Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 23

Kaddarar ramlah book 2 complete - Chapter 23

Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 23: Kaddarar ramlah book 2 complete Chapter 23. Momy ta shigo cikin ɗakin, tana murmushi amma a lokaci guda tana…

4,491 words

Momy ta shigo cikin ɗakin, tana murmushi amma a lokaci guda tana sauri “Autata,” ta ce, tana jawo hannuna muka fita muka shiga daƙin kasa ta rufo kofar. “Kin kirashi kuwa? Kin kira Asad ɗin?”

“Na kira Momy,” na ce cikin sanyi. “Amma wayarsa a kashe.”

“Okay to, ba damuwa,” ta ce tana ɗan murmushi. “Karbi wannan kazar, ki ci yanzu yana taimaka wajen ƙarfafa jiki, yana gyara mace, musamman ke da kika taba aure.”

Ta ɗora faranti a gabana, kazar nan ƴan kanana ne sai tace mun “Yanzu fa mace idan zata yi aure, sai ta kula da jikinta sosai. Mazan yanzu fa,” ta ɗan ɗaga kai tana dariya. “Ba su san mutunci ba idan mace ta zama sakara a kan gado. Ga yadda ake hada kayan hada kazar sai ki rubuta yanzu a google dinki kar na manta.”

Na ɗauki waya, zuciyata tana ɗan rawa saboda lkunya. “Momy…”

“ ke bansan shirme kunyar me zakiji dallah rubuta wannan kunyar ke kashe yaranmu ai, ki rubuta.”

Ta fara jeramun su “ATTARUHU, ALBASA, TAFARNUWA, SAIWAR MALMO, SASSAKEN BAURE, SAIWAR ZOGALE, CINNAMON, CARDAMOM, KANINFARI, TURMERIC, RAIHAN wato scent leaf GANYEN IDON ZAKARA, CITTA… duk wannan sai ki haɗa da kaji ki ci. Kazar nan tana gyara gaban macce sosai matsi karkiyi wasa daita.”

Na rufe wayar na ajiye “Momy, wannan kazar kam... zan iya cinye ta duka?”

“To me zai hana? Maza yanzu nan bakiga ƴan matan kaji baniba,” ta ce tana dariya. “Sai ki cinye yanzu, ki sha tsumin tafisu nan gaba.”

Na ɗago kai cikin mamaki. “Menene kuma tsumi Momy?” “Ai wannan na musamman ne,” ta ce tana fita tana dariya. “Zan kawo miki yanzu.” Ta dawo da wani karamin flask, ta bude, sai wani kamshi ya cika ɗakin ƙamshin kayan yaji da zuma da itatuwan da ban taɓa gani ba. “Wannan tsumin Nafisu ake kira,” ta ce tana nuna min takardar rubutu. “Ga yadda ake haɗawa CARDAMOM, SASSAKEN BAURE, CITTA, KANINFARI, KIMBA, MAZARKWAILA, RAKE, ZUMA, CINNAMON, MINANNAS, RAIHAN, NA’A NA’A, ƳAƳAN BAURE, da GARIN DABINO. Ki haɗa da ruwa kitafasasu sosai kinasha zakiga abun mamaki indai niimace.”

Na yi dariya sosai “Momy,wannan bayanin kamar likita.” “Ai ni na sha nasan mahimmacinsa auta,” ta ce tana rufe flask ɗin. “Ni dai na gaya miki, kin zama matar aure yau. Ki kula da kanki, kin ji lamarin maza sai da gyara.?”

Na ce, “To Momy,” cikin dariya, amma zuciyata tana ɗan kunya sosai.

Lokaci bai jima ba, sai muka ji an shigo falon da sauri Abba ne da wasu dattawa. Murmushin fuskar sa ya nuna farin ciki.

“Alhamdulillah!” Abba ya faɗa. “An daura auren ramlah da Asad babangida yau a ciƙin faɗar sarki akan kudin sadaki million daya.”

Na tsaya cak. Kalmar “an daura aure” ta daki kunnuwana kamar kiɗa mai sanyi. Momy ta rungume ni da murna. “Allah ya tabbatar Alhamdulilahi Allah mungode Allah yasaka albarka!” ta faɗa tana share hawayenta.

Nana hadiza

09030569336

[23/10, 1:54 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SITTIN

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Abba ya ja Momy gefe, muryarsa a hankali “Kaltume, Asad yana asibiti har yanzu. Jikinsa Sai a hankali banason kowa yaji dan sarki asirri yagayamun ansaka masa guba ne amma anyi nasarar cirewa. Sarki ya aika mota ana son Ramlah ta je ta duba shi kafin rana ta fadi.” “Subhanallah!” Momy ta ce cikin mamaki. “Har yanzu bai warke ba? Allah yabashi lafiya” Abba ya ce. “Da yake suna hana kowa ganinsa, sai dai ni ko Waziri ko su iyayen nasa. Amma Sarki da kansa yace taje ta ganshi danAllah ki shiryata yanzun nan tatfi ga driver can ta bayan gidan yazo sai taje ta dawo ko?.” “Yanzu ma kuwa yaya malam ai bansaniba wallahi mundaiji jiya bayajin dadi bamu dauka abun ya girma haka ba bari naje”. “ To madallah bari naje ni akwai abunda zanyi yanzu mutane sunata jirana.

Momy ta dawo wurina da sauri, fuskarta ta canza zuwa damuwa. “Auta,” ta ce cikin muryar da ta cike da tausayi. “Ki tashi yanzu, ki wanke makeup ɗin nan tunda ai kunga hotunan Ki saka hijab ko mayafi. Ashe Asad ɗin bai warke ba. Ki je ki duba shi.”

Kunya ta kamani. Na yi shiru ina kallonta, na kasa magana. “Momy, amma… yanzu fa,” na ce cikin sanyi. “Ni kadai…” “Eh mana, ke dawa kinason mutane su dirar masa baki ne wai me isa bakida wayo ne. Shi yasa ke kike da hakki fiye da kowa. Ki tafi yanzu ki ganshi. Kada ki bari nakara shigowa wallahi ranki xai ɓaci ga sadakinki nan 1m abba yabani a hannuna zan baki in zaki tafi.”

Nace to, na nufi toilet. Na cire duk foundation da lipstick, na wanke fuska da ruwa mai sanyi. Na fito, na ɗauki mayafina mai launin fari, na lullube jikina gaba ɗaya. A ƙasan zuciyata, bugun zuciyata na ƙaruwa. Ban san dalili ba, amma ina jin wani iri.

Na fito zuwa bayan gida, inda aka ajiye mota hadaddiya ni bantaɓa ganin irinta ba jet black limousine ce, mai tambarin gidan sarauta.

Na taɓa kofarta cikin jin nauyi “Bismillah,” na furta, na shiga.

Direban ya ja motar cikin nutsuwa. Gabadaya jiƙina bayajin dadi tsoro ma nakeji wai yau nice matar attajirin nan yaa Allahu nafaɗa cikin raina.

Motar ta shige cikin titin manyan gidaje, fitilun gari suna a kunne. Na kalli bayan gilashi, ganin yadda rana ke faduwa a hankali. “Ashe shiyasa bana samunsa awaya nafaɗa.” Direban ya kalle ni ta madubi. “Ranki yadade, mun kusa isa,” ya faɗa cikin ladabi.

“To, nagode,” na ce ina share kuncina.

Da muka isa Royal Crest Hospital, jami’an tsaro na fadar suka buɗe ƙofa. Wani dogo cikin uniform ya durƙusa. “Welcome, Your Highness.” Na fito cikin nutsuwa, na nufi cikin ginin da yake haske kamar lu’u-lu’u. Hasken fitilun ya daki mayafina, ya sa fuskar ta yi haske sosai. Likitoci suna tsaye suna jiran umarni. “Room 1A,” wani nurse ya ce, yana nuna hanyar da zan bi.

Da kyar na iya murɗa ƙofar dakin. Hannuna yana rawa, zuciyata na dukan da ba na iya misaltawa. Na yi sallama cikin muryar da ta bata fita sosai, sannan na tura ƙofar gaba ɗaya. Sai iska mai sanyi ta daki fuskata, tana ɗauke da ƙamshin hospital perfume wanda bantaɓa gani ba.

Kamar mai jirana naga Ya zubawa ƙofar idanu, idanunsa suka haɗu da nawa. Amma ni, sai na sunkuyar da kaina sumarsa ta kwanta gashin baƙinsa da ɗan gemun sa sunyi fakyau kana gani basai angayamaka ba yanajin jiki sosai. Dakyar ina sunkuyar da kaina na karasa ciƙin daƙin na dan tsaya gefen wata kujera nace “Ina wuni…” na faɗa cikin muryar da take rawa.

Ya kalle ni kawai, yana ajiyar zuciya mai nauyi. Fuskarsa cike da haske da rauni a lokaci guda, Ya zubamun idanuwansa dake gigitani idan na kalle su.

“Yaya jikin?” na ƙara tambaya cikin sanyi.

Babu amsa. Sai dai kawai numfashinsa yana fitowa a hankali, yana sauka kamar wanda yake ƙoƙarin tuna yadda ake magana.

“Allah ya ba da lafiya,” na ƙara faɗi, ina matsawa gefe, na ji kunya ta lullube ni gaba ɗaya.

Sai na ga ya ɗan miƙo min hannunsa ba da ƙarfi ba, kamar wanda yake son ya faɗi abu amma maganar ta makale a makogwaro.

“Menene, zaa baka?” na tambaye shi cikin murya mai taushi.

Ya ɗan ɗaga kai, idanunsa suka kama nawa, sannan da wata murya mai sanyi, amma cike da umarni da taushi, ya ce “Come.”

Na tsaya cak. Wannan kalmar “come” ɗin ta faɗo cikin kunnuwana da dan mamaki. Hannuna ya fara rawa. Na kalle shi jikinsa har yanzu da rauni, amma idanunsa suna magana da wani abu da ba zan iya musawa ba.

Da kyar na ɗaga ƙafata na matsa kadan. Sai ya sake miko hannunsa, yatsunsa suna ɗan jijjiga kamar yana roƙona da ido.

Na matsa gaba ɗan kadan, zuciyata na rawa kamar ana busa ganguna a cikinta.

Kafin na iya tambayar me yake so, sai na ji hannunsa ya cafko nawa. Ƙafafuwana suka tsaya, idona ya faɗa cikin nasa. A cikin dakika ɗaya, sai na ji yana ja ni da ƙarfi jikina ya bugu da nasa.

“wayyo” na furta cikin tsoro Rungumarsa ta zo ba tare da niyya ba, amma ta shige ni gaba ɗaya. Hannayensa suka rufe ni, ƙirjinsa ya daki bayana, zuciyarsa tana bugawa da sauri kamar ta wanda ya yi tsere. Wani irin zafi ya ratsani ko shakkah nasan na zazzabine amma kuma tsoro ya shige ni. Wani kalar numfashi da bantaɓaji naji yafara fitarwa a hankali Numfashinsa yana fita cikin sauri. Jikinsa ya fara rawa kamar wutar da take neman ƙarewa. A cikin kunnuwana sai na ji yana ƙoƙarin furta suna na “Ram… Ramlah…” amma muryarsa ta kasa fitowa. Sai naga jikinsa yafara wata kalar jijjiga sosai sai hakoransa suka shiga haɗewa idonsa kuma ya canza gaba daya.

“Doctor! Doctor!” na kira da ƙarfi, na fizge jikina daga nashi, zuciyata tana wani irin tsalle.

Kafin in kai bakin ƙofa, sai likitoci suka shigo da gudu. “What happened?” ɗaya daga cikinsu ya tambaya.

“He’s shaking! Jijjiga yake!” na amsa ina kuka.

Suka taru a kansa, suka fara gwaje-gwaje da allura. Na tsaya a gefe, hannuna yana rufe bakina, hawaye suna fita. “Oh Allah…” na furta, numfashina yana sarkewa. “Ya Allah ka kiyaye shi.” Suka yi masa allura, suka duba numfashinsa, suka kira sunan sa amma bai iya buɗe ido ba. Sai kawai na ji yana ƙoƙarin furta kalma ɗaya amma ba ta fito ba. “Ramlah…” Sai jikinsa ya mutu. numfashinsa ya daidaita kadan. Likitoci suka dubeni, suka ce cikin natsuwa “He’s fine now. He’s just weak. Please, calm down.” Na girgiza kai, hawaye suna ci gaba da zuba.

“But he tried to talk to me…”

“He will, soon,” Dr. Khalid ya ce cikin tausasawa. “But you need to rest too, Princess. You’re pale.”

Na fice daga dakin cikin rudani.amma zuciyata cike da ƙamshin sa ƙamshin da ba zan taɓa mantawa da shi ba.

A cikin mota, direban ya buɗe mini ƙofa cikin girmamawa. “Your Highness…”

“Drive…” na faɗa cikin murya mai sanyi.

Ina tafiya, hawaye suna gangarowa ba tare da iko ba. Da muka isa gida, Sama nayi saurin hayewa ina faman kuka Hajja Kaltume tayi saurin bina tana ta tarbata. Ta rike ni kafin na fadi. “Ramlah, yaya jikin nasa?”

“Momy…” na ce cikin murya mai rawa. “Jijjiga yake… hakoransa suna haɗuwa. Yayi kuka, Momy. Babba dashi.” Ta rungume ni tana rarrashi, tana shafe min hawaye da tafin hannunta. “Kidaina kuka, autata. Zai samu lafiya kin ji?.”

Na gyada kai, amma hawaye suka sake zubo. Na ɗaga kai sama ina kallon hasken rana da ke fita daga tagar gidanmu.

********

A can nesa, Momy tace na daina nuna damuwa kada mutane su zata auren dole ake mun na shirya ga su gimbiya nan zuwa daukarmu zuwa walima. Ina cikin ɗaki, muna shirin walima. Kayan da aka baza a kan gado sun cika ɗakin da ƙamshi turaren wuta, Bilkisu na gyarawa a gefe, ni kuma ina kallon kaina a madubi ina tunanin ko yaya jiƙinsa gashi wayarsa bata gurinsa. Sai kawai kofar ɗakin ta buɗe da karfi, Mom ta shigo daidai lokacin da Mai kwalliya tagama dauramun dankwali suna cikin saka mun Alkyabba.

Na ɗan murmusa, na gaisheta cikin ladabi, amma tana kallona kamar wacce taga kashi

“Ke dai ba haifaffiya bace ba, Ramlah. In ci fitsarinki, in ci kashinki! Shine yanzu zaki gujeni da kika dangwalo arziki? To aure ne fa, ki zauna mu gani. Sha sha sha kawai! Mijin ma da kike takama da shi, mijin wata ne. Wallahi Asad ba zai taɓa kaunarki haka ba dan kije kiji tahirin soyayyarsa da Ayshatu mace daya tamkar da dubu.!”

Kalmominta suka daki zuciyata tamkar dutsen da aka jefa cikin ruwan kwanciyar rai. Na tsaya na kalleta. Da nutsuwa, cikin murya mai sanyi amma cike da zafi, na ce mata “To Mom, nagode. Ba sai kin gaya min ba.”

Na juya, na fita daga ɗakin tana ta cigaba da maganganu Amma raina bai baci. Amma ban waiwaya ba.

Nana hadiza

09030569336

[24/10, 10:29 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SITTIN DA DAYA

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

Duk da cewa na dade ina mafarkin samun aure cikin farin ciki, ban taɓa tunanin rayuwa za ta kawo min irin wannan rana ba da zan tsaya a gaban manyan mutane, sarakuna, da gimbiya-gimbiya, Masu kudi wanda duniya Takeji dasu Matan gomnoni da minister duk duk sunzo,cikin wani haske da kyan gani da ya wuce misali. Na zama matar Yarima Asad, ɗan sarki mai daraja da ƙudi sosai wanda murya tasa kadai ke saka zuciyata dokawa kamar bugun tambari.

Walimar an yi ta ne a cikin fadar sarki, kuma komai ya kasance cikin tsari da kyan gani kamar ana kallo a fina-finan Indiya. Fitilu sun haskaka kowane kusurwa, ƙanshin turarenwuta da na flower petals ya gauraye iskar gurin har sai da naji kamar ina a cikin mafarki. Kowa da kowa ya shirya cikin Kaya masu tsada da kyau daga iyalan fada har zuwa bak’i na waje. Na godewa Allah da irin shigar da nayi Nayi kyau sosai.

A zuciyata, nake ta addu’a, “Ya Allah, ka bani nutsuwa dan wallahi Na gigice sosai da irin tsarin walimar haduwa iya haduwa wani irin taro da muke gani na a film din larabawa .”

Daga nesa na hangi hajja tana ta gaisawa da manyan baki, cikin fararen kaya masu ɗaukar ido. Fuskar ta cike da fara’a tanata gaisawa da mutane sai kuma nafara jin tsoron kada ban kai matakin gidan da aka saka ni ba.

Ana cikin haka sai Hajja, mahaifiyar sarki, ta taso da murmushi a fuskarta, tana cewa “Ramlah, zo nan yarinya. Ki tsaya kusa da ni, kowa yaga yadda amaryarmu take da nutsuwa da kunya.”

Na ƙaraso da ɗan jin nauyin kaina, na durƙusa kadan na gaishe ta, sannan na zauna a gefenta. Mutane suka rika taya ni murna, wasu suna rera yabo, wasu kuma suna aiko min da kyaututtuka kayan ado, tsabar kuɗi, zoben azurfa, turaruka, da zanen shadda masu launin da ban saba gani ba.

Amma a tsakanin murmushin da mutane ke yi, naga wata tana mun wani irin kallo da harara wanda ya dusar min da farin cikina a hankali. Na ɗaga kai, sai idona ya sauka kan wata mace kyakkyawa, doguwa, wacce idanunta ke cike da gaggawa da hassada Gimbiya Maryam.

Tana tsaye kamar wacce ke jiran damar nuna wani abu. Lokaci ɗaya sai ta juya ta yi tsaki, ta murmusa cikin raini, sannan ta ce cikin ƙasa da murya amma duk da haka najita “Wai an auro musu yar talakawa a cikin gidan sarauta? Lallai duniya tana canzawa ina Yarima ina yarimyar nan talakawa bafa sarauta kaɗai yake da’ita ba harda arzuki.”

Kalmar ta ta shiga kunne na kamar in saka kuka. Hannuna ya ɗan yi sanyi, amma na daure da murmushi, na ce a zuciyata, “Kai, Ramlah, kar ki nuna damuwa. Kaddarar ki ce, kuma Allah yana ji yana kuma gani.”

Kafin na iya maida hankali, sai na ji Hajja ta daga murya cikin ɓacin rai tace “Maryam! Kin san ba daidai bane irin wannan magana a wurin jama’a. Ki koyi da’a, domin babu talaka a wajen da Allah ya ɗaukaka, Canza lafazinki zai iya kaiki ga ɓacin rai ki kama girmanki kamin ranki yaɓaci. Wanda Allah ya zaba shi ne, kuma wannan yarinya tana da hankali da nutsuwa da tarbiya ba kudi mukeso ba Kar ki kuskura ki sake magana irin haka.”

Gimbiya Maryam ta duƙar da kai cikin kunyata, sai dai idanunta suna cike da bacin rai. Ni kuma na ji hawaye suna shirin tsiyaya, amma sai na yi saurin share su da hannuna na.

Bayan wannan walimar, aka raba abinci iri-iri, an yi rawa, an yi dariya, an yi addu’a. Amma ni a zuciyata, ba farin ciki kaɗai nake ji ba akwai fargaba, akwai sabuwar rayuwa da ban san yadda zata kasance ba.

Lokacin da rana ta fadi, fitilun fadar suka ƙara haskaka, kuma walimar ta ɗauki lokaci har zuwa ƙarfe 9 na dare. Na fara jin gajiya sosai. Duk wanda ya ganni yana cewa “ Amarya akwai kunya ta dace da gidan sarauta, akwai kamala da nutsuwa.”

A ƙarshe, bayan an watse, muka dawo gida tare da Momy da sauran ‘yan uwa. Da muka shiga gida, Momy ta kalle ni cikin taushi, ta ce “Ramlah, kirashi kiji ya jikinsa, kin san damuwa wani abu ne da ake nuna ga masoyi.” Na ɗan murmusa, na ce “To Momy.”

Na ɗauki wayata, na kira Yarima Asad, amma sai kawai na ji number not reachable. Na kalli Momy cikin mamaki, na ce “Bata shiga ba, Momy.” Ta dan kalli gefe, ta ce cikin nutsuwa “Ko ba numbarsa bace? Amma ai shi ne yakirani rannan da wannan lambar. To, dan Allah Ramlah, Anjima ki sake kiransa. Kulawa wani abu ne da yake gina soyayya. Wanda ya damu da kai, kaima kayi iya kokarinka wajen nuna damuwarka Ni wallahi sai yanzu nakara godiyawa Allah domin kinyi dacen dangin miji kiga yadda surukarki ke haba haba dake wallahi Alhamdulilah zamuce.” Na gyada kai cikin ladabi, na ce “In shaa Allah, Momy, zankirashi daga baya.” Da haka ta fita daga ɗakin, ta barni cikin tunani mai nauyi. Na zauna a gefen gadona, na dafa kaina da hannuwana biyu, na lumshe idanu. Na ji hawaye na taruwa, na ce cikin zuciyata “Ya Allah, ka taimakeni abisa rauni na. Ka sanya wannan ahali su kaunace ni, kar su rainani saboda asalina. Kai ka fi kowa sanin zuciyata.”

Iskar dakin ta motsa, sai na ji nutsuwa ta fara dawowa a hankali. A cikin wannan nutsuwa, na ji kamar muryar Yaya usman a cikin zuciyata tana cewa “Ramlah, ki kasance mai tawali’u da karfin zuciya. Ni a kaina ina alfahari dake.” Sai da na murmusa, na kwanta inaa addua

********

Dakin asibitin ya cika da sanyi ga wani dadɗadan kamshi mai dadi, fitilun da ke a saman bangon suna ta haskawa da launin fari. A gefe, injin oxygen yana yin piip… piip… cikin natsuwa. A hankali Yarima Asad ya motsa jikinsa, numfashinsa yana fita da wahala, yana ambaton sunan Allah cikin murya mai rauni.

Hannunsa ya kai kan kansa, yana jin wani irin ciwo mai nauyi da ke bugawa daga cikin ƙwaƙwalwarsa kamar ana danna masa wuta.

Ya lumshe ido da ƙyar, yana ƙoƙarin tuna inda yake. Sannan muryar da ya saba ji cikin natsuwa da ladabi ta doki kunnensa “Rankayadede, sannu. Kan naka ne yake ciwo ne?” Ya bude idanunsa a hankali, ya hango Dr. Khalid tsaye a gefensa, cikin farin rigar likita, hannunsa ɗauke da clipboard.

Yarima Asad ya ɗan ɗaga kai, yana jin raunin da ke tafiya ta bayan wuyansa. “Yes…” ya ce a hankali, yana ɗan jan numfashi. “But… ina Ramlah?”

Murmushi mai taushi ya bayyana a fuskar Dr. Khalid, wanda ya kalli sa cikin nutsuwa. “Ai ranka ya daɗe, ta zo ta ganka tun safe ta kuma tafi tun lokacin. Ni nekawai na tsaya domin in tabbatar da farkawarka.” Sai ya ɗan yi shiru, ya zura ido cikin takardunsa. “Amma kafin haka, akwai wasu tambayoyi da zanyi maka.” Asad ya juya ido gefe, yana dafe goshinsa. “Likita… inada wani issue. For the poison case, naji kamar na warke. Amma duk lokacin da na yunkura… ko lokacin da nake jin sha’awa… jikina yana rikicewa. Numfashina yana tsaya min. Har yau dazu, hakan ne ya same ni.”

Dr. Khalid ya ɗan tsaya shiru, yana kallon sa kamar yana tantance abinda zai faɗa.

Ya sauke numfashi, ya ɗan matsa kusa da gadon, yana magana cikin muryar da ta cika da natsuwa da hankali.

“Ranka yadade, abin da kake ji ba , ba zazzabi kawai bane. Mun gano cewa gubar da aka zuba maka tana ɗauke da wani sinadari mai haɗari sosaiana kiransa neuro-vasculine toxin. Ba wai yana kashe mutum kai tsaye ba, amma yana lalata jijiyoyin da ke haɗa kwakwalwa da zuciya. Wannan shi ne yasa kake fama da ciwon kai, wahalar numfashi, da rashin iya daidaita jikinka lokacin da bugun zuciyarka ya tashi.”

Ya ɗan ɗaga hannu sama yana nuna allurar da ke haɗe da jikin Asad. “Mun cire mafi yawanta daga jikin ka ta hanyar detox da dialysis, amma akwai ragowa. Wani ɓangare daga cikin sinadarin nan yana ajiye kansa a jijiyoyin da ke da alaƙa da zuciya da sha’awa. Idan hankalinka ya motsa ko jikinka ya fara bugawa da ƙarfi, sai wannan sinadari ya fara aiki, yana tsayar da numfashi na ɗan lokaci. Wannan ne yasa kake jin kamar zaka mutu duk lokacin da hakan ya faru.”

Yarima Asad ya kalli Dr. Khalid cikin mamaki da damuwa.

“To, likita… me hakan ke nufi? Zai iya zama barazana ne?” Dr. Khalid, yana kallon sa da tausayawa. “Zai iya, ranka ya daɗe. Amma idan muka kula da kai sosai ba. Za mu cigaba da cire dukkan sinadarin daga jikin ka cikin makonni. Abin da kake buƙata yanzu shine nutsuwa, da gujewa duk wani abu da zai tayar maka da bugun zuciya.”

Ya ɗan yi murmushi cikin ladabi, yana ƙara da cewa “Ka kwantar da hankalinka. Inshaa Allahu zaka warke. Amma ina so ka sani wannan gubar an tsara ta ne da niyyar kashe ka a hankali, ba a ɗan lokaci ba. Wannan ba kuskure bane. Wannan abu, ranka ya daɗe… makirci ne.”

Kalaman Dr. Khalid suka tsaya a kunnesa. Yarima Asad ya runtse idanunsa, ya dafa kansa, zuciyarsa tana dokawa cikin hargitsi. ya sauke numfashi.

Dr. Khalid ya tattara takardunsa, ya ce da muryar tausayi “Rest well, ranka ya daɗe. Allah Ya sa wannan kaddarar ta zama alheri gareka.”

Nana hadiza

09030569336

[24/10, 10:31 pm] Nd: ƘADDARAR RAMLAH

BOOK 2

SHAFI NA SITTIN DA BIYU

********

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

ArewaPEN @nanadiso10

https://www.arewapen.com/book?id=6883f9e574b8ea03fba06ae5

*********

*****

Cikin ndare, fitilun fadar da ke gefen shashen Waziri sun haska sosai. Hasken da ke fitowa daga bango yana bugawa kan gilashin tagogi, yana haifar da inuwa.

Gimbiya Maryam ce ke tsaye a bakin ƙofar, cikin doguwar rigar royal purple, da ɗankwalin da aka nannade a kansa da duwatsu masu sheƙi. Fuskar ta cika da tsantsar bacin rai, idanunta sun nuna damuwa da fushi lokaci guda.

Babu wanda ya san da zuwanta, saboda shigarta ta kasance kamar iska shiru, sirri, kuma cike da nufin ɓoye abu.

Waziri, wanda shima ke zaune a cikin ɗakin da ke cike da ƙamshin turaren itace da rubutattun takardu, ya ɗago kai lokacin da ya hangota.

“Lamari ya kwabe, Gimbiya,” ya faɗa cikin sirri, yana haɗa hannuwansa.

“Don Asad ya samu lafiya.”

Gimbiya Maryam ta juyo da sauri, fuskarta a haɗe kamar wacce aka watsa wa gishiri a ido. “Shi ne yasa kake kirana yanzu?!” ta furta cikin bacin rai. “Hankalina ya tashi sosai, Waziri. Ance Sarki ya tsananta bincike a fada, ko? An kori duk masu girki da masu hidima. Koda ‘yan tsaro ma an sake sabbi!”

Waziri ya yi dariya irin dariyar mutumin da yake da tabbacin abu. “Gimbiya, ai hakan ba komai bane. Kowa zasu tambaya, amma har yanzu ba su samu wanda ya saka gubar ba. Camera ta shashensa an duba babu abin da aka gani. Ana ci gaba da bincike, amma babu wata hujja.”

Ta juya da sauri tana dubansa da idanunta “Waziri, hankalina bai kwanta ba. Abin da ya bani mamaki shine yadda Asad ya farfaɗo! Bokon nan da naje wurinsa yace gabansa bazai taɓa aiki ba har abada! To me yasa yanzu ya samu lafiya gashi har da aure?”

Waziri ya yi dariya sosai, yana ɗan jingina da kujera yana sosa gemunsa. “Gimbiya Maryam, baki yarda da ni ba kenan. Nagayamiki, bansaka yara ba ni da kaina nayi. Wallahi ni na saka. Bayan mahaifiyarsa ta gama girki, sai na shiga da sunan yimata yamai jiki. Sai na tarar suna kammala abinci. Nayi amfani da wannan dama, na bude tukunyar, na saka sinadarin nan da kaina. Na tabbata, Gimbiya, asirinmu ba zai taɓa tonuwa ba.”

Maryam ta ɗan ja numfashi mai nauyi, “ kaga har hankalina ya kwamta waziri da ko bacci banyi ba Waziri. Wannan yarinyar da Asad ya aura wacce suke cewa Ramlah tayaya zamu raba su? Wallahi bana son ganin Yarima yana cikin farin ciki! Abin da nake so, labarin mutuwarsa ne, ba murmushinsa ba.”

Waziri ya ɗan juya mata ido, yana nuna alamun gargaɗi. “Kinga, ke matsar da hankalinki da maganar yar mutane. Burinmu ɗaya ne Asad ya mutu, ba wai mu kashe yarinyar ba. Idan kika fara da ita, asirinmu zai iya ballewa.”

Ya ɗan matsa kusa da ita yana magana a hankali, kamar yana rada “Yanzu dai Sarki ya fita shagaltar da kansa da harkar kasuwanci da manyan baki. Mu bari ya ɗan kwantar da hankali. Idan lokaci ya yi, sai mu ɗora sabon shirin. Amma yanzu ki ɓoye fushinki, ki zama kamar kina cikin farin ciki kada kisa damuwa.”

Gimbiya Maryam ta lumshe ido, “Idan Asad ya tsira daga wannan dole naga yakasance mai cike da tsanani kasan kuwa har kissa nayiwa sarki akan kar afitar dashi waje bakaga ba ayi maganar fiddashi ba ai kissata ce. ”

Waziri ya murmusa cikin gamsuwa, yana ɗan gyara rawaninsa. “Na aminta da ke, Gimbiya. Hakan zaisa gubar dakara bin jiƙinsa yanzu ki koma kada wani ya ganki.”

Ta jinjina kai, Ta fita da sauri, tana jingina da bango yayin da idanunta suka cika da duhu da ƙiyayya.

Waziri ya bita da ido, yana murmushi mai cike da mugunta “Wannan ita ce mace mai zuciya irin ta sarauta ta iya yin komai domin ta cimma burinta…”

**********

Tun daga lokacin da na buɗe ido da safe, nake jin hayaniya daga waje.yau ne wunin hajja kaltume kuma yau ne za’a kaini gidana

Muryar su Maryam da Nasiba sai dariya suke, suna ihun, kowannen su na bada labarai kala kala “Amarya har kin tashi yau za a kaiki gidanki dai yau za’a sha soyayya.” bilkisu dake gefe ce tace ni angon naki banga yana kira ba.”

Na tabe baki ina murmushi, ban ce komai ba.

Na nufi bayi nayi wanka cikin Sauri. saboda jikin nawa ma kamar baya da natsuwa yau tunda nasha wannan tsumin da zan kwanta sai naji hankali yana wani ɗan tashi tashi abunda rabon danaji tun bashari yanada rai.

Zuciyata cike take da tsoro da tambayoyi yau zan bar gidanmu.

Na saka super embellished lace, domin yau baza a yi mun full makeup lipstick ne kawai abakina sai kwalli da hoda dana saka.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull