune yake cikin katafaren gidansa da ke Dubai, falon kadai ka kallah kasan akwai dukiya ba kadan ba aciki Asad yana zaune a kan kujerarsa mai laushi, wayarsa a kunnensa yana hira da Hajja, mahaifiyarsa.
Muryarta cike da natsuwa da farin ciki take cewa “Asad, gaskiya an girmama mu sosai. Kowa yana fadin alkhairin yarinya naji dadi sosai da takasance nutsatsiya kuma mai hankali. Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya tsakaninka da Ramlatu.”
Sai kuma ta dan sauya murya cikin damuwa tace “Amma Asad, ina jin tsoro. Kai kasan ni mahaifiyarka ce, bana son yarinyata ta shiga cikin wahala ko zalunci akan aure dan haka wannan ma yarinyar inajinta kamar diyata Idan kasan bakada lafiyar kula da ita, dan Allah kar ka aureta. Banason yakasance kullum lamarinka yana bakin mutane Sunce cikakkiyar marainiya ce, bana son kaje ka aureta kana wahalar daita hakan ba tarbiya bace ace kowanne lokacin asirin gidanka a waje.”
Shiru Asad yayi na wasu sakanni, ya jingina da kujera yana goge fuskarsa da hankicif. Sai daga baya cikin natsuwa yace “In shaa Allahu, ranki ya daɗe. Ki kwantar da hankalinki. Bazan taɓa zama cikin masu zalunci ko son zuciya ba. Zan kula da ita yadda ya kamata kuma cikin ikon Allah ina fatan lafiya tasamu yanxu ranki yadade.”
Hajja ta sauke numfashi cikin jin dadi, tace “To mashaa Allah, Allah ya taimakeka Asad. Ina fatan alkhairi gareka. Amma fa, yaushe zaka taso gida?”
Asad ya dan murmusa yace “Zuwa nan da dare, In shaa Allahu. Ina so inyi wasu shirye-shirye kafin in taho.”
Tace “To Allah ya kiyaye hanya, ya tsareka daga sharrin mutane.”
Ya ce cikin ladabi “Amin Hajja. Na gode sosai.”
Ya kashe wayar yana kallon gilashin kofar da ke gabansa, zuciyarsa cike da tunani da nutsuwa. Duk da kalaman mahaifiyarsa, yana jin cewa ba zai taɓa juyawa daga niyyarsa ba auren Ramlatu tuni ya zama kaddararsa.
Bayan ya ajiye wayar, sai ga Nawal ta shigo falon cikin nutsuwa, tana da tsohon ciki da yake nuna cewa haihuwarta tana nan kusa. Tana shiga ta tsaya da girmamawa, sannan ta saki murmushi ta miƙa hannu tana aza nata cikin hannunsa.
Asad ya kalleta cikin tausayi da kulawa yace da ita “Baby, shine sai da kika fito? Ai nace miki ki huta, kiga cikin nan naki ko? Me yasa ba kya jin magana?”
Turo baki Nawal tayi kamar ƙaramar yarinya tace “Dady, inason ganin ka ne shiyasa. Kuma baka nuna min sabuwar mommy na ba. Kuma baka haɗa mu ba?”
Asad ya dan murmusa, yana girgiza kai yace “To ai nima bansan ta sosai ba tukuna, Nawal.”
Ta kwashe da dariya tace “Kai dady! Allah ya haɗaka da dukkan farin ciki tare da ita. In naganta zan gaya mata tayi sa’ar miji.”
Murmushi Asad yayi, yana kallonta da idon so yace “To yanzu me kike buƙata? Na san idan Nawal ta zo wajen dady, to akwai magana.”
Tace da dariya “Wallahi dady, babu komai. Banzo neman komai ba, kawai na zo in ganka ne. Kuma dan Allah kar ka hanani zuwa bikin nan, dole inzo.”
Asad ya gyara zamansa yace cikin natsuwa “A’a baby, ki zauna ki huta. Bayan bikin zamu zo tare, sai ki ganta. Ni yanzu ina da meeting a rana ta 6 da 8, kinga next week kenan ko.”
Nawal ta turo baki tace “To amma dady, fa sai aga kamar muna tayawa mamaah kishi. Gashi sis Amina ma tana da course ranar bikin, kaga kamar mu biyu bamuje ba.”
Ya saki murmushi yace “Bakomai baby, ki kwantar da hankalinki. Kiyi hakuri, ki kula da kanki sosai.”
Ta dan juya fuskarta tace da tausayi “Dady, please… kayi addu’a Allah ya baka farin ciki. Ka kula da kanka sosai. Ina son ganin kai cikin farin ciki, sosai.”
Asad ya kalleta cikin natsuwa, zuciyarsa ta lafa. Sai yace “Amin, baby. Allah yayi miki albarka, ya saukeki lafiya.”
Ta murmusa, ta tashi a hankali tana shafar cikinta tace “Amin dady, I love you.”
Ya murmusa shima yana kallonta har ta fita, zuciyarsa cike da soyayya da kuma natsuwar uba mai kula da iyalinsa.
**********
Da daddare na sauko daga sama da nufin na wuce gurin su anty na. Kafin in kai ƙofa, sai na ji Mom ta kwala min kira daga sitroom ɗinta. Cikin natsuwa na juya na shiga. Amma da idona ya sauka kan abin da ke gaban ta, gabana ya faɗi, jikina ya yi sanyi.
Na tsaya cak ina kallo akwatu na ne! An jera su a gefen ɗaki kusan sun ciye ko’ina cikin dakin, suna kyalli tamkar an fitar da su daga cikin fim. A hankali na fara bin su da ido, zuciyata na bugawa kamar ana danna ganguna. Ban san lokacin da kalmar ta subuce daga bakina ba na ce “Subhanallah… wannan fa?”
Sai matar Uncle Hamza ta murmusa ta ce “Duka naki ne, Auta!”
Na kasa magana. Na ci gaba da kallonsu, na fara kirga su ɗaya bayan ɗaya, sai na kasa kirga akwatunan ma gaba daya dozin huɗu kenan! Cikin zuciyata na faɗi “Yaa Allahu, yaa Rahmaanu!”
Mom ta kalle ni da murmushi tana faɗin “Auta, shock kika shiga kenan! Kin ga yanzu, kin dangwalo arziki. Allah ya sanya alkhairi a aurenki.”
Ban iya cewa komai ba, sai na ji hawayena suna gangarowa a hankali.
Sai matar Uncle Hamza ta ƙara da dariya ta ce “Ai harda sabuwar mota ma suka baki! Inajin price ɗinta yana tsakanin miliyan arba’in zuwa hamsin… ko ba haka ba Usman?”
Yaya Usman ya saki dariya yana kallon Mom ya ce “Ai gaskiya inajin tafi haka ma. Motar fa ba ƙarama bace,”
Suka yi dariya gaba ɗaya, hayaniya ta cika ɗakin. Ni kuwa na tsaya gefe ina murmushi cikin hawaye, zuciyata cike da godiya da mamaki Ban taɓa tsammanin haka ba akwatu, da mota sabuwa! Na sauke numfashi a hankali, na ce a raina “Allah ka sanya alkhairi, ka bani ikon zama mace tagari a gidan da zan shiga.”
Mom ta kalle ni tace da tausayi amma cikin natsuwa “Ki rage wannan kukan, Ramlatu. Lamarin Allah ne, ya wuce. Dukkan tunaninmu kishige. Ki je ki ci kazar nan da kankana, sannan ki hau sama ki jirani, zan zo yanzu.”
Na gyaɗa kai cikin ladabi nace,“To, Mom.”
Na nufi kitchen. Nan ma kowa fatan alkhairi yake min, wasu kuma suna kallona da harara. Hakan bai dame ni ba, sai kawai na ɗauki abincina na nufi dakin Umma da ke ƙasa.
A dakin, na tarar da Yaya Aliya, Mufeeda, da Zakiyya kowannensu yana zaune yana karanta littafi. Na kallesu cikin wasa nace “Wai ku ba za ku daina karatun nan ba ne?”
Yaya Aliya ta ɗan yi dariya tace “Kema fa na tura miki link din ArewaBook dinta, ki karanta littafinta. Sunanta Nana Diso, wallahi littafinta cike yake da darussa da fadakarwa. Ga dadi, ga soyayya. Baki isa kice kina karantawa baki amfana ba.”
Mufeeda ta ɗan jinjina kai tace “Ai gaskiya ne Ramlah. Ki karanta Rudin Zuciya ma shima nata littafin ne, yana da amfani sosai musamman ga irinmu masu sabon aure Zaki karu da ilimi akan zaman aure da rayuwa.”
Na yi shiru, ina ci abincina a hankali. Sai daga baya na ɗago nace “To, amma wai a ina zan samu littafin nan?”
Yaya Aliya ta amsa “Idan kina da wayar Android ko Chrome browser, sai ki je ArewaBook ko ArewaPen, ki yi searching da NanaDiso10. Za ki ga jerin littattafanta, ki zaɓi wanda kika fi so. Wallahi, ba zaki yi dana sanin karantawa ba. Zaki samu darussa masu yawa akan ilimin aure da zaman lafiya.”
Na murmusa nace “To, zan gwada insha Allahu. Amma yanzu dai bacci nake ji sosai. Bari na hau sama in kwanta.”
Suka kalle ni suna murmushi, kowanne yace “To, Amaryar mu ki huta.”
Na fice daga dakin cike da natsuwa, zuciyata tana sanyi da ƙaunar da suke nuna min.
******
Tun daga safiyar ranar Asabar aka fara rabon katin bikina. Gaba ɗaya gidanmu ya cika da hayaniya, dariya da annashuwa. Kowa cikin farin ciki yake, musamman manyan ’yan uwa da kawaye.
Akwatin katunan da aka kawo kuwa ba ƙarami ba ne zane ne mai launin zinariya da fari, an rubuta “Walimatul ‘Urs Asad & Ramlah” da kyakkyawar rubutu, har da tambarin gidan mu da na su. Katin yana da ƙamshi irin na turaren oud wanda tun daga nesa zaka ji kamshin shigar gidan masu ƙima .
Matar Uncle Hamza ce ta fara tsara yadda za a raba. Ita ce ta ce, Dole mu fara da dangin Abba da nasu mami, sannan mu wuce zuwa abokan aiki, daga baya sai na ƙawayen amarya.”
Ana ta rabon iv kowacce tagani sai ta yaba kyan iv din da kuma tsarinsa kana gani kasan na masu kudi ne bama sai anyi maka sharhi ba.