Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 19

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 19

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 19: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 19. Ranar gaba ɗaya gida ya cika da motoci masu hawa-hawa, saboda ana…

4,489 words

Ranar gaba ɗaya gida ya cika da motoci masu hawa-hawa, saboda ana fita da katuna zuwa gidan ‘yan uwa da abokai. Wasu kuma suka tafi kaiwa ofishin Abba da na su Asad.

Hajja kaltume kuwa tunda safe take ta karɓar kira daga yan uwa manyan abokan Abba, har da masu kira daga ƙasashen waje suna taya murna.

Bayan an kammala rabon katin biki, sai aka shiga sabon mataki rabo na anko kyauta. Wannan rabon kuwa ya fi komai ɗaukar hankali.

Tun safe aka fara shigo da akwatin kaya daga wajen ɗinki. Akwatuna ne masu launi, an rubuta “Team Amarya Ramlah & Asad 2025” da zane mai kyau An tsara ankon cikin nau’i daban-daban Ga na mata zanen lace mai launin mint green da gold, na maza shadda mai launin ruwan hoda mai sanyi, da bakin hula da ɗinki irin na manya. Ana shigowa da su a cikin manyan jaka, kowacce jaka tana ɗauke da sunan wanda aka tanada masa.

Matar Uncle Hamza ce ta ɗauka ta raba jama’a kashi-kashi akwai na dangin uwa, na dangin uba, na abokai, sannan na kawayen amarya.

Wani nishadi ne ya tashi a gidan. Kowa da yake karɓar nasa sai ka ga murmushi, ana yiwa juna dariya, “Lallai wannan biki ba ƙarami bane! Anko kyauta kuma super da manyan lace masu daukar ido! Allah ya saka da alkhairi.”

A ranar maryam kawata tazo da wasu friend dina wai har wayanda ma bama shiri sosai kowa sai shigemun yakeyi dan ace yasan mai biki anko kla biyi kyauta aka bawa kowa hatta kudin liki ya aiko dashi kowacce 100k cikin kawaye na nakasa fayyaci irin harkar girman da sukayi dan nikam bantaba gani ba sai dai naji labari.

Wasu cousin dina ne suka shiga kitchen basu san ina ta dayan bayan kitchem din ba nazo daukar tsumin da mom ta hadamun kaninfari ne da sassaken baure sai sassaken mangwaro da citta da kanjnfari da kankana da kwame wato baobab seed sai sugar ko zuma tunda nafara sha gaba daya jikina ya saki wani kasala nakeji… ina kokarin fita ta bayan kitchen din naji kareema tace wai habiba har yanxu baki samu numbarsa ba? Sai habiban tace ai wallahi kareema babu inda ban duba acikin wayarta ba banga numbarsa ba. Sai naji habiba tayi tsaki.tace ni wallahi Abunda yakawoni bikin nan kenan nasamu numbarsa nayi masa asiri ya aure ne ke bakiga harkar arzuki da wadata da yayi mata ba kinga motarta wallahi Allah kareema kamar na mutu dan bakin ciki…kasa motsi har suka bar kitchen din ina mamaki wato dai wannan rayuwar ba duk mai yimaka dariya bani ba masoyinka? Haka nakoma dakina kawayena sunata ɗaukar hotuna suna cewa “Team Amarya Let the countdown begin!”

Daga nan aka shirya ranar da za a saka ankon gaba ɗaya ranar ** kamu da dinner night. **

Sosai aka fara haɗaɗɗen shirin biki a gidan Mom. Tun daga ƙofar gida har cikin falon Mom, komai ya canza ana ta shige da fice, hayaniya da dariya kowacce hanya. Har yanzu dai Momy bata zo taga kayan lefen ba, amma Hajja Kaltume ta aika mata da dukkan kayan da aka tanada daga lefe, zuwa kayan bikin amarya, har da na kawayenta dama su iv.

Gaba ɗaya gidan ya koma tamkar wurin shirin fadar sarki. Kayan makeup, turaruka, abinci, da kayan dinki sun cika ko’ina. Ni kuma tun da safe aka fara yimun kitso sai kuma mai kunshi suka shigo suna yi min zane irin na manyan amare hatta kunshin ma sai da akasamu masu photograpy suka dauka shima daga gidan sarki aka turosu.

Gobe ne dai za a fara bikin, shi yasa yau komai yake tafiya da gaggawa. Gaskiya nagaji da zama saboda yanzu nayi ta gwajin din kayan dinkuna na da Abba ya bani dinkuna kusan kala ashirin (20), kowanne daban-daban daga lace, gown, material har zuwa aso-ebi na friends dinner.

Da gaske bana son wannan bidi’ar dinner, saboda bana sha’awar hayaniya, amma Mom ta dage tace, “Auta, dole sai an yi, tunda kowa zai gani. Wannan zamane yazo dashi, dole ayi komai cikin kyau da tsari.”

Sai kawai na yi murmushi, nace “To Mom,” saboda yanzu banida wacce tafita.

Nana hadiza

09030569336

[15/10, 6:09 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA ARBA'IN DA TARA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Duk kokarin da Momy ta yi na ɓoye hassadarta bai yi tasiri ba tun daga lokacin da ta ga lefen a waya take jin zafi a zuciyarta. Ko da Yaya Usman da sauran ‘yan uwa sun yi mata ta’aziyya, sai abin ya ƙara damunta. Ta yi ƙoƙarin neman lambar wayar As’ad amma Abba ba ya ajiye wayarsa gaba daya yadaina yarda daita kamar da hakan kuma ba ta iya samun damar da take so.

Ta zauna a kujera tana juyawa sakawa warware abubuwa ciƙin tunani sai lissafi take da hannunta tana jan tsaki ga zazzabi dake kokarin kwamtar da’ita Ba da daɗewa ba sai Abba ya dawo gida gidan, ya shigo da wasu manyan akwatuna masu tarin kaya aciki. Ya tsaya, ya yi sallama, sannan ya ajiye kayan yana kallon Momy da wata fuska yana murmushi sosai lokaci guda kuma da damuwa akasan ransa.

Abba ya zauna kusa da ita, ya ce cikin natsuwa “Jiya na gaya miki, ai zaaje gidan auta. Kin ce baki jin dadi, amma yau an gama jerin gidaje gidan nata babbane sosai acikin umguwar da sarki yake sannan kuma nashi sashen yafi na duk yaran gidan gaskiya, sai gidanta a birni. Hamza ya shirya komai, gobe zan je in gani.”

Momy ta ɗan kalleshi sannan ta ajiye ajiyar zuciya sannan tace “Allah ya sanya alkhairi, Abba. Jiki na kuwa bai daɗi sosai zazzabin ke rufeni kamar na wadi nake ji. Amma in har naji sauki zuwa gobe me zai hana ai sai in je ko?.”

Abba ya ɗan yi murmushi, ya shafa fuskarta da tausayi “To, Allah ya ba ki lafiya. Ni kuma zan tafi yanzu, ina da abubuwan da zan gani akwai abubuwa da nake son gyarawa kafin bikin.”

Momy ta yi shiru na ɗan lokaci, idanunta sun cika da damuwa. Ta yi ƙoƙarin boye takaicin zuciyarta, amma a ranta tana tunanin yadda za ta samu dama ta tsara yadda za a hana wannan auren ko a rage tasirinsa. Ta san cewa ba zatayi nasara ba ganin yadda kowa ya dauki auren da mahimmanci da kuma uban kudin da suke kashewa.

A gefe guda, zuciyarta tana cike da fargaba idan har wani abu bai faru ba tabbas zatashiga damuwa kuma zataji kamar ta mutu dan bakin ciki. Amma ta ƙyale kawai yau ko karfe dayan dare ne zata jira ta yaudareshi ta dauki numbarsa tana fata da roƙon Allah yabata hikima.

*****

Tsaye Bilkisu take bakin babban dandamalin garin wanda babu wasu mutanen kirki agurin sai ƴan shaye shaye itama wani abokinta ne ya haɗata dasu ya tabbatar mata duk wani shaidancin da takeso ayi mata salisu shine karshe. Wani dattijo mai ɗauke da shadda wacce taa tsufa ke zaune a can tsakiyar dandamalin, fuskarsa cike da girma da shakku. Idonsa ya zuba mata, yana kallonta daga sama har ƙasa da wancan irin kallon da ke iya karya ƙarfin zuciya.

“Ke yanzu,” ya ce da murya mai zurfi, “kin samu kuɗin biyanmu kuwa?”

Bilkisu ta yi murmushi ba irin murmushin farin ciki ba, sai irin wanda ke ɓoye mugun nufi. Ta bude jakarta cikin natsuwa, ta dauko rafar kuɗi sabbi, ta ajiye a gabansa. “Wannan kaɗan kenan, Salisu. Idan kuka yi min aikin yadda nake so, ina tabbatar maka da ninkin wannan, guda biyar,” ta ce tana kallon idonsa kai tsaye.

Ta dan ja numfashi, ta matsa kusa. “Ina so ku sace ta. Idan kun sace ta, ku kashe ta. Ku jefa gawarta cikin ruwa yadda babu wanda zai ji duriyarta. Wannan ne katin bikin, ga kuma adireshin komai. Don Allah, Salisu, kada asamu matsala.”

Salisu ya ɗauki katin, ya dubi hoton da ke hannunta hoton mace kyakkyawa da idanu masu kyan gaske, Ya lumshe ido, yana jin nauyin abin da zai aikata kamin ya kasheta dan wannan dole yaji dadi da’ita

“Ranki yaɗade,” ya ce cikin taushin murya, “bukatarki tabiya. Kisa a ranki an kasheta, an gama.”

Bilkisu ta miƙa hoton, ta sake jaddada: “Ga ta nan wannan ita ce amaryar Salisu. Kada ku bani matsala. Ka san hatsarina.”

Salisu ya gyara zama, ya kada kai. “Ki kwantar da hankalinki. Ba za ki taɓa jin matsala ba. Ki ɗauka aikin ya kammala.”

“Na gode,” ta ce da dariyar mugunta, ta juya tana barin wurin cikin isa. Rana na dusashewa, ƙura na ta motsi a cikin iska, ko kadan batajin tsoron irin sharrin data shirya.

A zuciyarta, ta yi murmushi yau zata koma gidan Hajiya Kaltume domin a gabatar da komai na bikin akan idonta, ta ga yadda za su fara bikin walima gobe. Ta san wurin zai cika da mutane, da dariya, da kida, amma ita kadai ta san abin da ke ɓoye a ƙasan. Idan komai ya tafi daidai, daga gobe Ramlah ba za ta sake bude ido ba.

“Idan aka kashe ta tabbas ni ce za a aura wa Asad.” Ta lumshe ido, ta ji wani irin daɗi mai ɗaci ya ratsa zuciyarta. Kwayar da ta ba su za su saka mata a baki idan ta mutu, babu wanda zai taɓa gano me ya faru.

Da wannan tunani, ta nufi gida kai tsaye. Ba ta tsaya ko ina ba, saboda zuciyarta ta riga ta yanke hukunci.

Da ta shiga gida, ta tarar da Momy a zaune tana duba wayarta. Da ta ji ƙarar ƙofa, ta ɗago kai cikin sauri.

“Wai ina kika je ne, Bilkisu? Tun da safe nake neman ki.”

Bilkisu ta yi murmushi, tana son boye fargabar da ke zuciyarta. “Ba koina, Momy. Na dan je gidan kawata ne kawai.”

Momy ta kalle ta da kallon rashin yarda, tana girgiza kai. “Kinga Bilkisu, wallahi ki kiyaye sosai. Na gaya miki, kada ki jawo mana wata masifa. Ina jin zuciyata tana min wani abu daban wanda kuma ban yarda dake ba.”

Ta yi shiru na ɗan lokaci, sai Bilkisu ta ce cikin muryar da ta yi kama da tayi laushi “Ni fa, Momy, na hakura. Allah ya kaddara ba mijina bane. Yanzu ma can gurinsu zan tafi, kawai in ga yadda ake shirin biki.”

Momy ta numfasa. “To shikenan. Ko kefa, dama ganinki adamuwa ne, shiyasa nake shiga damuwa nima, zan biyo baya idan na gama abinda nake.”

Bilkisu ta yi murmushi, tana kallonta cikin ido. A cikin ranta ta shiga magana “Sai dai idan ba jininki ce ni ba… amma wallahi, wallahi sai na ɗauki mataki da kaina.”

Ta jawo jakar ta, ta fita daga ɗaki, zuciyarta cike da shirin mugunta.

*******

Hajiya Kaltume ce ta taso ni , tana cewa in bar dakina in koma nata. Ta ce yanzu mutane sun zama abin tsoro, bata yarda da kowa ba Na ga tsoron da yake cikin fuskarta, shiyasa ban yi musu ba. Ta ce za ta bar kawayen Nawa tare da Yaya Aliya, ni kuma mu kwana tare a nata dakinta.

Na shiga dakinta cikin nutsuwa. Na cire hijab ɗina, na nufi bandaki na yi wanka. Ruwan zafi na ta sauka a jikina kamar yana goge duk wani tunani daga zuciyata. Na jima ina jin daɗin ruwan, ina tunanin abubuwa da dama tun daga shigowata gidan nan har zuwa irin shisshigin da nake gani a kullum wayanda basa kaunata adangin abba kowanne yanzu nunamun kauna yakeyi ana wani jana ajiki.

Akwai wani abu daban a gidan Hajiya Kaltume Wani sirri da ba kowa ke amfani dashi ba wato amfani da ruwan dumi abun tsarkinta na bandaki ma ruwan dumi ne aciki tunda nazo takemun fada akan na tabbatar kowanne lokaci ina amfani dashi . Tun farko ina jin kunyar ta sosai, amma yanzu kunyar ta fara gushewa, saboda yadda take nuna kulawa agareni sosai wallahi tamkar mahaifiyata sai nace dama tun farko itace ta karbeni.

Da na fito daga bandaki, sai ta shigo da murmushi a fuskarta.

“Wanka kika yi, Auta?” ta tambaye ni cikin taushin murya.

Na ce, “Eh, Mom, yanzu na fito.”

Ta ce, “To, yi sauri. Ki tafi sashen Baba, akwai bako yana jiran ki. Ga wannan red abaya ki sa, ki sa turare ma, don Allah ki yi sauri.”

Na so in tambaye ta wanene? amma sai na ji kamar bai dace ba, saboda yadda ta ke kallona da murmushi. Don haka kawai na ce, “To, Mom,” na ɗauki abayar na sa.

Na fesa turare, zuciyata tana bugawa a hankali. Na fito daga dakin cikin hanzari, na nufi sashen Baba kamar yadda ta umarta.

Da na isa harabar gidan, sai na tsaya na dubi ko’ina. Gidan ya cika da haske da motoci. Aƙalla motoci goma ne a jere, kowacce da masu tsaro a gefenta. Sautin takalmina na tashi a bene mai santsi, zuciyata kuma tana ta bugawa ba tare da sanin dalili ba.

Na karasa bakin ƙofar babban falo, na ɗan yi sallama a hankali. Na ji muryar da na sani tana cewa, “Shigo mana.”

Da na tura ƙofar, na shiga ciki. Idona ya sauka kan Yaya Usman da yake tsaye kusa da kujera yana duba agogo. Na tsaya cak.

“Yaya, kai ne?” na tambaya cikin mamaki.

Ya ɗago ya dubeni da ido, ya dan murmusa kadan. “Eh, ni ne. Ki yi sauri ki shiga ciki, yana jiran ki tun dazu. Kin san halinsa baya son jira.”

Na ji jikina ya saki. Wani irin sanyi ya ratsa jikina. Na ɗan dubi ƙofar da ke gaba, zuciyata ta cika da tambayoyi. Waye yake jira? Me yasa nake jin tsoro?

Na taka a hankali zuwa cikin falon, zuciyata na harbawa kamar ta so fito daga ƙirji.

Nana hadiza

09030569336

[16/10, 11:26 am] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Cikin sanyi na karasa babban falon. Bakina cike da sallama, na tura ƙofar a hankali.

Wani kamshin turare mai daɗi ya bugi hancina, har sai da zuciyata ta ɗan buga Dakin ya cika da iskar Ac mai sanyi, hasken fitila na haskawa. Da na ɗaga kai, idona ya sauka kansa.Yana zaune a kan kujera, sanye da farin kaya P.A ɗinsa na kusa da shi, yana nuna masa takardu.Na tsaya na kasa motsi, kamar ƙafafuna sun tsaya a wuri. Wani abu ya ratsa zuciyata wani irin shauƙi da tsoro a lokaci guda. Sai na ji P.A ɗin ya ce, “Okay, sir,” ya miƙe ya fita, sai zuciyata ta ƙara bugawa da ƙarfi. Na ji kamar duniya ta rage mutum biyu ni da shi. Na taka a hankali na shiga cikin dakin, na tsaya a kan carpet.

“Assalamu alaikum,” na faɗa cikin murya mai sanyi, sannan na zauna. Bai amsa ba. Sai kawai na ji shiru, sai numfashinsa da nawa ne suke haduwa cikin iska mai sanyi. Na daure, cikin rawar murya na ce, “In wuni.”

Ya ɗago kansa a hankali, idanunsa suka haɗu da nawa. Wani irin nutsuwa da sanyi ne suka lullube ni. Da muryarsa mai zurfi, wacce rabona da jin irinta tun da yakirani rannan, ya ce “You keep us waiting.”

Maganar tasa ta sa jikina ya ɗan yi sanyi. Ba tare da niyyar magana ba, sai kawai kalmar ta fito daga bakina “Kayi haƙuri, don Allah.”

Ya murmusa kadan, yana kallona kai tsaye, ya ce “Okay. Na zo ne in ganki, ki yi haƙuri wannan watan abubuwa sun min yawa. Na kasa samun lokaci sai yanzu.” Ya ɗan lumshe ido, sannan cikin ƙasaita ya ƙara da cewa “Ko gobe ma inada meeting, nayi cancel na yau ne saboda naxo na ganki.”

Wani sanyi ya ratsa zuciyata. Ban san me zan ce ba. Sai kawai na tsaya da hannuna a cinyata, na rasa abin cewa. Ya dan gyara zama, yana kallona sosai, kamar yana karanta tunanina. “Kayan da aka kawo miki… sun miki kyau kuwa ko akwai abunda kike bukatar kari?”

Na ɗago kai da sauri, sai kuma na lumshe ido, na kasa kallonsa. Maganar ta fita a ransa kamar wasa,ni mamaki nake wai uban kayan da aka kawomun ake tambayata sunyimun? Ikon Allah masu kudi suna shagalinsu wallahi.

Sai na ji muryarsa a hankali yace“Tell me… me kike buƙata?”

Cikin murya mai sanyi na ce, “Babu abin da nake buƙata.”

Ya ɗan yi shiru, idanunsa suna yawo a fuskata, daga idona zuwa lebuna. Wani irin yanayi ya rufe dakin amma zuciyata na fassara shiru da tsoronsa danake ji.

Sai ya ce, “Na ga IV ɗinku. Zan saka masu tsaro su kula da komai. Idan za a kai ki wani wuri, ki kira ni kai tsaye. Ba na son kowa ya tuka ki banda wanda zan turo zasu zauna anan duk abunda zakuyi har sai an kawoki gidana.”

A lokacin da yake magana, muryarsa ta yi sanyi sosai, har sai da tana kallesa saboda yadda naji. Idanunsa sun manne da nawa.Na kasa magana. Sai kawai na ɗan murmusa, ina jin zuciyata na tafarfasa da abu mai tsoro.

“Na gode,” na ce a hankali, murya na rawa. Sai ya murmusa a hankali, yana cewa “I don’t know why… but every time I see you, I forget the world.”

Wannan kalmar tasa ta tsaya a kunnena, kamar waka. Zuciyata ta buga, sai da na lumshe ido. Na kasa kallonsa kai tsaye. Idanuna na kasa, hannuwana a haɗe a gwiwata, zuciyata na bugawa kamar ana busa gangi a ciki.

Na ji shi ya gyara zamansa a hankali, kujerar ta yi ɗanyi ƙara. Iskar dakin ta canza, kamar AC ɗin ya sake ƙara sanyi. Amma a jikina, babu wani sanyi zafi nake ji, irin wanda yake fitowa daga zuciyar mutum da yake ƙoƙarin ɓoye abin da yake ji.

Na ɗago kai a hankali, idanuna suka haɗu da nasa. Idanunsa sun yi duhu kamar ruwa a cikin dare, suna kallona tamkar zai karanta tunanina. Sai na saukar da kai cikin kunya.

Na ɗago kai a hankali, zuciyata na dukan bugun da ban taɓa ji ba. Idanuna suka haɗu da nasa kuma a wannan lokacin naji wanj tsoro ganin yadda yake kallona sosai daga sama har kasa. “Ba ki san yadda nake ji ba,” ya ce cikin murya mai sanyi.

“Tun ranar farko da na ganki, hankalina ya kasa natsuwa. Kullum, ina so in sake ganin idonki.”

Zuciyata ta yi wani irin bugu. Na ji jikina ya saki, numfashina ya ƙi fita yadda ya kamata.

Na kasa magana. Sai kawai idanuna suka fara cika da ruwa.

Cikin ladabi na ɗaga kaina na kalle shi. Fuskar sa cike take da kwarjini, idanuwansa kuma suna da wani irin sanyi da ke ratsa zuciya kai tsaye. Duk da yake bai amsa sallamata ba, amma yadda yake tsaye, cikin natsuwa da kamala sai ka rantse da Allah cewa mutum ne da yake magana da zuciyarsa kafin yai da bakinsa.

Amma ina roƙonki, Bana son dinkin da zai bayyana jiki kikiyaye.”

Na yi mamakin yadda kalmar ta fita daga bakinsa cikin ladabi, amma har yanzu yana kallona. Idanunsa suka ɗan lumshe.

“Zan tafi yanzu,” na ce a hankali, “zan kira ki daga baya.”

Ya ɗan ɗaga kai yana murmushi ƙasa-ƙasa, yana faɗin

“Toh, sai da safe.”

A hankali nace masa Allah yakaimu bayan fitarsa nasaki numfashi sannan namike na nufi sashen mom duk yawanci an kwanta a palon kasa na sameta suna aiki nace mom na dawo. Hararata tayi tace ba dai haka kikaje ba kin turbune fuska kamar kunu cikin sanyin jiki naje aa mom. Fara’a dai kara miki kyau takeyi wannan rashin murmushin baya sanyaki kiyi kyau.” Murmushi kawai nayiwa mom bance komai ba na lika dakina naga duk kawayena wasu sunyi bacci.

Bayan na hau sama na shiga ɗaki, sai na cire kayan jikina na saka rigar bacci mai launin baby blue.. Na shimfiɗa kaina a filo, na rufe idanuwana cikin gajiya zuciyata cike da tunanin abinda ya faru a falon, muryarsa, yadda yake faɗin “I forget the world when I see you.”

Na rufe idona, amma hotonsa ya ci gaba da yawo a cikin tunanina..

Kafin numfashina ya daidaita, sai naji wayata ta fara ringing.Wayata na ta ringing. Sabuwar number, babu suna so special Zuciyarta ta buga sau uku kafin na iya ɗagawa..

Muryarsa ta fito a hankali mai sanyi, mai sarrafa numfashi. Sai naji yace “Finally… you picked up.”

Na kasa magana, ina sauraron yadda muryarsa ke nutsewa cikin kunnena kamar “I didn’t mean to wake you,”

ya ce cikin sanyin murya,

“but I just couldn’t sleep… not without hearing you, My Euphoria.”

Zuciyarta ta tsaya.

Numfashinta ya canza.

Kalaman sun ratsani har cikin jinin jikinta.

“who is this? Na tambaya, muryarta na rawa.

Sai murmushi ya biyo bayan shiru.

“The one who’s been losing sleep… because of you.”

Shiru ya sake mamaye tsakaninmu. Kawai ina jin saukar numfashina da nasa, suna haduwa a cikin layin kamar muna tsaye kusa da juna.

“Sleep well,”

ya faɗa a ƙarshe,

“and if you dream… dream of me.”

Call ɗin ya katse.

Zuciyata kuwa ta kasa sake komawa bacci...

*******

Fitilun mansion ɗinsa suna kunne, suna haskaka dukkanin bangaren nasa inda masu tsaro suke ko’ina asashen gidan.

Yana ciƙin daya daga cikin hadaddun dakunan sa da yafi kwanciya aciki wanda gaba daya an canza fasalinsu yanzu komai dake amsa suna sabo ne aciki.AC na busa sanyi, amma jikinsa zafi yake ji irin zafin da ba daga jiki yake fitowa ba, daga zuciya yake tasowa. Yana kwance a kan gadonsa mai faɗin da ya isa mutum biyar, hannunsa ɗaya a bayan kansa, ɗaya a cikin gashin kansa. Idanunsa suna kallon rufin, amma zuciyarsa tana kallon fuskarta.Kowane ƙaramar kalmarta, kowane kallon kunya da ta yi masa, suna yawo a cikin kwakwalwarsa tunda yadawo. Har zuwa ƙarfe biyu na dare, Asad bai iya bacci ba.

Yana juyawa a kan gadonsa, idanuwansa a rufe, amma tunaninsa yana kara yawa sosai ba kuma akan kowa bace ba face ramlah.

Hotonta ke yawo a idonsa yadda ta shigo falon cikin kunya, yadda ta kasa kallonsa kai tsaye, muryarta mai sanyi tana cewa “Kayi haƙuri don Allah.” Ya juyo gefe, ya sauke numfashi mai nauyi. Zuciyarsa ta cika da wani iri-irin sanyi mai daɗi feeling da bai san ta yadda yake taso masa ba. Ya daɗe da sanin ƙauna, amma wannan daban ce “Why her?” ya tambayi kansa cikin raɗa, yana murmushi kadan. “Why does everything else fade when I think of her?”

Sai ya miƙe daga gadon cikin natsuwa, ya nufi bandaki, ya ɗauro alwala da ruwan dumi.

Yayinda ruwan ke sauka a fuskarsa, zuciyarsa ta ji sanyi irin sanyi mai sa ka tuna cewa kai bawa ne, ba sarki ba.

Nana hadiza

09030569336

[16/10, 4:40 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA DAYA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Ya fito ya shimfiɗa dadduma a tsakiyar daki.

Fitilun gold lamp biyu ne kawai suke haskawa suka ba wa dakin hasken mai kyan gaske.

Yayi sallah cikin nutsuwa, kowanne sallah yana yi cike da tsoron Allah da cikakken tauhidi

A cikin sujuda ya tsaya na ɗan lokaci, zuciyarsa ta yi nauyi haɗe da yiwa Allah godiya. “Ya Allah, katabbatar mana da alheri aciƙin wannan aurem ka sanya albarka acikin Ka hada mu cikin halal, ka sanya soyayyarta ta zama silar kusancina da kai.” Kalmar “amin” ta fito daga bakinsa a hankali kamar hucin zuciya. Bayan sallah, ya zauna a kan dadduma, hannayensa biyu suna ɗaure da masbaha mai kyan gaske ko’ina na daƙin yana fitar da kamshi sosai Ya fara tasbihi cikin sanyi, kowanne subhanallah yana sauka a bakinsa cikin jin daɗi, kamar yana karanta sunan ta cikin sunayen Allah.

Iskar AC ta busa gashin kansa, amma a zuciyarsa akwai sanyi mai cike da natsuwa.

Daren da farko ya fara da wuta ta soyayya, yanzu ya koma cikin natsuwar ibada soyayya zuwa addu’a.

A hankali ya miƙe, ya je ya tsaya a gaban taga yana kallon sararin samaniya.

Hasken wata na faɗowa kan fuskar sa, yana haskaka idonsa masu nutsuwa da zurfin tunani.

“Allahumma barik fi hadhal hubb…” ya furta cikin nutsuwa, yana kallon sama.

“Ka sanya albarka a wannan soyayya, idan har ita ce kaddarata.”

Sai ya ɗan murmusa, Ya koma gadonsa cikin natsuwa, ya kwanta yana jin sanyi mai cike da farin ciki. Idanunsa suka lumshe a hankali,

zuciyarsa tana maimaita sunanta.

Da haka bacci ya fara shigarsa ba irin baccin gajiya ba, baccin natsuwar da zuciyar masoyi ke samu bayan ya roƙi Allah.

******

Tun bayan sallar asuba, jikinsa ya dauki nauyi. Zazzabi ya lullube shi gaba ɗaya amma ba irin wanda ake ganin sauki a kansa ba. Wannan nau’in da yake fita daga zuciya, wanda yake haɗa zafin jiki da nauyin tunani.

Da farko, ya yi ƙoƙarin yin tafiya a cikin falonsa, amma ƙafafunsa suka gaza ɗaukar nauyinsa. Sai ya koma kan royal couch ɗinsa, ya jingina, idanuwansa a rufe, hannunsa a goshinsa. Numfashinsa Nafidda wani tururin zafi.Iskar AC tana busawa da sanyi, tana motsa labbansa a hankali, amma shi kamar tana ƙara masa zafi ne.

Zazzabi ya ratsa shi daga ƙafa har kai, kamar ana zuba masa wuta a cikin jini.

Har lokacin da masu gyaran sashi suka iso don kula da bangaren, babu wanda ya samu shiga. Kofar falon nasa a rufe take tsarin gidan sarauta, sai da izini.

PA ɗinsa, Salis, ya zo sau biyu yana danna maɓallin shiga, yana kiran sunan mai gidansa cikin ladabi “Your Highness… are you alright, sir?” Shiru. Sai dai numfashi daga cikin ɗaki.

Ya sake bugawa da natsuwa, “Should I call the doctor, sir?” Shiru har yanzu.

Sai bayan kiran waya na uku, muryar Asad ta fito mai sanyi, amma cike da rauni da iko “Tell him to come… and don’t let anyone in.”

Wani sanyi ya ratsa Salis, saboda yadda muryar tasa ta fito cikin natsuwar da ba a saba jin irinta ba. Ya san maigidan nasa da jarumta.

Da labarin ya isa wajen Hajja mahaifiyarsa hankalinta ya tashi. Ba tare da sanar da Sarki ba, ta bar komai ta nufi bangaren Asad cikin hanzari. Masu tsaron kofar suka tsaya cikin girmamawa, amma sai ta ɗaga hannunta cikin iko “Ku ba ni hanya.”

Da ta shiga, ta tsaya cak.

Falon gaba ɗaya yana cike da iska mai sanyi, amma a idonta, ta ga zafin da ke ratsa jikinsa.

Asad yana kwance, ya lullube da bargo baki, hannunsa daya a gefe, numfashinsa kuma yana fita a hankali kamar yana shan iska da ƙyar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull