Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 21
Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 21: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 21. Dakin a nutse yake, sai ƙamshin turaren wuta ke yawo a hankali. Ko…
4,490 words
Dakin a nutse yake, sai ƙamshin turaren wuta ke yawo a hankali. Ko rabin dakinta dake gidan Asad baiyi ba inda take da ƴan aiki birjik babu abunda takeyi sai ci ta kwanta ta kashe kudi wannan matsiyacin gidan kuwa yan aikinta biyu bangarenta bai kai bangaren masu gadin Asad ba, wani bakin cikine ya turnuke ta tana kallon Fitilar gold lamp ɗaya ce kawai ke haskawa ta gefe, tana ba wa dakin haske. tana kwance a kan gado, idonta ya kumbura saboda kuka. Ta jawo bargo ta lullube jikinta, amma hawaye na ci gaba da zuba tana cikin damuwar da batasan yadda zatayi ba tasan Asad farin sani baya gamawa da abu yakara waiwayarsa ko da kasuwanci ne yasamu wulakanci acikinsa duk riba da kudin da zai samu baya kara kallon abun har abada.
A hankali aka turo ƙofar ɗakin.
Sai ƙamshin Attar Oud ya cika dakin wannan ƙamshi da ta saba jinsa ne idan Alhaji Muqaddam yana shigowa bangarenta.
Ya tsaya bakin ƙofa na ɗan lokaci yana kallonta. Sosai gabansa ya buga dan yana kaunarta sosai har cikin ransa shiyasa bayan sunyi sun tsarkaka yace mata shi aurenta zaiyi sai kuma yakara kallonta ya ja dogon tsaki, yana magana da muryarsa mai nauyi “Wai menene kike kuka love? Me kuma yafaru?”
Bai jira amsarta ba, ya ƙarasa kusa da gadon.
Cikin lallashi ya ɗan durƙusa, yana ƙoƙarin riƙota. Amma sai ta tashi da sauri, ta hankade hannunsa. “Nifa nagaji da wannan rayuwar, Muqaddam. Ka sake ni! Ka sawwake min, don Allah.”
Murmushi yayi, wanda bai nuna tausayi ba, sai ɗan izza. Ya girgiza kai yana cewa “Kin manta wannan gida nawa ne? A gidan Muqaddam ba a fita idan an shigo.
Ke kowaye bai isa yasanya na sakeki ba ina kaunarki na aureki ina sonki ne idan da bana son ai ban aurenki kinsani. Kuma na fa hanaki fita-fitan banza da kike yi. A yanzu za ki zauna gida kamar yadda matar aure ke yi yawon nan banaso hankalina baya samun nutsuwa idan yawon kikeso to kitabbata tare zamu dinga tafiya.”
Aisha ta ɗaga kai tana kallonsa da idanu masu cike da hawayen takaici. “Wallahi baka isa ba! Dole ka sake ni! Zan fi jin daɗi a titi fiye da wannan gidan.”
Yayi dariyar da ta fi kama da raini.
Ya ƙarasa kusa da ita sosai, har numfashinsa na dukan fuskarta. “Ban aure ki don nasake ki ba, Aysha. Na aure ki ne don ina son ki, kuma saboda na fi kowa sanin halinki.”
Ta miƙe a hankali, tana kallonsa da mamaki da jin tsoro lokaci guda. “Me kake nufi? Kana nufin kana zargina?”
Yayi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce da ɓacin rai “Zargi? Ai ba sabon abu bane idan na zarge ki. Ke fa ce wadda ta saba da bariki karki manta abariki muka haɗu fa.Ko kin manta ne?”
A nan ta tsaya cak.Zuciyarta ta buga.
Sai ta ji ƙirjinta ya ɗau zafi, hawaye suka cika mata ido har suka zubo. “Muqaddam… ka iya faɗa min komai, amma kar ka yi mini wannan zargin. Ka sani ban taɓa cutar da kai ba ban kuma bi kowanne namiji ba sai kai kaine kasani a bariki kuma kai ka yaudareni.”
Ya ɗaga hannu cikin natsuwa, yana dubanta da yanayin da ke tsakanin ƙauna “Shiyasa ma na aureki dan ina kaunarki Ki daina kuka, Aysha. Na aure ki saboda ina sonki, ina son in gyara ki. Amma ki sani, ko kina so, ko baki so ni ba zan sake ki ba. Do whatever you want, amma dai ke tawa ce.”
Ya miƙe, ya ɗauki hularsa daga kan kujera, ya kalli ta na karshe. Idonsa ya nuna bacin rai, amma zuciyarsa ta nuna kishin da ya fi ƙarfi da komai.
Sai ya juya ya fice daga ɗakin da sauri, ƙofar na yin ƙara yayin da ta rufe.
Aisha ta tsaya dafe da ƙirjinta, tana rawar jiki.
“Ya Allah…” ta furta cikin kuka, “ Wallahi banzama dakai gurin Asad zan koma nagayamaka.”
Ta zauna a kan gado, tana kuka mai sauti, har sai da numfashinta ya fara sarƙewa.
Sai ta jingina kanta da bango, tana tunanin rayuwarta daga farin ciki zuwa wannan duhun da ta tsinci kanta a ciki.
Wayarta ce ke ta ƙara a hannunta tana rawa saboda kuka. Aisha ta share hawayenta da bayan hannu, amma kafin ta iya magana ma, hawayen sun sake zubowa. Ta kalli hoton da ke kan fuskar wayar Ameenatu, ’yarta ce, wacce yanzu ta girma ta zama babbar mace kasancewa ba kasar nan tatashi ba har aurent zuwa rayuwarta.
Tana jin muryarta ta amsa cikin natsuwa “Hello Mamaa… hope you’re fine?”
Kukan da take riƙewa ya sake ƙwace mata.
Ta daure, ta ɗan shanye hawayen, tayi magana da murya mai rawa “Ameenatu… please, kin san kina da zuciya mai taushi.
Ki taimaka min… Daddy ɗinki, kada yaƙara aure. Ki ce masa… kar ya auri wata, ki gaya masa ni ce nake sonsa. Ni ce nafi dacewa da shi a duniya.”
Shiru na ɗan lokaci.
Sai daga can Ameenatu ta ce cikin mamaki “Mom, are you okay? Kina da aure fa. Me yasa kike magana haka?”
Aisha ta sauke numfashi da kyar, kamar mai neman iska. “I’m not okay, Ameenatu. Ba zan iya rayuwa ba idan bana kusa da Daddy ɗinku. Ban taɓa daina son sa ba. Please, kada ku bari ya sake aurar da wata.
Ni ce kawai na cancanci kasancewa da shi.”
Ameenatu ta yi shiru, muryarta ta canza zuwa ta bacin rai “Amma Mom, ke kika nemi ya sake ki. Ke kika gudu daga gare shi lokacin da ya fi bukatar ki. Yanzu kuma kina da aure. Kin manta da hakan?”
Ta ɗan sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce da kyar “Please, Mom. Ki kwantar da hankali.
Babu wanda zai iya tilasta wa Daddy abin da Allah ya rubuta masa ba. Wannan yarinyar yana kaunarta sosai kamr yadda naji bakin mai martaba da kansa ya nemi aure ta ba aura masa akayi ba kamar yadda ake masa kuma wannan shine abunda mukeso yasamu farinciki shima ke da kukayi shekatu manya dashi kika gujeshi kikace baida lafiya sai yanzu kina wata maganar da aure akanki? Which kinsan haramun ne Ki mayar da hankali a kan kanki da rayuwarki. I have a meeting now daga baya zamu yi magana.”
Sai ta kashe wayar. Aisha ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon wayar da idanunta hawaye yana zubo mata. Numfashinta ya tsaya kamar ana tsotsa daga jikinta. Ta rufe fuska da tafin hannayenta, tana kuka mai ƙarfi, irin wanda yake fitowa daga ƙasan zuciya.
“Ya Allah…inason Asad kasa muqaddam ya sakeni naje gurin masoyina mai kirana Ayashatuna.. ?”
Tana wannan yanayin ne sai ta tuna jiya da daddare lokacin da ta kama video a wayar Alhaji Muqaddam. Wata mace ce mai kyau sosai, sanye da riga mara nauyi tana dariya, tana faɗin “Baby, when are we meeting?”
Shi kuma yana murmushi yana ce mata “Soon… my Queen.” Cikin rawar jiki ta rufe videon lokacin, amma tun daga wancan rana hankalinta ya tashi. Kuma sukayi rikici sosai yakuma ce mata yadaina bin mata ai kuma wannan ma bazai kuma ba ya tuba Tana jin kamar duniya ta tsaya mata lokacin. “To me yasa kike kuka, Aisha?” ta tambayi kanta a hankali. “Ke kika nemi ya sake ki. Ke kika barshi. To me yasa yanzu kike jin haka da kina sonsa kika gujesa kema kinsan yafi karfinki Allah ne yabaki shi ko alokacin.?”
Ta zube ƙasa, tana kuka da ƙarfin hali.
Sai ta tuna da kalmarsa ta ƙarshe kafin ya fita dakin “Ni ba zan sake ki ba. Do whatever you want, you’re mine.” Sai wani sanyi ya ratsa jikinta gaba ɗaya. Idonta ya rufe, zuciyarta na bugawa. “Inajin tsoronsa… amma ina sonsa. Me yasa yake min haka? Ya Allah ka taimakeni.” Wayarta ta fāɗi daga hannunta.
Sai ta zube a ƙasa, tana murza kanta cikin bargo, tana kukan da ya fi karfin magana.
Da ƙyar ta iya furta “Nashiga uku… wallahi nashiga uku. Rayuwa ta ta rikice… me zan yi?”
A wancan lokaci kuwa, Muqaddam na cikin motarsa, yana duba hoton ta yana mamakin yadda komai sai tace Asad abun mamaki ma ance bashida lafiya kuma yaga aure zaiyi yarasa gane komai yanaso ace matansa ke shaidarsa shima kamar yadda Ake shaidar Asad koda da kwana daya ne Ayshatu bata manta shi kokuma alkhairinsa.Sai ya sauke murmushi yana cewa a hankali “Zan koya miki darasi, Aysha… cewa soyayya da iko ba wasa bane.”
*****
Tunda muka dawo gida, gaba ɗaya gidanmu ya cika da magana ɗaya zancen haduwar bikina da kuma kudin da aka kashe kowa kamun ramlah. Kowa da abinda yake faɗa. Wasu suna yabawa, wasu kuma suna mamaki. Har daga cikin dangin Abba, wasu suna tambayar hajja kaltume wao “Dan Allah tayaya Ramlah ta samu mijin arziki haka? To mu ma Allah ya taimake mu, yarana su ma su samu irin wannan!” Ni dai nayi shiru, na zauna ina murmushi kawai, amma zuciyata tana ta tafarfasa da kuma tsoro saboda nikaina mamaki nakeyi Abba yanada kudi ba laifi bazaka kirashi da talaka ba Amma irin kudin da dangin nan suke dashi ko bantaba gani ba. Tun farko Mumy tana ƙoƙarin kau da kai daga maganganun mutane, har ta gaji tafara yimusu magana akan suna haɗawa da mashaa Allah.
Daman gobe ne daurin aure a babban masallacin garinmu, kuma bayan sallar Juma’a za a yi walimar da mahaifiyar angona ta shirya. Sai kuma Hajja Kaltume wacce itama zata yi wunin amarya a gida. Mom kuwa babu yadda abba baiyi daita ba ko zatayi taro tace aa bata iyawa wai batada lafiya xatazo na hajja kaltume.
Su Yaya Aliya suka dage wai lallai sai an yi dinner party, amma Abba ya hana, yace kamun ma yazama al’ada ne da baza’ayi shi albarkar aure yake nema ba wannan shirmen ba. Haka aka hakura saboda idan Abba ya ce a’a, babu wanda zai canza ra’ayinsa.
Tunda muka dawo wata azababbiyar gajiya ta saukar mun wasu kawayena sunata tambayata wai ango baizo ba gaskiya kada kiyimana haka gobe ki barshi yazo ayi hotuna, murmushi kawai nayi musu. Su Yaya Aliya da Maryam suna hira a falo suna maganar yan fashin da aka turo mana jiya, amma ni ban tsaya sauraron su ba.dan nagaji sosai macce kawai nakeson yi Na shiga ɗaki, na cire kayana, nayi wanka, sannan na saka pyjamas dina da hula ta satin. Na haura gadon Mumy, dakin ya cika da ƙamshin turaren oudh.
Na rufe kaina da bargo, na lumshe ido.
“Wallahi ko yunwa bana ji. Gajiya ce kawai. Irin wannan hayaniyar da ake yi ban saba da’ita ba shiyasa duk na fita hankalina.”
Cikin nutsuwa naji sallamar Hajja Kaltume da matar Uncle Hamza daga ƙasa,
“Assalamu alaikum!”
Na tashi a hankali nace,
“Momy kece?”
Nana hadiza
09030569336
[19/10, 9:16 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA HAMSIN DA BIYAR
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Matar Uncle Hamza ta yi dariya tace,
“A’a Auta, . Har bacci amare da suke kaiwa karfe 1 suna hira ke kuma da wuri haka?.”
Na sosa kai nace, “Wallahi nagaji sosai, bacci nake ji kawai.” Sai Mumy ta zauna kusa dani, ta kalle ni da fuskar uwa mai tausayawa. “Ramlahtu,” ta ce cikin natsuwa, “tashi muyi magana.” Na zauna da ladabi nace, “Momy lafiya?”Ta sauke numfashi tace, “Lafiya lau. wannan aure naki ya jawo magana da yawa Auta, ki dage da addu’a, wannan gidan da zaki shiga ba ƙaramin gida bane. Ba wai masu kudi bane kawai, masu daraja ne da sarauta . Don haka, ki dage da addua, ki nemi Allah ya kare ki.”.
Na ɗaga kai nace, “In shaa Allah, Momy.”
Sai matar Uncle Hamza ta shigo da nata maganar, tana dariya, “Ni dai Auta, banji kunyi waya da angonki ba?”
Na ɗan murmusa nace, “Eh, bamuyi waya ba fa.”
Kafin ta sake magana, Yaya Aliya ta shigo da cup ɗin fura a hannu, tana cewa, “Mom, ai wallahi naji wai angon nan ba shi da lafiya. Pa ɗinsa ya gaya wa Maryam cewa bayajin dadi harma zai koma gida saboda rashin lafiya. Haka kuma mahaifiyarsa batazo event ɗin ba, sai kishiyoyinta kawai.”
Hajja Kaltume ta kalle ni da mamaki tace, “Autaa, baki da hankali kenan?
Me yasa zai kiraki ke kuma baki kirasa ba?”
Sai matar Uncle Hamza ta cafke maganar da sauri tana dariya, “Eh mana, to idan banda shirme. Irin waɗannan mazajen masu kudi, ba a barinsu haka ba. Yaya ai sai da kissa da salo, da kisisina. Ki kula sosai Auta, irin su ana rikesu da kyau
Ko da dan text message ne, ai da yaji dadi.”
Na turo baki nace, “To Momy, ai shi kansa yace yana sona.Shi ya kamata ya nemi ni.”
Nan fa Mumy ta kalle ni da mamaki “Autaaa! Ashe baki da hankali ?
Ke ce mace, ke zaki nuna taushinki.
Ba wai saboda kina da kunya ba ne, ki zama mai wayo, mai salo. Wacce zata iya daidaita miji da zafi da sanyi.”
Sai ta ɗan yi shiru kadan, sannan ta ɗora da “Ki koyi yadda ake magana mai taushi.
Kada ki zama mai yawan magana ko gardama. Ki zama mai natsuwa, mai kissa, mai tausayawa.Ki nuna masa cewa ke mace ce daban, wacce ake so a rike.”
Matar Uncle Hamza ta amsa da dariya tana cewa, “ ni mamaki ma tabani wallahi wai shi zai kirata irin wannan mazan da kowa ke nema shine zaki tsaya shirme lallai ma yarinyar nan kuma gaskiya Momy ke gayamiki, . Idan kika bi wannan shawarar, wallahi zakj rike shi.”
Na sunkuyar da kai cikin kunya nace, “To Momy, naji. Zan kirashi yanzu.”
Ta sauke ajiyar zuciya tace, “ kiji yarinya da wauta ai tunda yazo dinnan zakina zura kanki har sai kinji yafara baki mahimmanci gidan sarauta da suke da izza da takama ke kuma da ba kowa ba?.”
Ta miƙe ta shafi kaina tace, “. Ki tashi kiyi addu’a kafin ki kwanta kuma ki tabbatar kin nemesa komai dare.”
Na murmusa nace, “inshaa Allahu momy.”
Suka fice suna dariya, suka bar ni ina kallon fitilar dakin da ke haskawa Na janyo wayata a hankali daga gefen pillow. Zuciyata tana bugawa sosai. Na tsaya ina kallon sunansa a screen ɗin wayata Na dade ina kallon screen ɗin wayata. Lambar nan dai ce wacce ta kirani rannan Daman Hajja Kaltume ce ta saka min password a wayar tawa, saboda bata yarda da yawancin kawaye na ba. Na jingina a kan gado, na zuba wa wayar ido. Lambar nan tana nan, kamar tana kallona tana cewa “ki kira shi.” Amma zuciyata ta kasa yarda.
Na sha numfashi a hankali. “To idan na kirashi, me zan ce?” Na tambayi kaina cikin zuciyata Ban taba yin soyayya da gaske ba.
Tun lokacin Khalil wanda muka yi soyayya kadan-kadan kafin ya rasu, kuma ai ma ba soyayya ce sosai ba. Ni da shi abokai kawai muka kasance, sai daga baya na fara fahimtar cewa yana sona Amma kafin komai ya fara kyau, sai mutuwa ta rabamu. Tundaga lokacin, na daina kulawa da irin wadannan abubuwa. Ban taba jin feeling din soyayya da gaske ba. Yanzu kuma ga shi Asad mutum mai daraja, mai iko, mai nutsuwa, kuma duk da hakan yana nuna kulawa ta musamman gareni kyautar nan kadai da ahalinsa sukayi na miliyoyi yasanya naji ni bakowa bace ba “Me zance masa idan ya daga?” Na sake tambayar kaina, ina kallo cikin natsuwa.
Zuciyata ta dinga buga Na daure.Na danna kira. Wayar ta dauki ringing, amma bata shiga ba. Na jira har ta tsinke.Na sake kira.Na biyu, na uku, na hudu. Har zuwa karo na biyar. Sai kawai sakon ya fito a screen “Number not reachable.”
Na sauke ajiyar zuciya.
Na kalli wayar, naji kamar na jefar da ita.
“Shikenan, Allah ya sani nayi niyya.”
Na kashe wayar, na kwantar da ita a gefen pillow. Na jawo bargona na lullube jikina gaba daya. Amma bacci ya ki zuwa.
Zuciyata tana cike da tunani.
“Ko yana bacci ne?”
“Ko kuma jiƙin nasane?”
“Ko dai wayarsa ce ta mutu?”
Kowane tambaya yana zuwa yana tafiya, zuciyata na kara nauyi. Na sauke ajiyar zuciya mai nauyi, na kalli sama inda fitilar dakin ke haske. Natashi na kashe sannan nayi addu’oina Na rufe idona, amma zuciyata ta kasa natsuwa. Muryarsa ta dawo min a kunne kamar yana kusa da ni yana cewa “Every time I see you… I forget the world.”
Na janye bargona daga fuskata, numfashi yana fita a hankali. Kamar ina jin kamshin turarensa irin wanda ke da sanyi amma yana daɗa ƙara bugun zuciya.
Na juyo gefe, na rufe ido da hannu.
Allah yasa wannan aure nake shirin shiga ya zama na alheri dan wallahi tsoro nakeji. Idan shi ne kaddarata, ka bani nutsuwa.”
Daga nan na ja bargona har sama, na lumshe ido a hankali ina kara karanta adduoi
************
Bilkisu ce ke tuki cikin sauri, zuciyarta cike da tashin hankali. Girgizar tuƙin da take yi har tana neman hadari, amma bata damu ba saboda tashin hankalim datake ciki kuma tayi alwashi wallahi sai ta wulakanta salisu idan kinyi mata aiki yayi. Sai ta nufi hanyar bayan gari inda ‘yan daba da masu shaye-shaye ke taruwa.
Gaba daya wurin wari yakeyi sosai hayaƙin taba, amma Bilkisu ko ajikimta haka takara zura kanta ciƙin layin nasu.
Tayi parking ta fice daga mota cikin sauri,mayafinta yana kokarin waduwa amma saboda tsananin tashin hankali bata bi takansa ba.daga kanta tayi tana kiran suna “Salisu! Salisuuu! Kai ina kake?” shiru gurin kamar babu kowa. Sannan babu Ko ɗaya wanda ya amsa. Tayi gaba tana dube-dube har ta hango wani matashi yana zaune a jikin ƙofa yana hura hayaƙi. Ta nufe shi cikin fushi da hargowa. “Kai! Ina Salisu yake?” Matashin ya ɗago kai a hankali, ya yi dariya mai cike da raini. “Salisu fa? Hajiya, yanzu yana police station indai salisu ne.” Bilkisu ta tsaya cak!
Jikinta ya dan shiga rawa kirjinta ya dan buga “Police station kace?!” “Eh mana,” cewar saurayin yana juyar da sigari. “Yanzu aka kama su, sun je suyi fashi. An damkesu gaba ɗaya.” Numfashin Bilkisu ya tsaya. Ta dafe ƙirji cikin tashin hankali. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na shiga uku! Na lalace!” Ta juya da sauri ta koma motarta, ta shiga ta ja da gudu, tuni hawaye suka fara zuba. “Yanzu idan an gano ni fa? Idan sun tona min airi fa nayi fa? Yau nashiga uku an kamasu ta buka kan sitiyarin motarta tana kuka. Abba zai iya kasheni akan wannan zai iya korata idan yaji gaskiya.” Tana ta magana ita kaɗai har ta isa gida. Da ta shiga gidan, Momy tana zaune a falo tare da matan su Yaya Usman, suna hira.
Da suka ganta, sai kowacce ta kalle ta, amma Bilkisu ko kallon su bata yi ba, ta shige ɗaki kai tsaye. Momy ta miƙe tana faɗin “Ke Bilkisu! Bakigansu bani ba kikasa kai kika huce Tunda can gidan hajja kaltume zakuje to ku karasa kawai sai na karaso sukayi sallama suka tafi momy kuwa ta mike ta huce daƙin bilkisu tace Lafiya me ke damunki? Kinga mu kina tsallake mu kamar baki sanmu ba?” Bilkisu ta tsaya bakin ɗakin tana kuka sosai idonta sun cika da hawaye. Ta kalli Momy tace “Momy… wallahi na shiga uku. Kuskure nayi idan asirin ya tonu abba korata zaiyi yaya usman sai ya zaneni!” tafashe da kuka mai tsanani tana durkusawa “Kuskure kuma? Ke dan ubanki me kikaje kika aikata munfuka zaki jawomun masifa ko? Ko auren nawa kikeso yakare ne Wani irin kuskure kika yi?” momy ta faɗa tana fizgo rigarta. Bilkisu ta fashe da kuka, ta fara bata labarin komai yadda ta tafi wurin Salisu, yadda ta umarce su su sace Ramlah kuma su kasheta yanzu an kama su ‘yan sanda sun tafi da su.
Nana hadiza
09030569336
[20/10, 8:48 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH
BOOK 2
SHAFI NA HAMSIN DA SHIDA
********
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
ArewaPEN @nanadiso10
https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5
*********
Momy ta zuba mata ido na wasu daƙiƙu tana kallo, kafin ta tashi ta kwada mata mari. “Ke! Ashe baki da hankali?! Dan ubanki, wa ya gaya miki ki shiga irin wannan abu? Kinsan wanene mijinta kuwa? So kikeyi ubanki ya sakeni bilkisu me isa bazanji dadi dake baniba? Haka kikaga su usman da abbas sunayi ko ita ramlah haka kikaga tanayi?
Ke da kanki kika kai kanki gurin yan daba bilkisu saboda bakida hankali banace miki kibar komai a hannuna ba?” Bilkisu ta rusuna tana kuka kamar karamar yarinya. “Wallahi Momy kishi ne inason asad bakadan ba momy tun ina karama nakeson tun ban kai taba mumy Na kasa jurewa ganin yadda Ramlah ke samun kulawa daga kowa kowa sonta yakeyi kowa ita kowa kyauta yake mata kiga diamond fa suka bata, Na kasa!”
Momy ta kifa mata mari tana kallonta ta dafe kai cikin takaici, tana girgiza kai. “Kishi?
To wannan kishi naki zai kaiki gidan yari!
Eh tabbas ban taɓa sanin kina da hauka irin haka ba! Yanzu idan wannan lamari ya fito fili fa? Sai mu zama abin dariya a gaban mutane kuma kowa sai yagane banason auren nan!
Kuma kimsam mijinta sai ya bincika kinsani ai.”
Bilkisu ta sunkuyar da kai tana share hawaye.
“Momy don Allah ki taimaka min…
Kada a gane ni nasasu abba zai kashenj Kada a bari su tono maganar.” Momy ta tsareta da ido, tana numfashi cikin takaici.
“Kin ji abinda kika jefa kanki ciki?
Wallahi kin ja mana bala’i.
Amma tunda kin riga da kin aikata, ki bar komai a hannuna. Zan nemo hanyar rufe wannan maganar dan idan aka kamamun ke bansan yaya zanyi ba dama ace ramlah ce aka kama da mun huta.”
Ta juyo daga kofa tana faɗin magan cikin bacin rai “Amma ki sani Bilkisu… kin ɓata min rai sosai. Kuma idan wannan magana ta tona ki manta da ni gaba ɗaya dan wallahi mahaifinki yasakeni sai na hukuntaki sosai.”
Momy ta fita daga ɗakin da sauri, Bilkisu ta faɗa kan gado tana kuka sosai.
Tana riƙe da kanta tana fadin “Na shuga uku na lalace… wallahi na lalace… kishi ne kawai ya cutar da ni.”
Dakin ya cika da shiru sai hucin numfashinta da kukan da take yi a hankali. Wani irin bakin ciki ne ya lullubeta kishi da nadama suka haɗu suka tun kushe a zuciyarta.
Momy na fita daga ɗakin, zuciyarta kamar zata tashi da wuta. Ko takalmi bata saka ba, ta tsaya a tsakiyar falonta tana maimaita kalmomi cikin fushi “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Bilkisu ce zata tona min asiri? wannan yarinyar har yanzu bata san darajata ba?!”
Tayi wata ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ta juya da sauri ta koma ɗakin Bilkisu.
Kofar ta buɗe da karfi, Bilkisu dake kwance tana kuka ta zabura ta mike. “Momy don Allah ki yi hakuri...” Kafin ta karasa, Momy ta rufe ta da masifa da tsawa “Kina hauka ne?! Ke kike ce min nayi hakuri bayan kin jefa ni cikin bala’i irin wannan?!”
Ta karaso gabanta tana nuna ta da yatsa, idanunta sun canza launi saboda fushi.
“ Bayan ƴan shaye shayen har ƴan daba kike alaka dasu? Bilkisu, kika san menene kika aikata kuwa? Kinsan halin mahaifinki kuwa?
Wannan ba abun wasa bane! Idan wannan magana ta fito, zaki ga yadda gidan nan zai lalace dan na tabbata miki mahaifinki bai ragamun ballantana ke!”
Bilkisu ta sunkuyar da kai tana kuka, muryarta na rawa tace “Momy wallahi ban zata haka ba, na yi ne saboda kishi ne kawai”
“KISHI?!” Momy tayi mata ihu.
“Kishi da zai sa ki turo maharba su kashe mutum?! Ke wacece da zaki yanke rayuwar wata saboda namiji? Namijin da ko kin kashwta bazai kauna ce ki ba?.
Ko kin manta waye mijinta? Asad da kowa ke tsoron sunansa? Kina so mu mutu gaba ɗaya saboda wautarki!”
Ta daga hannu sama kamar zata doke ta, amma ta tsaya tana girgiza kai cikin takaici.
“Wallahi, Bilkisu, da ba ni ce mahaifiyarki ba, da yanzu da baki fita daga gidan nan da kafarki ba. Na rasa yadda na haifi yarinya mara hankali irin ki!”
Bilkisu ta durƙusa tana kuka sosai, hawaye na zuba kamar ruwan sama. “Momy kiyi hakuri don Allah, bazan kara ba, wallahi bazan sake ba.” Momy ta tsareta da kallo, idonta cike da takaici da fushi.
Ta taka zuwa bakin ƙofa,
Hawaye ya cika idon Bilkisu. “Momy don Allah ki taimaka min... kar ki yi haka dani...”
Momy ta yi dariya mai sanyi irin dariyar mace da ta gama yanke hukunci.
“Ai ni na riga da nayi laifi tun ranar da na bar ki kina wasa da tunaninki.
Na dauka kina da hankali, ashe zuciyarki ta cika da bakin ciki.
Kin jefa kanki cikin abin da ke iya lalata rayuwarki gaba daya.”
Ta kalle ta sosai, tana magana a hankali, kalma bayan kalma “Idan na kara jin sunan Salisu a bakinki, ko kuma naga an kiraki daga wajen da ya shafi wannan maganar,
sai dai ki fara addu’ar samun gafara.
Domin wallahi zan tabbatar baki sake tashi da kafa ba.”
Ta juyo ta fita daga dakin tana jan takalminta Bilkisu ta faɗa kan gado tana kuka kamar wacce aka zane.
Zuciyarta tana bugawa kamar zata fasa ƙirjinta. Muryarta na rawa tace “Na lalace… Momy ta tsane ni… Allah na tuba, Allah ka taimake ni.”
Tana faɗin haka ta dafe kanta, jikinta na rawa saboda tsoro da nadama.
Falon kuma daga can, Daga nan gidan ya sake yin shiru, amma a zuciyar Bilkisu, wutar tsoro da nadama na ci gaba da ruruwa.
Bayan fitarta daga ɗakin Bilkisu, Momy ta nufi ɗakinta kai tsaye.
Koda ta shiga, ta rufe ƙofa a hankali sannan ta jingina da ita.
Zuciyarta na bugawa ba saboda tsoro ba, amma saboda hanzarin da take buƙata wajen nemo mafita kafin abu ya lalace.
Ta zauna a kan kujerarta mai juyi, ta ɗauki wayarta tana tunani. “Idan Sarki ko Hajja Kaltume suka ji wannan magana, komai zai lalace,” ta faɗa a hankali tana murza yatsunta.
“Dole in kare kaina, dole in kare Bilkisu ko da kuwa zanyi ko menene.”
Ta ɗan yi shiru, tana sake duban wayarta.
Ta shiga contacts, ta danna wani suna da aka rubuta Yakaka Ita ce Momy ke kira idan tana cikin tashin hankali tunda itace ta riketa kanwar mahaifiyarta ce.
Wayar ta ɗauka da sautin muryarta “Zainabu? Lafiya dai? Na ji muryarki kamar kina cikini tashin hankali.”
“Wallahi Yakaka, ba lafiya.”
Kin san wannan yarinyar Bilkisu ta jawo min bala’i. Ta Tura ‘yan daba wasu sace ramlatu… mumy tabata labari duka kuma ankama su yanzu suna hannun ‘yan sanda.