Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 20

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 20

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 20: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 20. “Asad…” ta kira cikin murya mai rauni, tana matsowa kusa da shi.…

4,434 words

“Asad…” ta kira cikin murya mai rauni, tana matsowa kusa da shi. “Me yake damunka ne?.”

Ta kamo hannunsa, amma sai ta ji zafi jikinsa kamar wuta! “Ya Allah,” ta furta, hawaye na cika idonta. “An kira likita?”

Salis ya duƙa da girmamawa, “Eh, Hajja. Yana hanya.”

Nan Abba da Firdausi suka shigo da sauri. Fuskar Abba ta nuna tashin hankali, Firdausi kuma ta tsaya bakin ƙofa tana kallon ɗan’uwanta da ba ta taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba.

Lokacin da doctor personal ɗinsa ya shigo, ko motsi bai yi ba. Likitan ya duƙa da girmamawa, yana karɓar umarnin da babu wanda ya furta. Kallon da Asad ya yi masa kawai ya isa a matsayin magana.

“Sir, your temperature is high…”

Muryar likitan ta fita cikin girmamawa, hannunsa na rike da allura da kwayoyi.

Asad bai amsa ba. Idanunsa na bude kadan, yana kallon sama — hasken fitilun suna walƙiya a saman kansa. Duk cikin ɗakin sai kamshin turare mai sanyi da yake tashi.

Likita ya saka masa drip, ya danna allurar zazzabi a hannunsa, sannan ya gyara bargo a jikinsa. “Zan dawo sir, idan yanayin ya sauya.”

A lokacin ne aka buɗe ƙofar da sautin ƙafar takalman mata masu daraja.

Amaryar Sarki Hajja Zainab, matar farko ta shigo cikin nutsuwa, hannunta ɗauke da royal fan. Sai kuma sauran matan fadawa suka biyo bayanta, suna sanye da kayan aso-oke masu haske.

Da suka hango falon nasa, sai kowacce ta tsaya cak.

Idan kika dubi sashin, ba kamar sauran gidan ba. Ginin nasa daban yake kamar villa a cikin fada. Wani hotonsa na gefen dakin, kuma a tsakiyarsa Asad, sanye da farin rigar sarauta, yana kwance cikin natsuwa, idonsa a rufe.

Amaryar sarki ta kalli dakin tana mamaki.

“Subhanallah… wannan sashi kamar ba cikin gidan nan ba,” ta ce cikin murmushi.

“Haduwar sa, har yafi gidan Sultan.”

Wata daga cikin matan fadawa ta yi dariya mai natsuwa, tana cewa “Ke dai goggo, ai mai kudin garin ne fa. Tayaya za ki ga sashinsa kasa da haka?”

Amma bata tanka ba. Idanunta kawai suka tsaya kan Asad. Fuskar sa ta cika da wata irin nutsuwa.

Sai murya ta fito daga bayan labule Mai Martaba Sarki ne ya shigo, da alama an sanar masa. Ko da ya kalli ɗansa, sai ya tsaya na ɗan lokaci, fuskar sa a nutse.

“Ku barni dashi,” ya ce cikin murya mai sanyi, amma cike da iko. Nan take, matan suka sunkuyar da kai, kowacce ta fice da girmamawa. Koda suka fita, harabar sashin ta cika da shiru da tsoron fadawa babu wanda ke magana, babu wanda ke motsi, sai guard da ke tsaye da dogon rigar sarauta, hannunsu a bisa takubba.

A cikin ɗakin, Sarki ya ƙarasa kusa da shi, ya zauna a kujerar da ke gefe. “Asad…”

Ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli mahaifinsa.

Idanun sa sun yi ja, amma ba saboda ciwo kadai ba akwai wani abu mai zurfi a cikinsu, kamar ciwon da zuciya ke yi idan tana rikicewa da soyayya.

“Bana jin daɗi,” Asad ya faɗa cikin ƙasa da murya. “Jikina kamar wuta.”

Sarki ya lumshe ido kadan, yana kallonsa da tausayi da izza iri ɗaya.

“Jikinka ne ke ciwo, ko zuciyarka?”

Asad bai tanka ba. Amma yadda ya sauke numfashi, ya rufe idanu, ya isa amsa.

“Na san kai ba mai saurin yin rauni bane,”

Sarki ya cigaba, yana kallon ɗan nasa wanda duniya ke jin tsoron sa.

“Amma akwai ciwon da babu maganin likita… sai maganin zuciya.”

Asad ya juya kansa gefe, yana ƙoƙarin boye murmushi mai rauni. “Bana son magana yanzu.” Sarki ya miƙe, ya dora hannunsa kan kafadarsa.

“Ka huta, Asad. Jikinka zai warke, amma ka kula da zuciyarka kada ta zama silar raunin ka.”

Da ya fita, dakin ya sake komawa cikin shiru.

Sai kukan clock wall kawai ake ji, yana danna lokaci cikin natsuwa.

Bayan kowa ya fita daga sashin, ɗakin ya sake yin wani irin shiru mai nauyi

Asad ya rage numfashi a hankali, hannunsa ɗaya har yanzu yana sanye da drip, ɗayan kuma ya jingina a kan ƙirjinsa.

Zuciyarsa ta shiga wani yanayi da ba zai iya fassara ba.

Wani irin zafi ne ke ratsa jikinsa ba irin zafin jiki na zazzaɓi ba, wannan zafin yana fitowa ne daga zuciya zuwa jini.

Numfashinsa ya fara yin nauyi, fuskarsa ta ɗauki wani kalar haske mai haɗin gajiya da rikici.

Yaji kamar ana kiransa daga wani nesa, amma ba tare da murya ba kamar wata softer presence ce ke tsayawa kusa da shi tana kiran sunansa cikin zuciya.

Sai ya runtse ido da ƙarfi, hannunsa ya matse lallausan bargonsa.

A hankali jikinsa ya fara girgiza, wani irin feeling da zaice baitaba ji fa yataso masa ga wani irin sanyi da zafi suna haduwa a cikinsa kamar rikicin ruwa da wuta.

Yaji wani nauyi ya sauka a kirjin nasa, yana nishi cikin ƙasa da murya “Subhanallah…”

Cikin wannan yanayi, allurar da akai masa ta fara aiki. Sai jikinsa ya fara sauka a hankali.

Nana hadiza

09030569336

[16/10, 4:40 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA BIYU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Tunda muka farka da safe, gidanmu ya kacame da hayaniya. Anata hira da hidimar biki kai naga ikon Allah yadda kowa yado da kuma kaffa kaffa kada su bata tsari daman wani kawuna yacemun da yake mai kudi zan aura gashinan kowannen su yazo.

Kowanne sashe na gidan anata harkar abinci duba da masu abincin ma hajja kaltume ce ta dakko su daman da sassafe abba ya yanka sa da raguna biyu da zaayi jibi na abincin wuni.

A harabar gidan, ana gyara canopy, wasu suna jera souvenir, wasu kuma suna tsugunne suna soya nama. Kallon yadda kowa ke ta zirga-zirga nayi Abu ɗaya ne kawai ke zagaye a cikin zuciyata kakata.

Wacce har yanzu ban ji muryarta ba, balle in ganta shekaru sun ja abba baikai niba itama bata nemi ni ba amma ai bikina akeyi bai kamata baa sanar dasu ba.

Na jingina a jikin bango, hannuna riƙe da Tea mug, idanuna suna bin yadda Yaya Billy take ta faman tafiya tana bada umarni.

Kallon da take jifana da shi, sai ka rantse bata tsaneni ba nasan duk wannan hudubar mumy ce. Duk surutunta da nuna tana sona Amma ban kulata ba, ban da karfin zuciya yau

Sai kawai ta ƙaraso ta tsaya gabana, ta ce cikin murmushi “Ya kamata ki dan kwantar da hankalinki yau fa ranar bikin ki ce naga sai faman ɓata rai kikeyi.”

Na dan murmusa murmushin da bai kai ba.

“Yaya Billy, biki fa ba yana nufin babu abin da yake damuna ba.”

Ta dan yi shiru, ta juya tana cewa, “To dai nasaka a kawo breakfast gashinan kar inzo na same ki baki ci komai.”

Na tsaya na kalleta tana tafiya da heels ɗinta mai sauti, ta zauna tare da sauran manyan aunties suna dariya suna shan lemon aya da akayi kamar babu komai aciƙin ranta.

Na kalli tray ɗin breakfast da aka kawo min, amma cikina ya ƙi karɓa.

Sai na tashi a hankali na nufi inda Mumy take.

Tana zaune a babban royal couch, waya a kunnenta, tana magana da wata irin murya da ke mace mai iko da kuma kula da gida da girma. Na tsaya har ta gama, sai ta ɗago idanunta ta kalle ni.

Cikin nutsuwar da take da ita ta ce, “Auta, lafiya? Me yasa idonki duk yayi ja haka?”

Bansan lokacin da hawaye suka fara sauka a kuncina ba. Na kasa amsawa, sai kawai na furta cikin muryar da ta cika da rauni,

“Mamah… nake missing.”

Nan take ta aje wayar, ta kamo hannuna.

“Shine kike kuka? Auta kefa ba yarinya bace. Yanzu fa kin girma Amma gaskiya, abbanki bai kyauta ba… shi yajawo haka da tunfari bai ja rigima dasu ba inada tabbacin zasu nemiki”

Sai ta ja dogon numfashi, tana dubana “Mun kasa nemota, Auta. Mun kira amma babu wanda ya sameta. Har Usman ya turo ma wani bawan Allah a Dubai ya bincika… sai matar sa tace tana da masaniya da gidan kawjnkj. Da iznin Allah zasu kai mata sako yau.”

Na share hawayena a hankali, na ce “Na gode, Mumy.”

Ta shafi kuncina, tana cewa, “Kuskurene abbanki yayi, amma komai da dalili. Kinji ko? Kar ki bari hakan ya bata miki wannan rana. Nasan indai suna kasar zasuzo.”

Ina jin kalamanta suna ratsa zuciyata, amma har yanzu kamar ana tsaga ta da wuka.

Na zauna gefenta, hannuna riƙe da nata.

Sai dai kafin in sake numfashi, na ji anty Luba ta shigo da wata irin muryar wai ita alallai mai kaunata “ Amaryar mu da second mom daman tun tana yarinya ai kikeson rikonta zainabu ta hana yanzu gashinan dai ke zaki aurar daita. Wani kallo mom tayi mata dayasa tayi shiru sai kuma tace Nikuwa yaya anyi bincike akan mutumin nan kuwa?.” Harararta mumy tayi tace “ Aa ke ake jira kije kiyi.”

Wani murmushi ya sulale a fuskata

Na ɗago idanuna na kalli Mum, itama ta kalleta cikin natsuwa.

Dakin ya yi shiru, ana jin karar AC da sautin kwanukan servants da ke jera kayan dessert a kan table.

Wajen ƙarfe uku na rana ne lokacin da gidan ya sake cika da hayaniya mai daɗin sauraro.

A babban room aka ajiye manyan akwatuna masu ɗauke da kayan kwalliya kala-kala, sai kuma wata mota mai rubutun “House of Nabeelah Glam” a jiki. Ance daga wata jiha aka taho da ita, kwararriyar mai kwalliya ce da ake ji daita.

Cikin ɗan lokaci, falon amarya ya koma kamar royal studio. Masu daukar hoto suna ta shigar da camera, ring light, da ƙananan kayan haske. Wasu na ɗaukar bidiyo, wasu kuma suna rera waƙar amarya.

Na zauna akan kujera zuciyata na dukan bugun da ban taɓa jin irinsa ba.Babbar mai kwalliya ta shigo cikin kalar riga black-on-gold, tana sanye da gloves, ta tsaya ta kalle ni tsawon lokaci kafin ta murmusa.

“Ke ce amaryar?”

Na ɗan gyaɗa kai, ina murmushi cikin ladabi.

Ta ɗan nisa, sannan ta ce “Yau za mu nuna musu ma’anar kyau na halal. Kin san kuwa, akwai kyau, akwai kuma kwalliya.” dayake da turanci take magana nikam kadan kadan nake amsa mata

Ta zaro brush ɗinta ta soma aikin da kwarewa. Kamar wasan sihiri, ta fara sauya kalar fuskata a hankali. An shafa foundation, an gyara brows, an saka highlighter

Kowanne motsi nata yana da salo, tana aiki kamar mai zana hoto.

A gefe kuma, videographers suna rikodin komai. “Perfect shot!” ɗaya ya faɗa.

“Her eyes are glowing!” wani ya ƙara, yana matsawa kusa da madubi.

Kawayena suna gefe ana tayi musu kwalliya kowa sai zuzuta kwalliyata yake suma gaba dayansu daga gidan sarautar aka dauki nauyin kwalliyarsu wallahi masu kudi sunyi kai maganar arzuki akeyi anan bama sai an ja da nisa ba kowacce ta canza mu wasu kawayen nawa ma mundade rabona dasu amma suk sunzo Na murmusa, na ɗan ɗago kai, ina kallon kaina a cikin madubi.

A lokacin da ta gama contour, ta ɗan matsa gefe, ta ce “Look at yourself, bride.”

Na kalli madubi sai na tsaya cak..

Idanuna sun yi zurfi, leɓɓana suka yi nude pink, gashina kuwa an ɗaura shi cikin irin bridal bun mai ɗauke da tiny gold pins.

Kawayena suka yi ihu cikin mamaki.

“Ramlah! Inna lillahi! Ki kalli kanki wallahi kin canza gaba ɗaya damab mai kyau ce kuma an kara mata kayan ado!”

Mai kwalliyqr tace “Ai ba amarya bace wannan, Her Royal Bride ce!”

Na saki murmushi cikin nutsuwa, zuciyata na rawa. Sai dai ban san ko daga farin ciki ne, ko daga wani yanayi daban da na kasa fasaltawa ba ni har yanzu tsoro nakeji ina ganin kamar wannan bawan Allah yafi karfina gaba daya.

Mai kwalliyar ta ƙarasa ta ɗaura min headpiece ɗin da aka yi da ƙananan stones.

Da ta gama, ta matsa gefe, ta ɗan kalli sakamakon aikinta, sannan ta ɗan faɗi da jin daɗi “In sha Allah, ko a fadar sarki, ba a taɓa ganin amarya irinki ba gaskiya kinada kyau sosai mashaa Allah.”

Bance komai ba Gabadaya jikina kyalli yake asobei ɗin da aka ɗinka min gaba dayansa stone ne ajiƙinsa

Na ɗan miƙe tsaye, na kalli kaina gaba ɗaya a madubi. Na ɗan ɗora hannuna kan ƙirjina, na ce cikin zuciya “Allah Ka sanya albarka a wannan rana.”

Cikin lokaci kaɗan, videographer ya ɗan matsa ya ɗauki clip ɗin karshe, sannan ya ce “Perfect our royal bride is ready!”

Motoci sun cika harabar gidan su Mumy tun kafin ƙarfe huɗu Gaban kowace mota akwai masu tsaro sanye da uniform mai ɗauke da tambarin gidan sarauta, wasu kuma da dark shades da earpiece a kunnensu.

Harabar gidan ta koma kamar royal convoy na gaske A gefe ɗaya, mata da yara suna tsaye suna kallo, suna ɗan ɗaga wayoyinsu suna ɗaukar hotuna. Ni kuma ina tsaye a bakin falon mu, da veil ɗina mai launin gold, Maryam tana gyaramin ƙugiya, yayata Aliya kuma tana rike da mini bag ɗina tana murmushi.

Sai ta ce, “Auta, wallahi yau kamar bake ba Kinga yadda kowa yake kallonmu kuwa?”

Na ɗan murmusa cikin kunya, amma a zuciyata sai wani sanyi ke ratsa ni. Kowa yana cikin murna, amma zuciyata tana ta bugawa ban san dalilin ba.

Motar farko Range Rover black itace za mu shiga. Driver ɗin ya buɗe ƙofa cikin ladabi, yana cewa “Madam, your car is ready.”

Na kalli Maryam, ta ce min da dariya, “Toh, ranki yadade mu shiga mana kafin masu kallo su kalle kwalliyar.”

Muna shirin shiga kenan sai yaya Billy ta fito daga cikin gida, sanye da doguwar riga, tana riƙe da phone a hannu. Ta tsaya a bakin ƙofar mota, ta kalle mu da wani murmushi na marasa gaskiya “Aa gaskiya,” ta faɗa tana gyara rigarta, “ni bazan shiga wannan motar ba. Ku tafi kawai akwai mota a hannuna.”

Maryam ta ɗan kalle ni, muka yi ido hudu. Na murmusa kawai, nace cikin natsuwa “Toh, yaya. Allah ya tsare.” sai kuma ta jiyo tace “Amma wannan kayan ara kukayi ko? Dan yar gidan mai kudin africa shi tasanya abikinta.” Yaya Aliya tace ita kuma matar mai kudin kasashe ce kinga baxakiyi mamaki ba idan tasanya ai ko?.”

Na shiga mota a hankali, veil ɗina na dan rufe fuskata kadan, kamshin turarena yana cika cikin motar Driver ya rufe ƙofa a hankali, masu tsaro suka gyara tsayuwarsu, sannan convoy ɗin ya fara motsi a hankali.

Gaban mota biyu na gaba masu tsaro ne, a baya kuma wasu motocin suna bin mu.

Da muka fita daga ƙofar gida, sai iska mai sanyi ta rufe motar, tana motsa veil ɗina a hankali.

Yaya Aliya kuma sai masifa takeyi akan bilkisu tana gayamun inyi hankali daita wallahi dama take nema ta cutamun.

Na dafa hannunta a gefe, na ce mata cikin sanyi “Nasan halinta sosau yaya karki damu zan kiyaye.”

Ta murmusa, ta ce“Na faɗa miki, Auta. Kiyayyarta afili take nunamiki wallahi.”

Motocin suka cigaba da tafiya cikin nutsuwa, siren ɗin masu tsaro na tafe da sanyi, kamar ana busa waƙa.

Convoy ɗin ya ci gaba da tafiya cikin nutsuwa. Hasken titin yana haskawa a gilashin motoci, siren masu tsaro yana ta busa cikin sanyi, kamar ana rera waƙar amarya.

Iskar cikin dare tana motsa veil ɗina ta taga, motar kuma tana tafiya da kwanciyar hankali. Maryam na gefe ta lumshe ido tana murmushi, yayata Aliya kuwa tana ɗaukar bidiyo da wayarta

Sai kawai na ji ! motar gaba ta dan tsaya cak, tana yin squeak kamar an taka birki da gaggawa.

Driver ɗinmu ya taka birki shima da sauri, motar ta tsaya.

Nana hadiza

09030569336

[18/10, 9:21 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA UKU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

“Lafiya?” yaya aliya ta tambaya, zuciyata tana bugawa.

Masu tsaron gaba biyu suka fito, suka yi nuni da hannu cikin iska. A fili, an hango wani black motoci guda biyu da suka tsaya a tsakiyar titi, suna blocking hanya.

Hasken fitilunsu yana haskaka cikin duhu.

Wani daga ciki ya buɗe ƙofa, ya fito sanye da mask, yana riƙe da bindiga.

A nan zuciyata ta buga sosai “Yan fashi!”

Maryam ta kama hannuna da sauri, tana kallon waje da idanuwa suka faɗa.

Yayata Aliya itama ta shiga cikin tsoro, “Innalillahi! What’s happening?”

Masu tsaron baya suka fito da gaggawa.

Wani daga cikinsu ya ɗaga hannu yana magana cikin earpiece, yana cewa,

“Team A, seal the back route! Repeat seal the back route!”

Sai kallo kawai muke, cikin gaggawa fitilun convoy suka rufe da haske.

Hasken flash ya cika titi gaba ɗaya, motar gaba ta dan matsa gefe.

Sai kawai tak! tak! tak! aka fara jin sautin harbi amma duk masu tsaro sun rufe jikin motocin da garkuwa na musamman.

Driver ɗin ya juya yana cewa cikin sanyi, “Stay low. Don’t panic.”

Zuciyata na bugawa sosai, amma ina jin sautin siririn addu’a a bakina “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel…”

A gefe, Maryam sai zare idanuwa takeyi, yayata Aliya ta rufe kanta da veil.

Sai kawai muka ji dankarararrrrrr! wani daga cikin masu tsaron gaba ya jefa tear smoke wanda ya mamaye yan fashin, nan take suka fara gudu suna zubar da kayan su.

Cikin daƙiƙu kaɗan, motar police escort daga baya ta karaso da ƙarfi, tana rera siren mai ƙarfi.

“Ceasefire! Ceasefire!”

Sautin security commander ya cika titi.

A nan suka cafke su guda biyu suka tsare, sauran kuma suka tsere cikin duhu.

Masu tsaro suka rufe hanyar gaba da baya, suka tabbatar da komai lafiya.

Salis (PA ɗin Asad) wanda yake cikin motar na gaba, ya fito da hanzari, yana duba motar amarya da damuwa.

“Are you alright, Madam?”

Na ɗago kai a hankali, zuciyata har yanzu tana bugawa.

“Alhamdulillah,” na furta da kyar, muryata tana rawa.

Maryam ta kama hannuna, tana cewe karkiyi mana kuka danAllah ki bata kwalliyarki.”

Commander ɗin masu tsaro ya karaso, ya faɗa cikin muryar ladabi, “Madam, we’ve secured the route. You are safe now. We’ll move immediately.”Na jinjina kai a hankali.

Da muka iso babban Royal Event Hall, sai bugun zuciyata ya ƙaru.Hasken waje kamar rana fitilu, furanni, da ɗaurin ribbon.

Ana jiran isowata ne kawai.

A waje, Royal Guards suka tsaya a layi, kowanne da spear ɗinsa, fuska a tsaye kamar mutum-mutumi.

Na ji MC ɗin ya ɗaga mic da murya mai ladabi

“Ladies and Gentlemen, please rise for Her Royal Bride Princess Ramlah!”

Da wannan kalma, hall ɗin ya yi shiru.

Sannan kiɗan Yanni Aria ya fara tashi a hankali, hasken fitilu suka sauya zuwa white and gold. A wannan lokaci ne aka buɗe ƙofar hall ɗin spotlight ɗaya kawai ta hasko ni.

Na tsaya a bakin ƙofa, na ɗaga kaina a hankali.

Veil ɗina ya lulluɓe har ƙasa, yana kyalli kamar ruwa.

A hankali na fara tafiya cikin red carpet, furanni na sauka daga sama, masu ɗaukar hoto na Royal Media suna ɗaukar kowane motsi.

Na ji muryar wata mata daga baya tana cewa

“Subhanallah… wannan ita ce amaryar Asad?”

Na murmusa kadan, amma zuciyata tana rawa. Kiɗan ya ci gaba, violins suna busa cikin salo. Kawaye na suka rufa min baya cikin kaya masu emerald green,

Su Maryam da Aliya suna dariya suna lumshe ido, suna tura min ƙananan kalmomi kamar “slow, Auta, ki natsu!”

Na isa wajen Royal Wives Section inda matan sarki ke zaune cikin girma da izza.

Na tsaya, na sunkuyar da kai.

“Assalamu alaikum ,” na faɗa cikin ladabi.

Uwar gidan sarki, matar farko mai ɗauke da alkyabba, ta murmusa. “Wa alaikum salam, Ramlah. Allah ya sanya albarka a rayuwarki, ya kawo zaman lafiya.”

Sauran matan suka ce “Amin” cikin haɗin kai, suna kallona da murmushi mai taushi.

Na durƙusa kadan na gaishe da kowacce, sannan na miƙe da natsuwa.

Sai na nufi inda Mumy da mom suke zaune.

Lokacin da idona ya haɗu da nata, sai zuciyata ta lafa kamar an zuba min ruwan sanyi.

Ta miƙe tsaye da murmushi mai cike da tausayin uwa. Na durƙusa a gabanta cikin ladabi, na ce da murya mai laushi “Mumy, na gaishe ki.”

Ta kama hannuna a hankali, ta ɗago ni.

“Auta…” ta faɗa cikin nutsuwa, “Allah ya yi miki albarka. Kin yi kyau kamar bake ba.”

Hawaye suka cika idona, ta rungume ni a ƙirjinta. A wannan lokacin, camera flash ya haska, duk hall ɗin ya yi ihu da farin ciki. Na matsa na gaida Mumy dakyar ta iya amsawa.

MC ɗin ya ɗaga mic “Now ladies and gentlemen, let’s welcome the Royal Couple’s celebration the beginning of love and legacy!”

Sai instrumental music ya fara, masu rawa suka shiga cikin tsari. Fitilu suka rika walƙiya, masu ɗaukar hoto suna zagaye.

Ni kuma aka zaunar da ni a kujerar amarya royal white couch ɗin da aka ƙawata da crystals da furanni.Na zauna cikin nutsuwa, na ji kamar duniya ta tsaya.

Sai aka kira “Royal Family Entrance!”

Dangin Asad suka fara shigowa cikin jerin motoci, maza cikin fararen baban riga, mata cikin royal blue lace. A gaba akwai Abba, sannan sai yayan asad da wasu daga cikin ahalin sarki suka shigo cikin nutsuwa.

Dukkan mutane suka miƙe tsaye suna cewa, “Allah ya tsare Mai Martaba.”

Da suka karaso, sai MC ya ce “Yanzu lokaci ne da dangin ango za su kamun amarya.”

Duk kawayena da su mom antaso Sai aka kawo royal trays guda biyu ɗaya cike da diamonds da gold jewelry, ɗaya kuma da silk boxes. Wata mai magana daga bangaren dangin ango ta miƙe da murmushi, ta ce “A madadin gidan Asad, muna gabatar da wannan kyauta ga amaryarmu Ramlah, hasken gidansa. Wannan ba kayan ado kawai ba ne, alamar soyayya ce, amincewa, da girmamawa.”

Nan da nan hall ɗin ya cika da claps da ihu.

Na lumshe ido, hawaye masu sanyi suka gangaro. An buɗe kwalayen sai duwatsu suka haskaka, pure diamond set, sarka, zobe da ankle chain, kowanne yana kyalli sosai.

Maryam ta raɗa min tana dariya “Wallahi duk kin zama kamar queen Elizabeth gaskiya suna kaunarki.” Na yi dariya ina share hawayena.

Bayan haka ne aka fara kamun amarya.

Kiɗa ya tashi, DJ Smooth yana kunne “So Dake Raina” a cikin salo.

Kawaye na suka zagaye ni suna dariya, suna taya ni rawa, ana ɗaukar hotuna.

Ina zaune a kan kujerar amarya, zuciyata ta yi sanyi. Na kalli dukan jama’a iyayena, dangin Asad, matan fada, kawaye kowa yana murmushi sunata daukar hotuna.

A wannan lokacin, MC ya ɗaga mic ya ce

“Ladies and gentlemen, please prepare… for the entrance of Food of the event.”

Sai hall ɗin ya dauki shiru sai karar waka wani irin rabom abinci ne da bantaba ganin irinsa ba sannan kowamme set akwai pack acikin pack din atampha super ce da kudi haka kowa yasamu.

*******

Kamar daga sama, komai ya sauya a cikin mintuna kaɗan.

Bilkisu tana zaune a gefen kujerar Royal Hall, amma tun lokacin da aka buɗe kwalayen diamond, idonta ya cika da kwallah mai haɗe da zafi. Ta ji kamar zuciyarta ta tsaya cak lokacin da MC ya ce “These diamonds are worth over a hundred million naira, a royal gift from the groom’s family to his bride.”

Hannu ta saka ta dafa ƙirjinta.

Wani irin zafi ya taso mata daga ƙasan ciki zuwa wuya kishi, takaici, da rashin yarda duk a lokaci ɗaya. Kowa yana dariya, amma ita idonta yana cike da hawaye masu zafi.

Tayi ƙoƙarin ɓoye su, amma sai ta kasa.

Ta miƙe cikin hanzari, ta fice daga hall ɗin kamar wadda aka bi da wuta.

A waje iska ke busa veil ɗinta, ta jingina da motarta tana kiran Salisu, wanda tabasu aikin su kashe Ramlah. “Salis! Pick the call! Why are you not answering?”

Wayar ta ci gaba da ringing babu amsa.

Ta sake kiran sa, sau uku, sau huɗu shiru.

Tafara hararar wayar, numfashinta yana fita da huci. “To wannan ai abun mamaki ne… tayaya suka tsallake tarkon?, bayan antabbatar mun yan fashine a hanyar?”

Idanunta suka cika da hawaye, amma ba na rauni Tayi ƙoƙarin sakin murmushi, amma sai kuka ya kubce mata.

“Wallahi, sai na dauki mataki wallahi wallahi.”

Ta shiga mota, ta rufo ƙofa da ƙarfi.

Motar ta tashi da sauri kamar wadda ke guje wa zuciyarta.

********

A daya ɓangaren kuwa, Mumy, tana cikin wani irin tashin hankali da ba ta taɓa ji ba.

Tana kallon yadda aka buɗe kayan da aka kawo, yadda matan fada ke yaba kyautar, yadda kowa ke kiran sunan Ramlah.

Wani abu ya tsaya mata a makogwaro, kamar kashi mai kaifi.

“Wannan yarinyar ce za ta zama matar Maikuɗi? A gaban mutane kowa sonta yakeyi?.”

Ta ɗauki wayarta a hankali, ta buɗe contacts ɗin Abba, mahaifin Asad.

Tayi ƙoƙarin yin kiran kai tsaye, sai zuciyarta ta ce “A’a… kar ya gane dabarar.”

Sai ta yi tunani.

Numfashinta ya ɗan tsaya, sai ta koma ta duba numbar data kwafe daga cikin wayar Abba .

Ta shiga new message.

Ta rubuta cikin sauri, zuciyarta na bugawa kamar ganga.

“Ka binciki yarinyar da kake shirin aura. Kar ka bari kamanninta da ladabinta su ruɗe ka.

Akwai abubuwan da kake bukatar ka sani game da ita, amma daga gareta, ba zaka taɓa ganewa ba.

Tana da abubuwan da zata iya ɓoye maka har ka ɗauka mutuniyar kirki ce amma wallahi ba haka bane. Ka bude idonka kafin lokaci ya kure.”

Ta tsaya na ɗan lokaci, ta kalli rubutun.

Sai ta sake share shi gaba ɗaya, ta rubuta sabo da harshe mai ɗan kaushi, amma cike da sarkakiyar magana kamar ta manyan mata masu ilimi.

“Prince Asad, your silence doesn’t mean blindness.

Ka bincika kafin ka yi nadama.

Wata fuska na iya zama tsarki, amma zuciya na iya zama duhu.

Ina gaya maka wannan a matsayin uwa ba a yadda da dukkan kyawun da ido ke gani.”

Ta tura sakon.

Da ta danna send, hannunta ya ɗanyi rawa.

Ta lumshe ido, ta sauke numfashi.

Nana hadiza

09030569336

[18/10, 9:21 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA HUDU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull