Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 22

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 22

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 22: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 22. Idan sukace itace ta sakasu fa? Kinsan wallahi Allah kaberu sai ya…

4,491 words

Idan sukace itace ta sakasu fa? Kinsan wallahi Allah kaberu sai ya sakeni.”

Yakaka ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce cikin natsuwa “ Lallai Bilkisu ta tabbatar miki ita jininki ce, kiji yarinya da baƙin kishi kamar na uwar ta. To ki saurare ni, Zainabu Kada ki nuna komai yanzu Kada kowa ya ji cewa kin san da lamarin nan. Wannan ai bamatsala bace ba babba tunda daman yaran sun saba fashe da makami ko da ance bilkisu ce tasasu sai akaryata ita bilkisun sai tace cewa yayi yana sonta ita kuma tace bata kaunarsa shine yace sai yayi mata sharri.” Momy tasaka dariya sosai tace sai dake uwata takaina wallahi kaina ne ya kulle kinsan masu kudin nan basuda mutunci kuma yanzu abbansu kadan yake jira akaina.

Yakaka tace “ Ba dole kanki ya kulle ba yarinya tayo bakin halinki ina bilkisu ina aikin nan, ai karkiji komai babu abunda zai faru yanzu haka shi dan daban hukuma ta dade tana nemansa ma ba lallai wani yakawo turosa akayi ba.” “Kin faɗa gaskiya,” Momy ta ce, tana jinjina kai. “ Abunda dai nakeso dake yanzu shine danAllah ki cire bakin cikinki ayi bikin nan lafiya dake ba kowa sai yagane hassada kike ba, in banda hauka irin naki zainabu kici wahalar yarinya tun tana tsumma amma kibari wata ta aurar daita ai nice ke wallahi sai nayi arzuki da Ramlah ai hannun jari ce amma kin riga kin bata wayonki wallahi, kitashi ki tafi can gidan ayi komai dake.

“Zan yi hakan.

Yanzu ma daurin aure ne gobe, zan sa nuna duk farin ciki a fuskata.” “Yauwa ko kefa,” ta ce tana murmushi.”

Ta kashe wayar.

Sai lokacin Momy ta sauke dogon numfashi.

Ta tsaya ta kalli madubi, ta dafa fuskarta da hannu biyu.

“Zainabu… ki nutsu.

Ba lokaci bane na kuka ko nadama.

Ki yi wasa da hankali ki nuna kamar babu abin da ke damunki.”

Nana hadiza

09030569336

[20/10, 8:49 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA BAKWAI

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Ta juya ta buɗe wardrobe ɗinta, ta fito da wata abaya mai launin royal blue da duwatsu a gefe.Ta ɗaura gyale, ta kalli kanta a madubi.

“ Tabbas wannan aure ina bakin cikinsa amma naga idan ban kau da kaina ba to tabbas nice wacce zan rasa gidan aure na yanzu haka zan kara turawa Asad text wallahi har sai na saka masa zargin yarinyar nan.”

Ta fita daga ɗakin a hankali, tana tafiya cikin nutsuwa kamar babu abin da ke faruwa.

Amma a zuciyarta, wuta ce ta makirci da shirye-shirye ke ruruwa.

Daga nesa, Bilkisu ta leƙo daga ɗakinta tana kallon Momy ta nufa hanyar falon ƙasa.

Tana sakkowa da stress smile, tana murmushi kamar ba itace ta gama wanka mata maruka ba.

Bilkisu ta furta a hankali cikin kuka “Nasan momy wallahi sai takara hukuntani amma yadda naga tana murmushi bari naje na bata hakuri.”

“Dan Allah Momy, ki yi hakuri ki yafe min, kinji? Bazan sake ba, wallahi bazan sake ba. Ce wa Bilkisu tana kasa kusa da ita ba zan ƙara irin wannan magana ba. Idan kika yi fushi dani, Momy, yaya zan yi?”

Momy ta kalleta tundaga sama har kasa sannan taja numfashi tace “To bari kiji, Bilkisu wallahi! Wallahi Allah Billahillazi! Na rantse, idan na sake jin kin ambaci sunan As’ad a gidannan, idan ban karya ki ba, to tabbas sai na ragargaza bakin nan naki! As’ad yafi ƙarfin ki! Kin manta yadda kika lalata kanki? Kin manta yawon da kika yi a joints kina shaye-shaye da maza? Kin manta komai kenan ko?”

Ta matsa kusa da ita, muryarta ta ƙara zafi, kamar wacce take fitar da abunda yake cikin zuciyarta da ta dade tana boyewa.

“To tsaya ki ji, Bilkisu, kiraba kanki da tashin hankali! Idan kika kashe ta saboda shi, wallahi ba zai aure ki ba! Allah ya kiyaye, amma sai kin mutu a gidan yari! Kizo ki yi rayuwa a kurkuku har abada wanda yakashe kasheshi akeyi sha sha sha ke baki aureshi na kuma kin lallata rayuwarki.”

Ta ja numfashi mai nauyi sannan ta ƙara da kallonta “Kowa yasan past dinki fa kada ki manta har mari nakaiki bilkisu dan babanki yatsaya akanki ne da yanzu wani zancen ake kin lallata kamki da kawayen banza yanzu duk tarkon da nadinga yiwa Ramlah gashu kamki ya koma na aura mata dan shaye shaye dan tafara sai gashi ke kika fara nayi mata sharri kala kala duk abunda nayi mata ke kikeyi. Sha-sha-sha baki taɓa inganta rayuwarki ba! Kina son mutumin kirki, amma ke kanki ba mutuniyar kirki bace. Idan da kin gyara kanki, kina tunanin ba ke zai zaɓa ba? Sakara kawai mara tunani!”

Sai ta juya ta fice daga palon, ƙamshin turarenta ya bita. Wurin ya ɗauki shiru, Bilkisu kuwa ta tsaya cak, hawaye suna zuba sosai. Kafin ta juya taji sallamar ya usman karasawa tayi tana fadin yaya.. “menene bilkisu?” Yafaɗa yana kallonta. “ I wan’t to be a better person yaya zan canza zan zama mutuniyar kirki i don’t like komai nawa inason na zama kamar Ramlah.” Kallonta yayi suka zauna kan kujera yace “ zaki iya zama better than her bilkisu but sai kin daina daukar dabi’un mom please ki koma islamiyya ki gyara zuciyarki kinji.” “ But yaya ilove him wallahi sosai.” Murmushi yaya usman yayi yace “ bakomai kake nemi kasamu ba bilkisu kiyita addua Allah xai kawo miki wanda yafishi but try kizama yar uwa tagari kar yakasance kullum kokarin cutar yar uwarki kikeyi bayan tanada hakki aciki wasu daga ciƙin ƘADDARAR RAMLAH bilkisu kema kin bada gudunmawa. Kizama mutuniyar kirki sosai kinji. Okay yaya zan canza sosai.

********

Dakin gimbiya Maryam ya cika da kamshin turaraka kala kala, fitilun sun haska ko’ina, sai mirror wall dake nuna kowane motsi.

Tsakar dakin kuwa, Haneefah ce ta durƙusa a ƙasa, ta rufe fuska tana kuka kamar ranta zai fita.

Gimbiya Maryam ta tsaya a gabanta tana riƙe da gilashin ruwan lemonade, fuskarta a murtuke kamar me duk yaranta haneefah ce ƙadai matsalarta wallahi.

“Haneefah,” ta faɗa cikin muryar da ta cika da bacin rai “kashe kanki zakiyi saboda namiji? Me yasa kike raina kanki haka? Shi Yarima Asad din da yakamata yadinga haka saboda ke shine ke kikeyi sabida shi” Ranta a ɓace, gimbiya Maryam ta jefa gilashin a gefe paah! sai ruwa ya zuba a ƙasa. Yayar haneefah Saddika, wacce ke zaune a sofa tana tauna apple, ta ɗago da murmushi mara da rashin tausayi. Tace “To ai da kin barta ta kashe kanta, Mama,” ta faɗa tana murmushi.

“Canta dai tayi wa Yaraima karya saboda ita munafuka ce makaryaciya! Kin manta ita ce ta fara faɗin Asad ba shi da lafiya? Ita ce ta fara bata sunansa shifa yakula da ita yakaita karatu aurenta guda biyu shine yayi mata hidima amma karshe abunda ta saka masa dashi kenan.”

Cikin kuka Haneefah ta ɗago tana faɗi da murya mai rauni “ ke yaya abu baya taɓa wucewa a gurinki ko? Ai ban yi karya ba, gaskiya nake faɗa. Bashida lafiya ne, baku ga matarsa Ayshatu ta gudu ba? Ta rabu da shi saboda rashin lafiyar sa, Mamaki na ma danaga zai kara aure kinga kuwa yasamu lafiya kenan.”

Saddika ta juya mata ido, tana masifa “To idan ba shi da lafiya, to da zai sake aure? Da mutum ba shi da lafiya zai iya aure? Munafuka kawai! Ke da Asad dai sai daga nesa inshaa Allahu bazaki taba komawa gidansa ba.”

Gimbiya maryam tayi murmushi dan ita kadai tasan abunda ta shiryawa Asad har yasamu rauni kuma ko lokacin boka ya tabbatar mata gabansa bazai kara tashiba har ya mutu amma tayi mamakij yadda ya nemi aure ko dayake sadaukarwa tayi ko zaiyi aure sau goma to tabbas sai matan sun rabu dashi wannan kaɗai ya isa yasanya watarana ya hauka. Sai tabar tunaninta tace “Kunga ku saurara, kun san kuwa wacce Asad ya aura? Yarinyar ba ‘yar gidan kowa bace yar talakawa ce! Ubanta ma ba wani mai arzuki baniba amma yau ga shi, mai martaba Diamond ya bata kyauta dukkan mu babu wanda yataɓa samun irin wannan kyautar ta millions.”

Saddika ta yi dariya kadan, ta girgiza kai tana cin apple ɗinta.

“Mama, me ke ciki idan ya bata? Dan tana talaka? Ai dai abba Asad da kansa ne ya ce yana sonta, ba wani ya ce masa ya aureta ba. Me yasa kike shan wahala da abinda Allah ya rubuta?”

Haneefah ta share hawayenta da rigarta, tana goge hancinta sannan tace “Ni wallahi zan koma gidan Asad. Zan koma dakina, inason abuna.”

Saddika ta fashe da dariya mai ƙarfi. “Ke? Da Asad? Hahaha! Har abada babu wannan damar. Ki daina mafarki .”

Gimbiya Maryam ta juyo da sauri, ta daga hannu “Kuyi shiru, ku daina min dariya! Wallahi duk yadda zanyi sai ta koma! Na rantse da Allah, Haneefah dole ta koma gidan Asad. Ko da da dabara ne, ko da da kissa wannan yarinyar da take kiran kanta amarya sai tafita tabar gidan. Ba zan bari ta zauna cikin arzukin da ya kamata Haneefah ce aciki ba.” tafada da dabara dan haneefa ta kwantar da hankalinta amma ita burin asad ya mutu ne dan shine planning dinta nagaba.

Haneefah ta yi wani tsalle, ta rungume gimbiya Maryam tana kuka da dariya a lokaci guda. “Yauwa Mamata! Wallahi yauwa Mamata! Nagode! Wayyo dadi!”

Ta yi dariya mai ƙarfi, tana kicin-kicin kamar wacce ta samu ta koma. Saddika ta kalli su, ta murmusa cikin zancen zuciya

*******

Yana kwance cikin gado mai yalwa, fuskar sa ta yi fari kamar takarda. Zafin jikin sa ya yi sama fiye da yadda aka taɓa gani. Idanunsa sun rufe, jikin sa yana karkarwa kamar wanda yake cikin mafarki mara daɗi. A kusa da shi, Hajja cemahaifiyar sa, kyakkyawar mace mai kyan hali da nutsuwa tana zaune tana riƙe hannunsa da hawaye a idonta.

“Ranka yadade wallahi bana son ganin Asad haka…” ta faɗa cikin murya mai rauni, tana kallon mijinta.

Mai Martaba ya nisa, ya miƙe daga inda yake tsaye. “Ki kwantar da hankalinki, Safiyya. Likitoci suna kan hanyarsu daga Royal Crest. Ba za mu bari wani abu ya same shi ba inshaa Allahu Allah zai bashi lafiya ba dazu naga ƙin bashi abinci ba har kuna hira.”

Daga kanta tayi kawai batace komai ba

Duk da kalamansa, zuciyarsa tana rawa. Yarima Asad ba kawai ɗa bane gare shi shi ne komansa bai kasance babban ɗaba amma kuma yazama shine babba agidan duk wani abunda yakamata ba sai yasanar dashi ba, girmansa, alamar ikon gidan. Duk wanda ya san tarihin wannan gida, ya san cewa Asad shine al’amari mafi daraja a sarautar Babangida.

Sabis ɗin gida biyu suka shigo cikin hanzari, daya daga cikinsu yana riƙe da guntun ice pack, ɗayan kuma yana riƙe da wet towel.

“Mai Martaba, ga su.”

“Sanya towel ɗin a goshinsa, sai a daura ice pack ɗin a kirjinsa.”

Cikin mintuna kaɗan, aka ji karar motoci a bakin fadar. Likitoci uku ne suka fito cikin white coats, suna gudu, kowanne yana da stethoscope a wuyansa. Shugabansu, Dr. Khalid, babban likita ne da ake kira The King’s Healer saboda shi ne mai kula da lafiyar gidan sarauta tun shekaru da dama.

“How long has he been unconscious?” Dr. Khalil ya tambaya cikin Turanci.

“Almost thirty minutes,” Mai Martaba ya amsa da ƙasa-ƙasa, yana ƙoƙarin danne damuwa.

“Temperature?”

Nana hadiza

09030569336

[21/10, 10:39 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA TAKWAS

********

“Forty point five,” wani daga cikin fadawa ya amsa cikin rawar murya.

Dr. Khalid ya kalli Asad da kulawa, ya ɗora hannunsa a goshinsa, sannan ya dube likitocin sa. “Get the ambulance ready. He needs full monitoring. I don’t like this kind of heat it’s not normal fever.”

Zuciyar hajja ta karye. “Doctor, menene ? Fever ce kawai ko akwai wani abu daban?”

“We can’t say yet, Your Highness,” Dr. Khalil ya ce cikin ladabi. “But this is serious. We must move him now.”

A nan ne aka ga manyan bodyguards suna tattara kayan. Motar Range Rover black edition aka kawo da sauri, aka buɗe kofar baya. An ɗauki Asad a hankali, aka shimfiɗa shi a jikin gado mai cike da farar lallausar bedsheet, aka ɗaura masa oxygen mask, sannan convoy ɗin fadar ya fara motsi.

A cikin motar, Hajja tana kuka a hankali, tana riƙe hannun ɗanta, yayin da Mai Martaba ke zaune a gaba, yana kiran mutane ta waya.

“Tell them to clear the road! I don’t want any delay, not even one minute!”

Likitocin da ke cikin motar suna aiki da sauri.

“BP dropping, oxygen saturation 83%...”

“Increase the flow. Keep his head steady!”

Sai da suka isa bakin Royal Crest Private Hospital asibitin da ke da kyan gini kamar otal. Ginin mai bene bakwai, da gilashin da ke haske kamar ba akasar nan na. Ana shigar da su kai tsaye ta VIP Emergency Gate, wanda ake buɗewa kawai idan an kawo Royal Patients wato masu sarauta, ministoci, ko manyan attajirai.

Ana shigar da Asad cikin gaggawa, motar stretcher tana tura shi cikin corridor mai kamshi da sterile scent. Likitoci suna tserewa suna bin umarnin Dr. Khalid. “Prepare Room 1A, full life support!” “Get the ECG and IV line ready!”

Mai Martaba da Hajiya Safiyya suna bi a baya, suka tsaya a bakin ƙofar VIP Room. Babu wanda ya ce uffan. Sai fitilun asibiti da karar beeping monitor ke ba da sauti.

Bayan mintuna talatin da kawo shi suna zaune duk sunyi shiru Dr. Khalid ya fito, gumin sa yana sauka kamar wanda ya yi tsere.

“We stabilized him… for now,” ya ce cikin gajeren numfashi.

“Alhamdulillah,” Mai Martaba ya ce, yana godiya ga Allah.

“But, Your Highness,” Dr. Khalid ya ci gaba, “this is not an ordinary case. I need to know has he been stressed, or eaten something strange recently?”

“Nothing,” Hajja ta ce cikin muryar kuka. “He was just fine this morning. He even laughed with me before breakfast.”

Dr. Khalid ya gyada kai, yana kallon Mai Martaba. “This could be genetic… or poison. I will run tests immediately.”

Da zarar kalmar poison ta fito daga bakinsa, jikin Mai Martaba ya tsaya cak. Fadawan da ke tsaye suka kalli juna cikin firgici. Kalmar ta yi nauyi kamar an jefa dutse cikin kwano.

“Poison?” Hajja ta maimaita, hawaye na zubo mata.

“Doctor, ka tabbata?”

“Not yet, but we’ll find out soon. We have to keep this confidential. Please, no media, no outside contact.”Kalmar poisoning ta sauka kamar dutsi. Yanayin falon ya yi tsit. Mai Martaba ya gyara xamansa, shugaban masu gadi ya na murkushe hakora. Duk sun san cewa idan an tabbatar da cewa abincin gidan sarauta ne aka sanya guba a ciki, to abun zai zama babban laifi ya shafi mutunci, iko, hatta rayuka.

Gobe za a daura aure bakaramun biki suka shirya ba kowa yana murna da farin ciki Amma cikin ikon Allah ga yadda Angon yakasance dan har yanzu baisan wanda ke kansa ba. Mai martaba yaja Numfashi sai kuma ga doctor Amina tafito tace “What did he eat?” Dr. Amina ta tambaya cikin Turanci.

Dr. Khalil ya amsa. “He ate a stew with special spice and salad.” “Keep the leftovers and all utensils,” ta ce. “We will test them for common toxins and heavy metals. Also blood samples, urine, everything.”

An kama duk kayan abincin, an saka su cikin sterile bags. An dauki swabs daga plates, an duba utensils. Dukkan masu hidima da chefs an kulle su a daya wuri don tambaya babu wanda za’a ragawa akan hakan.

A cikin VIP room, monitors suna nuna yanayin jikin Asad kamar wani zane mai launin ja da kore. Hajja ta riko hannunsa, tana hawaye takasa jurewa gaba daya Mai Martaba ya zauna kusa da gadon, ya danna hannunsa a saman na Asad idanunsa sun nuna tsoro sosau ji yake kamar zai rasa shi.

“Doctor, is he going to be okay? Allah yatashi kafaɗunsa the wedding…” Mai Martaba ya ce a hankali, murya cike da ƙarfi da ƙetarewa.

“We will do everything possible, Your Highness,” Dr. Khalil ya ce. “This toxin acted fast, but we caught it quickly. There’s a chance a good chance with prompt detox and supportive care he will recover. But we must be realistic if it’s a severe toxin, he may need prolonged care.”

Kalmar chance ta yi nauyi sosai Amma kuma yasan Allah kadai ne keyi..

Sun fara maganin gaggawa IV fluids, activated charcoal (inda ya dace), gastric lavage idan an yi cikin lokaci, da antidotes idan an gano irin gubar. Dr. Amina ta yi umarnin a fara broad-spectrum antidotal therapy, har sai an iya gano takamaiman sinadarin.

A Cikin Masarautar,masu aikin kitchen da suka shirya abincin sun taru a cikin wani daki. An rufe kofar, an tambaye su daya bayan daya. Su sun ce cewa ba su ga wani abu daban sun bada shaida cewa duk sun aiwatar da kulawa da tsafta kuma su basuga bakon fuska ba kwata kwata.

A cikin asibiti, lokaci yana tafiya cikin lokaci..An aika samples zuwa lab blood, urine, leftover stew, salad dressing, hatta spoon da plate. Lab technicians sun yi aiki sosaj cikin gaggawa Sakamakon farko zai zo da daddare amma idan har wannan guba ce mai saurin aiki, sakamakon na iya bayyana cikin sauri kuma magani zai yi tasiri.

Mai Martaba ya kalle hajja, “If this is sabotage, I will find whoever did it. Whoever poisons my son poisons...”

Sai Hajja ta dafa hannunsa, tana cewa

“Mai Martaba, Allah ya taimaka. Amma yanzu mu fi karkata zuwa Asad. Dole ne mu yi addu’a da neman taimako. Gobe… asaki kowa duk wanda yayi masa haka rayuwa da yau da gobe baxata taɓa barinsa ba ni nayafe danAllah wanda yayi zai bayyana kanshi a sannu..”

Kwance yake gaba daya fuskarsa ta dashe ga wani jan numfashi da yakeyi a hankali A hankali yashiga motsa jiƙinsa yana ɗan bata fuska ciƙin wani karamar murya yace “ Ramlah. Duk suka jiyo suna kallonsa Abba da firdausi da zuwansu kenan suma suka tsaya suna kallonsa Dr. Khalid ya yi murmushi, Yace Alhamdulilahi. “He said her name. That’s good. It means he’s fighting. We will keep monitoring. For now, we treat, we test, and we secure everything.

A bakin VIP window, Mai Martaba ya tsaya, yana kallon fitilun gari da ke haskakawa a nesa. A cikin zuciyarsa akwai fargaba, amma kuma akwai karfin hali. Yau ce farkon gwaji ba kawai ga Asad ba, har ga dukkan gidan Masarauta domin kowa yashiga firgici.

A kan gadon, Yarima Asad ya buɗe idanunsa cikin rauni. Murmushin da ya fito daga bakinsa ya nuna cewa jikinsa ya dan samu sauƙi, amma idanunsa sun bayyana gajiya da zurfin tunani.

Dr. Khalid ya tsaya a gefen gado, yana karanta sakamakon jarrabawar jini.

“Good morning, Your Highness,” ya faɗa cikin ladabi. “How are you feeling today?”

“Better,” Asad ya amsa a hankali, murya mai laushi. “But my chest feels heavy… like something inside me is burning slowly.”

“That’s normal,” Dr. Khalid ya ce. “The toxin is leaving your system. You’re lucky, Yarima. If we came any later, it might have been different.”

Asad ya lumshe ido. Ya tuna da komai abincin da ya ci bayan yan sa’a kawai yaji yashiga wani yanayi, murmushin mahaifiyarsa, zafin da ya taso daga cikin jikinsa, da kuma muryar likitoci . Ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya tambaya cikin sanyin murya “Doctor… was it really poison?”

“Yes,” Dr. Khalid ya amsa kai tsaye. “We confirmed it early this morning. A rare toxin not common in food. It was placed intentionally.”

Kalmar intentionally ta daki kunnensa kamar karar wuka. Ya ja numfashi, idonsa suka ɗan lumshe “So someone tried to kill me?”

“It looks that way. But we will let the palace investigation confirm.”

Cikin wannan lokaci ne Hajja ta shigo cikin dakin, sanye da hijabi mai launin kore. Ta yi murmushi da hawaye a idonta. “Asad…” Tafada tana karasowa Alhamdulillah Allah na gode maka naji dadi sosai Allah yakara maka lafiya.” “Hajja…” ya faɗa cikin rauni, yana kama hannunta. “kidaina kuka naji sauki……”

“Allah yakara maka lafiya ɗana,” ta katse shi, tana share hawaye. “Kuma zamu bincika wanda yasanya maka gubar nan, insha Allah.”

Dr. Khalid ya gyada kai cikin girmamawa.

“He’s stable now. We will observe him for a few more hours. If his vitals remain good, he can return to the palace by noon.”

Nana hadiza

09030569336

[23/10, 1:48 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA HAMSIN DA TARA

********

Sai ta ji dadi sosai da maganar doctor tana Hamdala. “Allah ya saka da alheri, Doctor.” bari naje yanzu mamy ta karaso ita takama hidimar biƙin sunzo dazu kana bacci.

****

A cikin asibiti, A hankali ya tashi zaune kasancewa Antaimaka masa yayi brush wanka ne doctor yace sai xuwa anjima. Jikinsa ya yi sauƙi, idonsa sun buɗe sosai. Likitoci sun cire allurai, sun bar oxygen kawai. Ya zauna a hankali, ya dubi gefensa inda mahaifinsa ke tsaye, sanye da farar agbada da rawani fari.

“Yau rana ce mai albarka, ɗana,” Mai Martaba ya faɗa da murmushi. “Allah Ya baka lafiya. Na yi addu’a, kuma Allah Ya amsa. Alhamdulilah.”

Asad ya murmusa. “Na gode.”

Washegari.

Haske ya fara shiga dakin asibiti ta tagar gilashin, yana ratsa farin labulen da ke motsawa da iska mai sanyi. Sai kamshin turaren oud da ake amfani da shi wajen tsaftace dakin ke bayyana a hankali.

A kan gadon da ke tsakiyar ɗakin, Yarima Asad yana zaune, ya ɗan jingina da matashin kai, fuskarsa ta cika da annuri duk da ƙaramin rauni da ke bayyane a idonsa. Likitoci sun cire yawancin na’urori, sai karamin IV line a hannu alamar cewa jikinsa ya dawo da ƙarfi sosai.

Dr. Khalid yana tsaye a gefensa yana duba sakamakon gwaji, yayin da wani junior doctor ke gyara gadon da za a yi masa amfani da shi har sai an sallame shi.

“Alhamdulillah,” Dr. Khalid ya ce, yana kallon Asad. “Your recovery is impressive, Yarima. The body responded very well to treatment.”

“I feel better,” Asad ya ce a hankali, yana kallon labulen da iska ke motsawa. “Like the fever never happened. But... my heart feels strange.”

“Strange? How?”

“It’s beating faster... every time I think of her.”

Dr. Khalid ya murmusa cikin ladabi, yana fahimtar abin da yake nufi.

“Ramlah?”

“Yes,” Asad ya amsa, yana ɗan lumshe ido. “All night I kept hearing her name. Like her voice was calling me from far away. I don’t even know if it was real or a dream.”

Dr. Khalid ya ɗan murmusa, ya kalli takardunsa.

“Maybe it was love speaking louder than pain.”

Asad ya yi dariya kaɗan, yana ɗan goge gumin da ke goshinsa. “Love…” ya maimaita cikin nutsuwa. “yau daurin aure na Amma har yanzu ina asibiti.”

“By Allah’s mercy, you’ll attend your wedding before sunset,” Dr. Khalid ya tabbatar masa da murmushi. “You’re strong now.”

Sai dai kafin su gama, ƙofar ta buɗe cikin nutsuwa. Mai Martaba sarki Babangida III ya shigo, sanye da babban agbada mai launin shudi da zare.. A bayan sa akwai Waziri, wanda ke ɗauke da takardu da waya. A bayansu kuma, masu gadi suna tsaye cikin ladabi.

Dr. Khalid ya miƙe da girmamawa. “Ranka ya daɗe.” “Barka da safiya ina kwana.”

“Yaya jikin ɗana?”

“Alhamdulillah, ranka ya daɗe. Yanzu jikin sa yakara sauki sosai. Zamu iya sallamarsa zuwa yamma, idan babu wani canji duk da jiƙin nasa babu kwarin da zai iya kazar kazar.”

Mai Martaba ya gyada kai cikin natsuwa, ya ƙarasa kusa da gado. Asad ya miƙe kadan, yana murmushi da gajiya.

“Ranka yadade,” ya faɗa cikin ladabi.

“Asad ɗana, Alhamdulillah Allah yakara maka lafiya..” Mai Martaba ya riƙe hannunsa. Cikin idonsa akwai farin ciki, amma akwai kuma tunani mai zurfi irin wanda yake cikin zuciyar sarki da ya san komai ba kamar yadda ake gani ba.

“Babu damuwa,” ya ce. “Zamu tafi mu bar likitoci su kammala shirinsu. Kowa zai dawo zuwa yamma don ɗaukar ka gida. Amma,” ya ɗan juyo yana kallon Dr. Khalid, “ba kowa bane muka bada izinin shiga wajen sa har zuwa lokacin da za mu dawo. Sai dai ni, ko Waziri.”

Dr. Khalid ya durƙusa cikin girmamawa.“To, ranka ya daɗe. Zamu kiyaye.”

Mai Martaba ya juya, zai fita. Sai ya tsaya, ya dawo da sauri, yana kallon Dr. Khalid da idanu masu tambaya.

“Doctor… kamar jiya, na ji kana cewa yana kiran wani suna Ramlah ko…?”

Dr. Khalid ya dan yi shiru na ɗan lokaci.

“Eh, ranka ya daɗe,” ya ce a hankali. “Daman jiya lokacin da ya fara farkawa da sunan yafarka ku nakuji baniba kuma haka yau ma da sunanta yafarka. yana cikin ruɗani, yana kiran wannan sunan. Na tambaye shi cikin sanyi amma bai amsa ba. Na ce ko dai a kira ta, idan tana kusa, ta ganshi, baidai cemun komai ba.”

Mai Martaba ya dan lumshe ido, ya ɗauki numfashi mai nauyi. “Ramlah….” ya maimaita da sauti mai zurfi. “Eh, ranka ya daɗe. Idan da hali, ko ta zo ta ganshi na ɗan lokaci, sai ta koma.” “Babu damuwa,” Mai Martaba ya ce cikin murya mai ƙarfi amma cike da wani abu mai ɓoye. “Za mu kira ta.”

Ya yi tsit na ɗan lokaci, sannan ya juya, yana ficewa da Waziri a bayansa.

*********

Washegari da safe na farka da ƙamshin turaren wuta mai kajiji yana yawo cikin gidanmu. Rana ta shiga ta tagar ɗakina, tana haskaka curtain ɗin har yanzu gajiya bata sakeni ba har yanzu inajin jikina a mace sosai bama danaji ance bashida lafiya jiya ko yaji sauki? zuciyata tana rawa, Nayi saurin mikewa dan an kusa a daura auren kuma zamuyi hotuna sosai da yamma kuma can gidan zasuyi walima wanka nayi sauri nashiga dan nasan yanxu momy zatazo nasan sun shishigo ma ina bacci.

Gidan gaba ɗaya ya cika da motsi ana shiga ana fita, anyi abinci kala kala kamarsu tuwo, shinkafa, jollof, da abincin zamani kala-kala. Masu girki suna ta zuzzubawa waƴanda zasuci da safe. Ko dana lika ta window an cika sosai sai hayani da aketayi.

Sauka nayi kasa bayan nayi wanka su yaya aliya duk sun shirya tace nayi hanzari ga mai makeup nan tana jirana haka akafara kwalliyar masu daukar video sunayi.

Ko da aka gama Na tsaya a gaban madubi ina kallon kaina mai makeup ta gama aikin ta, fuskar ta tayi kyau sosai kasancewa light akayimun sai da yamma xaayi mun full makeup. Nasaka lace dina green da white sannan ta dauramun dankwalin sarkar da Abba yataɓa siyamun ta gold ita nasaka, Mashaa Allah nima nasan nayi kyau sosai ga dinkin yayi cif ajiƙina sosai.kwayena sai hotuna sukeyi suna zuzutani.

Maryam ce tace “Subhanallah,” na furta gaskiya kinyi kyau sauran ma suka dinga nayi kyau nikam kawai ina murmushi.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull